Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

*GARKUWAR FULANI*
10/4/20, 7:04 PM - Mmn Khalid: Zazzafan numfashi ya sauƙe, da ƙarfi ya fusge wayar daga hannun Saifuddeen, sosai hankalinshi ya tashi ransa yayi mummunan ɓaci dan ganin kalaman da Zaleeha ta rubutawa Saifuddeen tacikin text message, wani irin ɓaƙin ciki da ɓacin raine suka tokarewa Ahmad maƙoshi, shikam baisan meyasa Saifuddeen ya maƙalewa Zaleeha ba, yarinyar da bata ganin mutumci da ƙimarsa ko kaɗan, yarinyar da ta maida rashin kunya man shafawanta.
Ɓata fuska Saifuddeen yayi tare da miƙowa Ahmad hannu, alaman ya bashi wayarsa.
Fuska Ahmad ya haɗe sam babu alaman wasa akan fuskarsa haka ya juya ya nufi hanyar fita daga ɗakin, da kallo Saifuddeen ya bishi, wani ɗan guntun murmushi ya sake, haƙiƙa yasan Ahmad sam bayason aurensa da Zaleeha, ya kuma san dalili, amma yasan nanda wani lokaci kaɗan Ahamad ɗin zai fahimta.
Cikin   zafin zuciya haɗi da fusata Ahmad ya nufi ɓangaren Ummi.
Zaune Ummi take akan kujera gefenta kuwa Raliya ne zaune tana ta yabawa da koda d'inkunan zafafan laces ɗin dake gabanta, wanda Saifuddeen ne ya saya musu donyin fitan biki.
Murya can ƙasan maƙoshi Ahmad yayi sallama, inda ya kutsa kansa cikin falon, fuskar Ummi cike da fara'a ta amsa masa, saidai kuma yanayin yanda taga fuskarsa yasanya taji ba daɗi, domin Ahmad mutum ne me yawan fara'a, baƙaramin abu bane zai sanya kaga ya ɓata fuska.
Raliya kuwa ji tayi gabanta ya faɗi, sakamakon ganin mood ɗin mijin nata.
Zama Ahmad yayi akan sofa tare da tanƙwashe ƙafafunsa.
Dubansa Ummi tayi cikin sanyin murya haɗi da bayyanar da damuwarta tace.
"Ahmad lafiya kuwa?."
Ɗago idanunsa wanda sukayi jajur yayi ya kalli Ummin tare da miƙo mata wayar Saifuddeen dake hannunsa.
Amsan wayar Ummi tayi tare da kai dubanta ga screen ɗin wayar, wanda har yanzu screen ɗin keda haske bai ɗauke ba, wanda shi Saifuddeen azatonsa Ahmad baisan security ɗinsa ba, shiyasama yabar Ahmad yatafi da wayan, shikuwa Ahmad dama tun tuni yasan securityn Saifuddeen ɗin, don ranan agabansa Saifuddeen yacire wayartasa a security.

Idanu Ummi ta ƙurawa rubutun dake kan screen ɗin wayar, sannu ahankali take karanta saƙon, lokaci guda jikinta ya ɗauki wani irin rawa, take yanayin idanunta suka sauya daga farare zuwa ja,  aƙalla ta maimaita karanta saƙon yafi sau uku, batare da ta sani ba, sosai zafafan baƙaƙen maganganun da aka rubuta cikin saƙon ke yawo acikin brain ɗinta.
Babu abun dayafi ɗaga mata hankali kamar inda Zaleehan ta rubuta cewa.
```"Ka turo iyayenka su janye batun aurena da kai! Su zo su kwashi wannan tarkacen da kasa aka tarkato aka kawo mana jidali. In kuma kaki yin hakan ka kuskura ka bari akayi auren nan aka kawoni mushen gidan kunnan to.
Wallah Allah kenan``` Saifuddeen, in ka bari akayi auren nan cikin biyu za'ayi ɗaya ko in mutu ko ks matu!!!."

Sosai tunanin Ummi ya tsaya cak, wani irin matsanancin tsorone ya daki zuciyarta, sosai kalaman Zaleeha suka ɗaga mata hankali, tabbas tanayiwa ɗanta Saifuddeen tsantsar so, bakuma tason wani abu da zai cutar dashi,  tayaya ma amatsayinta na Uwa zata zuba idanu tana kallo ɗanta yakai kansa ga inda ake neman halakasa, tabbas acikin kalaman na Zaleeha tagano cewa bata ƙaunar Saifuddeen ko kaɗan,  sam bazata taɓa bari Saifuddeen ya auri macen da take da bushashshen zuciya ba.
Hawayen da suka cika idanunta tasoma ƙoƙarin shanyewa, cikin raunin daya bayyana akan fuskarta ta dubi Ahmad.
Shi ɗinma Ahmad dubanta yayi, cikin rauni yace.
"Ina takaicin tsananin son da Saifuddeen kewa Zaleeha, bata sonshi Ummi sam bata ƙaunarsa, bata ganin ƙima da darajarsa, tun awaje tana faɗa masa mugayen kalamai irin wannan inaga kuma idan anyi auren? ba fata nake ba Ummi amma sam banason abun dazai wargaza mana farin cikin mu, Saifuddeen kamar jigo yake agaremu baki ɗaya, bazan iya zuba idanuna naga ya jefa kansa cikin mawuyacin hali ba, Ummi zuciyar Zaleeha tayi zurfi sosai wajen tsanar Saifuddeen, saboda haka zata iyayin komai idan ya aureta."
Ɗan tsagaitawa da maganan yayi tare da maida ƙwallan da suka cika idanunsa, ci gaba yayi da cewa.
"Ai Nakasa Ba hauka bace bare tace baida hankali bazata iya zama da shiba, kuma Nakasar Saifuddeen bashi yake nuna cewa ya kasa ba,   mene aibun Saifuddeen Ummi? shin laifine don Allah Ya jarrabeshi da nakasa? ko kuwa laifine don yazamo kurma kuma gurgu, shi nakasashshe ba mutum bane kenan? Wallahi Ummi Saifuddeen bai dace da Zaleeha ba, saboda bata yarda da ƙaddara ba, hartanajin cewa ita watace, wacce ajinta ya ɗara nakasashshe, ta manta cewa da me lafiya da kuma nakasashshe duk halittar Allah Ne."

Ajiyar zuciya Ummi ta sauƙe tare da sakin wani murmushi wanda yafi kuka ciwo.
Cikin tsananin tausayin ɗannata Saifuddeen da irin ƙaddaran da Allah Ya ɗauro masa tace.
"Inajin tsoro Ahmad, Inajin tsoron abun da zai faru nan gaba, bana fatan yarinyarnan  Zaleeha ta cutarmin Saifuddeen cutarwa mafi muni."
Still ajiyar zuciya ta kuma sauƙewa, tare da miƙewa tsaye,  duban Ahmad takumayi cikin sanyin murya tace.
"Ahmad zanyi abun da ya dace, abunda  kowacce uwa zatayi dan kare rai da lafiyar danta zanyi abinda ya kamata ace  tayi a matsayina na uwa!."
Tana gama fad'in haka ta juya ta nufi hanyar ɗakinta.

Tuni hawaye sun wanke fuskan Raliya, duk da cewa bata karanta saƙon da Zaleehan ta turowa Saifuddeen ba amma tabbas ta fahimci duk abun dake faruwa, daga cikin kalaman na Ummi da kuma mijinta Ahmad.
Dubanta Ahmad yayi, itama kallonsa take, yayinda hawaye ke tsiyaya daga cikin idanunta, shin menene aibun Hamman'ta don yakasance gurgu kuma kurma? shima mutum ne kuma Namiji kamar kowa, yana da cikakkiyar lafiyansa na ɗa namiji, sannan gurguntan sa bazai zama kasawa agareshi ba, don meyasa Zaleeha zata ƙisa?
Kai Ahmad ya girgizawa Raliya alaman ta daina kuka.
Kasa jurewa tayi, hakan yasa ta faɗa cikin jikinsa tare da sakin kuka mai sauti.
Rungumeta yayi ƙam tare da sake jawota jikinsa,  nan yamiƙe tsaye tana ajikinsa suka nufi hanyar barin falon.
Suna fita suka yi karo da Hayatuddeen wanda shigowarsa cikin gidan kenan, sanye yake da white t shirt da kuma 3 guater jeans, hannunsa riƙe da wayarsa ƙiran Samsung yayinda kunnensa ke saƙale da earpiece,  yana ganinsu yaɗan yi turus tare da turo bakinsa gaba, har acikin ransa shikam yagaji da ganin Yayar tasa Raliya da Ahmad manne da juna sunashan soyayyarsu kamar tattabaru, kullum haka yake ganinsu liƙe da juna kamar wasu tif da taya.
Hararansa Raliya tayi da jajayen idanunta,  sake kwaɓe fuska yayi yana shirin yi musu halinnasa na shagwaɓa ne, Ahmad ya miƙo masa wayar Saifuddeen, batare da Ahmad ɗin yace komai ba yaja Raliya suka nufi ɓangarensu.
Da kallo Hayatuddeen ya bisu har suka ɓacewa ganinsa,  bakinsa ya taɓe ƙasa-ƙasa yace.
"Hegu fitinanu, kuyi dai nima dana ƙara girma, ai dai zanyi auren nan ehe, don haka duk wani me ɗagamin kafaɗa ma gwara ya daina, nima ai zanyi auren bawai ba zanyi ba."
Haka ya nufi ɓangaren na Saifuddeen yanata ƙunƙuni aransa.
Koda ya ƙarasa part ɗin a parlour ya had'u da Salisu dake saurin fita, dan sunyi mgna da Saifuddeen kam batun Rashida na son su kai musu kud'in walima, so shine ya fita da sauri dan kai mata kud'in,
cikin girmamawa yace.
"Ina kwana Ya Salisu."
"Lafiya lau Auta ya sakalci."
Salisu ya amsa mishi ba tare da ya tsaya ba,
Murmushi Hayatuddeen yayi tare da cewa.
"Manyan angwaye sai b'are-b'are suke uwa hanji a langa."
yana musu tsiya ya wuce ya nufi bedroom d'in Hamma
Saifuddeen din nashi zaune ya sameshi akan wheelchair ɗinsa, inda ya tasa laptop ɗinsa agaba ƙiran company'n apple yana dannawa.
Akan cinyar Saifuddeen ɗin ya ɗaura wayar tare da yin super ya faɗa kan lallausan gadon na Saifuddeen, lumshe idanu yayi yana me shaƙan daddaɗan ƙamshin na Hammansa, aransa yana fata ace watarana shima yazama kamar hamman nasa.
Saifuddeen kuwa murmushi kawai yayi tare da ɗaukan wayar tasa ya duba, ganin still akan message ɗin Zaleeha yake, yasanyashi sakin murmushi, domin jikinsa ya basa cewa Ahmad bai cire wayan a security ba balle yayi amfani dashi.
Cigaba yayi da aikinsa,yayinda time to time yake sipping exotic juice ɗin dake gefensa.


A wunin ranan masu gyarannan suka gama komai na side d'insu Saifuddeen kafin azahar sun gama komai na side d'in masu buga kitchen cabinets ma sunzo sun shirya komai ras.
masu fenti kuwa sun fento ko ina na gidan luggu da sak'o da yake sunada yawa kuma akwai kayan aiki kafin magrib dai sun gama komai gidan ya zama sabo fil yayi ras sai shek'i yakeyi da k'amshin sabon fenti.
In da akayiwa gidan fentin Coral color iya rabi daga k'asa kuma dama tayis ne manne royal color hakan yayi masifar kyau ya haska gidan,
cikin gidan kuwa Side d'in Ummi pumpkin color akasa daga saman pop d'in daga k'asa kuma navy blue mai shek'i,
hakama saman inda Hayatuddee yake, inda Saifuddeen yake kuwa ba'a tab'abashi ba dan bai jimaba,
Sai inda Raliya take mai mak'otaka da inda za'a ake shirin sa Zaleeha, mint green and white akayi mata komai yayi ras, sai wojen part d'in duka da aka fente da dark brown and daga d'an k'asan kuma tayis ne manne a jikin ginin,
sai farfajiyar wurin da yakeda d'an zagayeyyen ma dai-daicin lambun da yakeda yabanyar grass carpet wanda yayi kore shar, sai bishiyar mangoro mai fad'i da tsananin duhu wanda yake baje kan bishi yoyin dabino da ayaba da gwaiba dake gefenshi dan bishiyar mangoron bata da tsawo sosai, a k'asan kuwa fulawowi ne jere wanda sune suka zama garkuwan wurin sai ya zama in kana cikin wurin baza'a hangoka ba, cikin wurin kuwa sai wasu fulawi masu halittar tim-tim in ka gansu kamar kujeru, kana ga kan pompoms guda biyu wanda dasu akeyiwa wurin ban ruwa, daga tsakiya ciluk kuma wani k'arfe ne mai tsawo wanda yake manne da fitilar sola mai d'an karen haske.
sai irin kujerun silver nan da ake ajewa a asibitoci da wuraren shak'atawa, kujerun ne suka zageye wurin da k'asanshi ke wadace da koriyar ciyawar, ga sanyin tsirrai gana ruwan dake gudana a wurin ga na inuwar bishiyar mangoro dana dabino da gwaiba, uwa uba ga sanyin bishiyoyin ayaba kusan guda biyar da suka zagaye wurin,
daga cikin wojen wurin kuwa an lailayeshi da intalak, sai babban baranda mai fadin da aka laileyeshi da tayis fari k'al.
kana cikin parlour kuwa yasha fenti purple and cerise color sosai parlour yayi kyau hakama cikin two bedroom d'innan, kitchen d'inta kuwa an k'awatashi da durowowi masu kalar pink and white sosai aka k'awata kitchen d'in.
komai fa yayi ras sai shek'i da k'amshi gidan keyi,
hakama fulawin gidan duk anbi an musu sassariya an dai-dai tasu,
garden dake bayan part d'in Ummi ma an gyarashi sosai,
gida dai ko yanzu amarya tazo...

Juyi take tayi akan makeken gadon nata,  gaba ɗaya damuwa ya cika zuciyarta, wani irin zafi takeji acikin ƙirjinta,  rumtse idanunta tayi, take wasu irin hawaye masu zafi suka kwaranyo daga cikin idanunta, ya zatayi? wazata kaiwa kukanta ya share mata hawaye?  burinta shine koda mutum ɗaya ne ya fahimceta, amma ankasa samun hakan,  sosai zuwa yanzu ƴan uwanta keyi mata kallon wanda aljanu suka kama,  laɓɓanta ta ciza tare da sakin wani marayan kuka mai sauti, ta lura shi wannan nakasashen jikinshine a nakasashe zuciyarsa cike take da jarumta, dan ta fahimci duk baraza da ihu da hargowar da take mishi akan ransa da rayuwarshi a banza, babu alamun karaya bare fargaba ko d'igon tsoro, asalima sai tsoronshi dake cika mata idanu muddin ta kalli kwayar idanunshi koda na one second ne.
Juyi ta kumayi tare taune lip d'inta na k'asa ayanzu tafi buƙatarsa fiye da dacan baya, fatanta burinta, muradinta duk sun ta al'laƙane akansa, sam soyayya batayi mata adalci ba da ta jefata cikin mawuyacin hali,  hannunta ta sanya ta dafe dai-dai saitin zuciyarta dake bugawa, tanajin sonsa na fusgarta, wani irin maganaɗisun ƙaunarsane ke ƙara janta akowacce rana,   yaya zatayi da soyayyarsa dake ƙoƙarin fasa mata zuciya?
Ƙaddara tazo mata ayanda bata taɓa zata ba, ƙaddara ta zautar mata da tunani, har takai ga tanayin komai cikin zaucewar hankali.
Sosai tayi hugging pillow, ahankali taci gaba da rera kukanta, saida tayi kuka sosai kafun wani wahalallen bacci ya ɗauketa.

Washe gari.

Zaune suke su dukansu akan babban dinning table ɗin dake  cikin falon, Saifuddeen, Hayatuddeen da kuma Raliya, sai Ahmad wanda shigowarsa cikin falon kenan.
Ahankali Saifuddeen ke tsakalan abincin yana kaiwa bakinsa,  gaba ɗaya hankalinsa naga wayarsa dake riƙe ahannunsa, sosai yashiga busy tunda aka fara shirye-shiryen bikin, dan ma yanada tarin aminai dake ji da komai wani abinma sai dai kawai yaga anyi sosai suke shiryawa bikin inda ya kama yau saura kwana uku bikin.
Tunani yakeyi akan tirelar dake can harabar gidan nasu wanda aka kawo kayan Zaleeha. Tirelan cike yake dam da kayan Zaleeha wanda Ya Ahmad yayi mata komai na duniya wanda amare zasu buk'ata.
Wanda Habu ya bada shawaran kada a sauk'e kayan a gidansu a wuce dashi gidan Saifuddeen d'in acewarsa k'arin jidaline.
to koda ya gayawa Ahmad sai suka bawa driver'n tirelar hak'uri akan zasu biyashi abar kayan a ciki sai an gama gyaran side d'in amaryar sai su sauk'e kayan to su kuwa jin za'a biyasu yasa suka amince.
to an gama gyara a bisa tsarinsu dai gobe za'a zo a sauk'e kayan sannan tuni Salisu ya nemi masu had'a kayan su shirya za'a biyasu dubu saba'in kud'in aikinsu kana Maryam da Aunty Lubna zasu zo su kimtsa komai duk a goben...

Ummice ta ƙaraso cikin falon, cikin shirinta tsab, sosai tasha ado irin wanda ya bayyana cikar kamalarta, tana ƙarasowa cikin falon gaba ɗaya kallon ƴaƴan nata ya dawo gareta.
Ahankali Saifuddeen ya ɗago da kansa ya kalli Ummin nasa, ganin yanda tayi masa kyau yasanyashi sakin murmushi, tare dayi mata duban tsab, domin yaga alaman cewa fita zatayi.
Ƙarasowa dinning area'n Ummi tayi, hannu tasanya ta shafa kan autanta Hayatuddeen dake ta faman zuba wa cikinsa, spiring roll.
Fuska Saifuddeen ya kwaɓe tare da karyar da wuyansa gefe,
Matsanancin tausayinsa ne ya cika zuciyar Ummin, don sarai ta fuskanci abun da yake nufi, alamune dake nuni yanada yar damuwa can k'asan zuciyarshi wanda kuma baya son ta sani, ita kuwa in taga hakan bata matsa mishi kan ya sanar mata sai dai takanyi k'ok'arin sashi farin ciki, sai dai tasan yanzu koma menene aransa baya rasa nasaba da Zaleeha,
hannu tasa ta shafa kansa shima.
Murmushi yayi inda cikin body language ɗinsa yayi mata alaman da ina zataje.
Itama murmushin tayi tare da gyara tsayuwarta, duban ƴaƴan nata tayi dukansu, tare dayi musu bayani akan zuwanta Dukku da ta tsarashi yau da safe, sannan kuma ayau ɗin zata dawo, sosai suka ɗanyi mamaki sai-dai kuma sanin cewa ana tsaka da shirye-shiryen hidiman biki ne yasanya basu damu ba, don atunaninsu wani uzurine wanda ya shafi bikin zai kaita Dukkun.
Haka Ummi tayi sallama da su, inda dukansu suka rakota har compound ɗin gidan.
Saida suka ga tafiyarta kafun su dukansu suka koma cikin gida.

Kusan ƙarfe shabiyu da wasu ƴan mintuna Ummi suka iso cikin garin na Dukku me al'barka.
Kaitsaye gidan Bappa Ali suka sauƙa.
Sosai Aunty Mina tayi murnar ganin Ummin, nanfa lokaci ɗaya tacika mata gabanta da kayan ciye ciye, hadda dangin su fura da nono,
Sosai Ummi da Auntyn ke shan hiransu, kasancewar Bappa Alin bayanan, sunje gaisuwan wani abokinsu wanda bashida lafiya, shida Malam Ashiru.
Cikin ikon Allah Kuwa Ummi na idar da sallan azahar saiga Baffa Alin ya shigo, koda yaga Ummin yaji daɗi, saidai kuma zuciyarsa ta basa kan cewa ba lafiya ba, domin lafiya ƙalau babu abun da zaikawo Ummi Dukku ana tsaka da shirye shiryen bikin Saifuddeen kana kuma jiya-jiya nan sukaje amsa kiran nata.
Bayan sun gaisa da Bappa Alin ne Ummi ta gyara zama, lokaci ɗaya damuwa ya bayyana akan fuskarta, dubanta Baffa Ali yayi cikin sanyin murya yace.
"Lafiya kuwa? badai wanine bashida lafiya acikin gidan ba?."
Kai Ummi ta girgiza cikin ƙunan zuciya tace.
"Akan maganan auren Saifuddeen da yarinyar nanne, kamar yanda na faɗa muku kaida Malam Ashiru jiya cewa yarinyar nan batason Saifuddeen, tana masa barazanar matuƙar ya aureta zata kasheshi, to fa yanzu abin k'aruwa yakeyi dan bata daina ba, awancan karon kun tausasheni ta hanyar cewa nayi haƙuri nabari ayi auren, na haƙura badon raina yana soba, saidai ayanzu bazan iya haƙura ba, inamatuƙar jin tsoron abun da zai faru anan gaba, inatsoron rasa Saifuddeen, Bappa Ali kasan yanda Saifuddeen yake awojenmu dan Allah Kayi wani abu!."
Nan ta kwashe duk kan abun daya faru da kuma text message ɗin da ta karanta wanda Zaleehan ta turowa Saifuddeen ta faɗa masa.
Ajiyar zuciya maiƙarfi Bappa Ali yayi, tare da sanya hannu ya ɗan dafe kansa, tabbas zuwa yanzu yakamata yabita maganan Ummi, don kuwa tabbas ayanda Zaleehan ke faɗa da kuma bayyana tsanar Saifuddeen afili tabbas zata iya aikata koma miyene don ganin ta cutar dashi, tabbas shima zuwa yanzu kam yafara tsorata da al'amarin.
Ɗan jim yayi tare da gyara zamansa, cikin kulawa yace.
"Insha Allahu Ayau yau ɗinnan zan ɗauki Malam Ashiru mu tafi Gombe tun lokaci bai ƙure mana ba, haƙiƙa wannan lamari yayi tsaurin da dole sai manya sun shiga cikinsa, ki kwantar da hankalinki, Insha Allah zamuje mu samu shi Malam ɗin, zamuyi magana ta fahimta dashi, bakuma zamu ɓoye masa komai dake faruwa ba, tabbas nasan zai fahimce mu, shi kuma Saifuddeen Allah yabasa wata mace tagari wacce ke ƙaunarsa!."
Ajiyar zuciya mai ƙarfi Ummi ta sauƙe tare da cewa "Ameen!."
Har cikin ranta taɗanji sanyi, haka dai suka ɗan taɓa hira kaɗan kafun daga bisani tace zata koma.
Haka suka rakota har wajen mota inda Sule driver ke jiranta.
Haka Ummi suka kama hanyar shigowa cikin garin Gombe zuciyarta wasai, tanajin kamar ta raba Saifuddeen da ƙaya.
Tafiyar 1 hour ne kacal ya kawosu Gombe, inda ta koma gida zuciyarta cike da salama, saidai kuma ta wani ɓangare, cike take da tausayin Saifuddeen, domin kuwa koda sau goma zata kalleshi, to akowani kallo ɗaya, saita hango zazzafar ƙaunar da yakeyiwa Zaleeha acikin ƙwayan idanunsa.
Amma addu'a bata bar komai ba. Zata tayi masa addu'a akan Allah Ya musanya masa da mafi alkhairi.

Su Bappa Ali kuwa ƙarfe biyar dai-dai suka kamo hanyan zuwa garin Gombe shida Malam Ashiru, daga cikin abun da Ummi ta faɗa masa, ko ɗaya bai rage ba, haka ya labartawa Malam Ashiru komai, shikansa Malam Ashiru saida yaji zuciyarsa tayi masa ba daɗi, tabbas yasan sharrin ƙiyayya, ƙiyayya bata da daɗi sam, kuma takan rufewa mutum ido, yayi duk abun dayaga dama, musamman ma ga mace da auren mijin da bata so dan haka shima ya yarda baza'ayi wannan aurenba.

Ƙiran sallan Magriba acikin garin Gombe tayi musu, nan suka tsaya sukayi sallah, inda suna idarwa suka nufi gidan Dirankaɗi, wato Baban Ishaq kenan, kasancewar tunkan su taso sunyi masa bayanin komai sun kuma sanar dashi zuwansu, inda shikuma ya ƙira Baba Malam ya shaida masa cewa da anyi sallan Isha za su zo.
Koda suka ƙarasa gidan na Dirankaɗi, anan sukayi sallan Isha, daganan suka wuce zuwa G.R.A wato unguwar su Zaleeha.
Tarba me kyau suka samu daga Baba Malam, inda ya sauƙesu acikin babban falonsa, nan yasa aka cika musu gabansu da kayan ciye ciye,
hira kaɗan suka ɗan taɓa, kafun Dirankaɗi ya gyara zama inda ya fuskanci Baba Malam, cikin nutsuwa haɗi da halin dattako yashiga labartawa Baba Malam abun dake faruwa, da irin saƙon text message din da Zaleehan ke turawa Saifuddeen wanda suke ɗauke da barazana haɗi da baƙaƙen maganganu, inda ya ɗora da cewa.
"Kayi haƙuri Malam, amatsayinmu na manya masu hankali, baikamata ace mun zuba ido hakan na faruwa ba, haƙiƙa duk auren da akace akwai ƙiyayya acikinsa to mafi al'khairi shine barinsa, tabbas babu wani uba dazai so ɗansa ya rasa iri awannan gida naka mai cike da kamala haɗi da tarbiya, saidai kuma babu yanda zamuyi ɗaukan ƙaddara ya zame mana dole, saboda hakane mukazo baka haƙuri, kayi haƙuri Malam bisa dole munjanye nemawa Saifuddeen auren Zaleeha da mukayi, fatanmu shine Allah ya bawa kowannensu abokan zama nagari!."
Ajiyar zuciya Baba Malam ya sauƙe tare da ɗanyin jigum, tabbas Zaleeha nason dasa masa ciwon zuciya, sannan tanason zubar masa da ƙima da kuma mutumcinsa a idanun jama'a, saidai kuma yayi al'ƙawarin bazai taɓa bari hakan ya faru ba, gyara zamansa yayi tare da duban su Baffa Ali, cikin dattako haɗi da tausasa zance yace.
"Babu wani abu dazan faɗa muku face haƙuri, kuyi haƙuri, haƙiƙa nine nan mahaifin Zaleeha, sannan nike da ikon bada aurenta ga koma waye, tuntuni nakuma bada aurenta ga Saifuddeen, kamar yanda Zaleeha take ƴa awajena, hakama Saifuddeen, shi ba iya ɗalibina bane kaɗai, inajinsa kamar jinina, saboda haka kuyi haƙuri, kujanye batunkun fasa auren, Zaleeha ƴatace kuma inada ikon tanƙwarata duk yanda naga dama, kuyi haƙuri ku ɗauka cewa duk waƴannan abubuwan da takeyi yarinta ne kuma zata daina watarana, tabbas nasan yanzu giyar ƙuruciya ne ke ɗibanta, nan gaba kaɗan bazatayi abun da tayi yanzu ba."
Ɗan jim yayi tare da cigaba da cewa.
"Kuyi haƙuri dan Allah, Amatsayina na Uba agareta na baku haƙuri, kuma kamar yanda kuke sha'awar haɗa zuri'a dani, haka nima nake sha'awar haɗa zuri'a daku, musamman Saifuddeen daba kowani uba bane zaiƙi son zamowarsa suruki agaresa, kamar yanda na faɗa muku tun daga farko babu abun da zan faɗa daya wuce nace kuyi haƙuri insha Allah aurennan ba fashi."
Da sauri Malam Ashiru ya fara jujjuya kai a hankali tare da cewa.
"A a Malam kayi hak'uri abar batun auren nan mu kam mun janye.....!







BY
*GARKUWAR FULANI*
10/4/20, 7:04 PM - Mmn Khalid: Murmushi Baba Malam yayi irin nasu na manya, kana ya ɗanyi jim, haƙiƙa fasa auren Zaleeha bazai rage komai ba face mutuncinsa da kimarshi, mutuƙar kuwa aka fasa auren to tabbas ita da mahaifiyarta sun samu abun da suke so, sam shikuma bazai lamunci hakan ba, gyara zamansa yayi tare da kai dubansa ga su Baffa Ali da Malam Ashiru.
Cikin nutsuwa haɗi da kamala yace.
"Haƙiƙa nafahimci me kukeji agame da wannan auren, saidai kada ku manta mu daku ɗin kamar ƴan uwa muke,  dukanmu tsofaffine masu dattako da sanin ya kamata,  amatsayina kuma na mahaifi ga Zaleeha zan ƙirata na zaunar da ita nayi mata nasiha, insha Allah nasan zata fahimta, dan Allah kuyi haƙuri, rashin tunanine kawai irin na yaran zamani!."
Ajiyar zuciya su Baffa Ali suka sauƙe, cikin sanyin murya haɗi da fahimtar Baba Malam ɗin, Baffa Ali yace, "shikenan Malam Basheer babu komai, Allah yasa auren ya zama al'khairi agaresu, Allah kuma ya sawa Zaleeha so da ƙaunar Saifuddeen acikin zuciyarta, don shikam yana sonta sosai, fatan mu shine auren nasu yayi al'barka!."
Da "Ameen Ameen!." suka amsa su dukansu,  inda Baba Malam ya sauƙe ajiyar zuciya, sosai yaji girman na iyayen Saifuddeen ya ƙaru acikin idanunsa, nan suka ɗan tattauna maganganu masu muhimmanci, daga nan kuwa su Baffa Ali sukayiwa Baba Malam ɗin sallama,  har bakin motarsu Baba Malam ya rakosu, inda bai dawo cikin gida ba saida yaga tafiyarsu.
Zama yayi akan ɗaya daga cikin tausassun royal chairs ɗin da suka ƙawata haɗaɗɗen falon nasa, bayansa ya jingina da jikin kujeran tare da lumshe idanunsa,  cikin ransa haka yakejin ba daɗi, tunda yake baitaɓa sanya ranan auren ɗansa ko ƴarsa daga baya kuma akazo da maganar fasawa ba sai akan Zaleeha! duk kuma a dalilin taurin kai irin nata, tabbas Zaleeha tanason sashi yaji kunya a idanun mutanen da suke matuƙar ganin ƙimansa, amma babu komai zaiyi abun tubkar hanci tunda wuri,  wayarsa dake cikin al'jihun rigarsa ya laluɓo inda ya dannawa nombern Mama ƙira, bugu uku ana huɗu Mama ta ɗauki ƙiran, batare daya jira komai daga gareta ba yace.
"Kituromin Zaleeha." kitt ya kashe wayan, don sam baison abun dazai ɓata ransa da daren nan.
Bayan kamar minti shida dai-dai Mama tashigo cikin falon hannunta ɗauke da ɗan madaidaicin tray wanda samansa ke ɗauke da flask da kuma ƙananan cup guda biyu,  bakinta ɗauke da sallama ta ƙaraso

Please Login or Register in order to submit comment