Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yanzu. Kai tsaye wani babban shago na wuce na fara yi musu siyayya, buhun shinkafa, taliya, macaroni, mai ƙaramar jarka, maggi, gishiri, duk wani nau'in kayan abinci sai da na siya musu na fito da atm card ɗina aka cire kuɗin sama da dubu arba'in, wayata na duba naga anty ta turo min sunan drugs ɗin nan na shiga pharmacy na siya masa na haɗa masa da drinks, napep na ɗauka ya kaini gidan sannan ya taimaka min ya shigar min da kayan ciki lokacin ana ƙoƙarin kiran sallar magriba, har lokacin suna zaune tsuru cikin yunwa, ganin wannan kayan iya ta fara salati tama rasa irin godiyar da zata yi min nace babu komai su godewa Allah domin shine ya basu ba ni ba, fito da drugs ɗin nayi na miƙa mata nayi mata bayanin adadin yanda zai sha idan yaci abinci wanda tuni wannan budurwar da naji iyan ta kira da Amira tana can tana ƙoƙarin ɗora musu, ganin magriba tayi ya sani yi musu sallama na tafi suna ta yi min godiya, ni kuma ina ta jin daɗi acikin raina domin na yaye musu damuwa da ƙuncin da suka wuni aciki, tun jiya rabonsu da abinci suna zaune cikin yunwa kuma dama abbanmu kullum maganarshi akanmu mu yawaita sadaka da taimako da albashinmu, kar mu yadda mu ɗauki salary har yaƙare ba mu cire wani abu mun yi sadaka ba shiyasa duk lokacin da na ɗauki albashi sai nayi canji ƴan hamsin hamsin na dubu biyu na rabawa mabuƙata dake hanyar zuwa wurin aikina, bama ni kaɗai ba ku san duk ƴan gidan mu haka suke domin abba ya jima yana karantar damu falalar ciyarwa da sadaka saboda kowanne azumin duniya kullum sai an dafa abinci rabin buhu banda ƙosai da kunu duk na sadaka ne. Bayan na koma gida yaya faisal ya kirani mun ɗan sha hira kaɗan ya soma tambayar wai size ɗin takalmi na domin lefe na ya gama haɗuwa saura ƙiris kuma nan da wani watan may be za akawo, faɗa masa nayi muka yi sallama ina jin wani sabon tunani yana ziyartar zuciya ta................ ✍🏼




*_Ummi Shatu_*👌🏻
[1/5, 12:43] Maman K: ©️ *HASKE WRITERS ASSO*
_(Home of expert & perfect writers)_



*GARIN DAƊI......!*💍💍



*_NA_*


*_UMMI A'ISHA_*



*5*


~~~Sama sama nayi bacci ranar sakamakon tunane tunane da na kwana dasu fal raina, babu kalar tunanin da banyi ba akan aurenmu da yaya faisal,washe gari haka na tashi duku duku duk bacci bai isheni ba na kammala shirina cikin haɗaɗɗiyar jar gown wanda tasha adon stones, duwatsunne suka sake ƙara mata kyau tare da bayyanar da tsadarta, kamar koda yaushe rolling nayi da ɗan mayafin rigar bayan nasha turaruka masu sanyin ƙamshi. Saboda saurin da nake yi na inje in duba hashim yau ko breakfast banyi ba hakanne yasa Annie mita tana ta faɗan wai bana son cin abinci, ina ƙoƙarin fita kiran yaya faisal ya shigo cikin wayata, gaisawa kawai muka yi na sanar dashi cewa zan kirashi idan na ƙarasa office,

Yau ma napep na shiga kamar koda yaushe, gidansu hashim ya ajiyeni na biya shi kuɗinsa na shiga cikin gidan bakina ɗauke da sallama yayin da farin ciki ya cika zuciya ta wanda ba zai misaltu ba, kamar jiya yau ma suna zaune cikin ƴar ƙaramar runfarsu shi kuma yana kwance kan tabarma, cike da fara'a dukkaninsu suka amsa sallama ta, tun kafin na ƙaraso iya ke cewa Amira tayi gaggawar ɗauko tabarma ta shimfiɗa min, hakan kuwa akayi,

"lale marhabun, lale da maimunatu..... Yanzu kike tafe?" Iya keta faman faɗa cikin farin ciki,

"wallahi iya, ina kwana ya me jikin kuma?" na faɗa kaina a ƙasa cikin girmamawa,

"lafiya lau maimuna, ya mutanen gidan naku? Me jiki da sauƙi sosai, mun gode fa, mun gode Allah ya saka miki da alkhairi"

Murmushi nayi ina amsa gaisuwar Amira wacce ta tsugunna kusa dani tana gaisheni,

"Amira yi maza ki ƙarasa girkin mana ki zubo mata...." iya ta faɗa yayin da take ƙoƙarin shiga ɗaki, sai lokacin na maida hankali na kan hashim wanda ke kwance yana sauraren dukkan abubuwan dake wakana,

"barka da zuwa ranki ya daɗe...."

"sannu.... Ka tashi lafiya, ya jikin?" Na faɗa ina murmushi,

"lafiya lau, jiki kuma ai tuni ya samu lafiya tun lokacin da kika bashi magani..."

"ohh nice ma na bashi maganin?"

"kece mana..... Maimunatu haƙiƙa ban san da waɗanne irin kalmomi zanyi amfani wurin gode miki ba, tabbas ke WANI HASKE ce acikin rayuwa ta wadda nake sa ran zata magance min duk wani duhu dake lulluɓe dani...."

Jin kalamansa ya sani ƙura masa ido ina kallonsa tsawon mintuna daga bisani nayi murmushi nace,

" ba godiyarka nake buƙata ba hashim, Allah ya kamata ka godewa, tun da har nayi maka abunda kaji daɗi ai nima ban san ta inda Allah zai yi min sakayyar kyautata makan da nayi ba, karka damu wannan ba wani abu bane....."

"hakane.... Sai dai duk da haka bakina ba zai gushe wurin yi miki kyakkyawar addu'a ba, Allah ya saka miki da mafificin alkhairi....."

"amin yaya hashim" Amira ta amsa wadda zuwanta kenan tana ƙoƙarin ajiye min abincin da ta zubo min cikin wata madaidaiciyar silver mai murfi,

A zahirin gaskiya bani da sha'awar cin abincinsu amma saboda gudun kada su ji babu daɗi sai na buɗe nasa spoon ɗin da aka ɗoro min akai na fara ci, jalop ɗin taliya ce wadda tasha manja, ina ci muna hira da hashim har na ɗanci irin cin da ba zasu ga kamar na raina musu ba,

Sallama nayi musu domin zan wuce office, iya da Amira rakiya har ƙofar gida har sai da suka ga na samu napep na hau sannan suka koma muna masu ɗagawa juna hannu.

Misalin ƙarfe biyar na yamma na tashi daga office kai tsaye gidan su hashim na nufa bayan na tsaya wurin masu fruits na siya masa ayaba, da kankana da apple harda abarba, lokacin da na shiga gidan yana zaune yana shafa mai da alama wanka ya fito, ita kuma Amira na zaune gefensa riƙe da littafin akhdari tana biya masa yana gyara mata abin da yayi mutuƙar bani sha'awa kuma ya ƙayatar dani, yanzu ace makaho yana da wannan ilmin shida bai da ma ido to kai da kake da lafiyar ido kake gani tangararau wacce hujja zaka bada na rashin neman ilmi alhali annabi yace neman ilmin farilla ne akan dukkan musulmi? Zama nayi fuskata ɗauke da murmushi,

"sannu da zuwa anty Maimunatu" Amira ta faɗa tana bani wurin zama,

"yawwa Amira, ina iyan fa? “

" yanzun nan ta shiga maƙota amma ba jimawa zata yi ba "

" malam sannu da ƙoƙari.... Ashe muna tare da shehun malami, to ka shirya samun ƙarin ɗalibai ciki kuwa harda ni "

" wane ni, ina marar ido zai koyar da mai gani, ai iliminki yafi nawa ranki ya daɗe, ke ga arabi ga boko duk kin haɗa nikuwa kame kame ne kawai "

"duk da haka kai malami na ne, sai dai kawai idan ba zaka koyar daniba sai in haƙura"

"ni na isa, kaina bisa wuyana ranki ya daɗe"

Cikin wasa da barkwanci muka ɗan shafe lokaci muna hira har iya tadawo ta iske mu, ganin irin hidimar da nayo na kawo ya sanya ta rike baki tana faɗin wai ni bana gajiya ne, nan nace babu komai ai yi wa kaine daga ƙarshe nayi musu sallama na tafi nan Amira tabini ta rakani har titi.

Tsawon kwanaki biyar hashim ya ɗauka a gida yana rashin lafiya nikuma kullum sai naje gidan nasu safe da yamma har ya samu lafiya ya warke ras, nan muka cigaba da fita tare sannan kuma mu dawo tare hakan shi ya sake haifar mana da matsananciyar shaƙuwa a tsakanin mu, mun shaƙu ƙarshen shaƙuwa, nikuma na tsaya tsayin daka wurin ɗauke duk wata wahala tasa da ta gidan su, duk ƙarshen wata da zarar an yi salary zan je nayi musu siyayyar kayan abinci da dukkan kayan buƙatunsu na yau da kullum hatta sabulun wanka da omo sai na siya musu, hashim kuwa sittirar da zai saka ma nice ke siya masa kai daidai da ruwan sha wannan na hashim sai na siya masa saboda gujewa haɗarin kamuwa da cutar typhoid domin an ce tana dab da ta kama shi, wannan dalilinne yasa yanzu salary ɗina baya zama saɓanin da, kuma har yau ɗinnan na kasa sanarwa da kowa. Yau dai kam cikin nishaɗi na wuni sakamakon hirar da muka yi da hashim da safe lokacin da zamu fito ni zan zo office shi kuma zai je school,

"Maimunatu ba dan kar na zaƙe da yawa ba, ko kuma kar in yi kasada da nace wani abu.... Sai dai kuma bai kamata in faɗa ba duba da ko ni waye da kuma matsayina..... Ni bani da ido amma na jima ina dakon wani kaya mai nauyi acikin zuciya ta"

"hashim nifa raina yana ɓaci idan naji kana maganar idon nan, wai me kake nufi ne? Kawai ka fito ka sanar dani abin da ke ranka"

Murmushi yayi ya shafa haɓarsa,

"Maimuna tun ranar da na fara jin muryarki naji gabana ya faɗi, zuciyata ta buga da ƙarfi....... Tun daga ranar nake jin kamar bazan iya rayuwa ba idan babu ke.... Wallahi ina jin matsananciyar ƙaunarki acikin raina..... In short dai ni hashim ina son ki..... "

Shiru nayi kawai ina kallonsa na tsawon mintuna ba tare da nace wani abu ba hakan yasa shi ɓata fuska sannan cikin rashin walwala yace,

" kiyi haƙuri na san tsaurin ido nayi domin matsayina bai kai ba..... Wallahi sharrin zuciya ne da take kamuwa da son wanda ba sa'anta ba...."

"hmmm hashim kenan..... Ka daina faɗin haka, shi so babu ruwansa da ido, ko ji ko kyau, faɗawa cikin soyayya ta da kayi hakan ba tsaurin ido bane kamar yadda kake tunani..... Nima ina son ka"

Take ɓacin ran dake kan fuskar sa naga ya washe farin ciki ya maye gurbinsa, shiyasa cikin farin ciki muka rabu, nidai hashim yayi min domin ya iya kalamai masu sanyawa mace nutsuwa sannan baya ga makantar da ke tare dashi bai da wani makusa, shiyasa babu wata wata muka tsunduma kogin soyayya muka fara linƙaya muna gudanar da soyayyarmu cike da burgewa.

Yau dai na ƙuduri niyyar sanar da ƙawalli dan jin ra'ayinta wannan dalilinne yasa nayi tattaki ƙafa da ƙafa naje har gidan su na sameta,

Kwance na sameta tana karatun novel dama ƙawalli badai karance karance ba,

"wannan karance karancen naki ya kai yanzu ace kin zama marubuciya...."

Zaune ta tashi tana murmushi,

"Kisha kuruminki nan bada jimawa ba zan zama ƙwararriyar marubuciya tamkar phertymah Xarah ko Ayusha Mohd"

Dariya nayi sannan nace "ya dai kamata, yanzu dai na zo miki ne da wani labari ƙawalli, ki tayani ganin abin da ya dace, nayi sabon saurayi kuma wallahi ina jin sonsa a raina fiye da duk wani ɗa namiji....."

Tagumi tayi tana kallona tana sauraren labarin da nake bata na tun farkon haɗuwata da hashim har kawo yanzu............... ✍🏻



*Garin daɗi na kudine ga mai bukatar cigaban labarin sai ya turo 500 ta 0774712835 Aisha Ibrahim Access Bank sannan a tura shaidar biya ta 07044644433 ko kuma katin waya da shaidar biya ta wannan no 07044644433*



*_Ummi Shatu_*👌🏻

[1/5, 12:43] Maman K: ©️ *HASKE WRITERS ASSO.*
_(Home of expert & perfect writers)_




*GARIN DAƊI........!*💍💍


*_NA_*


*_UMMI A'ISHA_*


*Wattpad:ummishatu*




*6*




~~~Tagumi kawai ta rafka tana kallona batare da ta furta ko kalma ɗaya ba har sai da na gama bata labarin komai sannan ta sauke ajiyar zuciya mai ƙarfi ta janye tagumin da tayi ta kalleni fuskarta babu fara'a tace,

"maganar gaskiya widat banji daɗin wannan labarin naki ba sam..... Ta yaya za ki bari sheɗan yayi wasa da tunaninki, kinfa sani sarai cewar an yi miki miji sannan an bada ke, kin manta da maganar aurenku da yaya faisal ne? Wannan abun da kike yi kuskure ne kuma ya kamata ki farga, ko a shari'a babu kyau neman aure akan nema, tun wuri kiyi gaggawar fatattakar wannan mummunan lamarin tun kafin gida su sani nidai shine kawai shawararar da zan iya baki..... "

" ƙawalli da alama har yanzu baki fahimce ni ba.... Wallahi Allah shine shaida dama ban taɓa jin son yaya faisal acikin raina ba kuma kema kin sani saboda nasha faɗa miki, to yanzu Allah ya haɗani da irin wanda nake so saboda ni dama na fi son na auri mutumin da ya kwanta min har cikin raina ba wai irin yaya faisal ba wanda daidai da rana ɗaya ban taɓa jin sonsa ba.... "

Jin abin da na faɗa ya sanya Maryam zuba min idanuwanta gaba ɗaya tana kallona dan tama rasa abin da zata ce sai zuwa can tace dani,

" kiyi ta addu'a ƙawalli.... Dama idan aure yazo sometimes irin haka na faruwa, shaiɗan sai yayita ƙoƙarin shiga cikin lamarin dan ta wargaza komai yaga ba ayiba amma idan aka dage da addu'a sai kiga Allah ya daidaita komai..... Allah ya kyauta"

"amin ƙawalli na gode, bari naje gida dan kofa wanka banyiba na fito dan na zo na sanar dake..."

Tare muka rankaya zuwa gidan mu har wurin 8 muna tare sai lokacin na rakata ta tafi bayan ta yi min gargaɗin wai kar na kuskura na bari yaya faisal ko gida su fahimci maganar nan, da to kawai na bita domin maganar gaskiya yaya faisal ya jima da fara fahimtar akwai abin da ke faruwa ina jin wannan dalilinne ma yasa ya ɗan ja baya da kirana kuma da alama kamar fushi yayi dan yau kusan kwana shida kenan bai kirani a waya ba.

Zaune nake ina nazarin wani manual na na'ura mai ƙwaƙwalwa bayan nayi shirin bacci cikin riga da wando masu santsi light blue, jin ƙarar wayata ya sanya ni kallon agogon jikin wayar ƙarfe 11:30 na dare abin da yayi mutuƙar bani mamaki kenan saboda ganin kiran yaya faisal mutumin da ya shafe kusan wata bai nemeni ba nima ban nemeshi ba har yau ɗinnan da ya kirani, ɗagawa nayi ina son jin da wacce yazo, cikin taushin murya naji sallamarsa nan na amsa bayan na kishingiɗa na kuma rufe jibgegen littafin dake gabana,

"widat a haƙiƙanin gaskiya na kasa gane abin da yake faruwa... Gaba ɗaya kin sauya kuma kin canja daga yanda kike.... Dama da biyu kuma ina sane naƙi nemanki tsawon wannan lokacin saboda ina son gane gaskiyar abinda yake faruwa..... Widat meyasa kika daina so na? Nayi miki wani laifi ne ko kuma kinji wani mugun abu atare dani? "

Shiru na ɗanyi har sai da ya kira sunana dan tabbatar da cewa shin har yanzu ina kan layinne ko ta yanke, ajiyar zuciya nayi sannan cikin sanyin murya nace,

" yaya faisal duk abubuwan nan da ka faɗa babu ko ɗaya aciki wanda ya faru, ni banji wani abu marar daɗi a kanka ba.... Kawai dai...." shiru nayi na kasa ƙarasawa hakan yasa shi faɗin,

"ina jinki, ki faɗi duk abin da ke ranki widat kar kiji shakka..... Kawai dai me?"

Nauyin kalmar naji shiyasa na kasa faɗa, tayaya zance masa bana sonsa tun asali?

"yaya faisal a gaskiya dama tun can baya ni akwai wanda nake so kuma har yanzu muna tare dashi"

Shiru naji shima yayi na tsawon wasu mintuna kafin ya saki ajiyar zuciya,

"idan na fahimceki dai dama bakya so na har na turo gidanku? Anyway shikenan zan yi musu bayani yanda zasu fahimta, amma ki sani ni ina son ki kuma naso na rayu dake, da kin san irin girman sonki acikin zuciya ta da irin tanadin da nayi miki na kyakkyawar kulawa da ƙauna wallahi widat da kin zaɓeni a matsayin miji amma babu matsala Allah ya cigaba da tabbatar mana da duk abin da yafi zama alkhairi, nagode saida safe.... "

Ji nayi jikina yayi sanyi, sam banji daɗin yanayin da naji yaya faisal aciki ba wato yanayi na damuwa da ɓacin rai amma babu yadda na iya saboda nima zuciya ta na can wani wuri daban, daren ranar sai da na jima banyi bacci ba kafin bacci ɓarawo yayi nasarar ɗaukata.

Washe gari ina tsaka da bacci naji muryar Annie tana tashina, da mamaki fal cikin zuciya ta na tashi saboda a iya sanina dai yau weekend ne bare ko ince saboda fita aiki take tashina dan kar in makara,

"zo abbanku yana kiran ki...." daga haka ta juya ta fita daga cikin ɗakin, dogon hijabi na saka har ƙasa akan kayan baccina na fita idanuwa cike fal da bacci sakamakon rashin isasshen baccin da ban samu ba jiya,

Ina shiga falon Abba na hangi mama zaune da yaya Abdul hakim kusa da ita sai Annie itama zaune ɗan nesa da abba kaɗan, ganin irin yanda naga fuskokinsu ya tabbatar min da cewa ba ƙalau ba musamman ma yaya Abdul hakim dake ta faman aikin watso min harara kamar zai tashi ya bugeni,

"abba ina kwana, mama ina kwana...."


"lafiya lau maimunatu....." abba ya amsa yana zare farin gilashin dake idanuwansa, sunkuyar da kaina ƙasa nayi saboda na fahimci ni mai laifi ce saboda yadda babu wanda ya amsa gaisuwa ta sai iya abba kaɗai, tunani na ya katse sakamakon maganar abba da naji,

" maimunatu yaya kuka yi da faisal....?" tambayar da tayi mutuƙar gigita tunani na da hankali na gaba ɗaya dan ban san irin amsar da ya dace in bawa abba ba a wannan lokaci,

"maimunatu....." abba ya sake kiran sunana, "na'am abba"

"nace yaya kuka yi da faisal? Ina son ji"

Shirun dai na sake yi saboda ban san abin da zance ba,

"abba ai bata da gaskiya dan haka babu abin da zata iya cewa, wulaƙanci ne da ƙasƙanci ta gama yi wa faisal..... Ai ba zai yi mata ƙarya ba, duk abin da ya faɗa hakane...." yaya Abdul hakim yafaɗa cikin fushi da ɓacin rai,

"a'a ai akwai buƙatar muji daga bakin ta, gara ta faɗi koma menene da bakin ta"

"Mai shari'a babu batun aji daga bakin ta, mu muka haife ta ba ita ta haife mu ba, mu ne muke da iko da ita ba itace take da iko damu ba dan haka ya zama dole tayiwa dukkan dokar da muka shimfida biyayya, maganar auren ta da faisal ko tana so ko bata so sai an yi ta faƙat, idan kuwa bata amince ba to ta nemi wata uwar amma ba ni ba.... Nima ba ita kaɗai na haifa ba bare baƙin cikin ta yayi ajali na " Annie ta faɗa cikin fushi ta tashi ta fita, hawaye ne suka shiga wanke min kumatu babu ƙaƙƙautawa take naji tsanar yaya faisal tsana mai tsanani domin ta dalilinsa gashi zan samu matsala da gidan mu a karo na farko cikin tarihin rayuwa ta, Karon farko da mahaifiyata tayi fushi dani tare da alwashin mummunan sakamako a gare ni, kifewa nayi awurin ina gunjin kuka wiwi.

Tsawar da yaya Abdul hakim ya daka min itace tayi sanadiyyar haɗiye kuka na,

"ke.... Idan baki yi wa mutane shiru ba sai na zo nayi ball dake, marar kunya, ana ganin ki kamar me hankali ashe ba haka bane......."

Jin an ɗagoni yasanya ni ɗagowa ina kallon mama wadda ta riƙoni ta sani cikin jikin ta tana rarrashi, sai lokacin naji abba yayi gyaran murya alamar zai yi magana kuma maganar mai muhimmanci,

" maimunatu....... Kiyi haƙuri zan aura miki faisal wannan shine hukuncin da na yanke....."

Jin abinda kunnuwa suka jiye min take na nemi jina da ganina na rasa na zama nidai gani nan ne dai kawai nakasa gane a wanne irin yanayi nake........... ✍🏻


*Garin dadi littafin kudi ne ga mai bukatar cigaban labarin sai ya tura 500 ta 0774712835 Aisha Ibrahim Access Bank sai a tura evidence of payment ta wannan no 07044644433 ko a tura katin waya da shaidar biya wannan no 07044644433*


*_Ummi Shatu_*👌🏻
[1/5, 12:43] Maman K: ©️ *HASKE WRITERS ASSOCIATION.*
_(Home of expert & perfect writers?)_




*GARIN DAƊI......!*💍💍



_*NA*_


*_UMMI A'ISHA_*


*Wattpad:ummishatu*


From the writer of

KAMAR DA WASA
KUMALLON MATA
MIJIN MATACCIYA
SO DA ALAƘA & REST.....


*7*



~~~Hawaye ne kawai ke faman sintirin kaiwa da komowa akan kumatu na yayin da bakina ya kasa furta koda kalma guda,

"Abba hakan da kayi shine daidai, haka kawai yarinya tana neman ta mayar da mutane ƙananan mutane....." yaya Abdul hakim ya faɗa bayan ya miƙe yana ƙoƙarin fita daga cikin falon, ni ɗinma mama kamani tayi muka fita har lokacin ban bar zubar da hawaye ba,

Kai tsaye sashen mama muka shiga wadda dama tun can ni a sashenta ɗakina yake, zaunar dani tayi kan kujera sannan itama ta zauna kusa dani ta soma rarrashi na,

"haba widat.... Ya ina yi miki kallon mai hankali kuma kina ƙoƙarin ɓata rawar ki da tsalle? Ringiɗi ringiɗi aka yi maganar nan sai yanzu zaki dawo ki cewa yaron nan kin fasa auren sa bayan duka burikansa sun ta'alaƙƙa ne akan ki..... Ai Kinga kamar ba a kyauta ba idan aka yi masa haka ko? "

Cikin shassheƙar kuka na ɗago kaina na kalli mama,

" mama wallahi bana sonshi, ban taɓa son yaya Faisal ba koda na aure shi kawai zan zauna dashi ne amma ba dan wai ina son shi ba "

Jijjiga kai mama tayi tace" na fahimceki amma kin san abin da nake so dake? "

" a'a.... " na faɗa cikin kuka,

" ki kwantar da hankalinki ki cigaba da addu'a, kin san sau dayawa muna son abu amma kuma ba alkhairi bane atare damu, wanda kuma muke ƙi sai kiga daga ƙarshe ya zame mana alkhairin, dan haka abin da nake so dake shine ki daina wannan kukan ki share hawayenki kiyi addu'a akan Allah ya tabbatar miki da koma menene in dai shine alkhairi agareki duniyar ki da lahirarki.... "

" to mama"

Sai da ta ɗan sake yi min nasiha sannan na tashi na wuce ɗakina naje na cigaba da kuka na, ina yi ina tuna hashim yanzu kowacece zata iya sonshi har ta aure shi ta bashi irin kulawar da nake mafarkin bashi a koda yaushe? Da zarar na tuno wannan lamari sai inji na kasa jurewa.

Yinin ranar haka na yishi cikin damuwa da koke koke domin wuni nayi cur ina cikin ɗaki in banda kuka babu abin da nake yi a haka har ƙawalli ta zo ta iskeni, ganinta sanye da hijabin makaranta hakan ya tabbatar min da daga islamiyya ta dawo ko gida bata je ba ta shigo wurina,

Ganin yanayin da nake ciki yasa ta faɗin "subhanallahi, ƙawalli lafiya kuwa? Ko dai baki da lafiya ne?" ta ƙarasa maganar tana zama kusa dani, murya ta a dashe na tashi zaune kuma har lokacin kayan bacci ne ajikina dan yau ko wanka ban yiba,

"ƙawalli gara rashin lafiya da wannan halin da nake ciki.... Su Abba sun yanke shawarar aura min yaya faisal duk da na faɗa musu gaskiya cewar bana sonshi...... Saboda jiya da daddare na faɗa masa abin da ke raina cewa inada wanda nake so shine ya zagaye yaje ya fadawa yaya hakim, shi kuma ya faɗawa su abba..... "

" gaskiya ƙawalli lamarinki yanzu yana bani mutuƙar mamaki..... To menene abin damuwa dan su abba sun yanke hukunci akan ki.... Ki sani fa duk zaɓin da zasu yi miki ba zai taɓa zama sharri agareki ba sai dai ya zama alkhairi.... Dan Allah ki daina irin abubuwan nan na marassa ilmi, ni wallahi har kin sa naji raina zai ɓaci..... "

Jajayen idanuwana na buɗe na kalleta, lallai duk yadda aka yi ƙawalli bata san zafi da raɗaɗin rabuwa da masoyi ba shiyasa take furta irin waɗannan kalaman, ni dai har ta ƙaraci faɗanta ta tafi bana fuskantar abin da take cewa, bayan tafiyarta ina zaune kan sallaya bayan na idar da sallar magariba mama ta shigo cikin ɗakin,

"ƴar mama taso mana.... Zo muje maza"

Tashi nayi nabi bayanta har zuwa falonta, abinci ta nuna min babu musu na zuba na fara ci ba wai dan yana yi min daɗi a bakina ba, bayan na gama mama ta sake yi min nasiha sannan tace in je inbaiwa Annie haƙuri dan da alama fushi take dani kuma fushin iyaye akan ƴaƴansu babu kyau, kamar yadda tace haka na tashi naje na samu Annie tana zaune kan carpet ɗin salla da carbi a hannunta tana ja, durƙusawa nayi agabanta na fara bata hakuri

Please Login or Register in order to submit comment