Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kai tsaye ta nufi ɗakin Ummin.
Ɗan knocking ɗin ƙofar tayi.
Daga ciki Ummi ta bada go ahead ɗin shigowa.
Hakan yasa ahankali ta tura ƙofar ciki, ta shiga bakinta ɗauke da sallama.
A zaune Ummin take akan gado, Raleeya kuwa fitowarta kenan daga cikin bathroom ɗin Ummin, da alama wanke mata tayi.
Ganin Zaleeha yasa Ummi sakin murmushi. Ƙarasowa cikin ɗakin tayi, tare da ɗan durƙusawa agaban Ummi'n, cikin girmamawa tace. " Ummi dama inaso ne naje saloon, shine nace bana tambayeki idan kin barni sai naje." Murmushi Ummi tayi cikin kulawa tace. "Haba Zaleeha idan zakije saloon ɗin kuma sai kin nemi izinina, ai idan dai mijinki ya yardan miki kije kawai." Ƙasa ta ɗanyin da kanta, cikin wasa da ƴan yatsun hannunta tace.
"Shine yace duk inda zanje ina tambayanki, idan kinbarni sai naje." Murmushi Ummi tayi, tare da jinjina kanta, fuskarta ɗauke da zallan fara'a tace.
"Na amince miki, kije saloon ɗinki, Allah ya kiyaye hanya, akwai Sule driver, nasan zai kaiki ko kinaso kiyi driving da kanki?." Raleeya ce tayi carab ta cabke maganan cikin sauri tace.
"Ummi dan Allah nima zanje, dama two days ban yi saloon ba, kinga idan yaso bama sai Sule driver ya kaimu ba, ita zatayi driving ɗinmu ko?." tafaɗa tana kallon Zaleeha'n.
Kai Zaleeha ta jinjina mata tana murmushi, dan taji daɗin hakan, saboda itama bawai tanason fita ita ɗayan bane, dan ance wata tafiyar bibbiyu tafi dadi. Murmushi Ummi tayi tare da cewa.
"Kai Raleeya son yawo, to shikenan ai saiki tambayi mijinki idan ya barki ƙofa abude take." Cikin zumuɗi Raleeya tace.
"Ai namasan zai barni, bari naje na ƙirashi a waya."
taƙare maganan tana me fita waje. Zaleeha na ƙoƙarin miƙewa, Ummi ta zage zip ɗin jakan dake aje gefenta, kuɗi ta ciro wanda aƙalla zasu kai 10k miƙawa Zaleehan tayi, murya atausashe tace. "To gawannan sai ki biya saloon ɗin dashi." Idanu Zaleehan taɗan zaro tare da cewa. "Ummi ai kuɗin sunyi yawa."
Murmushi Ummi tayi, tare da girgiza mata kai, cike da ƙauna tace. "Idan Raleeya ne na bata, bazata ce sunyi yawa ba, saboda haka kema banaso kisake faɗin haka, ki amsa maza ku tafi sai kundawo, sannan kuyi driving a hankali." Cikin mutuntawa tasa hannu ta amshi, kudin tare da yiwa Ummin godiya, sannan ta fice daga cikin ɗakin, taji daɗin kuɗin da Ummin ta bata, duk da cewa ma tana da kuɗi, amma duka basu wuce 12k ba, dan koda Saifuddeen ma yace da ita, akwai kuɗi a drawer ɗinsa, idan tana da buƙata ta ɗauka, sam bata ɗauka ba. Tana zama afalo kuwa Raleeya ta fito itama cikin shirinta na doguwar riga, saidai nata me kalan ja ne, dan ta tambayi Ahmad ya barta, dama shi bame hana fita bane.
Atare suka fito compound ɗin gidan, zuƙeƙiyar motar Saifuddeen ƙiran mercedess benz Zaleehan tasawa key ɗin data ɗauko a ɗakinshi ta buɗe musu, Zaleehan ne ke driving, Raleeya kuwa na gefen me zaman banza, me gadi ne ya wangale musu gate ɗin gidan suka fice. Kaitsaye babban shagon saloon ɗin da Zaleehan ta saba zuwa suka nufa, suna zuwa kuwa akayi musu saloon ɗin, harma da wankin ƙafa akayiwa Zaleeha.
Basu wani ɗau lokaci ashagon ba, kwata kwata basu wuce 1hour and 30minute ba, aka kammala musu komai.

Koda suka dawo gida kuwa, lokacin har anyi sallan azahar, sallah kawai sukayi, suka wuce kitchine, sosai Zaleeha ta baje basiranta wajen shiryawa su Saifuddeen ɗin abincin tarba me rai da lafiya.
Basu gama abincin ba kuwa har tsawon awa 2 harma da wasu mintuna. Koda suka kammala agajiye suke hakan yasa kowacce ta wuce ɗaki taɗan kwanta, Zaleeha kuwa koda aka ƙira sallan la'asar, tashi tayi ta ɗauro alwala, tana idarwa kuwa ta sake komawa ta kwanta. Da misalin ƙarfe biyar da rabi kuwa ta kuma faɗawa bathroom, wanka tayi me rai da lafiya. Tana fitowa ta shafe jikinta da mai haɗi da turaruka masu azababben ƙamshi me kama zuciya,
zama tayi agaban mirror tare da tsantsarawa fuskarta kwalliya me kyau, duk da bata cika meckup ɗin akan fuskarta ba, amma tayi kyau sosai, drawern ta ta buɗe, inda ta zaro wani jan yadi na mata me masifar kyau da kuma tsada, dan aƙalla kuɗinsa yakai kusan 30k, ɗinkin riga da sket pieces akayiwa yadin, wanda aka ƙawata gaban rigan da black ɗin stones, sosai kayan suka zauna mata ajiki, sun kuwa fito da zallan kyawun surarta, dogon gashinta ta tubke, kana ta ɗaureshi da ribbom me golding colour, saboda akwai ratsin golding ajikin kayan nata. Wani irin haɗaɗɗen material saree me kalan golding ta ɗan yane jikinta dashi, kasancewar yana da shara shara sosai hakan yasa ko kaɗan bai ɓoye ado da kwalliyan nata ba, saima ƙarawa shigar tata kyau da yayi, dan tafito kaman sarauniya.

Ɓangaren su Saifuddeen kuwa ƙarfe 5:40 pm jirginsu ya sauƙa cikin Gombe International Aiport,
Ahmad da kuma Ishaq sune waƴanda sukaje tarosu, ƙwarai sun ji daɗin ganin yanda jikin Saifuddeen yayi kyau, suna shiga mota kuwa suka kamo hanyan gida. Acan gidan nasu kuwa, tuni sashin Ummi ya karɓi baƙoncin su Adda Rahama, harma dasu Wareesu, Zakariyya ma yazo suna nan tare da Hayatuddeen da kuma Khamis.

Horn ɗin motarsu da Zaleeha taji alaman cewa sun iso, yasa ta cikin sauri ta ƙarasa jikin windown ɗakin nata, ɗan yaye labule tayi waiko zata hangosu, amma gaba ɗaya shuke shuken dake wajen sun hanata ganinsu, hakan yasa ta koma cikin nutsuwa ta cigaba da kimtsa kanta. Saifuddeen kuwa, sashin Ummi suka wuce, baƙaramin farinciki Ummi tayi ba da ganinsa, musamman ma yanda taga jikin nasa ya miƙe ya samu lafiya, yana zaune abunsa, yasake kyau da burgewa, da'alama bashi da wani abun dake damunsa. Shima yaji daɗin ganin Ummin nasa sosai. Gasu Adda Rahama da farincikinsu ya kasa ɓoyuwa.

Zaleeha wanda ta fito daga sashinta, ahankali take tafiya tamkar wata tauraruwa, tayi kyau matuƙa, ƙamshi ne kawai ke tashi ajikinta, kaman wanda akayiwa ɓarin turare.
Tun isowarta kusa da sashin Ummin take jiyo surutan su Raleeya da kuma nasu Ishaq, idanunta taɗan lumshe sannan ta murɗa handle ɗin ƙofar, cikin ƴar siririyar muryarta tayi sallama anutse ta shigo cikin ɗakin, jin daddaɗan muryarta ya sashi juyowa, sauƙe idanunsa da yayi akan kyakkyawar fuskarta yasa shi ɗan lumshe idanunsa, zuciyarsa ce ta amsa saboda yanda yaga tayi kyau sosai. Wani irin lallausan murmushi ya sakar mata, tare da ɗan sake lumshe tsumamun idanunsa. Itama idanun ta lumshe dan ganinsa, yasa taji wani irin sanyi acikin ranta, ƙarasowa cikin falon tayi, kaitsaye wajen Ameenah ta nufa, fuskarta ɗauke da murmushi tace.
"Barka da dawowa Ummun Adeel ya hanya?".
Murmushi Ameena tayi tana meƙarewa Zaleehan kallon dan ko ita kanta, tasha jinin jikinta da kyawun Zaleehan. Cikin sakin fuska tace. "Yauwa Ammin Adeel, sannu da gida, hanya kam munshata saidai gajiyan zama da kuma ciwon jiki, shima nasan asannu zai watse." Murmushin Zaleehan tayi tare da sanya hannu ta ɗauki Adeel da tun shigowarta yake ta wuntsil wuntsil da hannunsa, yanaso yazo wajenta. Rungumeshi tayi tanayi masa wasa, ɗan juyowa tayi inda Saifuddeen ɗin ke zaune taɗan saci kallonsa, idanunsune suka gauraye acikin na juna dan dama shidinma kallonta yake, saurin lumshe idanunta tayi, asanyaye cikin daddaɗan muryanta tace.
"Sannu da dawowa ya jiki?."
Shiɗinma idanunsa ya lumshe saboda yanda yaji zazzaƙan muryarta ta ƙara daɗi, ga kuma ƙamshinta da gaba ɗaya ya cika masa hanci. Kansa ya jinjina mata alaman lafiya, tare da binta da wani irin fitinannen kallo, mai ɗauke da zallan kewa da kuma ƙauna.
Zama tayi agefen Zakariyya da kuma Hayatuddeen, sama sama take ɗan satan kallonsa, dan baƙaramin kyau taga ya ƙara ba, shiɗin ma dai satan kallonta yakeyi, dan tayi masa kyau sosai. Basu wani jima afalon Ummin ba, aka soma ƙiran sallan magriba. Saida ya koma part ɗinsa yaɗan watsa ruwa sannan ya wuce masallaci, Zaleeha kam kasancewar tana da alwala anan part ɗin Ummi tayi nata sallan ita da Raleeya, dan Ameena ma tatafi part ɗinta saboda tanaso taɗan watsawa jikinta ruwa.

Basu dawo daga masallacin ba saida akayi sallan Isha, atare dukansu dasu Ishaq suka dawo daga masallaci, nan falon Ummi suka baje, Zaleeha da kanta ta jere musu gaba ɗaya abincin da ta girka musu kala, da kuma drinks.
Ita da kanta tayi seving ɗinsu, duk motsin da zatayi kuwa akan idanunsa, dan baya ko ƙaunar ɗauke idanunsa akanta. Atare suka zauna dukansu sukaci abincin, hira sukeyi sosai, saidai duk acikin hiran nasu, Saifuddeen da body language yake magana, kasancewar Zaleeha na wajen.
Suna kammala cin bincin, Zaleeha ne ta tattare wajen, ɗaukan Adeel tayi ta ɗaura akan kafaɗanta, sannan ta fice daga cikin falon.

Tana fita Ahmad ya saki dariya tare da ɗan dukan kafaɗan Saifuddeen ɗin cikin yanayin tsokana yace.
"Kurman dole." dariya sukayi dukansu, ahankali yaɗan ja jikinsa tare da kwantar da kansa akan cinyan Ummi, hannu Ummi takai tana shafa gashin kansa, cikin kulawa haɗi da soyayyar dake tsakanin ɗa da uwa tace.
"Babana sannu ko, yanzu ya jikin naka." Akasalance haɗi da zallan shagwaɓa yace. "Da sauƙi sosai Ummina, yanzu ina iya kwanciya, da kuma tashi aduk sanda nakeso, banajin ciwon komai." Murmushi Ummin tayi cikin jin daɗi tace "Masha Allah. Allah Ubangiji ya ƙara maka lafiya da nisan kwana, ya kuma sa nan bada jimawa ba ka tsaya akan ƙafafunka."
Gaba ɗayansu da Ameen suka amsa, hira suka taɓa sosai, sai wajajen ƙarfe 9 sannan su Ishaq dasu Saleesu suka tafi, Hayatuddeen kuwa shida kansa ya maida Zakariyya gida.
Adda Rahama ma Dr.Adnan ne yazo ya ɗauketa, ita dasu Farouq, haka dai duk suka watse gidan ya zamana saura su kaɗai, Hayatuddeen da ya dawo daga kai Zakariyya gida, shi ya kwashi trollys ɗin Hamman nashi, ya fita dasu dan kai masa part ɗinsa.
Yana dawowa daga kai kayan kuwa, ya baje atsakiyan falon tare da ɗagowa ya kalli Hamman nasa, ɗan marairaice fuska yayi tare da cewa. "Hamma Saifuddeen kaga part ɗinka kuwa? wallahi komai tsab tsab, sai sheƙi yake, Adda Zaleeha ta gyara maka komai, ga ƙamshi da sanyi kaman karna fito, amma da yake babu wanda ba a damu dashi ba kamanni, haka akabarmin ɗakina kaca kaca kaman turken jaki, bayan kuma kune kuka ɓata."
ya ƙare maganan yana me ɗan turo bakinsa gaba.
Dariya suka sa masa su dukansu, cikin dariya Ameena tace.
"Ya isa kwantar da hankalinka tunda Ammin Adeel ta gyara masa nima zan gyara maka naka."
Murmushi ya ɗanyi tare da cewa.
"Yauwa dayafi kam, dan ai dama kune kuka ɓata." Murmushi sukayi dukansu, daga haka suka ci gaba da hiransu, sai wajajen goma sannan dukaninsu suka watse daga sashin Ummin,
Kowa part ɗinsa ya nufa, Ameena ma sashinta ta wuce, saboda tanaso ta bar Saifuddeen ɗin suɗan gana da Zaleeha. Saifuddeen kuwa, yana komawa part ɗinsa kwanciya yayi, idanunsa yaɗan lumshe yana jiran zuwan Zaleeha ko kuma Ameena da ya zati zata zo ta mishi saida safe, jin shiru har kusan 11 babu ɗaya daga cikinsu yasa shi gyara kwanciyarsa tare da ɗan lumshe idanunsa, kasancewar akwai gajiya ajikinsa, jiyasa yayi lib yana tsumayin Zaleeha, mintuna kaɗan bacci ya ɗaukesa.

Ɓangaren Zaleeha kuwa tana shiga sashinta kayan bacci ta sanya sannan ta kwanta, zuciyarta cike take da saƙe-saƙe kala-kala, tabbas tanason kasancewa dashi, saidai kuma haka ta samu kanta da kasa zuwa wajensa,
idanunta ta lumshe tuna kasantuwarsu na ranan yasa taji wani irin feeling na taso mata. Idanunta ta lumshe, tare da soma sauƙe ajiyar zuciya, bata wani jima tana tunaninsa ba, bacci ɓarawo ya ɗauketa. Washe gari da sape kuwa kusan atare Saifudeen da Ameena suka shigo sashin Ummi, Raleeya na kitchine, Zaleeha kuwa itace ke zaune afalon Ummi, dan Ummi tana ɗakinta bata fito ba tukum,
Bayan Zaleehan sun gaisa da Ameena ne taɗan saci kallonsa asanyaye tace.
"Ina kwana." Sam bai amsa mata ba, saima kallonta da yayi ya kuma ɗauke kai, haka taji wani iri acikin ranta, amma saita ɗan kawar da tunanin abun, kusa da ita Ameena ta zauna, hakanne yasa ta sanya hannunta ta ɗauke Adeel.Idanunta ta lumshe, tare da soma sauƙe ajiyar zuciya, bata wani jima tana tunaninsa ba, bacci ɓarawo ya ɗauketa.

Washe gari da safe kuwa kusan atare Saifudeen da Ameena suka shigo sashin Ummi, Raleeya na kitchine,
Zaleeha kuwa na zaune a falon, kasan cewar yanzu ta fito ɗakin Ummi Bayan Zaleehan sun gaisa da Ameena ne taɗan saci kallonsa asanyaye tace.
"Ina kwana." tura bakinshi yayi tare da kauda fuskarshi ba tare daya amsa mata ba, saima kallon Ameena da yayi ya kuma ɗauke kai, haka taji wani iri acikin ranta, amma saita ɗan kawar da tunanin abun, kusa da ita Ameena ta zauna, hakanne yasa ta sanya hannunta ta ɗauki Adeel, wasa ta somayi masa tana ɗan jagwal gwalasa, dubansu Saifuddeen ɗin yayi, tare da ɗan ɗaure fuska, cikin body language ɗinsa yace.
"Ba ruwanku dani".
cikin mmki Ameena ta kalleshi fahimtar abinda yake nufi yasa cikin kula tace.
"Ba ruwanmu da kai kuma? Me mukayi?".
Fuska ya tsuke dan sosai abinda sukayi mishi ya ɓata mishi rai,
ganin yadda ya haɗe fuskane yasa Zaleeha ɗan kallonshi ido cikin ido, haɗe fuska ya kuma yi tare da mata wani irin kallon mai wuyar fassara wa.
Ameena ce ta kuma cewa.
"Kayi haƙuri Abban Adeel me mukayi?".
Rubutu yayi a wayarshi kana ya juyo musu fuskar wayar.
"Kun san abunda kukayi ai! Kun kyauta, hakan yayi dai-dai ku tafi ku barni ni kaɗai a ɗaki kamar gouro mara mata, ace ina da mata biyu amman dan ba sona kukeyi ba, shine ku duka babu wacce ta leƙani kun barni ni ɗaya kamar mara gata".
Sosai fa ya nuna ɓacin ransa,
Ameena kuwa ido ta ɗan zaro cikin sanyi ta kalli Zaleeha tare da cewa.
"To Abban Adeel ni kuma me laifina a ciki? Wata biyu har kusan uku muna tare, tunda mun dawo gida ai sai in ɗan huta tunda bani ɗaya bace".
Kai ya jinjina mata alamar.
"Yes yayi kyau ki huta tunda ni jidali na zame muku".
Da sauri ta jujjuya kai tare da cewa.
"Am so sorry ba haka nake nufiba".
Sai ta kuma kalli Zaleeha data maida hankalinta kan Adeel cikin sanyi tace.
"Ammin Adeel meyasa? Zaki barshi shi ɗaya, dole yanada buƙatar kulawarmu, Please karki sake yin haka".
Kanta ta gyaɗa ba tare data kallesu ba,
shi kuwa Saifuddeen kwaffa yayi ya nufi ɗakin Ummi.

Su kuwa ƴar hira suka ɗanyi kana suka miƙe suka taya Raliya ƙarisa aiyukan,

Bayan sunyi breakfast ne, duk suka dawo falon Ummi, suna ɗan taɓa hira.
Ameena nace ta ɗan miƙe cikin sanyi tace.
"Ammin Adeel ga Adeel mana bari inje in ɗan yi bacci".
Cikin sanyin da kallon da Saifuddeen yake mata ya sakarmata tace.
"To ba matsala".
Bayan fitan Ameena ba jimawa, Ummi ta kalli Hayatuddeen tare da cewa.
"Auta tashi mana in ai ke ka, Gidan su Imran".
cikin zumuɗin yawo yace.
"To Ummi kawo aiken".
Ɗaki ta shiga jim kaɗan ta fito da wasu jakukkunan guda biyu tace.
"Yauwa gashi, in kaje kace, Ummanku ga wannan, ta rabawa sauran aminamta dashi zamuyi fitan biki".
To yace tare da amsarsu kana ya miƙe ya fita.
A hankali Zaleeha ta miƙe riƙe da Adeel a hannunta alamun zata fita.
cikin kula Ummi tace.
"Kin gaji da zaman ko?".
Murmushi tayi tare da cewa.
"Eh bacci nakeji".
Kai Ummi ta gyaɗa mata alamar taje tayi.
A hankali tabi bayan Hayatuddeen, tazo bakin ƙofa kenan tayi kiciɓis dashi,
da sauri taja da baya tare da cewa.
"Lafiya?". Cikin falon ya nufa tare da cewa.
"Kai Ummi kunga wani irin hadari kuwa, gaba ɗaya garin yayi baƙƙirin kamar dare ashe dan wuta a kunne yake shiyasa bamu ga duhunba.
Dariya Zaleeha tayi tare da cewa.
"To hadarin cinyeka zaiyi? Ina a motace zakaje?".
Kai ya jujjuya tare da cewa.
"Tab wlh bazan fitaba".
Murmushi tayi kana tasa kai ta fita.
Sai kuma ta dawo da sauri cikin ɗan zare ido tace.
"Hhhh Ummi kinga hadarin nan kuwa kai nima ya bani tsoro".
miƙa Ummin tayi ta window ta ɗan leƙa,
ai kuwa da sauri ta rurrufe windows ɗin cikin sauri tace.
"Maza Zaleeha jeki side ɗinku ki rurrufe muku windows ɗinku, dan hadarin daga ƙasa yake tasowa, Allah ya bamu dai-dai ƙarfi mu".
Amin Amin sukace baki ɗayansu.

Da sauri Zaleeha ta fice.

Shi kuwa Hayatuddeen ɗakinshi ya wuce.

Raliya kuma dama tana sama ita da Ahmad ɗin ta.

Ita kuwa Ummi komawa tayi ta zauna cikin kula tace.
"To sai ka buɗe bakin kai mgna wacce kake ɓoyewa warakar naka ta tafi. Murmushi yayi tare da cewa.
"To Ummi ai dole ne a ɓoye mata dan asan ina ta dosa".
Daƙuwa Ummi tai mishi tare da cewa.
"Wato har yanzu baka yarda da itaba".
Kanshi a jujjuya alamar a a ya yarda yana dai son tabbatarwa ne.
Murmushi ta ɗanyi kana tace.
"Yauwa batun auren Ishaq fa saura sati biyu ne ko?".
Gyara zamanshi yayi tare da cewa.
"Eh saura sati biyu ni sun sa lokacin yayi tsawo ma".
tv ta ɗan kalla tare da cewa.
"Bai wani tsoba, kasan shirye-shiryen biki yawane dasu ga cin kuɗi".
Kallonta ya ɗanyi tare dacewa.
"To Ummi mu dai a gefenmu mun shirya komai sai dai ko in su can wurin amarene".
Gyara zama tai da kyau kana tace.
"Yauwa dama ina son muyi batun aikin Zaleeha, ya kamata ayi mata adalci, ta koma bakin aikinta, tunda ita tanada aiki ba adalci mu ajeta a gida, ƴar uwarta kuma na zuwa wurin aiki".
Kici-kici yayi da fuskarshi kamar zaiyi kuka yace.
"Ummi itace tace tana son aikin ne?".
Da sauri tace.
"Eh ai ba sai tace ba".
Baki ya ɗan tura tare da cewa.
"To Ummi ki bari sai ta gaya min in ta nema shike nan in bata nemaba sai tayi ta zama a gida tana mana girki, dan kinji Ahmad ya nace yace min shi wai dole zai ƙaura zai koma gidanshi dan zai dauko Goggo Dada da babanshi, naso in hanashi, sai naga kuma gskyanshi a takure yake a nan".
Ya ƙarishe mgnar a ranshi kuma cewa yake.
"Ni da zata haƙura da aikin taji da aikina ai da yafi min, in wuni da ita shima ai aikine".
Ummi kuwa kai ta kawar tare da cewa.
"Eh nima haka yace min, harda cewa ya lura wayo muke mishi mun maida mishi mata ƴar aiki. Batun Zaleeha tai mana aiki in sun ƙaura kuma bata tasoba dole dai in nema mana ƴar aiki".
Dariya suka ɗanyi dan su kansu sun san Raliya na aikatawa.
shiru suka ɗanyi jin wani irin sanyi mai ɗan karen daɗi da yake ratsa saƙo da luggu na jikin ɗan adam, a take garin ya wani irin duhu mai ban mamaki,
daga can nesa kunnuwansu ke jiyo musu, sautin tahowan ruwa, shuuuuuuuuuuuuuuuuuuuuuu.
cikin azama Ummi tace.
"Baba tafi side ɗinku ruwa na zuwa".
Kanshi ya ɗan juya tare da cewa.
"Ummi zanyi bacci a nan".
Da sauri tace.
"A a tashi ka tafi ka bar ƴara su kadai a sashin naku babu na miji, jeka".
da sauri yace.
"Ummi akwai na miji mana, ga Adeel".
Dariya tayi tare da cewa.
"Ana batun mutune kana batun babyn roba".
Dariyar sa mai sauti yayi tare da cewa.
"Kai my Adeel ɗinne babyn roba".
Dariya tai tare da cewa.
"Ƙaton baby ma kuwa, maza tafi sai anjima ni zanje inyi bacci".
Juyawa yayi tare da cewa.
"To Ummi na tafi tunda korata akeyi".
Allah ya kiyaye hanya tace mishi.
Amin Amin yace kana ya fita.

Ita kuwa Ummi bedroom ɗinta ta wuce tana tafe tana mgna,
"Laah na mance bamuyi mgnar Zaleeha'n ba". jinjina kai tayi tare da cewa.
"Koda yake na fasama bazanyi mgnar ba, bari mu gani ai in dai cikine zai baiyana kansa".
tana shiga ta shiga bathroom al'wala tayi kana ta fito tayi walaha,
ta dade tana tasbihi kafin ta konta bisa gado, tuni kuma an kece da ruwa kamar da bakin ƙwarya.

Shi kuwa Saifuddeen yana fita,
yazo dai-dai mashigar side ɗinsu kenan aka kece da ruwan, duk da ƙara gudun kekenshi da yayi saida ya jiƙe,
kasan cewar ƙofar Ameena zai fara wuce, haka yasa yabi ta cikin falonta,
Yana shiga ya maida ƙofar ya rufe.
Yana zuwa tsakiyar falon da nufin zai wuce falonshi ya ganta konce bisa tattausan carpet ɗinta dake malale a tsakiyar kujerun,
tayi pillow da pillow kujerunta,
ga cup a gabanta da alama tea tasha, murmushi yayi ganin baccinta takeyi cikin salama.
Wucewa yayi falonshi,
kai tsaye bathroom nashi ya wuce, cire jiƙaƙƙun kayan yayi ya shanyasu, kana yayi wonka, da ruwan ɗumi yana fitowa ya fasha mai tare da fesa turare, kana yasa farar jallabiya har ƙasa ba tare daya sa komai a cikiba,
kan gadonshi ya hau, ya konta,
sai kuma ya jawo wayarshi,
time ya duba. du du du tara da arba'in da mituna biyu ne.

Lumshe ido yayi kana ya buɗesu text yayiwa Zaleeha ya tura mata.

Ita kuwa Zaleeha tunda ta dawo side ɗin nasu wonka tayi kana tasa riga da zani na tattausan atampa, rigar tayi cib-cib da jikinta,
Adeel kuwa yanata wasan shi.
falo suka fito, ta kunna tv ta fara kallo kenan aka kece da ruwa,
sai lokacin ta tuno da rufe windows ɗinta, haka yasa ta miƙe da sauri ta rurrufesu,
kana ta dawo ta zauna dariya tayi ganin Adeel nata lumshe ido alamun zaiyi bacci,

Please Login or Register in order to submit comment