Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

hakan yasa natafi don na duba meke tafiya acan, gaba ɗaya falon nasa cike yake da abokansa maza su, Ahmad, Jabeer, Ishaq, Saminu mijin Raihana, Wareesu, Saleesu, Mudassir, ibrahim, Rabi'u, Hisham, Jabeer da kuma abokanshi da sukayi karatu tare Hashim, Jafar,Abdulhakim. Gaddafi, Aziz da dai sauransu gaba ɗaƴansu sanye suke da tsadaddun shadda ƴan ubansu yayinda kowanne daga cikinsu yayi kyau sosai, gaba ɗayansu cike suke da farin ciki, domin dama ganin auren Saifuddeen ɗin shine cikar burinsu. dan duk da suna tare da taraddadin kar dai nakasar Saifuddeen tashiafi mazantakanshi to shiyasa ganin aurenshi shine burinsu.

Ahankali yake murza wheellchair ɗinsa, inda ya ƙarasa zuwa gaban dressing mirror, cikin nutsuwa yake shafawa haɗaɗɗiyar surar jikinsa body lotion, koda ya kammala cumb ya ɗauka inda yashiga taje lallausan sumar dake kansa, wanda ya kwanta luf-luf kamar ƙawataccen sajen dake kwance akan fuskarsa, body spray ya fesa ajikinsa me daɗin ƙamshi, kana ya tura wheelchair ɗinsa zuwa kan gadonsa, inda anan ya aje kayan da zai sa.
Cikin yanayi na nutsuwa da alamun gajiya da ɗan kazar-kazar ɗinshi kamar yanda ya saba ako da yaushe ya zura dogon wandon haɗaɗɗiyar getzner mai kalan white ajikinsa, yana gama saka wandon ya sanya rigar wacce ta kasance half jumper, cikin nutsuwa ya ɗauko babban garen kayan wanda aka yajiwa wani irin fitinannen aiki da surfani blue colour mai masifar kyau, cikin nutsuwa ya zurata akan rigar tasa, lokaci ɗaya yayi wani irin azababben kyau mai tafiya da zuciya, ahankali ya zura wasu haɗaɗɗun toms ƙiran Italy aƙafafunsa masu azabar kyau da tsada, yayinda takalman suka kasance blue colour, wato kalan aikin garen jikinsa kenan, wasu tsadaddun links masu tsadan gaske yasanya ahannuwan rigar, kana yaciro wani tsadadden wrist watch mai tsananin kyau da tsada daga cikin wani ɗan ƙaramin box, agogon rolex ne me masifar kyau, ɗaura agogon yayi ahannunsa na dama tare da ɗaukan haɗaɗɗiyar hulansa mai tsada wacce take da kalan blue ajikinta yasanya, tare da dai-dai-ta zamanta akansa.
Tabarakallahu ahasanul khaliƙiyn! wani irin fitinannen kyau Saifudeen yayi wanda tunda yake bai taɓayin irinsa ba, gawani azababben kwarjini da yayi, wani irin ƙyalli da walwali fuskarsa keyi, sajen nan nashi yayi lib-lib akan farar fatar kekyawar fuskarshi, jajayen laɓɓansa sai sheƙi sukeyi tamkar ya shafa musu mai, gashin girarshin nan ya kwanta lib gwanin ban sha'awa, yayinda getzener ɗin jikinsa kuwa keta shinning, getzner ne me masifar tsada da kyau, wanda aƙalla kuɗinta yakai 95k, sosai kuma kayan suka amshi jikinsa.
cikin nutsuwa ya ƙarasa gaban dressing mirror, kallon kansa yayi acikin madubin tare da sakin murmushi, shi kansa ya aminta da kyawu haɗi da cikar halittan da Allah yayi masa, shiyasa akullum yake gode masa, tabbas Allah abun godiya ne, sam bazai iya fasalta matsanancin farin cikin dayakejin kansa aciki ba, yau zuciyarsa zata samu cikar muradinta, wani haɗaɗɗen parfumed mai ƙamshi ya fesa.
Kana ahankali ya danna madannin kekensa, kaitsaye ya nufi hanyar fita daga cikin ɗakin, buɗe ƙofar yayi ya fito ahankali, idanu su Ahmad suka zuba masa, baƙaramin kyau yayi ba, wanda sukansu maza ƴan uwansa sun ƙyasa da gayun nasa inaga mata kuma? sosai suka shiga yaba tsantsar kyawun nasa, inda Ishaq keta tsokanansa, shidai Saifuddeen sai murmushi kawai yakeyi don kuwa yau yana cikin farin ciki, nanfa dukansu suka shiga yi masa hoto, bayan sun gama yi masa hotonne kuma suka shiga ɗaukan selfie dashi, inda sukayi kyau sosai, zuwa lokacin ƙarfe 10 har da kusan rabi tayi hakan yasa suka ɗunguma sukai waje, don kuwa ƙarfe 11 dai-dai ne za a ɗaura auren.
A falon Ummi kuwa tana ganin fitowansu ta ratso gefe tana zuwa Adda Rahma da Raihana da Raliya suka biyo bayanta, kanshi ta dafa tare da cewa.
"Allah ya bada sa'a Babana , yau kayi kyau sosai irin kyan da ban taɓa ganin kayiba."
Amin Amin sukace baki ɗanyansu, shi kuwa Saifuddeen alama ya mata da ya gode, su Adda Rahama kuwa selfie suketayi dashi. gannin zasu ɓata lokacine Salisu yace.
"Adda Rahma ku barmu mutafi".
to tace kana suka barsu.
Acan compound ɗin gidan kuwa su Hayatudden da abokansa ne tsaye, sosai matasan yaran sukayi kyau cikin shigarsu ta shadda sky blue wanda yayi masifar amsarsu, dukansu cike suke da farin ciki inda suketa ɗaukan hoto da sabuwar wayar ta Hayatudden iphone 7+ wanda Saifuddeen ne ya saya masa, fitowar su Saifuddeen yasa dukansu suka maida hankalinsu garesu, tuni Hayatuddeen ya shiga santin irin kyawun da Hamman nasa yayi, nan yashiga ɗaukan Hamman nasa hoto, daga bisani kuma yashiga yi musu selfie.
Cikin yanayi naɗan sauri sauri kowanne ya nufi mota don kuwa lokaci nata ƙurewa, wata zazzafar RANGE ROVER black colour sabuwa dal mai azabar kyau da sheƙi da ƙyalli Saifuddeen ya shiga, wanda musamman ya sayeta saboda da ita yakeson yin hidiman biki, Ishaq ne yashiga gefensa ya zauna, su Ahmad kuwa kowa motarsa ya shiga hakama sauran abokansa baki ɗaya dan babu ƙaranta, yayinda aka warewa Hayatuddeen da abokansa motarsu guda ɗaya zazzafa wanda suma da ita zasuyi chilling ɗinsu wajen bik.
su Baffa Ali da Malam Ashiru kuwa wata haɗaɗɗiyar mota ƙiran mercedes suka shiga don sune suke matsayin iyayen ango, Dirankaɗi ma yazo da abokansa, inda su Alhaji Khabeer da Alhaji Ibrahim, haɗi da Alhaji Ishaq Ba miskila, San Husssain Alhaji Yawale Alhaji Aliyu mai dilan leda Malam Habu dama sauran manyan ya kasuwa duka Ya Rabi'u ma yayan Ishaq na Abuja yazo haka Dr Aliyu .Ya Adnan da abokan
shi hakama bappa Ali da abokanshi da abokan Abbansu Saifuddeen suma sunzo don halartan ɗaurin auren, gaba ɗaya haka motocinsu sama da talatin da biyar suna jera reras akan titi line by line haka suke tafiya cikin nutsuwa.
Duk inda jeren motocin suka wuce sai anbisu da kallo ahaka har suka isa cikin unguwar NEW G.R.A, can gefe sukayi parking motocinsu, don kuwa ƙofar gidan su Zaleeha cike yake da mutane maƙil, manyan malamai, manyan ƴan kasuwa, da kuma ƴan siyasa duk sun samu zuwa ɗaurin auren, saboda Baba Malam mutum ne da sunansa ke yawo acikin Nigeria, kusan kowa ya sanshi, kana ga Yaya Ahmad da sanadinshi yasa pilot suka rinƙa dirowa birnin gombe da jiragensu dan halartan ɗaurin auren ga kuma sojojin da ys Aminu suma sun gayyato nasu mutanen. Raveel ma ya gayyato duk abokan aikinsu.
Isowar su Saifuddeen yasanya gaba ɗaya kallo ya dawo kansu, kowa kallon Saifuddeen yakeyi, wanda nagarta haɗi da haiba da kwarjini da kamalarsa ya cika idanun mutane, sam basai an faɗa maka ba da kallonsa zakagane cewa shine angon, sai-dai kuma da yawa suna mamakin kasancewarsa gurgu.
Cikin mutunta juna Baba Malam da tawagarsa suka amshi su Saifuddeen, kamar yanda lokaci baya jinkiri wajen zuwa 11:00 am dai-dai dubbanin jama'a suka shaida ɗaurin auren SAIFUDDEEN Muhammad Ahamad Dukku da kuma ZALEEHA Bashir Sulamain Dukku akan sadaki naira dubu ɗari...!


Littafina na kuɗine duk wanda ya fiddamin shi aradun Allah yaseeeeeeeen doooooooguwa buluƙutu baƙar mutuwa!



*BY*
*GARKUWAN FULANI*
10/4/20, 7:04 PM - Mmn Khalid: *Wannan shafi nakine kyauta gareki kekyawar ƴar jaridar vison FM Gombe inai miki fatan al'khairi Zaleeha Babangida Hari mai shirin Babu Nakasasshe sai rago, dake da jonapwd gombe inai muku fatan al'khairi godiya ta musamman gareka malam ishaq*


_ZAIBA MASU KARATU KADA KU SAKE A BAKU LABARI BIYA ƊARI 200 KACAL ki samu littafin Zaiba na Ummee Garkuwa littafi ɗaya maidarrusa da dama karanta Zaiba kisha dariya tausayi shauƙi bege ƙauna karanta Zaiba kisha barkwanci Sufi ga masu buƙata ku nemi Ummee Garkuwa 08037251895 ta wannan number_


Wani irin matsanancin farin ciki ne mai tarin yawa ya cika zuciyar Saifuddeen, haƙiƙa yau takasance rana ta mussaman agaresa ranan da bazai taɓa mantawa ba acikin ƙuɗɗin tarihin rayuwarsa, cikin ikon Allah yau gashi Zaleeha ta zamo mata agaresa, zata rayu cikin ƙarƙashin iko da damansa, zata zama itace aƙasansa ta tabbata matar nakasasshe, wani irin ƙayataccen murmushi kawai Saifuddeen ke sakewa, hakanan yakejin kansa dai-dai da kowani cikakken namiji,  cikin son tayasa murna Mutane suka dinga bashi hannu suna musabaha, kowa sai Allah yasanya al'khairi yakeyi masa,   haka yadinga amsar hannun mutane masu tayasa farinciki, hatta Ahmad da bawani son auren yake sosae ba yau yayi farinciki saboda auren Saifuddeen babban abune awajensu.
Kasancewar al'adan ƴan Gombe ne yin receiption bayan an gama ɗaurin aure to hakanne takasance ga Saifuddeen domin kuwa tuni sun tsara haɗaɗɗen receiption wanda zasu koma gida shida abokansa da kuma wasu daga cikin jama'ar ɗaurin auren don suyi, haka suka shiga mota aka nufi gidan nasu Saifuddeen.

Zazzafan zazzaɓine ajikinta har zuwa yau ɗin, yanzuma duƙunƙune take acikin blanket gaba ɗaya jikinta sai faman rawan ɗari yake, tun daga ɗakinnata tana iya jiyo sauti da hayaniyan mutane, wanda hakan shike ƙara affecting ɗinta, hartanajin kanta kamar zai rabe gida biyu, kwata kwata batason hayaniya,  turo ƙofar ɗakinnata akayi, Aunty Lubna da Maryam, da kuma ƙawarta Rashida ne suka ƙaraso cikin ɗakin, ganinta still a duƙunƙune cikin blanket yasanya su ƙarasowa daɗan sauri, Maryam ne taɗan yaye blanket ɗin tare da kai hannunta jikin Zaleehan nan taji zafi jau, 
"Subahanallahi! dama bakida lafiya ne Zaleeha?".
taƙare maganar tana me ƙara taɓa jikin Zaleehan.
"Zaleeha!." Aunty Lubna taƙira sunanta, ahankali ta ɗan buɗe rinannun idanunta ta kalli Aunty Lubna'n, murmushi Aunty Lubna tayi mata tare da zama agefen gadon,  ganin haka yasa Zaleeha ta haɗo duka ƙarfinta tashi tayi taɗan zauna tare da jingina bayanta da jikin saman gado,  hannu Aunty Lubna tasanya ta dafa kafaɗan Zaleehan cikin kulawa da kwantar da murya tace.
"Ki daina sa damuwa aranki Zaleeha, musamman a irin wannan ranan, yakamata ace yau kin aje duk wani makamen yaƙi da auren nan da kika ɗaura, sannan kin kori damuwa daga gareki,  ayanzu damuwar da zaki sa kanki bazai taimakeki da komaiba Zaleeha, babu amfanin wannan ƙuncin, yanzu lokacin da zaki bari zuciyarki ta huta ne, ayau kuma ayanzu an ɗaura aurenki da Saifuddeen, zaifi kyau ki rungumesa amatsayin miji bawai maƙiyi ba, saboda duk yanda kikakai ga ƙinsa, yanzu kin zama mallakinsa, zaki zauna aƙarƙashin ikonsa, yanzu komai zakiyi saida izininsa, saboda Allah yace girman miji ya zarce na iyaye, haka ku girmama mazajenku tamkar yanda zaku girmama iyayenku, harma fiye da haka, dan Allah Zaleeha kiyi haƙuri hakanan damuwar nan kibarta!."
Aunty Lubna taƙare maganar cikin lallashi.
Kuka Zaleeha tasanya tare da rumtse idanunta, wani irin ɗaci takeji amaƙoshinta, yayinda zuciyarta keyi mata zafi,  tabbas anyi mata abunda bataso, an aurar da ita ga wani ba mutumin da tafi so fiye da kowa ba,  take taji matsanancin tsanar Saifuddeen ya ƙara ninkuwa acikin zuciyarta, hartanajin zata iyayin komai don ganin ta nesanta kanta dashi, sannan kuma ta tozarta igiyar aurensa dake kanta, al'ƙawarine saita wulaƙanta aurensa, sam bazata zauna da nakasashshe ba!.

Cike da tsananin tausayinta Maryam ta kamo hannunta, cikin yanayin sanyinta tace.
"Zaleeha ke ƙanwatace, jini ɗayane ke yawo ajikinmu, tabbas inason duk wani abun da kikeso, haka kuma inaƙin abunda kike ƙi, saidai kuma Saifuddeen ba abun ƙi bane, irin Saifuddeen mata da yawa ke fata da burin samu amatsayin miji, kada ki taɓa dubansa da nakasarsa, domin NAKASA BA KASAWA BACE, haka kuma nakasa bata zama ciwo matuƙar ba nakasar zuciya bace, tabbas ina tayaki farincikin samun Saifuddeen, saboda inaji ajikina ko anan gaba koda bayan raina nasan cewa ƙanwata tasamu managarcin mijin dazai zame mata garkuwa, na tabbata koda ace yau kowa namu zai ƙare abarki ke ɗaya, bani da kokonto akan saifuddeen saboda nasan zai riƙeki da amana, bakuma zai taɓa bari ki wulaƙanta ba, nasan ayanzu kina ganin laifin Baba dama su Ya Ahmad da Ya Ameenu saboda sun aura miki wanda bakyaso."
Ɗan tsagaitawa da maganan maryam tayi tare da sakin murmushi,  ahankali ta cigaba inda tace.
"Watarana zakiyi alfahari da Baba Malam Zaleeha, zakuma kiji cewa yayi miki zaɓi irin wanda kowani uba ke fatan yiwa ƴarsa, tabbas nasani komin jimawa saikinyi al'fahari da zaɓin Baba Malam, sannan kuma kada kimanta cewar duk wanda yayi biyayya ga Iyayensa to har abada baya taɓa taɓewa."

Duk wannan maganganun da Maryam keyi Zaleeha bata buɗe idanunta ba haka kuma hawaye basu bar tsiyaya daga cikin idanun nata ba,  zuciyarta tayi tauri, ɓacin rai ya cikata, tsana ƙiyayya masu tsanani, sun riga da sunyi tasiri acikin jikinta da ƙarfin sirin da Ruda ke zuƙa Mama suna banka mata, saboda haka babu wani magana daza a faɗa don atausasata da zaiyi aiki acikin ƙwaƙwalwa da zuciyarta, hasalima ji take kamar ana ƙara mata yawan tsanar Saifuddeen ɗinne.
Duban Rasheeda Aunty Lubna tayi cikin kulawa tace, "Rasheeda kiyi abun daya dace, tasamu tayi wanka bari naje nakawo kayan da zata sa."
"To" Rashida ta amsa zuciyarta cike da tausayin Zaleeha, saidai kuma ta wani ɓangare wautan Zaleeha kawai take gani.
Su Aunty lubna na fita, Rasheeda ta kamo Zaleeha, da ƙarfi Zaleeha ta fusge hannunta daga na Rashida, cikin yanayi na faɗa-faɗa zaleeha tace.
"kada ma kice zaki faɗamin komai Rashida, babu abun da zaki faɗa min wanda zan fahimta, sannan kowani kalma zaki faɗa, zakiyi asaran yawun bakinki ne kawai, dan koda wasa bazan taɓa ɗauka ba."
Murmushi Rashida tayi tabbas tasan Zaleehan tana cikin ɓacin rai da baƙinciki, hakan yasama bazata biyeta ba, tasan tanajin haushinta ne saboda tabawa Saifuddeen da abokansa haɗin kai   wajen ganin antsara abubuwan biki sun tafi dai-dai.
Dawowar Aunty Lubna ne ta lallaɓa Zaleehan inda ta haɗa mata ruwan wanka,  ko acikin toilet ɗin da ƙyar Zaleehan ta iyayin wanka, domin gaba ɗaya jikinta babu kuzari, tana fitowa daga wankan aunty lubna ta kamata inda ta zaunar da ita akan stull,  da ƙyar ta iya shafawa jikinta mai,  aunty lubna dakanta taɗanyi mata light meckup akan fuskarta kasancewar tasan ba isashshen lafiya bane da ita,  yimata meckup me yawa kaman takurata ne,  doguwar rigar bababar  atamfar chiganvy  me kalan ja aunty lubna ta bata tace ta sanya, kanta yafara ciwo sosai hakan yasa batayi musuba ta amsa, ta zura ajikinta, sosai ɗinkin rigar tayi kyau yayinda tabi jikinta ta lafe, rigar irin A shape dinnan ne me faffaɗan hannu, an ɗameta daga ƙirji zuwa ciki yayinda daga ƙasa kuma aka faɗaɗata, haka hannun rigar akayishi mai faɗi, sosai yayi wa Zaleehan kyau musamman ma idan ka haɗa da kalan atamfar da takasance ja mai ratsin green colour,   dogon gashinta da akullum yake cikin gyara aunty lubna ta tubke mata shi akusan wuyanta, jan ribbom aka maƙala ajikin gashin, aunty lubna dakanta tayi mata ɗaurin ɗan kwali mai kyau, hakannema ya ƙara ƙawata shiganta, kama daga kan sarƙa ɗankunne, harma da awarwaro.duka na gold aka samata masu kyaun gaske,  aunty lubna naƙoƙarin yafa mata mayafi ajikinta ta shagwaɓe fuska tare da turo baki, hawayene suka cika idanunta, ganin haka yasa Aunty lubna sakin murmushi tare da kamata ta kwantar da'ita akan gado,  komawa aunty lubna tayi tasanarwa da ya Ahmad halin da Zaleehan ke ciki, nan take Ahmad yayiwa family doctor ɗinsu waya, babu ɓata lokaci kuwa sai gashi yazo,  sanin cewa batason allura ne yasanya likitan bata magunguna bayan ya auna yanayin jikinnata, magunguna masu ƙarfi ya bata, tare da ɗaura mata drip, don kuwa shima zai taimaka wajen bata ƙarfin jiki da kuzari.
Ko mintuna 20 ba ayi da samata drip ɗinba bacci ya ɗauketa.

Acan gidansu Saifuddeen kuwa receiption aka gabatar me rai da lafiya inda akayi ɓarin nairori wajen ƙawata haɗaɗɗen abinci da drinks ɗin da akasha, bayan anci ansha ne kuma aka bawa kowa takeaway wanda ke ɗauke da kayan ciye ciye dana shaye-shaye, kowani ledan takeaway kaza ne guda aciki anyi raping ɗinta da poil paper abun dai sai wanda ya gani, nan fa Saifuddeen da abokansa suka shiga ɗaukan hotuna kala-kala,  haka sukayita bidiri basu suka samu kansuba saida aka ƙira sallan azahar nanfa masu tafiya masallaci suka tafi masu tafiya gidama suka tafi, inda wasu sun koma gidane don suɗan huta kafun lokacin ɗauko amarya da kuma diner.
Gaba ɗaya gidan nasu Saifuddeen babu masaka tsinke, jama'ane takota ina, hatta ɓangaren saifuddeen dinma mutanene acikinsa maƙil.
Su Ahmad da ishaq ne suke zaune afalon sunata hiransu, wasu kuwa na kallo, kowadai da abunda yakeyi, Saifuddeen na cikinsu inda gaba ɗaya hankalinsa kekan laptop ɗinsa, da alamun wani aiki mai tsananin mahimmanci yakeyi, dan gaba ɗaya hankalinshi na kan System ɗin gaba ɗaya idanunshi sai yawo sukeyi a jikin fuskar laptop ɗin, ganin hayaninyar abokan nashi yayi yawa ne suna katse mishi hamzarine ya sashi sarrafa kekenshin ya shiga bedroom ɗinshi.

Abuja.
Kuka sosae Amina keyi hakan tatashi yau batajin daɗi wani irin abune takeji ya toshe mata maƙoshi, tabbas babu makawa tasan kishin Saifuddeen ne ke ɗawainiya da zuciyarta, har wani zafi zafi takeji aƙirjinta, tanason Saifuddeen so mai tarin yawa tana kuma kishinsa sosai, bata san dacewa soyayyar Saifuddeen yayi ƙarfi azuciyarta ba sai yau daya kasance ya auri wata ba'ita ba,  ahankali take fitar da sautin kukanta, wayarta ta ɗaga tare da kunnawa, take hoton Saifuddeen wanda akayi masa ɗazu inda Hayatuddeen ya ɗaura a status ɗinsa ya bayyana akan fuskarta, don tuni ta sauƙe hoton zuwa wayanta, sosai yayi mata masifar kyau acikin farar shaddan dake jikinsa, fuskarsa ta ƙurawa ido, tabbas kowa yagansa yasan yanacikin matsanancin farinciki,   rumtse idanunta tayi tare da sakin wasu zafafan hawaye, tabbas ta barwa Allah itakam, ta fawwala masa dukanin lamuranta, tasan zaiyi mata jagora, idan tana darai da kuma rabo tabbas tasan watarana zata mallaki saifuddeen amatsayin mijinta.

Kaduna, Asma'u Ahmad matawalle kuwa tun jinya da taga batun auren Saifuddeen sosai hankalinta ya tashi sai dai tasa a ranta babu wani na ƴa macen da zata hanata mallakar Saifuddeen a matsayin mijin aurenta, shiyasa daren jiya harda mafarkinta wai auren da ita aka ɗaura.

Ahmad ne yabi bayan Ishaq da ya shiga bedroom ɗin Saifuddeen, akan gado suka sameshi, yana zaune kana abokinshi Aziz Wanda ya kasance babban SS shima yana zaune gefenshi duk sun zubawa laptop ɗin idanu bisa dukkan alamu wani abun Saifuddeen ke nuna mishi, kana da alamun tashin hankali a fuskarsu.
Ahmad ne ya kalleshi da kyau kana ya zauna kan durowar gefen gadon,
ganin hakanne yasa Saifuddeen gyara zamanshi kana ya jingina bayanshi da kan allon gadon. Wayarshi ya ɗauka text ya turawa Umminshi cewa yana jin yunwa kuma ya gaji.
yana turawa ya ajiye wayar sannan ya ɗan miƙawa ishaq hannu suka yi irin gausuwarsu sanna ya kuma kalli Ahmad daketa mishi kallon tuhuma.
Da Sallama Ummi da Adda Rahma suka shigo falonshi dake cike da abokanshi gaisawa sukayi sannan suka wuce cikin uwar ɗakan,
yana ganin Umminshi ya ɗan kwaɓe fuska tare tanƙwashe kanshi bisa kafaɗunshi yayi rau-rau da manyan idanunshi da suke cike da tashin hankali da tarin gajiya,
da sauri Ummi ta zauna gefenshi,
murmushin jin daɗi yayi tare da raɓawa jikinta,
hannnta tasa kan goshinsa sai kuma tayi saurin sunkuyiwa ta leƙa fuskarsa tare da cewa.
"Meke damunka?." rumtse idonsa yayi da ƙarfi, sanna ya buɗesu,
Adda Rahma kuwa murmushi kawai taketayi a ranta take cewa.
"Hmmm shaleleln Ummi wannan ɗan shagwaɓan inaga randa duk ya kusanci matarma sai anyi jinya biyu mutun sam shi baya son wahala abu kaɗan sai yazo yayi ta narkewa Umminshi yana shogoɓa."
a fili kuwa ajiye kulolin abincin da suka kawo mishi tayi tare da zama ƙasa kan carpet ta kamo hannunshi alamun tausasawa,
sai kuma ta ɗan leƙo fuskar wayarshi da yake nunawa Ummi inda ya rubuta,
"Ummi sacemin ita akeson ayi, meyasa? me tayi musu? wayake shirya sacemin matata ranar da za'a kawo min ita gidana? me nayi musu?."
cikin kaɗuwa da tsoro Rahma ta mike tsaye tare da cewa.
"Su waye ne Saifuddeen meyasa zasu saceta?."
Ummi kuwa wani irin fargabane da tsoro ya rufeta jiki a mace ta kalli Ahmad da ishaq da Aziz ta musu bayanin abinda ya rubuta mata sosai Ishaq da Ahmad suka shiga ruɗani Aziz kuwa kai ya jinjina tare da cewa.
"To ai da sauƙi tunda mun gano shirinsu,
tun a zuwa ɗaurin aure Saifuddeen ya gano akwai baƙin ayarin motocin da suka shiga sahunmu kana ya ɗauki numbers ɗin motocin ya kuma bi diddigin inda aka sai motocin ashema a kamfanin Salisu ne, to yanzu bincike yazo mana da sauƙi dan Salisu ya bamu komai na masayin motocin harma da number wayarsa, shine ya bawa Saifuddeen damar bibibiyar kiran wayar dama motsinsu munji shirinsu na son sace Zaleeha."
wasu siraran hawayenesu ka zubowa Ummi murya a raunace tace .
"Aziz ku nemo hukuma a lamarin."
kai Saifuddeen ya jujjuya mata alamun a a,
shi kuwa aziz gyara zama yayi tare da cewa.
"Uhmmm Ummi kenan to ai su kansu Hukumar Saifuddeen ne idonsu, tunda duk wani tantirin daya gagaresu gane inda yake Saifuddeen suke miƙawa aikin bin diddiginshi ta na'ura mai ƙwoƙwalwa yake gano musu komai, to yake binciko tantiran da basu shafeshi bama bare wannan dake son sace mishi amarya, yanzu haka ya tsara komai ya kuma haɗe kiran wayar waɗancan da wayata, yanzu haka hatta motar da ya saya dan ɗauko amaryarshi suma sun sayi irinta, dan su samu damar sacetan, rashin sanin Saifuddeen yana ɗaya daga cikin tawagar UPSC, ne ya sasuyin wannan gangancin."
Adda Rahma kam gaba ɗaya hankaƙinta ya tashi, sai dai ganin yadda Saifuddeen ke basu ƙarfin guiwa yasa hankalinsu ya ɗan konta, Adda Rahman ne ta kalli Aziz tare da cewa.
"Wacce tawaga ce kuma UPSC?."
Cikin fidda nufashi yace.
"Ma'ana tawagar Union public service commission! sai dai sirrance yake musu aikin, ƙarƙashin jagorancin DSS."
Jinjina kai Adda Rahma tayi dan ta fahimci sirri Saifuddeen ke yi wanda ba'a cika son mutane su saniba, duk da sunsan yana tare da DSS amman basuyi zaton matsayin aikinshi ya kai nan ba.
nan suka ɗan sashi yaci abinci sannan suka fita suka tafi.


Ƙarfe 4 dai-dai kamar yanda al'adan gombawa takasance da yamma suke ɗauko aure kuma hakan ya samu asaline tun lokacin da ƙungiyar ƴan kalare suka fare da sace amare in za'a kaisu gidajen aurensu da dare shiyasa aka dawo da al'adar garin kai amarya gidanta da yamma ido na ganin idop.
Hakan yasa gaba ɗaya abokan saifuddeen sun shirya tsab don zuwa ɗauko amaryarsu, motoci ne masu uban yawa suka tanada don zuwa ɗauko auren, tuni su Ahmad, Ishaq, Salisu, Wareesu, Saminu, Mudassir, Jabeer, Hisham, ibrahim, Rabi'u, Aziz, Aryan, Gaddafi,duk sun kammala komai, kowa yasanja shiga irin ta alfarma.
Ahankali Saifuddeen yake tuƙa kekensa, har ya ƙaraso harabar gidan, sanye yake da ɗanyar shadda blue mai masifar kyau, sai shinning take yayi kyau matuƙa, saidai awannna karon baisanya gareba, hasalima rigar half jumper ce,  su Adda Rahama da suka fito don zuwa ɗauko aure tana ganin ƙaninnata taƙarasa garesa da sauri, yanaganinta ya sakar mata murmushi tare da shagwaɓe mata fuska kaman wanda zaiyi kuka,  murmushi Adda Rahama tayi tare da ƙarasowa ta shafa gefen fuskarsa, cike da ƙaunarsa tace.
"To sakalallen Ummi na farko yanda naga ka shagwaɓe fuskarnan so kake kace kagaji ko? ehem ai duk wata shagwaɓa Hayatuddeen awajenka ya koyota."
Murmushin daya bayyana fararen haƙwaransa yayi tare da ɗan lumshe idanunsa, hannunta ya kama inda ya ɗaura adai-dai saitin heart ɗinsa, dariya me haɗe da murmushi tayi, cikin jin daɗi ta dubesa inda tace.
"Kamar yanda kake cikin farinciki Saifuddeen haka muma muke, farincikinmu nayau bazai misaltuba angon Zaleeha!."
Yanzunkam dariya sosai Saifuddeen ɗin keyi saidai babu sauti, sosai maganan addan nasa tafaranta ransa, ganin yanda yake dariya yasa Adda Rahama lumshe idanunta tana mejin daɗi acikin ranta,  ita da kanta takoma bayansa inda ahankali take ɗan tura kekennasa, harsuka ƙarasa gaban wata hamshaƙiyar ƙatuwar mercedess benz 2019 mai azabar kyau da tsada, sabuwace dal sai shinning take tana ɗauke ido,  shida kansa ya shiga motar kamar yanda ya saba, inda Ahmad ya naɗe kekensa ya tura masa cikin both, nanfa kowa yashiga mota,  inda ƴan ɗauko amarya ma suka shiga tasu motar, ajere haka motoci ashirin da shidan ke tafiyan gwano akan babban titin, kasancewar Gombe akwai manyan tituna sannan kokusa babu ƙazanta akan gaba ɗaya titunansu, cikin motoci ashirin da shidan nan tsakiyarsu ta Saifuddeen take wanda cikintane za a ɗauko amarya.

Tunda ta kwanta

Please Login or Register in order to submit comment