Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ke cike da farin ciki yana kulada matarsa sanyin idanunshi tamkar ransa .

A hankali rayuwa ke juyawa watanni na tafiya tuni lokaci ya tafi.

Numan.

To zuwa yanzu dai Zaleeha tana jin zazamanta cikin garin Numan ɗin tamkar zama cikin kurku ne, domin hankalinta da nitsuwar kab basa jikinta,
Kullum da begen iyayenta da ƴan uwanta take kwana, musaman Adda Maryam da suna magana da ita.
Tana son komawa cikin ƴan uwanta tayiwa mahaifinta biyayya amman sai taji bazata iyaba.
Sauƙin ta ɗaya tana ɗan samun nitsuwa cikin musulmai ƴan uwanta na rugar fulanin nan,
do kuwa sosai sukayi sabo da Aisha, sannan kuma tana ɗebe mata kewa,
Damuwar da take ciki ya baiyana a jikinta domin ta rame fuskarsa tayi fiyau sai dai daga ɓangaren kyawunta kuwa sai abun da yaci gaba, dan wani irin fresh skin ɗinta yayi, komai nata yayi normal, fatarta takara haske da sheƙi sakamakon kayan fruits da take ci da kuma yanayin ni'imar wurin, ita kanta tanajin sauyi ajikinta sosai ramar da tayi sai yasa hancinta ya ƙara baiyana, daga gefe kuwa kullum Aisha saita kawo mata abinci daga gidansu, Man Liman kuwa sosai yake janta a jiki in tazo ta sameshi a gida har sun ɗan saba.

Yauma tana gidan su Aishan kasan cewar yau jumma'a ne bayan an sauƙo daga sallan jumma'an ne Man Liman ya iske su a tsakar gida ƙarƙashin bishiyar ceɗiya bisa dukkan alamu suma sallan sukayi.
Cikin girmamawa suka haɗa baki wurin ce mishi.
"Baffa sannu da dawowa."
Murmushi yayi tare da miƙa musu ledan cefen da ke hannunshi tare da ce musu.
"Yauwa sannunku tagwayen Baffa, kunyi sallanko?."
Murmushi sukayi tare da gyaɗa mishi kai alamun eh.
Man Liman dattijone me karamcin gaske,
Har ya wuce sai kuma ya juyo ya kalli Zaleeha cikin fullanci yace.
"Zaleehatu taho ki ɗan rubuta min wani abu, ke kuma Aisha wonke allon ƙarfen can ki miƙo min."
Da sauri sukace to tare da miƙewa.
A hankali Zaleeha ta shiga sashin baffa,
kan taburma ta sameshi bisa farin buzunshi, gefenshi ya nuna mata tare da cewa.
"Zauna nan wasiƙa zaki rubuta min zuwa ga sarkin numan, dan arnan garin sun samu a gaba."
Cikin ganin girman dottijon tace to.
Kana ya gaya mata duk abinda zata rubuta, ta rubuta mishi sannan ya kira wani ɗanshi ya kaiwa ɗan aikensu takardar.
Har ta yunƙura zata tashi sai kuma ta koma ta zauna jin yace.
"A a zauna Zaleehatu ban gama da keba."
Murmushi tayi tare da cewa.
"To". Gyara zamanshi yayi da kyau ya fuskanceta kana a hankali yace.
"Zaleeha."
jin yadda ya kirata yasa ta amsa a nitse, cikin kulawa yace.
"In na tambayeki wani abu zaki gaya min gaskiya, kuma. Sannan ban miki shisshigi bako?."
Da sauri ta jujjuya kanta tare da cewa.
"In sha Allah zan gaya maka iya gskyar da na sani. Kuma ka tambayeni duk abin da kakeso dan ka isa katambayenin."
Gyaran murya yayi tare da cewa.
"Ke ƴar wanne garine?."
Cikin nitsuwa tace.
"Baffa ni bagombiyace."
Kai ya gyaɗa cikin gamsuwa kana yace.
"Me sunan mahaifinki?."
a take idanunta suka cika da hawaye, murya na rawa tace.
"Sunan babana Malam Bashir Sulaiman Dukku."
Fuska cike da al'ajabi Man Liman yace.
"ikon Allah Malam Bashiru ne mahaifinki?".
cin mmki tace.
"Baffa ka sanshi ne?".
Kai ya jujjuya mata tare da cewa.
"Eh to ba a zahiri na sanshiba ina dai jin azuzzukan shi, a radio, shiyasa bai zama ɓoyeyyen mutunba".
Sai kuma ya gyara zama tare da zuba mata ido cikin kula yace.
"To amman meyasaki daga tambayar sunashi kika fara zubda hawaye?, kuma meya kawoki nan cikin arna kika zauna Zaleehatu gaya min meyasa?."
Hannunta tasa ta share hawayenta dake zuba tanajisa kamar matsayin Babanta mahaifi, cikin rawar murya ta bashi labarin duk abinda ya faru na sanadin gudowanta har kwana a gardin da takeyi bata ɓoye mishiba, ta ƙara da cewa.
"Ina so in koma in je in bawa Baba malam haƙuri inyi mishi biyayya kan zaɓin dayamin amman ji nake bazan iyaba gani nake kamar in na koma zan mutu, nasan babana da ƴan uwana duk sunyi fushi dani".
Nisawa yayi tare da gyara zama cikin kula yace.
"Ae bazaki komaba Zaleehatu sabida kafa akayi anan matuƙar ba'a karya sihirin dake jikinki ba, haka bazaki iya yiwa mahaifinki biyayya, kuma dolene yasa kikayi ta gudun ɗakinki kina kwana cikin ciyawayi, domin an miki turen sihiri a ƙarƙashin gadonki, muddin ba'a karya sihirinba ɗakin zaike miki duhu zaina baki tsoro, kuma sihirin da akayi miki kin maganshi a mafarki sai in kin manta ne koda yake an rufe bakinma bazaki iya faɗiwa ko abinda kikeji ba, nima kaina yau tsawon wata uku kenan ina miki tofi cikin abincin da ake mishi shiyasa kika samu damar min bayani da izinin Allah."
Shiru tayi cikin sanyi tace.
"Baffa bana son mijin da aka haɗani dashi wanda nacema ya taimakenin nan shine nakeso."
Murmushi yayi tare da cewa.
"Kada ki damu, dukkan wani farin cikinki yana ƙarƙashin inuwar mijin da aka aura miki, na nemi al'farma kada ki sake cewa bakya son mijinki, kuma kada ki sake cewa akwai wanda kikeso bayanshi kisa a ranki shine ya taimakeki kuma dashi aka haɗaki, sai kici gaba da yiwa shi wancan ɗin addu'ar Allah ya azirtashi da mafificiyar al'janna Allah ya taimakeshi fiye da yadda ya taimakeki, Allah yasa soyayyarshi a zuciyar maƙiyanshi soyayya ta rinjaƴi ƙiyayyarsa a zuƙatan makusan tansa wlh in kin masa haka kin gama mishi komai sannan in kin yiwa mahaifinki biyayya zaki samu dukkan salama. Kiyi min wannan al'ƙawarin ni kuwa daga yawau zan fara baki addu'oi insha Allah zaki rabu da duk wani sihiri kuma zaki koma ɗakinki."
Cikin jin sanyin da tunda ta gudo bataji ba tace.
"To baffa in sha Allah zanyi ta mishi addu'a, ngd da taimako."
Murmushi yayi kana a hankali yace.
"Akwai wacce ke zuga mahaifiyarki, kuma ta asirce mahaifiyarki ne, da bata isa ta mata musuba,duk abinda tasata ko bata so sai tayi, amman ina karya abin jikinki itama abinda ke jikinta zai karye domin sunan ALLAH a duk inda take zaije ya sameta".
Ganin tayi shiru ne ya sashi ɗan sahir tawa tare da cewa.
"Ko Mamanki bata da yar uwa da suke tare".
A hankali ta gyaɗa mishi kai tare da.
"Tana dasu ɗaya musul mace ɗaya kuwa arniya ce".
Murmushi yayi tare da cewa.
"Ba Shatuba ai ita hasken addini na jikinta da zuciyarta, ita ɗayar dai domin ita burinta Mamanku daku yaranta duk kuyi ridda ku koma addininsu, to kuma ya rigada Allah ya tsareku kana mahaifinku a tsaye yake a kanku kun kuma samu cikakkiyar tarbiya."
Ajiyan zuciya ya sauƙe tare da cewa.
"Akwai kuma ƙawayenki cikinsu wacca kikafi so ɗin ita ke cin dunduniyarki, amman da zaran kin samu waraka da abinda akayi miki, keda kanki zakiji bakya son mu'amala da ita".
Cikin mutuwan jiki tace.
"Baffa ina son komawa gida".
Murmushi yayi tare da cewa.
"Zaki koma in sha Allah, yanzu zamu fara addu'oi tsawon sati biyu, daga randa zamu fara miki rubutu kina sha kuma duk mafarkin da kikayi ki sanarmin".
Kai ta gyaɗa alamar to.
Hahira sukayi sosai da Baffa'n, nan ta ƙara faiyace mishi irin yanayin da takejin kanta aciki, wanda sau da yawa tanajin son komawa gida aranta, amma saita najin kaman kafata agarin akayi, cikin son kwantar mata da hankali Baffa'n yace.
"Insha Allah zai taimaka mata da wasu addu'o'i wanda zatana sha, da kuma wanda zata nayi."
Nan dai tayi masa godiya sosai, dan ita kanta tanajin son komawa gida acikin ranta.

Bayan wasu ƴan kwanaki ne kuma Baffan yasa, Aisha tayi ƙiranta, nan yabata wani ruwan addu'a yace tana sha tana shafawa jikinta.

Sai kuma haɗin ayatushshifa da ganyen magarya guda bakwai, da kuma zam-zam, yace tana amfani dasu, ƙara jaddada mata yawan yin azkar da kuma zama da al'wala yayi, nan dai tayi masa godiya sosai.
Cikin ikon Allah kuwa yau kwananta biyu da fara amfani da maganin, sannan kuma tanajin sauƙin wasu abubuwan.
Gashi daren jiya ne Adda Maryam taƙirata awaya, sosai kuma tayi mata nasiha, mai ratsa jiki, wanda kalamanta suka ƙara sanyawa taji gaba ɗaya jikinta yayi sanyi.

A gefen Solomon da matarsa kuwa zaman Zaleeha a gidansu yasa hasken addinin musulunci yana ratsa zuƙatansu, suna ganin daraja da kimar addinin musulunci fiye da nasu addinin har an kai matin da yanzu sun fara watsi da addininsu dan sai ayi lahadi uku basuje majami'arsuba, zuwa yanzu Zaleeha kuwa tana tallata musu addinin dayi musu tayi su shiga domin shine hanyar tsira, kana tana ƙyautata musu sosai da kuɗin dake hannunta irin kyautatawar da musulunci ya umarci musulmi yayiwa ahlul kitab dan da kyautata zasu ƙaunaci addinin su san addinine mai sauƙi da tausayawa, to zuwa yanzu dai Zaleeha na zaton musuluntar su Solomon da elizabet a ko wanne lokoci.


Kwanci tashi babu wuya, inda yanzu cikin Ameena yakai wata bakwai, sosai kuma yayi girma, dan kuwa zuwa yanzu daƙyar ma take iya taka ƙafafunta, dan sun kumbura sosai, saikace me haihuwa yau ko gobe, wannan daliline yasa ta ɗauki hutu awajen aikinsu, Ummi ne ke bata kulawa sosai.
Ɓangaren Adda Maryam ma kuwa yanzu cikinta nada wata shida itama, saidai girman cikin nata baikai na Ameena ba.

Yau tunsafe da ta tashi takejin wani irin matsanancin ciwon mara, haka takejin bayanta ya riƙe ƙam, gashi ƙafarta ta sake kumburi, da ƙyar dai take iya takawa, haka ta lallaɓa ta nufi ɓangaren Ummi tana zuwa kuwa ta iskesu zaune afalo, zama tayi itama tana cije laɓɓanta, ganin haka yasa Ummi da kanta ta haɗa mata emptyn shayi me zafi ta bata tace tasha.
Tana sha kuwa tariƙe bayanta da takejinsa kaman zai ɓalle, Ummi da Raliya ne sukayo kanta, abu kaman wasa fa saiga naƙuda ya tashiwa Ameena gadan gadan, nan Ummi ta ka mata, inda ita da Raliya suka sanyata amota,
hankalinsa Saifuddeen a tashe ya shiga motar yana tsoron abinda zai sami ɗanshi tunda yasan cikin bai kai haihuwa ba.
Ahmad ne yayi driving ɗinsu zuwa Medical center, suna zuwa kuwa abokan aikinta suka karɓeta hannu bibbiyu nan aka wuce da ita labour room.
Jigum-jigum haka su Ummi sukayi suna mejiran sakamako, hankalin Ummi atashe yake sosai, musamman da likitotin suka tabbatar musu da cewa haihuwace Ameenan zatayi, ma'ana ɗan abakwaini zaizo.

Da shigar da Ameena labour room ko 40 minute ba a rufa ba, wata nurse ta fito inda take sanar musu da cewa. "Ameenan ta haihu ta haifi ɗa namiji, kuma daga ita har yaron dukansu suna cikin ƙoshin lafiya."
Wannan magana ita tasanya dariya ya wanzu akan fuskokin su Ummi, Saifuddeen kuwa hamdala yayi tare da ɗaga hannunsa sama ya godewa Allah.
Nan Ummi tashiga ƙiran ƴan uwa da abokan arziki tana sanar musu, ana fito da Ameena zuwa ɗakin hutu kuwa, nurse ɗin tace zasu iya shiga.
Suna shiga ɗakin wata nurse ta miƙowa Ummi yaron, hawayene suka cika idanun Ummi abayyane tace.
"Alhamdulillah, masha Allah."
Saboda tsananin kaman Saifuddeen ɗinta da ta hango akan fuskar yaron, gashi yaron kamar ba bakwaini ba, dan yana da girmansa, tsabar fari kuwa har saida yayi wani jaja-jaja.
Miƙawa Saifuddeen tayi ya amshi yaron yana mejin tarin ƙaunarsa acikin ransa, rumgume yaron yayi aƙirjinsa yana murmushi, bayan yayi wa yaron huɗuba da ƙiran sallah acikin kunnensa.
Nan dai Su Adda Rahama da Raliya suka amshi yaron suma suna yabawa da irin kyautar da Allah yayi musu.

Kasancewar Ameena bata wani jigata ba, hakan yasa bayan ankimtsata aka basu sallama da ƙara bata shawarwarin yadda zata kula da ɗanta tunda ɗan bakwainine sun sallamesune sabida sanin ita ɗin sashin Doctors take, nan dai suka tattaro suka dawo gida.

Kusan kullum ƴan barka sai sunzo, Mamy da Adda Maryam ma sunzo barka, Inna matar Baba Bello ma tazo yi musu barka. Ana sauran kwana uku suna Raihana ta diro garin na Gombe, da Aliyun ta takwaran bappa Alinsu (Affan) ɗinta kenan sosai itama tayi murna da ganin ɗan Hamma'nta. Ranan washe garin suna ne dangin Ameena suka zo, Aunty's ɗinta dama Sister's ɗinta duk sunzo daga Abuja wasu daga Jada.
Ranan suna kuwa yaro yaci sunan MUHAMMAD BASHEER. wato takwaran Baba Malam kenan, inda za'ana ƙiran yaron sa sunan. (Adeel) wannan karamci da Saifuddeen yayiwa Baba Malam yasashi matuƙar jin daɗi, bama iya shi ba, harta ga ƴaƴansa sunji matuƙar daɗi, haka Baba Malam da Mamy suka cika akwati guda da kayan yaro masu kyau'n gaske.
Nan dai akasha shagalin suna wanda yasamu hallaran mutane da yawa, dan dayawan danginsu na Dukku ma sunzo, ga kuma dangin Ameena. Adda Maryam ma tazo, duk da cewa cikinta na sata laulayi gashi dai yanzu har ya kai wata shida amman har yanzu yana sata laulayi. amma hakan baihanata zuwa ba.
Sosai Saifuddeen yayi ɓarin naira ranan sunan, dan anci ansha, sannan an rarraba kyautuka gaduk wanda yazo.
Aranan kuwa ya damƙawa Ameena makullin sabuwar motar daya saya mata, saboda tsabar daɗi Ameena har ƙwalla saida tayi.
Shikuwa Saifuddeen yayi hakanne saboda sauƙe haƙƙinta, dan bai kyautuwa ace yasawa Zaleeha mota da kuɗinsa, amma ita Ameenan bai saya mata ba, duk da cewa Zaleehan tariga zuwa kafun ita, sannan kuma ma motar Amina tafi ta Zaleeha kyau da kuma tsada.

Anyi taron suna an watse, inda Ummi dasu Adda Rahama suka nunawa Ameena gata sosai, dan kaya suka mata baɗan kaɗan ba, Hayatuddeen ma ba a barsa abaya ba, dan rigunan yaro har kala 6 ya saya masu kyaun gaske, Ameenan kuwa turamen vlisco ya saya mata guda biyu masu tsada, asusun da yakeyi musamman ya fasa dan yin shagalin sunan.
Hatta Zakariyya ma saida ya sayawa ɗan Hamma Saifuddeen ɗin riguna masu kyau.
Hakama Ya Ahmad da yaji labarin Baba malam akayiwa mai suna sosai ya goggojesu
Babu wani ɗaya daga cikin abokan Saifuddeen kuwa dabai kawo nasa kayan ba, sosai sukayi bajinta.
Abun saidai ace masha Allah.

Haka rayuwa tatafi har Ameena tayi wata biyu da haihuwa, wanda yanzu ta gama wanka, sannan tana bawa ɗanta kulawa sosai yanda ya dace, idan kaga yaron kuwa bazaka taɓa cewa bakwaini bane, saidai in anfaɗa maka, dan yana da girman jiki.
Sannan yarone me shiga rai sosai.
Kasancewar ta cika wata biyu da haihuwa hakan yasa ta shirya tsab inda su Ummi da Saifuddeen suka cikata da abubuwan al'khairi, nan ta tafi Abuja, kwananta uku acan ta dawo, tana dawowa kuwa ta koma bakin aikinta, don dama hutun 2 month kawai suka bata.


Acan Numan kuwa Abubuwa sunyiwa Zaleeha sauƙi sosai, inda ta kama addu'a sosai, ruwan addu'a kuwa kullum shi take sha, Alhamdulillah taji sauƙin abubuwa da yawa, dan yanzu begen gidane gaba ɗaya ya cika zuciyarta.

Yau tun da safe ta shirya tatafi gidan su Aisha nan ta samu Baffa agida dan bai fita gona ba bayan sun gaisa ya bata rubutun da ya mata tasha,
nanne yake tambayanta ko daga fara maganin nata zuwa yanzu ko taji sauyi ajikinta?
Sosai kuwa tagaya masa irin sauyin da taji,
Gyaran murya yayi tare da cewa.
"Tunda kika fara shan rubutun nan nece miki duk mafarkin da kikayi ki gaya min shin har yau bakiyi mafarkin komai ba?."
Da sauri ta kalleshi cikin al'ajabi tace.
"Baffa jiya nayi mafarkin daya bani mmki dan na taɓa yin makamancinsa".
Gyara zama yayi tare da fuskantarta da kyau yace.
"Mafarkin me kikayi?".
Gyara maya fita tayi tare cewa.
"Nayi mafarkin, da'a cikin mafarkin naga wani ƙaton maciji baƙiƙƙirin ya fito daga ƙarƙashin gadona na gidan Saifuddeen, wanda acikin mafarkin ne kuma naga Baba Malam yana cikin ɗakin ni kuma ina ta waje bakin ƙofar shiga ɗakin ta gefe, naji Baba Malam na cemin, in dawo gida in dawo ɗakinna in zauna, yanzu babu komai babu wani abu wanda zai cutar da ni a ɗakin.
Har yana ce min in matsa a baƙin ƙogar kada macicijin ya taɓa ni."
Cikin sauri da fargaba Baffa yace.
"Macijin yataɓaki?."
kai ta jujjuya tare da cewa.
"A a bai taɓani." ajiyan zuciya ya sauƙe tare da gyara zama.
Ita kuwa Zaleeha cikin sanyi tace.
"Na dai ga Macijin kuma na taɓa yin mafarkinshi, tun randa akaje akayi jeren kayana a gidan Saifuddeen nayi mafarkin wai ina kan gado sai macijin ya shigo ina ganinshi ƙato ya lume ƙarƙashi gadona.
To randa aka kaini gidanma na sake yin mafarkin."

Jinjina kai Baffa yayi bayan yagama jin kalaman nata cikin jin daɗi yace.
"Alhamdulillah. babu komai sai al'khairi kuma Insha Allah duk wani asirin dake jikinki yanzu ya karye, babushi a jikinki sannan yadda kikaga macijin nan ya shiga ƙasan gadonki haka sihiri yayi ta ratsaki, kuma yanzu yadda kikaga macin ya fita daga ƙasan gadonki to sihirin ya bar jikinki da ɗakinki, kuma zan baki maganin tsarin jiki tayanda insha Allah Allah zaikareki da dukkan wani sharri zakiyi amfani dashi sau uku."
Cikin wani irin begen gida da son komawa cikin ahlinta tace.
"Baffa ina son komawa yau in dai zan samu mota".
Cikin jin daɗi da gamsuwa da cewa ta samu waraka yace.
"Kiyi haƙuri sai gobe, tabbas kam tafiyar ta karato, dan haka kiyi haƙuri yanzu zan baki mgnin tsari kiyi wonka dashi sau uku yanzu in kin koma sai kuma da yamma, sai kuma gobe da asuba ki ƙarashi."
Don dole da kimar dottijon ta haƙura dan ji take tamkar ta zama tsunstsuwa tayi fiffige ta fire ta koma gida,ji yakeyi kamar ta rumtse idonta ta buɗe su ta ganta gaban Baba Malam ya mata duk hukuncin daya dace da ita ta nemi yafiyarshi da sanya al'barkanshi.
Ae kuwa bata bar gidan ba saida ya haɗa mata magungunan tsari, wanda duk addu'o'i ne, nan yake ce mata.
"Insha Allah takusa komawa gida."
Tajima agidan nasu Aisha kafun take komawa gida.

A ranar ne kuma Solomon da matarsa sukayi mata tambayar da ta bata mmki, suna tambayarta in mutun zai musulunta me da me zaiyi kuɗi kamar nawa zai kashe,
wannan abu ya sata jin karsashi ta zauna tayi musu bayanin komai na sauƙin musulunci, sai suke ce mata to suna son musulunta to amman sai sun gayawa sarkin majami'arsu. Tace su gaya mata da dole sai sun gaya mishi ,
sai sukace ta bari nanda sati ɗaya zasu gaya mata.

A safiyar ranar dai kuma A Gombe.

Saifuddeen ne zaune akan wheelchair ɗinsa, yana riƙe da Adeel ɗan wata uku ya shiga na uɗu wanda ya ƙara girma yakuma yi wayo yayi kuɓul-kuɓul, wasa yakeyiwa yaron yana me shafa lallausan gashin kansa, wanda yayi shige da nasa, sosai yakejin ƙauna da son yaron acikin ransa.
Ƙurawa yaron idanu yayi aransa.yana me cewa.
"Badan ƙaddara ta kawo Hajia Ameena rabo ba, da yanzu wannan yaron ajikinki zai fito Zaleeha, amman ba damuwa in sha Allah kema naki yana jikina in Allah ya yarda ni dake sai mun samar da abu ɗaya ina ji a jikina kin kusa dawowa gareni, kin gama naki zaki dawo ki tadda nawa. Wai toms in kin dawo me zakice? Ina kikaje? Meyasaki tafiya?".
Yayiwa kansa tambayar tare daɗan lumshe idanunsa, tabbas yayi kewar Zaleeha sosai musamman cikin kwanakin nan tana yawa faɗo mishi cikin rai, ya rasa dalili gashi yanzu sam ta daina hawa online kuma duk sabida yana mata mgna da number sa ta siirin nan dama tace mishi zata goge whatsapp gaba ɗaya kuma ta goge ɗin acewarta ita matar aurece.

Ameena ne tafito daga cikin ɗaki cikin shirinta na zuwa wajen aiki, ƙarasowa wajen su tayi cike da ƙaunarsu, ranƙwafowa tayi inda ta mannawa Saifuddeen din kiss akan laɓɓansa, sannan ta ɗaga yaron zuwa kafaɗanta, cikin kulawa ta ce da Saifuddeen ɗin.
"Saimun dawo" hannu ta ɗaga masa sannan ta fice, dan tayi late.
Shikuwa Saifuddeen laptop dinsa ya ɗauka, inda ya shiga cikin file ɗin da yake aje hotunan Zaleeha, view ɗin wani hoton Zaleehan yayi yana kallo, sosai tayi kyau acikin hoton dimple ɗinta ya zubawa ido, dan tana sanye ne da doguwar rigar da ta amshi jikinta, yajima yana kallon hoton kafun ya rufe laptop ɗin ya nufi ɗaki.


Ameena kuwa saida tabiya ta wajen Ummi tayi mata sallama kafun take wucewa wajen aikin.

Federal medical center.

Baba Malam ne da Ya Ameenu haɗe da Mamy, da kuma Ya Habu ke tsaye, sunyi jigum, matsanancin damuwane kwance biss fuskokinsu, sakamakon kawo Maryam haihuwa da sukayi, gashi kuma ance dole saidai ayi mata theatre.

Wasu nurses biyu ne suka turo wani ɗan dogon gado da Maryam ɗin ke kwance akai, ansanya mata kayan theatre, dai-dai sunzo wucewa ta wajen su Baba Malam ɗinne, Maryam ta sanya hannunta ta kamo na Baba Malam, tare da cewa.
"Baba Malam kazo mana kayi min addu'a kafin a shiga dani."
da sauri Baba Malam ya dubeta cikin tausayawa yace.
"To Maryam zan miki addu'a kinjiko ƴata mai sunan ƴar uwata insha Allah zaki haihu lafiya da yardan Allah."
ganin nos ɗin zasu shiga da itane yasa ta kallesu cikin sanyin murya tace.
"Dan Allah in mun shiga ku kirawo min Babana da mijina suzo akwa abinda zan ce musu kafin ayi aikin."
yanayin nitsuwarta ne yasa sukace.
"To". Suna shigar da ita ɗan falon da za'a ratsa a shiga ainhin ɗakin tiyatan.
Nan suka tsaida gadon kana ɗaya nos ɗin ta fito ta kira su Baba Malam da Ya Ameenu.

Suna shiga ta yunƙura ta tashi zaune cikin sanyi tasa hannunta da yayi sanyi ƙalau tamkar ƙanƙara ta riƙo hannun mahaifinta.
Kai ta girgiza take kuma saiga hawaye sun silalo daga cikin idanunta, cikin muryarta dake fita da sanyi tace.
"Baba Malam ka yafe mi ninaji ajikina cewa bazan tashi ba Baba, dan Allah kayafemin in akwai laifin da nayi maka."
Da sauri Baba malam ya riƙe hannunta tare da cewa.
"Ni kam bakiyi komai ba Maryam, koda ko kinyi min na yafe miki duniya da lahira, bare ni baki min komai ba face biyayya, ubangiji ya yassare miki rayuwar duniya data lahira."
Hannu tasa ta share hawayenta murya na rawa tace.
"Nagode Babana."
Da ƙarfi zuciyar Baba Malam ta buga jin yadda ta kirashi, kama hannunta yayi da kyau jin tana cewa.
"Sannan kuma ina neman wata al'farma a wurinka Babana".
Zuciya a tsinke yace.
"Wacce al'farmace Maryam gaya min".
Lumshe idanunta tayi wasu zafafan hawaye suka kwaranyo mota, cikin sanyin murya tace.
"Dan Allah ina son ka dawo da Mama dan Allah, ka kuma yafewa ƴar uwata Zaleeha, dan Allah Baba kayafe mana baki ɗayanmu Baba Malam ka yafewa Zaleeha dan kada rayuwa tayi mata muni bance kada kayi fushi ka nuna mata illar abinda tayiba, amman kada kuyi dogon fushi da ita, sannan in Mamana tazo kace mats na nemi yafiyarta, ta gafarta min".
Sai kuma ta fara kuka murya na rawa taci gaba da cewa.
"Baba malam Nasan duk inda Zaleeha take. Duk inda take a faɗin wannan duniyar in dai tana raye in taji rasuwata zata zo, dan Allah idan tazo kace mata na ajiye mata saƙo a cikin durowar gadona, kuma kada taje ita kaɗai in zata ɗauka taje ita da Mijinta Saifuddeen sannan kacewa. Ya Ahmad da Zakariyya kada suyi dogon fushi da Zaleeha su zame mata madadina."
taƙare maganar tana dhessheƙan kuka, kai Baba Malam ya jijjiga lokaci ɗaya hawaye suka cika idanunsa, hannunta ya kama ƙam cikin matsanancin ƙaunar ƴartasa yace.
"Insha Allah zaki tashi Maryam, za ayi miki aiki lafiya, kidaina faɗin irin waƴannan maganganun."

Murmushi tayi tare da kamo hannun Ya Ameenu wanda tuni hawaye sun wanke masa fuska, cikin matsanancin ƙaunar mijin nata tace.
"Inaji ajikina cewa zan barka Yayana, zantafi inda bazaka sake ganinka ba, kakulamin da Ayman ɗinmu kaji, sannan kayafemin duk wani abu danayi maka."
Kuka Ya Ameenu ya fashe dashi tare da durƙushewa awajen, don bayajin zai iya cewa komai.
Mamy ma kuka take, nan ita da Ya Habu suka kama hannun Maryam ɗin, murya asanyaye Mamy tace.
"Ki daina faɗin haka Maryam zaki tashi da yardan Allah."
Hannun Mamyn Maryam tasake riƙewa sosai, cikin muryan kuka tace.
"Ku yafemin Mamy, idan Zaleeha ta dawo kice mata nace tabi mijinta sauda ƙafa tayi masa biyayya, danni kam bazan samu daman faɗa mata hakan da bakina ba.
Ya Habu kaima kayafemin, sannan kada kuyi dogon fushi da Zaleeha."
Kukane ya ƙwace wa Mamy, da Ya Habu, Baba malam ma hawaye yake sosai.
Ganin haka yasa nurses ɗin suka tura keken sukayi ciki da Maryam ɗin, tana kallon Ya Ameenu shima

Please Login or Register in order to submit comment