Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

muka sha wanda ya haddasa mana wannan makarar dan har gari yayi haske tarr,

Bathroom na shiga na yi alwala da ruwan ɗumi sannan na fito lokacin har shi ya idar yana karatun alqur'ani mai tsarki, gefenshi naje nima na tada salla bayan na saka dogon hijabi har ƙasa wanda ke ajiye wurin dama duka kayana ƙawalli da Bishra sun shirya min komai sun saka shi inda ya dace a ajiye sh.

Har nayi sallama bai gama karatun da yake yi ba, zikirin da annabi ya koyar na safiya da marece nima na fara karantawa ina zaune kusa dashi, juyowa yayi ya kalleni nikuma na sunkuyar da kaina,

"Good morning...." na ce dashi kaina a ƙasa,

"morning my baby.... How was your night"

Shiru nayi ban amsa ba sai ma casbaha da na ɗauka zan soma ja, hannun shi naji yasa ya kwantoni gefen jikinshi,

"Baby....... Zan je Kaduna yanzu.... Insha Allah zuwa yamma i will be back to you"

Sai lokacin na ɗaga idona na kalle shi jin abin da ya faɗa,

"me ya faru a Kaduna?"

"mommy bata da lafiya, zan je in dubata"

Duk da ban san mahaifiyarsa ba sannan babu abin da ya taɓa haɗani da ita sai da naji gabana yayi masifar faɗuwa, cikin dauriya tare da ƙarfin hali nace,

"In shirya mu tafi tare?"

"no baby.... Kiyi zamanki zan je ni ɗaya, za muje tare wata rana mu gaisheta"

Ɓata fuska nayi bayan na shagwaɓe zan yi masa shagwaɓar da na saba,

"Sorry baby.... Come here... Yanzu ai inada hanyoyi da yawa na rarrashinki" ya faɗa yana ɗagoni gaba ɗaya zuwa kan jikinsa,

"Ni na haƙura" na faɗa ina ƙoƙarin zamewa,

"no..." yace dani yana kissing ɗin goshina, sakina yayi ya tashi ya shiga toilet, karatun alqur'ani na cigaba da yi ina nan zaune har ya fito daga shi sai short iya cinya shiyasa tunda na kalle shi sau ɗaya ban ƙara ba na mayar da kaina ƙasa duk da yanata yimin magana jifa jifa, fita yayi zuwa ɗayan bedroom ɗin mintuna kaɗan sai gashi ya dawo riƙe da kayanshi, light blue ɗin shadda da hula, sakawa yayi sannan na tashi da zummar zuwa kitchen dan in dafa masa ko ruwan zafi ne ya sha tea, hannuna ya riƙo yana fesa turaren dake kan mirror ɗina,

"ina zaki je?"

"Zan duba ko da akwai abin da zan baka a matsayin breakfast"

"no, ba zan ci komai ba, is too early ai"

"ko tea kasha to" na sake faɗa ina kallon fuskarsa,

"no, sai naje Kaduna insha Allah, ki kwanta kiyi bacci"


"Allah ya kai ka lafiya ya dawo dakai lafiya, ka gaida mommy ka dubata, Allah ya bata lafiya, agaida su daddy da kowa da kowa"

"Duk zasu ji"

Wayarshi ya ɗauka sai wallet ɗin shi muka fita tare yana riƙe dani, kissing juna muka yi sannan ya tafi nikuma na mayar da gidana na rufe na koma ciki, gado na hau na sake kwanciya sai kuma naji duk shirun babu daɗi da babu motsinsa, wayata na kunna na kira shi,

"Baby.... Ki kwanta kiyi bacci kafin na dawo"

"ni na manta in tambaye ka.... Daren jiya kuwa kayi bacci?"

Dariya naji yayi kafin ya bani amsa, "nayi mana"

"Are you serious?"

"yeah am serious baby"

"Ok a dawo lafiya"

"thank you baby, kiyi bacci anjima kaɗan zan tashe ki kici abinci"

"ok my love... Bye"

Katse wayar nayi bayan yagama kissing ɗina ta cikin wayar, murmushi kawai nake yi ina jin sonshi na ninkuwa yana sake hauhawa cikin raina, baccin na kwanta kamar yadda yace, inata tunane tunane dan gani nake kamar duk abubuwan dake faruwa a cikin mafarki ne ba a zahiri ba, jina nake kamar zan ji an tasheni daga wannan dogon mafarkin da nake yi. Bacci na nayi a nutse har zuwa 12 na rana sai lokacin na tashi cikina a rarake kamar na shekara ban ci abinci ba, brush na sake yi sannan na zauna naci kaza ta da fresh milk nayi hani'an, wanka na shiga nayi na fito na zauna na shirya, wayata na ɗauka nan naga miss calls din Samz da massage ɗin shi guda ɗaya, kiran Bishra ne ya shigo ina ɗagawa naji tace min wai in buɗe mata ƙofa tana waje, atamfa na saka maroon mai zanen tabarma, ƙofa naje na buɗewa Bishra muka dawo tare tana ɗauke da manyan food flasks,

Sarƙa da ɗan kunne na saka da abun hannu, sannan na koma wurin Bishra wacce ke falo tana sake gyara min shi, sai lokacin na zauna na ƙarewa felon kallo wanda komai yaji Ƙarshen gata na san ƴan gidanmu sun nuna min, a yanzu bani da abin da zan yi sai godiya ga Allah domin yagama cika min burina na duniya, abincin da Bishra ta kawo ban ci ba asalima ko buɗewa banyi ba na ajiye kan dining, bayan azahar su Anty suka zo da sauran matan yayuna su Anty jalila wanda suka kawo min kayan gara, dam aka cika min store da kayan abinci dan hatta gishiri da Maggi duk an kawo iya kayan miya ne kaɗai zance ba a kawo min ba, ƙawalli kam bata zo ba sai waya da ta kirani ta soma tsokana ta wai nice harda jinya akan ance baza a aura min samz ba to yau gashi nan mun kwana tare ya naji karon? Dariya nayi nace mata kanta ake ji ni banji komai ba, zuwa yamma su anty suka tafi harda Bishra ya rage daga ni sai hali na, sai dai muna waya dashi har zuwa lokacin da zai taho, wanka na sake yi na tsantsara kwalliya saboda ya taɓa cemin wai yana son kwalliya ni kuma yaga kamar bata dameni ba dan Allah irinƙa yi masa, har jan baki na saka na sha turare ina jiran zuwansa, shi kam duk hankalinsa a tashe yake saboda yanda yaga jikin mommy, duk ta fita hayyacinta ta rame kuma ta zabge saboda tsabagen tashin hankalin da ta ɗorawa kanta haka kawai babu gaira bare dalili, jininta ya hau sosai fiye da ko yaushe, har yaje ya taho bata san yaje ba dan tana kwance rai a hannun Allah. Magribar fari ya dawo, cikin farin ciki da ɗoki naje na buɗe masa ƙofa yana shigowa na rungumeshi ina yi masa oyoyo, rungume ni yayi hannunsa riƙe da leda wadda ya taho mana da fruits, ina maƙale dashi bayan ya rufe ƙofar muka shiga ciki, tare muka yi salla bayan mun idar nake tambayarshi jikin mommy yace min da sauƙi duk da naga tsantsar damuwa shimfiɗe akan fuskarshi, abinci na gabatar mana wanda aka kawo mana daga gida muka ci tare inata janshi da hira dan in rabashi da damuwar da yake ciki. Sosai muka sake da juna wanda hakan ba ƙaramin daɗi yayi min ba, ina kwance cikin jikinsa ina kallo shi kuma yana danna laptop ɗinsa, wani sabon film ɗin hausa nake kallo mai shegen kyau a wata tashar hausa da ake nunawa inata bashi labarin kyawun film ɗin duk da hankalinsa na kan system ɗinsa amma dai yana amsa min da "uhmmmm" ko "ayya" ahaka har muka kai 1 na dare yanda idonsa yake a soye ƙyas babu bacci haka nima nawa idon yake babu ko alamar bacci dan wuni nayi ina bacci da rana, kashe kallon yayi ya kashe laptop ɗinsa ya ɗaukeni yana cewa, "let us go and sleep", laptop ɗin tashi na riƙe masa har zuwa cikin bedroom, akan bedside drawer na ajiye masa shi kuma yana tsaye yana rage kayan jikinsa,

"Baby.... Zo muyi wanka"

"No..." na faɗa ina maƙale kafaɗa,

"Ok bari in rage miki wannan"

Sarƙar da ke wuyana ya cire min da earrings ɗina zuwa kan abun hannu, hannuna ya kama wai to shi in rakashi, da wayo da komai sai da ya kaini cikin toilet ɗin, ruwan zafi ya tara cikin tangamemen abun wankan dake girke cikin toilet ɗin kafin ya sirka da ruwan sanyi, juyowa yayi ya kalleni wacce ke tsaye nayi tsumu tsumu ina zullumi,

"Matsoraciya...... Oya enter"

"nidai gaskiya a'a" na faɗa ina bubbuga ƙafafu a ƙasa, na fara yi masa shagwaɓa kenan ban ankare ba naji yayi sama dani ya ajiye cikin ruwan, shima shiga yayi ya jani jikinsa nan ya fara ƙoƙarin rage min kayan jikina ba dan kar yayi min kallon ƴar ƙauye ba nikam da ba yarda zanyi in zauna haka tik agabansa ba Allah ma ya sani dan ban taɓa samun kaina a hakan ba kuma a gaban wani gardi sai yau, bai barni da ko pant ba haka nayita ɓuya ajikinsa ina maƙaleshi duk da shima ɗin babu sauƙi ko kunya ta bai ji ba ya tuɓe agabana wai wanka zai yi ai har da wata hausa yayi shi a lallai bahaushe wai ranar wanka ai ba a ɓoye cibi.

Tare yayi mana wankan ya wanke ni tas sannan muka fito bayan ya gama tsokane tsokanensa, turare nasha sosai duk da yanata sinsinar fatata wai ƙamshi nake kamar nayi wanka da turare, dariya nayi sannan nabi lafiyar gado bayan na saka night gown ɗina light pink, agogon dake kan bedside drawer na kalla ƙarfe 1:30 na dare, tunda naga ya nufo gadon daga shi sai ɗan pant irin na maza dama naji gabana ya faɗi, nidai wannan ƙira tashi ta jima tana bani tsoro ji nake kamar na ɗebo ruwan dahuwar kaina dan kamar yafi ƙarfina ko a auren ma amma na dage sai da na aureshi, "wataƙila ma kasheni zai yi a daren farko" na faɗa acikin raina ban san maganar ta fito ba,

"baby..... Tsoron me kike ji? Ki kwantar da hankalinki abun ai ba dambe bane ko kokawa..... Babu wahala, zo ki gani"

Da farko dai a tsorace nake amma irin yanayin kalar soyayyar da yashiga nuna min sai na saki jiki na warware dashi muna bawa juna farin ciki da nishaɗi har tsawon wani lokaci wanda har ni da kaina sai da na ƙagu da mai afkuwa ta afku, tambayata naji yana yi wai addu'ar da ake yi lokacin dan ya taɓa ji wani malami yana faɗa cikin wa'azinsa, karanta masa nayi ina faɗa shima yana maimaitawa, ni dai babu abin da zan iya tunawa kawai dai naji kamar irin asamu glass ɗin nan ayita duka har yayi kwatsa kwatsa sannan a ɓurma shi kusan haka naji Samz yayi min take naji wani abu yana fita daga jikina kamar ruwa sai dai amma yafi ruwa kauri kwata kwata ban kawo araina wai jini bane duk da uban zugi da raɗaɗin da nake fama dashi, jin wani sashe na jikina nake kamar ba ajikina ba, a gajiye kuma awahale ya barni inata tsaga kukana kamar wata ƙaramar yarinya, ihu kam yasha shi dan har sai da muryata ta dishe, daƙyar da siɗin goshi ya iya rarrashi na a wannan dare har na samu nayi bacci jikina duk tsami, rungume ni yayi bayan yayi wanka ya dawo, bacci nayi marar daɗi dan tunda uwata ta kawoni duniya ban taɓa jin ciwo makamancin wannan ba da naji amma wani abun mamaki da al'ajabi duk da wannan abun da ya yi min banji haushinsa ko sonsa ya ragu daga cikin zuciyata ba wannan son yana nan tare da tarin ƙaunar da nake yi masa suna sake ninkuwa..................✍🏻


*Garin dadi littafin kudi ne ga mai bukatar cigaban labarin sai ya tura 500 ta 0774712835 Aisha Ibrahim Access Bank sai a tura evidence of payment ta wannan no 07044644433 ko a tura katin waya da shaidar biya wannan no 07044644433*


_*Ummi Shatu*_👌🏻
[1/5, 12:43] Maman K: ©️ *HASKE WRITERS ASSOCIATION*
_(Home of experts & perfect Writers)_



*GARIN DAƊI......!*💍💍



*_NA_*


_*UMMI A'ISHA*_


PAID BOOK #500

*Wattpad:ummishatu*


{32}

*Ina kuke manyan mata ƴan ƙwalisa ma'abota son gyara da kece raini, maza ku garzayo ku nemi maman Maryam domin samun lafiyayyu kuma haɗaɗɗun Lagos lace wanda zaku iya samun ɗinkakku da kuma sabbi a ledarsu, kaya iya zaɓinki, gefe ɗaya muna da GHT product, zaku samu,*

~MAI DA TSOHUWA YARINYA

~FEMALE CARE

~REODEO

~VIGOR MAX

~ LONGZIT

~B CLEAR

*DUK ZAKU SAMU WADANNAN KAYA CIKIN SAUKI DA RAHUSA MAZA KU NEMI MAMAN MARYAM AKAN WANNAN NO 07080222187, SIYAN NA GARI MAIDA KUƊI GIDA.....*


~~~Ban san tsawon lokacin da na ɗauka ina shaƙar baccin wahala ba domin lokacin da na tashi tuni har rana ta fito, a hankali na buɗe idanuwana, ni kaɗaice acikin ɗakin hakan yasa na maida hankali na wurin tunanin yadda zanyi in tashi har in kai kaina bathroom saboda gaba ɗaya ilahirin jijiyoyin jikina sun ɗaure sai uban tsamin jiki da nake fama dashi take na tuno hirarmu da Ƙawalli tun shekarun baya wai taji ance jijiyoyi 40 kuma duk sai an tsinka su, duk da ina fama da kaina hakan bai hanani dariya ba araina ina cewa ai wataƙila ma ni jijiyoyin da Samz ya tsinka sun kai 100 irin wannan azaba haka,

Samu nayi na yunƙura na tashi zaune, nan take idona ya sauka kan jinin da ya fita a jikina daren jiya faca-faca ai ban san lokacin da na ƙwalla ƙara ba wadda saida naji ƙasa na ya amsa sai kuma na fashe da kuka, ƙofa naga ya buɗe ya shigo yana sanye cikin blue black ɗin t shirt da baƙin trouser daga gani fita yayi ya dawo,

"am sorry baby.... Me ya saki kuka?" naji ya faɗa lokacin da yake hawowa kan gadon, da jajayen idona na kalleshi amma bance komai ba sai cije baki da nake yi, shima idanuwansa ne suka sauka kan jinin da na gani wanda shi dama already ya ganshi, kama ni yayi yasa a jikinsa yana rarrashi na amma na kasa yin shiru ni kaina ban san dalilin kuka na ba shin raɗaɗin da nake ji da zugi ko kuma farin cikin na kawo martaba ta inda ya dace, ko kuwa takaicin rabuwa da abin da na jima tare dashi,

"Baby..... Menene abin kuka wai? Dama ba ni kike yiwa tanadi ba?"

Kai na girgiza masa alamar shi nake yiwa,

"ok to ai idan nine farin ciki zaki yi tunda gashi kin bani abina kuma nayi farin ciki.... Kin sani cikin duniyar da ban taɓa zuwanta ba, banma san da ita ba sai jiya, thank you baby... Am grateful"

Duk da naji daɗin kalamansa amma hakan bai sa na daina kukan ba, daƙyar dai ya lallaɓa ni da taimakonsa na shiga toilet, saida na daure na shiga ruwan zafi sosai na gasa ko ina na jikina amma duk da haka jina nake kamar ba daidai ba kai anya mutumin nan aika aikar da yayi min ba sai na dangano da hospital ba? Wallahi jina nake kamar sai an ɗinke ni dan ina jina da banbanci sosai akan yanda nake da,

Wankan tsarki nayi da ruwan ɗumi sannan na fito ina ɗaure da towel har lokacin jikina banji ya gama warwarewa ba daga tsamin da yayi sai dai ya ragu da kaso mai yawa, baya cikin ɗakin dan haka na sake na shirya na saka kayana sannan nayi salla, ina idarwa na koma saman gado na kwanta dan tun kafin infito ya cire bedsheet ɗin yasa wani, ina nan kwance ina tunanin rayuwa da abubuwan da suka faru daren jiya wanda basu da maraba da duniyar mutuwa naji motsin shigowarshi, lumshe idanuwa na nayi har ya ƙaraso kan gadon,

"am soo sorry baby i left you alone..... Muna tare da yayanki ne wai your friend has made a yummy breakfast for us.... Tashi ki gani"

Sai lokacin na buɗe idona ina kallon farantin da yake riƙe dashi sosai abin ya bani mamaki jin wai yaya Abdul hakeem ne ya kawo mana breakfast ɗin da Ƙawalli tayi kuma wai harda zama su yi hira da Samz koda yake naga yayan ya sauko tunda jimawa amma ada kafin auren mu babu wanda ya tsana sama da Samz baki da baki ya faɗa min wai wallahi ya tsani wannan kafirin ɗan iskan saurayin nawa kuma idan ya sake ganina dashi sai ya targaɗa ni, kuma shine yayi kutun kutun ɗin da su Abba suka rabani dashi dan kusan kowa a lokacin kallon ɗan iska yake yiwa samz gani suke kawai yazo ne dan ya gurɓata min rayuwa, ni kaɗai na yarda dashi kuma na san ba ɗan iska bane,

"Baby..... Tashi mana" ya sake faɗa cikin sigar rarrashi da kwantar da murya, a hankali na tashi na zauna ina kallon abincin da ya fara buɗewa, wasu ƴan ƙananan food flasks ne gwanin sha'awa daidai cikin mutum biyu har guda huɗu,

Na farko soyayyiyar awara da ƙwai ne aciki sai ɗayan mai ɗauke da soyayyen dankali da ƙwai, ɗayan kuma sos ce aciki sai na Ƙarshen wanda aka zubo farfesun kayan ciki, ai tunda naga awara naji yawuna ya tsinke ai ni da Ƙawalli mun san ta kan kwaɗayi lokacin da muna yara gaba ɗaya kuɗin mu wurin masu awara take tafiya, ta san ina bala'in son awara shiyasa ta yimin shi kuma oga tayi masa dankali, hannu na miƙa zan ɗauki awarar ya ɗauke, ɓata fuska nayi zanyi masa kuka,

"My crying baby........" da kansa ya fara bani ina ci, awarar tayi daɗi danma babu yaji sai sos, ganin ina shirin cinyewa shi bai ci ba ya sani kallonsa nace,

"kai fa?"

"No... Wannan ai na baby ne, ki ci kawai"

Sai da na ƙoshi dam sannan shima yaci dankalin ya ɗauko min ruwa na sha duk ina zaune saman gado kamar wata sarauniya, kwanciya nayi a jikinsa atare muka yi bacci har wurin azahar dan bugun da ake yiwa gate ne ma ya tashe mu dan duk wayoyinmu suna kashe, shi ya fita jimm kaɗan sai gashi ya dawo wai abinci aka kawo mana daga gidanmu su Anty na amma sunƙi shigowa wai sauri suke akwai inda zasu je, murmushi nayi na tashi na shiga toilet nayi alwala na fito, shi kam masallaci ya fita, bayan na idar na rakuɓe jikin gado ina tasbihi har ya dawo,

"Baby wai lafiya kuwa?"

Girgiza masa kai nayi nace "Ji nake kamar na yage fa"

Zaro ido yayi kafin ya kama ni na mike tsaye muka zauna gefen gado,

"baby kin yage kamar wata paper.... Let me see"

Babu musu na kwanta na buɗe masa ƙafafuna ya duba,ɓoye firgicinsa yayi yace,

"anjima sai muje clinic a duba ki...."

"ka yaga ni ko?" na faɗa ina ƙoƙarin yin ƙwalla,

"no baby.... Babu komai fa" ya faɗa cikin sigar kwantar da hankali, tashi nayi muka fita falo muka ci abinci ya kunna mana zee world ni dai a kwance na wuni dan duk jina nake a gajiye tunda na tashi yau banyi komai ba sai ci sai kwanciya har magriba lokacin ne yace in shirya ya rakani clinic a duba ni, shiryawa nayi kafin ya dawo daga salla cikin wani c green ɗin lashi mai ɗigon silver da adon stones ajiki, dama ƙamshi yanzu ko ban shafa turare ba fatata ƙamshi take yi, hijabi na saka na ɗauko sabon takalmi flat na saka na zauna a falo ina jiran sa kuma har lokacin ban kunna wayata ba araina inata tunanin dalilin da ya hana ƴan gidanmu zuwa yau dan hatta Bishra ma da nasa rai da zuwanta itama ɗin bata zo ba kamar ta san abin da ya faru, a haka ya dawo ya same ni muka fita yana tambayata ina ya dace muje, tunawa nayi da wani ɗan ƙaramin asibiti da nake raka anty idan ta zo Dr ɗin mace ce kuma likitar mata, napep ya tare mana muka hau har zuwa asibitin,babu wani ɓata lokaci ya buɗe min folder muka shiga wurin Dr Aziza dama inata addu'a kar Allah ya haɗani da idon sani, tare dashi muka shiga dan shi yayi mata bayanin ma matsalata ni kunya bata barni ba, kan ɗan ƙaramin gadon da aka tanada saboda duba patient ta umarceni in hau zata duba ni, saida ta cajeni tsaf sannan na sauko na koma mazaunina na zauna itama ta dawo kan kujerarta,

"Ango na dubata ba wata matsala bace.....Illa rashin sabo, sannan size ɗin is too much for her dan haka dole sai ka rinƙa bi da ita a hankali..... Ba sai nayi mata ɗinki ba kawai zan bata wani ɗan ƙaramin cream da zata rinƙa shafawa but kaima sai ka ɗan ɗaga mata ƙafa for some days Koda kwana biyar ne zuwa 1 week, kafin sannan raunukan dake wurin sun warke dan ta ɗan jijji rauni.... "

Wani daɗi naji da naji tace ya barni na huta na ƴan kwanaki, dan kamar ta shiga zuciya ta taga abin da ke raina, haka muka baro ofishin Dr Aziza tana ta tsokanata bayan ta bani ƴan shawarwari kan in dimanci tsarki da ruwan ɗumi hakan zai taimaka min sosai sannan kullum in rinƙa shafa wannan cream ɗin har can ciki sau biyu zuwa uku. Sai da muka fara tsayawa ta pharmacy ya siyi maganin sannan muka fita,ta wani restaurant muka biya yayi mana take away na dinner sannan muka wuce gida, sallar isha muka yi sannan muka ci abincin da muka taho dashi, ni dai yau da wuri nayi wanka dan bacci nake ji, a falo na barshi yana kallo yana waya da ƙannenshi wanda ko sau ɗaya bamu taɓa gaisawa dasu ba, ina zaune gaban mirror ina shafa haɗaɗɗiyar humrar da anty ta siya min tun daga garin Maiduguri ya shigo, sanye nake da farar night gown ɗina marar nauyi da kauri, yana riƙe da maganin da muka siyo wanda bai da wani girma dan dududu girmanshi bai wuce na ɗan ƙaramin Maclean ba amma cikinsa kamar Vaseline bai da wata maraba dashi,

"Kamar kinyi shirin bacci ko?"

Kai na ɗaga masa,

"yau baza a jirani ba?"

"Bacci nake ji..."

"ok.... Zo in saka miki maganin"

"uhmm uhmm...." nace dashi ina maƙale kafaɗa, hannuna ya kama ya zaunar dani gefen gado,

"Ba kya son ki warke da wuri? Ki tausaya min mana"

Murmushi nayi araina nace nima ai jiya ba tausaya min ɗin kayi ba, kwanciya nayi ya shafa min maganin sannan na kwanta shi kuma ya tashi ya fita falo, babu ɓata lokaci bacci yayi gaba dani, shi kam dama idan da sabo ya saba kwarabniyar dare, kallo ya tisa a gaba har wurin 1 sannan ya shigo yayi wanka yazo ya kwanta kusa dani tare da jawoni jikinsa, jikina yana haɗuwa da nashi na farka,

"am sorry bada niyya na tashe ki ba..." ya raɗa min a hankali,

"wai sai yanzu zaka kwanta?" na tambaye shi bayan na kwantar da kaina cikin ƙirjinsa,

"yanzun ma ba bacci nake jiba kawai na gaji da zama ni ɗaya ne ina son inji ɗumin jikin ki...."

"Nima tun ɗazu nake son ka shigo, ka barni inata jin sanyi"

"shine kuma ba zaki faɗa min ba, to koma baccinki"

"No, muyi hira"

"No,ina son in ganki kina bacci.... Bacci na yi miki kyau"

"nidai a'a nima ina son ganin baccin ka"

"OK to bari muga waye zai fara baccin"

Hira muka cigaba da yi har bacci yasamu nasarar saceni shi dai ban san lokacin da yayi ba kuma duk da haka ya rigani tashi.

Haka muka kasance cikin so da ƙaunar juna har tsawon kwanaki biyar koda yaushe cikin riritani yake da bani kulawa sannan har lokacin ban fara girki ba take away yake iyo mana kullum da zarar nayi maganar girki kuma sai yace ba yanzu ba in bari in huta in sake warwarewa, iya kawaici yayi wurin bin dokar Dr dan cewa yayi a maimakon kwanaki biyar zuwa shidan da tace shi ya hakura sai bayan kwana goma lokacin na gama warkewa, shaƙuwar da muka yi yanzu ta musamman ce fiye da ta baya shiyasa yau da ya sanar dani wai zai koma aiki jibi dan haka gobe da yamma zai tafi Kaduna zai kwana acan washe gari ya ƙarasa Abuja sai naji duk hankali na ya tashi, wuni muka yi yana rarrashi na tare da yimin alƙawarin wai ranar Friday zai dawo muyi weekend tare wannan dama shine dalilin da yasa bai so zamana a Kano ba dan zamu yi nesa da juna sannan su aikin su babu ɗaga ƙafa dama 2 weeks ya nema kuma daƙyar ma aka bashi 10 days, ni dai daƙyar na saki raina muka kwana cikin farin ciki amma da zarar na tuna tafiyar nan tasa sai inji ƙwalla, da kansa ya kira

Please Login or Register in order to submit comment