Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

bacci ba ita ta tashiba sai 3:40 cikin ikon Allah kuwa jikinnata yayi sauƙi sosai don koda tatashi babu abun da takeji,  don taɗan samu kuzari ajikinta, still  Aunty Lubna da Maryam da Aunty Shatu ne suka tsaya kaida fata inda sukaga tasake sabon wanka,  to fa yanzukam meckup aka tsantsara afuskartata ta musamman,  kayan da tasa kuwa ya banbanta dana ɗazu, duk da kasancewarsu duka dogin riguna ne, saidai wannan na wani tsadadden shadda lace ne me matsifar kyau, shima ɗindai akwai ratsin ja ajikinsa, sosai yayi bala'in yi mata kyau, ɗauri ɗankwali aka zizara mata tare da yane mata jiki da babban mayafi, wasu tsadaddun sarka da ɗan kunne aka sanya mata, turare kuwa kusan ma wanka akayi mata dashi, don wani irin masifaffen ƙamshi take.
Gefe kuwa Rashida da Balkeesu ne zaune, balkeesu sai washe haƙoran munafurci take, yayinda take ta saƙa sharri acikin zuciyarta, bakomai yasama tazo ɗaukan auren ba face matsanancin gulma dake cinta tana son taje taga gidan kurma gurgun tunda Mama ta hanasu ganin kayan auren kam.

Cikin nutsuwa tarin motocin suka ƙaraso ƙofar gidan nasu Zaleeha, su Adda Rahama waƴanda sune zasu shiga gidan don fito da amarya suka fiffito, kaitsaye suka nufi cikin gidan.
Shi kuwa Saifuddeen ido ya ɗan lumshe tare da yin murmushi ganin wata benzz irin tasa tazo kusa dashi ta tsaya kana yaga a ƙalla yanzu motocin sun kai talatin banda guda biyar wanda sukazo suka samu a cikin ƙaton harabar gidan duk da girman wurin saida ya tsuke ya musu kaɗan wata motar har tana gogar wata, lips ɗinshi ya ɗan lasa gano harda motocin masu sun sace Zaleeha ne a wurin.

A cikin gida kuwa Aunty Lubna ce ta shiryata tsab inda ta rufe mata fuskarta da mayafin laffaya mai tsananin tsada da ƙyalli dake jikinta, Goggo Maryama ƙanwar Baba malam da Aunty Aisha ƙanwar Mama ce suka kamata harzuwa falon Baba Malam, inda Ya Ahamd, Ya Aminu, Malam Adam harma da Mamy ke zaune, nasiha sosai Baba Malam da yayunnata sukayi mata, inda suka gargaɗeta sosai akan zaman auren nata, nasiha sukayi mata irin mai ratsa zuciya da jiki, nasihace irin wanda ke nutsar da duk wata ƴa mace, saidai kuma ko kaɗan Zaleeha babu abu ɗaya data ɗauka daga cikin nasihartasu, hasalima kukan baƙinciki kawai takeyi, sukuma take suka cika da tausayinta domin kuwa duk atunaninsu nasihar tasuce ta tsumata har take kuka.
Ganin kukan nata yaƙarune yasanya Aunty Aisha da goggonta ƙanwar Baba Malam suka kamata, domin kuwa tuni Maryam itama tasa kukan rabuwa da ƴar uwartata, haka Zaleeha take kuka sosai, yayinda ayanzu take kukan mai dalilai biyu, dalilin farko shine auren ta da aka ɗaura da wanda bataso, dalili na biyu kuwa shine dalilin dake sa ko wacce amarya kuka da zubda ƙolla tanajin bege da kewa da zafin barin gidannasu da zatayi, tabbas tasan zatayi matsanancin kewar yayu da ƴan uwanta, hakanan takejin duk ba daɗi, haka Aunty Lubna da Goggo suka riƙota har zuwa compound ɗin gidan, kuka take sosai, tanamejin tsananin baƙinciki aranta don kuwa kowani taku ɗaya da zatayi zuciyarta tafasa takeyi, yayinda wani irin malolon baƙin ciki ke cika zuciyarta, sosai takejin takaicin kaita gidan Saifuddeen da za'ayi.
Haka suka nufi wajen motocin tare da tarin zugar ƴan rakiyar amarya wanda dama tuntuni su ake jira, Balkisu da Rasheeda ne tafe wanda dama mota ɗaya sukeson shiga da amarya, babuma kamar balkeesu don ita da biyu ma takeson zama kusa da Zaleehan, dan so take taƙara zugata sosae.

a cikin motocin kuwa text Saifuddeen ya turawa Aziz na numbers ɗin motocin da suke zargi,
amsa ya tura mishi da cewa.
"Ba matsala duk nabisu na sace iskar tayun bayansu, sai ta motar dake kusa damu nan na barta amman naja tamu mutar na matsesu basuma da damar motsawa, na kuma gayawa Ahmad ya fito cikin motar taku yayiwa amarya jagora ,zakaga gefen hagu da daman ku akwai mata uku uku sojojine cikin farin kaya."
murmushi mai cike da nasara Saifuddeen yayi.

Shi kuwa Ahmad yana ganin fitowarsu yayi saurin ƙarasawa garesu, shiyayi musu jagora zuwa motar da za'a sanya amarya wato wanda Saifuddeen ke ciki, shida kansa Ahmad ya buɗe mata ƙofar motar, Aunty Lubna ne ta sata cikin motar, ganin Saifuddeen zaune acikin motar yayinda hankalinsa gaba ɗaya kekan laptop ɗinsa, yasanyata sakin murmushi, lallai tajinjinawa ƙauna irin na Saifuddeen da sauri ta kamo hannun goggo Maryama dake shirin shiga tace.
"Tsaya Goggo angon yana ciki, shi yazo ɗaukan amaryarshi da kanshi."
Ahmad ne ya ɗanyi murmushi tare da cewa.
"Sabida tsarone babbar yaya ba don tsoro ba."
dariya sukayi cikin happy Balkeesu ne tay kamar bata jisuba tasoma ƙoƙarin shiga motar, da sauri ta ɗan dawo da baya ganin Saifuddeen hakimce acikin motar haibarsa da kimarsa da kwarjinta sun bugi zuciyarta shakkarshi mai yawa ta rufeta, bisa ɗole taja da baya,
Ya Ahmad da Adda Maryam ma dake gefensu murmushin jin daɗi sukayi sabida sunga tarin so da kulawar Saifuddeen a kan ƙanwar tasi, dan ya gayawa ya Ahmad duk abinda ke faruwa na son sace amarya, ya faɗa mishine da kashedin karfa wasu suzo su basu amarya su jira sai sunzo da kansu
.Su Bilkeesu kuwa bisa dolensu suka shiga wata mota ta daban.

Ahankali duka motocin ke tafiya a jere a jere.

Sosai hankalin yaran Dalla yayi matuƙar tashi ganin duk motocin sun fice sun barsu sai nasu kawai ,nasun kuma duk sunyi faci, sai ƙwaya ɗayar nan,
koda suka shaidawa Dalla hankalinshi yayi masifar tashi to waya gano shirinsu, waya ɓata mishi tsarin sace matar wannan gurgun kurman,
dole a tsorace suka fita da motocin a haka suka lallaɓa suka isa wurin mai sa iska,
yayinda duk abinda sukeyi Saifuddeen na ganinsu a system ɗinshi ta sanadin na'urar bibiya da ya bawa Hayatuddeen ya liƙa musu a jikin motar da take irin tasa.

Tunda tashiga cikin motar ta cusa kanta atsakankanun cinyoyinta kuka take sosai har kaman zata shide, samma batasan dawa take tare ba acikin motarba, ta gefen ido yake kallonta, hakan ne ya tabbatar mishi kuka takeyi.
Sosai yakejin kukan nata na taɓa masa zuciya da jiki dan jikinshi ya bashi kuka take ga kuma alamu yana ganin yadda ta takure tana shessheƙa, saidai kuma tun shigowarta motar ko ɗago kansa baiyi ba, gaba ɗaya ya maida idanunsa akan system na laptop ɗinsa, saidai kuma duka hankalinsa na gareta, ɗan ɗagowa yayi tare da numfasawa, cikin nutsuwa ya rufe laptop ɗin bayan ya saita abinda zai naɗe mishi diddigin yaran Dalla sai dai akasi kaɗan da aka samu lokacin da yasa yayi ƙarancin binsu har inda zasu isa,
ido ya zuba mata cikin jin tausayinta yasan halinda mata kan shiga lokacin da suke barin gidan iyayensu zuwa gidan mazansu, dan bai mance auren Raihana ba da Adda Rahma ke badu labarin daga cikin gombe har suka isa Kaduna Raihana bata bar kukaba sai ta ɗanyi shiru sai kuma taci gaba har suna mata dariya wai hutawa takeyi bare da dama sun san Raihana saurin kuka gareta,
ido ya lumshe tare da buɗesu ya zuba mata su, ahankali ya sanya duka hannuwansa akan kafaɗunta, ɗan ɗagota yayi kaɗan,
ita kuwa Zaleeha jin anriƙe kafaɗunta ne yasanyata yin tunanin Aunty Lubna ce, hakan yasa batare data buɗe idanunta ba, haka bata yaye mayafin dake kanta ba, tafaɗa jikinsa, sakin sabon kuka tayi tare da sanya hannuwanta duka ta zagaye cikinsa, cikin kukan fitar hayyaci tace.
"Dan Allah Aunty Lubna ku maidani gida, wallahi bana son barin gida,karku kaini cikin bare ban sansuba basu sanniba, wlh bana sonsa, natsanesa, ko ganinsa banason yi, mutuwa zanyi matuƙar kuka kaini gidansa, dan Allah Aunty ki taimakeni, taƙare maganar tana me cusa kanta cikin ajikinsa.
Ahankali ya lumshe idanunsa, tare da sanya duka hannuwansa ya ƙara jawota jikinsa, wasu irin tagwayen ajiyar zuciya ya rinƙa sauƙewa take wani irin zazzafan shauƙi ya shiga ratsa zuciyarsa da jikinsa.
Jin wani masifaffen ƙamshi mai azabar daɗin ji da shaƙa wanda bata taɓa jin irinsa ba na shiga cikin hancinta wanda ba ƙamshin Aunty Lubna bane yasanyata ɗan jan jikinta baya, ahankali ta ɗago kanta, azabure tawani irin jan jikinta baya, kallon fuskarsa da yayi masifar kyau wanda ita da kanta sauda ta ganshi kamar balarabe, ganin shinne yasanya komai ya ƙwace mata, wani irin baƙin ciki ne ya cika zuciyarta take tasaki kuka tare da maida kanta ƙasa, wani irin tafasa zuciyarta keyi mata.
Ƙawataccen murmushi Saifuddeen yayi tare da maida bayansa ya jingina da jikin kujeran, lumshe idanunsa yayi yayinda yake shaƙan dadaaɗan ƙamshinta, runguman da tayi masa yasanya yaji wani abu na tsargawa ta cikin jikinsa, sam baiyi yunƙurin sake taɓa ta ba, haka kuma bai hanata kukan da takeyi ba, ahaka har suka iso cikin katafaren gidannasu.

Nan fa ƴan kawo amarya kowa yacika da mamakin haɗuwar gida, masu son auren sai masha Allah kawai suketa cewa,
Goggo Maryama ce ta riƙeta inda tace tashiga gidan da ƙafar dama haɗi da bismillah, ranta aƙuntace haka tayi bismillah duk da cewa bawai ganin gabanta takeyi ba, zuwa yanzu tama daina kukan, jira kawai take Saifuddeen yace da ita wani abu ta sauƙe masa kwandon bala'i.
Baƙaramin mamaki kyan ɓanagaren na Zaleeha ƴan uwanta sukayi ba, don kuwa komai yayi harma ya zarcewa tunaninsu, koda Balkeesu taga uwar dukiyar da aka kashewa Zaleeha, dakuma irin tsaruwan gidan al'afarma part ɗin nata, saida taji wani abu kaman mashi ya caki zuciyarta, sam bata ɗauka haɗuwar wajen zaikai har haka ba.
Acan cikin ɗaki aka zaunar da Zaleeha.
Sannu ahankali jama'a ke watsewa don nan da wasu awanni za a gudanar da diner, Rasheda ma tatafi don zuwa taho da me meckup ɗin da zatayiwa amarya, hakanne yabawa Balkeesu daman ƙara hurewa Zaleehan kunne, sam tace da ita tadaina asaran hawayenta, tabari idan hidiman biki ya kammala plant ɗinsu da suka haɗa sai ya fara aiki, sosai Zaleeha kuwa tahau kan maganan na Balkeesu ta zauna wanda zugan bilkeesu da asirin mma yazo iri ɗaya.

Kamar yanda al'adan Gombawa yake aduk sanda aka kawo amarya gidansu ango, to fa akan tarbesu da kayan ciye ciye dana shaye shaye, hakance takasance agidansu Saifuddeen dan kuwa sosai aka cikawa su Zaleeha kayan ciye ciye, komai cikin wadata akayisa, abun ma har mamaki yake bawa wasu daga cikin dangin Zaleeha don kuwa kuɗi sosae gidan su Saifuddeen ɗin ke kashewa wajen ƙawata komai nasu, kamar basajin ciwon kuɗin.
Ya Habu kuwa da ya Aminu har cikin ɗakin suka shigo suka gargaɗeta akan batun diner muddin tayi abinda zai kunya tasu Habu yace.
"Wlh rabaki gida biyu zanyi kin sanni ba mutun cine da niba, ni ba irin ya Ahmad bane."
Dolenta ta nitsu koda suka tafi ko motsin kirki bata kuma yiba.

Kasancewar ƙarfe 8:00 pm dai-dai za a fara gudanar da diner'n hakan yasa amarya Zaleeha tana idar da sallan isha aka soma tsantsara mata meckup akan fuskarta, musamman aka ɗauko ƙwararriyar meyin meckup inda tazo ta baje basirarta akan fuskar Zaleeha, wani irin haɗaɗɗen meckup aka tsantsara akan fuskar Zaleeha wanda yayi bala'in fito da kyawun fuskarta,
dakanta ta zura wata haɗaɗɗiyar fitted weeding gown mai azabar kyau, jifa jifa aka sanya ratsin fari ajikin rigar, rigace irin doguwa ɗinnan wanda har sharan ƙasa take, sosai rigan takama jikinta tazauna ɗas, inda gefe da gefen waist ɗin rigar aka sanya wani irin yadi mai sharara wanda yake da masifar tsawo, haɗuwar rigar ya zarce misali, musamman ma yanda ya zauna ajikinta yayi ɗas, tabbas ko ba a faɗaba kallo ɗaya zakaiwa rigar kasan da cewa taja maƙudan kuɗaɗe wajen tsarata,
haɗaɗɗen ɗaurin ɗan kwali irin na amare aka kafa mata akanta, bayan anyi parking dogon gashinta atsakiyar kanta, inda aka sanya mata wani haɗaɗɗen sarƙan gold mai tsananin kyau da tsada, dagakan ɗankunne har zoben dake hannunta duka na gold ne, masu masifar tsada da kyau, wani irin takalmi mai masifar tsini ta sanya aƙafafunta, bakaɗanba tayi kyau nafitar hankali, harwani ɗauke ido take, turare kuwa kamar ɓarinsa akayi ajikinta, sosai Zaleeha tayi kyau cikin shigarta ta diner, inda kowa ke yabawa da tsantsar kyawun da Allah yayiwa Zaleeha, ita kanta Zaleeha tasan cewa ayau ɗin tayi kyau.

Gombe International Hotel

Sosai aka ƙawata babban falon wanda ananne za a gudanar da diner ɗin, anyiwa wajen ƙawa naban mamaki tare da haɗaɗɗen decoration na peach and white, sannan kuma daga sama adon decoration blue akayi mai masifar kyau, gurin acike yake da jama'a , inda kowani team da kalan shigarsu, gabaki ɗaya abokan Saifuddeen shigar shadda blue colour ce ajikinsu, inda gefe guda kuwa su Hayatuddeen ke sanye da peach colour ɗin shadda, daga gefe kuwa su Adda Rahama suka tsantsara ado cikin wani tsadadden farin lace mai adon blue, gurin tuni yacika da jama'a zuwan ango da amarya kawai ake jira.

Ɓangaren Zaleeha kuwa ana gama tsantsara mata kwalliya Rasheeda ta sanar dasu zuwan ango, hakan yasa aka ƙara ƙawata mata adon nata, Balkeesu da Rasheeda na riƙe da ƙasan rigarta dake jan ƙasa suka nufi compound ɗin gidan.

Saifuddeen ne zaune acikin wata rantsatstsiyar mota yabala'in yin kyau acikin farar shadda mai peach colour ɗin aiki dake jikinsa, yayi kyau fiye daduk wani tunani mai tunani, idanunsane suka sauƙa akan tauraruwar amaryarsa wanda tsananin kyawun da tayi yaso zautar dashi.
A hankali suke taku tamkar wahainiyoyi, suna isa gab ɓakin motar Saifuddeen ya...!


Littafin nan na kuɗine in kika ganshi a woje to na satane kuma yaseeen doguwa aradu in kina buƙata turo katin mtn na 300 kacal ta wannan number 09097853276 ko kuma kimin transfer ta 0005388578 jaiz bank Aisha Aliyu Garkuwa.

By
*GARKUWAR FULANI*
10/4/20, 7:04 PM - Mmn Khalid: _Shafinga ƙyauta ne gareke babana, Ali Wambai, inai maka fatan al'khairi a rayuwarka, yaro mai sunan manya Allah yasa ka samu nagarta irin na masu sunan naka_


A hankali ya lumshe Kyawawan idanunshi, tare da furta.
"Masha Allah!." a cikin zuciyarshi sosai tayi masa kyau acikin shigar wedding gown ɗin nata, har wani ƙyallin kyau take kamar wata tauraruwa, komai nata yazama wani na musamman,  cikin nutsuwa haɗi dajan aji irin na amare suka ƙaraso wajen motar Saifuddeen ɗin, da sauri Sule driver ya ƙaraso inda ya buɗe murfin motar da kansa, idanunta dake cikin wani ɗan siririn mayafi ta rumtse sakamakon ƙamshinsa da yadaki hancinta, sakamakon buɗe marfin motar da akayi, da taimakon Balkeesu tashiga cikin motar, ƙasa-ƙasa Balkeesu ke kallon Saifuddeen, sosai yayi bala'in yin kyau, saikace wani balarabe, komai nasa is perfect, sosai Saifuddeen ya haɗu, haƙiƙa musamman a irin wannan rana ko maƙiyinsa bai isa kushesa ba.
Zaleeha na gama shiga cikin motar Sule driver ya maida murfin motar ya rufe.
wata muguwar hararan Balkeesu ta abkawa Sule driver, cikin takaici tabi Rasheeda suka shiga wata mota ta daban.

Ahankali Sule driver ke tafiya dasu acikin motar,   idanu Saifuddeen ya lumshe tare da jingina bayansa da jikin kujeran motar, sosai yake shaƙan daddaɗan ƙamshinta, hakanan haɗewar ƙamshin turarensa da nata  suka ba da wani irin yanayi me daɗin gaske, irin yanayin ƙamshin nan mai sauƙar da kasala uwa uba ga sanyi Ac da motar ke busa musu,    cikin nutsuwa ya ɗaura hannunsa ɗaya akan nata hannun, take haɗuwar lallausan fatar jikinsu waje ɗaya ya ƙara sauƙar masa da kasala, cikin ƙunan rai da hatsala Zaleeha tayi yunƙurin janye hannunta baya, amman sai ta gaza hakan jin ya rumtse tafin hannunta cikin nashi sosai zuciyarta ke tafasa, gefe guda kuwa ga ƙamshin turarensa wanda gaba ɗaya yabi ya cika mata hanci yana birkita mata kwanya sai shaƙar daddaɗan ƙamshin nashi takeyi, wanda tsabar tsanan da tayiwa mai turaren yasa take ta son cusawa ranta tsanan ƙamshin turaren nasa har wani abu me ɗaci-ɗaci take rayawa kanta takeji acikin maƙoshinta, zuwa yanzu har rasa yanda zata misalta tsanarsa aranta takeyi,  komai bayayi mata daɗi, tana daurewa ne kawai don plant ɗinsu da suka shirya yakai ga ci, ga kuma gargaɗin ya Habu wanda tasan ba mitunci ne dashi ba, bacin haka babu wani abu da zaisanyata zuwa wannan banzan diner'n toma da wanne angon zata taka ta shiga.
Ganin tajanye hannunta daga cikin nasa yasanyashi maida kansa jikin lallausan kujeran motar, numfashi yake fitarwa ahankali, yayinda wani irin kasala ke sake lulluɓe masa jiki.
Kowannensu zuciyarsa ɗauke take da tunani kala-kala shi ji da gani yake kamar bata tsiraba daga sharrin masu son saceta da haryanzu hidimar bikin bata barshi ya gama bincikosu ba,
ita kuwa ji take da zama kusa dashi gwara zama kusa da bakin kura.
A haka suka ƙaraso babban wajen wanda aka ƙawatasa iya ƙawatuwa, wato Gombe International Hotel, sosai wajen ya haɗu komai gwanin burgewa ga kuma tsaron da dole yasa yaran Dalla barin wurin.
Acan cikin babban hall din da za'a gudanar da diner ɗin kuwa, kowa zuwan ango da amarya kawai yake jira,  gaba ɗaya mutanen dake wajen zuciyarsu awanke take da farinciki, yayin dasu Hayatuddeen keta ɗaukan pictures, suma zuwan ango da amarya kawai suke jira kafun nan abasu filin cashewa, don al'ƙawarine yau sai gaba ɗayansu sunnu nawa Hamma Saifuddeen ɗin gata, wannan rana itace ranan da Hayatuddeen dakuma gaba ɗaya dangin da abokan Saifuddeen ke jira, hakan yasa suke fata da burin faranta ran ɗan uwannasu tahanyar ƙawata masa bikin nasa yanda zaiyi armashi.
Labarin isowar ango da amarya da MC yajine yasanyashi soma labartawa jama'an wajen cewa.
"Allah yayiwa ango da amarya isowa."
Nanfa kowa ya zubawa ƙofar hall ɗin ido, gaba ɗaya mutanen wajen sun zaƙu dason ganin amarya da angon.
Ishaq wanda yasha dakakkiyar shaddarsa blue tare da wani haɗaɗɗen glass, wanda idan baka san shiba bazaka taɓa shaida cewa makaho bane, don kuwa komai nasa irin na masu gani yakeyi,  Ishaq da kuma Ahmad haɗi da Hisham da kuma Aziz wanda yana ɗaya daga cikin abokan Saifuddeen wanda sukayi Gombe State University tare sune suka fita don zuwa taro ango da amarya, wanda dama tuni su Balkeesu da Rashida suna da ƙannan Ya Aminu yaran Yayan Baba malam da yara Goggo Maryam da dai sauran ƴan uwan amarya waje, don kuwa sune suka riƙewa amarya Zaleeha ƙasan rigarta dake da matsanancin tsawo, wanda dole ya zama sai an riƙe mata shi.
Sule driver ne ya ya buɗewa Saifuddeen ƙofar motar tare da ware masa sabuwar kekensa mai azabar kyau, har wani ɗauke ido da ƙyallinta keyi
Cikin azama da alamun iya sarrafa kai da cikar nitsuwa ya hawa kan keken Saifuddeen ya dai-daita zamanshi hakan kuwa sai yayi bala'in ƙarawa kwalliyar tasa armashi, don kuwa wani irin kwarjini ne yasake bayyana atattare dashi, zamansa akan  wheelchair ɗin nasa sai ya ƙara masa girma da wani irin kima, ya fito tamkar jinin sarauta sule driver ne ya buɗewa Zaleeha murfin motar, ahankali ta zuro da kyawawan ƙafafunta wanda sukaji tsadaddun takalma masu kalan pitch,  tana gama fitowa daga cikin motar, su Rasheeda suka tattaro ƙasan rigar nata inda suka riƙe mata shi, ahankali Saifuddeen ya danna madannin wheelchair ɗin, take yasoma tafiya dashi, cikin nutsuwa yaƙaraso inda Zaleehan ke tsaye, kasan ceqarshi dogo, kuma wheelchair ɗin yafi sauran tudu, kana tanada maddan da za'a ƙara tunda ko a rage sai ya zama yayi tsawo in ka hankosu zakayi zaton a tsaye yake hannunshi yasa ya kamo nata ya ɗan haɗe tafukan hannunsu ya rumtse.
Ahankali suka soma takawa inda yake sarrafa wheelchair ɗinsa cikin nutsuwa, wani irin haɗuwa da burgewa tsarin tafiyan tasu ya bada, duk dacewa shi yanakan wheelchair ne, amma kuma sai hakan yaƙarawa kwalliyar tasu armashi, don kuwa zamansa akan wheelchair'n ya bayyana tsantsar ajinsa da kuma kwarjininsa da kima da kamala uwa uba ƙasaita, hakan yasa mutane da yawa zasuyi masa kallon zallan ajine da kasaita yasanyashi naɗewa akan kujeran, wanda saima ka lura sosai zaka iya gane cewa wheelchair ne don kuwa kujera ce mai tsananin tsadan gaske, musamman aka kawo masa ita daga Germany.
Ishaq da Ahamad ne ke biye dasu, saikuma su Rashida dake riƙe da jelan rigarta, bayansu kuwa Aziz da wasu matasa wanda sune zasu bada tsoro a wurun dan yanzuma akwai mashunan UD da suke zargi a wurin.
Jabeer ne da kuma Hisham ke biye dasu Ahmad ɗin a baya, sosai tsarin nasu yayi kyau,  cikin nutsuwa suka kutso kansu cikin hall ɗin.
Lokaci guda mutane suka somayin hanmdala sakamakon ganinsu, dan sunyi bala'in burgesu, nanfa Diamond Photograpgy suka soma aikinsu na ɗaukan hoto, sosai akeyi musu hoto, ga wani sassanya kiɗa dake tashi. Ahmad da ishaq da Salisu da Aziz kuwa da yayyafin kuɗi suka biyo bayan ango da amrya,
yayinda rashida kuwa ke fesa wani abu mai ɗan karen ƙamshi kana yana bada kalan wal-wali.
ɗaukansu hotuna tako ina, don sun bala'in yin kyau da dacewa, yanayin yanda Saifuddeen ke hakimce akan kujeransa shiya ƙara zautar da mutane, don hakan ya masifar ɗago ajinsa, sosai yayiwa kowa kwarjini, take ƴan matan da suka samu halartan wajen diner'n suka mato akansa, sosai dayawan mutane ke hamdala da godewa Allah, don kuwa tabbas Saifuddeen ya cika cikakken namiji kuma ingarma, maiji da tashen kyau haɗi da kwarjini,  haka kuma mutane da yawa ke yaba tsananin kyawun da amarya Zaleeha tayi, don kuwa kowa na iya hango beauty face ɗinta ta cikin wani ɗan abun da aka ɗiga mata akanta wanda yaɗan rufe gefen fuskarta kaɗan, sosai su Adda Rahama ke yaba kyawu da haɗuwar Zaleeha, tabbas sai yanzu suka tabbatar da cewa bawai abanza Saifuddeen ya nace akan cewa sai ita ba, haƙiƙa Zaleeha tacika mace abunso ga kowani irin ɗa namiji, sannan kyawunta ya isa kyau,  sosai kowa yaga dacewarsu da Saifuddeen ɗin, don kuwa kyaune ya gauraya da kyau.
Wani irin cool music  na Ed sheeran mc ya sakar musu irin mai taɓa zuciyar nan, hakanne ya ƙara bawa tafiyar da sukeyi armashi,  Hayatuddeen da abokansa ne suka zo sunayi musu live vedio, 
Ahaka har suka ƙarasa wajen da aka ƙawata domin zaman ango da amarya, wajene wanda aka ƙawatasa da decoration mai kyaun gaske, wanda akayi amfani da colours irin na kayan dake jikin ango da amarya,  cikin nutsuwa Saifuddeen yayunƙura ya sauƙa daga kan kekensa cikin nutsuwa haɗi da salon mai armashi ya hau kan wata rantsatstsiyar royal chair wanda tagaji da haɗuwa,  Rasheeda ne ta zaunar da Zaleeha agab dashi har takai ga jikinsu naɗan gogan na juna.
Kamar yanda aka saba ango da amarya na zuwa wajen diner ake fara gudanar da shagulgula hakanne yasanya babu wani ɓata lokaci MC yabuƙaci da babban abokin ango akan yazo yaɗan basu biography na ango.
Ishaq wanda fuskarsa ke ɗauke da murmushine yataso inda ya ratsa cikin yawan jama'an tamkar wanda yake gani haka yaƙarasa gaban MC, mike  ya karɓa inda yayi gyaran murya, cikin nutsuwa haɗi da kamala yasoma bada ɗan taƙaitaccen tarihin Saifuddeen ɗin, sosai biography'n na Saifuddeen ya taɓa zuciyar kusan gaba ɗaya mutane dake wajen, duk da cewa in brief Ishaq ɗin yayi komai, amma tabbas rayuwar Saifuddeen cike take da al'amura masu sosa zuciya, dayawan mutanen da basusan Saifuddeen ɗin ba, sai alokacinne ma suka san da cewa shiɗin kurmane, koda Ishaq yagama bada ɗan taƙaitaccen tarihin na saifuddeen, take jama'an wajen suka soma tafi,  sosai aka jinjina gwarzantaka irin na Saifuddeen don haƙiƙa yacika Namiji. Ishaq na komawa, still Mc yasake buƙatan babbar ƙawar amarya don tazo ta bada biography na amarya.
Tsulum Balkeesu tasoma ƙoƙarin miƙewa zuciyarta cike da mugunta, don kuwa dama tuni tagama kitsa kalaman da zata faɗa agame da amaryan, haka kuma tashirya gasawa Ango magana afakaice, saidai kafun ta farga  sai tsintar muryar Rasheeda tayi acikin kunnuwanta, wanda sanin halin Balkeesun da mugun nufinta ne yasanya Rasheeda rigata zuwa, don tabbas tasan balallai abun da Balkeesu zata  faɗa yazamanto al'khairi ba, wannan ranan kuwa ta farinciki ce, sam batason aɓata ran kowa, sudai da suka ɗaukawa kansu dala ba gammo sai suyita fama.
Cikin nutsuwa Rasheeda ta ɗan bada taƙaitaccen tarihin Zaleeha, wanda kuma iya abun da ta sani ta faɗa, nan mutane da yawa suka ƙara gaskata cewa lallai Amaryar Saifuddeen ɗin ƴar ƙwalisa ce, don aɗan biography ɗinnata

Please Login or Register in order to submit comment