Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

heart ɗina baby.... Idan kin tafi karki manta dani, zamu haɗu a Abuja, but pls don't brake my heart" sallama muka yi ya rakoni har masauki yana tafiya naga alert na 200k daga gareshi wai kuɗin flight, text na tura masa na godiya araina ina tunanin ina yasamu account details ɗina daga ƙarshe na tuna ai mun rubuta jikin attendance,muna dab da tafiya naga massage ɗinshi,

_I love you._ shine abin da ya turo reply na mai da masa ina jin kewarsa acikin raina............✍🏻


*Garin dadi littafin kudi ne ga mai bukatar cigaban labarin sai ya tura 500 ta 0774712835 Aisha Ibrahim Access Bank sai a tura evidence of payment ta wannan no 07044644433 ko a tura katin waya da shaidar biya wannan no 07044644433*



*_Ummi Shatu_*👌🏻

[1/5, 12:43] Maman K: ©️ *HASKE WRITERS ASSOCIATION*
_(Home of expert & perfect writers)_



*GARIN DAƊI......!*💍💍



*_NA_*

_*UMMI A'ISHA*_


*Wattpad:ummishatu*


21


*Ina kuke manyan mata ƴan ƙwalisa ma'abota son gyara da kece raini, maza ku garzayo ku nemi maman Maryam domin samun lafiyayyu kuma haɗaɗɗun Lagos lace wanda zaku iya samun ɗinkakku da kuma sabbi a ledarsu, kaya iya zaɓinki, gefe ɗaya muna da GHT product, zaku samu,*

~MAI DA TSOHUWA YARINYA

~FEMALE CARE

~REODEO

~VIGOR MAX

~ LONGZIT

~B CLEAR

*DUK ZAKU SAMU WADANNAN KAYA CIKIN SAUKI DA RAHUSA MAZA KU NEMI MAMAN MARYAM AKAN WANNAN NO 07080222187, SIYAN NA GARI MAIDA KUƊI GIDA.....*

~~~Sake buɗe idanuwa nayi da kyau ina kallonsa dan gaskata shi ɗin ne ko kuma wani ne me kama da shi tabbas Yaya Faisal ne, ko kaɗan ban nuna cewa na ganshi ba sai shine yake ta waiwayenmu bayan ya wuce mu, zuwa can ya sake dawowa, wannan karon bai wuce ba yayi mana sallama, ni kaɗai ce na amsa banda samz wanda ke riƙe da hannu na har lokacin,

"Kamar Widat ko?"

"Ehh nice" na bashi amsa kaina tsaye,

"Ashe haka kuka yi da madam ɗina.... Wallahi ban san ta turo miki wannan massage ɗinba tayi blocking ɗin ki sai jiya take faɗa min no wonder naga 2 days bana ganin ki online bana ganin status ɗin ki ashe blocking ɗin ki tayi bayan ta goge contact ɗin ki.... "

" Ayya babu komai ai nayi tunanin ma ko kaine "

" Haba haba wallahi bani bane, kuma da farko itace fa ta nuna min tana son in haɗa ku kuyi zumunci may be taje wasu sun zugota ne, dan Allah kiyi hakuri "

" karka damu ya wuce, nima Allah ya bani nawa rabon gashi... " na nuna samz da ɗayan hannuna wanda bai riƙe ba, kuma da biyu nayi dan Samz yafi yaya Faisal komai da ake buƙata wurin namiji, cikakken namiji ne har over matsalar shi ɗaya shi Christian ne,

"Masha Allah, Allah ya tabbatar da alkhairi" ya faɗa yana barin wurin, sai bayan da ya tafi sannan samz ya matsa hannuna yana tambaya ta,

"baby wannan waye?"

"Family friends muke dasu, a gidanmu ya zauna yayi karatu, da ya soni amma yanzu yayi aure shine matarshi take kishi dani"

"Kin fi matarshi kyau shiyasa take kishi dake..... I love you baby"

Lumshe idanuwa na nayi kafin na bashi amsa da,

"I love you too"

"Ki bani labarin ki pls....."

"Labarina kamar yaya?" na buƙata ina kallon kyakkyawar fuskar shi, i mean komai da ya shafeki, abubuwan da kike so da wanda bakya so.... "

Ɗan maƙale kafaɗa nayi kaɗan na turo baki tare da faɗin" uhmm... Kai ka fara " murmushi kawai naga yayi dama nidai ban taɓa ganin fushinsa ba ko me nayi masa ko nace masa sai dai inga yayi dariya ko murmushi,

" Ai ni kin sanni sannan kin ɗan san abubuwa a kaina, abin da ya rage wanda baki sani ba babu yawa sosai...."

"To ka faɗa min wanda ban sani ba...." zuba min ido yayi kafin yace "Baby kece last born a gidanku?"

"no am second to the last, me ka gani and why did you ask?"

"kina da shagwaɓa, shagwaɓarki tayi yawa....I thought ko kece last born, shagwaɓarki na burgeni kuma tana yi miki kyau and tana ɗaya daga cikin abubuwan da nake so atare dake..... Soo keep it up"

Hararar wasa nayi masa sannan cikin turo baki nace "ni ai fushi nake yi dakai.... Kayi min laifi idan baka sani ba"

"Really? Haba baby"

"Ehh mana"

"ok am so sorry, laifin me nayi?"

"kuɗin da ka turo min na menene? Gaskiya nidai bana so ka daina idan har ba so kake yi in daina kula ka ba, dan idan ka cigaba da yimin kyauta irin haka zan fara tunanin ko da wata manufa kake sona...."

"no,no baby, kar kiyi min mummunar fahimta dan Allah, ina son ki da gaske ba da wani abun ba, ki fahimceni dan Allah"

"shikenan amma dai ka rage, kyautar tayi yawa"

Mun jima a wannan wurin muna hira saida muka ci muka sha sannan muka tafi tare har unguwar su Anty ya rakani daga nan muka yi sallama ya juya, daren ranar raba dare muka yi muna hira dan har 3 muka kai saboda shi wai baya baccin dare shiyasa na taya shi hira ranar duk da yana ta kora ta wai ya sallameni in kwanta in yi bacci amma naƙi tun yana ƙi har ya dawo ya haƙura hira ta fara daɗi yana ta bani labarin lokacin da yana school da irin ƙin jin da yayi lokacin, washe gari ai wuni nayi ina bacci, tun daga lokacin nima na koyi ƙin baccin dare dan hirarmu mai daɗi bata tashi sai dare yayi, cikin kwanakin da nayi a Abuja kafin na koma Kano munyi mutuƙar shaƙuwa dashi, satina ɗaya na koma gida, a ranar da na dira ƙawalli na zuwa na fara bata labarin samz da labarin irin son da muke yi wa juna,

"Lallai widat matsalar ki bata ƙarewa... Yanzu kuma ki rasa wanda zaki jajiɓo sai kafiri? Widat Christian fa, duk mazan duniyar nan hausa Fulani ki kasa samun wanda yayi miki har sai kin ɗauko Christian? To wallahi bari in faɗa miki gaskiya wannan guy ɗin ba don Allah yake sonki ba.... Akwai abin da yake so atare dake wanda da zarar ya samu keda shi za ku yi hannun riga.... Ke koda bayan kunyi aure ma wallahi ba abun yarda bane shi dan tsaf zai yi ƙoƙarin rinjayarki dan haka ki rufawa kanki asiri ki rabu dashi tun wuri tun kafin duniya ta sani ta fara zagin ki tana yi miki tofin Allah tsine..... "

" Haba ƙawalli maimakon ki bani ƙwarin gwiwar yin soyayya dashi amma kece zaki yi discouraging ɗina? Ƴanmata nawa ya tsallake yazo gare ni? Sannan shi bada wata manufa yake so na ba da aure muke son junanmu "

" Hmm ke yanzu ko ance ki auri wannan sai ki aure shi? Ƙazami manemin mata mashayin giya.... Uwa uba yaranki, suma zasu zama confuse saboda fsmilyn baban su kafirai ne na uwa kuma musulmi irin wannan ne ba fata ake yi ba zaki ga yara sun zama mix kuma ko bayan ya musulunta to ki sani wata rana zai iya komawa ruwa "

" Samz baya bin mata kuma baya shan giya "

" ta ya akayi kika sani? "

“munyi maganar dashi kuma shida bakin sa ya faɗa min"

"hmmmmm kin taɓa ganin wanda ya faɗi laifinsa da bakin sa musamman a wurin da yake ganin zai iya rasa damarsa? Wannan samz ɗin ba mijin aure bane tun wuri ma ki sani, dan haka kiyi tunani" daga haka ta tattara tsarabarta da na kawo mata ta fita ta barni zaune tsumu tsumu kamar kazar da taji gishiri, gaba ɗaya ji nayi duniyar tayi min ƙunci komai ya tsaya min kuma bana jin dadinsa sannan sam bana cikin yanayi na farin ciki wannan dalilin ne ma yasa na kashe wayata nayi zaune cikin bedroom ɗina ina nazari tare da tunanin mafita........



*Garin dadi littafin kudi ne ga mai bukatar cigaban labarin sai ya tura 500 ta 0774712835 Aisha Ibrahim Access Bank sai a tura evidence of payment ta wannan no 07044644433 ko a tura katin waya da shaidar biya wannan no 07044644433*



_*Ummi Shatu*_👌🏻
[1/5, 12:43] Maman K: ©️ *HASKE WRITERS ASSOCIATION*
_(Home of experts & perfect Writers)_




*GARIN DAƊI.......!*💍💍



*_NA_*


_*UMMI A'ISHA*_


PAID BOOK

*Wattpad:ummishatu*



Life is like a camera lens. Focus only on what’s important and you will capture it perfectly.



24

*Ina kuke manyan mata ƴan ƙwalisa ma'abota son gyara da kece raini, maza ku garzayo ku nemi maman Maryam domin samun lafiyayyu kuma haɗaɗɗun Lagos lace wanda zaku iya samun ɗinkakku da kuma sabbi a ledarsu, kaya iya zaɓinki, gefe ɗaya muna da GHT product, zaku samu,*

~MAI DA TSOHUWA YARINYA

~FEMALE CARE

~REODEO

~VIGOR MAX

~ LONGZIT

~B CLEAR

*DUK ZAKU SAMU WADANNAN KAYA CIKIN SAUKI DA RAHUSA MAZA KU NEMI MAMAN MARYAM AKAN WANNAN NO 07080222187, SIYAN NA GARI MAIDA KUƊI GIDA.....*

~~~Ƙarshen tashin hankali na shige shi irin wanda ban taɓa shiga ba dan ko lokacin da Hashim ya yaudare ni ya kuma juya min baya ban samu kaina cikin ƙunci damuwa da tashin hankali kwatankwacin wannan ba, abubuwa ne goma da ishirin suka taru suka yimin yawa cikin lokaci ƙanƙani na lalace na fita kamannina rabona da Samz kuwa tun ranar da su Abba suka yimin iyaka dashi dan wayata ma na kasheta na ajiye bana amfani da ita gaba ɗaya nabi na takura kaina, aikin da muke yi kuwa daƙyar na iya ƙarasa shi muna gamawa kuma na kwanta asibiti sai da nayi sati biyu ana yimin ƙarin ruwa da allurai sannan muka koma gida kuma har lokacin ba wai na manta da Samz bane ko na daina sonsa a'a har lokacin yana nan maƙale acikin raina, ni kaina ban san wanne irin so nake yi wa wannan bawan Allah ba ga yawan mafarki dashi da nake yi wanda har ya zame min jiki dan kusan kullum sai na ganshi cikin mafarki na. Tun bayan da aka sallamo ni daga asibiti ban sake yin lafiya ba kullum ni kenan kwantarwa a asibiti kamar wata me sikila kullum cikin rashin lafiya nake bini bini zaka ganni da cannula a hannu cikin haka aka saka ranar bikin ƙawalli da yaya Abdul Hakim nidai kawai lallaɓawa nake yi amma ba wai wata lafiya gare ni ba, ƙawalli kuwa cemin take dan Allah in taimaka kar in ƙara kwanciya gabannin bikin nan, duk lokacin da ta faɗi haka murmushi kawai nake yi ko in yi dariya danni ji nake kamar tawa ta kusa ƙarewa saboda wannan jinyace jinyacen da nake tayi bana cikakken wata guda sai an bani gado a hospital an ƙaƙƙara min ruwa Annie duk fushin da ta ɗauka dani yanzu ta sauko kullum cikin rarrashi na take tana cewa in kwantar da hankali na in dai akan Samz ne zasu aura min shi muddin idan ya musulunta dama ba wai basa sonshi bane addini ne bai bada damar inyi wata mu'amala dashi ba bare har maganar aure ta shigo in dai bai musulunta ba, kullum nasiha take yimin akan in rage damuwa in cigaba da addu'a tare da neman zaɓin Allah amma bata jin daɗin wannan rama da rashin lafiyar da kullum nake cikinta daga ƙarshe tace ko zan je gidan Anty inyi kwana biyu a'a nace mata saboda bana son zuwa ko ina a yanzu nafi son in zauna a gida,

Shima Abba kwanaki uku da suka wuce da kansa ya kirani yayi min nasiha akan in saki raina indaina damuwa wai idan ma akan maganar auren da yace zai yi minne da duk wanda yasamu ya fasa ba zai aura min wanda bana so ba zai jira har lokacin da zan samu wanda raina ya kwanta dashi kuma na gabatar musu dashi a matsayin wanda nake so saboda shi duk a tunaninshi wannan maganar ita na saka a raina take damuna nan kuwa ba haka bane tsabar tsananin ƙulafucin son Samz ne keta wahalar dani yana ɗawainiya da rayuwata wanda ni kaina ban da yanda zanyi, tunda jimawa dama muka ƙulla ƙawance da zaman ɗaki bani da aiki zai zama a ɗaki dan sai ka zo gidan ka wuni harma ka kwana baka san ina gidan ba sai idan Abba ne ya aika a kirani ko su mama,

Kamar koda yaushe yauma ina kwance a ɗakina bayan na gama gyara shi na wanke toilet na yanke farata na, ƙawalli ce ta shigo bakinta ɗauke sa sallama ganina kwance da cannula a hannuna ya sata ɓata fuska tana faɗin,

"ubangiji Allah dai yasa lafiyarki ƙalau...."

"lafiya ta Lau, me kika gani?"

Zama tayi gefen gado na tana shaƙar ƙamshin turaren tsinken da na kunna wanda ke tashi daga can jikin ƙofar toilet ɗina,

"na ganki ne a kwance, wai ƙawalli me yasa zaki rinƙa zama shiru? Ki ɗauko wayarki haka mana ko kya rinƙa rage kaɗaici"

"uhmm uhmm bana buƙata,ko ranar Abba ma sai da yace zai bani kuɗi in sai waya nace ina da ita, kawai bana so ne yanzu"

"Amma widat wannan damuwar da kike ciki fa tayi yawa dan Allah ki rage, ai idan so cuta ne to haƙuri magani ne fa"

"hakane.... Allah ya bani iko"

"amin, ki tashi muje ki rakani kasuwar kwari dan Allah"

Ban binciki me zata siyo ba na miƙe na shirya muka tafi, sai a hanya take sanar dani wai material zamu siyo wanda zata saka ranar dinner jiya da daddare yaya Abdul Hakim ya tura mata kuɗin, nice na zaɓi duk abubuwan da zata saka tun daga kan material ɗin zuwa takalmi, da duk wani abu da zata saka ranar bikin sai dab da magriba sannan muka baro kasuwa wanda tun zuwanmu wani yaro ya maƙale min shagon na mahaifinsu ne daga ƙarshe ma shi ne ya mayar damu gida ƙawalli sai wani biye masa take yi ni kuwa a raina nace wallahi yamin yaro nan take samz ya faɗo min namiji har namiji ashe ba rabona bane.
***

Jikinta har rawa yake saboda bala'i da masifa baka jin komai sai ƙarar sautin masifar ta wanda ta cika falon dashi,

"Ni Deborah ni za ayiwa wannan munafurcin da rainin hankalin? Ni yau kake faɗawa zaka bar addinin da ka taso aciki zaka koma wani? Wannan ba zai taɓa faruwa ba, ni ban haifi ɗan da zai zama musulmi ba Samuel.... Idan har mahaifinka shine ya zuga ka ko kuma yayi maka huɗuba to ina son in tunatar dakai abin da ka manta, kana dai ganin irin ƙyama da tsanar da dangin mahaifinku ke nuna mana, ko abinci nayi na basu basa ci idan abu ya fito daga hannuna basa ci, duk duniya bani da maƙiya sama dasu amma yanzu shine zaka zo kace min zaka musulunta...."

Sunkuyar da kansa yayi ƙasa sannan cikin sanyin murya yace,

" Am sorry mommy..... Ni yanzu na girma na san abin da ya dace da wanda bai dace da rayuwa ta ba and Daddy ba shine ya nemi da in musulunta ba in fact ko maganar ma bai sani ba, sannan mommy ai kowa yana da ikon zaɓar addinin da yayi niyya....." tun kafin ya rufe bakin sa yaji ta ɗauke shi da mari wanda rabon da tayi masa wani abu mai kama da wannan tun kafin ya mallaki hankalin kansa dan bama zai iya tuna rabon da ta ɗora hannunta a kansa ba da sunan mari ko duka dan duk cikin ƴaƴanta babu wanda take so kamar sa gashi yana tsananin jin tausayinta dan ko abu yaci ya rage sai ya kawo mata amma yau shine ke ƙoƙarin watsa mata ƙasa a ido wai zai koma addinin babansa,

"Samuel ni mahaifiyarka ni kake faɗawa kana da ikon yin duk addinin da ka zaɓa? Wallahi in dai nice na haife ka to babu kai babu musulunci idan kuwa ka bijirewa magana ta to sai na yi maka addu'ar la'anta...."

"Kiyi haƙuri mommy amma nikam daga yau na bar addinin kiristanci...." daga haka ya tashi ya fita yana fita mahaifinsa shi kuma na shigowa,

"Maman Maryam me yake faruwa nake jiyo hayaniya tun daga gate?"

Wata uwar harara ta watsa masa idunwanta har juyawa suke dan ɓacin rai,

"Allah ya isa tsakanina daku kai da ɗan uwanka da kuka haɗa baki zaku rabani da ɗana kuma wallahi sai kunga abin da zai biyo baya dan ba yafewa zanyi ba..."

Cikin baƙin ciki da ɓacin rai ta faɗa ɗaki ta ɗauko Bible ɗin ta ta fita tana kuka bako ina zata je ba sai church ɗinsu wurin pastor dan ayi ma ɗan ta addu'a asirin da aka yi masa ya karye kamar yadda take tunani, dama tun farko wannan dalilinne yasa ta tsani uncle ɗinsu Samuel saboda shida iyalansa gaba ɗaya musulmai ne kuma tana zargin da sa hannun sa wurin musuluntar da Samuel ke ikirarin zai yi,duk da bata bari yaranta su raɓi gidan uncle Sadiq kamar yanda suke kiransa amma yau shine za a haɗa baki a cutar mata da ɗa, ita fa ko hutu bata bari yaranta suje masa duk da suna kusa, lokacin da taje church rufuwa akayi akanta ana yi mata addu'a sakamakon kururuwar da ta shiga da ita. Shi kuwa Samz ɓacin rai da damuwa ne suka sa ya ɗauki jakar sa ya bar gidan kuma aranar ya koma inda ya fito wato Abuja.
***
Shirye shiryen biki muke yi sosai daga gidanmu har gidan su ƙawalli, nice akan komai wanda ya shafi amarya da ƙawayenta danma bama shiri da angon sosai duk abin da na buƙata sai munyi faɗa kafin ya bani wani lokacin ma sai nayi fushi sai ƙawalli tasa baki sannan zai bada, daga ni har ƙawalli mun zama busy domin biki saura sati ɗaya amarya har anfara yi mata gyaran jiki tun sati biyu da ya wuce, nidai cikin Ikon Allah tunda bikin ya ƙarato ban kwanta jinya ba,

Yau tunda na tashi ban zauna ba nice gidan ƙunshi da kasuwa nice wurin teloli dan can gidan ƙunshi ma nabar ƙawalli, na karɓo ɗinkunan nawa na dawo kenan ina shiga gida na haɗu da Bishra sai na ji tana cewa,

"yawwa gama ta nan ta dawo... Ga yaya widat ɗin nan"

"menene?" na buƙata ina riƙe da kayana da na ƙawalli wanda na karɓo,

"baƙo kika yi.... Yana falon Abba"

Gabana ne naji ya yanke ya faɗi dan duk baƙon da zai tsallake side ɗinsu yaya Abdul Hakim yawuce Guest room ya tafi har falon Abba kasan ba ƙaramin baƙo bane, ni dai haushi ne ya kama ni dan nasan ta yuyu wani ne ya zo neman aure na kuma sai yabi ta sama, raina a ɓace na shiga falon Abba, tabbas na hango mutum kan kujera amma ban ko kalle shi ba na nemi wuri na zauna, sanye nake da English wears riga da skirt sai nasa dogon hijabi wanda yaje min har ƙasa, wasa nake da hannuna wanda ya sha jan lalle da baƙi, fuskata fayau sakamakon ramar da nayi ta sanadiyyar jinyar da na shassha,

"Baby...." Kamar daga sama na jiyo amon muryar da kullum nake bege wadda ko daga bacci na tashi idan na jita sai na shaidata, cikin sauri tare da bugun zuciya wadda zuciya ta ke yi na waiwaya inda najiyo sautin dan ganin shi ɗin ne da gaske ko yaya?.............✍🏻


*Garin dadi littafin kudi ne ga mai bukatar cigaban labarin sai ya tura 500 ta 0774712835 Aisha Ibrahim Access Bank sai a tura evidence of payment ta wannan no 07044644433 ko a tura katin waya da shaidar biya wannan no 07044644433*


*_Ummi Shatu_*👌🏻
[1/5, 12:43] Maman K: ©️ *HASKE WRITERS ASSOCIATION*
_(Home of experts & perfect Writers)_



*GARIN DAƊI.....!*💍💍




*_NA_*



*_UMMI A'ISHA_*


*Wattpad :ummishatu*


PAID BOOK

23


*Ina kuke manyan mata ƴan ƙwalisa ma'abota son gyara da kece raini, maza ku garzayo ku nemi maman Maryam domin samun lafiyayyu kuma haɗaɗɗun Lagos lace wanda zaku iya samun ɗinkakku da kuma sabbi a ledarsu, kaya iya zaɓinki, gefe ɗaya muna da GHT product, zaku samu,*

~MAI DA TSOHUWA YARINYA

~FEMALE CARE

~REODEO

~VIGOR MAX

~ LONGZIT

~B CLEAR

*DUK ZAKU SAMU WADANNAN KAYA CIKIN SAUKI DA RAHUSA MAZA KU NEMI MAMAN MARYAM AKAN WANNAN NO 07080222187, SIYAN NA GARI MAIDA KUƊI GIDA.....*

~~~Ina ƙoƙarin saka fashion earrings ɗina ƙawalli ta shigo, juyawa nayi na kalleta kallo irin na neman ƙarin bayani,

"Malama fito mu tafi...." ta faɗa tana ƙoƙarin fita daga cikin ɗakin, flat shoe ɗina na saka na bi bayanta, sai bayan da muka fita daga cikin gidan sannan take sanar dani ai taje ta tambayi su mama zan rakata Kurna gidan su ummansu wadda ta aiketa,

"Na gode ƙawalli....... Allah ya bar zumunci ya kuma barmu tare"

"Kar ki damu ai kin fi ga haka....."

Napep muka samu muka hau, sai da ta fara kaini har Guest house ɗin da Samz sannan tace dani bayan ta kalleni,

"Ki saka face mask kiyi basaja idan ba so kike wani ya ganki ba, sannan ki bi a hankali dan wannan uban ƙamshin da kike zubawa kina iya tada hankalin maza, asha soyayya lafiya kar a ƙone, 6 daidai mu haɗu anan...." Shawararta nabi na saka face mask sannan na shiga, sai da na shiga harabar Hotel ɗin sannan na kira Samz,

" Hello baby...... " ya faɗa muryarshi ƙasa ƙasa,

"Fito ina jiranka...."

Wayar naji ya kashe cike da farin ciki, mintuna kaɗan sai gashi ya fito, tunda na hango shi nake kallonsa daga ƙasa har sama kawai hango rayuwar mu nake bayan munyi aure, "Maimunatu ko ina zaki kai wannan basamuden mutumin...." wani sashe na zuciya ta ya faɗa, "Inda duk wata mace ke kai namiji, kema zaki iya" ɗayan ɓangaren ya sake bani amsa, murmushi nake yi araina ina sake hasaso yanda zamu kasance matsayin miji da mata, agabana ya tsaya sai na ganni na zama wata ƴar ƙarama a gabansa domin yana da tsayi sosai kuma yana da ɗan jiki madaidaici shiyasa za asa shi sahun giants,

"Tunanin me kike yi?" ya buƙata yana kallon fuskata, ƙasa nayi da kaina ina murmushi,

"Tunanin rayuwar mu bayan munyi aure"

Dariya naga yayi sannan ya nuna min hanya alamar muje bayan yace "let's go baby", jerawa muka yi har wurin wasu kujeru dake ajiye a gefen swimming pool, nan yaja min ɗaya na zauna sannan shima ya zauna, yau sanye yake da jeans black sai t shirt mai gajeren hannu itama black kansa babu hula amma duk da haka yayi mutuƙar kyau,

Kallo na yayi bayan ya zauna "Na san abin da kike tunani ai"

"ok to me nake tunani? Ka faɗa tunda ka sani"

"No ba sai na faɗa ba amma believe me na sani"

"shiyasa ai nace ka faɗa tunda ka sani"

"ok, kin yarda in faɗa?"

"na yarda" na faɗa ina ɗaga masa kai,

"Kina tunanin may be nayi miki girma ko? Shine kawai abin da zaki tuna a yanzu i know"

"a'a ni ba wannan nake tunani ba" na faɗa fuskata a dake duk da gaskiya ya faɗa abin da nake tunani kenan amma sai na dake nace sam ni ba wannan nake tunawa ba,

"ok to idan ba wannan kike tunawa ba me kike tunani?"

"ni kawai tunanin da nake yi gamu nan da yaran mu muna zaune cikin farin ciki"

"Ok na yarda but ta yaya za ayi tunanin samun yara ba tare da an tuna wannan abun ba?" haɗe rai nayi na ɗaure fuska kuma na ƙi nace komai, ganin haka ya sashi yin murmushi ya fara rarrashi na,

"is ok baby.... Am sorry, yakike"

"lafiya Lau" na faɗa batare da na kalleshi ba,

"Baby kin ƙara kumatu... Kin manta abin da na faɗa miki ko?" hararar shagwaɓa nayi masa bayan na narke fuska zanyi kuka,

"Allah ba zan yarda ba" na faɗa cike da shagwaɓa,

"To ki fara exercise" ya faɗa cikin tsokana,

"A'a" na maƙale kafaɗa, shagwaɓa nayi ta yi masa har lokacin tafiya ta yayi, daƙyar muka rabu dan nidai harda hawaye na sai da naji yace in dai kuka zan rinƙa yi idan yazo to ba zai ƙara zuwa ba sannan na haɗiye kuka na muka yi sallama na wuce inda muka yi da Ƙawalli zamu haɗu shi kuma ya koma ciki shima tasa zuciyar babu daɗi kawai ya daure ne kar in fahimta in sake shiga damuwa, ina tsaye bakin titi ina jiran ƙawalli muna waya dashi,

"Wannan kukan da kike yi baby yana taɓa zuciya ta fa gashi banda abunda zan rarrasheki dashi a

Please Login or Register in order to submit comment