Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

haka ya sani nima bin bayan su dan na fahimci kishi ya rufe masa idanu dan haka zai iya aikata komai,

Jibgarta na samu yana yi kamar Allah ne ya aiko shi ga jini ta bakinta da hancinta sakamakon marikan da yayi mata masu zafi, ai ganin zai iya lahantata ya sani saurin zuwa na rikeshi ina roƙonsa,

"Sweet dan Allah ka rabu da ita..... Pls and pls..... Dan Allah...."

Da ƙyar ya saurare ni har na samu nasarar janyoshi muka fito falo, kallona ya shiga yi tun daga sama har ƙasa kafin ya sake komawa cikin bedroom ɗin nan na sake bin bayansa, tarar dashi nayi yana zuba mini kayana cikin bag sai huci yake, nidai ina tsaye ina kallon ikon Allah banyi magana ba har ya kammala ya rufe ya janyo jakar ya damƙi hannuna ya janyo ni fuuuuhhhh, muna fitowa falo su mommy na shigowa, tsayawa duk suka yi suna kallonmu musamman mommy,

"Samuel..... Lafiya kake? Ina zaka je?" mommy ta watso masa wannan tambayar tana bina da kallon tsana saboda har lokacin hannunsa riƙe yake da nawa,

"mommy zamu bar muku wannan gidan har zuwa lokacin da zaku tafi saboda bazan iya barin Matata ta cigaba da zama anan ba tare daku, wannan yarinyar amana ce a wurina, amana iyayenta suka bani ita and duk abinda ya sameta sai Allah ya tambayeni saboda yanzu nine komai nata bata da kowa anan sai ni..... "

" Samuel...... Samuel... Wai kana hauka ne? Baka da wata magana a koda yaushe sai ta matarka? Ita kaɗai ce damuwar ka da matsalarka? Nida yan uwanka ba damuwarka bane ko? Kai iya matarka kawai ka sani saboda da gold akayi ta.... "

Fitowar Felicia tana kuka shine sanadiyyar da gaba ɗaya hankula suka koma kanta, da gudu ta tafi ta faɗa jikin mommy tana kuka tare da sanar da ita irin uban jibgar da samz yayi mata,

" mommy ki daina sauraren wannan makirar yarinyar dan duk abinda zata faɗa miki ba gaskiya bane, ta yaya zata zo ta rinka kokarin sai ta afkawa Matata? Akan me? To gaskiya na gaji i will not take this....... Zan tafi da matata in kula da ita tunda duk wahalar da take yi muku bakwa gani "

" Kaine babban makaryaci Samuel..... Saboda matarka ka zabi ka ɓata da kowa ko? Matarka tafi maka kowa, duk abinda ta faɗa maka komai girmansa kanka ɗauka yake, yanzu ta zo ta shirya maka karya akan Felicia amma ka yarda.... Naga alama nan gaba ni kaina sai ta rabani da kai....."

"mommy......"

Dakatar dashi cikin tsawa tayi tare da ɗaga masa hannu alamar bata son jin komai, ni dai tuni na jima da soma zubar da hawaye saboda bakin ciki da bacin rai domin kiri kiri su mommy suka goyi bayan Felicia suka ce wai sharri nake yi mata dan kawai ina bakin cikin zaman su atare dani kuma ina son raba samz da yan uwansa,

"mommy babu maganar karya fa cikin wannan maganar saboda ki dubi jikin ta duk yakushi ne sannan har kayanta dake jikinta ta yaga, shima wannan din sharri ne ko set up kamar yadda kika fada?"

"kai samz ni matarka bata isa tayi wasa da tunani na ba kamar yadda tayi wasa da naka, in your stupidity duk abinda matarka ta fada hakane ko? Wannan karya ne, karya take yiwa Felicia dama ni na san tunda ka auri yarinyar nan to sai ta rabaka da kowa naka, she's a bad luck to our family...... Shiyasa tun farko ban goyi bayan ka aureta ba amma ka ƙi, to babu inda zaka je da ita, dole taci gaba da zama tare damu har zuwa lokacin da zamu tafi..... "

" mommy wannan ne bazai taba yuyuwa ba, bazan bari ku kashe yarinyar mutane ba, tunda ku dai kun zaɓi zama anan to ga gidan nan mun bar muku, duk wani evidence da zai iya satisfying dinki kan abinda yarinyar nan ta fada gashi nan na nuna miki amma kin rufe idonki kin ki gani saboda kiyayyar da kike yi mata, gaskiya wannan kiyayyar tayi yawa, bazan iya cigaba da barin ta tare da ku ba..... "

Daga haka ya fizgi hannuna nikuma na soma kokarin turjewa saboda bana son in bishi inja masa fushin mahaifiya amma wani kallo da yayi min ni kaina sai da na san yau ran ƴan mazan ya ɓaci duk da haka ban bishi ta sauki ba amma haka ya figeni bayan ya dauki wayata yasa cikin aljihu ya tisani a gaba har bakin titi inda ya tare mana abin hawa, har ga Allah bana cikin farin ciki da abinda yayiwa mahaifiyarsa dan ko babu komai itace sama da komai a gareshi a duniya amma sai dai na fahimci shima yau ransa ya baci ne,

Kuka nake yi amma bai saurare ni ba har muka je lodge ɗin da yace mai taxi ya kai mu, fito da kayan yayi ya biyashi sannan ya sake tisani a gaba zuwa ciki, apartments ne masu kyau da tsari na yan gayu wanda aka gina musamman da ma'aurata, mafi yawa masu honeymoon ke zuwa wurin su yi hutunsu dan kai ba zakace a ƙasa Nigeria kake ba, Allah kaɗai ya san yawan kudin da ya biya sai shi,

Kama hannuna yayi muka bi bayan ɗaya daga cikin ma'aikatan har zuwa apartment din da aka bamu, komai yaji tamkar a ƙasar turai sai dai sam bana farin ciki da hakan, da ace zuwan daɗi muka yi na san da zamu sha soyayya har mu gaji saboda yanayin wurin ma kadai ya isa jefaka cikin shauki da begen masoyinka sai dai amma kash wannan zuwan zuwane na bacin rai da takaici.

Ganin cikin matsanancin bacin rai yake shiyasa banyi masa magana ba na zuba masa ido, alwala ya shiga yayi domin lokacin salla ya yi wannan shine ɗaya daga cikin abinda ke kara burgeni dashi sam baya wasa da salla kuma baya sakaci da ita, duk abinda yake yi da zarar lokaci yayi zai bari yaje yayi salla, nima alwalar na shiga nayi bayan na yi wanka dagaske Felicia ta yayyakusheni dan har su kirjina da saman fuskata shiyasa sai da nayi mata Allah ya isa babu adadi, lokacin da na fito daure da towel yana kwance gefen gado har ya idar da salla amma kallo ɗaya zaka yi masa ka gane cikin damuwa yake, kayana na bude sai lokacin naga ashe harda nashi ya debo,wata farar doguwar riga marar nauyi na dauko na saka bayan na shafa turare, hijabi na saka naje nayi sallar nima, na jima cikin sujjadata ina kaiwa Allah kuka na idanuwana suna zubar da hawaye saboda ahalin yanzu nidai banda wata matsala da ta wuce ta dangin miji ban rasa komai ba sai soyayyar uwar miji da danginsa, wallahi sai yanzu na yarda idan mace zata yi addu'a akan aure is good ta hada harda uwar miji da dangin miji tare da abokan miji bawai iya miji nagari kadai zata roka ba dan ko mijin ya kasance na gari idan danginsa da mahaifiyarsa ba na gari bane to is another challenge, babu masifar da ta wuce ace dangin miji sun tsaneka especially ma mahaifiyarsa dan zaman bazai taba yi maka dadi ba komai soyayyarka da miji tunda ni kaina shaida ce, wasu addu'o'in na sake yi bayan na idar da sallar sannan na mike na nufi inda yake kwance gefen gado cikin damuwa, ni kaina acikin damuwar nake wadda kusan zan iya cewa tafi tashi domin babu dadi ace a kanka a samu sabani tsakanin uwa da ɗa wallahi a duk lokacin da na tuna hakan ina tsintar kaina cikin tsananin damuwa da bakin ciki marar misaltuwa duk da nasan har awurin Allah ban da laifi to amma na kasa samun sukuni acikin zuciyata, jikina a sanyaye na zauna gefensa tare da kamo hannayensa masu taushi na rike cikin nawa ina murzawa.........
[1/5, 12:43] Maman K: G*D


*Ina kuke manyan mata ƴan ƙwalisa ma'abota son gyara da kece raini, maza ku garzayo ku nemi maman Maryam domin samun lafiyayyu kuma haɗaɗɗun Lagos lace wanda zaku iya samun ɗinkakku da kuma sabbi a ledarsu, kaya iya zaɓinki, gefe ɗaya muna da GHT product, zaku samu,*

~MAI DA TSOHUWA YARINYA

~FEMALE CARE

~REODEO

~VIGOR MAX

~ LONGZIT

~B CLEAR

*DUK ZAKU SAMU WADANNAN KAYA CIKIN SAUKI DA RAHUSA MAZA KU NEMI MAMAN MARYAM AKAN WANNAN NO 07080222187, SIYAN NA GARI MAIDA KUƊI GIDA.....*



{40}



~~~Idanuwansa masu kyau da jan hankali ya buɗe ya zuba min yana kallona kamar yadda nima nake kallonsa da nawa koɗaɗɗun idanuwan,

"Boo..... Dan Allah ina neman alfarma, abubuwan da kayi baka kyauta ba bai kamata ka zama mai yin musayar yawu da mommy ba....." kstseni yayi ta hanyar faɗin,

"is ok baby...... Bana son wannan maganar yanzu, dan Allah ki rabu dani inji da abu daya, wacce irin biyayya ce ban yiwa mommy ba? Wacce biyayya ce bana yi mata tun daga lokacin da na mallaki hankalin kaina har zuwa yanzu? Amma duk da haka mommy bata gani, bata appreciating duk wani effort nawa.... "

" duk da haka uwa uwace bae, ba a taɓa yin fushi da ita..... "

" kinga dan Allah kar ki dameni..... " daga haka ya zare hannunsa daga cikin nawa ya juya tare da gyara kwanciyarsa, na san abinda ya faru ne yake yi masa zafi sannan gefe ɗaya ga kishin abinda Felicia tayi wadannan dalilan nasan ko bai faɗa min ba sune ke hana zuciyarsa sukuni a wannan lokacin amma koma dai menene zan bashi lokaci har ya huce sannan bazan ƙosa ba bare gajiyawa zan cigaba da nuna masa muhimmanci mommy a gareshi koda kuwa yankan naman jikinsa take yi.
***
Tun bayan tafiyar mu mommy ke ɓaɓatu su Felicia na sake zugata suna cewa ai na riga da na gama tsafe samz sai abinda na saka shi yake yi, duk wani abu wanda na hanashi tofa bai isa yayi ba yanzu gashi nan harda ita mahaifiyarshi na rabasu,

"Mommy ki duba kiga irin wulakancin da samz ke yi min duk wannan bai isheshi ba har sai da matarshi tayi min ƙarya da sharrin abinda banyi ba shikuma ya yarda, yanzu gashi ya tafi ya barki saboda ita bayan kina matsayin mahaifiyarshi...... This is very unfortunate...... Mtsww" Felicia ta fada cikin zuga tare da makirci, wani dogon tsaki Mary ta ja kafin ta kalli mommy cikin zafin zuciya tace,

"mommy..... Ki rabu dasu kawai ki saka musu ido, dole wata rana zai neme mu da kansa tunda mune dolensa, duk lokacin da matar tashi ta gama cinye masa kudin nashi ta gudu ta barshi ai dole wurinmu zai dawo...."

"Wannan ba magana bace, akan me za asaka musu ido abarta har tayi nasara akanshi? Mommy kiyi duk abinda zaki iya ki rabashi da ita koba komai ke mahaifiyarshi ce kece kika sha wahalarshi har ya girma ya zama wani abu ta ganshi ta aura, babu maganar abar mata shi har ta kai shi ƙasa..... Mtswww ni ina mamakin ma yadda wannan yar yarinyar take juyashi kamar wata babbar mace " Hadiza ta faɗa cikin ɓacin rai, ita dai duk mommy tana zaune tana saurarensu bata sake magana ba saboda ɓacin rai amma a cikin ranta ta ɗaukarwa kanta alwashin ba zata taɓa bari nida samz mu kasance ba saboda gani take kamar nazo in rabata da gudan jininta ne,

"ai kamar ma gani nayi tana da ciki..... Inahhh bazan taɓa haɗa zuri'a da waɗannan mutanen ba, wallahi bazan taɓa bari a haifi wannan cikin ba..... Bazai taɓa yuyuwa ba har abada" duk cikin zuciyarta take waɗannan maganganun bata bari wani daga cikin yaran nata yaji ba wannan dalilin ne yasa taji tana alla alla gari ya waye su koma Kaduna taje ta fara neman mafita.
***
Kamar yadda yace in rabu dashi ƙyaleshi nayi domin na san irin yadda yake ji a cikin ransa, har muka yi sallar ishah sai bayan da aka kawo mana abinci sannan ya tuna da batun abincina wato waina da kunu kamar yadda shi kadai nake iya ci a halin yanzu, cikin damuwa ya matso gareni ya rike hannuwana fuskar sa ƙunshe da tausayi na yace,

"baby.... Abincinki ya za ayi? Ko inje in fita yanzu ko zan samo miki?"

Girgiza masa kai nayi ina shafa fuskarsa nace,

"A'a sweet bana jin yunwa ai, a ƙoshe nake"

"no baby, ko ke bakya jin yunwa it may be babynmu yana bukatar abinci"

Murmushi nayi na girgiza masa kai nace,

"to zan ci wannan wanda aka kawo"

"tnx baby but Allah yasa ya zauna a cikinki i prayed"

"Insha Allah darling" na fada ina murmushi, abincin ya dauko kacokan ya kawo gabana ya soma budewa, tuwon semo ne miyar ogu sai snacks danginsu meat pie spring rolls etc, snacks din naci sosai dan kusan ma duk ni na cinye shi iya tuwon kadai yaci, shirin bacci muka yi bayan mun kammala, har lokacin ba a daidai yake ba akwai sauran fushi atare dashi, ni dai kasa bacci nayi inata sake sake acikin raina, na rasa wa yadace in tunkara da wannan matsalar tawa domin bana son ta shafi kowa dake kusa dani tunda kowa na duniya da ka gani yana da tashi kalar matsalar shiyasa babu bukatar ka kara masa damuwa da taka gara ka barshi shima yaji da tasa damuwar, na jima idanuwana biyu duk da bana danasanin auren samz domin bani da wata matsala dashi amma ina takaicin auren nan da uwar miji bata kaunata da wannan tunane tunanen bacci yayi gaba dani ina kwance killace cikin kirjinsa.

Da safe ya rigani tashi dan lokacin da na farka ma gani nayi baya cikin dakin kuma na san duk yadda akayi ya tafi ya samo min abinda zan cine,

Wanka na shiga nayi na fito har lokacin zuciyata babu dadi banyi wata doguwar kwalliya ba duk da na san shi uban gayyar yana son ganina cikin kwalliyar, atamfa na saka dinkin riga da skirt wanda ahalin yanzu har sun fara kamani, turare nasha ta ko ina sannan na fita falo, wurin fa ya hadu komai da akwai harda su kitchen idan kana da bukatar girka wani abu komai dai zamzam tamkar agidanka, kallo na ɗan kunna dan in dan debe kewa, wayata na ɗauka na kira anty,

"amarya...."

Cikin jin kunya nace "Haba anty har yanzu a amarya nake?"

"ehh mana, ko kin tsufa?"

Dariya kawai nayi nace "anty yagida ya aiki? Ina su fawaz?"

"duk suna nan lafiya.... Gashi can wurin bishra"

Hadani dasu tayi duk muka gaggaisa sannan muka yi sallama bayan ta dan kara bani shawarwarin yanda zan kula da gidana da mijina harda danginsa gaba daya duk da ban fada mata matsalata ba, su Annie na kira suma muka gaisa gaba daya sannan muka yi sallama, ina shirin kiran kawalli sai gashi ta kirani video call dariya nayi nace ƴar halak acikin raina kafin na daga kiran.

"amarsu ya ake ciki?" nace da ita bayan na daga kiran ina kallonta tana kwance cikin bedroom dinta,

"Ranki ya dade.....wow kawalli wanna falon fa Ina kuka je?"

Dariya nayi na fara haska mata ko ina na cikin falon zuwa bedroom da kitchen ina bata labarin zuwanmu apartment din amma kuma na ɓoye mata ainihin dalilin da yasa muka baro inda samz yake muka dawo nan da naji ta matsa da tambaya ma sai kawai nace mata hutawa muka zo yi, dariya tayi kafin tace,

"lallai kina shagalinki ƙawalli...."

"to ba dole ba" na bata amsa ina dariya tare da kallonta sosai dan cikinta har ya dan fito, mun jima muna hira kamar yadda muka saba kafin muka yi sallama na ajiye wayar, sake daukar wayar tawa nayi dan kiran samz amma kuma wayarshi a kashe nan na hakura na tashi na jona tv na fara kallon tashar mbc Drama, ina kallo ina gyangyadi da haka har ya dawo ya sameni, zama yayi gefena bayan na taro shi ta hanyar rungumeshi,

"Kin tashi daga baccin?" yace dani yana sakani gefen jikinsa,

"uhmmm.... Ina kwana?"

"lafiya lau my love, hope kin tashi lafiya?"

Kai na daga masa ina jinsa yana shafar wuyana da fuskata inda Felicia ta yayyakusheni jiya,

"Ga abincinki....." murmushi nayi yawuna yana tsinkewa, sake maƙaleshi nayi kafin nayi masa kiss akan lips ɗinsa,

"Thank you honey.... Kai kuma me zaka ci?"

"nayi order za a kawo min yanzu..."

Sake sunbatarshi nayi a fuska nace "that's my boo..."

Murmushi yayi ya sake kusantani da jikinsa ya soma bani abincin ina ci har sai da na ƙoshi,ban jima da kammala cin nawa ba shima aka kawo masa nashi ya fita ya karbo, nice nan na ciyar dashi kamar yadda yayi min,

"baby anjima zamu koma gida....."

Jin abin da yace ya sani kallon shi fuskata dauke da alamar son jin karin bayani, idanuwana ya hure min da iskar bakinshi yana kallona, lumshe idon nayi na bude naci gaba da kallonsa ina zaune rashe rashe kan cinyarsa,

"me ya faru zamu koma anjima?"

"su mommy sun tafi Kaduna yau"

"ya akayi ka sani? Kaje kunyi sallama ne?"

Girgiza min kai yayi yana wasa da yan yatsun hannuna,

"naje wurin ahmad da safe"

"amma shine ka kasa karasawa wurin su??"

Zuba min ido yayi ba tare da ya bani amsa ba, ganin dagaske dai bazai amsa min ba ya sani soma tsokanarshi ta hanyar yi masa cakulkuli, rike duka hannuwana yayi yana dariya yana cemin,

"baby you are asking for trouble...... You know how i get when you touched me like this...."

Dariya nayi na yunƙura zan tashi in gudu ya rikeni yana cewa ban isa ba sake cakulkularsa nayi kafin na gudu ya tashi ya biyoni, sunkuyawa yayi na haye bayansa muka cigaba da zagaye falon har zuwa wani lokaci.

Kamar yadda yace a ranar muka bar wannan apartment din muka koma gidansa, ahmad yayiwa waya yazo ya bude mana gidan domin dama shine ya rufe bayan su mommy sun tafi, kamar yadda na tsammata komai kaca kaca kamar irin nayi shekara bana gidan, tare da taimakonsa muka gyara ko ina, Turaren tsinke na kunna bayan na gama kintsa ɗakin na sake shimfida wani bedsheet din na cire wancan,

Sai da na tabbatar da yana cikin farin ciki sosai bayan mun gama shan soyayyarmu sannan na kwantar da murya na soma yi masa magana cikin jan hankali da shagwaɓa ina shafa sumar kansa wanda ke kwance saman kirji na,

"Boo.... Dan Allah ina son kayi min wani abu"

Shi duk a zatonshi wata bukata nake da ita ta kudi or something like that shiyasa yayi saurin cewa,

"Baby don't beg me please, duk abinda na mallaka naki ne, am here for you...."

"Nagode darling but ba maganar abinda ka mallaka bane..... So nake idan mommy ta dan huta kamar nan da 5 days kaje har gida ka bata hakuri akan abinda ya faru"

"saboda me?" ya bukata yana makale hannuna guda daya cikin nasa,

"saboda ta yuyu tana fushi da kai nikuma bana son hakan, bae ka san duk duniya babu wani fushi sama da na iyaye domin annabi yace fushin Allah yana daga cikin fushin iyaye.... Duk wadda iyayen sa ke fushi dashi to Allah ma fushi yake yi dashi, dan Allah kar kace A'a kayi hakuri kaje ka bata hakuri, yin hakan ba wai yana nuna Kaine mai laifi ba a'a kawai yana nuna kai mai biyayya ne agareta da gujewa fushinta.... "

Shiru naji ya ɗanyi na ɗan wasu sakanni kafin yayi kissing chest dina ya sake a karo na biyu,

"thank you baby.... Thanks for your love and care.... I love you soo much, goshinsa nayi kissing nima ina murmushi zuciyata dauke da farin cikin nasarar da nayi har ya amince da abinda nake so, " I love you too darling.... " na fada ina sake hugging dinsa......

*Garin dadi littafin kudi ne ga mai bukatar cigaban labarin sai ya tura 500 ta 0774712835 Aisha Ibrahim Access Bank sai a tura evidence of payment ta wannan no 07044644433 ko a tura katin waya da shaidar biya wannan no 07044644433*



*_Ummi Shatour_*✍🏻

[1/5, 12:43] Maman K: G*D


{41}


*Ina kuke manyan mata ƴan ƙwalisa ma'abota son gyara da kece raini, maza ku garzayo ku nemi maman Maryam domin samun lafiyayyu kuma haɗaɗɗun Lagos lace wanda zaku iya samun ɗinkakku da kuma sabbi a ledarsu, kaya iya zaɓinki, gefe ɗaya muna da GHT product, zaku samu,*

~MAI DA TSOHUWA YARINYA

~FEMALE CARE

~REODEO

~VIGOR MAX

~ LONGZIT

~B CLEAR

*DUK ZAKU SAMU WADANNAN KAYA CIKIN SAUKI DA RAHUSA MAZA KU NEMI MAMAN MARYAM AKAN WANNAN NO 07080222187, SIYAN NA GARI MAIDA KUƊI GIDA.....*


~~~Har talatainin dare idona biyu banyi bacci ba ina taya shi hira kamar yadda ya saba raba dare ba tare da yayi bacci ba,

"Baby....."

"uhmmm...." na amsa cikin shagwaba,

"yi bacci.... Dare yayi"

"kaima kayi bacci"

"no, ni zan kula dake a lokacin da kike bacci"

"ni ban yarda ba....."

"please mana baby...."

Tashi zaune nayi ina yin hamma dan tunda ya ambaci baccin naji yayi min dirar mikiya,

"what?" ya tambaye ni cikin kulawa,

"fitsari zanyi sannan zan sha ruwa...."

"Duk ke daya?" ya bukata cikin tsokana, kai na daga masa ina lumshe idanuwa alamar bacci,

"ok lets go..."

Daukata yayi har cikin bathroom nayi abinda zanyi na gama daga karshe na daura alwala shima yayi sannan muka fito, falo yaje ya dauko min ruwa yayinda nikuma nake kokarin kwanciya,

"ni mai sanyi nake so...."

"baby bakya jin magana ko? So kike mura ya kamaki keda babynmu?"

"babu abinda zai faru, ni bana son marar sanyi dan baya kashe min kishin ruwa"

"to babu mai sanyi sai dai in saka miki yayi sanyi"

"toh"

Juyawa yayi ya sake fita nikuma na kwanta tare da yin addu'a, ko minti biyu banyi ba bacci ya kwasheni dama yanzu haka nake bani da wahalar bacci kuma kowanne lokaci zuwa min yake yi bawai sai iya dare ba, cikin baccina wanda ya fara nisa naji shi yana tashina a hankali bawan Allah wanda ni harma na manta da batun ruwan duk da dagaske ruwan sanyin nake so,

"baby tashi ki sha ruwan gashi....."

Kasa tashi nayi har sai da ya sake maimaitawa sannan na tashi dakyar ya bani nasha sannan na sake komawa na kwanta shi dai ban san lokacin da yayi bacci ba.

***

"mom..... Wallahi ba laifi na bane, nayi duk iyakacin kokarina wurin ganin naja ra'ayin samz ya kulani amma duk abin yaki yuyuwa.... Kwata kwata yaki saurarata, kamar ba namiji ba haka yake sam babu wata da yake gani a gabansa sai wannan matar tashi banda ita bai damu da kowacce mace ba "

Fushin dake kan fuskarta ne ya sake karuwa cikin harzuka tace,

" Felicia kin bani kunya, i don't want to hear stories, abinda kika iya kenan koda yaushe, namiji guda daya kin kasa karkato da hankalinsa zuwa gareki har ki mallakeshi.... Kefa da bakin ki kika faɗa min matarshi ƙaramar yarinya ce you are older than her, kin fita wayo da duk wata dabara ta rayuwa to amma ya kika tsaya kina wasa da damarki har kina ikirarin hakura? Kin manta burinmu ne da kudurinmu a kansu? Ke kadai ce hope dina acikin wannan tafiyar idan kika yi giving up ki tabbata da duk wani burinmu da tanadinmu ya rushe...... " madam comfort ta fada cikin fushi wanda ya jima da bayyana akan fuskarta,

" mom ba wai nayi giving up bane, kawai dai na gaji ne, na gaji da wannan wahalar akan samz, wulakanta ni yake ako ina kuma a koda yaushe..... "

" haka zaki cigaba da hakuri ki daure har zuwa lokacin da hakarmu zata cimma ruwa, ki sani duk abu mai daraja samunsa baya zuwa cikin sauki kuma dole sai an sha wuya, kar ki sare kuma karki karaya, ki sani burin ki zai cika zaki samu samz kuma zaki mallakeshi mutukar baki giving up ba haka kuma burinmu zai cika........ "

" hakane mommy, tabbas kin sake bani kwarin gwiwa, ada na zama discouraged saboda irin yanda naga kamar babu hanyar cikar burinmu amma yanzu wadannan words ɗin naki sunyi encouraging dina kuma sun sake yimin ƙaimi na jin burina zai iya cika cikin kowanne lokaci.... "

" Haka nake son ji, keep your hope alive, kije kici gaba da kokari, ni mahaifiyarki ina baki tabbacin nasara tana tare dake "

" Thank you mom "

" you are welcome my dear"

Cikin bedroom ɗinta ta shiga ta zauna bakin gado ta soma kiran no samz sai dai amma tana ta ringing ba a dauka amma duk da haka bata hakura ba sake kira tayi bayan ta katse nan dinma ba a dauka ba atakaice dai sai da tayi masa miss calls guda biyar sannan ta hakura.
***
Cikin kwanakin biyu

Please Login or Register in order to submit comment