Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

nakeji, ka duba fa kaga, lokaci ɗaya tafige ta fita hayyacinta, bata da wani abunyi sai kuka kowa nata ya juya mata baya."

Fuska ya ya mutsa tare da sake taɓe bakinsa,
bata damu da yanayin yanda taga fuskar tasa ba, ta sake cewa. "Yanzu ya za'ayi da ita kenan? kuma ma naji jikinta da zafi sosai, kodai zaka ƙira Abban su Faruq ne yazo ya duba ta."

Cikin halin ko inkula ya ɗage kafaɗunsa sama, alaman.
"Shifa babu ruwansa da duk wani abu daya shafeta."
Baki Adda Rahama ta saki tana kallonsa, dan kuwa koda wasa bata taɓa tunanin zaiyi fushi da Zaleehan har haka ba, tunda yake a duniya bai taɓa nuna ƙulafacinsa kan komaiba sai a kanta.
Shikuwa Saifuddeen ganin irin duban da Umminsa keyi masa ne,ya sashi murza wheelchair ɗinsa, kai tsaye ya fice daga cikin ɗakin, ko kallon inda Zaleehan ke kwance bai sake yi ba.
Ganin ya fita ne yasa Ummi sakin ajiyar zuciya tare da lumshe idanunta, hannunta takai inda ta shiga ɗan jijjiga Zaleeha'n.

Ahankali taɗan buɗe idanunta wanda suka ƙanƙance saboda tsabar kuka, da wani irin firgici haɗi da tsananin tsoro ta tashi, ɗan lumshe idanunta tayi, take mafarkin da tayi yanzun yadawo cikin tunaninta, kasancewar aɗan kwanciyan da tayi har tayi mafarki wai tasake komawa gidan Baba Malam, sannan awannan karon shi da kansa yaja hannunta ya fitar da ita daga gidan, tare dayin mummunan furuci agareta, inda yace.
"Daga yau ta cire kanta daga sahun ƴaƴansa, ta manta da cewa shiɗin mahaifinta ne, saboda shi ya jima da manta cewa ya haifi wata ƴa me suna Zaleeha."
wannan mafarkin shiya daɗa hautsuna tunaninta, kana ya ƙara mata fargaba me yawa acikin ranta, ƙoƙarin sakin wani sabon kuka take, Ummi ta dafa ta, cikin sanyi tace.
"Dan Allah na roƙeki Zaleeha kibar kukan nan haka, kuka baya taɓa maganin damuwa, addu'a shi ya kamata kiyi ako da yaushe, nasan da cewa Baba Malam na fushi dake, amma hakan bawai yana nufin cewa bazai taɓa yafe miki ba ne. Insha Allah zai yafe miki, sannan kada ki manta Baba Malam yana fushi dake ne saboda kin baƙanta ransa, kin kuma ƙi yi masa biyyya, to idan har Baba Malam zaiyi fushi dake har haka, Allah' n daya halicceki kuma fa, wani irin fushi kike tunanin yakeyi dake? nasan kinsan da cewa fushin Allah Yana tare da fushin iyaye da miji, saboda haka kiyi sallah ki roƙi Allah gafara, sanadin haka sai kiga Allah yasa Baba Malam ya yafe miki, sannan kisawa zuciyarki nutsuwa, da salama, tashi maza kije ki ɗauro alwala kizo kiyi sallah." Ummi ta faɗi maganar cikin yanayin lallashi. cikin sheshsheƙa ta gyaɗa kanta, tare da soma yunƙurin tashi daga kan gadon, sai-dai gaba ɗaya babu ƙarfi ajikinta, Adda Rahama ne ta taimaka mata, ita ta kamata ta kaita har cikin bathroom.
acikin toilet ɗin ma kuka take haka ta ɗauro alwala. Koda ta fito nan ta samu Ummi ta shumfuɗa mata darduma tare da aje mata sabon hijab, ganin bakowa acikin ɗakinne yasa, jiki asanyaye ta ƙarasa ta ɗauki hijab ɗin ta sanya, tare da tada sallah.
Da ƙyar ƙafafunta suke iya ɗaukanta, saboda yanda takejin jikinta ba ƙarfi.
Koda takai sujjadar ƙarshe na cikin sallan nata, fashewa tayi da wani irin kuka mai tsananin taɓa zucia, kuka take sosai tana me neman gafara awajen Allah, saida tayi kuka sosai har da shiɗewa kafun ta ɗago daga sujjadan, tana sallame sallan kuwa ta jingina bayanta da jikin gado. Ummi da tunɗazu ke tsaye abakin ƙofar shigowa duk wani kukan na Zaleeha akan kunnenta, hawayen da suka cika idanun ta ne suka samu daman gangarowa, saurin share hawayen nata tayi tare da ƙarasowa cikin ɗakin. Zama tayi tare da aje plate ɗin abincin dake hannunta, cikin sanyi ta ƙira sunan Zaleeha'n. Ɗago jajayen idanunta tayi ta kalli Umm'in, plate ɗin abincin Ummi ta turo mata gabanta, cikin kulawa tace. "Kukan ya isa haka, ki samu kici abinci." girgiza kanta tayi cikin muryarta dake rawa, haɗe da sarƙewa tace. "Bazan iyaba Ummi, bazan iya cin abinci ba, banajin daɗin bakina, komai na duniya baya min daɗi, inajin kamar ma babu yawu acikin bakina, banajin komai acikin zuciyata sai ƙunci da baƙincikin rayuwa, bana sha'awar komai yanzu aduniyata sai yafiyan Baba Malam da Hamma Saif, bazan taɓa iya cin abinci naji daɗinsa abakina ba harsai ranan da Baba Malam ya yafemin, zuciyata zafi takemin Ummi, Babana mafi soyuwa agareni yana fushi dani, Ummi Baba Malam bayason ganina, naje gidansa yasa Ya Habu ya koreni, ƴan uwana duk sun tsaneni, gashi ƴar uwata ta tafi tabarni, Adda Maryam ta bar duniya batare dana sake sanyata acikin idanuna ba, shikenan yanzu bani da wata Adda aduniya, Inama mutuwa ni ta ɗauka ba ita ba, inama da ace mutuwa zatamin gata wajen kusantani da ƴar uwata, bazan iya jure fushin Baba Malam akaina ba Ummi, nima mutuwa zanyi Ummi.....".
Kasa ƙarasa maganan tayi, sakamakon kukan me tsananin ƙarfi da ya ƙwace mata, Ummi kanta kasa daurewa tayi, hakanne yasa ta jawo Zaleehan jikinta ta rungume.
Jinta ajikin Ummi yasa ta ƙanƙame Ummin tana kukan fitar hayyaci, mai ɗauke da tsananin dana sanin abun da ta aikata a baya.

Hawayene suka silalo daga cikin Idanun Hayatuddeen, wanda duk wani kalaman da Zaleehan ke faɗa, ya jisu raɗau akan kunnuwansa, dan yajima tsaye abakin ƙofar batare da sun san da zuwan sa ba, sosai jikinsa yayi sanyi, dajin kalaman nata, domin dama Raleeya ta faɗa masa cewa, Zaleehan har suma tayi ɗazu, shine Ummi ta ɗauketa takaita ɗakinta, jin cewa Adda Zaleehan na ɗakin Ummin ne yasashi nufo ɗakin, saboda halin ko inkula daya nuna mata ɗazu, yasan dole zataji ba daɗi acikin ranta.

Ahankali ya shiga taka ƙafafunsa wanda sukayi masa nauyi, ƙarasawa inda suke yayi, tare da zubewa akan guiwowinsa, cikin wata irin murya dake fitar da tsananin rauninsa yace "Adda Zaleeha, meya sameki? meyasa kike kuka, dan Allah kibar kuka kinji."

Jin sauƙar Muryar Hayatuddeen acikin kunnuwanta yasa, ta juyo da sauri, ganin shine kuwa yasa ta zare jikinta daga na Ummi, faɗawa jikin Hayatuddeen ɗin tayi, tare da sakin kukan da yafi wanda tayi abaya ciwo, dan jin Hayatuddeen takeyi tamkar Zakariyya. Shima Hayatuddeen ɗin kukane ya ƙwace masa, cikin kukan nata tace. "Hayatuddeen ya zanyi Baba Malam yayi fushi dani, haka Ya Ahmad ma da Aunty Lubna duk sunyi fushi dani, babu wani wanda yake saurara ta, basason ko ganina akusa dasu, Mamy ma fushi take dani, gashi Ya Ameenu ya zama abun tausayi, Adda Maryam ta tafi ta barmu."
Ɗagowa daga jikinsa tayi tare da kamo hannayensa, cikin kuka taci gaba da cewa. "Baba Malam yace kar na sake zuwa gidansa, hatta Ziyada ƙanwata ma fushi take dani, Zakariyya ma nasan adole yake kulani, Hayatuddeen ya zanyi? ina zansa rayuwata? kowa baya sona, kowa guduna yake, babu wasu wanda ke rarrashina sai su Ummi, inajin kamar zuciyata zata fashe, duk wani majinginan danake tinƙaho dashi ya ruguje, rayuwata tayi mini zafi, har inajin gwamma mutuwa ta da rayuwata." taƙare maganar tana me sake komawa ta raɓa jikinsa ta riƙesa ƙam, kuka kuwa yinshi take harda majina.
Duk yanda yaso shanye kukansa kasawa yayi, hakan yasa ya sake rungumeta ya fashe da kuka, saida yayi kuka sosai sannan ahankali ya shiga shafa bayanta, cikin sanyin murya yace. "Kiyi haƙuri kinji Adda Zaleeha, ki daina kuka, idan duka mutanen duniya zasu ƙiki, ni da Zakariyya bazamu taɓa kinki ba, kiyi shiru kinji, nasan Baba Malam yayi fushi, amma zai yafe miki."
Kai Ummi ta jinjina cikin son kwantar mata da hankali tace.
"Ƙwarai kuwa Insha Allah Baba Malam zai yafe miki, yanzu dai ki samu kici abincin kinji." Cikin sheshsheƙan kuka tace.
"Ummi bazan iya ci ba, ko tea ɗin ɗazu dana sha haka najisa kaman maɗaci, gaba ɗaya kaman yanda zuciyata take babu ɗanɗano acikinta, haka bakina ma, banajin daɗin komai."
cikin tausayawa Ummi tace.
"To akawo miki fresh milk kisha ko kaɗanne?"
Batason yawaita yin musu da Ummi hakan yasa ta ɗan gyaɗa kanta, dai-dai lokacin kuwa Raleeya ta shigo, nan Ummi tace da ita, ta kawowa Zaleehan fresh milk.
Babu ɓata lokaci kuwa takawo fresh milk ɗin me sanyi.
Karɓan cup ɗin Hayatuddeen yayi, cike da tausayinta yace. "Adda Zaleeha, ki tashi kisha kinji."
bazata iya janye jikinta daga garesa ba, saboda tanajin ya zame mata kamar majingina, hakan yasa ahankali taɗan ɗago kanta dake masifar sarawa, cikin kulawa Hayatuddeen ya shiga bata fresh milk ɗin abakinta, sam kwata kwata batajin daɗi ko ɗanɗano abakinta, jima take kamar magani take sha, kurɓo huɗu kawai tayi ta janye bakinta daga jikin ƙofin, har yanzu sheshsheƙan kuka take, gashi jikinta ya sake ɗaukan zafi sosai, komawa jikin Hayatuddeen ɗin tayi ta kwanta, tana ta faman fusgar numfashinta dake neman ƙwace wa. Ummi, Adda Rahama, Raleeya, har zuwa kan Hayatuddeen babu wanda ya gusa da ga kusa da ita, wani irin kulawa haɗi da tattali na musamman suke bata, sosai suke faɗa mata kalaman dazai kwantar mata da hankali..
Suna nan azaune har aka ƙirayi sallan la'asar, Ummi ne tace da Adda Rahama da kuma Raliya su shiga kitchine su ɗaura abinci, kasancewar tunda akayi rasuwa'n kullum sai sunkai abinci gidan su Zaleeha.
Nandai Hayatuddeen ma ya tashi ya wuce massallaci, itama Zaleehan sallah tayi, nan kan carpet ta kwanta tana masassara saboda zazzafan zazzaɓin ya soma cin ƙarfinta.
Su Adda Rahama kuwa suna kammala girkin, nan cikin wasu manyan food flask suka juye abincin.
Kamar kullum dama Hayatuddeen da Raleeya ne ke kai abincin, to yau ɗin ma dai hakanne, ta kasance dan sune suka kai abincin, Hayatuddeen ne ke driving, kasancewar yanzu hannunsa yaɗan faɗa wajen iya tuƙin mota, saboda Khamis na koya masa tuƙin time to time, babu laifi kuma yaɗan iya.
Koda suka ƙarasa gidan su Zaleehan bayan sun sake yi musu gaisuwa, Hayatuddeen ne ya kamo hannun Zakariyya da Imran ƙanin Ishaq wanda da Babansu yazo, zagawa sukayi wajen da babu yalwar mutane. ɗan karyar da wuya Hayatuddeen yayi, cikin sanyi haɗi da damuwar dake bayyane akan fuskarsa yace. "Zakariyya Adda Zaleeha taje gida bata da lafiya sosai, gaba ɗaya jikinta zafi kaman wuta, har suma tayi, dan Allah abawa Baba Malam haƙuri ya yafe mata, tana cikin matsanancin damuwa, kuka yazama tamkar abinci agareta."

Idanun Zakariyya ne suka cicciko da ƙwallan tausayin ƴar uwartasa, ɗan lumshe idanunsa yayi, yana mejin tausayinsu su dukansu, tabbas yasan akwai ƙauna me zafi atsakaninsu, wanda koda ace babu auren Hamma Saifuddeen akan Zaleeha, idan Hayatuddeen yaganta cikin damuwa zai ji ƙanta, kuma gashi nan damuwa ta bayyana ƙarara akan fuskarsa, sunyi imani cewa duk wani damuwan ɗayansu nasune su duka.
Cikin sanyi yasa hannu ya share hawayensa, muryarsa asanyaye yace. "Hayatuddeen nima bansan ya zanyi ba, Baba Malam yace. Bayason sake ganinta, yana fushi da ita sosai, kuma ta basa haƙuri ma yaƙi haƙura."
Sosai jikin Hayatuddeen da Imran yayi sanyi, dole da addu'a kawai zasu taya ta, dan basu da wani zaɓin daya wuce hakan.

Fitowar Adda Raleeya daga cikin gidan ne, yasa sukayi shiru da zancen, ƙarasowa wajen da su Zakariyyan suke tayi, ganinta yasa Hayatuddeen duban Zakariyya murya asanyaye yace.
"Mu zamu wuce."
Har bakin mota Zakariyya da Imran suka rakasu, saida yaga tafiyarsu sannan suka komawa cikin gida, zuciyarsa gaba ɗaya ba dadi, sosai tausayin Zaleehan ke damunsa.

Koda su Hayatuddeen suka koma gida kuwa kai tsaye ɗakin Ummi suka wuce. Har yanzun Zaleeha na duƙunƙune waje ɗaya, gefenta Ummi da Adda Rahama ne zaune.
Ƙarasowa cikin ɗakin Hayatuddeen yayi tare da zama akusa da ita, hannunta ya kamo, hakan yasa ta ɗago ta dubeshi da idanunta wanda sukai jajur, murmushi yaɗan ƙaƙalo akan fuskarsa, cikin kulawa yace.
"Adda Zaleeha kukan ki ya kusa ƙarewa Insha Allah, Baba Malam zai yafe miki nan bada jimawa ba, kuma Ya Ahmad ma da kansa yace agaisheki."
Zabura tayi tare da matsowa gab dashi, idanunta ta zuba masa, kansa ya jinjina mata alaman dagaske yake, idanunta ta lumshe, take kuma wasu sabin hawaye suka zubo mata, matsawa kusa dashi tayi tare da ɗaura kanta akan kafaɗansa, hannunsa ta riƙe ƙam tana sauƙe ajiyar zuciya.
Ganin haka yasa su Ummi sakin ajiyar zuciya suma, dan gaba ɗayansu burinsu bai wuce ganinta cikin nutsuwa ba.

Da misalin ƙarfe 6:20 pm Ameena tashigo cikin gidan, wanda dawowarta daga wajen aiki kenan, kai tsaye falon Ummi ta nufa bakinta ɗauke da sallama,
saidai rashin ganin kowa acikin falon yasa taɗan shiga mamaki, saboda yawancin lokuta falon Ummin bai rabuwa dasu Raleeya ko kuma auta Hayatuddeen, gashi yau kuma falon shiru babu motsin kowa.
Ganin haka yasa kaitsaye ta nufi ɗakin Ummi'n, hannunta riƙe da Adeel. Ƙwanƙwasa ƙofar ɗakin tayi, Adda Rahama dake zaune gefen Zaleehan ne ta bada izinin shigowa, nan ta tura ƙofar ɗakin ta shigo, bakinta ɗauke da sallama. Kusan dukansu ne suka amsa mata sallaman cikin kula, ƙarasowa cikin ɗakin tayi tana me mamakin ganin yanda suka taru su duka acikin ɗakin, cikin nutsuwa ta gaishe da Adda Rahama, amsa mata tayi tare dasa hannu ta karɓi Adeel, idanunta ne suka sauƙa akan kyakkyawar matashiyar budurwar dake zaune ta jingina jikinta dana Ummi, kanta kuwa na kan kafaɗan Hayatuddeen, wani irin bugawa taji ƙirjinta yayi, cikin nutsuwa tace. "Ummi sannu da gida." cikin kulawa da so Ummi tace.
"Yauwa Aminatu sannu, ya wajen aikin naku?" Ummi tayi mata tambayar batare da ta ɗago kai ta kalleta ba, saboda gaba ɗaya hankalinta naga Zaleeha, magungunan zazzaɓin da Hayatuddeen ɗin ya seyo, shi take ƙoƙarin ɓallewa dan bawa Zaleehan tasha.
Ƙurawa Zaleehan idanu Ameena tayi, cikin ranta tace.
"Ina su Ummi suka samo wannan balarabiya'n?" Tabbas tasan Zaleeha a hoto sai dai ashema rage kyanta hoto keyi, tabbas ita kallon balarabiya tayiwa Zaleeha'n, saboda kwata-kwata yanayinta baiyi kama dana mutanen Nigeria ba, musamman idan akayi duba da yanda dogon gashin kanta ya kwanto har zuwa gadon bayanta, ga kuma farin fatarta wanda yake na musamman ne, bawai irin farin fatar nan bane da wasu ke mutane ke ƙarawa da mai, natural fari ne me kyau da ɗaukar hankali, uwa uba matsanancin kyawun da tagani atattare da Zaleeha'n.
Cikin zuciyarta ta ƙara tambayar kanta, ko itaɗin wacece. Tunaninta ne ya katse alokacin da taji Ummi tace.
"Zaleeha tashi kisha maganin kinji, nasan zuwa anjima kaɗan zafin zazzaɓin zai sauƙa."
Wani irin luguden duka Ameena taji ƙirjinta nayi, cikin ranta ta maimaita sunan Zaleeha, take tunaninta ya bata cewa, itace Zaleeha matar Saifuddeen, ƙura mata idanu Ameena tayi, take kuma sai taji wani irin abu ya tokare maƙoshinta, wani irin haushin da tsanar Zaleehan ne taji ya cika mata zuciya, duban Hayatuddeen dake riƙe da hannun Zaleehan tayi, gani tayi idanunsa sunyi rau-rau kamar zaiyi kuka, tunda ta shigo ma ko ɗago kai baiyi ya kalleta ba, Raleeya da Adda Rahama ta kuma kallo, suma gani tayi rabin hankalin na kan Adeel gaba ɗaya rabin hankalinsu nakan Zaleeha'n, Ummi kuwa dama tuni hankalinta akan Zaleehan yake. Laɓɓanta ta cije, tare dajin wani abu na zazzafan kishi akan Zaleeha'n, bakomai kuwa yasa hakan ba, face tsananin kyawun Zaleehan da ta gani, ga kuma yanda su Ummi ke nan nan da ita, ganin cewa gabaki ɗayansu hankalinsu a tashe yake hakan yasa taja da baya, tana sakin murmushin dayafi kuka ciwo, ta fice daga cikin ɗakin, sam su hankalinsu ma ba'a kanta yake ba, shiyasa basusan cewa ta fita daga ɗakin ba.
Zaleeha kuwa asanyaye ta karɓi maganin tasha, lokacinne kuma aka soma ƙiraye ƙirayen Sallan magriba. Ameena kuwa tana shiga ɗakinta, tayi wurgi da jakanta ranta amatuƙar ɓace.
Iska ta furzar ta bakinta, tare da sanya hannu ta kama ƙugunta, ahankali ta taka ta ƙarasa gaban mirrror, tsayawa tayi tare dayin shiru tana ƙarewa kanta kallo, idanunta ta rumtse da ƙarfi, sam koda  wasa, koda kuwa makaho bazai taɓa haɗa kyawun Zaleeha da nata ba, ita kamma mecece akyau?  idanunta ne suka sake hasasho mata Zaleeha, take taji gabanta ya faɗi,   tabbas hanyar jirgi daban haka ma kuma ta mota daban,  zamewa tayi ta zauna akan gadonta, wani irin haushin Zaleeha da matsanancin kishinta ne ke tokare mata maƙoshi,  taɓe baki tayi abayyane tace.  "Jiyanda suke wani nannan da ita saikace wata ƴar gold,  gaba ɗayansu kulawa suke nuna mata, jiyanda duk Hayatuddeen ya wani liƙe mata, hmmm." 
kanta ta jinjina ganin zancen zuci bazai kaita ba, yasa ta miƙe tsaye kai tsaye ta wuce toilet.        Gaba ɗaya ta mance a fagen kishi da aurataiya ba'a surka kyau a mizani   ta mance cewa kowa ya iya Allonsa ya wonkene mata nawane munana na bugawa a mujalla kuma sune star a gidajensu           

Can ɗakin Ummi kuwa ƙiran sallan magriba da akayi ne yasa Hayatuddeen tashi ya wuce masallaci, Raleeya ma ɗakinta ta koma don yin sallah, Adda Rahama kuwa shirye-shiryen   tafiya ta somayi,  sam bama da niyan kaiwa dare tazo ba, saidai ganin halin da Zaleeha take ciki yasa bata tafi da wuri ba.             
Zaleeha kuwa babu laifi ta ɗanji sauƙin zazzaɓi da kuma ciwon kan daya rufeta. 
Hakan yasa ta ɗauro alwala tazo ta gabatar da sallah, koda ta idar da sallan bata tashi akan sallayan ba, jingina tayi da jikin gadon Ummi, tare da lumshe idanunta, wasu siraran hawaye ne suka biyo ta gefen idanunta suka sauƙa akan fuskarta.             Dai-dai lokacin Ummi ta shigo cikin ɗakin,  ƙarasowa jikin gadon tayi ta zauna.
  Cikin kulawa ta ƙira sunan Zaleeha'n,  ahankali taɗan ɗago kanta ta kali Ummi'n. kafaɗunta Ummi ta dafa cikin son sake bata karfin guiwa tace.       
"ki kwantar da hankalinki, Insha Allah gobe  zamuje za'a bawa Baba Malam haƙuri, kuma nasan zai haƙura ya yafe miki, sannan kuma Baba Malam ba tsanarki yayi ba, hakama ƴan uwanki, kawai dai suna fushi dake ne,  saboda abun da kikayi baki kyauta ba sam, bawai dan kina auren Saifuddeen bane yasa nace haka, a'a  ina faɗa miki hakane dan ni matsayin  ƴa na ɗauke ki, ke macece Zaleeha, duk kuwa mace me tarbiya irinki ba a santa da gudu ta bar gida ba, haka kuma ɗabi'ar guduwa ma sam bai kamata ace mace ta ɗaukesa ba,  bazan tursasaki faɗamin dalilin dayasa kika gudu ba, saboda nasan dama tuntuni bakyason auren ki da Saifuddeen, bakya sonshi dole akayi miki amma kuma duk da haka bai kamata ki tsalleke iyayenki ki tafi can wata duniya ba,  nasan kinyi nadama kwarai,  kuma insha Allah Allah Zai karɓi tubanki, kuma Baba Malam ma nasan zai yafe miki,  kawai dai yana fushi ne saboda yanda kikayi watsi dasu, amma nasan da zaran anbasa baki zai yafe miki, saidai kuma ina fatan zaki kiyaye gaba,  sannan kowata kikaga zata aikata irin abun da kika aikata zaki haneta."       Tuni hawaye sun gama wankewa Zaleeha fuska, tabbas tasan bata kyauta ba, kunyar Ummi ta rufeta yadda ta gane cewa bata son ɗanta ita kuma duk da haka bai hanata so taɓa.   wanda dalilin hakanne kuma kowa ke fushi da ita, ƴan uwanta sun ƙita saboda abun da ta aikata, Babanta mahaifi ya koreta duk akan abun da ta aikata, tabbas Ummi ta cika uwa ta gari, abun so ga kowa, ta aikata musu laifi amma sun ƙaunace ta, alokacin da kowa ya nuna mata tsana, su kuma sunjawota jikinsu, Babanta ya koreta, su kuma sun amsheta duk da laifin da ta aika ta musu suka bata mafaka,  tayaya zata fara misalta girman halaccinsu agareta? abune me girma da bazai kwatantu ba,  kukane ya ƙwace mata sai kawai ta kifa kanta akan cinyar Ummi, ta saki kuka'n.  
Awannan karon Ummi batayi yunƙurin hanata kukan ba, saboda ko ba komai shi kukanne zai rage mata zafi da raɗaɗin zuciya.  
Saida Ummi taga kukan yayi yawa sannan tashiga ɗan bubbuga bayan zaleehan tana shafa kanta.   
  Sannu ahankali ta rage sautin kukan nata, shiru tayi tana sakin ajiyar zuciya.   
Ganin haka ne yasa Ummi kamo hannunta suka fice daga cikin ɗakin, kai tsaye ɗakin dake gefen na Ummi'n,  Ummi takaita, wanda yake ɗakin su Raleeya ne wanda sukai budurci acikinsa, kuma nanne masauƙin Goggo Dada da Aunty Meena in sun zo, akimtse ɗakin yake sannan babu wani hargitsi acikinsa, akan gado Ummi ta zaunar da ita, toilet ɗin ɗakin ta shiga ta  haɗawa Zaleehan ruwan wanka me ɗan ɗumi.     Dubanta Ummi tayi cikin kulawa tace.
   "Kishiga kiyi wanka, zuwa gobe an gane key ɗin side ɗinki, dan yanzu na tambayi Hammansu key ɗin yace baisan inda key ɗin yakeba sai ya nema,
shiga na kiyi wonka sai kizo ki kwanta, ko za ki ci abinci nasa Hayatuddeen ya kawo miki."
Asanyaye  ta  girgiza kanta alaman
"A'a"   jinjina kai Ummi tayi sannan ta fice daga cikin ɗakin, tana mai tuna za'ayi daga da Saifuddeen dan tasan batun wai shi baisan inda key ɗin side Zaleeha yakeba duk cikin fushine ta lura ya fusata sosai da Zaleeha.   

Ita kuwa Zaleehan       cikin sanyi ta tashi ta shiga toilet

Please Login or Register in order to submit comment