Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register



"Ƙawalli ta faɗa min kuma....." shiru nayi ban ƙarasa ba dan naso in yi suɓutar baki ince Samz ma yace nayi ƙiba akan tsoffin pics ɗin da na tura masa wanda na ɗauka lokacin da na zo Abuja before mu tafi Lagos,

" To kinga ashe ba ma ni kaɗai na gani ba...... "

Murmushi kawai nayi a raina ina sake tuna shi, na san ta dalilinshi ne na samu tarin farin ciki da kwanciyar hankalin da har nake iya cin abinci in ƙoshi wanda har ya sani ƙiba, haka kuma ta dslilinsa ne farin cikin da na rasa ya dawo, ban taɓa sanin na kamu da sonshi har haka ba sai yanzu da na ɗan yi nesa dashi dan bana cikakken mintuna uku sai na tuna shi a cikin raina. Lokacin da muka ƙarasa gidan Anty salla nayi na zauna muna ta hira da ita inata bata labarin Lagos da abubuwan da suka faffaru wurin training,

"Baki bani labarinsa ba shi kuma"

"Waye kuma Anty?"

Dariya tayi kafin tace "Shi ƙanin nawa mana"

"Anty waye ya faɗa miki?"

"Sai an faɗa min? Ai da ganin yanda hankalinki ya kwanta na gane kin samu wani wanda ya iya kula da ke kuma....."

Tashi nayi na gudu bedroom ina ce mata zan bata labarinsa amma ba yanzu ba, sai da nayi wanka na gama shirin bacci sannan na kunna wayata, ina buɗeta massages ɗin Samz suka fara tururuwar shigowa, tun kafin na gama karantawa kuma kiran shi ya shigo,

" Hello Darling...." na faɗa murya ta can ƙasa,

"Yes Sweetie..... Sai yanzu ake samun ki?"

"Yi haƙuri wallahi kana raina..."

"Ya kike? Kin je gida lafiya?"

"Lafiya Lau...."

"I miss you baby...... Kinci abinci?"

"I miss you more..... Na ci ɗan kaɗan"

"why? Bana son kina cin abinci kaɗan baby"

"Kafi son in ci da yawa in yi ƙiba sosai.... Kana ji Anty ta fara cewa nayi ƙiba sosai"

"Nima ai na faɗa miki..... Amma idan kin ƙara kaɗan ki barta haka..... Idan kika yi nauyi da yawa ba zan rinka ɗaukar ki ba...." tun kafin ya ƙarasa na shagwaɓe fuska cikin shagwaɓa kamar zanyi kuka nace,

"Ba zaka rinƙa ɗauka na ba?" na faɗa kamar zanyi kuka,

"Ehh mana, idan kina so in rinƙa ɗaukar ki kar kiyi nauyi da yawa"

"uhmm uhmmm.... Ni dai a'a" ni kaina bana sanin na iya shagwaɓa sai idan ina tare da Samz ban san dalili ba sai in yi ta masa shagwaɓa shi kuma yana biye min yana rarrashi na kamar wata baby koda yake da babyn ma yake kirana,

"ok is alright..... Zan rinƙa ɗaukar ki, har goyaki zan rinƙa yi, ko abinci a baki zan rinƙa baki, ni zan rinƙa yi miki wanka ina shirya ki" jin ya ambaci wanka ya sani faɗin,

"uhmm uhmmm" cikin shagwaɓa,

"Kina jin kunya ko, karki damu kwana ɗaya za muyi tare zaki ji kin daina jin kunya ta"

"uhmmm" na sake faɗi cikin shagwaɓa,

"Hmmmmm baby kenan...." ya faɗa cikin harshen Hausa abin da yayi mutuƙar bani mamaki dan kwata kwata ban san ya iya ba saboda ban taɓa jin sa yayi ba,

"Baby..... Ya za ayi in ganki gobe?" ya sake tambaya ta da hausa,

"Wai dama kana jin hausa?"

Dariya naji yayi kafin ya bani amsa da "Uhumm"

"Ohh Allah shine baka taɓa nuna min ka iya ba.... Allah ya soni ban taɓa gulmarka agabanka ba da hausa"

"Da kin yi ma da sai inji in yi shiru kamar ban ji ba"

"Gobe da yaushe zaka dawo?"

"Ƙarfe 9 na safe"

"ok zuwa yamma dai, za muyi waya duk yadda ake ciki za ka jini"

"ok baby..... Kina jin bacci?"

Kafaɗa na maƙale kamar yana gabana yana kallo na,

"Ni ban gaji da jin muryarka ba...."

"Nima ban gaji da jin taki muryar ba kawai dai bana son in takura miki gashi kin gaji ko..."

"Gajiyar training ce da kuka rinƙa tara mana ita a zaune..."

Dariya naji yayi sannan yace, "Kinga masu miji sun huta yanzu suna can ana rage musu gajiya..... Kema da matata ce da tuni na rage miki ita"

"ka ƙara min wata dai" na faɗa acikin raina a fili kuma ce masa nayi "Dama ana rage gajiya ne? Ta yaya?"

Murmushi yayi "zan gwada miki amma ba yanzu ba, sai mun zama abu guda"

"to shikenan, zan jira"

"kiyi bacci ki huta, oya close your eyes...." a hankali na lumshe idanuwa na ina sauraren kalaman da yake faɗa min ban san lokacin da bacci ya kwashe ni ba ko addu'a sai da na farka misalin ƙarfe 2:30 nayi fitsari nayi alwala sannan nai addu'ar na sake kwanciya babu ɓata lokaci wani baccin yayi gaba dani ban sake tashi ba sai bayan asubah, 6 na safe ina tuƙunƙune amma ba bacci nake yi ba naga kiransa, tsokana ta ya fara yi wai jiya bacci babu sallama, baki na turo masa da yake video call ne yana ganina ina ganinsa,

"Ba Kaine ba ka sani baccin dole...." dariya yayi ya shafa sumar kan shi ya kalleni da wannan shanyanyun idanuwan nasa masu ɗaukar hankali,

"ke ki godewa Allah ma kina iya bacci da zarar kin kwanta, ni duk abin da zanyi bana iya bacci sai after 2 wani lokacin ma har 4 idona biyu"

"me yasa?"

"kawai na riga da na saba ne tunda jimawa" kwanciya ta na gyara na kalleshi sosai,

"to me kake yi?"

"just Games, watching movies etc" ya faɗa yana yimin murmushi araina nace daɗin musulunci kenan da ace musulmi ne ya samu wannan damar da sai yaita sallolinsa da karatun Alqur'ani tunda har asuba yake kaiwa wani lokacin baiyi bacci ba,

"Amma kuma kaje asibiti kaga Dr?"

"yeah naje, babu wani problem fa lafiya ta ƙalau"

"Ai kuwa akwai matsala, yanzu da kana da mata ya kenan?"

"Babu baccin dare, zaki yita tayani hira har lokacin baccina yayi sai muyi baccin tare..."

"uhmm... Uhmm.... Nidai baccina zanyi in barka"

"ai kuwa baki isaba.... Kema hana ki bacci zan yi"

"Za mu gani ai"

"ki dai shirya dan babu baccin dare sai baccin safe"

"wai kai dan baka yi shikenan kowa ma ba zai yi ba? Ni zanyi bacci na kai kuma zaka yita games ɗinka da kallon films har lokacin baccinka yayi"

"No, wannan ai lokacin da nake ni ɗaya ne babu abokin hira, amma idan muka yi aure ai kinga na samu abin da yafi Games da Films ɗebe kewa"

"nidai a'a"

"To shikenan na yarda zaki yi bacci tun 8... Ba zan hanaki ba"

"yawwa ehh"

Dariya yayi yace wai zanyi bayani, har 8 muka kai muna hira kafin muka yi sallama na sake komawa bacci, sai after 10 na tashi nayi wanka na shirya na san yanzu Samz ya sauka, text massage na tura masa ina tambayarsa ko ya sauka, reply ya dawo min dashi yace ehh bai kirani bane dan baya son ya tasheni a bacci, murmushi nayi na zauna dan yin breakfast wadda mai aikin Anty ta haɗa saboda ita yanzu cikinta ya fara girma ba kowanne aiki take yiba. Tun ƙarfe 3 nake tunanin ta yadda zan tunkari Anty da maganar fita dan munyi da Samz cewa zamu haɗu around 4 o'clock sai dai ban san ta yadda zan faɗawa Anty ba dan nasan a yanzu dai ba kowane zai fahimce ni ba duk wadda yaji ina soyayya dashi a matsayinsa na wadda ba musulmi ba fassara ɗaya za ayi mana cewa iskanci muke kawai wannan fassarar na daɗe da saninta acikin ƙabilar Hausa Fulani duk lokacin da saurayi musulmi ke soyayya da yarinyar da ba musulma ba kallon ɗan iska ake yi masa to nima na san duk wanda ya ji kallon da zai yi min kenan kaɗanne zasu yi wa lamarin kyakkyawar fahimta shiyasa da ya nemi da in bashi address ɗin gidan Anty akan wai shi zai zo har gidan naƙi nace mu haɗu kawai a inda yace da farko,

Bedroom ɗin Anty na shiga duk da ban san ƙaryar da zanyi mata ba domin ba halina bane kuma ban saba ba, tana kwance tana duba wani kundi (Nigerian constitution), zama nayi gefen gadonta,

"Anty sannu da hutawa"

Ajiye littafin tayi ta kalleni fuskar ta ƙunshe da murmushi,

"Yawwa Widat, ya akayi?"

"Anty ina so ne zan fita...."

"Ina zaki je?"

"Dama Anty wani ne da muka haɗu dashi a wurin training ɗin nan to wai yana son yazo wurina ni kuma bana son yazo yanzu shine sai nace masa zan je saloon dama yau to za mu haɗu acan...."

"Widat kenan.... Ai darajar budurwa saurayi ya taka ƙafa da ƙafa yaje gidan su ba wai su rinƙa haɗuwa a waje ba amma ku ƴanmatan yanzu ban san menene matsalar ku ba bakwa son hira a gida sai dai wuraren shaƙatawa..... Shikenan tunda ɓoye mana shi akeyi wata rana dai dole mu ganshi idan auren ya taso"

Dariya nayi na tashi na fita naje na sake shiryawa na fito nayiwa Anty sallama na fita bayan tayi min jan kunne da gargaɗi akan in kula kuma in dawo before 6,saloon na fara zuwa aka wanke min kaina aka gyara tun lokacin da aka fara yimin gyaran gashin muke chaten da Samz ina faɗa masa shagon yace yasan wurin, alert na gani na 50k da nayi masa magana sai cewa yayi wai kuɗin saloon ɗinne, gyara rolling ɗina nayi na fita daga shagon bayan angama min, ina fita na ganshi tsaye daga gefe ya sha p cap yana latsa wayar shi na ganshi sarai amma sai nayi kamar ban ganshi ba na wuce,

"Hey baby...." ya faɗa tare da biyo bayana, ban kula shi ba nayi gaba na cigaba da tafiya ta dan har ga Allah banji daɗin kuɗin nan da ya sake turo min ba me hakan yake nufi? Dab dani yazo muka jera amma ban ko kalleshi ba, a ƙafa muke tafiya har muka ƙarasa wani ɗan ƙaramin wurin hutawa, ganin inata fushi na ƙi kula shi ya sa shi niyyar sake tsokanata, yarinyar da ta kawo mana drinks da snacks ɗin da yayi order yake yiwa magana wai kitsonta yayi masa kyau, harara nake aika musu daga shi har ita kamar idona zai fito waje, hannuna naji ya riƙo bayan ta tafi,

"Am sorry baby....." ya faɗa yana murza ƴan yatsuna, wata hararar na sake aika masa amma duk da haka bai saki hannun nawa ba saima sake damƙeshi da yayi wanda hakan yayi daidai da shigowar............



*Garin dadi littafin kudi ne ga mai bukatar cigaban labarin sai ya tura 500 ta 0774712835 Aisha Ibrahim Access Bank sai a tura evidence of payment ta wannan no 07044644433 ko a tura katin waya da shaidar biya wannan no 07044644433*



_*Ummi Shatu*_👌🏻
[1/5, 12:43] Maman K: ©️ *HASKE WRITERS ASSOCIATION*
_(Home of expert & perfect Writers)_




*GARIN DAƊI.........!*💍💍




_*NA*_


*_UMMI A'ISHA_*



*Wattpad:ummishatu*



19


*Ina kuke manyan mata ƴan ƙwalisa ma'abota son gyara da kece raini, maza ku garzayo ku nemi maman Maryam domin samun lafiyayyu kuma haɗaɗɗun Lagos lace wanda zaku iya samun ɗinkakku da kuma sabbi a ledarsu, kaya iya zaɓinki, gefe ɗaya muna da GHT product, zaku samu,*

~MAI DA TSOHUWA YARINYA

~FEMALE CARE

~REODEO

~VIGOR MAX

~ LONGZIT

~B CLEAR

*DUK ZAKU SAMU WADANNAN KAYA CIKIN SAUKI DA RAHUSA MAZA KU NEMI MAMAN MARYAM AKAN WANNAN NO 07080222187, SIYAN NA GARI MAIDA KUƊI GIDA.....*


~~~Jin abinda nace yasa shi yin murmushi kafin ya ɗauke idonsa daga kaina yana kallon wani wuri, zuba masa ido nayi ina kallonsa, sai yanzu na san inda asalin kyau yake, ada ina yiwa Hashim kallon kyakkyawa sai yanzu na gane ashe nayi kuskure a baya domin ga inda asalin kyawun yake wurin samz dan hatta ƙwayar idonsa kaɗai mai mutuƙar ɗaukar hankali ce, idanuwan nasa gaba ɗaya kuwa sexy eyes gareshi ma'abota kyau da sanya shauƙi, shi dai ba fari bane haka kuma ba za asa shi sahun baƙaƙe ba, ganin zai juyo gare ni yasa ni saurin ɗauke idona daga kansa,

"Mommy na ke son in auri Felicia..... Duk da a karon farko ni na ganta ina so amma daga baya sai na ji ta fita daga raina.... Amma ita mahaifiyata har gobe tana son in aure ta nikuma na faɗa mata ba zan iya auren ta ba...." sai lokacin na ɗaga idona na kalle shi jin abin da yace,

" To amma me yasa ka fara sonta a karon farko daga baya kuma ka sauya ra'ayinka?"

" Da farko tabbas nine na ganta ina sonta kuma har na faɗa mata muka fara soyayya na kai ta gidanmu na gabatar da ita sai daga baya na gane ba matar aure na bace...."

"Me yasa ta zama ba matar aurenka ba?" na sake tambayarsa har lokacin idona na kansa,

"Lesbian ce...."

"Ya aka yi ka sani?"

Murmushi naga yayi sannan ya sunkuyar da kansa ƙasa ya ɗago yana kallo na,

"baby kin san wani abu? Zaki yi kyau da Barrister" murmushi nayi nima na bashi amsa da,

"to ai brothers ɗina gaba ɗaya da elder sister ɗina lawyers ne...... Mu 3 ne kaɗai muka saki layi"

"ke ai computer guru ce..."

"ka fini iyawa ai.... Baka bani amsar tambaya ta ba"

"uhmmmmm...... Muna tare da ita sai na fara noticing wasu abubuwa atare da ita.... Sai inga pics na mata a phone ɗinta daga ƙarshe bakina da nata ta faɗa min tana yi kuma wai gaskiya bata jin zata daina sai dai muyi aure a haka.... Har fa wani state ɗin take tafiya yawo wurin mace, ba zan iya auren macen da take aikata irin wannan abun ba "

Nidai har ga Allah ban taɓa sanin akwai masu hankali a addinin su samz ba kamar haka,

" Wannan shi ne dalilin da yasa ka rabu da ita? "

" Shine kaɗai dalili...... Bana son mace mai bin maza ko mata "

" Kai baka yi? " na tambaye shi dan kore zargi domin inata wasi wasin ko yana neman mata ko baya yi ko yana shan giya ko ba yayi,

"What?" Shima ya buƙata,

"Dan Allah kar ka ɗauki magana ta da wata manufa.... Kana shan giya ko baka sha sannan kana kula mata ko baka yi?"

Shiru naga yayi ya zuba min ido wanda har sai da naji ina ma banyi masa tambayar ba araina dan ta yuyu ko ta ɓata masa rai,

"kayi haƙuri idan har tambayata ta ɓata maka rai...."

"No baby..... Baki ɓata min rai ba kawai dai ina farin cikin samun kamilar mace ne.... Ban taɓa kula matan banza ba kuma ba na shan giya...."

Ajiyar zuciya na sauke jin amsar da ta fito daga bakin sa, hannunshi na kalla da har lokacin ke rike da nawa,

"ka sakar min hannu mana...."

"am sorry....." ya fada ba tare da ya saki ɗin ba,

"I want to kiss you......." wani mugun kallo na yi nasa sannan na fincike hannuwana na miƙe ina gyara mayafin kaina, afusace na kai hannu zan ɗauki handbag ɗina amma yayi saurin riƙeta,

"Haba baby me nayi? Kiyi haƙuri"

"ohh tambaya ta ma kake yi abin da kayi? Ai ban san wannan shi ne dalilin da yasa ka ɗauko ni ka kawoni nan ba, yanzun nan ka gama faɗa min wai kai baka bin matan banza ashe you are a professional liar"

"am very sorry..... Ba abin da nake nufi ba kenan"

"Ka bani handbag ɗina zan tafi"

"am sorry baby, ki zauna mu ƙarasa magana..... Ba zan sake ba pls forgive me, i won't misbehave again i beg" ya ƙarasa maganar yana haɗe hannuwansa wuri guda alamar roƙo da neman afuwa, tsaye nayi kawai ni ban tafi ba kuma ban zauna ba, miƙewa tsaye shima yayi yana kallo na, ni kam nabi na haɗe rai na tamke girar sama da ƙasa kamar ban taɓa dariya ba,

"am soo sorry baby....." ya sake faɗa yana riƙo hannuna, zama nayi ba tare da na kalleshi ba,

"pls smile.... Ki daina fushi haka"

Shiru ne ya ɗan ratsa kamar na minti biyu kafin naji yace,

"baby how old are you?" ɗan kallonsa nayi muka haɗa ido dan shi ɗinma ni yake kallo,

"kai zaka fara faɗar naka...."

"amma ai ni na fara tambaya"

"uhmmmm" na ɗaga masa kai,

"ok, well.... Am 34 going to 35 nan da 4 months"

"ashe ma ka tsufa" na faɗa cikin tsokana amma sai na fuske kamar maganar ba daga bakina ta fito ba,

"dagaske na tsufa? Zan so mu raba tsufan tare" ya faɗa yana murmushi,nima murmushin nayi,

"Daga nan idan angama training ina zaki tafi? Kano?"

"no, Abuja zan koma ta can zan wuce Kano"

"Ok, zan ganki a Abuja ɗin before ki tafi"

"babu problem"

"amma idan kika koma gida zan rinƙa samun ganin ki? Ba zan iya 2 weeks ban ganki ba" ya faɗa cikin langaɓar da kai alamun ban tausayi kuma dagaske ya ban tausayin dan na fahimci da gasken gaske yake sona ssɓanin ni da nake son sa sama sama amma shi son da yake yimin irin na do or die ne,

"Karka damu zaka rinƙa ganina duk lokacin da ka so...."

"Naji daɗin haka..."

Mun jima sosai muna hira yana bani labarai daban daban wadanda wasu sun shafi rayuwarsa, har ɗan bakin ruwan nan ya rakani za ayi min hoto, takalma na na cire na sa ƙafa ta guda ɗaya tamkar wadda aka jonawa lantarki haka naji an fisgoni ga wani uban shock dake neman jana cikin ruwan ai babu shiri na riƙoshi bama ƙaramar riƙewa ba dan ƙanƙameshi nayi na rufe idona gam ni kaina ban san ina tsoron ruwa ba har haka sai yau dan har kaina ya soma juyawa ina jin jiri yana ɗaukana kamar zan faɗi kawai hango girma da yawan ruwan nake yi, ashe daga nesa ne yake burge ni yanzu kuma da na zo kusa dashi sai naji ya tada min da hankali, kasa tafiya nayi sai rawa da jikina ke yi kamar ana kaɗa min mazari idanuwa na a rufe gam, ganin kamar bana cikin hayyacina ya sashi sunkuyawa ya ɗaukeni kamar wata baby zuwa gefen ruwan, ni kam ban ma san ya ɗaukenin ba sai ƙara ƙanƙameshi da nayi kamar rayuwa ta tana manne dashi, tsawon mintuna biyar ban dawo cikin hayyacina ba, a hankali na fara buɗe idanuwa na ina salati har na buɗesu gaba ɗaya akanshi dake durƙushe yana riƙe dani,

"Am sorry baby na kawoki wurin da bakya so"

Girgiza kai nayi ina ƙokarin raba jikina da nasa, "Karka damu ina son wurin... Kawai dai ban taɓa shiga ruwa bane"

"Kar ki damu next time idan mun dawo zaki shiga kuma ba zaki ji tsoro ba..... Ni ina son ruwa sosai dan har swimming nake yi"

Zaro ido nayi ina kallonsa kafin na miƙe "nikam duk ranar da na shiga ina jin mutuwa zanyi dan tsoro nake...."

"Babu abin da zai sameki ai tare zamu shiga and i will stay by your side...." duk da ya faɗi haka ji nake kamar ba zan iya ba nikam, fara tafiya nayi na barshi nan durƙushe yana kallo na ƙafa ta babu takalmi, wurin da takalman mu suke na nufa na saka nawa na rataya handbag ɗina ina jiran sa yazo mu tafi, sai da ya gama ɗaukata a hotuna ni ban san yana yi ba sannan ya taso yasa takalminsa tare da riƙo hannu na, kallonsa nayi alamar tuhuma amma sai ya ɗauke kai ya fara tafiya yana jana nan nabi bayan sa, da yake magrib ta yi saura ƙiris shiyasa wurin yayi wahalar abun hawa dan bamu samu drop ba sai taxi ɗin da ta cika babu space sai na mutum ɗaya lallai sai yau na san na zo Lagos dan yawancin yan matan da suka zo wurin da samarin su kan cinyar samarin suka hau muma kuma hakan ake so muyi araina nace ashe zan kwana anan, sanin da samz yayi na ni ba zan iya hakan ba sai yace in shiga in tafi shi zai taho, girgiza kai nayi nace nidai nafi son mu tafi tare dole muna ji muna gani wannan taxi ɗin ta tafi bayan wasu sun shiga, a ƙafa muka fara tafiya jin ya sake kama min hannu ya sani fincikewa cigaba da tafiya muka yi amma ganin babu haza ni da kaina na kama hannun sa na riƙe da hannu biyu murmushi yayi yace,

"Ba dai bakya jin magana ba, waye ya faɗa miki nan Kano ne, you must hold my hand whether you like it or not....." baki na turo masa ina kallonsa,

"what eva...." ya faɗa yana kallo na bayan ya ɗaga kafaɗa, sai da muka yi ƴar tafiya sannan muka samu taxi itanma kuma a cike cewa yayi kawai in shiga gaba in tafi ni ɗaya amma na maƙale kafaɗa,

"mu tafi tare..." na faɗa ina kalle kalle dan tsoro nake ji in shiga wannan motar cike da maza da mata ba su fi biyu ba ni ɗaya kar aje a sace ni,

"ok muje...."

Shi ya fara shiga kafin ni, zaman dai duk a takure dan abin da bana so ɗin dai babu yadda na iya dole sai da jikina ya mannu da nashi,ni jina nake kamar akan ƙaya amma shi ya ciro wayar shi yana kallon ball alamar ma abin ko a jikinshi, har masaukinmu ya kai ni sannan ya wuce, ina shiga anty Salma tace yanzu take shirin kirana ta jini shiru ga magriba tayi, zama nayi na fara bata labarin ruwan da ya tsorata ni yau, dariya ta rinƙa yi tana cewa anya kuwa za a kai ni ƙasar Turai honey moon.

Mun jima muna hira da anty Salma yau dan har wurin 10 muka kai, shirin bacci nayi na janyo wayata da yake tana silent miss calls ɗin samz na gani sai na yaya Abdul Rashid duk ciki babu wanda nabi dan naga dare ya fara yi, kashe wayar nayi na kwanta, abubuwan da suka faru ɗazu sune suka fara dawo min, hirarmu da samz da lokutan da muka ɗebe tare, dan so kam ina sonshi har cikin raina fiye da yadda naso kowanne saurayi a baya asali ma sonshi ne ya mantar dani son kowanne namiji sai shi ɗaya, begen sa da tunanin sa fal raina nayi bacci. Shirye shiryen tafiya muke ta yi dan mun gama training sai aiki da za mu kama bayan mun koma gida munyi hutun sati biyu, kasuwa muka shiga nida anty Salma muka sha siyayyar tsaraba, Mama, Annie, ƙawalli dasu Islam yaran anty duk babu wanda ban yi wa tsaraba ba ita kuma anty na siya mata dogayen riguna na shan iska wanda zata yi renon cikinta dashi agajiye lis muka dawo dan ba ƙaramin yawo muka yi ba, rabona da samz kuwa tun shekaran jiya da aka gama training dan jiya da yau duk mun fita nida Anty Salma wadda keta alla alla agama training mu tafi taje taga yaranta dan bata da aiki sai kallon hotonsu da yin waya dasu ta rinƙa tambayarsu ɗaya bayan ɗaya yau me da me suka yi, wani lokacin zama kawai nake yi inyita kallon ta idan tana waya dasu araina ina cewa watakila nima wata rana haka zanyi, koda wa zanyi auren har in haihu Allah kaɗai masanin gaibu, wataƙila da samz, duk lokacin da na tuna hakan sai in yi murmushi araina ince da zan samu beautiful kids in dai samz ne ubansu waɗannan idanuwan sune ke shagaltar dani idan ina kallonsa, zan so in haifi yara masu da kama dashi idan har Allah ya ƙaddara tarayyarmu matsayin miji da mata, washe gari zamu tafi amma jirgin ƙarfe hudun yamma zamu bi, bayan na gama shiryawa misalin 11 yazo muka fita inata faɗa masa nidai kar ya kai ni wurin ruwan nan dan bana so, dariya yake yimin wai yau zai koya min ruwa daga yau na daina tsoron ruwa, kama ni yayi muka shiga cikin jirgin ruwan matuƙin ya tashe shi muka fara tafiya a hankali, hannaye na cikin nashi yana faɗa min irin girman son da yake yimin har ga Allah ban san mun zo tsakiyar ruwan ba domin kalaman da samz ke sanar dani masu zaƙi fiye da zaƙin zuma, ina kallon gefena naganmu a tsakiyar ruwa falala sake maƙale hannun sa nayi ina ƙokarin matsawa kusa dashi, duk da a tsorace nake haka na daure muka je ƙarshen ruwan muka sake dawowa,

"Dan Allah kar ki braking

Please Login or Register in order to submit comment