Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

nayi domin in bashi hakuri tunda already kunnuwa na sunji dukkan abinda ya faru amma sam sai bai saurareni ba yi yayi ma kamar bai san dani awurinba lallai wannan shine illar ka yanke hukunci ba tare da bincike ba kuma wannan shine mafi girman kuskuren da mata muke yi duk yadda muji ya kai da sonki da lallabaki idan kika sake kika koya masa irin wannan fushin to sai kin sha wahala domin zaki dade baki samo kansa ba,

"Boo..... Am very sorry please" haka naketa maimaitawa amma bai kula ni ba har muka ji karar door bell shi yatashi yaje ya bude ni ina zaune na takure wuri daya kamar wata marainiya, Samha ce sunkwi sunkwi ta shigo munafuka kamar wata ta Allah ashe itama bude mata wuta mijinta yayi bayan samz ya sanar dashi duk abinda ya faru daga karshe yace tazo ta warware abinda ta kulla idan ba haka ba gobe a gidansu zata kwana dama kuma ya gaji da halinta da rashin kintsinta aure ko shekara ba ayiba amma duk tabi ta isheshi shine ta taho babu shiri dan ta wanke samz,

"na zo in baku hakuri ne akan abinda na fada, wallahi ban fada dan in haddasa muku fitina ba, kawai na fada ne dan....."

"dan me? Kin ga lokacin da na shigo dasu cikin gidan nan?" girgiza kai tayi kafin tace "A'a"

"to kuma shine zaki zo kice mata yanmata nake kawowa?"

"kayi hakuri wallahi tuntuben harshe ne...."

"what eva dai this will be the last time da zaki shigo gidana.... Kar na sake ganinki cikin gidan nan" daga haka ya juya ya wuce cikin bedroom ya bar mu nan nida ita,

"widat kiyi hakuri ban zaci abin zai kai haka ba...."

"to ai yayi miki kyau reporter, aku mai bakin magana, Allah ya isa tsakanina dake...." daga haka nace ta fita ta bar min gidana ban barta ta tsara komai ba tana fita na mayar da kofa na rufe na koma ciki.

Tun daga wannan lokacin ya sauya min wanda sai da naji gaba daya zaman gidan ya fita a kaina, bai daina bani kulawar da ya saba bani ba amma sai dai baya sakar min fuska, idan ya kirani kawai tambaya ta zai yi ya nake Ina bukatar wani abu daga haka sai ya kashe, idan nayi masa abinci zai ci amma babu irin wannan wasan da rahar kamar yadda muka saba,baya wani hira dani yanzu kamar da, ko wurin bacci ina can kuryar gado shi kuma yana farko wannan abu yana damuna, kullum sai nayi kukan bakin cikin wannan abun gashi banga fuska ba bare inyi masa magiya, haka kuma duk yadda naso in ja ra'ayinsa in hilaceshi har ya manta da fushin da yake yi abun ya faskara,

Yau tsawon kwana biyu kenan amma ji nake kamar mun shekara cikin wannan ukubar, kafin na tashi ma har ya shirya ya fita kasancewar na makara, ina shirin sauka daga kan gadon naga ya kirani normal call ba video call ba kamar yadda muka saba, dauka nayi amma sai na gagara cewa komai sakamakon ƙwallar da ta cika min ido haka kuma kuka yazo ya tsaya min shiyasa nasan ko yaya na bude baki da niyyar magana kukane zai ci karfina,

"hello.... Are you sleeping?" naji ya fada,

"no" na bashi amsa,

"ok how are you doing?"

"fine" na fada a takaice hawaye na bin kumatuna,

"ok, do you need something?"

"no"

"ok" daga haka ya katse wayar nan na zauna nafara kuka babu kakkautawa har tsawon wani lokaci, gaskiya ba zan iya cigaba da wannan zaman yana nuna min halin ko in kula ba gara kawai in san inda dare yayi min, kamar yadda na saba babu abinda banyi masa ba tun daga kan girki, haɗa ruwan wanka da dukkan abinda na san na saba yi masa kafin ya dawo, zama nayi cikin tunani to ko in kira yaya Abdul Hakeem in sanar dashi duk abinda yake faruwa may be shi zai iya gyara kuskuren da nayi duk da dai na san zan sha faɗa kamar babu gobe,

Ina ta wannan tunane tunanen har ya dawo nan naje na karbo bag ɗinshi da bakar ledar da yazo mana da ita, cikin bedroom na kai sannan na zo na hada masa fruits salad na kai masa inda yake zaune yana cin abinci,

Har lokacin kwanciya bacci babu wata hira ko tattaunawa da ta gudana a tsakaninmu haka naje na kwanta cike da damuwa da bakin ciki shi dai ban san lokacin da ya shigo ba sai farkawa nayi na hangoshi can nesa dani yana baccinsa abinda ya sake yimin ciwo kenan shiyasa asussubar fari na soma shirya kayana cikin babbar jaka gara in koma gida koda hakan na nufin zanje in fuskanci bacin ran da yafi wannan wanda na tafi saboda shi amma gaskiya na ƙosa kuma na gaji da wannan zaman da muke yi dashi na kai da ƙafafu kwata kwata zaman auren ya fita daga kaina kuma na gaji dashi a cikin kwanaki uku kacal, duk da na san iyayena da sauran ƴan uwana baza su yi farin ciki da wannan zuwan nawa ba tunda yaushe ma na dawo? Kuma ma duk ba wannan ba koda zuwanne zuwan farin ciki bada wata matsala ba shi ake doki da zumudin ganinka amma ba irin nawa zuwan ba na matsala da rashin jituwa to sai dai amma kuma ni kaina bani da zabi wanda ya wuce in tarkata nawa inawa in bar masa gidansa in bashi space ta yuyu hakan shine abinda yake bukata a halin yanzu........



*_Ummi Shatu_*👌🏻
[1/5, 12:43] Maman K: {55}



*Ina kuke manyan mata ƴan ƙwalisa ma'abota son gyara da kece raini, maza ku garzayo ku nemi maman Maryam domin samun lafiyayyu kuma haɗaɗɗun Lagos lace wanda zaku iya samun ɗinkakku da kuma sabbi a ledarsu, kaya iya zaɓinki, gefe ɗaya muna da GHT product, zaku samu,*

~MAI DA TSOHUWA YARINYA

~FEMALE CARE

~REODEO

~VIGOR MAX

~ LONGZIT

~B CLEAR

*DUK ZAKU SAMU WADANNAN KAYA CIKIN SAUKI DA RAHUSA MAZA KU NEMI MAMAN MARYAM AKAN WANNAN NO 07080222187, SIYAN NA GARI MAIDA KUƊI GIDA.....*


~~~Ina haɗa kayana ina share hawayen da yake sauka kan kuncina a haka ya shigo ya sameni wanda dawowarsa kenan daga masallaci tun bayan da ya fita sallar asubah, tsayawa yayi yana kallona kafin naji yace,

"wannan kayan fa??"

"Kano zanje..." na bashi amsa ba tare da na kalleshi ba,

"yaushe kika dawo daga Kanon da har zaki sake komawa? Ko wani abu ya faru a gida?"

Dakatawa nayi daga abinda nake yi dama tuni hawaye sun wanke min fuska ga wasu sabbi suna zarya da sintiri bisa kuncina,

"Babu abinda ya faru a gida, kawai naga kamar ka gaji da zama dani ne shiyasa zan bar maka gidan dan wannan kora da halin da kake yimin ya isa haka..... Yau 3 days baka kulani baka yimin magana"

Zama yayi kusa dani yajani jikinsa ya rungume ai kamar jira dama nake take na fashe da kuka,

"baby Kin bata min rai ne da yawa, ta yaya wata zata zo ta fada miki magana akaina and you start misbehaving instead of you to explain everything to me..... Am very sorry ni ban gaji da zama dake ba, shikenan ya wuce, don't go anywhere please..... Kinga idan kika tafi gida relatives dinki zasu iya rabani dake suce ba zaki dawo ba tunda bana kulawa dake ina takura miki, am soo sorry please, forgive me "
Har lokacin ban daina kukan da nake yi ba na shagwaba tabbas abinda ya fada gaskiya ne banyi aiki da hankali ba bare tunani bayan ya bani dukkan dama kowacce iri da zan zauna inyi magana dashi amma maimakon haka sai kishi ya rufe min idanu kawai na hau dokin zuciya naƙi yarda muyi magana ta fahimta kuma na fuskanci hakan shine ya bata masa rai fiye da maganganun da na fada,

"stop crying baby, kiyi hakuri"

Kai na daga masa amma har lokacin kukan nake yi haka yaci gaba da rarrashi na har nayi shiru daga karshe shine ya dauki kayan ya mayar dasu inda na ciro su ya sake dawowa wurina ya kama hannuwana ya rike yana kallona.
***

Tun bayan da suka bar wurin samz suke faman tunanin abin yi ko kuma hanyar da za su bullowa lamarin amma sun gagara samun mafita domin sun jarraba duk wata hanya da dabara wurin ganin ya amshi tayin soyayyar da Shalele tayi masa amma abin ya faskara ko kuma yaci tura,

Idanuwanta jajur take kallon Malika ranta kuma a cunkushe,

"Malika na rasa yadda zanyi..... Baki da wata dabara ne wadda kike ganin idan munbi watakila in samu karbuwa awurinsa?"

"Hmmmm sai yanzu hankalina ya kai kan wata dabara wadda tun afarko ita ya kamata ace mun fara bi kuma ta yuyu da tuni yanzu wani zancen ake yi ba wannan ba Shalele amma sai dai ban san yanda zaki karɓi maganar ba...."

"yaya kuwa zan karbeta matsawar burina zai kai ga cika?"

Gyara zama Malika tayi kafin tayi kasa kasa da murya kamar tana gudun kada wani yajisu,

"Tunda munyi duk iyakar kokarinmu mun kasa shawo kansa mun gwada duk wata dabara tamu amma abun ya faskara to yanzu ina ganin Lokaci yayi da zamu juya tunaninsa, lokaci yayi da zamu mallakeshi ta wata hanyar koda kuwa baya so kuma koda hakan na nufin wata zata rasa shi ke kuma zaki mallakeshi..... "

" am Malika ban fahimceki ba, ban fahimci abinda kike nufi ba.... " Shalele ta bukata cikin rashin fahimta,

" ina nufin zamu je mu hadashi da malamai..... "

Ɗan shiru Shalele tayi kamar wadda take nazarin maganar da ta fada kafin ta dubeta tace,

" amma kina ganin hakan babu matsala? Nifa bana son kauce hanya akan abin duniya, kar kaje ka rasa lahirarka akan duniya "

" Haba Haba, haba Shalele ke kanki kin san ai bazan yi haka ba, tayaya zanje wurin wadanda suke shirka, wannan fa kawai normal malami ne zamu je mu nemi taimako ya taya mu da addu'a kan Allah ya karkato da hankalin wannan bawan Allahn zuwa gareki, ai ko a cikin musulunci sunna ce ta rayuwa ka nemi dan uwanka ya tayaka da addu'a akan wata bukata taka ko wani buri naka, to mu dinma hakan zamuyi.... "
Jin abinda Malika tace sai ta dan yamutsa fuska tayi murmushi tace,

"to shikenan hakane kuma na fahimceki yanzu yaushe kike ganin yadace muje?"

"wa? Ai da zafi zafi ake dukan karfe hajiya, a yanzu ba sai anjima ba zamuje ayi duk abinda yadace"

"kema kin san hajiya ba zata taba barina in fita yanzu ba"

"to ai babu matsala ni ba sai in wakilceki ba? Ni sai inje inyi masa bayanin dukkan damuwarki da bukatarki da kuma abinda muke so ya rokar mana...."

"shikenan hakan yayi, nagode ƙawata, Allah yabar mu tare yabar zumunci"

"amin, ai babu komai kawata kema kin san Kinfi karfin haka awurina kuma zan iya yin komai dan ganin kin samu farin ciki kin samu abinda kike so, yanzu me kike ganin zamu bashi domin sadaka tunda kin san aikin ki babban aikine kawata amma babu matsala kome kika bashi baki fadi ba saboda zaki samu biyan bukata "

Tsamm Shalele tayi ta tsaya tana kallon ta kafin tace" Malika wai yaushe kika san malamai ne da har kike ta rattabo jawabi a kansu haka? "

" wallahi bawai sanin su nayi ba, kin san anty Rabi'a kanwar maman mu wadda ta jima bata haihu dinnan ba to itace fa aka hada ta da shi taje ta bukaci ya taimaka mata da addu'a kuma yana yimata ko shekara ba ayiba ta samu ciki yanzu kinga yaran ta biyar.... Ajere a jere "

" masha Allah, to me zan bashi matsayin sadaka.... "

" ni ina ganin kar muyi approaching dinshi da kudi, mu bashi abinda idan ya gani zai dage ya mayar da hankali yayi mana aiki "

" kamar me kenan? "

" Gold...... A cikin gold dinki ki bada guda daya akai masa "

" kai Malika, gold fa kika ce, so kike hajiya tayi bandata"

"Ranar biyan bukata wallahi rai ba a bakin komai yake ba, ni da ace nice idan har bukatata zata biya to ko rayuwata ce zan iya badawa, haba Shalele ni sai nake ganin kamar baki damu da ki mallaki wannan guy dinba, kamar duk abubuwan da kike fada a kansa karya ne, kamar duk girman son da kike ikirarin kinayi duk wasa ne.... "

" kema kanki kin san ina sonsa kuma ina son in mallakeshi... "

" to idan kuwa hakane sai ki shirya rasa komai dan mallakarsa ciki kuwa har da abubuwan da kika mallaka masu tsada "

" hakane, to yanzu wanne zan baki daga ciki?"

"acikin bangles dinki ki bada koda guda biyu ne mukai masa mu gani"

"ok tom ina zuwa"

Da ga haka ta nufi wurin tangamemiyar wardrobe ɗin ta bayan ta bude ta dauko wani dan karamin box wanda saida ta saka wasu pin kafin ya bude, nan ta ciro awarwaraye daka daka kirar India sai sheki suke da daukar ido, guda shida ne iri daya sai wasu suma guda shidan daban kirar Dubai, guda biyu ta debo da ciki ta mayar akwatin ta rufe ta sakashi cikin ma'adanarshi ta rufe ta dawo wurin Malika wacce ke zaune tana latsa wayar ta,

"kawata gashi..... Wannan ai sunyi ko?"

"ehh to sai dai naje sannan zanji daga gareshi, kin san kamar yadda na fada miki tun farko aikin naki babba ne na san sai anyi yanka an zubar da jinin shanu ko rakuma dan ayi sadaka banda sauran abubuwa, babu damuwa dai kuma na san Insha Allah ba zata gagara ba, amma fa maganar nan ta zama sirri tsakaninmu kawata karki yi gangancin fadawa kowa ciki harda hajiya dan aiki zai iya lalacewa "

" hauka nake zan fadawa hajiya?? Hajiya taji na bada bangles dinnan ai na shiga uku.....Allah dai yasa mu dace "

" Insha Allah, Insha Allah zamu dace kuma zaki ce na fada miki, bari ma ki gani in tashi inje"

"to shikenan nagode kawata, duk yadda ake ciki zamuyi waya"

Tare suka fita ta rakata har harabar gidan wanda yake makeke sannan tangamemen gaske, samarin gidan suna nan sai buga kwallon kwando suke yi tare da abokansu gefe daya kuma wasu suna buga table tennis, ita dai Malika yau ko hajiya bata shiga ta yiwa sallama ba gudun kada hajiyan ta gane. Ita kuwa shalele bayan ta raka Malika shiga cikin su Jalil tayi suka cigaba da buga table tennis domin ta iya sosai kuma ta kware a wannan fannin, wasan da ya kaisu har magriba kafin su shiga cikin gida, koda wasa bata sanar da hajiya abinda ya faru ba duk da kuwa hajiyan nata tambayarta yaushe Malika ta tafi bata yi mata sallama ba? Yadda Malikan ta gargadeta akan ta iya bakinta haka tayi koda wasa bata sanarwa da kowa ba,

Da daddare tana shirin kwanciya bacci taji kiran Malika cikin zakuwa da son jin abinda ke tafiya ta dauki wayar,

"kawata ya ake ciki ne?"

"alhamdulillah, albishirinki..."

"goro...." ta fada cikin shagwaba tana kokarin kwanciya,

"mun gama da matsalar ki Insha Allah domin malam ya bani tabbacin insha Allah wannan guy din zai kiraki da kansa daga nan zuwa gobe, idan kuma har hakan bata faru ba zuwa 1 week malam yace in sake komawa zai sake sabon wani aikin na musamman"

Hamadala shalele tayi kafin ta sake gyara kwanciyar ta cikin tsantsar farin ciki,

"Alhamdulillah.... Kai gaskiya amma naji dadin jin wannan labarin kawata, yanzu kenan in jira call dinsa?"

"Enhem....."

"thank you soo much kawata, Allah yabar zumuncinmu"

"amin kawata, don't mention it"

Sallama suka yi ta katse wayar ai tun daga wannan lokaci ta fara zaman jiran kiran samz amma har karfe 1 na dare shuru daga karshe ma bata san lokacin da bacci ya dauketa ba,

Washe gari tana farkawa da wayarta ta fara dan itace abu na farko da ta fara janyowa ta duba wai ko zata ga miss calls dinsa amma babu ko daya haka ta sauka daga kan gadon duk ranta babu dadi ta shiga bathroom, gaba daya a yan kwanakin wuni take da waya atare da ita tana jiran kiran samz amma ko alamun hakan babu, idan ta kira Malika tayi mata complain sai tace ta kara hakuri kuma kar ta sake ta kirashi ko ta tura masa text malam yace da kansa zai nemeta a haka har kwana bakwai din ta cika nan Malika ta sake dawowa,

"Gaskiya na fara sarewa da lamarin nan Malika.... Anya kuwa kina ganin guy dinnan zan samu kansa?"

"ki kwantar da hankalinki kawata zaki samo kansa very soon kawai dai muci gaba da bin umarnin malam, dama yace idan 7 days tayi bai nemeki ba to in sake komawa kuma yanzun nan zan koma"

"yawwa dan Allah tashi ki koma maza maza, faka faka kawata...."

"akwai bukatar mu sake kai masa wani abu hakan kadai zai sa yayi mana aikin da yadace"

"me kuma zamu sake kai masa Malika?"

"Gold, matsawar kina son burin ki ya cika to fa yazama wajibi ki bude hannuwanki shalele...."

Shiru shalele tayi ta gagara koda motsi bata son ta rasa hanyar mallakar samz haka kuma bata son tayi abinda daga baya zata zo tana cizan yatsa dan idan hajiya ta gane abinda suke kullawa a bayan fage tabbas kashin ta yagama bushewa......



*Sakkwatawa, zamfarawa, mazauna Kebbi kuna ina? Wannan garabasar taku ce kuyi maza maza ku garzayo ku kwashi garabasar kayayyaki cikin farashi mai sauƙi, siyan daya ko sari, dan more wannan garabasar masa ku garzaya ku shiga wannan link domin kasancewa cikin gidan sauki* 👇🏻👇🏻

https://chat.whatsapp.com/E5Q6ce8rZhY25J32dauHRu


_*Ummi Shatu*_👌🏻

[1/5, 12:43] Maman K: {56}


*Ina kuke manyan mata ƴan ƙwalisa ma'abota son gyara da kece raini, maza ku garzayo ku nemi maman Maryam domin samun lafiyayyu kuma haɗaɗɗun Lagos lace wanda zaku iya samun ɗinkakku da kuma sabbi a ledarsu, kaya iya zaɓinki, gefe ɗaya muna da GHT product, zaku samu,*

~MAI DA TSOHUWA YARINYA

~FEMALE CARE

~REODEO

~VIGOR MAX

~ LONGZIT

~B CLEAR

*DUK ZAKU SAMU WADANNAN KAYA CIKIN SAUKI DA RAHUSA MAZA KU NEMI MAMAN MARYAM AKAN WANNAN NO 07080222187, SIYAN NA GARI MAIDA KUƊI GIDA.....*


~~~Rasa yanda zatayi tayi dan gaba daya ta zama confused, ta san duk abinda Malika ta fada gaskiyane idan har tana son samz dagaske sannan tana son ta mallakeshi to ya zama dole ta iya hakurin rasa komai, ya zama wajibi ta shirya salwantar da duk wani abu wanda ta mallaka kamar yadda Malika ta faɗa, to amma gefe ɗaya tana ji acikin zuciyarta kamar bata kyauta ba kuma idan har hajiya ta san wannan labarin to mai rabasu sai Allah sai dai da yake abinda zuciya ke so nan ta yakice wannan tunanin a ranta kawai ta tashi taje ta sake debo bangles wannan karon guda hudu Malika ta karɓa sannan tayi mata sallama ta tafi tana sake jaddada mata cewa ta jira result mai kyau.
***

"Baby kiyi hakuri amma bana son ki sake repeating irin wannan laifin da kika yimin Kinji?" naji ya fada yana kallon fuskata yayin da hannuwana ke cikin nasa, kai na daga masa kuma har lokacin ban daina zubar da hawaye ba,

"ki daina kuka.... Ai ya wuce, mun shirya yanzu...."

Harararsa nayi cikin nuna so da kauna nace "ka bani wahala...."

"am very sorry my love, come here, zo muyi bacci" duk da na san ba baccin bane amma haka na biye masa nan muka fada duniyar ma'aurata wanda kowannenmu ya nuna bajinta karshe wurin samarwa da dan uwansa farin ciki,

Kasancewar zai je office a gurguje na shiga kitchen duk da yana cewa in bari kawai idan yaje office zai yi breakfast amma nace lalalalah nice nan zan hada masa ko yaci ko ya tafi dashi duk wanda yayi masa sai ya zaba aciki,

Ba wani abu mai wahala na yiba saboda lokaci ya tafi bread kadai nayi toasting bayan na soya ƙwai sai na dama custard, lokacin da na dauko kayan na fito daga cikin kitchen har ya fito falo yana kokarin balle botiran gaban rigarshi Kasancewar suit ya saka, ajiye kayan nayi na karasa gabansa ina balle masa gaba daya ya cika falon da kamshinsa,

"kin sa na makara baby" ya fada yana riko waist dina tare da shafa waist bits din dake daure kuguna,

"am very sorry, yanzu zaka tafi ai.... Zo kayi breakfast"

Kamar wani karamin yaro haka nayita cuccusa masa har ya koshi sannan na rakashi ya tafi bayan na sumbaci goshinsa da lips dinsa, ciki na koma ina jin a yanzu bani da wata sauran damuwa kuma. Ko 30 minutes bai fi ba da tafiya ya kirani video call, narke murya nayi na shagwabe nace,

"dama kuwa kamar ka san yanzu nake cewa zan kiraka in tambayi izinin fita...."

"ina zaki je?"

"kasuwa, ina son inje in iyo cefane in zo inyi maka girki"

"bana son ki fita baby, ki dafa min abinda yake available wanda kike bukata kuma babu just text me sai in taho miki dashi"

"ni dai dan Allah A'a, dan Allah ka barni inje in siyo wallahi bazan jima ba yanzu zan dawo"

"baby idan kika fita maza kallonki suke wasu ma tunani zasuyi ko baki da aure su fara sonki"

"wallahi zan saka mask in rufe fuska ta kuma shigar matan aure zanyi"

"ok to ki shirya in gani idan kinyi kyau da yawa you are not going anywhere"

Tashi nayi ina dariya na shirya cikin bakar doguwar riga na saka hijabi dogo sannan na saka face maks amma duk da haka rigima ya tayar da kyar na lallabashi ya yarda ya barni bayan ya kakkafa min dokoki nace ehh duk na yarda, kudin cefanen ya turo min dashi duk da nace masa da akwai amma sai da naga alert dinshi, rufe gidan nayi na fita. Kamar yadda na daukar masa alkawari iya abinda ya kai ni kadai nayi na dawo gida amma fa duk da haka nasha kira a waya sai kace wadda zata ɓata har sai da nace masa gani a gida na dawo sannan ya hakura ya tsagaita min da wannan kiran,

Kitchen na shiga na dora mana girki domin harma naso in makara, couscous da vegetables soup nayi sai fattoush salad A'a na hada gefe daya kuma na hada coconut milk shake, ina cikin aikin ban kai ga karasawa ba ya dawo, da gudu na tafi na tareshi tare da ɗaleshi kamar zamu fadi, rikeni yayi gam yana shakar kamshin da jikina keyi dama sanye nake cikin wata farar riga armless amma na danyi kwalliya harda sarka da dan kunne nasa,

"baby kina wannan kamshin kika fita?"

"A'a boo, dazun nan fa nayi wanka na shafa turaren saboda kai..."

"thank you baby, I love you"

"love you too" Tare muka karasa girkin muka baje a falo muka ci, kamar yadda muka saba maraja'ar karatun da muka saba yi muka yi, wanda kuma bai gama fahimta ba na ƙara masa haske, bayan duk mun kammala na dube shi cikin taushin murya nace,

"sweet nazo da wata bukata amma ban sani ba ko zaka amince"

"baby dan Allah ki kwantar da hankalinki, baki da magana koda yaushe sai maganar ciki, dan Allah ki daina damun kanki Allah yana sane damu bai manta damu ba kuma zai bamu a lokacin da ya dace"

Murmushi nayi saboda jin abin da yace saboda shi duk tunaninshi maganar ciki zanyi kamar yadda na saba ko kuma maganar zuwa ganin Dr sai dai a wannan karon ba haka bane,

"sweet what do you think?"

"baby ai na san duk maganarki bata wuce ta ciki..."

Kumatunsa na ja kafin na bashi amsa da "wannan karon to baka canki daidai ba, ɗazu da na fita kasuwa naga wani abu da ya burgeni shine nace zanyi shawara da kai idan har ka amince sai nima inyi joining...."

Jana jikinsa yayi ya rungume kafin yace "what's it baby?"

"Ɗazu naga wani shago na snacks leemat delicacies, wallahi abun ya burgeni idan zaka barni zanyi joining classes ɗinta har nima in zama expert a wannan fannin...."

Ina wasa da hannunshi dake cikin nawa naji yace,

"baby shine kadai bukatarki?" kai na daga masa,

"indai hakan zai saka ki cikin farin ciki zanyi miki, zan barki kiyi joining classes din"

Rungumeshi nayi kam kam ina kissing dinshi tako ina,

"baby duk murnar ce wannan? Please i need more...."

Dariya nayi na cigaba da sumbatarsa dama na san zai yi wahala yaki amincewa

Please Login or Register in order to submit comment