Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

assignment din sannan muka koma maraja'ar karatun da muke yi tare,

Na rigashi yin bacci amma koda na farka cikin dare sai naga idanuwanshi biyu kuma da alama tunani yake yi,

"sweet wai meke faruwa?"

"nothing baby, me kika gani?"

"kamar kana cikin damuwa"

"babu komai baby, kawai na kasa bacci ne"

Duk yadda na dage akan sai ya sanar dani damuwarsa kin fada min yayi yace babu komai bacci ya kasa daga karshe dole haka na hakura muka dan taba hira har zuwa lokacin da baccin ya sake daukata.

Tsawon kwanaki ya dauka yana cikin tunani da damuwa wadda ni na kasa gane kanta saboda Felicia ta matsa masa da maganar wai ciki haka itama mommy wadda labarin tuni har yaje kunnenta dan takanas madam comfort taje tayi mata albishir ai mommy tamkar zata yi tsalle akan kaya saboda murna, yanzu kam sun samo hanyar da zasu tirsasa shi ya auri Felicia cikin sauki ko yana so ko baya so kuwa, duk sun bi sun jagula masa lissafi kullum sai Felicia ta kirashi duk da baya dauka hakanne yasa ta sanar da mommynshi wai baya daukar wayarta, cikin fushi mommy ta kirashi lokacin yana office,

"mommy...."

"Samuel wai dan Allah Meyasa kake son sai ka kashe ni lokacin mutuwata baiyi ba?"

"mommy me kuma na yi yanzu?"

"Meyasa baka daukar wayar Felicia? Yarinyar da gashi nan itace zata zama uwar yayanka, abinda muke ta nema sai yanzu gashi nan za asamu daga gareta"

"mommy wai maganar me kike yi ne nifa ban gane ba"

"maganar da nake yi shine lokacin da ka kusanci Felicia she was ovulating dan haka zata iya yuyuwa ta samu ciki dan haka ka shirya karbar baby sannan dole ka aureta domin itace zata haifa maka yara, ita kuma waccar mayyar ya zama wajibi ka rabu da ita know this and know peace.... " daga haka ta katse wayar tana huci cike da takaici, sake shiga damuwa yayi wanda ranar ko gida bai dawo da wuri ba saboda baya son ya dawo in ganshi in gane, lokacin da na kirashi dan naga lokacin dawowarshi har ya wuce cemin yayi wai meeting suke yi, ranar bashi ya dawo ba sai bayan sallar ishah lokacin nayi jiransa har na gaji amma koda ya dawo haka na tareshi da murna da kulawa, yaƙe yake ta faman yi wanda yafi dariya ciwo,

"sweet yau ka jima a office ko tunawa dani baka yi ko...." na fada cikin shagwaba,

"am sorry baby, ni ai ban isa kin tunawa dake ba, har nayi aiki na gama kina nan cikin zuciyata, ko kin manta ne you are my heart beat....." ya karasa faɗa yana jan hancina, dariya muka yi gaba daya na rakashi ciki yayi dukkan abinda ya saba na daga al'adarsa.

Tun daga lokacin ya shiga damuwa sai yayi kamar zai fada min sai ya fasa sau wurin uku yana cemin yana son muyi magana muhimmiya amma sai ya fasa daga karshe yaki faɗa yau ma abinda yayi min kenan amma sai na share shikuma duk tsoron da yake yi kar ya fada min in bijire sannan baya son kin fada min daga baya zance yazo ya fito shima inki yi masa uzuri dan yaga abin nasu Felicia babu sauƙi,

Yau kasancewar weekend ne kuma yana gida sakani yayi a gaba yanata kallona yayin da nake zaune gabansa ina goge masa kananun kayansa da na wanke jiya, duk dagowar da zanyi sai inga ni yake kallo sai yayi min murmushi nima inyi masa a haka har wurin sau hudu,

"sweet wai me kake kallo ne?" na fada ina harararsa cikin wasa,

"baby ke nake kallo mana...."

Ban kai ga bashi amsa ba muka jiyo karar wayarshi daga cikin bedroom, tashi yayi ya wuce ciki ni kuma na cigaba da abinda nake yi, yana zuwa yaga Felicia ce nan ya dauka amma ransa a bace,

"samz kaki bari muyi magana ta fahimta ko? To duk abinda yafaru karka yi blaming dina kace nayi blackmailing dinka....."

"Felicia wai meye burin ki akaina? Wacce manufa kike son cimmawa akaina?"

"babu wata manufa kawai just accept the fact cewa Ina dauke da cikin ka kuma very soon zan sanar da matarka..."

"na yarda, I accept it, ni dama ai neman cikin nake ban samu ba, dama ina bukatar yara, shikenan babu damuwa kije kiyi rainon cikin bayan kin haihu ki kawo min ina so...." Kitt yaji ta kashe wayar nan ya dawo falo inda nake duk jikinsa a sanyaye,

"baby ina so muyi magana please..."

"ehemmm ina jinka sweet"

"dan Allah baby duk abinda kika ji akaina karki rabu dani karki guje min..."

Kashe iron din nayi na zuba masa ido don gaskiya na fara gajiya da wannan abun da yake yimin kuma yaki sanar dani ko menene,

"sweet gaskiya yau ka fada min koma menene idan ba haka ba inyi maka daru, kullum sai kace zaka fada min abu amma sai ka gagara, wai me yake faruwa ne?"

Ganin yanda nayi dagaske kuma na tsare shi da ido alamar yau fa sai naji komai yasa shi yin ajiyar zuciya ya Kalleni na tsawon wasu mintuna sannan naji yace,

" baby ta yuyu fa matsalar rashin samun cikin nan daga gareni ne..... "

" to kuma shine menene sweet? Duk yadda Allah ya tsara mana daidai ne, idan muna son yara zamu iya daukowa awurin yan uwa.... Ni indai wannan shine damuwarka to ka daina damuwa, kamar yadda kace indaina damuwa in barwa Allah to kaima ka daina damuwa ka barwa Allah sannan ni ina ganin yakamata mu sake zuwa muga Dr akan wannan maganar sai kuma muci gaba da addu'a har zuwa lokacin da Allah zai amsa rokonmu "

Matsowa naga yayi jikina ya rungume ni yana shafa kaina kuma tun daga lokacin naga kamar damuwar tasa tayi sauki, washe gari muka tafi hospital kamar yadda muka saba zuwa muga Dr lokaci zuwa lokaci nan ya sake tabbatar mana da cewa lafiyar mu ƙalau gaba daya kuma zamu iya samun rabo a kowanne lokaci, haka muka dawo gida cike da kwarin gwiwa.

Duk yadda su madam comfort suka rinka bibiyarsa da sharri suna son lallai sai ciki ya tabbata daga karshe dole hakura suka yi saboda cikin dai bai tabbata ba cikin bakin ciki da bacin rai suka sanar da mommy cewa ciki bai shiga ba nan mommy ta kirashi tana masifa tana cewa to sai ya zuba ruwa akasa ya sha gashi nan cikin da ake zaton Felicia ta samu ashe bai shiga ba, wani ihu ya saka yana tsalle ai da gudu na fito daga cikin kitchen ina son ganin me ke faruwa ina fitowa ya daukeni ya soma juyawa dani yana dagani sama yana dariya, tambayarsa nake tayi amma yaki fada min menene daga karshe yaje ya fada damu kan kujera yana dariya, tun daga wannan lokacin muka rabu da wannan damuwa wadda dama ni ban san da ita ba nan yabi ya goge gaba daya layin Felicia muka ci gaba da rayuwar mu cikin farin ciki, a yanzu har na kusa kammala karatu na kuma ina yin business dina kadan kadan har na soma bunkasa.

A kwana a tashi har na kammala karatu na saura karbo certificate kawai wanda da taimako kuma da jajircewar mijina na samu na kammala, ina gamawa kamar yadda ya tsara ya soma shirye shiryen budemin makeken restaurant batare da sanina ba saboda ni na tafi Kano ma kawalli ta haihu ta haifi yaro namiji kuma da yake na jima banje ba shiyasa ya barni in dan kwana biyu inyi zumunci in kakkai ziyara duk inda ya dace shiyasa sai da nayi sati uku sannan na dawo cike da kewar yan gida sai dai ta wuri daya nake jin dadi nake farin ciki itama anty sun kusa dawowa Abuja domin mijin nata ya gama aikin da yaje yi a cross river to murnar da nake ta yi ta kusa ta dawo in samu wurin zuwa, hararata yayi lokacin da na fada masa,

"idan antyn ta dawo haka zaki je ki tare a gidanta ko yaya?"

"ehh mana, ai har weekend zan rinka zuwa mata.."

"sai mu tafi tare"

Dariya ya bani dan na fuskanci maganar tawa bata samu wurin zama ba awurinsa,na dawo da kwana biyar mommy ta zo kuma wannan karon ita kadai tazo babu dan rakiya dama kuma ta sanar dashi cewar zata zo nima kuma ya fada min, har acikin raina banji bakin cikin zuwanta ba duk da na san ba lallai mu rabu lafiya ba amma sai na nuna masa ina maraba kuma ina murna da zuwan nata,

Lokacin da ta karaso yana office ni kuma na gama girki kenan ina karasa shirya shi akan table, jin doorbell na kara da sauri naje na bude nan naga itace,

"sannu da zuwa mommy" na fada ina kokarin karbar jakar hannunta, kaucewa tayi tana hararata sannan cikin bala'i naji tace,

"don't mama me, am not your mama... Munafuka ai na san bakya farin ciki da zuwa na...." daga haka ta wuce ciki ta barni tsaye wani abu yana kai kawo acikin raina............



*_Ummi Shatu_*👌🏻
[1/16, 14:50] Maman K: 64


*Ina kuke manyan mata ƴan ƙwalisa ma'abota son gyara da kece raini, maza ku garzayo ku nemi maman Maryam domin samun lafiyayyu kuma haɗaɗɗun Lagos lace wanda zaku iya samun ɗinkakku da kuma sabbi a ledarsu, kaya iya zaɓinki, gefe ɗaya muna da GHT product, zaku samu*,

~MAI DA TSOHUWA YARINYA

~FEMALE CARE

~REODEO

~VIGOR MAX

~ LONGZIT

~B CLEAR

*DUK ZAKU SAMU WADANNAN KAYA CIKIN SAUKI DA RAHUSA MAZA KU NEMI MAMAN MARYAM AKAN WANNAN NO 07080222187, SIYAN NA GARI MAIDA KUƊI GIDA.....*


~~~Na jima a tsaye ina nazari daga karshe na maida kofar na rufe na wuce kitchen na debo flates da cups na bita cikin falon inda take zaune tana karewa ko ina kallo dake cikin falon,

"sannu da zuwa mommy" na fada a karo na biyu tare da tsugunnawa domin gaida ita duk da taki amsawa sai faman faɗa take yi,

"An bi an tsafe min yaro an juyar masa da tunani baya iya tuna iyayen sa da yan uwansa, gaba daya yazo ya tare anan sai abinda aka ce masa yake yi duk da an gagara haifa masa yara....."

Shiru nayi nidai ban tanka ba kuma ban tashi ba domin samz yana da wani matsayi da girma acikin zuciyata wadda hakan bazai taba barina in mayarwa da mahaifiyarsa ba duk abinda zata fada min kuwa, yanda idan mahaifiyata zata fada min duk abinda taso kuma in danne bazan yi tunanin mayar mata ba haka nake ji acikin raina zan danne duk abinda mahaifiyarsa zata fada min batare da na mayar mata ba duk da nasan idan mahaifiyata ce ba zata taba fada min abinda zai zama tashin hankali ko bacin rai ba to amma itama duk da bata sona kuma bata kaunata zata ci albarkacin danta wannan kimar tasa dole ta shafeta, ba zan taba yin kuskuren wulakantata ba insha Allah koda kuwa ita din zata cigaba da wulakantani,

"mommy ga abinci nan idan akwai wani abu da kike bukata sai kiyi magana...."

"munafukar banza munafukar wofi wallahi ko kin so ko kin ki ko kina tsafi da bakin kare sai na rabaki da ɗana..."

Ina jin ta amma ban ko juyo ba bayan na tashi, bedroom na wuce na iske ya nata kirana a waya nan na dauka na nemi wuri na zauna duk da kalamanta sun bata min rai amma sai na hadiye cikin farin ciki da soyayya na dauki wayar tasa,

" hey boo... "

" baby ina kika shiga ne?"

"sorry naje na taro mommy ne"

"ta karaso?"

"ehh tana falo zata ci abinci"

"baby hope babu wani problem?"

"babu problem din komai sweet..... Allah ya dawo min da kai lafiya"

"idan na dawo me zaki bani?" ya fada cikin shagwaba saboda yasan am off,

"soyayya"

"to shikenan baby, sai na dawo"

"a dawo lafiya" na fada ina kissing dinshi ta cikin wayar, shima kissing dina yayi kafin ya katse wayar. Gani nayi bai dace in zo cikin daki in zauna ba ita kuma in barta afalo nan na sake tashi na fita tana zaune tana kokarin zuba abincin nan na samu wuri na zauna idanuwana suna kan tv,

"ban taba ganin masifaffiyar mayyar yarinya ba irin wannan..... Yanda kika kama min kurwar yaro kika rike Insha Allah sai kin sake shi ko kina so ko bakya so, dangin matsafa mayu....."

Raina idan yayi dubu sai da naji ya fadi saboda zagin da take yimin ya fara tsallakawa har kan iyayena amma dai ban bari nayi hawaye ko bacin raina ya fitoba bare har ta gane hakan ya bata min rai ko ya taba zuciyata a haka ya dawo ya same mu tana cigaba da zagina kamar yadda ta saba, shi dai sai da ya nuna bacin ransa,

Fuskar sa a raunane muka shiga bedroom dinmu bacin rai karara kan fuskarsa,

"baby dan Allah kiyi hakuri da halin mommy...."

Hannunsa na kama na rike cikin sanyin murya nace,

"bana son inji kana bani hakuri akan abinda yazama dole inyi sweet..... Mommy komai lalacewa dai matsayin mahaifiya take a gareni, yadda zanyi hakuri da Annie haka zanyi hakuri da ita dan haka kama daina bani hakuri dan Allah..... Tashi kayi wanka"

Kwanciya yayi akan cinyata yana fada min "nagode baby, Allah ya saka miki da alkhairi, Allah yayi miki albarka"

"uhmmmmm wannan kalma taka ta karshe ita nafi so nafi kaunar ji daga gareka...."

"Allah yayi miki albarka baby, Allah ya baki aljannah"

"amin ya Allah tare dakai sweet..."

Sai da ya tabbatar da banida sauran damuwa sannan ya shiga wankan, bayan ya fito ya shirya muka fita falo tare inda mommy ke zaune, abinci na kawo masa yana ci suna hira nidai da wayo da dabara na sulale na basu wuri na koma bedroom ina shiga naga wayata anata kirana koda na duba bakuwar no na gani, da sallama na dauka,

"wa'alaikumussalam warahmatullah Maimunatu widat...."

Tsam nayi da raina ina kokarin tuno inda na san wannan muryar,

"Maimunatu Hashim ke magana..." ai ina ji naji jikina yafara rawa zuciyata tana bugawa, menene kuma alakata dashi yanzu da zai kirani a daidai wannan lokaci?, meyake nema awurina?

"Maimunatu dan Allah kiyi magana mana inji muryarki....."

"kai menene haka? Karka sake kirana ni matar aure ce...." daga haka na katse wayar na wuce na koma falo bayan na ajiyeta kan bedside drawer, duk da bana jin dadin zaman falon amma yafi min zaman cikin bedroom din ni daya saboda banma saba zama ni kadai ba matsawar yana nan,

Sai da muka raba dare sosai a falo wadda daga karshe ni gajiya nayi na wuce ciki na barsu, ina zuwa na samu miss calls rututu wanda duk na Hashim ne, tsaki na ja banbi ta kai ba dan a zahiri ban san me yake nema daga gareni ba kuma, shirin bacci na nayi cikin farar rigar bacci mai shegen kyawu marar nauyi na shafa turare na kwanta lamo ina jiransa, wayata na jawo na tura masa massage kamar haka _sweet zanyi bacci sai ka shigo, i love you_ ai ko mintuna biyu ba ayiba sai ga reply ya turo min _please baby kar kiyi bacci ki barni mana am coming_, murmushi nayi ban sake tura masa komai ba na saka wayar a silent babu jimawa bacci ya dauke ni ban san ma lokacin da ya shigo ba, zama yayi gefena ya riko hannuna,

"baby.... Shine kika yi bacci kika barni?"

Cikin bacci najishi ganin baccin nawa yayi nisa yasa shima yayi shirin bacci yazo ya kwanta, wayata yaga tana blinking kasancewar a silent take ganin no ce sai ya dauka amma sai yaji shiru anki ayi magana, kashe wayar yayi gaba daya ya kwanta a bayana ya rungumeni,

Tunda mommy tazo zama yaki yimin dadi dan komai idonta akai banda masifa da zagin kare dangi da take yimin kusan kullum haka zata sakani a gaba ta karemin tanadi ga gorin bana haihuwa duk da abin baya yimin ciwo amma wani lokacin bana jin dadi danma dai na taba samun cikin hakanne idan na tuna yake dan faranta min raina,

Ban taba fada masa irin zaman da muke yi ba saboda idanuwansa suna gane masa idan yana nan kuma akan haka yake yin laifi a wurinta saboda yana fada mata abubuwan da take yimin basa yi masa dadi kuma basu dace ba, kwananta uku amma tabi duk ta gundiri kowa,

Yanda Hashim ya sakoni a gaba da kira sai da naji kamar in sanar da mijina abinda ke faruwa saboda gudun matsala amma sai na ja bakina nayi shiru ban fada masa ba, muna zaune yau dashi bayan ya dawo daga aiki Hashim ya kafa kirana shi a lallai so yake sai yayi magana dani amma naki dauka shikuma bai tambayeni waye ba hakan ya jawo hankalin mommy kanmu,

"waye yake kiran matarka a waya? Wannan kadai ya isa ya tabbatar maka da cewa akwai abinda yarinyar nan take boye maka....."

"mommy......"

"dalla yimin shiru ka rufe min baki lusari, asarrarren banza asarrarren wofi, banda kai shashasha ne sannan ta gama da kai kana ji kana gani ana kiran ta a waya taki ta dauka amma shine ba zaka tuhume ta ba kaji waye ke kiran ta, idan har babu zamba cikin aminci acikin wannan lamarin meyasa baza ta dauki wayar ba? "

Ban jira naji karshen tirka tirkar tasu ba na tashi na bar falon nan taci gaba da fadar duk abinda ta san zai sakawa samz shakku da zargi tsakaninmu,

" ko tantama bana yi wannan yarinyar cin amanar ka take yi, dama kuma mata irin wadannan wadanda basa haihuwa sunfi sauran mata amfani da irin wannan damar wurin cin amanar mazajensu tunda ba ciki zasu dauka ba...."

"Haba mommy wai dan Allah wannan wanne irin magana kike yi? Nidai am quite sure matata bazata taɓa cin amanata ba...."

"dama ai na san ba zaka yarda ba tunda baka cikin hayyacinka..." bai iya cigaba da saurarenta ba ya biyoni ciki inda nake zaune ina zubar da hawaye, duk yadda naso in danne amma na kasa saboda cin zarafin na mommy yayi yawa,

Tsugunnawa yayi a gabana ya rike hannuna," am sorry baby.... Please stop crying "

" sweet wai me na yiwa mommy da ta tsaneni? Me nayi mata da bata kaunata? Menene laifina?"

"baby ki daina fadar haka, ni ina son ki kuma bazan daina sonki ba har karshen rayuwata sannan i trust you 100%"

Haka yaci gaba da rarrashina har na daina kukan, sakamakon wannan kukan da nayi shikenan na soma dan zazzabi da ciwon kai amma sai na boye masa ban bari ya sani ba har sai da aka kwana biyu lokacin ya dan fara yawa,

Shi da kansa ya fahimci bana jin dadi shiyasa yace in zauna in huta zai yi girkin tunda bana jin dadi, a falo na hikimce bayan na lallaba nayi wanka nasa atamfa dark blue Sai kamshi nake, sai da ya tambayeni wai me zai dafa mana nace jallop saboda dan zazzabin malaria dinnan da nake yi duk bakina babu taste yadda ya kamta,

Ina nan zaune ina kallo naji door bell na ƙara alamar mommy ta dawo dan tun sassafe ta fita, shine yaje ya bude mata nan ta shigo tana kallon sa sama da kasa ganin kamar daga kitchen ya fito,

"kai Samuel me kake yi haka?"

"mommy girki nake yi...."

"yanzu Samuel saboda tsabar baka cikin hayyacinka kai ne kake yi mata girki? Ka fita ka nemo sannan kuma ka dafa mata dan rashin tausayi? Ita yar gidan uban waye? Haka taga uban ta yana yiwa uwarta a gida? yarinya ta mayar da kai bawanta...."

"widat...... Wannan fa?"

Gaba daya juyawa muka yi dan ganin mai maganar wadda ina kyautata zaton kusan tare suka shigo da mommy kuma komai a kunnenta akayi,

"Anty..." na fada cikin mamakin ganinta kuma bama ni kadai ba shi kansa yayi mamakin ganinta,

"widat wai me yake faruwa ne?"

"anty sannu da zuwa, mommynsu ce...." na bata amsa idanuwana na taruwa da kwalla,

"to me yake faruwa?"

"babu komai anty" ya fada cikin sauri,

"ban gane babu komai ba, babu komai amma shine nazo na tarar da hayaniya?"

"kwarai kuwa dole ki ji hayaniya tunda wannan yarinyar ba yar arziki bace.... Bata da tausayi kuma bata da imani"

"mommy stop it please...." ya fada cikin damuwa,

"A'a ka barta ta fadi duk abinda ke ranta Muhammad, sai yanzu na fahimci irin zaman da widat keyi tare da ku wanda ta boye bata sanar damu ba da tuni munyiwa tufkar hanci.... Amma dan Allah mommy wanne laifi yarinyar nan tayi miki da har kika sakota a gaba? "

" babu laifin da tayi min sai na auren ɗana without my consent.... Kuma aurensu ba zai taba albarka ba tunda ban saka albarka ba,sannan ta mayar min da yaro tamkar bawanta sai juya shi take yi son ranta,to wallahi tallahi sai na kawo karshen zamanta atare dashi... "

" wannan shine kadai laifinta a gareki? To kiyi hakuri Insha Allah daga yau zata bar miki danki har abada inyaso sai ki aura masa duk wacce tayi miki kuma kike so.... "

Nidai in banda kuka babu abinda nake yi jin musayar yawun dasu anty suke yi ita da mommy shikuma sai kokarin bawa anty hakuri yake amma ina bata saurare shi ba saboda itama ta gama hawa dokin zuciya kuma ta fusata, bedroom ta jani ta sakani hada kayana, ina kuka ina hadawa shi kuwa har ciki ya biyo mu yana bawa anty hakuri amma bata kulashi ba ita kuma mommy tana falo tana cigaba da fadar bakaken maganganu, mayafina na dauka bayan na gama hada kayana anty ta kama hannuna muka fita yayin da shikuma yake biye damu yana kokarin riko hannuna..........



_*Ummi Shatu*_👌🏻

[1/17, 15:36] Maman K: 65

*Ina kuke manyan mata ƴan ƙwalisa ma'abota son gyara da kece raini, maza ku garzayo ku nemi maman Maryam domin samun lafiyayyu kuma haɗaɗɗun Lagos lace wanda zaku iya samun ɗinkakku da kuma sabbi a ledarsu, kaya iya zaɓinki, gefe ɗaya muna da GHT product, zaku samu,*

~MAI DA TSOHUWA YARINYA

~FEMALE CARE

~REODEO

~VIGOR MAX

~ LONGZIT

~B CLEAR

*DUK ZAKU SAMU WADANNAN KAYA CIKIN SAUKI DA RAHUSA MAZA KU NEMI MAMAN MARYAM AKAN WANNAN NO 07080222187, SIYAN NA GARI MAIDA KUƊI GIDA.....*

~~~Bani da zabi wanda ya wuce inbi anty tunda abin ya kwaɓe iya kwaɓewa yayinda shi kuma yake biye da mu yana bawa anty hakuri,

"Anty dan Allah kar ki biyewa mommy kiyi hakuri kar ki tafi min da mata, i love her and she loves me too...."

Anty ko uffan banji tace masa ba har muka sauka muka fita daga cikin gidan sa'armu daya ma babu wanda ya ga fitar tamu, motar anty dake ajiye kofar gidan muka shiga har lokacin yana tsaye yana magiya amma anty bata tanka masa ba ni dai kasa ma ko kallonsa nayi saboda zuciyata a karye take mutuka,

Yanayin yanda naga anty ta figi motarta kadai ya isa tabbatar min da cewa ranta ya kai mutuka wurin baci nidai in banda kuka babu abinda nake yi har muka karasa gidan anty har lokacin ba tace min ko kanzil ba, muna zuwa ta nuna min ɗakin Islam domin yanzu gidan anyi masa canjin fasali gaba daya dan itama mijinta ya sake samun babban matsayi a fanninsu na lauyoyi tun suna calabar lokacin ma har walima suka yi acan,

Ɗakin Islam din na shiga har lokacin kuka nake wanda ban san na meye ba amma nafi danganta shi da kukan bakin cikin rabuwata dashi, sai da nayi me isata sannan nayi shiru na tashi zaune ina bin dakin Islam din da kallo wadda ya sha sabon fenti da wallpaper pink da purple ga furnitures dinta suma haka yanzu haka ss2 take,

"girman ɗan mutum ba wuya...." na fada cikin raina tare da shiga cikin bathroom nayi alwala nazo nayi salla, na jima ina addu'a kafin na fita, iya Aslam da Sultan na gani wadanda ke zaune suna cin abinci, nima joining din su nayi na zauna na zuba abincin yawuna yana tsinkewa tun kafin in fara ci saboda dambun couscous ne sai tashin kamshi yake, sai da na gama na koshi sannan Anty ta fito ita da fawas,

Wurinta na koma inda take zaune cikin falo tana kokarin kama channel a tv,

"Barka da fitowa anty..."

"widat, kin ci abinci?"

"ehh naci anty"

"masha Allah, naji dadin jin hakan, ki kwantar da hankalinki kar ki daga hankalinki kuma kar ki sakawa zuciyarki damuwa ba wai rabaki da mijinki zanyi ba amma ya zama dole in ƙwato miki yancinki awurin mahaifiyarsa.... Yadda take son danta kema fa

Please Login or Register in order to submit comment