Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

banason Ummi tafara tunanin cewa ina tauye miki haƙƙi, idan wani abu nayi miki ki faɗamin, kinsa kanki aɗaki kin kwana kuka, saboda kina yarda da abun da zuciyarki da shaiɗan ke raya miki, sannan sun tambayeki kince musu mura ne ke damunki, su mahaukata ne da bazasu gane cewar kuka kikayi ba, ki dubi fuskarki, ki dubi yanda idanunki suka bayyana alamun kuka, meyasa ba zaki nutsu ki maida hankalin ki ba? Meyasa kike haka?". Hawayen da suka zubo daga cikin idanunta ta sharce, murya na rawa tace.
"Dan Allah kayi haƙuri."
Kansa yaɗan jinjina mata alaman yaji, sannan kuma ta kiyaye, dan abun da tayi ɗin ya sosa ransa, bai kamata ace tana fushi batare da ƙwaƙƙwaran dalili ba, Allah Ma yasani yana iyaka ƙoƙarinsa wajen ganin bai tauye mata haƙƙinta ba.
Buɗe murfin motar yayi ya fice, kaitsaye part ɗinsa ya nufa, dan yanaso yaje yaɗan huta. Itakuwa Ameena gaba ɗaya jikinta amace yake, dan tasan bata da gaskiya, gefe guda kuwa ga wani irin soyayyarsa dake ratsa ta, ita har ga Allah tasan Zaleeha batayi mata komaiba kuma itama bawai tsanar Zaleeha takeyi ba, sai dai tana jin kishinta, haka tayiwa motar key, asanyaye ta fice daga cikin gida. Ta tafi tasan in taje wurin aiki ƙawarta Samira zata ƙara kwantar mata da hankali, ita kanta tasan Samira ƙawace ta gari.

Acan falon Ummi kuwa cikin nutsuwa suka kammala break fast ɗin, Zaleeha da Raleeya ne suka kimtsa dinning area'n, inda Raleeya ta zuba kwanukan da suka ɓata acikin injin wanke wanke, nan falon Ummi suka zauna suna ɗan taɓa hira. Ganin lokaci na ɗan jane, yasa suka sake komawa kitchine ɗin, lunch suka ɗaura, basu wani yi girki me wahala ba, hakan yasa cikin mintuna kaɗan suka kammala, Raleeya ne ta haye sama dan agajiye take jinta sosai, itama Zaleeha part ɗinta ta nufa, Adeel ɗauke akan kafaɗanta, koda ta isa ɗakinta, akan gado ta aje Adeel ɗin sannan ta jefa masa ɗan ƙaramin pillow dan yayi wasa dashi, kayan jikinta ta rage, sannan ta shiga wanka, koda ta fito wata ƴar riga marar nauyi tasanya, sannan ta haye saman gadon, jawo Adeel jikinta tayi tare da ɗaurasa akan cikinta, ahankali take shafa bayansa, ahaka har bacci ya ɗaukesu. Ahankali yaɗan buɗe idanunsa, wanda suka ɗanyi ja, saboda baccin da yayi, wayarsa dake ɗaure kan bedside ya ɗauka, ganin ƙarfe 12:15 pm yasashi tashi zaune, wheelchair ɗinsa ya jawo tare da hawa kai, kaitsaye toilet ya wuce, wanka yayi ya fito sanye da rigar wanka ajikinsa, ɗan ƙaramin towel ne ahannunsa, yana tsane gashin kansa, koda ya kammala body lotion me daɗin ƙamshi ya shafa ajikinsa, wasu riga da wandon shadda na getzner ya sanya wanda sukai masa masifar kyau, tsab yagama shirya kansa tare da fesa turare, wayarsa da kuma laptop ɗinsa ya ɗauka sannan ya fice daga cikin ɗakin.
Kaitsaye part ɗin Ummi ya nufa.
Babu kowa a falon Ummin, ko ina shiru, dan tun 11 Hayatuddeen ya tafi school, Raleeya da Ummi kuwa kowa na ɗakinsa.
A falon ya ɗan tsaya jim ya ɗanyi dan yasan a irin wannan lokacin Ummi ma bacci takeyi,
A hankali ya juya ya fita, a harabar gidan ya ɗan tsaya kamar zai wuce wurinsu Sule sai kuma ya juya ya nufi side ɗinshi da matanshi ƙofar falon Zaleeha ya buɗe ya shiga a hankali yake sarrafa keken nashi, shiru falon nata sai sautin AC da kuma karatun ƙur'an da ta saka wanda yake tashi a hankali,
kamar zai juya ya fita kuma sai yaji zuciyarshi nayi mishi jagora zuwa cikin ɗakin nata,
a hankali ya tura ƙofan,
tare da sarrafa kekenshi cikin nitsuwa ya isa tsakiyar ɗakin, ido ya zuba mata ganin yadda take konce ruggume da Adeel,
idonshi ya lumshe tare da fidda sassanyan numfashi, a ranshi yace.
"Uhumm to wannan konciya a bakin gado ai juyi ɗaya zakiyi ki yarmin da yaro ƙasa ki fasa min kanshi."
dan gaba ɗaya ƙarfin konciyar nata a bakin gadon ne, sarrafa kekenshin yayi a hankali ya iso bakin gadon, cikin nitsuwa yasa hannu ya tallafi Adeel tare da ɗauke shi daga kan ƙirjinta,
ya ɗan roggofo da niyar kontar da Adeel ɗin bayanta kenan,
cikin bacci taji kamar yaron zai faɗo ba tare data buɗe ido taɓa tayi maza ta ruggumeshi,
madadin ta ruggumi ɗan sai ta ruggumi uban,
da sauri ya kontar da Adeel daketa bacci sai, ido ya ɗan zaro jin yadda ta ruggumeshi gam a jikinta,
idon ya zuba mata, yana mai maganar zuci.
"Wayyo Allah zata lalata min al'wala".
Ita kuwa Zaleeha cikin baccin ta fahimci wannan ba Adeel ta rugguma ba, da sauri ta buɗe idanunta tare dayi sauri ta sakeshi, ido ta zazzaro kana ta mirgina baya,
da sauri ya riko hannunta ganin zata mirgina kan Adeel,
cikin mayen bacci tace.
"Bacci zanyi".
Ido ya tsura mata tare da jujjuya mata su kana ya mata mgna da yarensu na kurame.
"To na hanaki baccin ne, daga zuwana kin shaƙoni kin ruggume."
Ya ƙare kwatance dayi mata nuni da rugguma,
baki ta ɗan tura tare da cewa.
"Ni ai Adeel nake son rugguma ba kaiba".
Sake hannunta yayi tare da mata alamun.
"Karya kikeyi".
ita dai gefe ta koma ta konta tasa Adeel a gaba,
shi kuwa juyawa yayi ya fita dan baison worwore al'walanshi.

Yana fita ta maida ajiyan zuciya tare da shafa kan Adeel kana sukaci gaba da bacci su.

Shi kuwa suna fita shida Sule kasuwa suka wuce,
Nan ya zazzagaya shagunanshi dan duba hada-hadarsu dan sun kusa suyi zaman lissafin cinikin shekara da ribar da suka shigar da sanin zakkar daya dace su fidda,
Sai da ya gama zagayawa shida Ahmad da Mudassir kana da Warisu.
Sannan ya wuce, ya gaggaida su Alhaji Yawale, Ba miskila, Alhakin Isha, Alhaji kabiru, uban gidansu na dilan leda Alhaji Aliyu, domin baya mance duk matakin da yake ciki a rayuwa sanadin pure water da leda dasu magine ya kai wannan matsayin.

Daga kasuwa ofishin su na Jonapwd ya wuce,
yana shiga ciki ana ƙoƙarin shiga sallan azahar, nan ya shiga jam'i akayi salla.
Bayan an idar ne ya wuce ofishin Ishaq, tare da jagoranci Sani,
cikin yadda suka saba mgna yake mishi bayanin Malam Ishaq yana cikin G.S.U sai dai yanzu zai dawo,
aiko suna nan zaune Ishaq ya shigo,
Murmushi yayi tare dabin gefen table ɗinshi ya matso kusa da kujerar da yasan nan Saifuddeen ke zama hannu ya bashi tare da cewa.
"Ango mai mata biyu, sai yau aka tuno mu?".
Hannunshi Saifuddeen ya kama tare da rubuta mishi,
"Kai Isha banda sharri last week mafa nazo dani akayi mitin".
Murmushi Ishaq yayi lakacin daji saƙon aminin nashi, gyara zama yayi kana yace.
"Eh ai yanzu zuwanka sati-sati ne."
Murmushi sukayi baki ɗaya kana sukaci gaba da hira,
A nanne Saifuddeen ke cewa Ishaq ya kamata fa ya tsaida batun aure duk abokansu sunyi aure sai shida Mudassir suka rage,
a nan Ishaq ke ce mishi su shirya shima nashi nan tafe dan sun gama dai-dai tawa da Rashida ƙawar Zaleeha,
sosai Saifuddeen yaji daɗin haka dan yasan Rashida tanada mutumci da kima,
nan dai sukayi tashan hirarsu ta abokai.

Sai da yamma ya baro wurin Ishaq kana, ya nufi gida.


A gidan kuwa tuni Zaleeha da Raliya sun gama aikin abincin dare.
Amina ma ta dawo wurin aikinta

Duk suna zaune a falon Ummi sunata ɗan taɓa hira.
Duk da Ameena najin zuciyarta babu daɗi dan har yanzu data dawo dataje ɗakinta saida taji ƙamshin turaren Zaleeha a jikin rigar Adeel amman ta danne.

Shi kuwa Saifuddeen kai tsaye side ɗinsu ya wuce ganin magrib ta gabato, ruwa ya ɗan watsa kana ya zura jallabiya ya fito ya nufi masallaci,
Hayatuddeen na biye dashi a baya,
a bakin gate suka samu Ahmad ma nayin al'wala daga nan suka wuce masallaci.
Sune basu dawo gidaba saida akayi sallan isha.

Suna dawowa suka zauna duk sukaci abinci,
daga nan Ahmad ya haura sama dan a matuƙar gajiye yake, in ya ɗanyi bacci kafin Raliya ta gama hiranta ta dawo zaiji dama-dama ya samu raya daren


Hira suke ɗanyi yayinda Zaleeha ke zaune ƙasa kan carpet, tasa Adeel a kan cinya tana yanke mishi farce.

Ameena kuwa ta zuba musu ido,har ranta tasan ba soyayyar ganin ido Zaleeha keyiwa ɗanta ba,
to amman ita ta kasa jin ta dena kishin Zaleeha a ranta, ganin yadda tayi zugum tayi tagumine yasa Ummi ta kalleta cikin kulawa da nitsuwa tace.
"Ameena zo".
Tana faɗin haka ta wuce tayi cikin ɗakin ta.
Cikin sanyi Ameena ta miƙe tabi bayanta,
a bakin gado ta samu Ummi na zaune, cikin yin ƙasa da kai ta ƙaraso cikin ɗakin,inda Ummi ta nuna mata nan ta zauna sunkuyar da kanta tayi a hankali tace.
"Ummi gani".
ido Ummi ta zuba mata sai kuma ta gyara zama cikin kulawa da son gane matsalar Ameena tace.
"Ameena meke damunki?".
A hankali ta jujjuya kai alamun babu.
Cikin kula Ummi tace.
"Kinga Ameena kada kiyi min haka,kinji ni matsayin ƴa na ɗauke ku,muddin kinada matsala ki gaya min, in inada damar yaye miki ita zan yaye miki ita in kuma bani da dama, zan tayaki da addu'a da shawarwari, dan haka gaya min meke damunki yadda bazan so Ahmad ya tozarta Raliya ba bazanso Saifuddeen ya tozar takuba, gaya min me yayi miki,ni nasan na isa dashi".
Cikin rauni da sanyin murya tace.
"Babu abin da yamin Ummi,wlh Hamma bai min komaiba".
cikin gamsuwa Ummi tace to menene matsalarki meke damunki?".
Kai ta ɗan rausayar tare da cewa.
"Ba komai Ummi wlh Hamma bai min komaiba."
Cikin kula Ummi tace.
"To Alhamdulillah dan ni shi na zarga, tunda kuma kince bai miki komaiba, shikenan, amman ki saki ranki ki dena sa damuwa a ranki, bana son ganin kina tagumi kinji ko tashi kije kuyi hiranku da ƴan uwanki".
Cikin jin daɗi da ganin daraja da kimar Ummi da mijinta ta miƙe ta fita tana mai yin mgnar zuciya.
"Ameena ki sassauta wa kanki kishi bayin Allah nan basu rageki da komaiba wacce kikeyi dominta ma bata saniba".
A hankali ta fito falon gefen Zaleeha ta zauna, cikin kula Zaleeha ta kalleta tare da cewa.
"Ummu Adeel bashi yasha nono naga yanata mutsu-mutsu".
Murmushi ta ɗanyi kana ta ɗauke shi ta bashi nono.
Shikuwa Saifuddeen ido ya zuba musu a yadda suke jeren,
hamdala yakeyi da godewa Allah daya azirtashi da matan da ko wacce da nasabarta,
murmushi yayiwa Ameena tare da jinjina mata kai alamun tayi kyau.
kauda idonta tayi dan sai take ga kamar ba'a yayi mata ya za'ayi yace tayi kyau bayan ga Zaleeha kusa da ita bata san cewa kowa da irin sirrin kyanta ba.
ganin yadda ta tsuke fuskane ya sashi jin ba daɗi.
"To wai me nayi mata,ko dai ta daina so nane yasa duk abinda nai mata sai ta juyashi marar daɗi".
Yana cikin mgnar zucin yaga ta miƙawa Zaleeha Adeel ta miƙe ta fita,
da ido ya bita,
Raleya ce ta kalleta cikin kula tace.
"Aunty Ameena har zaki shiga?".
Kai ta gyaɗa mata, jin Hayatuddeen yace.
"To saida safe Aunty Ameena".
Yasa ta ɗan juyo tare da cewa.
"To auta Allah ya bamu al'khairi".
Baki ya tura tare da cewa.
"Wai auta nida har inada yara sai kuyi ta cemin auta yanzu in Adeel ya fara mgna shima ba sai yabi bakinku yace min autanba".
Murmushi tayi ta fice,
Zaleeha kuwa dariya ta ɗanyi tare da cewa.
"Ya isa ya cema auta ai kai Appinshi ne".
miƙa yayi tare da konciya bisa kujerar da yake.

Amina kuwa tana shiga ɗakinta bakin gado ta zauna tanajin tana son danne zazzafan kishinta kenan yanzu yauma a ɗakin Zaleeha zai kwana,
kwanciya tayi tare da kife kanta bisa pillow ta saki nannauyan numfashi.
Ita dai ALLAH ya sani da Saifuddeen zai saki Zaleeha wlh da tanaso da kuma tafi kowa jin daɗi.
ɗago kanta tayi ta ɗauki woyarta jin alamun saƙo ya shigo mata.
buɗe saƙon tayi ganin sunan Abban Adeel hannu tasa ta share hawayenta lokacin data karanta abinda ya turo mata.
"Kin tafi kinje kin fara kukan ko?."
Da sauri ta tura mishi amsa.
"A a wonkafa zanyi".
ajiyan zuciya ta sauƙe sanda taga saƙonshi.
"Kin tabbata ba kuka kikeyi ba?".
Da sauri tace.
"Eh."
"Yauwa Ummu Adeel haka nake son ji,kinji ko kada in sake ganin kina min kukan da babu dalili,in laifi nayi miki ki gaya min banfi ƙarfin in baki haƙuri ba".
Wannan text ɗin yayi masifar sata jin daɗin, sai kuma shaiɗan ya kisa mata.
"Ke sokuwa kika san me yake gaya mata ita kuma?".
Take ta kife kanta taci gaba tubka da worwora amman tana mai yiwa kanta faɗan ta zauna lfy da mijinta da abokiyar zamanta.

A can falon Ummi kuwa, yana gama text ɗin da yakeyi ya fice ya nufi side dinshi dan zaije yayi shirin bacci.

Ita kuwa Zaleeha bacci takeji sosai to amman tsoro tafiya da Adeel takeji tana son tafiya dashi tana kuma tsoro sabida kada Abbanshi yaje karɓanshi ya mata tijara irin ta jiya shiyasa take shirin kontar dashi a nan ta gudu ta barwa Raliya shi, ai in bata tafi da ɗanshiba bazai bitaba.

Raliya ce ta miƙe tare dayi musu saida safe ta haura sama,
Ummi ce da yanzun ta fito tare da Raliya ta kalli Zaleeha dake ƙoƙarin kontar da Adeel tace.
"A a Zaleeha har yanzu kina nanne, dare yayi ai sha ɗaya saurafa, tashi ki ɗauki coffee ɗin Babana ki kai mishi".
Da ƙarfi taji cikinta yayi wani ƙugi,wannan shine anyi gudun gara an tadda zago,
amman ba halin yiwa Ummi musu bare gardama,
a hankali ta miƙe goya Adeel tayi sannan ta ɗauki tray ɗin da aka shiryawa Hamma Saif ɗin coffee ɗin shi,
jiki a mace tayi musu saida safe ta juna ta nufi side ɗinsu.

A hankali ta tura ƙofar falonshi ta shiga da sallama, cikin nitsuwa take taku ta shiga falon nashi da bata taɓa gangancin shigaba,
ganin ba kowa yasa tayi sauri-sauri gudu-gudu ta ajiye mishi tray ɗin bisa dinnin table ɗin shi,
ta juya ta fita da sassarfa kamar wacce za'a kama ko tsarin falon bata gama ganinba.


Shi kuwa Saifuddeen tuni yayi wonka shi ya shirya cikin wasu tattausan riga da wondo na bacci masu kalar sarararin samaniya, ya fesa turare yayi ras dashi sai ƙamshi yakeyi.

Daga falonshi kai tsaye ɗakin Ameena ya nufa.

A kan gado ya hangota tana zaune tasa kanta cikin guiwowinsa bisa alamu tunani takeyi,
jin motsinshi ne yasata ɗan ɗagowa ta kalleshi,
sai kuma ta meda kanta ƙasa da alamun bata son ganinshi ne ko haushinshine ma takeji bata dai son ta gaza danne kishinta ne.
shi kam lamarin Ameena ya tsaya mishi a rai don ya rasa me zai mata ta saki ranta,
a hankali ya iso bakin gadon hannunshi ya miƙa mata alamun tazo,
cikin jin haushin sa dan gani take ai duk abinda yakeyi mata zaiyiwa Zaleeha, hararanshi ta ɗanyi cikin son danne kishinta tace.
"Dan Allah ka fitarmin a ɗaki ka tafi can wurin maikai saida safe".
Kanshi ya jinjina mata kana ya zuba mata ido.
Da sauri ta sauƙo kan gadon jiyo muryar Zaleeha na sallama a falon ta.
Hannunta tasa ta share hawayenta tare da fitowa,
cikin kirsa take kallon Zaleeha sama da ƙasa,
murmushin da bai kai zuci ba tayi jin Zaleeha na cewa.
"Ga Adeel kar ya tashi dare-dare yayi ta kuka".
Motsowa tayi jikin Zaleeha da ta ɗan sunkuya ta kunce abun goyon, cikin kirsa tace.
"Ae kam ya iya rigama kamar na Abbanshi,shima gaya can a ɗaki yanata min rigama, nace inji da ɗanka inji da kai".
Murmushi Zaleeha tayi tare da cewa.
"Saida safe".
Harara ta mannawa Zaleeha tare da cewa.
"Allah ya bamu al'khairi".

Amin Amin Zaleeha tace tare da ficewa ta koma side ɗinta.

Kai tsaye bathroom ta shiga,wonka tayi soso da sabulu kana tazo ta kimtsa cikin tattausan rigan baccinta mai tsawo har guiwa.

Kasancewar tana tsoron duhune yasa ta bar wuta ɗakin a kunne,
konciya tayi bisa gadonta tare da jawo borgo ta shiga ciki ta konta tayi lib tana sauƙe numfashi dan tana tare da gajiya.


Ita kuwa Ameena tana komawa cikin bedroom ɗinta gado ta hau cikin jin ba daɗi ta juyo ta kalli Saifuddeen baki ta tura tare da cewa.
"To sai ka tafi ai tunda ga ɗana an dawo min dashi sai kuje can kuci juna".
Zuwa yanzu dariya Ameena ke bashi dan fushinta mara daliline,
dan haka juyawa kawai yayi ya fita.

Falonshin ya shiga nan ya samu coffee ɗinshi, shida kanshi ya haɗawa kanshi dai-dai misalin abinda zai sha, saida ya sha sannan ya ɗan zaro wayarshi a saman lips ɗinshi yace.
"Shabiyu harda kwata".

Lumshe yayi lokacin daya nufi side ɗin zali a ranshi yace.
"Itama tanada haƙƙi a kaina dole in san ya ta kwana ya ta tashi.

A hankali yake sarrafa kekenshin har ya isa bakin ƙofar ɗakinta mamaki yayi ganin yadda ta bar wutan ɗakin a kunne, cikin nitsuwa ya tura ƙofar ya shiga,
ita kuwa Zaleeha bacci ya ɗan fara fizgarta shiyasa bata san da shigowanshi ba,
a hankali ya isa bakin gadon.
Da sauri Zaleeha ta buɗe idanunta jin mitsin mutun wuƙi-wuƙi tayi da idanunta ganin shine, da sauri, ta ɗan matsa gefe cikin tsoronshi da muryar bacci tace.
"Menene? Nifa na maida Adeel wurin Mamanahi,baya wurina! Kuma na kai maka coffee ɗinka falonka!".
ta ƙarashi magar cikin tanayin rau-rau da idanunta, dan ita batama san lokacin data meda Adeel yana ɗakin Ameena ba.
Baki shine ya ɗan taɓe tare da buɗa kafaɗu shi kana ya mata alama.
"To an ce miki Adeel nazo karɓane? Ko dai bani da enci da damar shiga ɗakin ne sai kin bani izini ne?".
Ya ƙarashi maganar cikin alamun tambaya.
Kai ta karyar bisa kafaɗa cikin sanyi tace mishi.
"A a".
Kanshi ya jinjina tare da mata alamun.
"To naza kwana a ɗakin nan ɗinne".
A take sai ga hawaye shar-shar a fuskarta cikin rauni da sanyin ta tace.
"To shike".
Sai kuma ya zuba mata ido ganin ta ɗauki pillow ta sauƙo daga kan gadon da alamun zata fita ne.
Da sauri yasa hannunshin ya fizgota kana ya ajiyeta kan gadon a gaban shi, ya zama suna fuskantar juna,
cikin yarensu ya mata magana.
"Ok yanzunma can cikin garding ɗin zaki koma ki kwana ne?".
Kai ta jujjuya mishi kamar ƙaramar yarinya murya can ƙasa tace.
"A a".
Cikin tsareta da ido yace.
"To ina zakije ki kwana? Sannan ni kurane da in na shigo kike gudana gaba ɗaya jikinki na rawa".
Ya ƙarshe magar da mata alama da kyau yadda zata gane.
A hankali tace mishi.
"A a". Tare kuma da girgiza kai alamar a a yadda zai gane.
Cikin bada ubarni da yaransa yace mata.
"To hau ki kwana". Ba musu ta haura kan gadon ta dugungune wuri ɗaya.
Cikin kula yake kallon yadda gaba ɗaya jikinta ke karkarwa, a hankali yake mata misali da cewa.
"Nifa babu abinda zan miki,ki nitsu ki konta kiyi baccinki, sai da safe".
Kai ta gyaɗa mishi tare da sauƙe nannauyan ajiyan zuciya.
Shiru yayi yana ƙare mata kallo gaba ɗaya ta rame, fuskarta tayi fiyau, kuma har yanzu akwai damu da jimamin rashin ƴar uwarta.
Da wannan tunanin ya juya ya fita bayan ya kashe mata wutan ɗakin, sabida bata cikin yanayi mai daɗin da zata iya fahimta ko jin daɗi wani abun da zaiyi mata shiyasa bari dai ya ɗaga mata ƙafa.


Washe gari da, kuwa ranar Ameena zata karɓi Saifuddeen domin ya gama kwanakin shi biyu na ɗakin Zaleeha.

Da yamma Ummi na zaune a ɗakinta tana kwaɓa lallen gargajiya da takeso tasa a daren yau ɗin Zaleeha ta shigo gefenta ta zauna,
cikin nitsuwa ta gaidata,
ganin tayi shirune yasa Ummi cewa.
"Kinyi shiru Zaleeha me kikeso?".
Cikin sanyin yanayin da rayuwarta ta dawo ciki tace.
"Uhum Ummi dama gobene za'ayi sadaka bakwai ɗin Adda Maryam, kuma ina son zuwa Ummi a gayawa Hamma Saif mana dama ina son zuwane in na samu".
Murmushi Ummi tayi tare da cewa.
"To Zaleeha ni zan tamɓayan miki,keda mijinki kije ki tambaye shi da kanki kinji ko karkiyi haka".
Cikin nitsuwa ta gyaɗa kanta alamar to kana ta miƙe ta fita,
binta da ido Ummi tayi a fili tace.
"Uhmmm Saifuddeen ya sawa yarinyar nan tsoronshi, da shakkarsa ban san meyasaba, yarinya duk ta zama shiru-shiru abar tausayi".


Ita kuwa Zaleeha yau tunda safema bata kuma ganin Hamma Saif ɗin ba, dan yau tunda safe ya tafi Office ɗinsu na SS.
Dan sun samu wani bayani kan Dalla ya kusa dawowa.

To ta dai sa a ranta zata daure ta tambaye shi koda zai gwatsaletan ne.

Gab da magriba ta fito daga falon Ummi kenan tana ruggume da Adeel tazo gab bakin kofar shiga side ɗinsune tayi kiciɓis dashi.
yayinda Ameena kuwa tana falon Ummin dan yanzu ta dawo

A hankali ta ɗan raɓa gefe,
shi kuwa hannu ya miƙo mata alamun ta bashi Adeel ba musu ta miƙa mishi Adeel,
cikin sanyi tace.
"Ina wuni ya aiki?".
Kai ya gyaɗa mata alamun Alhamdulillah, shafa kan Adeel yayi tare da miƙo matashi ya mata alamun.
"Je ki ajiyeshi kiyi salla lokaci yayi kar kije ki tasashi gaba kuyita dariya."
Kai ta jinjina kana a hankali tace.
"Uhum Hamma Saif".
Ido ya zuba mata dan duk duniya ita ɗaya yaji tana kiranshi da wannan sunan".
Ganin tayi shirune ya sashi ɗaga mata hannu alamun lfy dai ko?
Cikin inda-inda tace.
"Uhum dama gobene za'ayi sadakan bakwai ɗin Adda Maryam to kuma ina son zuwa in ka amince ka yerje min?".
Karo na forko kenan da Zaleeha ta nemi izininshi akan abu, shiyasa yaji kanshi tamkar wani sarki,
ita kuwa ganin yayi shirune yasa ta rumtse idanunta da suka cika da hawaye,
Cikin sanyi tace.
"Dan Allah kayi haƙuri, ka bani izinin zuwa inaso inje inga ƴan uwana".
Kanshi ya jinjina mata alamun
"Allah ya kaimu".
Cikin jin daɗi tace Amin Amin kana ta sunkuyo ta karɓi Adeel sannan ta wuce tayi ciki, shi kuma ya wuce ya nufi ƙofar gida.

Amina kuwa dake tsaye bakin falon Ummin ta cika tayi fam tuni sheiɗan ya shiga ingizata, sunkuyowan da Zaleeha tayi ta bashi Adeel ɗin nan sai takega kamar, sumbatar ta Saifuddeen yayi, hakan kuma sheiɗan ya raya mata.
"To ai dai duk iyayinta yau dai kam girkinkine, tunda taci kwana biyunta ai sai ta bar miki mijinki yau kam".
Wani irin kishi da tsanar Zaleeha ne suka cika mata ciki da zuciya.
gaba ɗaya ta hautsine a haka ta nufi side ɗinta dan yin sallan magriba.

Koda sukaci abincin dere suka ɗanyi hira,
ganin yadda Ameena ke watsa mishi harara ya sashi sanin lallai yau akwai aiki,


A can gidan Baba malam kuwa,
Ziyada ne ke zaune gaban Baba Malam a cikin falonshi sai ya Ahmad da Malam Adam , da kuma ya Ameenu,
shiru sukayi baki ɗayansu,
cikin tattausan lafazi Baba Malam ya kira Ziyada.
"Ziyada".
Cikin nitsuwarta irin ta Adda Maryam tace.
"Na'am".
A hankali yace.
"Wata al'farma nake nema a wurinki in Allah yasa kin amince zanji daɗin hakan,
Amman fa bawai umarni nake bakiba al'farmace nake nema".
Ɗago kanta tayi wanda ida nunta tuni sun cika da kwalla cikin sanyin murya tace.
"Baba malam al'farma kuma?".
Kai ya gyaɗa mata alamar eh,
da sauri tace.
"A a baba ka bani umarni kawai, ko wanne irine zan bishi domin nasan bazaka sani yin abinda ya saɓawa shariya ba".
Cikin jin daɗi ya fuskaceta da kyau, murya a tausashe yace.
"Ga ɗan uwanki Ameenu mijin yayarki Maryam, ko zaki amince in aura masa ke in mishi madadin Maryam dake? Kije ki zauna ki raini ɗan ƴar uwarki?."
Kai ta sunkuyar hawaye na zuba murya na rawa tace.
"Na amince Baba Malam na yarda in dai Ya Ameenu ya amince nima na amince".
Wani irin sassanyan ajiyan zuciya Baba Malam ya sauƙe,
Ya Ameenu kuwa ido ya zuba wa Baba Malam cikin tsananin mamaki da kaɗuwa,
Ya Ahmad da Malam Adam kuwa sosai sukaji daɗin wannan batun.
Shiru ya Ameenu yayi jin Baba Malam na ce mishi.
"Ameenu ga Ziyada na baka ita, gobe da asuba in sha Allah za'a ɗaura muku aure in ka amince ta koma ɗakin ƴar uwarta".
Kai ya jinjina hawaye na zuba yace.
"Nagode Baba Malam Allah ya saka da al'khairi ya jiƙan Maryam".
Amin Amin sukace baki ɗayansu kana Baba Malam yace Ziyada ta tafi cikin gida.

Nan suka ajiye batun ɗaura auren gobe da asuba.


Ƙarfe tara dai-dai Mamy ta shigo falon Mama ta sanar mata kiran Baba Malam, wanda tunda ta dawo gidan bai kulata ba,
Don tuni ya dai-dai ta larin aurenshi da ita.

Jiki a mace ta

Please Login or Register in order to submit comment