Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ba, gaba daya abinda yazo ran kowa shine saceni aka yi musamman ma yanzu da yin garkuwa da mutane yazama tamkar sana'ar yau da kullum ga wasu mutanen amma kuma sai tunani ya canja saboda mai gadi ya tabbatar masa da cewa da kafata na fita dauke da akwati babba sai dai ban sanar dashi inda zanje ba ai take ya rufe shi da fada wai Meyasa ya barni na fita amma amsar da maigadin ya bashi sai tasa jikinsa yayi sanyi kuma yaga yana da gaskiya tunda ai na saba fita sannan bai taba kafa masa dokar ya hanani fita ba to a wannan karon saboda me zai hana ni alhali baya daga cikin sharrudan da aka saka masa? Ciki ya koma hankali a tashe ya shiga bedroom dina nan yaga sim cards dina da na zubar gaban gadona, rasa abinda yake yi masa dadi yayi to yanzu wacce amsa zai bawa iyayena da yan uwana tunda ta sanadiyyarsa na gudu? Ai tun a ranar ya yi watsi da maganar aure ya koma fafutukar nemana kamar yadda can gida suma suke yi don hankalin iyayenmu mata ya tashi sosai musamman ma mama sai dai duk inda aka kai cigiya sai ace ba a ganni ba daga karshe dai aka rasa gane meya faru dani dan sun fara zargin to ko bayan da na fito aka sace ni, tun dai ba a son zancen ya yadu har sai da ya yadu shi dai yafi kowa shiga tashin hankali dan ko isasshen bacci baya yi saboda bai san awanne hali nake ba.

Ni kam ina can hankalina duk da bazan ce a kwance yake ɗari bisa ɗari ba amma dai ya dan kwanta sai dai matsalar tunda na zo da sati ɗaya nake fama da zazzabi da tashin zuciya ga ciwon ciki, da dafarko nayi tunanin ko canjin weather ne amma sai naji abun kullum kara gaba yake yi dan har nayi 6 weeks da zuwa babu shiri na nemi asibiti naje, anyiyyi min tests da dukkan abinda ya dace kafin daga baya Dr ya tabbatar min da ina da ciki tsawon sati 7, rasa abinda zanyi nayi dan murna, ban san lokacin da na fara hawaye ba har na dawo masaukina, salla nayi raka'a biyu dan nuna godiyata ga ubangiji Allah, murna da bakin ciki nake yi duk a lokaci ɗaya, ga burina ya cika amma kuma bana kusa da samz, kifa kaina nayi jikin gado ina kuka ina tuna ta yadda ma har wannan cikin ya shiga dan tun bayan da maganar karin aurensa ta taso shikenan na daina jin son kasancewa dashi sam bana bari mu hada shinfida ko wannan dinma ranar da karfinsa yayi amfani wurin samun biyan bukatarsa dan acewarsa ya kai gaɓar da bazai iya jurewa ba shi kuma ba mazinaci bane, a tunzure kuma a masifance cikin ƙuluwa nace masa,

"ai sai ka jira har ranar da za a kawo maka amaryar taka inyaso sai ka biya...." bai jira ni na karasa fadar abinda zan fada ba naji ya hadani da jikinsa ta ƙarfin tuwo, kokawa muka yi sosai abinda ko daren farkon mu banyi masa irin wannan gardamar ba amma ranar yakushi da cizo babu wanda bai sha ba duk ya daure har sai da samu abinda yake so, daga karshe ya rungume ni yana rarrashi na,

"Haba baby duk kin canja kin daina zaman lafiya dani.... Kiyi hakuri, Allah yayi miki albarka Allah yasa ki samu ciki yau...." banza nayi masa sai kuka da nake ta faman yi daga karshe na bar masa dakin na koma dakina na sama kuma tun daga wannan lokaci ban sake wasarere da kofata ba bare har ya shigo kuma gashi wannan haduwar a ita muka samu rabon,

" Allah sarki ashe Allah ya amshi addu'ar ka.... " na fada ina hawaye, ina cike da farin ciki amma ta wani bangaren bakin ciki nake bakin cikin ga abun dadi yasamu amma babu wanda zan sanarwa, da ace ina gida wannan abun ya faru da ban san farin cikin da zai yi ba shi da sauran dangina wanda keta tayani da addu'ar dacewa kuma suke karfafa min gwiwa kan kar in cire rai kar in yanke tsammani. Haka naci gaba da kula da kaina babu yabo babu fallasa dan wani lokacin in samu kaina cikin damuwa wani lokacin kuma inji ni babu damuwar, amma fa duk ranar da na tuna aurensa sai inji duniyar tayi min kunci,

A can gida kuwa maganar aure an ajiyeta a gefe ita dama mommy babu abinda ya dameta ta dai san zai kara aure kamar yadda yajima da yi mata alkawari, ranar tana zaune Hadiza nayi mata kitso sai ga madam comfort da Felicia dukkanin su a fusace,

"Wallahi ban taba sanin ke munafuka bace sai yanzu maman Mary, shine dan tsabar munafurci muna nan muna jiran samz yazo ya auri Felicia ashe ke kin gama zaba masa matar da zai aura?"

"madam comfort wacce irin magana kike yi ne wai?"

"Haba da Allah mommy, stop this pretending mana, ai kin san komai, ashe dama kina da wadda danki zai aura shine ni kuka rinka bata min lokaci na a banza dan tsabar mugunta, wallahi ba zan taba yafe muku ba..." Felicia ta fada cikin rashin kunya,

"ohhh..... I see..... Wato da dan nawa ma ya aureki haka zaki rinka fada min magana cikin reni da wulakanci? To ashe gara da bai aureki ba"

"sai me dan be aureni ba? Zan auri wanda ya fishi ai tunda ba shi kadai ne namijin da ya rage ba..."

"ke ki shiga hankalinki, mommy kike fadama haka" Hadiza ta fada bayan ta Mike tsaye tana nuna mata yatsa,

"ta fada mata din, dan danta bai auri Felicia ba sai me? Aikin banza dan ma da ba sonsa take yiba, da tana sonsa zata je ta yi masa asiri ta hana shi haihuwa? Ƙaryar banza, to wallahi yanda kuka batawa yata lokaci nima sai na bata muku lokaci zaki gani, banza wacce bata daraja yaranta da mijinta.... "

Faɗa dai aka yi kaca kaca harda su gore gore nan aka rabu babu dadi baram baram dutse a hannun riga, dan bakin ciki mommy harda kuka saboda irin gorin da madam comfort ta yiyyi mata a gaban yaranta da mijinta dan shima daddy ya dawo ya iske fadan shine ma ya raba amma da bacacciya aka so ayi, daren ranar bata yi bacci ba saboda bata taba sanin munirat samz zai aura ba sai dasu madam comfort suka zo wannan dalilin ne yasa sassafe ta tafi Kano gidan anty Amina suma taje tayi musu wankin babban bargo tace samz bazai auri munirat ba dan haka su dawo musu da komai wanda aka kai da sunan kayan aure, itama munirat din da yake kunya bata isheta ba fitowa tayi ta shigarwa mahaifiyarta tacewa mommy,

"Ba zai yuyu ki zo mana har gida kici mana mutunci ba.... Aure ai ba dole aka yiwa dan naki ba kuma da kike cewa waya mutu wa yai rai aure ne babu fashi sai anyi shi, sai na auri dan naki kuma sai yadda nayi dashi, ni ba wannan sakaryar matar tasa bace da kika saba tozartawa wallahi kina yimin zan yi miki babu uban da nake tsoro..... " duk da anty Amina tana ta hana munirat amma bata hanuba sai da ta kai aya daga karshe sai janyeta anty Amina tayi ta kai cikin daki ta rufe, ita kuwa mommy cikin takaici tace,

" Wallahi Samuel ba zai taɓa aure a gidan nan ba, zan nuna muku ni na haife shi kuma na isa dashi...."

"ta Allah ba taki ba, uwar bakin hali" anty Amina ta bata amsa, mommy bata kara tankawa ba tafita daga gidan ta koma kuma adaren ranar ta kira samz tace indai ita ta haife shi to bata yarda ba ya auri munirat wannan maganar auren kar a kara yin ta, shi dai dama yanzu bata karin aure yake yi ba ta nemana yake dan kullum abin yana ransa dashi yake kwana yake tashi.

Lokacin da na cika wata uku da zuwa kusan kullum sai nayi mafarki amma kuma idan na tashi sai in kasa tuna abinda nagani a cikin mafarkin wannan dalilin ne yasa naji gaba daya hankalina ya tattara ya koma gida dan ina son inje inga me ke faruwa duk na san kawo yanzu kam yayi aurensa watakila ma har an samu rabo, dama bani da matsalar kudi saboda ina dasu fal account nan na fara shirin komawa kuma ba wai dan na hakura bane kawai dai ina ji a jikina akwai abinda yake faruwa,

Misalin karfe goma na dare jirginmu ya sauka kai tsaye gidan anty na wuce banma nemi hanyar gidana ba dan na gama yardarwa kaina yanzu yayi aurensa,

"widat.... Yanzu kin kyauta kenan ki tafi kibar gida duk kibi ki dagawa kowa hankali?" anty ta fada lokacin da na shiga,

"kuyi hakuri anty nima bani da yadda zanyi ne dole ce ta sakani...."

"za ki yi wa Abba bayani"

"anty yayi auren ko?"

"ban sani ba" ta bani amsa tana hararata duk kuwa da tayi murnar ganina dan tun a lokacin ta fara sanarwa da ƴan gida na dawo shi kam uban gayyar lokacin da yaji labarin dawowata ai acikin daren yaso yazo gidan anty amma ta hanashi tace dare yayi yanzu yai hakuri zuwa gobe, duk da a gajiye nake amma sai da muka jima bamuyi bacci ba saboda mu nata gaisawa da yan uwa ta waya,

Washe gari sai ga yan gidanmu mota guda sun iyo sammako ciki harda Abba, duk da na shassha fada amma kuma kowa barka yake yi da ganina dan kallo daya zaka yimin ka tabbatar da ba daga cikin wahala na fito ba sai dai har lokacin babu wanda ya amsa min tambayar da nake ta yi musu cewa yanzu samz yayi aurensa ko? Abba dai sai da yayi min fada sosai yace kar na kara irin wannan kuskuren in tafi in bar gida komai rintsi, duk ciki babu wanda ya fahimci inada ciki sai kawalli ban san ya akayi ta gane ba amma kawai sai ji nayi tace "ashe sai da ya kunsa miki sannan kika gudu ko" duka na kai mata nace "ke kika sani" saboda ni bana ma son jin batunsa , suna shirin tafiya shi kuma yana zuwa, ai daki na gudu dan bana son in ganshi tunda na san yanzu kam me afkuwa ta riga da ta afku, anty ce ta biyoni har cikin dakin tace in fito inbi mijina mu tafi bazan sake kwanar mata a gida ba, ina turo baki fuskata a cunkushe na fito islam tana biye dani ta janyo min akwati na,

A falo muka sameshi suna magana da anty ban tsaya na wani kalle shi ba nayi gaba duk da haka na kula ya dan fada gaskiya ba kamar yadda yake ba kuma hakan na san yana da alaka da bacewa ta, har mota suka rakamu sannan suka juya shi kuma yayi mata key muka fita daga gidan, hannu ya miko min alamar wai mu gaisa amma sai na dauke kaina,

"baby abinda kika yi kin kyauta kenan? Kin tafi kin barni ban san halin da kike ciki ba?" nan dinma shirun nayi masa ina jinsa da haka har muka je gida, shi da kansa ya dauki akwatin nawa muka shiga ciki kuma komai yana nan kamar yadda na tafi na barshi,

"baby me yasa kika yimin haka?"

Kallonsa nayi ido cikin ido kuma cikin masifa nace "yanzun ma ba zama nazo yiba, ai na fada maka sai dai ka zaba ko ni ko ita..."

"ok, I choose you baby..." ya fada yana kokarin matsowa jikina bayan ya ajiye akwatin,

"wannan kuma daga baya kenan, tunda har ka riga da ka aurota kaga kenan ita ka zaba...."

"baby.... Wai wa na aura?" yace dani bayan yayi nasarar hadani da jikinsa ya tallafo kumatuna da hannayensa yana kokarin hada idanuwanshi da nawa,

"ita munirat din...."

Sunkuyowa naga yayi ya jona bakinsa kan nawa duk da ban so hakanba dan yana daya daga cikin weak point dina kuma shima yasan hakan shiyasa duk yadda naso in tureshi na kasa,

"baby ban auri kowa ba fa, dama auren da zanyi ba wai dan na daina sonki bane, kiyi hakuri kar ki sake tafiya ki barni please and please...."

Sai da naji haka sannan naji raina yayi fari zugin dake raina ya kau har ban san lokacin da na kankameshi ba tamkar zan koma cikin cikinsa,

" ka san me? " na fada cikin rada bayan na kai bakina kusa da kunnensa,

" no baby.... "

" am pregnant.... " na fada ina kissing kumatunsa,

"Baby are you serious?" yace dani yana dagani sama tare da soma juyawa dani,

"am serious boo...."

"Alhamdulillah...."

"addu'ar da kayi min ranar nan ita Allah ya karɓa, kaga tun daga ranar nan bamu kara yiba har na tafi..."

"baby you are so wicked..... Kin hanani hakkina bayan kin san is part of my life...."

"am very sorry"

"don't sorry me kawai ki biya ni...."

"to ka bari sai Babyn yayi kwari"

"A'a baby, nace zan kara aure kin ki amma kina yimin rowar kanki"

"to na daina...."

Hmmm dama yaya lafiyar kura, ai bai wani daga min kafa ba ranar sai da ya kashe kishin ruwarshi, tunda na dawo yake lallabani yake kulawa dani sai abinda naso, ya hanani komai sai iya dawainiyarshi kadai, babu inda nake zuwa tun bayan dawowata dan restaurant dina ma sau ɗaya naje tun daga nan ban koma ba saboda Abdallah yana kula da komai yadda ya kamata.

A kwana a tashi sai ganina nayi na zama wata jibgegiya kamar ana hura min iska, dama kuma kusan kowa idan ya ganni lokacin cewa ake wai anya ba ƴan biyu zan haifa ba ban gaskata zancen kowa ba har sai da naje scanning naji Dr yace twins ne mace da namiji, babu wanda na fadawa sai samz wanda farin cikinsa kamar yaso yafi nawa cikin murna naji yace "dama ai nima nayi expecting haka baby saboda wannan cikin yafi wancan girma"

"kalli yadda nayi muni...." na fada cikin shagwaba,

"ni ban taba ganin muni atare dake ba baby, a koda yaushe kyau kike kara yimin" duk lokacin da nace nayi muni haka yake fada min sai inji hankalina ya kwanta, babu abinda nake iya yi komai shi yake yimin dan ko zama nayi sai ya ɗagani, ya debo min masu aiki guda biyu wanda su ke yimin yan aikace aikacen gida ni dai sai fita exercise da nake yi amma baya dashi bana aikin komai saboda dagaske cikin nan yayi min nauyi bada wasa ba, shine keta zumudin siyayyar kayan babies this time around amma ni babu abinda na siya sai wanda na san ya zama dole, nidai addu'ata bata wuce Allah ya bani lafiya ya bani yara masu albarka masu tausayi da tsoron Allah, date Dr ya bani wanda zanje acire yaran dan acewarsa sunyi girma da yawa idan aka ce za a jira in haihu da kaina za a iya samun matsala, da naso in tashi hankali na amma sai anty dashi suka rinka kwantar min da hankali har anty nace min ita na manta duk haihuwar ta cs ne kuma gata nan lafiya lau, itace ma ta raka ni asibitin ranar da za ayi min cs din,

Bayan an fito dani na farfado anty ta matso tana yimin albishir wanda ni ba ganewa nake ba saboda ciwon da cikina keyi sannan wurin yankan shima ciwo yake yimin sosai, ko ganin yaran banyi ba sai washe gari lokacin na ɗanji dama dama, a maimakon yara biyu sai naga uku biyu maza daya mace ashe shiyasa tun jiya anty keta yimin albishir ban ji ba, kowa fuskarsa cike da annuri nidai mamaki ne yaso sumar dani ganin mommyn samz da kannen shi sun zo anata murna da sam barka dasu hakan ba karamin dadi yayi min ba, bayan sun tattafi ya rage daga anty sai Islam yarta anty ke bani labarin wai mommy yanzu ta sauko sosai tayi laushi ko me ya faru oho ashe ita kuwa mommy gani tayi wannan masifar da take ba riba kuma babu mai dauka dai ni ɗin shiyasa ta yiwa kanta faɗa ta tara yaranta tace gara su rikeni hannu bibbiyu dan da alama ko mutuwa tayi nice kadai zan iya rikesu sannan abubuwa da yawa nike saka mijina yayi musu kai wani ma da kudina nake yi duk da nasan kuma basa kaunata, muna zaune da babies din agabana an jeresu samz ya shigo tare da Ahmad abokinsa da matarsa sai wata wacce kamar dai na santa nan suka dubani suka dauki jariran suna yi musu addu'a kuma sai lokacin na gane ashe shalele ce dan tayi ƙiba ne sanaddiyar tsohon cikin da take dauke dashi shiyasa ban gane ta da farko ba, sai bayan da suka firfita har anty ya rage iya nida ita sannan take sanar dani tayi aure kuma ga yadda suka yi da Malika kawarta wacce yanzu duniya ta juyawa baya sakamakon cin amana da zamba cikin aminci da ta rinka yiwa mutane ciki har da ita duk da ita tazo har gida ta nemi afuwarta, mun jima muna hira har sai da mijinta ya dawo sannan tayi min sallama ta tafi bayan ta karbi no dita tace zata zo min har gida.

Lokacin da aka sallameni su anty gida suka yi niyyar tafiya dani amma naki nace idan na tafi waye zai kula da boo? Ni gara in zauna agidana kawai kuma hakan ba karamin dadi ya yiwa samz ba anty kuwa cewa tayi inje inyita zama idan kafin arba'in ya sake yimin wani cikin can ta matse mana dariya nayi araina nace da dai in barshi cikin takura gara anyi hakan, sai da na warke ras sannan aka yi shagalin suna wanda walima kadai akayi dama already an radawa yara suna Ahmad, Muhammad ita kuma macen A'isha, yanzu dai alhamdulillah bani da bakin ciki ko damuwar komai haƙika duk abinda kaga Allah ya jinkirta maka to ka kyautata masa zato kuma kayi hakuri ta yuyu lokacin da zai baka ninka maka zai yi, haka kuma kar ka zama me rama kiyayya da kiyayya kabi a sannu kayi hakuri watakila nan gaba makiyin zai zame maka masoyi, ni dai yanzu ko ba zance dangin mijina suna sona ba to ba zance suna kina ba, ƴaya na kuwa kowa yana sonsu yana kokarin kulawa dasu, Mijina kuwa abin alfahari na har gobe yace ina nan a gurbin da ya ajiyeni ban sauya ba, yarana suna da wata uku muka tafi Kano hutu kuma ta can muka halarci bikin munirat wanda aka hada tare da kanwarta Nusaiba, a gajiye muka dawo gida saboda ranar mun sha yawo gashi shima yace min wai yana nan zuwa yau ko gobe saboda na kwaso yara mun baroshi shi kadai duk gidan babu dadi na san tunda ya fada to babu fashi zai zo din shiyasa na shirya tsaf domin tarɓarsa...........


ALHAMDULILLAH

Anan labarin GARIN DAƊI ya kammala fatan mun nishaɗantu kuma mun ilmantu, sai mun haɗu cikin labari na gaba da yardar Allah, taku a har kullum Ummi A'isha.



*_Ummi Shatu_*👌🏻


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Please Login or Register in order to submit comment