Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

shafawa, cikin tausayawa tace.
"Ya isa hakanan yi haƙuri ki daina kukan kinji, sannu ko."
Kanta ta shiga girgizawa, dan bazata iya tsaida kukan nata ba, saboda wani irin ciwo da zafi da takeji aƙasanta, ga kuma wani irin zazzafan zazzaɓin da lokaci ɗaya ya sauƙar mata,
Ummi ne ta dubi Adda Rahma, wanda tausayin Zaleehan yasa yanayinta ya sauya, idanunta duk sun kawo ruwa.
Cikin sanyi Ummi tace. "Nahaɗa mata ruwan wanka, kamata kuje toilet, dan Allah Rahma kiyi mata duk wani abun daya dace duk wani abu da kika san zaki iya yiwa Raliya ko Raihana kiyi mata".
Sai ta kuma kalli Zaleeha cikin tausayawa tace.
"Daure Addanku ta taimaka miki,ki ɗauketa kamar Adda Maryam ɗinki kinjiko."
Kai Zaleeha ta gyaɗa cikin sanyi da zubda hawaye tayi ƙasa da kanta dan azabar kunyar Ummi da takeji.
Ita kuwa Ummi murya a tausashe tace.
"Bari naje nasa anemo mata magani, dannaji jikinta da zafi kaman wuta."
Kai Adda Rahama ta jinjina, cikin tausayawa ta jawo Zaleehan, da ƙyar ta iya ɗago ta, saboda yanda ta kasa tsayuwa da ƙafafunta, Cikin lallami Adda Rahama ta jata zuwa cikin toilet ɗin dake cikin ɗakin.

Dr Adnan kuwa koda ya isa ɗakin Hayatuddeen, duƙufa yayi akan Saifuddeen wanda zuwa yanzu bayan nasa ya sake riƙewa sosai. Hankalin Dr Adnan ne ya tashi saboda yanda yaga jikin Saifuddeen ɗin, ya sake ɗaukan zafi. Hayatuddeen kuwa ganin Dr Adnan yazo ya sa ya tashi ya fita daga ɗakin, zuciyarsa cike da murna ya ciro wayarsa daga cikin aljihu, inda ya dannawa numbern Zakariyya ƙira. Wayar bata wani jima tana ringing ba Zakariyya ya ɗauka.
Murmushi Hayatuddeen yayi, cikin jin daɗi yace. "Zakariyya kunnuwan Hammana sun buɗu, Hammana ya warke daga cutar kurumta Zakariyya".
Jin maganan Hayatuddeen ɗin yasa jikin Zakariyya ya ɗauki rawa, samun kansa yayi cikin wani irin farin ciki, dan sosai abun ya taɓa zuciyarsa, cikin matsanancin farinciki yace.
"Masha Allah Alhamdulillah, Hayatuddeen yanzu Hamma Saifuddeen najin magana kenan?" Cikin matsanancin farinciki Hayatuddeen yace.
"Eh Zakariyya, ni narasa inda zansa kaina ma saboda farinciki, yanzu Hammana ya zama kaman kowa, saidai kuma dan Allah kada ka faɗawa kowa hakan, dan Hamma Saifuddeen da kansa yace bayason Adda Zaleeha ta sani, wanda kuma bansan menene dalilinsa nayin hakan ba."
Kai Zakariyya ya jinjina, cikin tsananin jin daɗi yace.
"Insha Allah bazan faɗa mata ba Hayatuddeen, anjima kaɗan nima zanzo, bazan iya jurewa ba Hayatuddeen zanzo naga Hamma na kuma ji muryarsa."
Kai Hayatuddeen ya jinjina, tare da cewa. "Shikenan Zakariyya sai kazo, saidai kuma tun ɗazu Hamma Saifuddeen ke cewa bayansa nayi masa ciwo, amma yanzu Ya Adnan yazo yana dubashi."
Cike da zumuɗi Zakariyya yace. "Ganinan zuwa Hayatuddeen, kuma insha Allah komai zai dai-da-ita."

Acan sashin Saifuddeen kuwa, Ummi naganin shigansu cikin toilet, ta fita daga cikin ɗakin, saboda tanaso taje ta duba Saifuddeen. Adda Rahama kuwa cikin kulawa haɗi da lallami tace da Zaleeha ta cire kayan jikinta, tare da miƙo mata towel tace ta ɗaura kana ta juya mata baya dan kauda idonta kanta, da ƙyar ta iya cire kayan nata, sannan ta ɗaura towel ɗin cikin hikima yadda bata tsaya ba komai a jikinta ba.
Da ƙyar Adda Rahama ta iya zaunar da ita acikin ruwan zafi'n, wani irin narkekken ƙara ta sake, saboda yanda taji ƙasanta na mata zafi da raɗaɗi kaman an watsa mata barkono, kuka ta saka tana ɗan yayyarfa hannunta.
Cike da tausayinta Adda Rahama tace "Sannu ko kiyi haƙuri kinji, idan ruwan ya gama ratsaki, insha Allah zaki ɗanji sauƙi."
Asakalce ta ɗan jinjina kanta, duk da zafin da takeji haka ta ɗan daure ruwan ɗumin ya ratsa cikin jikinta, saida ruwan yaɗan fara salancewa, sannan Adda Rahama ta sake zuba mata wani ruwan me ɗumi, tana sake shiga ruwan kuwa gumi ya fara fesowa daga jikinta, taji zafi sosai saidai bakaman na farko ba. Saida Adda Rahama tasa mata ruwan ɗumi sau uku, sannan ta fita inda tace mata taɗan ƙoƙarta tayi wanka tsarki.

Ummi kuwa daga ɗakin kaitsaye sashinta ta wuce, anan ɗakin Hayatuddeen tasamu Dr Adnan ya saka Saifuddeen ɗin agaba, yana ta faman auna jikinsa.
Cikin kulawa, akuma sanyaye tace.
"Dr Adnan ya jikin nasan dai? Babu wata matsala kam dai ko?".
Ɗan numfasawa Dr Adnan yayi, haɗe da cewa.
"To jikin nasa dai da sauƙi, za 'ace, yanzu so nake naji problem ɗin nasa, dan ina tunanin ma saina ƙira Dr.Aleeyu na faɗa masa ko akwai shawarwarin da zai bamu".
Kai Ummi ta jinjina, tare da sakin wani gauron numfashi, ganin yanda Saifuddeen ɗin keta cije lips ɗinsa ne, yasa ta juyawa ta fice daga cikin ɗakin, kaitsaye kitchine tawuce, dan tanaso taɗan haɗawa Zaleeha tea. Zaleeha kuwa da zazzaɓi yayi mata wani irin mummunan kamu, da ƙyar ta iyayin wankan tsarki da kyar ta ɗaura towel a jikinta kana ta zauna bakin baf ɗin, akasalance da muryarta wanda bata fita ta shiga ƙiran sunan Adda Rahama,
Adda Rahama wanda ta gama kimtsa kan gadon da suka ɓata, jin Zaleehan na ƙiranta ne yasa ta nufi banɗakin, tana shiga Zaleehan ta miƙo mata hannu, cikin sheshsheƙan kuka tace. "Ki riƙeni Adda Rahama jiri nakeji, cikin jikina da ƙafafuna duk ciwo sukemin".
Cikin tausayawa Adda Rahama ta riƙota, haɗe da cewa.
"Sannu kinji kiyi hakuri kinji, Ummi zata kawo miki magani zai daina insha Allah."
ahaka suka fito daga cikin toilet ɗin, duk taku ɗaya da Zaleehan zatayi saita rumtse idanunta, saboda yanda takejin zafi aƙasanta.
Akan gado Adda Rahama ta zaunar da ita, sannan ta fice daga cikin ɗakin, kaitsaye tanan cikin falon Saifuddeen ɗin ta samu shiga sashin Zaleeha, direct ɗakin Zaleehan ta wuce, wata ƴar doguwar riga marar nauyi tare da hijab Adda Rahama ta ɗauko mata, sannan ta dawo ɗakin. Akwance tasamu Zaleehan tana ta faman sakin ajiyar zuciya akai akai alamun tasha kukanta daren jiya ta ƙoshi.
Tashinta Adda Rahama tayi, tare da bata rigan tace ta saka, akasalance haka ta saka rigan, sai faman sakin sheshsheƙan kuka take. Hijab ɗin Adda Rahama ta sanya mata sannan tace da ita, ta tashi tayi Sallah.
Haka kuwa tayi sallan tana sakin sheshsheƙan kuka, ko tsayuwa mekyau bata iyawa, dole saida ta jingina, tana idar da sallan kuwa ta fashe da kuka, dai-dai lokacin Ummi ta shigo cikin ɗakin hannunta ɗauke da cup ɗin tea, wanda ta haɗa sa me kaurin gaske.
Ganin Zaleehan na kuka yasa ta ƙaraso cikin ɗakin da sauri.
Zama tayi akan gado, tare da jawo Zaleehan ta zaunar da ita, cikin kulawa tace.
"Yi haƙuri kinji, ga tea nan na haɗo miki, kisha nasan zaki ɗan samu ƙarfin jikinki." Awahalce ta girgiza kanta, cikin sheshsheƙan kuka tace.
"Ummi bazan iya sha ba, banajin dadin bakina, kuma jiri nakeji, kaina ciwo yakemin."
Cikin tausayawa haɗi da lallashi, Ummi tace.
"To naji kiyi haƙuri kisha kinji, idan kika ɗansha saina kawo miki magani." Adda Rahama ne ta karɓi kofin tea ɗin takai kan bakin Zaleehan, ashagwaɓe hawaye na tsiyaya daga cikin idanunta haka ta ɗansha tea ɗin, ko rabin cup ɗin bata shaba, ta koma ta kwanta, jikinta sai rawan sanyi yake saboda zazzaɓi, ganin hakane yasa Ummi rufa mata blanket, tare da gyara mata kwanciyanta.

Adda Rahma kuwa ganin ta konta yasa ta fita da sauri dan tana marari da begen jin muryar ƙanin nata kai tsaye ɗakin Hayatuddeen ta nufa.

Acan ɗakin Hayatuddeen kuwa Raleeya ce taturo ƙofar ɗakin ahankali ta shigo. Ɗan tsaye tayi tana kallon Dr Adnan wanda tazo da niyar gaidashi ganin hankalinshi kab na kan Saifuddeen ne yasa ta tsaya kallonshi shida Ahmad wanda suka saka Saifuddeen ɗin agaba, Dr Adnan ne yake ta faman auna tempreture'n Saifuddeen ɗin.
Jin motsin shigowa ɗakin, yasa Dr Adnan juyowa , ganin Raleeya tsaye ya sashi cewa. "Taɗan basu guri yanaso ya duba Saifuddeen ɗin." Babu musu kuwa ta fita, ganin ba abun da zatayi ne yasa ta wuce kitchine dan ɗaura musu break fast, ahanzarce kuwa ta soma haɗa musu break fast ɗin asauƙaƙe, wanda tasan bazai ɗauki lokaci ba.

Adda Rahma kuwa kai tsaye ɗakin Hayatuddeen ɗin ta nufa dan su Faruq sunce mata can yake,
da sassarfa ta ƙarasa cikin ɗakin, tana cewa.
"Salamu alaikum, ina ɗan uwana yake?".
Murmushi Ahmad yayi tare da cewa.
"Gashi nan Adda Rahma yana ta mana raki".
Dai-dai lokacin ta ƙarasa cikin ɗakin da sauri ta iso gabanshi har tana gogan jikin ya Adnan cikin kaɗuwa tace.
"Saifuddeen kayi magana mana inji".
Wani irin murmushin ƙarfin hali yayi dan ciwon da yakeji, murya a sarƙafe yace.
"Na'am Adda Rahma,".
wasu irin zafafan hawayen farin cikine suka wonke mata ido cikin ɗaga sauti tace.
"Alhamdulillah, Allah mun gode maka da wannan ni'imar ya Allah ka ƙara mana nima da samun lafiyar sawunshi".
Amin Amin sukace baki ɗayansu, kana Dr Adnan yace to ta matsa mishi yayi aikinshi, cikin jin daɗi ta nufi kitchin inda take jiyo muryar Hammanshin da Raliya murna sukayiwa juna kana ta fita ta koma side ɗin Saifuddeen ɗin wurin Zaleeha.

Dr Adnan kuwa ganin Rahama ta fita, ya sashi ɗan ɗago kansa ya dubi Saifuddeen ɗin, cikin kulawa yace.
"Nakasa gano sanadin tashin ciwon bayankan nan tunda babu cikakkun na'urorin a wurina wanda zanyi bincike dasu, ka faɗi akan bayan naka ne? ko kuma wani abu ne ya samu bayan?." Ɗan lumshe idanunsa, yayi cikin sassanyar murya yace.
"Ba faɗuwa nayi ba." Idanu Dr Adnan ya zuba masa, saida ya nazarce sa naɗan wasu sakanni kafun yace.
"To meya faru?." can cikin ƙasa da murya yace.
"disvirgin ɗin Zaleeha nayi, tun alokacin naji bayan ya riƙe yana min ciwo sosai.
please Ya Adnan mu koma india, inajin bayana kaman zai ɓalle." Ajiyar zuciya Dr Adnan ya sauƙe, dan sai yanzu ne ya gano cewa, saboda Saifuddeen ɗin yayi sex da Zaleeha ne hakan ya faru.
Ahmad kuwa dariyar mugunta yayi tare da cewa.
"Hege uban ƴan longomi, wani ne ya aikeka ka jogalo ɓalgaceccen ƙugunka kazo kana mana raki da sakalci ji yadda kuka gigita mana Ummi kaida matarka mai shegen raki ko kunya bakwai".
Ya Adnan kanshi saida yayi dariya, shi kuwa Saifuddeen fuska ya tsuke.
Cikin nutsuwa motar Ameena ta kutso kai cikin gidan, wanda dawowanta daga wajen aiki kenan, anutse ta gama dai-dai-ta parking ɗin motar, saɓa Adeel akafaɗanta tayi, sannan ta buɗe motar ta fito, kaitsaye sashin Ummi ta nufa, duk da cewar agajiye takejin kanta, amma ta riga da ta saba, kullum idan ta dawo sashin Ummi take fara zuwa.
Da sallama ɗauke abakinta ta shiga cikin falon.
Shigarta kuwa yayi dai-dai da fitowan Raleeya daga kitchine. Ganin Ameena yasa Raleeya ƙarasowa gareta da gudu, faɗawa jikinta tayi ta rungumeta ƙam, fuska ɗauke da mamaki Ameena tace.
"Raleeya farincikin me kikeyi haka?." Murmushi me kama da dariya, Raleeya tayi, cike da farinciki tace.
"Ranan yau ta kasance ranar farin cikinmune baki ɗaya mu yau ranace mafi kyau acikin rayuwarmu, bansan tayaya zan nuna miki farincikin danake ciki ba Aunty Ameena".
Idanu Ameena ta zuba mata, hakanan taji zuciyarta na bugawa, cike da zaƙuwa tace. "Meyake faruwane Raleeya, dan Allah faɗamin, inajin kirjina na bugawa da sauri-sauri" Murmushi Raleeya tayi, tare da yi mata nuni da ɗakin Hayatuddeen, cikin farinciki tace.
"Kishiga ɗakin Hayatuddeen Hamma Saifuddeen nacan." Jin haka yasa Ameena cikin sauri ta nufi ɗakin Hayatuddeen ɗin. A ƙarfi ta tura ƙofar ɗakin ta shiga.
Jin motsin shigowan mutum yasa su dukansu suka kai kallonsu ga ƙofan shigowa ɗakin. Idanu ta zubawa Saifuddeen dake kwance wani irin tsorone ya rufeta ganin yadda yake konce to farin cikinme Raliya keyi bata bayan kuma taga alamun mijinta ba lfy, bata kao aya a tunanin nataba taga, yana miƙo mata hannu, cikin sassanyar muryarsa mai nuna baida lfy yace.
" _Aminatu_ bani Adeel." Kamar amafarki haka Ameena taji sautin muryarsa acikin kunnuwanta, a razane taɗan zaro idanunta, sosai jikinta ya ɗauki rawa, bakinta na rawa haka ma muryarta tace.
"Abban Adeel, kaine kake magana ko kuwa gizo ido da kunnuwana suke yimin."
Idanunsa yaɗan lumshe tare da jinjina mata kai, cikin son bata ƙarfin guiwa yace.
"Ni ne Aminatu, ba gizo kikeji ba."
Cikin wani irin yanayin farin ciki da wani irin gudu mai kamar sassarfa ta ƙaraso cikin ɗakin tare da faɗawa jikinsa ta ruggumeshi gam-gam kamar mai tsoron a kwace mata shi, cikin tsananin farin ciki tasaki wani irin kukan farinciki, sam ta ma manta da su Dr.Adnan dake cikin ɗakin.
Hannunshin yasa ya dai-dai ta kanta dake kanshi cikin sanyin murya tace.
"Aminatu Zaki ƙara ɓalle bayan ki rasa na yin lilo gaba".
Cikin wata irin yar salama da jin daɗi tasa hannu ta shafi gefen fuskarsa, cikin matsanancin farinciki tace.
"Alhamdulillah Ya Allah, Alhandulillah." Murmushin ƙarfin hali yaɗan sakar mata, tare da sanya hannu ya amshi Adeel, dake ta dariya yana wutsil-wutsil da ƙafafunsa kamar yasan farin cikin da sukeyi.
Rungume yaron nasa yayi, yanajin wani matsanancin farinciki acikin ransa.
Ameena kuwa ɗan sharce hawayen dake cikin idanunta tayi, tuna cewa su Dr Adnan na ɗakin yasa ta ɗan janye jikinta baya, tare da cewa.
"Abban Adeel yaushe ka fara magana?." Kasa amsa mata yayi saboda yanda yaji bayansa na wani irin duka, idanunsa ya rumtse da ƙarfi sosai, Dr Adnan ne yaɗan riƙe masa hannu, tare da zaro wayarsa, numbern Dr Aleeyu ya laluɓo, sannan ya danna masa ƙira. Bugu ɗaya kuwa ya ɗauka.
Bayan sun gaisane Dr Adnan ya ɗan gyara zamansa.
Cikin nutsuwa yacewa Dr Aleeyu.
"Sir jikin Saifuddeen ne fa ya tashi sosai fa, amman kunnuwansa kuma sun buɗu yanzu duk wani motsi yanaji, sai-dai amma tun ɗazu yake ta complain cewar bayansa ya riƙe, yanzu haka ko zama da kyau baya iyawa, nakasa gano kan matsalan nasa, dan harma yace wai ko zamu koma India ne." Sosai Dr.Aleeyu yaji daɗin buɗuwar kunnuwan Saifuddeen ɗin, saidai jin wata matsala da ta kunno kai duk sai yaji babu daɗi acikin ransa, sai-dai yasan hakan ma wani matakin nasara ne a jinyar tasa dogon numfashi yaja cikin kulawa yace.
"Ai dama lokacin komawarsa india yayi harma ya wuce, bansan me yasa bayason komawa asibiti ba, lalle ya zama dole amaidashi india, dole anjima zan biyo jirgi nazo, zan taho da wasu allurai da magunguna wanda xasu ɗan rage masa pain kafin a samu wucewa dashi India, ka gayawa Ahmad ya fara nema musu damar tafiya tun daga yanzu yayi musu bukin ta online."
Cikin jin daɗin hakan Dr. Adnan yace.
"Okay Sir shikenan sai kazo".
da haka sukayi sallama, yana ajiye wayar kuwa Ummi ta shigo cikin ɗakin.
Ganin Ummi yasa Ameena tashi da sauri ta ƙarasa jikin Ummin cikin tsananin farinciki tace. "Alhamdulillahi Ummi, kunnuwan Abban Adeel sun buɗe ya fara jin magana, Alhamdulillah Ummi, tabbas Allah abun godiya ne."
Kai Ummi ta jinjina tare da cewa.
"Tabbas Ameena Allah abun godiyane, gashi cikin ikonsa ya buɗe masa kunnuwansa." Murmushi Ameenan tayi tana kallonsa, ji take kaman ta maidashi cikin jikinta tsabar murna.
Dr Adnan ne yayiwa Ummi bayanin yanda sukayi da Dr Aleeyu, sosai Ummi taji zuciyarta, ta gamsu da zuwan Dr Aleeyun saboda, yanda taga Saifuddeen nacije laɓɓansa, tasan yanajin ciwo sosai.
Ameena ne ta kalli Umm'in, cikin kulawa tace.
"Ummi ina Zaleeha?" Ɗan jim Ummi tayi cike da tausayawa tace. "Zaleeha bata da Lafiya, yanzu haka tanacan sashin Saifuddeen, akwance sai rawan sanyi take, zazzaɓi ne me zafi ya sauƙar mata, so nake idan Dr Adnan ya gama da Saifuddeen, sai muje yaɗan duba ta."
Idanu Ameena ta zaro tare da cewa. "Subahanallah, Allah sarki bari naje na duba ta, ko akwai wani taimakon da zan iya bata".
Kai Ummi ta jinjina, sannan Ameenan ta juya nufin fita,
sai kuma ta tsaya jin an riko hannunta ganin Saifuddeen ne yasa ta matsoshi cikin lumshe ido yace.
"Aminatu Kada ki ce mata kunnena ya buɗu kuma ina iya mgna, kinji ko Ummu Adeel".
Cikin jin daɗin yadda yake yawan kiranta da yadda yake kiranta Aminatu kana da mmki ta gyaɗa kai a ranta tace.
"To meyasa za'a ɓoye mata wannan abin farin ciki, to ko dan bata da lfy ne".
Kai kawai ta gyaɗa kana ta juya ta fita daga cikin ɗakin.

Kamar yanda Ummi ta faɗa mata kuwa, kaitsaye sashin Saifuddeen ɗin ta wuce, ganin bata ganta afalo ba, yasa tayi tunanin cewa tana ɗaki.
Tana shiga kuwa ta samu Adda Rahama zaune agefenta, dan har yanzu Zaleehan bata daina sakin sheshsheƙan kuka ba.
Ƙarasowa cikin ɗakin tayi, cikin kulawa ta zauna abakin gadon tare dakai hannu taɗan taɓa wuyan Zaleehan, jin jikin Zaleehan zafi zau yasa tace.
"Subahanallahi Ammin Adeel sannu ya jikin naki?".
Kai kawai Zaleeha ta iya jinjina mata dan batajin zata iya wani dogon magana.
Ɗan sake taɓa jikin Zaleehan tayi, tare da duban Adda Rahama, tace.
"Adda Rahama miyene yake damunta bayan zazzaɓi?."
Ajiyar zuciya Adda Rahama tayi, asanyaye tace.
"Tace min tanajin jiri da kuma ciwo acikin jikinta, danko tafiya ma batayi da kyau, nadaiyi mata sit bath, amma gashi nan dai sai rawan sanyi take." Wani irin ƙaton abune ya daki ƙirjin da ran Ameena, har saida taji kanta yaɗan juya mata duhu ya gilmawa ganinta, take ta gano matsalan Zaleeha'n, murmushi taɗanyi tare dayin ƙasa da kanta tana jin wani sassanyan abu a ranta da zuciyarta da sauri ta katse shaiɗan da yin tasbihi, gaba ɗaya ji tayi jikinta yayi sanyi, sai-dai kuma yauɗin ranace ta daban agaresu ranace ta farin ciki su budurcin Zaleeha ya zame musu abin al'fahari tunda sanadin ƙarɓarsa a samu gagarumar nasara a rayuwar mijinta abin soyuwa.
Wayarta ta ciro inda ta laluɓo numbern wata ogarsu Dr Fateema, wanda take nan kusa dasu dan gidanta baida wani nisa, Dr Fateeman na ɗagawa, ta matsa ɗan gefe tare dayi mata bayani, kan cewa suna da patient agida, sannan tayiwa Dr Fateeman bayani, kan cewa ita bazata iya aikin ba.
Da yake Dr Fateema'n, macece mai sauƙin kai hakan yasa tace wa Ameenan gatanan zuwa, dan dama tana gida bata fita ba. Babu wani jimawa kuwa, saigata tazo, ganin yanda jikin Zaleehan yayi zafi sosai yasa tace su bata waje, zata dubata.

Babu musu kuwa Adda Rahama da Ameena suka koma falo.
Duba Zaleehan tayi, sosai, ganin babu rauni sosai aƙasan nata yasa ta bata wasu magunguna tasha, wata alluran kashe zafi da zogi tayi mata, sannan ta ɗaura mata drip tare dasa alluran zazzaɓi.
Cikin abun da baiwuce 10 minute ba bacci ya ɗauki Zaleeha.
Dr Fateema na fitowa daga ɗakin su Ameena suka nufota cikin sauri. Ameena ce tace.
"Dr Yajikin nata?." Ɗan murmushi Dr Fateema'n tayi, tare da cewa.
"Ku kwantar da hankalinku, jikinta da sauƙi, dan harma ta samu bacci, kuma bawani babban damuwa bane, kunsan dama yawanci irin haka yana faruwa idan akayi dis virgin ɗin mace, mussamman idan ya zamana namijin yaje mata da ƙarfi, ko kuma manhood ɗinsa ya zamana, yafi ƙarfin privet part ɗinta, wanda sai ahankali ne kuma zata saba, thank god ma babu rauni sosai ajikinta, yanzu dai tana da buƙatar hutu, so please abarta taɗan huta." Jinjina kai sukayi su dukansu cike da gamsuwa,
Ameena kuwa ido ta rumtse jin hawayen kishi zasu zubo mata a ranta tace.
"Ashe da kam duk kishin banza nakeyi nagodewa Allah dayasa bai kusanceta tun ina kan jahilin kishin nanba na sani da mutuwa zanyi. Har waje kuwa Ameena ta raka Doctor ɗin.
Saida taga tafiyarta sannan ta dawo gida tana tafe tana mgnar zuciya da share hawaye.
"Ai kam dole taji azaba dan Abban Adeel ingarman namiji ne".

Ganin Zaleehan na bacci, yasa Adda Rahama jawo ƙofan ɗakin ta rufe, sukuma suka koma sashin Ummi.

Suna zuwa kuwa suka samu Raleeya ta kammala breakfast, da ƙyar Adda Rahama tasa Saifuddeen ya ɗanci wani abu acikinsa, dan yace musu ji yake bayansa na harbawa. Ɓangaren Zakariyya kuwa suna gama waya da Hayatuddeen, cikin gida ya wuce, anan falon Baba Malam yasamu Mama da kuma Mamy, harma da Ya Ahmad, anan yake sanar musu cewa, jikin Saifuddeen ɗin ya tashi.
Sosai Baba Malam ya shiga damuwa, nan yace su Mama su shirya idan akayi sallan azahar zasuje su dubashi.


Ameena ma ta kira Daddy ta sanar mishi batun jikin Saifuddeen kuma yace yana nan tafe gobe,
hakama ta kira Mamanta ta sanar mata, inda ta haɗata da Ummi suka gaisa, ta jajanta mata jikin Hamma Saif ɗin kana tace suma in Allah ya nufa

Please Login or Register in order to submit comment