Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ne fa akaina, to me yasa zan ɓata lokacina nakuma ɗaukarwa kaina zunubi wajen magan, da Rabeel wanda kuma bai zama lalle dole sai munyi magana ba."

Hararan wayar Balkeesu tayi, kamar Zaleehan na ganinta, taɓe baki tayi tare da faɗin.
"Uhummm su aure manya, dama naƙira ne kawai don naji ykk, da kuma dalilin ƙin ɗaga wayar Rabeel da kikayi."
Ɗan jim Zaleeha tayi tare da cewa.
"Bani da wani dalili naƙin ɗaga wayarsa sai na darajar auren dake kaina, kuma ma koda zai ƙira sau 100 bazan ɗaga wayarsa ba, saboda ina da aure, kuma shi ba muharrami na bane babu yadda za'ayi nayi magana dashi ina matar aure."
"Okay." Balkeesu ta faɗa ataƙaice tare da kashe ƙiran,
ita so take taga rayuwar Zaleeha tazama lalatacciya ta yadda zata samu damar maye gurbinta a ma'aikarsu da kuma gidan Saifuddeen, amman ta kaicinta ɗaya Zaleeha nada riƙo da mutuncinta na ɗiyamace musulma tana kare budurcinta da lallaɓashi tamkar ranta ga ibada.

Ita kuwa Zaleeha aje wayar tayi tare da maida hankalinta akan laptop ɗinta.

Itan kuwa Balkeesu tana kashe wayan, ta saki dariyan mugunta, inda a fili tace.
"Ko ahaka aka tsaya awasan nasamu kaɗan daga cikin abun danakeso tunda ko yanzu shirinki na mushaƙata ya dawo hannuna."

Can ɓangaren su Baba Malam kuwa, gaba ɗaya sun fita daga sha'anin Zaleeha, ko zancenta ma Baba Malam baiso ayi masa.
Maryam kuwa sosai take cikin damuwa, domin kullum da tunanin ƴan uwa da kuma mahaifiyarta take wuni, ganin yanda ta damu sosai ne, yasa Ya Ameenu ɗaukan ta ya kaita wajen Baba Malam, nan Baba Malam yayi mata kalamai irin na mahaifa masu kwantar da zuciya, tare da sa mata al'barka, hakan kuwa yasa zuciyarta ta saki, kaɗan daga cikin damuwarta ya kau.

Rayuwar Mama a Ɓilliri kuwa abun yazo mata cikin wani irin yanayi, komai ba yayi mata daɗi, zaman takura kawai takeyi agarin nasu, yayinda Zahira kuwa kullum bata da wani aiki, sai ƙworafi da mita, kan cewar ita lallai saida Maman ta maida ita gida, ita kuwa Mama har yanzu gani take kamar Baba Malam ɗin zai sauƙo yace su dawo gidan, don tasawa kanta aƙidar cewa bazata taɓa ƙiransa ta basa haƙuri ba, har sai shida kansa ya gaji yace su dawo.
To gatanan dai rayuwar batayi mata daɗi, abinci ma bata samun wanda takeso, gaba ɗaya komai yayi mata duhu, badon komai ba kuwa saidan tana rayuwa acikin mutanen da gabansu da kuma bayansu duk duhu ne, basa ɗauke da haske ko kaɗan, zaman Ɓillirin sam baya yi mata daɗi Babanta kuwa duk da kafurine yaga rashin kyauta warta, shiyasa ya tsananta mata yace gata ga ƙauyen ta zauna kuma damuna na dawowa noma zatayi, Zahiri kuwa ji take kamar a rami take gida ba wuta bare fanka ko AC ba Radio bare tv babu firij bare kayan more rayuwa babu gado bare lafiyayyan katifa babu ƙamshin komai sai warin burkutu, rayuwa dai ta masu tsamari gashi ita Zahira an katse mata karatu ta. Ruda kuwa Addan Mama daɗi hakan taji dan ko yanzu ta samu sun zama dai-dai da ƙanwar tata, itama ta wahalan dai.

Bayan Kwana Uku, da turawa Ya Ahmad kuɗin lefe, Baba Malam da kansa ya kimtsa, inda ya tsara tafiyarsu Abuja, shi da Dirankaɗi, da kuma Bappa Ali, yayinda za suje nemawa Saifuddeen auren Ameena, Alhaji Naseer Maichanji shine mariƙi ga Ameena, wanda yake ɗan kasuwa ne sosai, hakan yasa mafi yawancin mutane sun sanshi, koda zasuyi tafiyar tasu ta yanzun da expriance ɗinsu zasu tafi, kasancewar Dirankaɗi yasan Alhaji Naseer wanda a binciken da Dr Adnan yayi akan Amina a wurin Dr Aliyu ne sukaji komai na Amina.
ananne Dirankadi ya gane ɗiyar tsohon abokin kasuwancishi shiɗin, har ma number'n wayarsa yana dashi, domin sun sha haɗa busineess dashi Alhaji Naseer ɗin tun shekarun baya.
To kuma bisa jagorancin Dirankadin zasuyi tafiyar da tuni sun sanarwa Alhaji Nasir Daddy kenan zuwan nasu.

Ɓangaren Saifuddeen kuwa shi har yanzu ganin abun yake, kamar almara, musamman idan ya tuna da cewar.
"Ameena ɗin bazawara ce." Sai yaji sam shi bazai iya mu'amala da ita ba.

Ƙarfe 10 na safiya dai-dai jirgin da zai ɗaga zuwa Abuja, ya kwashi su Baba Malam da Bappa Ali. Inda suka tafi da niyar cewa bazasu dawo nan Gombe ba sai an tsaida lokaci da kuma ranan aure, don suna sa ran cewa.
"Insha Allah Alhaji Naseer ɗin bazai hanasu ɗiyarsa ba."

Sun isa garin Abuja lafiya, inda Ya Ahmad da kansa yaje ɗauko su a airport, nan fa dukansu suka shiga motar, kaitsaye unguwar Asokoro suka nufa, wanda anan gidan su Ameena yake.

Yayinda duk abinda akeyi Amina bata da labari.

Maigadi ne ya wangale musu gate ɗin gidan, nan cikin parking space ɗin gidan Ya Ahmad yayi parking, dai-dai lokacin wani ɗan Dattijon mutumi me cike da kamala, wanda yasha adonsa cikin manyan kaya, yafito daga cikin wata ƙofa, ganinsu da yayi yasa ya nufosu cikin sauri, fuskarsa ɗauke da fara'a ya miƙa musu hannu, nan suka shiga gaisawa cikin mutunta juna, kai tsaye yayi musu jagora zuwa ɓangarensa, wani babban falo ne mai kyau, inda anan yake tarban baƙinsa masu mahimmanci.
Zama sukayi, tare da sake sabon gaisuwa.
Duban Dirankaɗi Alhaji Naseer yayi tare da cewa.
"Alhaji Ma'aruf ashe rai kan ga rai?."
Murmushin manya Dirankaɗi yayi tare da cewa.

"Ƙwarai kuwa Alhaji Naseer, gashi bayan lokaci mai tsawo da muka ɗauka gashi kuma mun sake haɗuwa."

Shima Alhaji Naseer ɗin murmishi yayi tare da cewa.
"Allah Mai iko, gashi kuwa harda Malam Bashir Sulaiman Dukku kuka zo, a gaskiya yau gidana yana ɗauke da manya manyan baƙi, masha Allah sannunku da zuwa."
ya ƙarishe maganar yana miƙawa Baffa Ali hannu

Dai dai lokacin masu aiki suka shigo, nan suka cika musu gaba da kayan ciye ciye harma da dangin su snacks.

Drinks ɗin kaɗai suka ɗan taɓa, nan Baba Malam da kansa ya gyara zama, duban Alhaji Naseer yayi tare da cewa.
"Nasan zakayi mamakin ganinmu, to amma ance wanda yake da buƙata shi yake zuwa, ko ba haka ba?."
Nan dukansu suka jinjina kai, inda Alhaji Naseer yace.
"Ƙwarai haka ne."
Ajiyar zuciya Baba Malam ya sauƙe tare da cewa.
"To kamar dai yanda ka ganmu dukan mu nan al'khairi ne ya kawo mu, dan kuwa munzo newa ɗan mu auren ɗiyar ka Ameena, muna fatan Allah yasa ba ai mata miji ba."

Ajiyar zuciya Alhaji Naseer ya sauƙe, tare da ɗan numfasawa, cikin murna haɗi da farin cikin ganin manyan malamai sunzo neman haɗa zuriya dashi a hankali yace.
"Masha Allah, Haƙiƙa naji daɗin wannan zancen naku ƙwarai, sannan kuma ba aiwa Ameena miji ba, saidai kuma bazan ɓoye muku ba, magana ta gaskiya banine mahaifin Ameena ba, nine dai mariƙinta, dani da mahaifinta kuwa uwa ɗaya uba ɗaya muke, sannan kuma magana ta biyu dai ita ce, Ameena ba budurwa bace, bazawara ce, don kuwa ta taɓa aure, ta auri ɗan wajena Amir, sai-dai kuma da yake Allah bai tsara zamansu tare ba, sati ɗaya kacal auren yayi Allah ya kawo ƙarshensa, sannan ahalin yanzu dai babu wani wanda ta tsayar mazaunin wanda zata aura."

Ajiyar zuciya suka sauƙe su dukansu, cikin gamsuwa Baba Malam ya gyara zama, inda ya fuskanci Alhaji Naseer, cikin yanayin dattako yace.
"Alhamdulillah, duk da kafun muzo bamusan da wannan magana ba, koda muka jita yanzu kuwa bazaisa mu fasa niya da kuma ƙudurin dake ranmu ba, saidai kuma muma zamu faɗa muku cewar ɗan mu na ɗauke da laluri, wanda idan akayi dubida ƙaddara ce wanda zata iya hawa kan kowa, sannan kuma duk cikinmun nan babu wanda baisan cewa, Lafiya da rashinta duk na Allah bane, sannan shike sawa bawa cuta, kuma shike yaye masa, sannan lalurar da ɗan mu kedashi, bai tauyesa daga zama cikakken ɗa namiji ba, domin yana da lafiyar da zai iya kusantar mace, sannan yana da wadatar da zai iya zama da mace, saboda haka muna fatan hakan bazaisa ku hanamu ƴarku ba, saboda shi aure nufi ne na Allah, matar mutum kuma ance kabarinsa."

Bappa Ali ne ya gyara zama tare da soma yiwa Alhaji Naseer ƙarin bayani, dan gane da larurar Saifuddeen ɗin, bai ɓoye masa komai ba, ya fayyace masa komai yanda zai fahimta.

Jinjina kai Alhaji Naseer yayi tare da cewa.
"Nafahimce ku, ƙwarai kuma ai nakasa ba kasawa bace, kana nakasashshe zai iyayin abun da wani mai lafiyan ma bai iyawa, tabbas kuma idan na fahimta kune iyayen Saifuddeen ko?."
Cikin Mamaki suka kalli juna, Dirankaɗi ne yace.
"Ƙwarai kuwa, amma dama kasan Saifuddeen ɗinne?"
Murmushi Alhaji Naseer yayi inda yace.

"Ƙwarai kuwa, ai sanadiyar ita Ameenan nasanshi, don ita ta kula dashi lokacin da yayi jinya anan, sannan kuma koda suka koma india, danaje wani business ɗina naje har New Delhi na dubasa, gaskiya ni kaina na yarda da ƙwazon sa, don dagani matashi ne mai tsayayyar zuciya, tabbas wannan nakasa tasa bazata sa mu hanaku auren Ameena ba, sai-dai kuma kunsan cewa itaɗin bazawara ce, ba budurwa bace daza'ayi mata dole, saboda haka idan kunbani dama zan shiga ciki don na tambayo ra'ayi da kuma zaɓinta, sannan zan ƙira ɗan uwana awaya zan sanar dashi nasan bazaiƙi amincewa ba."
Nan su Baba Malam sukaji daɗin hakan sosai, har saida murnarsu takasa ɓoyuwa, Nan dai Alhaji Naseer ya miƙe ya wuce cikin gida, inda yace su bashi mintina kaɗan.

Acan cikin gida kuwa, koda yasamu Momma da maganar sosai tashiga mamaki, sai-dai kuma wani tunani daya faɗo ranta, hakan yasata sakin murmushi tare da cewa.
"Masha Allah, ae kuwa nasan Ameena ba zata ƙi ba, bana ƙirawo maka ita yanzun nan saikaji ta bakinta."
Nan Momma tawuce ɗakin Ameena, koda Momma ta shaidawa Ameena ƙiran da Daddyn nasu keyi mata, hakan taji gabanta yaɗan faɗi, hijab ta zura ajikinta sannan ta nufi falon.

Durƙusawa tayi agaban Daddy'n nasu, cikin rusunawa tace.
"Daddy gani."

Dubanta Alhaji Naseer yayi cikin kulawa, yayi mata bayanin komai.
Mamaki, haɗi da zallan farin ciki ne suka cika zuciyar Ameena, wannan shi ake ƙira da ƙarfin ikon Allah, haɗi da kuma falalar addu'a, tabbas ko kaɗan bata taɓa kawowa aranta cewa zata samu Saifuddeen anan kusa ba, tabbas takai kukanta wajen ubangiji gashi kuma ya amsa addu'arta, inda ya share hawayenta, alokacin da bata zata ba.
"Ameena kinyi shiru."
Maganan Daddyn ya katseta.
Murmushi tayi, cikin sassanyar murya tace.
"Idan dai har ka aminta da auren Daddy nima na amince, bani da wani zaɓi sai naka."

Farin ciki da jin daɗi ne suka lulluɓe zuciyar Daddy, nan yashiga sanya mata al'barka, inda yace tatashi taje.
Wayarsa ya zaro, inda ya ƙira Alhaji Sadam, wato Baban Ameena, koda Baban Ameenan ya ɗauka, nan Alhaji Naseer ya labarta masa komai, hakanan Alhaji Sadam yaji zuciyarsa ta aminta da batun, nan take yace ya amince, inda yace da ƙanin nasa yayi komai, ai Ameena ƴarsa ce.

Nan fa Alhaji Naseer ya koma falon tarban baƙinsa, nan yasanar dasu Baba Malam Amincewar Ameena, da kuma mahaifinta, take suka cika da tsananin farinciki, sosai sukaji daɗi, ƙwarai kuma sun yaba da karamcin mutanen.
Nan take suka tsaida magana, inda anan wurin a take Baba Malam yabada sadaki Naira dubu Hamsin, sannan ya kuma ce nan da kwana uku za a kawo kayan lefe, ananne Alhaji Naseer ya yanke musu lokacin biki, wato nan da sati biyu masu zuwa, domin kuwa dukansu ajiƙe suke da naira saboda haka babu wani amfanin jan bikin yayi nesa.
Haka suka rabu cikin mutunta juna, kowa zuciyarsa fes.

Ɓangaren Ameena kuwa tana shiga ɗaki, tsalle ta buga cikin matsanancin mamaki tace.
"Ya Allah idan mafarki nake ka tasheni na farka ka kuma tabbatarmin dashi a zahiri. Wayyo Allah na wai dagaske Saifuddeen zai aureni? zan zama mata agaresa, wayyo Allah na!! Alhamdulillah."
Sulalewa ƙasa tayi inda tayi sujjadan godiya ga Allah, cikin matsanancin jin daɗi tace.
"Tabbas Allah Shi kaɗaine bashida wani abokin tarayya, sannan shike isar mana da komai namu."
faɗawa kan gado tayi cikin matsanancin murma tayi hugging pillow.
Nan fa tashiga birgima akan gado tana dariya, mai ɗauke da tsananin farinciki.



Littafina na kuɗine ga mai buƙata ya min mgna ta wannan no ɗin 09097853276.





     *By*
*GARKUWAN FULANI*
10/4/20, 7:04 PM - Mmn Khalid: Sbp egwl
Ɓangaren su  Baba Malam kuwa, kai tsaye gidan Ya Ahmad suka koma, inda anan suka ɗan huce gajiyansu, zama sukayi suna maida batun karamci da kuma halin dattako irin na iyayen Ameena'n, tabbas sun shaida cewa suna da mutumci, kana kowani mutum zai so haɗa zuri'a dasu.                                      
Da misalin ƙarfe 6 na yammaci jirgin da zai maidasu Gombe zai tashi, hakan yasa 5::40  pm  ababban filin airport na Nnamdi Azikwe International Airport Abuja.   
Ƙarfe shida dai-dai kuwa jirginsu ya tashi, bayan Baba Malam ya ƙara jaddadawa Ya Ahmad, maganan haɗo lefe da wuri, nan Ya Ahmad yace.
"Insha Allah zaisa Aunty Lubna ta haɗo lefen, nan bada jimawa ba."                                       Bakwai dai-dai jirgin da ya ɗaukosu daga Abuja zuwa Gombe, ya sauƙa acikin Gombe International Airport.              Ya Ameenu  da kuma Ahmad ne sukazo ɗaukarsu anan airport ɗin.                                          Motar Ya Ameenu Baba Malam ya shiga, inda Bappa Ali da Dirankadi kuwa suka shiga motar Ahmad, don sune zasu je suiwa Ummi bayanin duk abun da ya wakana.                            Haka suka rabu da juna cikin aminci da salama.           
Tun daga yanayin yanda Ahmad yaga fuskokinsu ɗauke da annuri, hakan yasa shi fahimtar cewa lallai anyi nasara tafiya tayi kyau, sosai kuwa yaji sanyi azuciyarsa.                          
Koda suka ƙarasa gidan, a falon na Ummi suka zauna, cikin nutsuwa kuwa Bappa Ali da Dirankadi sukaiwa Ummi bayanin komai, sosai Ummi ta cika da farin ciki haɗi da jin daɗi,  haka kuma lokacin da aka sanya auren yayi mata daɗi sosai, dama ba ta son aja lokacin, nan dai  tasa aka kawowa su Bappa Alin kayan ciye ciye,  nan suka ɗan taɓa, daga haka Dirankadi ya ƙirayi driver'nsa,  nan ya zo ya maidasa gida, shikuwa Bappa Ali anan zai kwana, kasancewar qdare yayi, idan yaso gobe da safe, Ahmad ko sule driver ɗaya daga cikinsu zai maidashi.                          

Can ɓangaren Saifuddeen kuwa, ganin sun dage da gaske suke maganar auren yasa, wunin yau duk bai fito waje ba, anan ɓangarensa ya zauna, yayinda ya maida hankalinsa kan Laptop ɗinsa yana aiwatar da sabon aikin da shugaban DSS suka bashi.
Koda ya dawo sallan Isha, kai tsaye part ɗinsa ya koma,  kasancewar yau din ana yanayin sanyi hakan yasa  shi kwanciya da wuri, luf yayi acikin lallausan bargonsa, inda ya ɓoye kansa acikin bargon, ajiyar zuciya ya sauƙe tare da lumshe idanunsa, tunaninta ne kwance acikin zuciyarsa, sau da yawa idan ya tuna da ƙiriniya da kuma rashin ji irinta na yarintarta dama yanzun da takega ta girma, yakan samu kansa da sakin murmushi.  Da haka bacci ya ɗaukesa.

Washegari.

Tun da ya dawo daga sallan asuba ya koma bacci, bashine  kuwa ya farka ba sai wajen ƙarfe 10:30 am.    Ahankali yazuro da ƙafafunsa ƙasa, tare da jawo wheellchair ɗinsa, wanda akullum take kusa dashi, sam baya bari tayi masa nisa, hawa samanta yayi, kai tsaye ya nufi toilet, koda ya shiga ruwan wanka mai ɗam ɗumi ya haɗawa kansa, cikin haɗaɗɗen jakuzzie, nan ya zuba turaren wanka mai daɗin ƙamshi acikin ruwan,  Luf ya kwanta acikin jakuzzien tare da ɗan lumshe idanunsa. Sama da mintuna 10 ya ɗauka ahaka, yayinda yakejin daɗin ruwan, kasancewar ruwan nada ɗan ɗumi, shiyasa yakejin daɗi yanayin, domin kuwa yanzu ana weather ne na sanyi hunturu.  
Wanka yayi kana ya ya rufe jikinsa da wani fari ƙal ɗin towel,  haka ya nufi ƙofar fita daga cikin toilet ɗin, jikinsa ɗauke da danshin ruwa, yayinda kwantaccen sajen dake kan fuskarsa ya ƙara lafewa, saman kumatunsa.
Kaitsaye gaban drawer ɗinsa ya nufa, inda ya zaro kayan da zaisa, wani ƙaramin towel ya ɗauka sannan ya shiga goge ruwan dake jikinsa, yana kammalawa, ya ɗauki handryer wanda  dashi yayi amfani wajen busar da tarin sumar dake kansa, cumb yasa inda yaƙara gyara lallausan sajensa, yayi kyau matuƙa, wani body lotion mai sauƙin ƙamshi ya shafa ajikinsa,  dogon wandon pencil jeans ya sanya, kana ya zura wata haɗaɗɗiyar riga, wanda take kaman na sanyi domin harda hulanta, kasancewar rigar nada kalan grey hakan yasa sosai tayi masa kyau, yayinda agaban rigar aka rubuta NIKE da manyan baƙaƙe,  wasu combat shoe wanda suma na company'n NIKE ɗin ne ya sanya aƙafafunsa, sosai shigar tayi masa kyau, saiya fito kaman irin shahararren jarumin ƙwallon ƙafa,  wani simple watch ya ɗaura akan tsintsiyar hannunsa,  kana ya feshe gaba ɗaya jikinsa da turare, take ɗakin ya gauraya da daddaɗan ƙamshin turarensa.      Wayoyinsa ƙiran iPhone da kuma Samsung ya ɗauka, kana ya zura su cikin ajihun dake jikin haɗaɗɗiyar rigar tasa.
Daga part ɗinnasa kai tsaye barayin Ummi ya nufa.
Tun kafun isowarsa falon nata, ƙamshin turarensa ya rigayesa isowa.
Cikin nutsuwa ya ƙarasa shigowa cikin falon,   Hayatuddeen ne zaune akan dinning area, yayinda ya saka pepper meat soup agaba sai sha yake.  Ƙarasowa dinning area ɗin yayi, dubansa Hayatuddeen yayi cikin kulawa yace.
"Barka da fitowa Hammana."
Kai ya jinjinawa Hayatuddeen din bayan yasaki taƙaitaccen murmushi, dai-dai lokacin Ummi tafito daga ɗakinta, ganin Saifuddeen ɗin yasa ta sakin murmushi cikin kulawa tace.
"Masha Allah ka fito kenan, yanzu fa nake cewa Hayatuddeen ya gama ya ƙiraka, kazo kayi break fast." 
Ummi taƙare maganar tana mejan kujera wanda take facing na Saifuddeen ta zauna, duk dama shi always akan wheellchair ɗinsa yake zama.
   Raliya ce tafito daga cikin kitchine, hannunta ɗauke da plate.  Ganin Hamman nata yasata sakin murmushi, cikin nutsuwa tace.
"G/N Hamma."  
Kansa ya jinjina mata alaman ya amsa, zagayowa ɓangaren da yake tayi, nan ta aje masa plate ɗin da ta fito dashi daga kitchine ɗin, wanda saman sa ke ɗauke da roasted fish, wanda yaji kayan haɗi, hadda lemon tsami.   murmushi Saifuddeen yayi tare da dubanta, hannu ya jinjina mata alaman "Thanks."  Itama murmushin tayi, don dama tayi hakanne don ta faranta masa, kasancewar tasan yanason roasted fish.
Nan ta zauna, inda suka shiga cin breakfast ɗin cikin nutsuwa,  Ya lura dukaninsu suna cikin farinciki, musamman ma Umminsa, wanda duk bayan ƴan mintuna kaɗan take sakin murmushi, haka dai suka kammala break ɗin nasu, nan ya dawo cikin falon Ummin ya kwanta,  Hayatuddeen kuwa ɗaki ya koma, inda shima yayi shiga shigen irin ta hamman nasa, nan yafito riƙe da jakarsa ta makaranta, duban Ummi dake zaune afalon yayi, cikin sangarta haɗi da zallan shagwaɓa yace.
"Ummi zan tafi school, 11:30 muke da lecture."
Batare da Ummi ta ɗago kanta ba tace.
"To Autana adawo lafiya."
Jin haka yasashi ɓata fuska ashagwaɓe
yace.
"Ummi kuɗin hannuna fa ya ƙare."
Murmushi Ummi tayi, don dama tasan kwanan zancen.
Dubansa tayi tare da cewa.
"Kullum sai an baka kuɗi Hayatuddeen sai kace ƙaramin yaro."
Cikin tura baki yace.
"Ni ban san ammafin buɗe min ac da Hamma Saifuddeen yayiba, ya tarkata komai ya riƙe ko Atm ɗin ban taɓa riƙewa koda na wuni ɗayaba, sai dai inyi ta ganin Arlet yanata shiga ba sauƙi, ina ganin miliyoyi amman bani da damar taɓasu."
Dariya Ummi tayi hakama Saifuddeen, dan zancen autan nasu ya nuna burinshi na a bashi kuɗi ya fara lalata.
Shi kuwa auta sake shagwaɓe mata yayi, wai adole sai ta bashi kuɗi, saikace ƙaramin yaro, nan Ahmad yashigo ya iske suna maganan, Ahmad ne ya ciro 5k daga cikin aljihunsa, inda ya bawa Hayatuddeen ɗin, nan Hayatuddeen yasaki murmushi sannan yasakai yafice daga cikin falon.
Nan Ahmad ya zauna acikin falon suka shiga ɗan taɓa hira da Ummi, Saifuddeen kuwa, luf yayi tare da lumshe idanunsa, kamar wanda ke bacci.

Abuja Nigeria.

Kwana biyu kenan da zuwan su Baba Malam Abujan, yayinda yau
Tsab Aunty Lubna da kuma wata ƙawarta, mai suna Samira suka shiga cikin shoprite, don haɗo kayan auren, ba laifi kaya masu kyau da kuma tsada suka sayo, duk da cewa ran Aunty Lubna baiso ƙara auren na Saifuddeen ba tanajin taya Zaleeha kishi, tana kuma tausayawa Zaleeha a gaba, to amma tasan cewa koma menene hakan shine dai-dai, don itama guduwan da Zaleehan tayi ya sosa mata zuciya.
Akwatuna goma sha biyu suka saya, kana kuma suka cikasu da kaya, sannan kuma suka saya wasu uku daban wanda ciki aka sanya kayan uwa da na uba.
Haka dai suka dawo gida bayan motarsu cike da kaya.
Aranan kuwa Ya Ahmad ya ƙira Baba Malam, inda yasanar dashi cewa, anagama haɗa kayan auren.
Kasancewar da dare ne Ya Ahmad da Baba Malam ɗin sukai waya, hakan yasa washe gari da safe, Baba Malam yaƙirayi Bappa Ali ya sanar masa, nan Bappa Ali yace.
"Zai sanar da Ummin, sai susa ranan da za'a kai kayan."

Hakan kuwa akayi don bayan sallan Azahar Ummi na zaune akan sallaya, sallame sallan ta kenan, wayarta tasoma ruri, ɗaga ƙiran tayi, bayan sun gaisa da Bappa Ali'n ne kuma, yake shaida mata cewar.
"An kammala haɗa kayan auren, yanzun ita zata sanya ranan da za akai kayan."
Cikin jindaɗi da gamsuwa Ummi tace.
"Masha Allah, amma ni sai nake ga kamar ku ya kamata kutsai da ranan kai lefen, tunda dai auren bawani lokaci mai tsawo aka ɗauka masa ba, yanzu gashi kamar wasa har anci kwana uku acikin ranakun."
Cike da gamsuwa Bappa Ali yace.
"Tunda yau takasance asabar ne, to ranan litinin da safe, sai waƴanda zasu kai lefen su shirya."
Nan Ummi take sanar dashi cewa.
"Goggo dada, Adda Rahama, da kuma Ahmad, sai kuma Hayatuddeen, sune wanda zasuje, amma bawai kai tsaye abujan zasu nufa ba, a Kaduna gidan Raihana zasu sauƙa tukun."
Nan dai tace ya kawo shawaransa. Cikin gamsuwa Bappa Ali yace mata.
"Hakan ma yayi."
Nan akayanke cewa, ranan litinin zasu kai lefen.
Ummi na gama waya da Bappa Ali'n, numbern Adda Rahama ta ƙira, nan take shaida mata duk yanda sukayi da Bappan nasu, sosai itama Adda Rahama tayi na'am da hakan. Nan dai sukayi sallama.

Numan.

Zaman Zaleeha a numan ya miƙa sosai, duk da cewa bawai tanajin daɗin rayuwa acikin ƙauyen bane, amma babu laifi tana ɗan samun abun da take ɗan so, tunda da kuɗi a hannunta, rayuwa take cike da kaɗaici, saidai wani lokaci wayarta da kuma tsohuwar laptop ɗinta suke ɗebe mata kewa.
Sai kuma wata sabuwar ƙawa wacce take ƴar fulani da tayi, inda sun haɗu ne, abakin kogi, don wani lokaci Zaleeha kan zuwa bakin kogin ta zauna, itakuwa sabuwar ƙawar Zaleehan mai suna Aisha, anan cikin wani ɗan ƙaramin rugar fulani dake kusa da Numan ɗin take, wanda yake rugace na zallan fulani sannan kuma dukansu musulmai ne, babu christan ko ɗaya acikinsu, tun Zaleeha bata sake da Aishan ba, har dai zuwa yanzu suka sama, domin kuwa taji daɗin haɗuwa da Aishan, kasancewar sosai Aishan ke ɗebe mata kewa, ta wani ɓangare kuwa mamaki take, kasancewar ansan cewa fulani suna aurar da ƴaƴansu da wuri, sai gashi ita kuma Aishan karatu ma take acikin birni, inda take aji biyu a university, wato level two, duka duka Aishan bazata ɗarawa Zaleehan ba, domin kusan ma kansu ɗaya, haka ma dai shekarunsu, sai-dai Zaleehan tafi Aishan cika dama duk wani abu na gogewa.
Yanzu ma dai tsab ta gama shirinta, cikin wani riga da sket na material masu kyaun gaske, wani babban mayafi ta yafa ajikinta, wanda yazo har ƙasa ya ɓoye duk wani kyawun surarta, waya da kuma power bank ɗinta ta ɗauka, duban Aishan dake zaune tayi.
Aishan ma dubanta tayi, ganin Zaleehan ta kammala shirinta yasa tace.
"Masha Allah, kinga yanda kikayi kyau kuwa, sau dayawa ina mamakin ki,

Please Login or Register in order to submit comment