Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Felicia ta matsa masa da kira wadda ni kaina sai da na fahimci hakan dan bata tashi kiran sai da daddare ko da safe before ya fita office amma ban taba magana ba dan banma san waye mai kiran ba kawai dai naga baya dauka ko kuma sai dai inga yayi tsaki ya katse kiran nidai idone nawa sannan duk da damar da ya bani na wai zan iya daukar wayarshi a duk sa'ilin da naso ko nake doubting akan wani abu nake son in duba to ƙofa a bude take, duk da hakan ban taɓa garaje ko rawar kan ɗaukar masa waya ba sannan ko kiransa akayi ina kusa da wayar bana gigin dauka koda kuwa baya kusa,

Yanzun ma zaune muke a falo bayan na gama shan uban fruits din da na sakashi a gaba muka je muka siyo dan shi nake ta sha'awa tunda na tashi amma ban fada masa ba har ya fita office kuma lokacin da yake office dinma munyi waya har ya bukaci jin abinda nake bukata inyaso sai ya taho min dashi amma nace babu komai dan nima ina son fitar so nake mu fita tare shiyasa sai da na bari ya dawo bayan yayi wanka yaci abincin da yau dai na samu na girka masa wato white yam sai sos din alayyahu da albasa,

Lokacin da yaga abincin fada ya fara yimin cikin kwantar da murya ba wai cikin zafi ko tsawa ba a'a cikin sanyi da rarrashi,

"Haba baby..... Wa ya saki wannan aikin? Bakya son kamshin abinci amma shine zaki je ki wahalar min da kanki?"

"boo zan iya ne fa, kuma laifine dan na yiwa mijina girki?" na fada cikin shagwaba ina turo baki,

"ba laifi bane baby but...... Kinga situation dinki,in fact bana son duk wani abu wanda zai baki wahala....."

"to ai wannan bai bani wahala ba sweet, na gaji da kallon ka kana cin abincin restaurant, duk restaurant din Abuja bana jin akwai wanda baka je Kaci abinci ba, sannan ai kayi kokari dan tunda nazo garin nan ban taba dafa maka abinci ba sai yau......"

"come here..... Did you vomited?"

Jikinsa na shige kamar yadda ya bukata sannan na girgiza kaina alamar a'a,

"thank you baby amma dan Allah daga wannan kar ki sake bana bukata, zan cigaba da zuwa restaurant ni ban dauki hakan a matsayin gazawarki ko careless ba....."

"Nidai gaskiya ban yarda ba...." na ce dashi cikin shagwaba, kumatuna yaja ya fara cin abincin yana bani labarin wai abokinshi ahmad ya samo matar aure a Kano harma anje masa tambaya, fatan alkhairi nayi kafin nace,

"ka gama ka rakani in siyo fruits...."

Kallona yayi sannan ya bani amsa da "to me yasa baki kirani na taho miki dashi ba?"

"ina son in fita ne nima"

"kina son yawo dai, anyways nima ina son ki sha fruits din it's good for your health" turo masa baki nayi dan na gane abinda yake nufi dama tun ba yanzu ba yana son insha fruits saboda yana samun abinda yake bukata sosai to sai gashi kuma yau na nema da kaina, nima na san yau sai abinda hali yayi kawai dan zan ci ƙaniyata a hannunsa.

Taren muka fita bayan ya kammala cin abincin muna tafe muna hirarmu kamar wani saurayi da budurwa wanda suka yi nutso cikin tsinkar furen soyayya, komai da komai ya hado min ya siyo tun daga kan lemo, ayaba, kankana, gwanda, abarba sai kuma tufa, haka ya lodo su ya zo ya yanyanka min da yake ina so sosai na sha sauran ya saka cin fridge, salla nayi bayan na huta sannan na tashi dan inje inyi shirin bacci, wayarshi ya bani akan in saka masa a charge domin shi wani aiki yake yi akan system dinshi,

Ina shiga bedroom ina saka chargen na ga kira ya shigo haka na juya naje na kai masa amma bai dauka ba ya katse wayar ya bani haka aka yi ta kira tun ina wanka ina ji shima kuma ina da yaƙinin ya jiyo, shiryawa nayi nabi lafiyar gado saboda yanzu abu kadan sai inji na gaji aiki ba aiki ba sai in ji gajiya ta taru min to haka kawai ma banyi aikin komai ba jina nake kasala tana damuna bare kuma ace nayi aiki komai ƙanƙantarsa. Na dan fara bacci sama sama naji shigowarsa kuma hakan yayi daidai da shigowar wani kiran cikin wayarsa, bude ido na nayi kafin na gyara kwanciyata,

"am soo sorry baby, phone dina ta tadaki ko"

'No " nace ina gyara kwanciya ta, wanka ya shiga kafin ya fito na sake komawa baccina, cikin baccin najishi cikin jikina yana shafa kaina, ni dai dadin bacci bai barni naji maganar da yake yi ba sakamakon kiransa da aka sake yi awaya........


*Garin dadi littafin kudi ne ga mai bukatar cigaban labarin sai ya tura 500 ta 0774712835 Aisha Ibrahim Access Bank sai a tura evidence of payment ta wannan no 07044644433 ko a tura katin waya da shaidar biya wannan no 07044644433*


*_Ummi Shatu_*👌🏻
[1/5, 12:43] Maman K: {43}

*Ina kuke manyan mata ƴan ƙwalisa ma'abota son gyara da kece raini, maza ku garzayo ku nemi maman Maryam domin samun lafiyayyu kuma haɗaɗɗun Lagos lace wanda zaku iya samun ɗinkakku da kuma sabbi a ledarsu, kaya iya zaɓinki, gefe ɗaya muna da GHT product, zaku samu,*

~MAI DA TSOHUWA YARINYA

~FEMALE CARE

~REODEO

~VIGOR MAX

~ LONGZIT

~B CLEAR

*DUK ZAKU SAMU WADANNAN KAYA CIKIN SAUKI DA RAHUSA MAZA KU NEMI MAMAN MARYAM AKAN WANNAN NO 07080222187, SIYAN NA GARI MAIDA KUƊI GIDA.....*


~~~Fitarshi tayi daidai da shigowar kira wayarta, cikin rashin ƙwarin jiki ta miƙa hannu ta ɗauka saboda ganin aminyar tata ce madam comfort,

"Maman Mary komai lafiya?" ta fada daga cikin wayar dan son bugar cikinta da mararin jin yadda ake ciki bayan ƴarta ta gama tsegunta mata komai,

"Ina fa lafiya maman Feli... Ai babu maganar lafiya anan, wallahi na rasa ya zanyi da wannan yarinyar dake neman rabani da yarona, komai da muka yi last time yanzu duk ya lalace, duk wani shirinmu am quite sure ya lalace akan yaran nan....."

"to yanzu menene mafita? Ai ba wai zamu hakura bane zamu sake samo solution ne, we most definitely need to find a solution to this problem....."

"hakane to amma ke ya kike ganin ya dace ayi?"

Dama abinda take son ji kenan shiyasa sai da ta kiftawa Felicia dake zaune kusa da ita ido sannan ta bawa mommy amsa da,

"ki bani time zan yi tunani inyaso sai in zo...."

"babu matsala.... Nagode sosai madam comfort, Thank you"

Katse wayar suka yi har lokacin dai mommy bata gama jin dacin da take ji game dani ba na kiyayyar da take yi min.

Shi kam bayan yabar wurin mommy sallama ya koma suka yi da daddy daga nan ya bibbiya ta wurin friends da abokan arziki wanda har yanzu da ya musulunta bai daina mutunci da zumunci da su ba shiyasa bai baro Kaduna ba sai la'asar lokacin nikam na zuba ido har na gaji gashi na kasa cin abinci shi nake ta jira amma ganin bai dawo ba yasa na dafa noodles naci, jin na ɗanji karfin jikina yasa na gyara ko ina nayi wanke wanke na shasshare ko ina na goge shiyasa na gaji lis,

Zuwa bayan magrib ya karaso lokacin nayi jiran har na gaji, zumburo baki nayi lokacin da naje taroshi, murmushi yayi ya dagani sannan ya sakani ajikinsa tare da sunkuyowa yayi hugging dina shima yana dariya,

"baby me kuma ya faru? Kin matsa min sai naje Kaduna, na yarda naje na dawo kuma na samu kina fushi, me ya faru?"

"ni ba fushi nake yi ba..... Ya ka baro su mommy? Ta hakura?"

Har lokacin muna rungume da juna kamar wadanda suka shekara basa tare,

"mommy fa ba zata taba hakura ba my love.... Ki cire wannan tunanin da damuwar daga ranki dan na san halin mommy, if she says yes is yes and her no is no, soo ki daina wahalar da kanki wurin ganin sai mommy ta so ki ko ta kaunaceki saboda is hardly hakan ta kasance..... "

Hawaye ne suka fara zuba daga cikin idanuwana dandanan saboda jin kalamansa, wannan wacce irin kaddara ce? Menene laifina a rayuwa dan kawai na kaunaci ɗanta saboda Allah kuma da zuciya daya? Menene laifina dan na zauna tare da ɗanta a matsayin matarsa? Jin alamun kuka nake yi yasa shi saurin ɗago fuskata yana lashe hawayen dake fita cikin kulawa, daukata yayi zuwa saman kujera ya fara lallashi na,

"baby menene abin kuka? Ni ai ina son ki ina kaunarki, i love you with all my heart..... And zan cigaba da sonki har zuwa lokacin da zan daina numfashi"

Na san duk yadda zanyi masa bayani bazai taba fahimtata ba amma ta yaya zan iya samun nutsuwa da kwanciyar hankali alhali mahaifiyarsa da danginsa basa sona kuma basa kaunata kai bama su da burin da ya wuce na suga sun rabani dashi, rarrashina yacigaba da yi har na samu nayi shiru na daina kukan buy akwai hawaye saman kuncina basu daina sauka ba,

"Ga abinci muje kaci....."

"no baby, you are the real meal that i want now......"

Harararshi nayi yana goge min hawayen,

"am not in the mood...." na fada ina turo baki,

"Haba baby yau fa 3 days kenan...."

"Bana jin dadi ai...."

"to shikenan baby...."

Gaba daya jikina yagama yin sanyi da lamarin mommy da danginsa shiyasa komai cikin sanyin jiki nake yin sa ni ban san me zanyi musu su soni ba haka ban san me zanyi in wanke kaina daga zargin laifin da suke yi min ba wanda ban san na aikata ba gashi bana son tattauna maganar da kowa a family dinmu dan gudun abinda zai je yazo, dama idan ban manta ba sai da anty ta fada min tace min insa araina bazasu taba sona ba kuma gashi dagasken hakane gashi yanzu nagani da idanuwana,

Shirin bacci ma duk a sanyaye na yi na kammala nazo na sameshi yana ta fama da aiki a system dinshi yau daya da bai je office ba aiki har ya tarar masa yayi masa yawa, ajiye laptop ɗin yayi a gefe yayi min masauki a jikinsa yana taba wuyana dan jin halin da jikina yake ciki shin akwai zazzabi ko babu,

"baby ya jikin naki?"

"da sauki sweet" na fada ina hadiye bakin cikin da ni kadai na sani dan har na fara tambayar kaina wai meyasa ma na aure shi ne? Yanzu da ace bahaushe na aura asali dan uwana wanda kowa nasa gaba da baya musulmai ne ai da ban fuskanci kalubale irin wannan ba amma yanzu gashi tun aure bai je ko ina ba na fara fuskantar damuwa danma bada gareshi bane daga danginsa ne,koda yake haka fa gaba daya rayuwar take kowa da kalar irin tashi kaddarar, kuma ko babu komai akwai dunbin lada ga wanda yayi sanadiyyar shiriyar wani musamman ma ya karbi musulunci,

Nayi nisa cikin tunani na naji ya dage sai kokarin birkita min tunani yake da soyayyarsa mai mutukar sanyi kai samz akwai nacin jaraba yau dai tunda ya rantse sai ya karbi hakkinsa sai ya karɓa din shiyasa na hakura na daddaure na biye shi har ya samu abinda yake so. Da kanshi yaje ya hada mana ruwan wanka sannan yazo ya daukeni muka je muka tsaftace jikinmu tare sannan muka dawo yaci gaba da aikinsa nikuma nayi baccina na barshi, nidai duk da abin yana damuna amma ban yarda na sakashi araina har ya hanani samun farin ciki da mijina ba haka na hakura na cire komai daga raina muka cigaba da zaman lafiyar mu, kullum sai munyi waya da yan gidanmu da ƙawalli haka nayita kirkirarma kaina abubuwan debe kewa a duk sa'ilin da baya nan dan karma wata damuwa ta shigeni har ta hanani sukuni.

Tun cikina yana wata biyar muka fara siyan kayan baby duk wani abu da nagani online wanda yayi min haka zanyi order na biya dama bani da matsalar kudi saboda yana ajiye min kudi a account dina every month shiyasa duka abubuwan ma ba sai na tambayeshi kudin siyansu ba, ko yau ma sai da naga wata baby walker a wani page nan ruwan ido ya hanani zabar wadda tayi min shiyasa lokacin da ya dawo bayan ya huta nake nuna masa dan ya tayani zaba,

"to baby idan kuma twins ne fa?"

"sai mu kara daya daga baya"

Dariya yayi yace "kawai muyi order din biyun yanzu"

Ku san komai tare dashi muke siya dan yanzu cikin yana da watanni bakwai,ita kuma ƙawalli haihuwa ko yau ko gobe dan cikinta ya girma sosai, duk da ina cewa bazan je Kano ba har sai na haihu amma yanzu ji nayi bazan iya ba saboda gaba daya hankalina ya koma kan gida ina so inje inga halin da kowa ke ciki,

Yau kam cike nake da murna saboda zuwan bakin da ban san da zuwan su ba saboda zuwan bazata suka yi min wato yaya Abdurrahman da matarshi anty Rahinatu harda yaransu guda biyu Amir da Amira, kasancewar weekend ne shima yau yana gida, muna ta sharar bacci wayata ta tada ni, ba karamin dadi naji ba saboda zuwan su babu shiri na tashe shi dan bani da cefane nan ya fita dan zuwa kasuwa,

"ikon Allah ashe masu haihuwar suna da yawa, weedat kice da bamu zo ba sai dai muji haihuwa muyi ta mamaki......" anty Rahinatu ta fada cikin tsokana dariya kawai nayi na kasa bata amsa saboda kunya, duk da na saka hijabi kan doguwar rigar jikina ta atamfa sai da cikina ya fito saboda ya girma babu laifi,

" uwar mita koda yaushe yaya kun ki zuwa kunki zuwa to yau dai gashi mun zo shikenan?" yaya Abdurrahman yace dani lokacin da na kawo masa kayan motsa baki gabanshi,

"wallahi naji dadi sosai yaya, Allah ya saka da alkhairi yabar zumunci"

"weedat an girma, Masha Allah ubangiji Allah ya kara zaman lafiya yabar soyayya"

"amin anty, yagida ya aiki? Ai da baki zo ba anty da fushi zanyi muku Kota chat in daina kulaku"

"gashi mun wanke kanmu, ayi mana afuwa"

Tare da anty Rahina muka shiga kitchen muka yi girki bayan samz ya dawo daga kasuwa ya iyo siyayya kaca kaca,shinkafa muka dafa muka yi vegetables soup hadaddiya wadda ta wadatu da naman kaza da ganyayyaki sannan muka hada fruits salad, sosai shima naga samz ya sake da yaya Abdurrahman suna ta shan hirarsu Muma muna tamu nida Anty Rahina, ni duk atunanina kwana za suyi amma sai yaya yace tafiya zasu yi, nidai ban so haka ba amma babu yadda na iya, lemuka da chocolate yaya ya kakkawo min ni abinma har dariya ya bani sai kace wata karamar yarinya, sai ko gurasa kamar yasan ina ta sha'awarta kwana biyun nan, nidai bani da abinda zan basu sai ko kudi da samz ya bama su Amira wannan dinma dakyar iyayen suka barsu suka karɓa, sallama muka yi dasu suka tafi anty tana cemin sai mun hadu a Kano idan ƙawalli ta haihu, ƙwalla naji ta taru a idona bayan sun tafi nan naji kamar inbisu nima kai gaskiya dole inje Kano kwana kusa Insha Allah,

Riƙo hannuna yayi muka dawo ciki yana tsokanata, "haba baby dama har yanzu baki daina kukan ganin ƴan gida ba? Na zaci kin waye tunda kika gane daɗin zama dani...." na san ba haka yake son faɗa ba kawai kaucewa yayi ganin na tsareshi da idanuwana,

"ba gaskiya na fada bane? Dan Allah yanzu zaki iya yin wata ɗaya batare dani ba? Kema kin san nasan ba zaki iyaba..." yana gama faɗa yaja baya dan yasan yanzu bana iya binsa da gudu muyi tsere shiyasa sau tari duk abubuwan da yaso faɗa fadinsu kawai yake ya gudu ina ji ina gani babu yadda na iya sai dai kawai nasa masa ido,

Murmushi nayi na sunkuyar da kaina dan tabbas abinda ya fada gaskiya ne ayanzu dai bana jin in ba wani ƙadari na Allah ba bana jin zan iya koda sati biyu batare dashi ba dan ya gama mamaye raina,

"in zo in duba baby? Yau throughout ban duba shi ba..."

Rabuwa nayi dashi na nemi wuri na zauna kan kujera ina bubbude kayan da su yaya Abdurrahman suka kawo min, harda dakakken ƙuli ƙuli, kusa dani naji ya dawo yana shafa cikina,

"na san kin gaji ko?" kai na ɗaga masa ina sake narke masa, ƙafafuwa na ya fara matsa min a hankali kamar yadda ya saba yimin koda yaushe.

***

"kamar yadda na alƙawarta miki cewa zan zo miki da mafita to gashi na cika alƙawari, ungo wannan, karki yi wasa dashi maman Mary ki tabbatar duk yadda zakiyi wannan yarinyar taci a abinci, idan har taci ina mai tabbatar miki da shikenan burinki zai cika dan ɗanki bazai cigaba da zama da ita ba duk da yana sonta dan dole zai rabu da ita.... " madam comfort ta faɗa tana mikawa mommy wani ɗan ƙullin garin magani dake nannade cikin bakar leda wanda ta ciroshi daga handbag dinta, karba mommy tayi tana yi mata godiya sai dai kuma tunani take shin ta ina zata ganni bare har ta saka min maganin in ci? Ta san dai koshi idan ta bashi bazai yarda da hakan ba bare har ya bani in ci, kamar madam comfort ta shiga zuciyarta taga abinda take tunani taji tace,

"yanzu aiki ya rage ga naki domin ni na gama nawa.... Kiyi duk iya yinki ki aiwatar da wannan aikin batare da jinkiri ba, idan har kika yi jinkiri kuwa to fa kina ji kina gani komai zai fi karfinki...." daga haka ta saba jakarta ta kara gaba saboda dama church zata je ta biyo ta nan..........


*Garin dadi littafin kudi ne ga mai bukatar cigaban labarin sai ya tura 500 ta 0774712835 Aisha Ibrahim Access Bank sai a tura evidence of payment ta wannan no 07044644433 ko a tura katin waya da shaidar biya wannan no 07044644433*


*_Ummi Shatu_*👌🏻
[1/5, 12:43] Maman K: {44}


*Ina kuke manyan mata ƴan ƙwalisa ma'abota son gyara da kece raini, maza ku garzayo ku nemi maman Maryam domin samun lafiyayyu kuma haɗaɗɗun Lagos lace wanda zaku iya samun ɗinkakku da kuma sabbi a ledarsu, kaya iya zaɓinki, gefe ɗaya muna da GHT product, zaku samu*

~MAI DA TSOHUWA YARINYA

~FEMALE CARE

~REODEO

~VIGOR MAX

~ LONGZIT

~B CLEAR

*DUK ZAKU SAMU WADANNAN KAYA CIKIN SAUKI DA RAHUSA MAZA KU NEMI MAMAN MARYAM AKAN WANNAN NO 07080222187, SIYAN NA GARI MAIDA KUƊI GIDA.....*


~~~Tagumi mommy ta rafka tana son samo mafita dan ba karamin aiki madam comfort ta haɗata dashi ba, tayaya yanzu ita zata samu damar aiwatar da wannan aikin?

"No way...." ta fada a hankali bayan ta yi ɗan karamin tsaki,

"mommy what's wrong with you?" shine abinda taji Hadiza tace wadda shigowarta kenan cikin falon tana kokarin zama kusa da ita,

"Hadiza ina son inje inga halin da brother dinku yake ciki shida matarsa...."

"ahhh mommy ba kwanan nan yazo ba? Me kuma ya sake faruwa?"

"babu abinda ya faru kawai yanzu hankali na da tunanina yakoma gareshi ne ina son ganin halin da yake ciki"

"to shikenan mommy you can go tunda kince haka"

So take ta san ta inda yadace ta sanar da daddy maganar zuwanta Abuja amma ta rasa ta ina yadace ta fara, daurewa tayi tai ta maza tayi kundunbala yana shigowa taje ta sameshi da maganar,

Yana zaune ya ajiye dan ƙunshin da ya shigo dashi yana jira ta zo ya bata taje ta kafsata musu, yaji tace,

"yawwa baban Mary dama ina so ka shigo in fada maka ina son zanje Abuja cikin week dinnan...."

"lafiya?"

"lafiya lau, ina son inje inga halin da yarona yake ciki da matarsa"

"a wanne dalili? Naga bai dade da zuwa ba kuma ku dinma baku wani jima da dawowa ba, duk wannan zaman da kuka je kuka yi bai isa ya nuna miki irin halin da suke ciki ba har sai kin sake komawa yanzu?"

Cikin faɗa da hargagi kamar yadda ta saba ta dube shi tace" to koma can na koma na tare ai gidan ɗanane ko? Sai me dan ban jima da dawowa ba na koma "

" kinga ki bude kunnenki da kyau kiji abinda zan fada miki, tabbas gidan yaronki ne idan kin koma can kin tare babu wani aibu sai dai ni baza ayi wannan badakalar dani ba dan haka babu inda zakije ko menene ki kirashi a waya kiji, idan kuma ba haka ba kika kuskura kika sa kafa kika bar gidan nan to sai dai ki nemi wani gidan amma banda wannan dan na gaji kuma bazan dauki wannan ba... " jin yadda yayi maganar cikin kakkausar murya yasata shan jinin jikinta dan bai taba yi mata haka ba sai yau saboda shi mutum ne mai mutukar hakuri sannan yana da kawaici ta san tunda taji yace ya gaji to ya gaji dinne kuma da alama tura ta fara kaiwa bango shiyasa ta shiga taitayinta duk da bakinta baiyi shiru ba amma ta cire maganar tafiyar daga ranta sai dai ta nemi wata hayar,haka dai taci gaba da mita shi dai yana jinta bai kara cemata komai ba dan dama ya riga da ya saba da wannan fadan nata na yau da kullum sai dai yafara gajiya lokaci yayi da yake ganin ya dace ya nuna mata karfin ikonsa shima a matsayinsa na mai gida wanda take karkashinsa,

Hakura tayi ta kira samz din ta buƙaci wasu kudade kamar yadda ta saba, bai tambayi dalilin bukatar kudin ko ya jira wani karin bayani ba ya tura mata kudin kamar yadda ya saba dan bata taba tambayarsa yace baida shi ba koda kuwa bashi dashi din saboda ya san duk abinda ya bata ko yayi mata bai faɗi ba haka kuma nasararsa tana da alaka da ita,takanas ta shirya ta je gidan maman Felicia ta sanar da ita halin da ake ciki na cewa daddy fa ya kafa ya tsare ya hanata zuwa ko ina kuma yace zai dauki tsattsauran mataki akanta idan har ta kuskura taje, bayan sun gama jajantawa daga karshe suka tsayar da matsaya guda daya na cewa madam comfort zata koma inda ta karbo maganin inyaso sai a canja dabara.

***

Yau tunda asuba da na hau online naga yaya Abdul hakim ya turo pic din baby ta WhatsApp group din yan gidanmu wai ƙawalli ta haihu misalin ƙarfe 2:30 na dare dama jiya tace min edd dinta ya cika har ta dan gota da kwana biyu kuma har yanzu bata jin ciwo ko alamun komai, wani tsalle naso in tashi in daka amma sai dai babu dama duk da haka ban kasa nuna farin cikina ta wata hanyar ba, samz dake kusa dani kam shagwabe fuska yafara yi saboda zan tafi Kano in barshi, dariya nake ta yi masa harda gwalo, hoton babyn naketa kallo wanda kana gani kasan yan gidanmu ya iyo sambalele dashi,

"baby idan kika je kwana nawa zaki yi?" Ya bukata yana kallona fuskarshi ta nuna alamun wai in tausaya masa, dariya nayi na rungumeshi sosai cikin kirjina nace,

"duk yanda kace my love...
Idanma kace kar naje ai haka zan hakura"

"a'a zaki je but bana son ki tafi ki barni" ya faɗa yana shafa cikina,

"kaima ai zaka je, bazan tafi in barka ba my love...."

"kwana nawa zakiyi?"

"duk yadda kace sweet"

"2 days yayi?"

Murmushi nayi na ɗaga masa kai duk kuwa da nasan kwana biyu yayi min kaɗan tunda harme ma nayi akwana biyu na dawo? Ni ai da gani nake ma sai nafi 2 weeks dan rabona da Kanon anjima,

"yayi miki kaɗan ko?"

"uhmmmm" nace ina ɗaga masa kai, hannuwana ya riƙe duka biyu cikin nasa yana matsawa a hankali,

"to ki faɗa da kanki yanda kike so"

"ni idan yadda nake so ne kawai dai sai ka ganni fa saboda babu rana"

Dariya naga yayi kafin ya girgiza kansa "Haba baby guduwa zakiyi ki barni? I need you"

"to ai kaga na jima fa banga ƴan gida ba"

"Tom shikenan.... Amma keda kika ce da ba zaki je ba sai kin haihu"

"tab dane ai, yanzu na fasa zan je"

"kin zama marar kunya dai yanzu"

Dariya nayi dan ji nake tamkar inyi fuffuke in tashi in ganni acikin Kano, tun daga ranar na fara hada kayana sai kace idan na tafi na tafi kenan shi kansa sai da yace "baby wannan kayan ai yayi yawa

Please Login or Register in order to submit comment