Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yanzu..... Da dai munyi aure ne..."

Murmushi nayi nace "Idan munyi auren kanada abunda zaka rarrasheni?"

"Ehh but idan na faɗa miki faɗa za muyi kuma fushi kike yi"

"Ba zamu yi faɗa ba yau, ina son ji, tell me pls"

"Seriously? OK i will hug you and kiss you...... Sannan zan goyaki"

Murmushi nayi ina rufe fuskata kamar yana kallo na,

"Ashe ni yar gata ce"

"yeah you are my baby ai, kinga dole in kula dake, i will do everything to make you happy......"

"Na gode Darling...."

"ke kuma wanne irin rarrashi zaki rinka yimin?"

"i will do the same thing for you"

"no.... Ni ba wannan nake so ba" ya faɗa cikin kwaikwayon murya ta irin yanda nake yi masa idan ina shagwaɓa,

"faɗa min abinda kake so...."

"you" ya bani amsa cikin zakin muryarsa,

"don't worry am all yours"

"I hope soo" ya sake faɗa yana fusgo maganar daƙyar, har saida ƙawalli tazo sannan muka yi sallama muka kama hanya da Ƙawalli ina sake bata labarin Samz, har gidanmu muka je da ita tacewa su mama mun dawo sannan na rakata ta tafi.

Da daddare lokacin da muka yi waya dashi sai naji muryarsa wani iri alamar bai da lafiya koda na tambaye shi sai yace ehh amma kuma yin duniya nayi akan ya faɗa min abinda ke damunsa yaƙi daga ƙarshe ma da na matsa masa da tambaya sai yace wai kansa ke ciwo, karo na biyu kenan ina tambayarsa rashin lafiyar sa yana ƙin faɗa min idan na takura sai yace ciwon kai, haƙura nayi na rabu dashi na tambaye shi ko ya sha magani yace min ya sha, duk da bai da lafiya hakan bai hana mu raba dare muna hira ba anan ma yake sanar dani wai yayi booking flight 7 zai bar Kano domin yana da aiki a office saboda shi da NGOS yake aiki amma parmanent staff ne ba on contract ba, sai da bacci yaci ƙarfina sannan muka yi sallama na kwanta. Haka lamarin yaci gaba da gudana cikin so da ƙaunar juna tare da shaƙuwa mai ƙarfi tsakanin mu sai dai iya ƙawalli ce kaɗai ta san muna soyayya dashi kuma duk lokacin da yazo ganina ita ke shiga ta fita har mu samu mu haɗu muga juna,

Tuni muka yi nisa a aikin da muke yi wanda har mun ci 8 weeks yanzu, Samz koda yaushe muna maƙale da juna a waya, video call ko voice call, gefe ɗaya kuma shirye shiryen bikin ƙawalli da yaya Abdul Hakim wanda keta ƙaratowa yasake chaja min kai, ranar da Samz yazo na ƙarshe ban san wanda ya ganmu tare dashi ba har yaje gidanmu ya faɗa nidai kawai Abba ya kirani yayi min kaca kaca akan Samz sannan yace lallai lallai in rabu dashi tunda ba addininmu ɗaya ba dama ni tunda naji Abba yace,

"Maimunatu da wanne saurayi aka ganki jiya a First class Guest lodge?" naji ƴan hanjin cikina sun kaɗa,

"Abba Samuel ne" na faɗa jikina yana kyarma,

"menene alaƙarki dashi yana Christian kina musulma?"

"Abba saurayi na ne..."

Ai tun kafin na ƙarasa naji su Annie sun ɗauki salati, Annie tashi tayi zata zo ta rufeni da duka mama ta hana, nan Annie ta fara faɗa tana cewa,

"Widat kashe ni kike son kiyi ne? So kike baƙin cikin ki ya kashe ni? To wallahi daga yau ban yarda ki sake kula wannan yaronba matsawar ba musulunta yayi ha wannan kam ba zan hana ba, amma in dai kika sake kula shi ban yafe miki ba, babu ke babu shi har abada ko a hanya ban yarda ki sake kula shi ba "

Kuka na fashe dashi saboda jin abin da Annie tace, na san ta bani horo mai tsanani domin abune da zai wahalar da zuciya ta da gangar jikina gaba ɗaya, rabuwa da Samz tamkar yanke numfashi nane a doron ƙasa, Abba kuwa cewa yayi,

"Na baki nanda watanni biyu ki fito da miji in yi miki aure idan kuma ba haka ba to zan aura miki duk wanda na samu tunda Allah ya gani nayi iya yina ganin na aurar dake ga zaɓin zuciyar ki amma kina neman ki jawo min magana kina bin saurayi har hotel kuma abin haushi saurayin ma wanda ba musulmi ba "

Da kuka na shiga ɗakina na kwanta ranar naci kuka kamar wadda uwarta ta mutu daga ƙarshe na jawo wayata na turawa samz da text massage minti ɗaya da tafiyar massage ɗin sai ga kiransa,

" Baby me yake faruwa? "

" Samz ka san ina sonka, kuma babban burina shine inga munyi aure mun zauna a inuwa ɗaya, kuma Hakan ba zata taɓa faruwa ba har sai idan ka musulunta, Abba da Annie sunyi min iyaka da kai sunce kar na sake kulaka har sai idan ka karɓi musulunci, hakan shine kaɗai zai ba mu lasisin mallakar juna...... "

Girgiza kai yake yi daga inda yake zaune, bai ce min komai ba ya katse wayar wanda hakan ya bani tabbacin munyi bankwana dashi na har abada...........✍🏻


*Garin dadi littafin kudi ne ga mai bukatar cigaban labarin sai ya tura 500 ta 0774712835 Aisha Ibrahim Access Bank sai a tura evidence of payment ta wannan no 07044644433 ko a tura katin waya da shaidar biya wannan no 07044644433*



_*Ummi Shatu*_👌🏻
[1/5, 12:43] Maman K: ©️ *HASKE WRITERS ASSOCIATION*
_(Home of expert & perfect Writers)_




*GARIN DAƊI......!*💍💍



*_NA_*


_*UMMI A'ISHA*_


PAID BOOK

*Wattpad:ummishatu*


22

*Ina kuke manyan mata ƴan ƙwalisa ma'abota son gyara da kece raini, maza ku garzayo ku nemi maman Maryam domin samun lafiyayyu kuma haɗaɗɗun Lagos lace wanda zaku iya samun ɗinkakku da kuma sabbi a ledarsu, kaya iya zaɓinki, gefe ɗaya muna da GHT product, zaku samu,*

~MAI DA TSOHUWA YARINYA

~FEMALE CARE

~REODEO

~VIGOR MAX

~ LONGZIT

~B CLEAR

*DUK ZAKU SAMU WADANNAN KAYA CIKIN SAUKI DA RAHUSA MAZA KU NEMI MAMAN MARYAM AKAN WANNAN NO 07080222187, SIYAN NA GARI MAIDA KUƊI GIDA.....*


~~~Daren ranar gaba ɗaya bacci ƙauracewa idona yayi damuwa cunkushe fal raina, zuciya ta tana ta saƙa min abubuwa da dama game da tarayya ta da Samz musamman ma idan na tuno irin maganganun da Ƙawalli ta faɗa, tabbas nima nasan duk abubuwan da ta faɗa babu ja ko ƙarya acikin su sai dai amma shi so ba kaine kake zaɓawa kanka wanda zaka so ba zuciyar ka ce ke da wannan ikon, ganin wankin hula na shirin kaini dare ya sani tashi na shiga toilet na ɗauro alwala na fito na zo na fara sallar nafila, na jima kuma na daɗe goshina a ƙasa inata addu'a akan neman zaɓin Allah dangane da lamarina da Samz, addu'a ta bata wuce idan har shigowarsa rayuwata babu alkhairi to Allah yayi gaggawar cire shi araina kuma ya kawo min musulmi ɗan uwana wanda zai soni tsakani da Allah, idan kuma akwai alkhairi a tarayyarmu dashi ubangiji Allah ya sauƙaƙa lamarin ya cika mana burinmu,

Saida nayi karatun littafi mai tsarki na karanta suratul Qasas sannan na kwanta lokacin misalin ƙarfe uku da yan mintuna na dare, ina kwanciya babu jimawa bacci ya ɗaukeni zuciya ta fess babu sauran damuwa, duk wannan ɓacin ran ya gushe sakamakon ayoyin Allah da na karanta a wannan dare, abin da ban sani ba shine shima samz cikin damuwar yake saboda ya saba da duk daren duniya sai munyi hira amma yau wayata a kashe tun bayan da Ƙawalli ta bar gidanmu, haka ya kwana cikin damuwa da rashin sanin takamaimai abin da ya faru da har yasa na kashe waya ya kasa samu na, shi dama ba baccin dare yake yiba shiyasa haka ya kwana cikin damuwa.

Nikam yau da farin ciki na tashi kamar anyi min albishir kuma wani abin mamaki ji nayi ina ɗokin jin muryar samz kamar irin na shekara ban ji shi ɗinnan ba, shiyasa tun ina kan gadona na kunna wayata na kira shi ko wanka banyi ba brush kaɗai nayi, katse kiran nawa naga yayi sai gashi ya kirani video call, murmushi nayi na kalli jikina na tabbatar da babu matsala domin sanye nake da riga da wando na bacci peach masu ɗan kauri sai pink ɗin hula akaina,

"Baby..... What happened?? “

Murmushi nayi na sunkuyar da kaina ƙasa ina mutsuttsuka ido,

" Good morning...... " na faɗa ina lumshe idona,

" Ba zan amsa ba ɗago idonki in ganki first.... "

Ɗagowa nayi na kalleshi shima yana kallo na,

" kin yi bacci jiya?" kai na ɗaga masa,

"OK, me yasa kika kashe wayarki?"

"Ban jin dadi, kaina ke ciwo amma yanzu ya daina da na samu bacci"

"OK sorry...... Kin yi breakfast?"

"A'a, yanzu na tashi ai"

"ok kiyi breakfast ina kallon ki..... Idan kin gama zan kwanta in yi bacci"

"OK bani 2 minutes"

Wayar na ajiye akan gado na nafi ta zuwa kitchen, ruwan zafi na zuba a cup na saka lipton da sugar sannan na zuba ɗumamen tuwo na koma ɗaki, har lokacin yana kan waya bai kashe ba sai dai ya ajiye ta shima yana wani abu a system ɗinsa,

"Am back Darling....."

"Me zaki ci?"

"tuwo, ka san nayi missing ɗumame, a Lagos bakwa ba mu tuwo na dawo gidan anty itama babu tuwo....."

"Baby rigima.... Ok bari in zauna in kalli laumarki...."

Dariya nayi na fara cin tuwo na ina ce masa ai tawa ƙarama ce akan tasa,ina ci muna hira da haka har na cinye sai lokacin muka yi sallama dan zai kwanta yayi bacci, ni kuma wanka nayi na shirya na fita wurin su mama naje muka sha hira nayi ta basu labarin Lagos da Abuja, wurin ƙarfe 12 na nufi gidan su ƙawalli,

A tsakar gida na sameta tana gyaran ɗanyen zogale wanda zata yi dambu, mayafi na nacire na lanƙaye a sama sannan na ɗauko bokitin ƙarfe na zauna,

"Yan mata.... Umma fa?" na faɗa ina gyara zamana,

"Ta je asibitin malam...." ta bani amsa batare da ta ɗagoba,

"waye bai da lafiya? “

" wani aminin mahaifi su ne, shi ne taje duba shi "

" ayya Allah ya bashi lafiya "

" amin"

"Baki tambayi Samz ba" na fada cikin sigar jan magana"

Dakatawa tayi daga abin da take yi ta Kalleni,

"au baki hakura da maganar samz ɗinnan ba ko widat? Wai widat kin kuwa san halin da kike ƙokarin jefa kanki? Soyayya da arne?"

"Ƙawalli kenan abin da nake nuna miki daban abin da kike kallo daban, kin kasa fahimtata"

"ai bazan taɓa fahimtar ki ba indai akan wannan maganar ne ƙawalli na faɗa miki wannan guy ɗin wallahi yaudararki zai yi, kawai zai yi amfani da son da kike yi masa ne idan ya tabbatar kin gama kamuwa, Allah tun wuri kiyi nesa dashi"

"bazan iya ba ƙawalli, wallahi ba zan iya rabuwa dashi ba, ke bana ma jin zan iya rayuwa batare da shi ba, rabuwa dashi kamar rabuwa da numfashi na ne....."

"Tirƙashi..... Lallai kin yi nisa, to yanzu idan akace ya fito kuyi aure sai ayi yaya? Kin dai san babu yadda za ayi kuyi aure a haka ko? Dole acikin biyu ayi ɗaya ko dai ya musulunta ko kuma ku rabu, ke ni bama na jin zai iya musulunta kuma koda ya musulunta ɗin akwai wata a ƙasa wallahi da sauran rina a kaba..... "

" wai dan Allah me yasa kike negative thinking akan samz, nifa jikina yana bani alkhairi ne haɗuwa ta dashi, sannan tun farko ni na fara sonshi har shima ya kamu da so na, kuma bai taɓa yimin maganar addininsa ba ko tallarsa.... Wallahi Maryam ba zan ɓoye miki ba ina yi masa wani irin mahaukacin so wanda ban taɓa yi wa wani ɗa namiji ba "

Cike da tsananin mamaki take kallo na har saida na dasa aya,

" Ikon Allah.... Gaskiya ƙawalli ba dan nayi miki kyakkyawan sani ba kuma na san irin tarbiyar da kika samu daga gidan da kika fito haka na san abin da zaki iya aikatawa da wanda ba za ki iya ba da nace wani abu....." murmushi nayi nace, "faɗi duk abin da ke ranki sai in wayar miki da kai idan ba haka bane"

"wallahi wallahi ba dan nayi miki farin saniba zance ko kun ɗanɗana juna shiyasa kuka mayincewa juna....." ko kaɗan ban ji haushin kalamanta ba madadin haka ma dariya suka sani sai da nayi mai isata sannan na bata amsa,

"Dama na san hakan zata faru ƙawalli, bake kaɗai ba kusan duk wanda zai ji muna soyayya da Samz abinda zai fara zuwa ransa kenan.... Sai dai wallahi ba haka bane, nida shi mun yi wa junanmu alƙawarin insha Allah baza muyi koda kiss ba sai bayan munyi aure bare har mu aikata alfasha.... Wallahi ƙawalli samz yana da nutsuwa kuma i trust him 100%, ni nasan baya shan giya kuma baya neman mata, bayan ya faɗa min da bakin sa saida na sake bincikawa da kaina ba tare da ya sani ba kuma har yau bai sani ba.... Har ɗakin da ya sauka a hotel lokacin da muna training naje dan in duba shi amma har na dubashi na fito bai ko yi yinƙurin kama hannu na ba, bayan na fito sai da naje wurin masu kula da hotel ɗin da shige da ficen mutane muka yi magana dasu na yi musu tambayoyi akan shi amma duk amsar ɗaya ce babu macen da ta taɓa zuwa wurin sa sai ni kuma bai taɓa yin order ɗin giya ba..... Kinga tunda abubuwan nasa basu wani ƙazanta ba ni ina ji ajikina nan gaba zai iya karɓar shahada, ni kaina ban taɓa zaton zan samu kaina dumu dumu cikin soyayyar wanda ba musulmi ba dan sanin kanki ne nafi kowa ƙyamatarsu da tsanarsu dan komai daɗin abu indai ya fito daga hannun su wallahi nabar abin kenan har abada kuma indai naci to sai nayi amai idan daga baya akace min sun taɓa, nidai kawai na ɗauki wannan a matsayin jarrabawa dan haka addu'a kawai nake buƙata...... " ajiyar zuciya ta sauke jikin ta duk yayi sanyi da maganganu na,

" Tabbas kam jarrabawa ce, Ubangiji Allah ya baki ikon ci, muga pics dinsa dan Allah "

Wayata na miƙa mata bayan na fito mata da pics ɗinsa,

" Wayyo ni Allah, GARIN DAƊI NA NESA, irin wannan haɗaɗɗen guy haka ƙawata... Ina ma musulmi ne, dole ki ruɗe ashe ba a banza ba "

Murmushi nayi dan har ga Allah a karon farko nidai ba kyawunsa ne yaja ni na faɗa sonshi ba haka kawai naji yayi min, hira sosai muka yi da Ƙawalli dan har saida ta kammala dambun nan muka ci sannan nayi mata sallama na koma gida. Soyayyar mu muka cigaba da yi nida samz, bayan dawowa ta da sati ɗaya yamin waya wai zai zo kano ya ganni, duk atunina da wasa yake yi shiyasa nayi dariya nace ina jira, zuwa yamma sai ya sake kirana wai gashi a kano ya sauka a wani guests palace in bashi address ɗin gidanmu zai zo, ai babu shiri na tashi daga kwancen da nake ina hutawa,

"Wai dagaske ka zo?" na faɗa idanuwana awaje,

"yeah am serious baby....". Ya bani amsa, rasa abin cewa nayi dan ni dai ko giyar wake nake sha bazan bari Samz yazo gidanmu ba dan masifar Yaya Abdul Hakim ma kaɗai ta isheni kafin azo kansu mama wanda kullum maganar su kar mu zubar musu da mutunci a idon duniya,

" Baby baki ce komai ba...." jin maganar sa yasa na dawo hayyacina,

"Cutie..... Dan Allah ka fahimce ni, wallahi ban san dagaske kake yiba da bazan barka ka zo ba saboda zuwanka gidanmu zai haifar min da matsaloli masu tarin yawa...."

"to yanzu ya za ayi? Nidai dole ina son ganin ki, bazan iya hakura in tafi ban ganki ba.... Tunda baki son in zo gidanku to a ina zamu haɗu, zaki zo Guest house ɗin da na sauka?"

"No cutie, nanfa Kano ne, Baban mu da brothers ɗina an san su sosai, idan na zo hotel wurin ka za asamu matsalar da tafi wacce za a samu idan ka zo gida..."

"OK yanzu kina nufin bazan ganki ba gaba ɗaya? Nace zan zo gidanku kin ƙi, nace ke ki zo nan ma kin ƙi..." ya faɗa cike da damuwa ni kaina acikin damuwar nake da kuma tarin ruɗani gaba ɗaya ban san menene mafita ba, jin ya kashe wayar ya tabbatar min da cewa wataƙila fushi yayi ko dai wani abu me kama da haka, hijabi na ɗauka, sai da na tabbatar babu wanda ya ganni sannan na sulale na bar gidan, gidan su ƙawalli na shiga inata cin uban sauri, ina shiga ummansu tace wai ban haɗu da ita ba dan itama wai yanzun nan ta fita unguwa, sake juyawa nayi cikin damuwa na fita, ina fitowa muka yi kiciɓus da ita,

"yan mata lafiya kuwa, saurin me kike yi haka?" ta faɗa tana kama hannuna, abin da ya fito dani na kwashe na faɗa mata na ƙare maganar da cewa,

"Ni yanzu ban san yanda zanyi in ganshi ba wallahi dan bani da wata dabara"

"Karki damu, kije gida ki shirya gani nan zuwa, Allah yayi zamu haɗu dan har na tari napep zamu tafi na duba handbag ɗina naga ashe ban ɗauki kuɗin ba, kije ina zuwa"

Cikin farin ciki na juya na koma gida ina zuwa na hau shiri cikin wata lafiyayyar stones grown nasha turare kamar wadda zan je gasar sarauniyar ƙamshi, ban wani ɓatawa kaina lokaci ba wurin yin doguwar kwalliya na ɗauki wayata da side bag ɗina ina jiran ƙarasowarta...........✍🏻




*Garin dadi littafin kudi ne ga mai bukatar cigaban labarin sai ya tura 500 ta 0774712835 Aisha Ibrahim Access Bank sai a tura evidence of payment ta wannan no 07044644433 ko a tura katin waya da shaidar biya wannan no 07044644433*



*_Ummi Shatu_*👌🏻
[1/5, 12:43] Maman K: ©️ *HASKE WRITERS ASSOCIATIONS*
_(Home of experts & perfect Writers)_




*GARIN DAƊI....!*💍💍



*_NA_*

*_UMMI A'ISHA_*


PAID BOOK 500


*Wattpad:ummishatu*



25


*Ina kuke manyan mata ƴan ƙwalisa ma'abota son gyara da kece raini, maza ku garzayo ku nemi maman Maryam domin samun lafiyayyu kuma haɗaɗɗun Lagos lace wanda zaku iya samun ɗinkakku da kuma sabbi a ledarsu, kaya iya zaɓinki, gefe ɗaya muna da GHT product, zaku samu,*

~MAI DA TSOHUWA YARINYA

~FEMALE CARE

~REODEO

~VIGOR MAX

~ LONGZIT

~B CLEAR

*DUK ZAKU SAMU WADANNAN KAYA CIKIN SAUKI DA RAHUSA MAZA KU NEMI MAMAN MARYAM AKAN WANNAN NO 07080222187, SIYAN NA GARI MAIDA KUƊI GIDA.....*


~~~Tabbas shi ɗinne nake gani kamar a mafarki yayi kyau har ya gaji cikin milk colour ɗin yadi na maza ɗinkin half jamfa kansa sanye da hula ya ɗaura agogon azurfa a hannunsa, sam babu abin da ya canja na daga halittarsa yana nan kamar yadda na san shi sai ma kyau da kwarjini da ya ƙara,

Zumbur na miƙe tsaye ina sake kallonshi fuskata ɗauke da mamaki sannan ga tsantsar farin ciki wanda ya taru ya haɗu da mamakin da nake ciki, shima tsayen ya miƙe yana kallona fuskarshi ɗauke da murmushi, ai ban san lokacin da na kwasa a guje ba na tafi gareshi, ina zuwa ya buɗe min hannuwansa sai kuma na tsaya turus sake buɗe min hannuwan nashi yayi, saida na rufe fuska ta da hannaye na sannan na iya ƙarasawa na shige jikinsa, rungumeni yayi yana dariya, nima rungume shi nayi tsantsam kamar ina tsoron kada ya sake tafiya ya barni.

Mun jima tsaye rungume da juna ina cikin ƙirjinsa ina shaƙar ƙamshin turaren da ke fita daga jikinsa gaba ɗaya ma na manta da cewa a falon Abba muke, sai da na tuna sannan na shiga kiciniyar raba jikina da nashi, duk da haka bai sake ni gaba ɗaya ba yana riƙe da hannuwana duka guda biyu muna zaune a kujera ɗaya sai kallon juna muke kamar zamu cinye junanmu,

"Baby..... Why all this silent? Yanzu kin kyauta kenan? You broke my heart...."

Murmushi nayi na sunkuyar da kaina ƙasa ina tunanin amsar da ya dace in bashi,

"Ba kaine ba ka tafi ka barni...." na faɗa cikin shagwaɓa ina turo masa baki,

"Am sorry baby..."

"ni ban haƙura ba, sai kayi min alƙawari guda ɗaya"

"Faɗa min ko menene am ready to do it...."

"Sai kayi min alƙawarin ba zaka sake tafiya ka barni ba"

Murmushi naga yayi kafin ya ɗauke idonsa daga kan ƙunshin hannuna ya kalleni,

"OK i promise you bazan sake tafiya in barki ba and i have a good news da zan faɗa miki"

"Gist me please" na faɗa ina kallonsa,

"well.... Am a Muslim now"

Ai jin maganar tasa nayi kamar cikin mafarki, rasa abin da zan yi nayi sai kawai na sake rungume shi ina jin ƙwallar farin ciki tana ƙokarin zubowa daga idanuwa na,

"Samz are you kidding me?" na buƙata cikin zaƙuwa,

"no am not..... Am serious baby"

"Thank you Cutie, thank you for saving my life......"

Ɗago fuskata yayi yana kallona kallo sosai irin na ƙurulla,

"baby naga kin canja, kin yi rashin lafiya ne?"

Kai na ɗaga masa ina murmushi,

"ayya sorry, kin samu sauƙi yanzu"

"Ehh na samu sauƙi, ya aka yi ka musulunta? Gidanku basu hana ka ba?"

Murmushi naga yayi idanuwansa akan hannuwana,

"Daddy na musulmi ne....."

"wai dagaske? Wow"

"seriously...... Shida uncle ɗina duk musulmai ne, mommy na ce Christian.... Amma shi Dad ɗinmu asali Christian ne sai daga baya ya musulunta shi kuma uncle ɗina tun asali dama musulmi ne...."

"Amma naji daɗin wannan labarin, soo what's your name now?"

Murmushi yayi ya sunkuyar da kai kafin ya ɗago ya kalleni,

"Guess it...."

Ɗan shiru nayi alamar tunani tsawon minti ɗaya nace,

"Muhammad..."

"uhmm kin kusa dai.... My dad is used to call me Muhammad but akwai inkiya"

"Wow..... I love you" na faɗa ina ɓoye fuskata,

"I love you too baby..... Kin rame amma kin fi kyau a haka"

Kallon jikina nayi dan ni kaina na san na rame amma maganar ma nafi kyau a haka bata taso ba sai dai shi ban san me ya gani ba, a haka anty ta shigo ta same mu tana ɗauke da babban tire na silva da kanta, fruits ne da abinci da juice da ruwa, bayan anty ta fita ina ƙasa ina zuba masa abinci naji yace,

"Ai lokacin da na zo naga mutane har gabana ya faɗi nayi zaton ko ke za ayi wa aure"

Sai da na ɗan dara sannan nace, "to da ni ɗin ce da ya zaka yi?"

"Allah da ba zan yarda ba, zan tada riot har sai an bani matata"

Dariya na sake yi bayan na gama zuba masa abincin nace,

"Ta ina na zama matarka?"

"matata ce mana, nan da 2 months"

"Ohh harma kayi fixing date shine ban sani ba"

Biye min yayi naci gaba da tsokanar shi har ya ci abincin ya gama, ni dai yau jina nake kamar ba ni ba dan tamkar a mafarki, mun jima muna hira dan har magrib saida yayi sallar magriba sannan ya tafi, a daren ranar Abba ya kirani yake tambaya ta wai ina son Muhammad zan aure shi? Shiru nayi na kasa bada amsa dan shine kaɗai namijin da nake so a halin yanzu daga ƙarshe Abba yace to in tashi inje amma zai ɗauki shiruna a matsayin ehh,

Ina komawa ɗaki na ɗauko wayata daga cikin drawer ɗin madubina wadda ke ajiye wata da watanni nan na kunnata ina kunnuwa massages suka yi ta shigowa wanda mafi yawa na samz ne, daren ranar kuwa kusan kwana muka yi muna waya dashi, washe gari ya koma Abuja ni kuma ranar muka fara bikin gidanmu dan ranar ne kamu, nida amarya wurin kwalliya muka je aka cancaremu aka fito mana da ainihin kyawun mu tun a wurin nayi pics na turawa abin ƙaunata, ita kuma ƙawalli sai tsokanata take wai in yi ingama nima nan da 2 months ne ni duk ban ɗauki maganar ta wani serious ba kamar yadda bana ɗaukar ta Samz serious idan yace saura namu nan da 2 months, cikin farin da annashuwa muka yi kamu muka gama, Ƙarshen gajiya na gaji dan ko Samz yau ba muyi doguwar hira ba,

Ranar ɗaurin aure sai gashi ya zo, ya sha farar shaddarshi ƙal dama can shi gwanin saka manyan kaya ne kuma suna yi masa kyau, a ranar ya koma bayan mun sha hira na kai masa abinci yaci,

Please Login or Register in order to submit comment