Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

halin ruwa ba banda haka anty Amina mace mai kirki mai haba haba da mutane amma ita kuma sai bata ɗauko halinta ba tayo nata halin daban na wulakanci da shan kamshi dan inba wulakanci ba mutum ya zo gidanku ai ka girmama shi ka karramashi gami da mutunta shi, ban wani damuba dan dama ni na saba da irin wannan wulakancin na dangin miji sai dai abinda ya bani mamaki kuma ya daure min kai shine ita kuma me nayi mata ko menene damuwarta dani?

Ganin bani da wannan amsar ya sani tashi na fita na koma wurin su, mamakine ya so sumar dani ganin Munira ta sake tana hira da mijina sosai harda su kyakyata dariya ban bi ta kasu ba dan ko babu komai yar uwarshi ce na maida hankali na kan tuwon da Anty Amina ta ɗumama min ta kawo min tuwon semo miyar busasshiyar kuɓewa harda yajin daddawa da man shanu ai nan na zauna na kwashi abina son raina ina jin hirar da suke yi. Sai dai abinda ya so ɗaure min kai guda ɗayane irin shisshigewar da naga yarinyar tana yiwa samz wanda nidai ban san dalili ba amma zaƙewar naga kamar taso tayi yawa sai dai ban saniba ko dama can haka suke yi duk lokacin da yazo gidan ma'ana ko haka suke zama su sake suyita shan hira shiyasa naketa fafutukar ganin na kori shaidan daga cikin zuciyata batare da yayi tasiri ba amma sai na ji na gagara hakan abinka da kishi nan ya fara rufe min duk wata kofa dake cikin zuciyata,kame bakina nayi na kama kaina wuri guda dan bana ko tanka musu bare in sa musu baki cikin abinda suke tattaunawa wanda su ya shafa atoh su ya shafa mana tunda maganar karatun ita Munira din suke yi, koda aka gabatar masa da abinci yace bazai ci tuwo ba nan ta tada fi'ili da fallin wai zata dafa masa noodles, ina jin kunyar gwasaleta yaji shiyasa bai hana ba yace toh nan ta shiga cikin kitchen kanta yana rawa jim kaɗan aka fito,

"uncle Samz da ƙwai zaka ci ko da geisha?"

"Any one..." ya bata amsa a takaice nan ta sake komawa nidai duk ina zaune ina kallon ikon Allah amma ban tanka ba,

Lokacin da ta kawo noodles ɗin kirana yayi wai in zo inci ai kam take naga yarinya ta ɗaure fuska tamau ta wani ɓata rai kamar wadda aka aikowa da saƙon mutuwa, murmushi nayi nace masa "ai ko kai kaga na sake cin wani abincin yanzu sai ka bincikeni tunda kaga uban tuwon da na haƙa" dariya suka yi gaba ɗaya banda Munira wadda har lokacin bata saki fuskarta ba nidai ban saurareta ba lokacin salla nayi na mike na gabatar, bayan na idar yace ya kamata mu tafi kamar kuwa dama ya san na gaji da zaman gida kawai nake son tafiya washe gari kuma agidanmu nake son inje in wuni dama zuwan shi ne ya hanani zuwa. Tun a hanya ya fuskanci akwai matsala saboda yadda nayi gumm da bakina bana amsa shi haka kuma naƙi nayi koda murmushi bare dariya, kayan da anty Amina ta bani kuwa Humra da turaren wuta tunda na cillasu kujerar baya ban sake bi ko ta kansu ba haka kuma sama sama nake amsa masa daga uhmmm sai uhmmm uhmmm na ɗauke kaina na juya ina kallon window, hannuna naji ya riko yana yimin magana,

"Baby..... Kina fushi dani ne?"

Shiru nayi masa ban amsa ba, kai a takaice dai har muka je gida ban saki fuska ba sannan muna shiga na kwaso masa abincin da na girka da rana dan kawai ina so yaki ci in tada daru,

"Haba baby a gabanki fa naci abinci...."

Cikin bacin rai na katse shi dan dama a wuya nake kuma kiris nake jira,

"to akan me zaka ci abincin acan tunda ka san ka tafi kabar wani anan wanda na dafa maka.... Oh wato ni gani ban iya girki ba abincina babu daɗi shiyasa zaka je ka zauna ka saki fuska kana dariya kana kwasar girkin wata...."

"baby...... Why are you like this? Come here, wannan cikin yafara saki masifa bayan da ba haka kike ba"

"babu wani masifa da ciki ya sakani maganar gaskiya ne, yarinyar da ko magana bata yimin ba tunda naje gidansu take daure fuska tana hararata ashe saboda kai take ta bina da kallon banza and the same girl da kaje ka saka a gaba kana yiwa dariya harda tayi maka abinci Kaci ni ka dawo ka ki cin nawa.... "

Kallona naga ya zauna yana yi kafin daga bisani ya mika min hannu alamar inje gareshi amma sai na wani dauke kai naki zuwa na tsaye masa aka ina jira inga zai ci ko ba zai ci ba, ni bakin cikina yadda ya zauna yaita wani yi mata dariya harda cin abincinta,

"am very sorry baby, zan ci anjima kinga yanzu am full....."

"Nifa ban yarda ba sai Kaci abincin nan..." daga haka na wuce cikin bedroom dina ina hawayen sakarci saboda ni kaina na san baida wani laifi akan abinda nake tuhumarsa dashi.........

*Garin dadi littafin kudi ne ga mai bukatar cigaban labarin sai ya tura 500 ta 0774712835 Aisha Ibrahim Access Bank sai a tura evidence of payment ta wannan no 07044644433 ko a tura katin waya da shaidar biya wannan no 07044644433*

*_Ummi Shatu_*👌🏻

[1/5, 12:43] Maman K: {46}


*Ina kuke manyan mata ƴan ƙwalisa ma'abota son gyara da kece raini, maza ku garzayo ku nemi maman Maryam domin samun lafiyayyu kuma haɗaɗɗun Lagos lace wanda zaku iya samun ɗinkakku da kuma sabbi a ledarsu, kaya iya zaɓinki, gefe ɗaya muna da GHT product, zaku samu,*

~MAI DA TSOHUWA YARINYA

~FEMALE CARE

~REODEO

~VIGOR MAX

~ LONGZIT

~B CLEAR

*DUK ZAKU SAMU WADANNAN KAYA CIKIN SAUKI DA RAHUSA MAZA KU NEMI MAMAN MARYAM AKAN WANNAN NO 07080222187, SIYAN NA GARI MAIDA KUƊI GIDA.....*


~~~Ina shiga cikin bedroom din ko zama banyi ba naji shigowarsa shima alamar biyoni yayi, ina kokarin zama ya rikoni tare da zaunar dani cikin jikinsa,

"am very sorry my love..... Kiyi hakuri zan ci, zo muje in ci a gabanki ki gani....."

Shiru nayi ina sauraren ban bakin da yake yimin tare da share min hawayena,

"ban san cewa ranki zai baci ba amma kiyi hakuri bazan sake ba...."

Duk da cewa a ƙoshe yake amma haka yaketa cakular abincin bayan mun koma falo ya samu nasarar shawo kaina, ɗauke abincin nayi na saka cikin fridge tunda na riga da na huce na koma normal kamar babu wani abu da ya faru,

Tun dab da lokacin kwanciyata na fara jin cikina da marata suna ciwo amma sai na daure ban fada masa ba, wanka nayi na kwanta ina jin ciwon yana ƙaruwa ahaka na samu bacci ya daukeni bayan nagama azkhar din kwanciya bacci, cikin dare ciwo ya sake tashi yace muje zuwa yayinda bacci kuma ya ƙaurace min dan azaba, zaune na tashi na zauna na zubawa sarautar Allah ido shikuma yana kwance yana ta baccinsa wanda na san bawai ya wani jima da ɗaukarsa bane, na jima zaune kafin na samu ya dan lafa min na sake komawa bacci zuwa asubah na sake tashi,

Bathroom na shiga domin kama ruwa nan naga ashe ma bleeding nake ban sani ba ga wani irin murdawa da marata keyi abin ba sauki, ganin jinin da nayine ya firgita ni shiyasa na koma na tashe shi. Sai lokacin ya san halin da nake ciki cikin firgici ya riƙeni yana cewa,

"Baby yi sauri muje hospital.... Bana son wani abu ya sameki ko cikin dake jikinki....."

Kai na ɗaga masa ina cije lips ɗina duka biyu a haka dai ya taimaka min na cire rigar baccin jikina na saka doguwar riga da hijabi muka yi salla sannan muka tafi,

Muna zuwa likita ya shiga dubani nan ya tabbatarwa da samz cikin jikina ya lalace sai dai ni bai fada min ba dan kada hankalina ya tashi saboda ko yanzun ma cikin tashin hankali nake, faɗin irin baƙar azabar da na sha kuwa ɓata lokaci ne kuma har lokacin babu wanda ya sani daga ni sai shi sai zuwa azahar bayan cikin ya gama faduwa sannan samz ya kira yaya Abdul hakim ya sanar dashi nan shima yaje gida ya fada musu shiyasa kafin kace me asibiti ya cika da ƴan gidanmu nikam ina can ina bacci banma san wacce wainar ake toyawa ba. Zuwa la'asar na tashi daga baccin wahalar da na sha nan naga Anty, mama,Bishra, anty salaha ganin na farka duk suka yo kaina suna yimin sannu, tea anty ta hada min sannan ta zubo min abinci, da ido naketa neman samz amma da dukkan alamu baya cikin ɗakin dan da ace yana nan ai da na ganshi may be yaje gida ko kuma yana waje, nan dai duk suka shiga jajanta min ɓarin da nayi, ni dai a ɓoye na keta kuka na ban bari wani ya gani ba, zuwa magriba su Annie suka ƙaraso ita da Abba da yaya Abdul hakim wanda shine ya kawo su, basu jima da zuwa ba samz ya dawo dauke da fruits cikin leda da drinks harda balangu, kaya dai kaca kaca na ciye ciye haka ya kawo, bamu samu kebewa dashi ba saboda mutane har sai bayan ishah lokacin da duk ƴan gidanmu suka tafi sai iya Bishra kadai da aka bar min wanda zamu kwana tare

Misalin ƙarfe 9 ya shigo ya zauna kusa dani yana yimin sannu, ai kamar dama jira nake nan na fara kuka shikuma ya shiga rarrashi na yana bani baki,

"yanzu duk yadda muka ƙwallafa rai akan cikin nan ashe ba zai ma zo duniya ba...." na fada cikin kuka, hannuwana ya rike cikin nasa yana sake rarrashi na da kalamai masu dadi,

"babu komai baby haka Allah ya so kuma insha Allah zai sake bamu wani mai albarka.... Ki kwantar da hankalinki Kinji...."

Kai na ɗaga masa ina sauraren kalaman da yake yimin na kwantar da hankali da samar da nutsuwa cikin zuciya, muna nan tare dashi har wurin 10 sai da yaga na ware na sake sosai sannan yayi mana saida safe ya tafi,

Kwana na biyu a asibitin kafin aka bamu sallama, kai tsaye gidanmu aka wuce dani dan su anty sunce sai an kula dani sosai, a ranar shikuma ya koma Abuja saboda aiki, kamar yadda yake ta cewa in kwantar da hankali na kar in saka damuwa acikin raina kwantar da hankalin nawa nayi shiyasa nayi fes dani ban wani lalace ba.

A ɓangaren mommy kuwa bayan sun gama ƙulle ƙullensu da shirye shiryensu ita da aminiyar tata daga ƙarshe taji labari mai daɗi daga bakin samz dan shine da bakinsa ya sanar mata da wai na samu miscarriage lokacin da abun ya faru kuma yakara da cemata ina asibiti ma lokacin ko sallamata ba ayi ba, ko da wasa bata nuna masa tayi farin ciki ko bakin ciki ba dama kuma ya riga da yasan duk wani lamari wanda ya shafeni to bata damu dashi ba shiyasa abin bai wani dameshi ko bashi mamaki ba amma acan ƙasan zuciyarta taji dadin labarin da yaje mata dashi dan dama bata da wani buri wanda ya wuce taga wannan cikin nawa ya lalace dan tace ba zata taba hada jini damu ba shiyasa babu ɓata lokaci ta sanarwa da aminiyar tata wadda bafa hakura suka yiba a'a sun sake ɗaura ɗamarar cigaba da yaƙar zaman lafiyarmu dashi.

Bayan tafiyar shi kullum muna tare a waya tun daga safe har zuwa lokacin kwanciya bacci shi kansa ya yaba da irin yadda yaga na saki raina kuma na kwantar da hankalina nayi Kumari ban bari na lalace ba, satinshi biyu da tafiya yazo kuma tun kafin yazo yake cewa wai a gida zai sameni?

"Gidanmu....." na bashi amsa dan na fahimci inda zancen nasa yake son zuwa,

"Gidanmu nida ke?"

"gidan iyayena...."

Dariya yayi ya kwantar da murya yace "baby ba zamu hadu agidanmu ba inyaso after na tafi sai ki koma"

"lallai ma sannunka..... A'a gaskiya"

"to shikenan sai nazo"

"tom, me zan dafa maka?"

"ni ke kadai nake bukata, you are the real meal...."


"yen yen yen....."


"yen yen yen yen...." shima ya fada cikin kwaikwayon muryata, dariya muka yi gaba daya kafin muka yi sallama na ajiye wayar,

Girki nayi masa da kaina farfesun kifi sai sakwara da miyar dage dage kuma da wuri yazo dan lokacin da yazo ba afi 12 ba,

Farar shadda ya saka da hula dara baƙa, nikam ban yi wata kwalliya ba dan yadda naga take takensa tun kafin yazo yasa na shiga taitayina, powder kadai na shafa sai kwalli sai ko dan lipstick da na goga ta wuri ɗaya nayi kuskure da na daddage nasha turare kamar anyi ɓarinsa bayan kuma na san yana daya daga cikin abubuwan dake jan ra'ayinsa, baƙar doguwar riga na saka na yafa dan siririn mayafinta na fita na sameshi falon saukar baƙi yana waya da daddynsu, ganin shigowa ta ya mika min hannu na maƙale kafada naƙi zuwa murmushi yayi ganin na zauna can nesa dashi,

"Ehh daddy ina Kano yanzu haka naje duba jikin Maimunatu kasan tun last tafiyan da nayi ban dawo ba sai yanzu.... Gata...."

"Gashi daddy zai yi magana dake...."

Dama na san ba zai barni nesa dashi ba kuma da biyu yacewa daddy bari ya bani wayar wato dai dole sai nazo kusa dashi, ai kuwa ina zuwa ya zaunar ni kusa dashi ya riƙeni, gaisawa muka yi da daddy ya sake duba ni dama kuma muna gaisawa a wayata lokaci zuwa lokaci, bayan munyi sallama ina kokarin tashi ya riƙeni yana kokarin saka idanuwansa cikin nawa amma naki,a gurguje yayi sallama da daddy sannan ya ɗago kaina,

"baby yakike?"

"am fine dear..."

"bakya missing dina? Nifa i have been missing you a lot"

"Same here...." na fada ina kissing ɗinsa a kumatunsa guda ɗaya,

"to yaushe zaki dawo? Ko zamu tafi tare?"

"a'a ba tare zamu tafi ba"

"sai yaushe?"

"nan da 2 weeks"

"Haba baby.... 2 weeks yayi yawa"

"zo Kaci abinci inyaso sai muyi maganar tafiyar daga baya"

Yana manne dani yaci abinci duk ya hanani sakat ya hanani motsawa nan da can, a takaice dai a gidan ya wuni, duk sai da muka bi sashen su mama da Annie na kai shi ya gaida su daya bayan daya, koda muka fito cemin yayi wai to in rakashi gidanmu last time yayi mantuwa dan Allah in rakashi ya ɗauko, dariya nayi na sake maƙale hannunshi dake cikin nawa,

"wai dan Allah menene matsalarka? Idan kayi hakuri ma ai na kusa dawowa"

"ba zaki raka ni ba?"

"ka bari idan ka tashi tafiya sai ka biya ka dauka daga can sai ka wuce"

"baby wayonki yayi yawa" ya fada yana lakuce min hanci, "kaima haka" dariya yayi kawai bai sake maganar ba, zuwa yamma yayi mana sallama ya tafi kuma a ranar da daddare Abba yake cewa su mama ai yadace nima in tattara in koma tunda dai lafiya nake babu wata matsala amma sai mama tace adai kara barina in warware in kara koda sati biyu ne inyaso sai in tafi,

Ai ina fada masa abinda gida suka ce ya fara murna wai da ya zaci baza a barni in dawo yanzu ba sai nayi irin wata biyun nan zuwa biyar dariya nayi nace haba sai kace ana hauka. Lokacin da na fara lissafin tafiya ziyara na kakkaiwa yan uwa da abokan arziki kafin in koma dan idan na tafi ban san lokacin dawowata ba sai Allah shiyasa wannan karon kayana na kwasa rankatakaf kaɗan na bari, naje gidan ƙawalli na wuni Irfan ɗinta har yayi wayo sosai ya girma kai kace yayi wata uku, ƙunshi nayi da kitso da duk wani gyara wanda na san ya dace inyi, washe gari na koma, lokacin da naje bai taso daga office ba amma ya kusa, duk da bana nan amma gidan babu wani datti mai yawa da alama yana kula da gidan kuma yana gyarawa.

Tun kafin ya dawo na shiga kitchen na dora mana girki inata dariyar zumundinsa ni kadai dan sai murna yake yana cewa wai shi yau ango yake, noodles na dafa mana jallop nasa kifi da vegetables dan ita kadai ce mai sauƙin dafawa,bayan na gama na sake gyara jikina na caba kwalliya nasa wani leshi fited gown ɗaya daga cikin wanda na ɗinka zuwa na Kano a sunan ƙawalli,

Ƙarfe 6 ya shigo, da gudu na ƙarasa na rungumeshi tare da daleshi, rungumeni shima yayi yana sinsinar jikina cikin farin ciki da tsantsar soyayya,

"welcome back my baby love...."

Ya yaba da kwalliyata sosai dan sai farin ciki yake yana saka min albarka, kai gaskiya munyi missing juna ba kaɗan ba, haka dai muka kwana cikin farin ciki bayan mun raba dare muna shan soyayya kamar waɗanda suka shekara basa tare, cike da farin ciki da ƙaunar juna muka yi bacci nidai saboda tsabar gajiyar da na kwasa washe gari ko tashi banyi ba ina bacci ya shirya ya tafi office bai tasheni ba, sai 10 sannan na tashi wannan dinma yunwa ce ta tadani, mamaki ne ya kama ni lokacin da na kunna wayata naga time wai har 10, kamar dama jirana yake in kunna wayar sai ga kiransa, da murnata na daga kiran ina kokarin sauka daga kan gado,

"Ina kwana...." na fada cikin shagwaba,

"morning my love.... Kin tashi"

"na tashi yanzu, shine ka tafi baka tasheni na ganka ba"

"am very sorry, bari in kiraki video call sai ki ganni"

Brush naje nayi sannan na wuce kitchen muna yin vedio call din ina kallonsa yana kallona, kwai kadai na soya sai tea da na hada nasha, sai bayan da na kammala sannan muka yi sallama saboda shima zai shiga meeting, muna yin sallama na yunkura zan tashi dan inje inyi wanka na soma jin kukan mage da na kare duk lokaci guda........


*Garin dadi littafin kudi ne ga mai bukatar cigaban labarin sai ya tura 500 ta 0774712835 Aisha Ibrahim Access Bank sai a tura evidence of payment ta wannan no 07044644433 ko a tura katin waya da shaidar biya wannan no 07044644433*


*_Ummi Shatu_*👌🏻
[1/5, 12:43] Maman K: {47}

*Ina kuke manyan mata ƴan ƙwalisa ma'abota son gyara da kece raini, maza ku garzayo ku nemi maman Maryam domin samun lafiyayyu kuma haɗaɗɗun Lagos lace wanda zaku iya samun ɗinkakku da kuma sabbi a ledarsu, kaya iya zaɓinki, gefe ɗaya muna da GHT product, zaku samu,*

~MAI DA TSOHUWA YARINYA

~FEMALE CARE

~REODEO

~VIGOR MAX

~ LONGZIT

~B CLEAR

*DUK ZAKU SAMU WADANNAN KAYA CIKIN SAUKI DA RAHUSA MAZA KU NEMI MAMAN MARYAM AKAN WANNAN NO 07080222187, SIYAN NA GARI MAIDA KUƊI GIDA.....*


~~~Bazan iya kwatanta yanayin tsoro da firgici da na shiga a lokacin ba domin gaba daya komai ya kwance min haka na nemi addu'a a bakina ko daya na rasa, jikina kuwa tamkar mazari dan tsabar rawa da kakkarwa, tamkar zan suma dan tsabar tsorata to abune da baka san dashi ba kuma baka kwana dashi ba sannan na tabbata a gidan babu kare kuma babu mage to idan da akwai ma tayaya zasu shigo har cikin part dinmu? Koda na bude idanuwana baƙake na gansu sidik gwanin ban tsoro kowanne ya bude baki babu kyan gani sai lokacin na samu addu'a tazo bakina na fara ƙwallawa da ƙarfi cikin rawar murya da rawar jiki, da rarrafe da jan jiki na samu na shige cikin bedroom har lokacin cikin tsananin tashin hankali nake, ina shiga na sakawa ƙofar key wayata ma ashe can na barota,

Da wannan tashin hankalin na wuni ranar ina cikin bedroom kunshe na kasa koda bude kofar ne bare in iya fita falo duk da ina jiyo karar wayata anata kirana tun jimawa, har cikin bedroom ɗin ma tsoronsa nake dan ko toilet na kasa shiga saboda gani nake kamar zan gansu aciki gashi sai gizo suke yimin acikin idanuwana, addu'a naketa yi ina karawa amma har lokacin a firgice nake, zuwa yamma ya dawo ko time din tashinsa bai bari yayi ba ya taho saboda yanata kirana amma wayar nata ringing ba a dauka shiyasa ya taho da wuri dan ya dubani yaga ko lafiya,

Ina bude ƙofar bedroom din bayan yayi knocking na tabbatar shine na fada jikinsa ina kuka daga ni sai rigar bacci wadda ko wanka ban samu damar yiba haka na wuni cikin tsoro da fargaba,

"baby.... What's happening??"

"Wallahi wani baƙin kare ne da bakar mage acikin gidan nan, muna gama waya da kai na gansu kamar zasu cinyeni...."

"what? Acikin gidan nan?"

Tare muka koma falo ina makalkale dashi muka je ya shiga duba ko ina har su kitchen amma babu alamar komai aciki daga karshe ya tisani da tambayar wai anya ba mafarki nayi ba ko kuma kawai firgita nayi ba?

"baby are you sure ba mafarki bane?"

"wallahi sweet ba mafarki bane da idona na gansu"

"ok am sorry"

Har bathroom sai da ya rakani sannan nayi wanka na fito ga uwar yunwa dake ciciyata, sama sama na shirya ban bata lokaci wurin kwalliya ba muka wuce kitchen na dora mana abinci. Tun daga wannan rana na kasa sakewa acikin gidan kullum cikin fargaba nake saboda zan iya ganinsu kowanne lokaci kamar yadda suke yimin gizo ba dare ba rana amma sunfi yimin a lokacin da baya nan, idan yana nan koda weekend bana ganin komai kuma bana jin kukan komai amma da zarar baya nan shikenan nikuma zaman lafiyata ya kare sai gane gane da jin koke koken mage da haushin kare gaba daya duk sai zaman gidan naji ya isheni ya fita a kaina kamar in tattara in gudu haka nake ji duk nabi nayi fiki fiki dani shi da kansa sai ya fara tausaya min yace bari mu kira anty mu sanar mata, da kansa ya kirata ranar bayan ya dawo daga aiki da daddare bani wayar yayi na zayyane mata komai da nake ji kuma nake gani nan anty tace to in dage da addu'a sannan in kiyaye duka azkhar haka kuma in yawaita karatun alqur'ani mai girma da saurarensa daga karshe tace mu samo ƴayan habbatussauda in rinka zubawa a garwashi ina turara gidan dashi kamar yadda ake saka turaren wuta,

Bani ba shi kansa gidan ya fita masa akai saboda gaba daya yaga a takure nake wannan dalilin yasa ya fara neman gida babu shiri dan yace gara mu tashi mu canja gida sai dai baya son nesa da wurin aiki yafi son inda yake dan kurkusa da wurin aikinsa, cikin sa'a ranar yazo min da labarin an samu wani estate kamar wannan wanda muke ciki kuma wani dan office din su ne ma ya sama masa saboda shima aciki yake tare da matarsa wadda basu wuce 4 months da aure ba wai itama kuma daga Kano ya aurota amma shi asalinsa dan zaria ne,

Cikin lokaci kanakani yabiya kudin gida yayi komai muka fara harhada kayanmu nidai farin ciki ai kamar zanyi tsalle akan kaya saboda na fishi matsuwa da mubar gidan daman,

Compound ne mai kyau upstairs kuma kowanne akwai mutane aciki ma'aikata, mu dai muna sama kuma opposite muke da wannan ɗan office din su samz mai suna Kabir kamar yadda naji yana faɗa sai dai ban taɓa ganinsa ba har zuwa lokacin da muka tare, bayan mun tare da kwana biyu sai gasu sun zo mana bayan sallar magriba, muna zaune muna kallon series a tashar zee world suka yi mana knocking, dogon hijabina na saka saboda daga ni sai riga armless iya cibiya da dan wando rigar iya cinyata shikuma boxer ne kadai a jikinsa ma ko riga babu, ciki ya shiga ya sako farar jallabiya sannan ya wuce ya bude ƙofar, ganin Kabir yasa shi fadada fara'arsa tare da mika masa hannu bayan yabawa Samha hanya alamar ta shiga ciki,

Ina zaune kan kujera na nutsu ina kallo dan bana son kallon ya wuceni naji sallamarta, fuska ta da fara'a na amsa mata duk da ban santa ba kuma banma taba ganinta ba sai yau, tasha turare babu laifi dan sai da yafara yimin sallama kafin ita tayi,

Harga Allah tun daga shigarta da yanayinya nasha jinin jikina dan tamkar yar duniya haka na ganta saboda yanzu rayuwa ta canja duk yadda mutum yake yanayinsa kadai zai fassara maka wanene shi, kuma ko ada

Please Login or Register in order to submit comment