Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register



"a ina zaka ganni ma bare har hakan ta faru..."

"wallahi baby idan na kamaki ko......."

"Ahh to ko dai kar in dawo? Gaskiya idan wani abun kake shirya min sai inyi zamana a Kano"

Dariya yayi ya girgiza kai "baby darunki yawa ne dashi, gashi nan kina ta yimin kwalele...."

"ehh mana, kaga saloon din da aka yimin" na fada ina sake haska masa ko ina,

"bakya missing dina ko?"

"inayi mana"

"ban yarda ba"

"haba boo"

"zan zo in ganki"

"ina jiranka hubby"

Mun jima muna hira sannan muka yi sallama naje naci gaba da hidimata shikuma yakoma gida bayan yayi sallar ishah. Tun daga wannan lokacin Felicia bata sake uzzura masa ba har tsawon kwana biyu lokacin ana igobe zai taho daurin auren Bishra,

Yana dawowa daga office ya ganta kwance ita kadai tana rawar dari alamar zazzabi take yi, kamar yayi biris da ita ya wuce amma sai ya kasa nan ya tsaya yana tambayarta me yake faruwa,

"Am having fiver...... And headache"

"ayya sorry amma ina su mommy?"

"sunje church"

"ok" daga haka yawuce bedroom dama bama rasa pcm nan ya dauko mata yakawo sannan ya wuce kitchen yakawo mata abinci da ruwa daga haka yakoma daki amma duk da haka taji dadin kulawar da ya nuna mata kuma hakanne ya sake bata kwarin gwiwar cigaba da pushing watakila hakarta zata cimma ruwa.

Nidai sai murna nake ta yi saboda yau zai zo duk da naga sai rigima yaketa yimin wai idan yazo kwana zai yi sai mu tafi gidanmu mu kwana gobe sai ya koma Abuja tun jiya muke wannan rikicin har yau bamu kare ba dan tunda yaga nasha kwalliya nayi lalle na fito dass dani tamkar nice amaryar shikenan yabi ya rikice min,

"to ke wai me yasa zaki wahalar da bawan Allah, mutum yayi missing matarsa ba sai ki barshi ya sake ba idan yazo...." kawali ta fada wacce ke zaune kusa dani tana jin dramar da muka gama yi dashi,

"kin jiki wani in barshi ya sake, gidanmu fa yake maganar wai zan bishi mu kwana..."

"to menene aciki?"

"uhmmm dama haka zaki fada, amma gashi nan ko ke da kike garin kin taho nan kin tare har sai an gama biki sannan zaki koma gidan ki amma shine ni kike wani fadin in bishi"

"to wai menene aciki? Malama kawai in zaki bar bawan Allah ya sha amarcinsa ki barshi idan bazaki barshi ba ki daina wahalar dashi kuma da kike maganar ni nazo na tare ina gari kaza da kaza ai wallahi dan mijina bai nemeni bane, ko yanzu ya nemeni sai na tafi.... "

" kajita kamar gaske "

" wallahi dagaske nake, ko yanzu Abban Irfan yace kule zance cass to ba zaman sa nake ba... Ke kin san mijinki yana da kulafucinki irin wannan koda yaushe sai ki zauna cikin shiri, daga ya dan ji mararinki ya taho sai ki karbeshi ki barshi ya sakata ya wala amma sai kiyita wani gudunsa kuma ahakan kike cewa bakya son kishiya...... "

" malama zanyi miki rashin mutunci, meya kawo maganar kishiya kuma cikin wannan maganar? "

" idan bakya barinsa yayi son ransa mana, sai gudun mutum kike yana sake nanuke miki.... "

" sai kiyi kuma " na fada ina kokarin tashi dan bar mata wurinma gaba daya dan tunda ta ambaci kishiyar nan naji na kule saboda ni bana son jin duk wani abu wanda ya danganci zan raba mijina da wata yanzun nan sai inji hankalina ya tashi bana son kowacce mace ta rabeshi,

Tunda yazo ban ganshi ba domin wurin daurin aure ya wuce dama yau daurin aure da dinner za ayi washe gari kuma ayi wuni sai araka amarya gidanta, sai da aka taso daga daurin auren sannan yakaraso gidanmu shida yaya Abdul Hakeem mutumin nasa, yana ta kiran wayata ma amma tana can nasa a caji a dakin mama ban san yana yi ba mukuma muna tsakar gida muna fama da baki domin angwayen ma sun shigo anata hotuna saida yaya Abdul Hakeem yazo ya kirani yace in zo ga mijina can yazo sannan na tuna nayi sauri na fita,

Tun daga nesa yake kallona da na shigo falon, ai da gudu na karasa na rungume shi ina cewa,

"oyoyo sweet....am happy to see you"

Rungumeni shima yayi yana shakar kamshin jikina,skirt da riga ne a jikina na material da muka dinka golden color kuma babu laifi yayi min cif cif a jikina,

"baby kinyi kyau...."

"thank you darling..." na fada ina kissing lips dinsa, shima kissing lips dina yayi yana cewa "I miss you baby...."

"I miss you too sweet" ahaka kawalli ta shigo ta riskemu duk da ta jima tana yi mana sallama da knocking amma bamu jiba dan mun dan shagala kadan saboda tunda nazo ya dage yana son sai yaga chest dina nikuma inata kokarin guduwa, zuwan kawalli ne ya sama min lafiya nan suka gaisa ita dai a kunyace ta gaida shi wanda na san iya shege ne kawai irin nata kuma zan sha tsiya sai dai in toshe kunnena, tana fita ya sake kokarin damkoni nan na marairaice nayi kasa da murya cikin rada nace,

"wai dan Allah saurin me kake yi ne? Ba kace tare zamu kwana ba yau? Kayi hakuri mana har sai mun kebe kaga yanzu wallahi wani zai iya zuwa sai aji kunya... Kayi hakuri anjima sai kayi duk yadda kake so" na fada ina rike hannunsa,

"baby wayo zakiyi min ko..."

"am serious sweet..."

Dakyar na samu na lallabashi ya yarda na bashi abincin yaci ya sha drinks sannan na rakashi ciki yayiwa su Annie Allah ya sanya alkhairi daga nan muka yi hotuna dashi yawuce gidanmu sai da daddare zai zo ya kai ni dinner. Ina shiga ciki bayan tafiyarsa kawalli ta kafa tsokanata wai haka nake tafiya da hankalin bawan Allah duk insa ya susuce ya manta inda yake, dariya nayi nace mata,

"to ke ya kika gani? Ai sukari bai farin banza ba"

"ehh ai na gani kam, kina ta gigita bawan Allah, wai menene sirrin?"

"kema Kinfi kowa sanin bana shaye shayen wannan magungunan na mata..... Kawai dai na rasa dalilin da yasa yake manne min"

"Ba kina shan zuma ba... Shi dai yasan me yake ji ai"

"kya dai ji dashi, banda zumar da madara bana shan komai sai fruits sai ko almiski, kema kuma shaida ce"

"to ai gashi nan duk kinbi kin tafi da tunaninsa"

"kanki ake ji fa"

Lokacin dinner din ai ko karasawa baiyi ba yazo nikuma lokacin kwalliya ma ake yi mana dama lokacin da muka rabu gida yaje ya sha bacci bayan ya tashi ya tafi car wash ya kai motata aka wanke, kwazozozon da ƙawalli keta faman yimin na wai na bar bawan Allah tun dazu yana jirana shi ya jawo hankalin anty har ta kai ga cewa abar wannan kwalliyar haka inba yanzu za a gama ba, nan mai kwalliyar ta takaita tabar min duk da hakanma naji anata zuzuta kyawun da nayi harda masu tsokanata wai karfa insa a kasa gane amaryar adauka nice dan wani milk color din leshi dan ubansu nasaka mai digon blue color dinkin fited gown ce sai aka daura min blue color din head ni kaina na san na sha kyau har na gaji, ni kadai na fita na sameshi cikin mota yana waya da mommy, sai da ya gama nima lokacin inata snapping kaina awayata naji ya kwanto jikina yana zagaye cikina da hannunshi,

"baby irin wannan kyau haka...... Kinyi kyau sosai"

"thank you sweet" na fada ina yi mana hoton tare, sai da nagama daukarmu sannan muka bar kofar gidanmu muka nufi hall din da za a gudanar da dinner din wanda already an gama shirya komai baki sun zo anata entertaining din su, sai da nayi dagaske kafin ya barni muka shiga hall din amma da ya matse ni acikin mota sai fitinata yake, ai koda muka shiga hall din sai kallo ya dawo kanmu tamkar mune ango da amaryar,

Dinner din ta kayatar yadda ya kamata wurin karfe 10 aka tashi kawalli sai dariya take yimin saboda yanda samz ya kafa ya tsare yau dai dagaske so yake sai mun kwana tare, lokacin da aka tashi ban yiwa kowa sallama ba bare asanma binsa zanyi kawai nemata akayi kamar walkiya aka rasa, gasasshiyar kaza ya tsaya ya siya mana da ice cream sannan muka wuce gida kuma tun acikin mota ya soma shan sha'aninsa har muka karasa gida, bedroom din da ya sauka ne kawai mai dan dama dama ahakan shima sai da ya gyara lokacin da yaje dan ya danyi kura tunda ni ba acan na sauka ba, kazar muka ci nidai sai turo baki nake saboda daukonin da yayi daga cikin dangi na san chapter din yau ta wuceni wacce aka saba yi kowanne dare kafin a kwanta,

Wanka muka yi tare kafin mu kwanta nidai saboda gajiya ta taru tayi min yawa ban san lokacin da nayi bacci na barshi ba, washe gari da sassafe na tashi nayi masa breakfast nayi wanka duk yana kwance yana bacci bayan na fito daga wankan ina daure da towel naje zan tashe shi,

"sweet...... Sweet....."

Bude idanuwansa yayi ganina daure da towel ya sashi miko min hannu na makale kafada,

"haba mana baby, zo mana, dan Allah ki daina yimin rowa"

"sweet dan Allah ka barni haka...." na fada kamar zanyi kuka,

"no baby, dan Allah ki tausaya min..... Baby a wurinki fa ke kadai zan samu nutsuwa, please my sweet baby..."

Ai a takaice dai sai azahar na koma gida bayan na rakashi airport ya tafi, haka na fuske ina ji su anty Rahina da antynmu suna maganar amma nayi fuska ita kuwa kawalli sai tsokanata take wai dama can munafurci ne yasa nake cewa ni bazan bishi ba ashe nima ina son bin nasa to da wannan taba ka lashen ai da binsa nayi muka tafi Abujan muka je muka cinye junanmu banza nayi mata na dauki Irfan muka fita...........


*Garin dadi littafin kudi ne ga mai bukatar cigaban labarin sai ya tuntuɓi marubuciyar kai tsaye ta wannan no 07044644433*


_*Ummi Shatu*_👌🏻

[1/10, 11:39] Maman K: 60


*Ina kuke manyan mata ƴan ƙwalisa ma'abota son gyara da kece raini, maza ku garzayo ku nemi maman Maryam domin samun lafiyayyu kuma haɗaɗɗun Lagos lace wanda zaku iya samun ɗinkakku da kuma sabbi a ledarsu, kaya iya zaɓinki, gefe ɗaya muna da GHT product, zaku samu,*

~MAI DA TSOHUWA YARINYA

~FEMALE CARE

~REODEO

~VIGOR MAX

~ LONGZIT

~B CLEAR

*DUK ZAKU SAMU WADANNAN KAYA CIKIN SAUKI DA RAHUSA MAZA KU NEMI MAMAN MARYAM AKAN WANNAN NO 07080222187, SIYAN NA GARI MAIDA KUƊI GIDA.....*


~~~Tunda Malika ta soma karɓar gold ɗin shalele bata hakura ba har sai da taga ta karbi fiye da rabi wanda koda yaushe maganar guda ɗaya ce za ashawo mata kan samz ya kaunaceta har su kai ga aure amma duk a banza shuru kamar an shuka dusa sannan kuma tana gargadarta da karta kuskura ta sanarwa da hajiyansu gashi yanzu tunda ta karɓi sarkarta tace zata dawo mata da ita malam kawai zata kaiwa ya gani har yau shuru take jinta babu ita babu alamunta,

Duk abun duniya yabi ya isheta sai faman kiran layinta take yi amma bata samu daga karshe ta dauki motarta ta fita domin neman ta amma babbar matsalar itace bata ma san ta inda zata fara neman nata ba,

Tun bayan fitarta ta lura da wata mota da take binta duk inda tayi hakan yasa ta nemi wuri tayi parking inda mutane ke zirga zirga, wani kyakkyawan matashi taga ya fito daga cikin motar dake bibiyarta ya nufo tata, glass din saitinta yayi knocking nan ta sauke tana kallonsa,

"Barka da yamma ranki ya dade"

"yawwa barka dai" ta fada cikin rashin son hayaniya da damu,

"dan Allah idan bazaki damu ba ina son ki bani contact dinki domin nafi shekara daya ina nema amma an hanani dan ance min ma wai anyi miki miji nikuma na gagara mantawa dake...."

Ganin yanda ya marairaice yasa tayi niyyar bashi amma so take ta fara sanin a inda yaji cewar anyi mata mijin aure wanda ba haka bane,

" waye yace maka anyi min miji kuma awurin wa kake neman contact din nawa? "

" akwai wata ƙawarki Malika.... Tare na fara ganinku ita kuma na santa shine naketa bibiyarta akan ta bani no dinki ko ta ta hadani dake amma taki tace anyi miki mijin aure kuma koda ta hadamu ma ba lallai na dace ba saboda bazaki taba saurarata ba "

Shiru shalele tayi tana nazari daga karshe ta bashi no din nata suka yi sallama yana cike da farin ciki ya juya ya tafi Affan Umar faruk kenan matashin saurayi kwararre a fannin kimiyya da fasahar zamani, shalele fasa zuwa neman Malika tayi kawai sai ta juya ta koma gida dan lamarin kawancensu da Malika yana bukatar ta zauna tayi dogon tunani, Meyasa Malika zata yi mata haka? Wanne irin kawance suke yi? Haka ranar ta kwana tana tunani daga karshe ta fahimci abinda Malikan ke yi mata wato zagon kasa da kuma tarin hassada baya ga cin dunduniyarta da take yi bayan duk irin tarin alkhairin da take yi mata domin iyayen Malikan ba wasu masu karfi bane, bata sake tsinkewa da lamarin Malikan ba har sai da Affan yazo nan ya fede mata biri har wutsiya kan lamarin nan ta rasa wanne irin mataki ya dace ta dauka akan Malika.

***
Koda samz ya koma gida mommy dorawa tayi daga inda ta tsaya akan lamarin samz da Felicia sai dai amma ita Felicia din yaga kamar ta danyi sanyi dan ta daina damunsa da takura masa yanzu mommy ce kadai ke nata,

Bayan kwana biyu da komawarshi su mommyn suka fara shirin tafiya Kaduna amma banda Felicia wanda shi kwata kwata bai san da wannan shirin nata ba ita kuma mommy da yake babu ruwanta bata hanata ko ta tisata a gaba sun tafi ba, goma ta arziki ya hada musu amma sai yaji mommy tace,

"ga Felicia nan ita sai nan da 2 days sannan zata dawo Kaduna..."

"mommy wannan kuma wacce irin magana kike yi? Felicia ba muharramata bace tayaya zamu zauna gida daya tare da ita"

"to koma dai menene zata zauna kuma wallahi ban yarda ka koreta ba a wannan karon idan kuma har ka koreta bawai saboda son ranta tabar gidan nan ba zaka ga yadda zamu kwashe dakai..."

"mommy gaskiya nidai za a takura min ne kawai"

"koma me zaka fada ka fada amma tana nan a gidan nan"

Shiru yayi bai kara cewa komai ba daga karshe ya shiga daki ya rufe kan shi yana tunani shi yanzu ina zai je tunda dama wurin ahmad ne to gashi shi dinma yayi aure, baya son neighbors su fahimci da wata acikin gidan wani ya kawo min rahoto har asamu matsala, har su mommy suka tafi bai fito ba sai lokacin sallar magriba nan ya fice yabar gidan gaba daya kuma bashi ya dawo ba sai misalin karfe 10, bai ji ko motsinta ba ya wuce ciki yayi wanka yayi shirin bacci ya dauki laptop dinshi ya soma rage wani aiki da yake yi,

Shigowar Felicia yasa shi dakatawa daga aikin da yake yi ya kalleta,

"Samz....." ta fada bayan ta tsugunna tare da ajiye gwiwowinta akasa a gabanshi,

Zuba mata ido kawai yayi cike da bakin ciki batare da ya tanka ba hakan ya bata damar cigaba, hannu ta kai kan nasa zata fara shafawa yayi saurin janyewa ya ajiye laptop din tare da mikewa ya fice daga cikin bedroom din nan tabi bayanshi da gudu tana shan gabansa duk da haka bai tsaya ba har suka isa falo,

"ki matsa min ahanya, zan fita in bar miki gidan tunda hakan kike so...."

"samz bai kamata ba abubuwan da kake yimin, saboda me kaida gidan ka zaka fita? Kayi hakuri indai dan nice"

Cikin bedroom ta koma ta rufe ta zauna ta rafka tagumi tana tunanin me yadace tayi ne wai? "you have to take some fertility pills..." wani bangare na zuciyarta ya fada mata nan ta saki murmushi ta rungume pillow, bai sake jin duriyarta ba har gari ya waye ya shirya ya tafi office nikam dama kusan kwana muka yi muna waya yana tambayata yaushe zan dawo nace masa sai na huta yace wai A'a in dawo zai yimin maganin gajiyar dariya nayi nace masa to ina nan dawowa ya shirya. Bayan tafiyar su mommy da kwana biyu da misalin karfe 12 na dare bayan mun gama waya yaji knocking a kofar dakinmu, tashi yayi ya bude nan yaga Felicia sanye cikin rigar bacci tana kuka shabe shabe,

"Felicia what's happening?"

Shigewa cikin bedroom din tayi cikin sanyin murya tare da nuna tsantsar nadama yaji tace,

"zuwa nayi in baka hakuri akan duk abubuwan da nayi maka.... Ka yafe min sannan ka manta komai, saboda hankalina ya kasa kwanciya..... Samz ka tsaneni yanzu bayan ada ni kafi so fiye da kowacce mace, kayi hakuri ka yafe min zan tafi in bar muku gidan ku"

Shiru yayi yana tuna baya wato lokacin da suka fara haduwa anan Abuja a Nysc camp kuma tun anan suka kulla soyayya har suka shaku cikin kankanin lokaci haka kuma tare suka zauna bayan fitowarsu daga camp har suka kammala service dinsu amma babu abinda ya taba shiga tsakaninsu duk da tsananin kyawun da take dashi dan fara ce cikakkiyar mace mai kyakkyawan jiki,

Ganin irin kukan da take yasa yaji zuciyarsa ta karye har ya gaza cewa komai daga karshe ya dagota yana share mata hawayen da take yi,

Cikin karyayyiyar murya ya soma rarrashinta wanda shi kansa bai san dalili ba shi dai kawai yasan a tsawon rayuwarsa baya son ace shine yazama silar zubar hawayen wani musamman ma mace sannan baya kaunar yaga mace tana kuka koda kuwa bai da alaka da ita kuma ko bai santa ba,

"am very sorry Felicia.... Pls stop crying...." ya fada cikin sanyin murya wadda Felicia ke jin hakan har cikin ranta, tunda take dashi ko kuma tun lokacin da ta san shi bata taba samun kusanci dashi kamar haka ba dan ko ada lokacin da suke zaune tare gida daya baya bari ta kusanceshi kamar haka, bata taba sanin zata samu wannan damar ba irinta yau, sake narke masa tayi tana kukan da ta san dole zai taba zuciyarsa saboda wani irin kuka take yi wanda baya fita sosai,

"kiyi hakuri..... Pls ki daina kuka ya isa haka..... Am very sorry"

Haka yaci gaba da rarrashinta yayinda ita kuma take sake shige masa har bai san lokacin da wani abu wanda bazai iya fassarawa ba ya gifta gaba dayansu wata duniya suka shiga wacce basu shirya zuwanta ba daidai wannan lokaci, gaba ɗayansu cikin wani yanayi suke shi dai samz sam bai farga ba har sai da mai afkuwa ta afku nan yayi lamo bayan ya kwanta cikin tunani kala kala,

"yanzu shikenan naci amanar widat? Innalillahi..... Gaskiya am very stupid" wannan shine abinda yaketa maimaitawa tun bayan da komai ya kammala, juya mata baya yayi yana ta jan tsaki yana tunani da irin farin cikin da muke kasancewa a duk lokacin da muka kasance cikin irin wannan yanayin,soyayya yake nuna min kamar zai hadiyeni,

Cikin tsananin farin ciki marar misaltuwa Felicia ta dubeshi duk da ya juya mata baya kuma yana ta faman jan tsaki hakan bai hanata matsawa jikinsa ba ta dora hannun ta kan wuyansa tana shafa shi, lallai sai yau ta yarda cewa idan har baka yi giving up ba a komai to zaka iya dacewa wata rana, duk da bawai dole tayi masa ba amma ta lura da sai fushi yake ta yi kamar me dan sai ture hannunta yake daga karshe ya tashi ya wuce cikin bathroom yayi wanka cike da bacin rai da kunci, ita kuwa Felicia me take banda murna sai murmushi take ita ɗaya tana tuna yanayin da suka kasance dazu, tana jinsa ya sakarwa kansa ruwa yaki fitowa har bacci ya dan soma daukarta,

Ransa babu dadi fuskarshi a daure ya fito daga cikin bathroom din ko ganinta baya son yi bare ya tuna abinda ya faru, shi babban bakin cikinsa ko lokacin da bai yi aure ba bai taba aikata zina ba amma yau gashi yayi duk da yana da aure, ransa a bace taji yana yi mata magana,

"Felicia..... Tashi ki fita zanyi bacci"

Sama sama taji abinda yake cewa ta dan dago kanta tana kallonsa cike da mamaki dan ita a tunaninta zai dan lallabata ya tarairayeta amma sai taga sabanin haka, maimakon taga yana farin ciki sai taga yana fushi,

"wai bakya jina ne? Tashi ki fita...."

Batace masa komai ba ta kwashi kayanta ta fita ranta fari tas dan farin ciki da murna, ji take kamar ta kira mommynta ta sanar da ita abinda ya wakana amma kuma dare yayi dole sai dai ta jira safiya kafin tayi mata wannan albishir din,

Bayan fitar ta zama yayi ya dafe kansa yana jin kamar ya kirani ya sanar dani cin amanar da yayi min amma sai wani bangare na zuciyarsa ya gargadeshi da kar ya soma tafka wannan kuskuren domin a zafin kishina tsaf zan ki dawowa, ko na shiga wani hali saboda yasan babu abinda na tsana irin inga wata mace ta rabeshi,

"am very sorry baby, ki yafe min naci amanar ki...." haka yaketa maimaitawa amma ya kasa kirana bare ya sanar dani, gyara gadon yayi ya kwanta bayan ya canja bedsheet daga wanda suka kwanta akai, gaba daya daren ranar kasa bacci yayi sai tsantsar damuwa da nadama da ya tsinci kansa a ciki sai dab da asubah sannan bacci ya daukeshi mai cike da mafarkai kala kala................


*Garin dadi littafin kudi ne ga mai bukatar cigaban labarin sai ya tuntuɓi marubuciyar kai tsaye ta wannan no 07044644433*


_*Ummi Shatu*_👌🏻
[1/11, 10:45] Maman K: 61


*Ina kuke manyan mata ƴan ƙwalisa ma'abota son gyara da kece raini, maza ku garzayo ku nemi maman Maryam domin samun lafiyayyu kuma haɗaɗɗun Lagos lace wanda zaku iya samun ɗinkakku da kuma sabbi a ledarsu, kaya iya zaɓinki, gefe ɗaya muna da GHT product, zaku samu,*

~MAI DA TSOHUWA YARINYA

~FEMALE CARE

~REODEO

~VIGOR MAX

~ LONGZIT

~B CLEAR

*DUK ZAKU SAMU WADANNAN KAYA CIKIN SAUKI DA RAHUSA MAZA KU NEMI MAMAN MARYAM AKAN WANNAN NO 07080222187, SIYAN NA GARI MAIDA KUƊI GIDA.....*


~~~Ba shi kaɗai ba nima daren ranar dakyar na iya bacci sai dai ko ka kadan ban kawo komai araina ba haka kuma ban kawo rashin baccina da kuncin da nake ciki yana da nasaba da samz ba,

Washe gari makara yayi sosai dan sai karfe 6 sannan ya tashi, yana tashi ya tuna da abinda ya faru tsakaninsu da Felicia ai take wani sabon bakin ciki ya ziyarci zuciyar sa wanda har sai da yaji kansa ya sara, cike da damuwa ya wuce cikin bathroom yayi alwala ya fito ya zo yayi salla wanda ya jima yana istigfari dan yasan ya aikata babban laifi mai girma domin zina tana daga cikin manya manyan laifuffuka kamar yadda yaji malamai na fada, koda wasa baya son ya kirani ko yaji muryata yau asalima tausayi nake bashi saboda irin yadda ya san ina tsananin sonsa kuma na bashi dukkan yarda 100% amma gashi ya gaza rike amanata yaci min amana, gaba ɗaya ji yayi baya sha'awar komai yanzu komai ya fitar masa arai tsabar damuwa da tashin hankalin da yake ciki ciwon kai da zazzabi yaji ya rufe shi.

Kwanan farin ciki Felicia tayi gari yana wayewa asubar fari ta kira madam comfort tana dauka cikin karaji taji tace,

"mommy...... Burinmu ya kusa cika.... Komai ya kammala"

"wow.... Congratulations my dear"

"thank you mommy"

"yanzu menene abu na gaba??"

"mommy sai na dawo....."

"Allah ya dawo dake lafiya my dear..."

Bacci ta koma wadda bata yiba saboda tsabar murna, ba ita ta tashi ba sai bayan karfe 10, wanka tayi ta sha wata matsiyaciyar riga pink iya cinya mai siririn hannu, bedroom din da samz yake ciki ta nufa amma sai taji a rufe tayi ta knocking amma shiru bai budeba, kitchen ta shiga ta dafa noodles ta fito ta zauna taci daidai lokacin shikuma yasamu ya tashi yayi wanka ya saka kananan kaya yafito, zaune ya hangota tagama cin abinci tana jiyo motsin fitowarsa ta taso cikin kwarkwasa zata yi hugging dinsa yayi saurin tureta,

"honey....."

"karki sake kirana da honey..... Kin san me? Duk abinda ya faru tsakaninmu daren jiya it was a mistake kuma bana fatan hakan

Please Login or Register in order to submit comment