Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

mata kudi da idona naga text massage ta turo maka tana yi maka godiya kuma tana kiranka da darling, akan na nuna bacin raina shine zaka kira gidanmu ka fada musu a kirani ana yi min faɗa........ " na fada cikin kuka,

" kiyi hakuri ba zan sake ba...... Ki daina kuka please.... "

" kana jin irin fadan da yaya yayi min.... "

" ba zan sake ba kiyi hakuri my baby love " ya faɗa yana sake hadani da jikinsa, kuka nake yi sosai mai dauke da dalilai biyu, na farko massage din da na gani na biyu kuma fadan da yaya Abdul hakeem yayi min,

" kiyi hakuri baby.... " shine abinda yake ta cemin yana share min hawayen,

" baby munira fa na turawa 20k wai tana school but trust me wallahi ban tura mata da wata manufa ba and babu komai tsakaninmu sai zumunci, ta tambaye ni kudi kinga bai kamata in hanata ba tunda matsayin kanwa take gareni......" idanuwana jajur hawaye na bin kumatuna na kalleshi,

" babu komai tsakanin ku amma shine harda kiranka da darling?"

"kiyi hakuri zan fada mata kar ta sake tunda bakya so..... Ni ina ta so kiyi kiyi ki gama period in baki baby amma shine zaki rinka fushi dani?" jin abinda yace ya sani kallonsa yana share min hawayen nace,

"to ai ban gama ba kuma may be sai next tomorrow....." murmushi yayi acikin ransa dama yasan tunda yayi maganar ciki to zai samo kaina da wuri dan ya fahimci yanzu shi kadai ne damuwata, matsalata kuma burina, bani da wani buri wanda ya wuce inga na samu ciki amma shiru kamar an shuka dusa,

" ai babu problem koma yaushe ne zan jiraki ki gama...."

"ni dai sweet ina tsoro....."

"tsoron me kike yi baby?"

"Allah yasa mu samu cikin nan.... Bana son ka kara aure saboda bana haihuwa"

"baby wannan wanne irin magana ne kuma? Babu auren da zan kara kuma zaki haihu at the right time Insha Allah....." ya fada yana kissing bakina,

Lafewa nayi cikin jikansa ina cewa "Allah yasa"

"amin but stop crying baby...."

"ba kaine ba....." na fada cikin shagwaba ina turo baki,

"to ai na baki hakuri, baki huce ba?" kai na ɗaga masa,

"in riƙe cikina kenan bakya so?"

Harararsa nayi bayan na turo baki na shagwabe fuska,

"wannan kuma ai hakkina ne...."

Dariya yayi ya sumbaci lips ɗin nawa ya sake rungume ni yana shafa bayana,

"baby sarkin rigima, muje kici abinci...."

"ni bazan ci ba..."

"please my love....."

Lallabani yayita yi har muka ci abincin muka gama sannan na ɗan warware, shi dai dukufa yayi yana aiki a system dinsa nikuma ina kallo har dare ya raba, jikinsa na matsa nayi pillow da cinyarsa anan bacci ya kwasheni. Wasa wasa kafin mu baro Lagos sai da na murmure jikina yayi lumi lumi subul subul sai uban sheki da ɗaukar ido nake shiyasa duk wanda yaga yanda nake glowing zai dauka ciki gareni amma ni da shi mun san ba cikin bane kawai weather din garin ne ta karbeni haka kuma samz ya kula dani sosai kamar yadda nima na kula dashi a takaice dai mun kula da junanmu yadda ya kamata mun zuba soyayya mun bawa junanmu farin ciki kamar babu gobe, koda suka gama aikinma bamu tafi ba yace sai mun ƙara 2 weeks ya ɗan huta sannan sai mu koma Abuja, ai kuwa na gayawa yan garinmu dan koda yaushe yana nanuke dani wuni zamuyi cikin daki daga bacci sai rigimarsa dan babu inda yake zuwa idan na shagwabe fuska zanyi complain sai yace wai to shikenan tunda bana son cikin kai gaskiya samz akwai wayo koda yake ai wanda ya fika ya fika shiyasa dole wayonsa yafi naka kuma idan idanuwanka suka rufe da son abu tofa babu wahala an ɗana maka tarko ka faɗa shiyasa yake yimin wayo shikuma yadda jikina yayi kyaune halittu na suka sake cika gaba da baya sune suke sake rudarshi baya iya hakuri dani wannan dalilin ne yasa yanzu na gane samun ciki kawai rabone daga Allah idan ya baka ya baka idan bai baka ba kuma sai dai haƙuri. Duk da bani da ciki amma hakan bai hanani lodar kayan baby ba lokacin da muka shiga kasuwa, kaya na siya sosai sannan na sissiyi ƙananan kaya dan na fuskanci yafi sonsu idan yana tare dani, shima na siya masa inner wears da kayan bacci amma bai sani ba har sai da muka koma gida da ina sake dudduba kayan anan ya gani, yau dai da wuri nayi bacci saboda gajiyar da na debo a kasuwa,

Munje duk inda ya dace muje dan bude ido da shakatawa sannan muka koma Abuja, makota na duk babu wadda ban yiwa tsaraba ba haka yan uwa da danginsa duk na sissiya musu duk da na san bafa lallai in burge ba ko inyi gwaninta dama dai kawai dan Allah nayi dan na san baza ataba yaba min ba.

Washe garin ranar da muka dawo abokinsa Ahmad ya kawo matarsa muka wuni tare da ita dan kusanma ita ta tayani yan gyare gyaren da na tashi dasu na gidana saboda ko ina yayi datti, mai nutsuwa da ita da kamun kai babu ballagazanci da shirme irin na wasu matan tabbas na yaba da kirkinta da nutsuwarta shiyasa nima na sake da ita, sai da suka dawo daga office muka ci abinci tare dasu sannan ya dauketa suka tafi, ai muna shigowa ciki da rakiyar su ya jani jikinsa yana shagwabewa "baby yau munyi fada da ke....."

"tunda munyi fada to bari inje inyi kallona......"

Makale ni yayi yana hararata, "ina zaki je? Bayan yau wuni guda baki kulani ba..."

"oh my God, duk da nayi bakuwar so kake in sakata a gaba ina waya da kai saboda kawai ni nafi kowa miji a duniya...."

"yes nah...."

"am sorry boo...." na fada ina kissing lips dinsa,

"ni ban hakura ba....." ya fada cikin shagwaba, nima shagwabar na fara yi masa har tsawon wani lokaci kafin ince masa,

"sweet ina son zanje Kano...."

Dakatawa yayi daga wasan da yake yi da kunnena guda daya,

"baby any problem?"

"babu komai boo kawai ina son inga gida ne...."

"ni kuma sai kibarni da wa?" murmushi nayi na rungume kansa a kirjina ina shafawa, "ai zan kasance da kai cikin kowanne lokaci sweet"

"zaki yimin wayo dai kawai" ya fada yana cigaba da wasa da kunnena kuma cikin shagwaba,

"no darling....."

Da lallama da rarrashi da wayo dai na samu ya amince ya barni zanje amma wai 1 week kadai ya amince inyi, hakanma yayi tunda kawai ganin gidane sai tsarabarsu da zan kai musu ba suna ake yi ko biki ba bare ince yayi min kadan, babu wanda na fadawa zan zo bare a hanani zuwa duk da cewa rabona da gidan tun haihuwar ƙawalli gashi yanzu Irfan din tsaiwa yake yana neman fara tafiya sai ko lokacin da muka je bikin abokinsa wannan kuma bama na saka shi cikin lissafi dan babu inda naje, ranar Juma'a da safe ya rakani airport na tafi shikuma ya koma gida.....


_*Ummi Shatu*_👌🏻
[1/5, 12:43] Maman K: {51}


Ina kuke manyan mata ƴan ƙwalisa ma'abota son gyara da kece raini, maza ku garzayo ku nemi maman Maryam domin samun lafiyayyu kuma haɗaɗɗun Lagos lace wanda zaku iya samun ɗinkakku da kuma sabbi a ledarsu, kaya iya zaɓinki, gefe ɗaya muna da GHT product, zaku samu,

~MAI DA TSOHUWA YARINYA

~FEMALE CARE

~REODEO

~VIGOR MAX

~ LONGZIT

~B CLEAR

DUK ZAKU SAMU WADANNAN KAYA CIKIN SAUKI DA RAHUSA MAZA KU NEMI MAMAN MARYAM AKAN WANNAN NO 07080222187, SIYAN NA GARI MAIDA KUƊI GIDA.....


~~~Gaba ɗaya hankalinta da tunaninta na ga kyakkyawar halittar da ta gani shiyasa driving ɗin a sannu take yi har ta ƙarasa airport, samun Jalil tayi yana ta faman mita domin jirginsu yajima da sauka sannan yajima rabonsa da ƙasar shiyasa yake jin kamar yayi tsuntsuwa ya tafi kawai ba tare da ya jira shalelen ba wacce itace ke binsa ma'ana daga shi sai ita,

"you are very stupid..... For how long zanyita jiranki" yace da ita lokacin da ta karasa inda yake zaune yana jiran ta,

"am very sorry yaya Jalil...."


"Hmmmmm finally..." ya faɗa yana sabar jakarshi,

Sun hau hanya sun fara tafiya ya dube ta yace "shalele wai har yanzu babu wani labari a kasa?"

"wanne iri kenan?"

"aurenki mana, yanzu ai kowa aurenki yake jira, ni i thought kafin na dawo daga Malay ma zan zo in samu anyi aurenki...."

"oh yaya Jalil kudai baku da magana sai ta aurena wai haka kuka gaji dani ban saniba?"

"ba gajiya muka yi dake ba kawai muna sone muga kema mun Mika ki ga wanda ya dace....."

"to har yanzu dai, kuma ni ko saurayin ma bani da shi"

"Haba, karya kike, kyakkyawar budurwa kamar ki"

Dariya suka yi gaba daya suka cigaba da tattauna maganar har suka isa gida nan ta wuce bedroom ta barsu anata marhaban lale da zuwan sa, Malika ta kira awaya tace tazo da sauri akwai labari, mintuna 30 sai ga Malika ta karaso nan suka wuce daki suka ƙule Jalil yana tsokanarsu yana cewa ashe har yanzu suna nan da wannan munafurcin nasu na zaman cikin ɗakin,

"Malika you know what? Am in love....."

"wow...... Bani insha" Malika ta fada cikin mamaki dan ita dai a duk zamanta da Suhaila bata taba jin ta yaba da wani ba bare har tace tana sonshi,

"Ɗazu zanje dauko yaya Jalil a Airport na ga wani kyakkyawan guy...."

"umm humm sai akayi yaya?"

"sai nayi ta binshi har zuwa office din su, ban san komai a kansa ba amma dai na bama wani assignment akan ya nemo min dukkan abinda ya shafe shi"

Ajiyar zuciya Malika ta sauke kafin tace "shalele anya kuwa kina ganin babu damuwa? Idan kuma yana da aure fa??"

"dan Allah bari wanne irin yana da aure, kin ganshi kuwa very handsome? I don't think yana da aure gaskiya...."

"Idan kuma yana da shi fa?"

Zubama Malika ido tayi na tsawon lokaci kafin tace "bazan iya jurewa ba, koda yana da aure to ya zame masa wajibi ya rabu da ita sannan ni ya aureni dan kema kanki kin san ina da zafin kishi kuma ba zan taba iya hada mijina da wata ba"

"amma anya shalele tunaninki yana baki daidai kuwa? Anya ba zamu yaudari kanmu ba idan har muka tsaya akan wannan matsayar? Ta yaya zamu yaudari zaukatanmu da cewa idan har yana da aure zai rabu da matarsa dan kawai saboda ke? Sake tunani dai...."

"Malika ni ina ganin ma kawai mu bar wannan maganar mu jira feedback daga wurin wannan guy din dan bama na son maganar yana da aure, what i believe is he's single.... Not married"

"ok Allah yasa haka...."

Wayarta ta dauka ta kira Gabriel daya daga cikin securities din wurin aikin su samz wanda ta bawa aikin binciko mata komai da ya shafi samz, har tayi ta katse bai dauka ba haka yasa ta rabu dashi bata ƙara kiransa ba sai da daddare nan suka yi magana ya dan sanar da ita wadansu abubuwan da ya sani game dashi sauran kuma yace sai ya bincika sa'annan zai nemeta,

Tun a ranar ya soma gudanar mata da bincike cikin sirri yayin da ita kuma taci gaba da yi masa ɓarin kudi kamar babu gobe ataƙaice dai shine ya binciko komai tun daga kan phone no har zuwa inda samz ke zaune amma bai sanar da ita cewa yana da aure ba har sai bayan da soyayyar tayi nisa da girman da ba zata iya jurewa ba acikin zuciyarta, ranar da Gabriel ya sanar da ita cewa gobe ne birthday din samz kamar yadda ya binciko date of birth dinshi wani tsadadden boutique suka tafi ita da Malika wanda ke nan garin Abuja na manyan yara suka je suka ragargaji kudi suka iyo siyayyar gift ta aika masa duk da ta tuttura masa massages sau shurin masaki amma babu reply hakan bai sa ta hakura ko taji gwiwarta tayi sanyi ba asalima wani ƙaimi ya ƙara mata. Haka ta cigaba da bibiyarsa batare da ya sani ba wani lokacin haka kawai zata fita sassafe taje tayi parking daidai office dinsu dan kawai ta ganshi, tana ganinsa zata juya ta koma gida, ranar da suka je tare da Malika ta ganshi shiru Malika tayi na tsawon lokaci har sai da Suhaila ta yi mata magana wurin sau uku sannan ta ajiye wani gwauron numfashi tace,

"shalele guy dinnan kamar yana da aure..."

"me yasa kika ce haka?"

"ki yarda dani yana da aure, ki duba kiga yanayin nutsuwarsa, he's very calm and gentle......."

"wai dan Allah Malika meyasa kike son sai kin daga min hankali? Bari na kira Gabriel"

Wayarta ta ɗauka ta kira Gabriel yana dauka ta fara fada kamar yana ganinta "Gabriel i don't want to hear stories, tunda jimawa na ce maka ka binciko min if samz is married or not but up to now ka gagara..."

"sorry ma, zan binciko in the next 2 days i promise you"

"ina jiranka..."

Cikin kwanaki biyu ya binciko mata kuma ya sanar da ita cewa samz fa yana da aure hatta sunan matar da address din gidan da komai sai da ya sanar da ita nan hankalinta ya tashi ta rasa inda zata saka kanta daga karshe suka yanke shawarar su zo har gida su shaƙa min kuɗi ko wai zan bar musu mijina sai dai fa duk da kaca kacan da nayi musu hakan bai sa sun sauka daga doron turbar da suke kai ba.
***
Shirin tafiya Lagos muke yi sakamakon wani aiki da aka tura samz wanda zai je ya yi wata ɗaya, da dafarko tsokanata yayi yace min "baby zanje Lagos zanyi 1 month zaki zauna anan ko Kano zaki koma sai na dawo kema sai ki dawo?" kwance nake a jikinsa amma sai da na tashi saboda firgici na ɓata rai sannan na turo baki,

"ni kai zan bi bazan iya zama ni ɗaya ba...."

"no baby, ba zan tafi dake ba...."

"saboda me?" na bukata ina zaro ido,

"saboda rowa kike yimin yanzu.... Idan munje ma rowa zaki tayi min"

Idanuwana na rufe da tafukan hannuna ina murmushi,

"wai kai baka gajiya ne?"

"uhmmm" ya bani amsa yana bude fuskata,

"to kayi hakuri na daina..."

"baby ke raguwa ce.... Kina cewa you want to get pregnant, da haka zaki samu?"

Kallonsa nayi fuskata har tayi narai narai saboda ya fama min inda yake yimin kaikayi,

"yawwa ranar ina yi maka magana but you didn't take it serious....... Nace ko za muje hospital muga Dr?"

"for what?"

"kaga har yanzu ban kara samun ciki ba"

Hannayena ya kama duka biyun ya rike bayan ya matso jikina sosai,

"baby.... Sau nawa zan fada miki ki kwantar da hankalinki akan maganar cikin nan, karki tayar da hankalinki ai ba muyi jimawar da zamu shiga damuwa akan bamu samu ciki ba......"

"boo ba zaka gane ba, kaga yanzu kowa zai dawo da hankali kaina tunda wancan cikin ya lalace kuma yanzu an dan kwana biyu"

"karki damu baby, komai lokaci ne kuma Allah ke yi, zaki samu ciki a lokacin da Allah ya so kuma a lokacin da hakan shine alkhairi agaremu"

Murmushi nayi na rungumeshi araina ina jin sanyi da nutsuwa suna shigata.

A cikin satin muka shirya muka tafi birnin iko Ikon Allah, duk da aiki yaje yi amma hakan bai sa mun kasa fita yawon shakatawa da bude ido ba, har tausayi yake bani saboda yadda baya samun hutu yadda ya kamata kullum sassafe yake fita bazai dawo ba sai magriba kuma yana dawowa zamu fita, nidai wuni nake a ɗakin da muka sauka cikin wani katafaren hotel hadadde kuma ƙayatacce amma bana leka ko ƙofa idan ya fita har sai ya dawo haka kuma tunda muka zo ruwa ake yi kamar da bakin ƙwarya kullum sai anyi ga uban sanyi duk da asauran wurare yanayin rani ne wato dry season,

Wuni nake Ina kallo da chaten dan bani da wani abun yi ni ba aikin gida ba ba girki ba har gajiya nake da bacci shiyasa muke fita da daddare kuma wannan dalilin ne ina jin yasa na fara hada ƙiba daga zuwanmu, ko ƙawalli da ta ganni lokacin 2 weeks da zuwanmu cemin tayi,

"ƙawalli anya kuwa ba ciki gareki ba naga kumatunki sun hau....."

Kumatun nawa na shafa kafin nace "ƙawalli ciki kuma? Babu wani ciki"

"to Allah ya kawo ƴan biyu amma nidai ban yarda ba"

Duk yadda na fada mata kin yarda tayi sai hakura nayi na barta amma ni na san ba ciki bane dan yanzu haka ma period nake tun shekaran jiya na fara shima sai nasa yan guntun ƙunƙunin yake tun jiya saboda ina period ina jinsa shiyasa lokacin da ina da ciki yake ta shan bidirinsa babu abinda yake kawo masa cikas,

Batun Felicia da shalele kuwa duk ciki babu wacce ta hakura ko tayi sanyi, yanda suka sako samz a gaba tamkar zasu ci babu abin yana mutukar yimin zafi amma bana nuna masa duk da yasan nima a bangaren kishi babu dama ne,

Yau bayan ya dawo daga aiki saloon ya rakani, ganin ana huda kunne da hanci awurin yace wai idan zan amince zai so a huda min kunne a kara min guda uku akan ɗayan da nake dashi dan yaga awurin wata jiya awurin aikin su kuma yayi masa kyau but yana tausayi na kar a huhhuda min jiki ni kuwa tunda ya riga ya fada naji sai nayi zan samu nutsuwa tunda har ya fada da bakinsa yana so to gara inyi masa ya gani awurina akan ya gani a wajen wata yayi sha'awa, daurewa nayi aka huda min harda hanci aka saka min barima kuma ba yabon kai ba duk sunyi masifar yimin kyau, muna komawa ya gama waya da mommy ya ajiye wayar kusa dani ya shiga bathroom kawai naga text ya shigo kuma ta ɗan saman da yake bata gama tafiya sleep ba da haske sai kawai naga anturo 'I received your alert, tnx alot darling Allah ya kara arziki" wannan shine kadai abinda na iya gani kenan naji raina ya baci zuciyata ta harzuka.....



*_Ummi Shatu_*👌🏻
[1/5, 12:43] Maman K: {54}


*Ina kuke manyan mata ƴan ƙwalisa ma'abota son gyara da kece raini, maza ku garzayo ku nemi maman Maryam domin samun lafiyayyu kuma haɗaɗɗun Lagos lace wanda zaku iya samun ɗinkakku da kuma sabbi a ledarsu, kaya iya zaɓinki, gefe ɗaya muna da GHT product, zaku samu,*

~MAI DA TSOHUWA YARINYA

~FEMALE CARE

~REODEO

~VIGOR MAX

~ LONGZIT

~B CLEAR

*DUK ZAKU SAMU WADANNAN KAYA CIKIN SAUKI DA RAHUSA MAZA KU NEMI MAMAN MARYAM AKAN WANNAN NO 07080222187, SIYAN NA GARI MAIDA KUƊI GIDA.....*


~~~Ganin yadda nayi kutin kutin da fuska na hade rai ta san lallai dagaske dai ba yarda zanyi in kama zancen da tazo min dashi yasa ta tashi ta fita tana sake jaddada min ita mai ƙaunata ce shiyasa ta fada min kuma da ace bata kaunata da ba zata kawo min wannan rahoton ba, nidai gaba daya tasa jikina yayi sanyi na gagara yin aikace aikace na cikin nutsuwa kamar yadda na faro, gashi zuciyata ta kasa yarda da abinda tazo min dashi sannan ta kasa karyata hakan saboda maza a wannan zamanin ba abin yarda bane kuma ba a shaidarsu dan su suka fi komai saurin canjawa, gashi ita wannan maganar ba wai magana ce da zan dauketa inje in kaiwa wani acikin compound din namu dan bincike ko wani abu mai kama da haka ba shiyasa na rasa ya zan bullowa lamarin dan zuciyata tayi mutukar sosuwa.

Da ƙyar dai na iya daurewa na ƙarasa ayyukana na samu wuri na zauna inata sake sake da tunane tunane har lokacin da ya dawo, babu yabo babu fallasa nayi masa sannu da zuwa bayan yayi hugging ɗina, ban fasa yi masa komai da na saba ba amma fa komai ina yine cikin rashin walwala,

"baby whats wrong with you?" yace dani yana rike hannuna bayan na kammala gabatar masa da abinci,

"babu komai..." na bashi amsa ba tare da na kalleshi ba,

"baby kiyi hakuri idan akan rashin baki samu ciki bane, insha Allah ubangiji Allah bazai barmuhaka ba zai bamu masu albarka Kinji...."

"uhmmm" nace masa daga haka ban sake cewa komai ba, kuma duk yadda yaso na saki jiki na ware kamar yadda muka saba hakan bai samu ba dan gaba daya zuciyata a kuntace take bana cikin farin ciki kwata kwata,

Tsawon kwanaki biyu muka ɗauka ina wannan halayyar wadda ni akaran kaina bawai dan ina so nake yiba A'a kawai bacin ran da nake cikine yasa bana iya sakin jiki dashi kamar yadda na saba, bani kadai abun yake damu ba kuma har dashi sai dai shi yafi danganta hakan da rashin samun cikin da banyi ba duk a tunaninsa shine ya sakani cikin wannan damuwar. Yau bayan ya dawo daga aiki turkeni yayi akan lallai sai na fada masa abinda yake faruwa da har na canja haka,

"baby bakya boye min komai me yasa yanzu zaki fara boye min? Ki fada min damuwarki dan bana son wannan fushin naki wallahi yana cutar dani da yawa...."

"nifa babu komai...."

"maganar babu komai ma ai bata taso ba, just tell me your mind..... Koda hakan bazai yimin dadi ba" jin abinda yace ya sakani yin dan jim kaɗan kafin nayi gyaran murya nace,

"yanzu rayuwa ta sauya duk abinda mutum yake aikatawa ko kuma yake yi a boye mutane suna sani dan yanzu kiwon mutum ake yi ba na dabba ba..... Kuma bama wannan ba ko cututtukan zamani da ake cewa ana dauka ta hanyar neman matan banza dagaske ne ba karya ba dan dayawa sun dauka wasu ma hakan shi ya zama ajalinsu.... " ina kaiwa nan na tashi na wuce cikin bedroom na barshi yana nazarin maganganu na dan kwata kwata bai fahimce su ba,

" wannan wacce irin magana ce? Me take son cewa ne? Matan banza? Cututtukan zamani? Yanzu kiwon mutum ake ba na dabba ba? Duk me ya kawo wadannan maganganun?" kawai da yaga bazai gane komai ba ai tashi yayi ya biyoni cikin ɗakin inda nake zaune da wayata a hannu ina duba massages din da naga yaya Abdurahman ya tura cikin group din yan gidanmu,

" baby.... Tashi ina so muyi magana please "

" bayan wacce muka yi?"

Na fada batare da na kalleshi ba kuma ban daina abinda nake yiba,

"yes, saboda ni ban gane abinda kike magana a kai ba, kince wai matan banza kince cututtukan zamani blah blah blah, wait what exactly are you talking about?"

"abinda dai kunnenka yaji shine abinda na fada....."

"shut up..... Ki fada min abinda kike son faɗa straight forward....." ya fada cikin zafi irin zafin da bai taba yimin magana da shi ba sai yau babu shiri na tashi zaune na ajiye wayar idanuwana suna taruwa da kwalla jikina a mutukar sanyaye,

"ba Kaine ba lokacin da bana nan kake kawo yanmata ba gidan nan....."

"ni? Da bakya nan nake kawo yanmata?" ya tambayeni yana nuna kansa bacin rai yana sake bayyana yana lullube fuskarsa,

"waye ya fada miki wannan maganar?"

"ni dai haka aka fada min kuma wadda ya fada ya tabbatar min da cewa ya ganka"

Bai kara magana ba naga ya juya ya fita, nan na tashi nabishi amma batare da ya sani ba yana zuwa falo ya dauki wayar shi ya soma kiran no Kabir bugu biyu ya dauka, magana na jiyo shi yana yi cikin bacin rai,

"Kabir ka jawa matarka kunne kar ta sake zuwa cikin gida na..... Tazo ta kawowa mata ta maganganun ƙarya ta haddasa mana misunderstanding, kuma na san babu wadda yazo ya fadawa matata wannan maganar sai ita saboda ranar da yaran suka zo itace ta ganmu, yanmata guda biyu sun zo gidana da na fito na gansu all i thought was wurin matata suka zo amma suka ce dama purposely saboda ni suka zo anan bakin kofa muka gama duk maganar da zamuyi suka tafi na dawo ciki amma matarka tazo tana fadawa matata wai da bata nan ina kawo mata.... Menene haka? " jin yadda yake magana ni kaina na san ransa ya baci shima Kabir haka kuma hakuri kawai yake bashi yana cewa zai dauki mataki akai, lokacin da ya katse wayar matsawa

Please Login or Register in order to submit comment