Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

awurinka..."

"baby waye wannan?"

"sunansa Hashim"

"kin san shi ne?"

"ehh na san shi tunda jimawa"

"ok indai kin san shi babu problem you can see him"

"thank you dear, Allah ya kara maka lafiya"

"amin baby, i love you"

"I love you too"

Muna gama wayar na turawa Hashim da text massage nace zai iya zuwa duk lokacin da yasamu time daga nan nafita falo dan ganin me ke wakana shin antyn ta sauko ko har yanzu dai tana saman, na jima a falon ganin bata fito ba ya tabbatar min da tana wurin daddy har lokacin.

Shi kam samz washe gari Kaduna ya tafi yaje ya samu daddy ya zayyane masa duk abinda ya faru sannan ya kara da cewa dan Allah da daddy din da uncle dinsa suje su dawo masa da matarsa domin anty tace ba zan dawo ba har sai komai ya gyaru ma'ana sai mommy taji aranta ba zata sake yimin abinda tayi ba, bayan ya gama fadawa daddy duk abinda ya faru yace yayi hakuri kar ya dauki mataki akan mommy sannan shi ba kararta ya kawo ba, haƙika ran daddy ya baci sosai irin bacin da samz yajima bai gani ba, cikin fushi ya tashi ya nufi falon mommy inda take ciki kwance tana hutawa dan bata jima da dawowa daga kasuwa ba,

"Maman Hadiza tashi ina son Magana dake...." daddy ya fada a fusace samz yana biye dashi amma shi ba haka ya so ba,

"Baban Samuel me ke faruwa?"

"lokacin da kika tafi Abuja me kika ce min?"

"nace maka zanje inga Dr saboda ciwon kirjina ya matsa min"

"to Dr din kika gani da kika je ko kuma gaban kanki da naki yi kika je kika yi?"

"ban fahimceka ba"

"ai bazaki fahimta ba, to naji duk diban albarkar da kika je kika yiwa yar mutane saboda ke baki san darajar aurenki ba shiyasa kike so ki kashewa wata nata auren, dama na fada miki na gaji da halin ki kawai ina zama dake ne saboda yara amma tunda har yanzu baki sallama kin gane ba ina mai tabbatar miki da dab nake da in sallameki kije can ki koma inda kika fito, ya yaro suna zaune da matarsa lafiya amma kin dage karfi da yaji sai kin rabasu? Ba a auren ke aka aureki har aka zauna dake duk kuwa da irin mugun halinki, to wallahi tallahi na gaji sannan na kai bango da wannan halin naki, idan har auren yaran nan ya mutu to kema ki fara lissafa kanki a sahun zawarawa.... " daga haka daddy ya juya ya fita ransa a mutukar bace, zama samz yayi gefen mommy wadda ke bin sa da kallon tuhuma tun bayan shigowarsa,

" ka zabi matarka akaina ko? Wato kai ka yarda in bar gidan ku akan ka rabu da matarka, wallahi nayi dana sanin haihuwarka samz, da na san haka zaka yimin bayan ka girma da tun farko gara ace na barar da cikinka"

"kiyi hakuri mommy, wallahi ban zabi matata sama dake ba Allah ma ya sani, kiyi hakuri" tashi tayi tabar masa wurin daga karshe shima ya tashi ya fita, a ranar daddy ya tafi Kano suka je gidanmu shi da uncle Ahmad, su gidanmu ma sai ranar suka san abinda ke faruwa nan Abba ya kira anty yace ta mayar dani gidana Insha Allah babu abinda zai sake faruwa dan an tsawatarwa da mommy sosai, duk da haka da daddy ya koma gida sai da ya sake yiwa mommy kashedin kar ta sake shiga shirgin samz da matarsa,cikin bakin ciki ta kada baki tace,

"yanzu me kake nufi ne? Kana nufin na koma gefe na nade hannuna ina ji ina gani yarona yana cikin wani hali na cutuwa? Yarinyar nan bata haihuwa shekara da shekaru har ƙaryar ciki tayi, magana ta gaskiya ni ina son ganin jikoki na, idan har zai ci gaba da zama da ita to ya zama dole ya kara aure ya auri matar da zata haihu "

" to ita haihuwa wai ba ta Allah bace? Ke shekara nawa kika shafe da muka yi aure kafin kika haihu? "

" ehh tabbas haihuwa ta Allah ce kuma ba kowa yake bawa ba, sannan da kake maganar nima sai da na jima kafin na haihu ai bazaka yi comparing case dina da nasu ba tunda nasu is different, ni lokacin da nayi aure ai banda shekaru kuma lokacin ba a haihuwa daga anyi aure, amma yanzu fa? Ana yin aure kafin shekara ta zagayo wani an haihu amma ita gashi nan shekara nawa yanzu? Wallahi dole yakara aure koda hakan shi zai zama silar da zaka sakeni " ganin da daddy yayi cewar idan ya daka ta tata tofa za a iya haifar dan da babu ido shiyasa ya rabu da ita taci gaba da babatunta.


Ni kam ina dakin Islam a kwance ban san me yake faruwa ba naga anty ta shigo tashi zaune nayi," anty maimakon ki kirani sai kuma ki zo da kanki"

"babu komai widat, Abba ne ya kirani"

"to me ya faru anty?"

"Abba yace iyayen mijinki sun je sun sameshi sun bashi hakuri kan abinda ya faru..... Amma Abba yace ba zaki koma ba"

"to shikenan anty Allah yasa hakan shi yafi alkhairi"

Murmushi naga tayi ta kama hannuna "ai na zaci zanga kin rusa ihu kina cewa ke sai kin koma to da wasa nake Abba yace in raka ki"

"Haba anty sai kace a zamanin jahiliyya? Ai duk hukuncin da iyaye suka yi daidai ne domin ba zasu taba cutar dakai ba"

"hakane, Allah yayi miki albarka,anjima sai mu raka ki ko"

"to shikenan anty duk yadda kika ce hakan za ayi"

"ehh gara mu rakaki kije kici gaba da jinyarsa"

Dariya nayi na rufe fuskata bance komai ba amma can cikin zuciyata wani irin farin ciki nake ji da dadi marar misaltuwa,

Sai da muka yi sallar ishah sannan anty ta kwashe mu nida yaranta gaba daya muka tafi, da alama shima yasan da zuwanmu duk da bamuyi waya dashi ba amma kamar zaman jiranmu yake yi, duka muka shiga bayan ya bude mana kofa sai lokacin yaran suka ga gidana nan duk suka fara rige rigen cewa zasu zo min hutu girgiza kai anty tayi tana cewa ba yanzu ba ai ba azuwama amare hutu,

"Haba anty ni din yanzu amarya ce?"

"haka dai kamar na gani" ta fada cikin tsokana,

"A'a anty gashi nan yana shirin kara ta biyu" na fada ina hararsa,

"au wai dagaske?" anty ta bukata cikin murmushi tana kallonsa, "A'a anty babu ruwana.... Kar ku tafi ku barni da rigima" ya karashe maganar yana kallona, sun dan jima a gidan kafin suka yi mana sallama muka raka su, muna dawowa yajani jikinsa ya rungume yana kissing goshi na,

"baby kinyi missing dina?"

"yes my dear...."

"am very sorry baby"

Fadin irin yadda muka kula da junanmu a wannan daren bata bakine domin mun nunawa junanmu soyayya kamar babu gobe, washe gari kam bai je office ba zama yayi muka cigaba da shan soyayyarmu muka wuni muna bacci zuwa yamma na samu sakon Hashim wanda ke son zuwa anjima, sanarwa da samz nayi shine ya tura masa da address dinmu nan na shiga kitchen na shirya mana abinci da abin sha,

Bayan sallar magriba ya fita domin shigo dashi nikuma na canja dressing dina daga na shan iska da shakatawa zuwa decent dress inda na saka doguwar riga ta atamfa Holland coffee color na yafa milk color din mayafi na fito, ina fitowa naji alamun shigowarsu, koda suka shigo zubama juna ido muka yi gaba ɗaya kowa yana kallon yanda ɗaya ya canja, shi dai cike da burgewa yake kallona dan na zama katuwa fiye da yadda ya sanni ada, yanzu na yi ƙiba na kara zama hajiya haka duk wanda ya ganni ya san babu wahala ko damuwa atare dani yayin da nikuma nake kallonsa cike da mamaki dan sai naga kamar hannunsa guda daya da matsala banda yaga yaga da naga yayi duk ya zuke ya rame fuskarsa babu komai sai idanuwana da hanci, sannan irin kayan dake jikinsa kadai sun isa sanar dakai wahala da kuncin rayuwar da yake ciki, kai gaskiya rayuwa da duniya abar tsoro ce kuma sai yau na sake tabbatar da hakan dan ban taba zaton zanga Hashim cikin wannan halin ba na ƙaƙa naka yi,

"Bismillah...." naji samz ya faɗa bayan ya kama hannuna yana nunawa Hashim wurin zama domin da alama baya son wannan kallon da yaga munata yiwa juna shiyasa watakila ya katse shi ta hanyar yin hakan,

"baby kawo mana abincin muci ko...." yace dani tare da bin bayana har zuwa cikin kitchen nan muka debo kayan tare har zuwa inda Hashim ke zaune yana bin ko ina na falon da kallo a ransa yana fadin "Allah sarki Maimunatu baiwar Allah.... Hakika Allah baya bacci gashi nan ya bata reasonable and matured miji suna zaune cikin farin ciki...."

"baby bana son wannan kallon da kike yi masa fa" naji samz ya fada bayan ya bugi kafadata da hannunshi lokacin da muke kokarin fitowa daga cikin kitchen..........



*_Ummi Shatu_*👌🏻
[1/22, 09:32] Maman K: 68

*Ina kuke manyan mata ƴan ƙwalisa ma'abota son gyara da kece raini, maza ku garzayo ku nemi maman Maryam domin samun lafiyayyu kuma haɗaɗɗun Lagos lace wanda zaku iya samun ɗinkakku da kuma sabbi a ledarsu, kaya iya zaɓinki, gefe ɗaya muna da GHT product, zaku samu,*

~MAI DA TSOHUWA YARINYA

~FEMALE CARE

~REODEO

~VIGOR MAX

~ LONGZIT

~B CLEAR

*DUK ZAKU SAMU WADANNAN KAYA CIKIN SAUKI DA RAHUSA MAZA KU NEMI MAMAN MARYAM AKAN WANNAN NO 07080222187, SIYAN NA GARI MAIDA KUƊI GIDA.....*


~~~Sunkuyar da kaina nayi ina murmushi kafin a hankali ince masa "baka da matsala Hubby", tare da shi muka je muka jera komai bisa katuwar dardumar da na shinfida, fried rice na dafa sai violent salad sai grilled chicken shikenan sai na hada strawberry milkshake, ni na zuba ma Hashim yayin da shi kuma samz ya zuba mana tare wanda naji dadin hakan dama tare muka saba cin abincinmu shiyasa yanzunma bamu raba kwano ba, bismillah samz yayi masa nan ya sauko muka fara cin abincin lokaci daya bayan mun gama Hashim ya dube mu gaba daya cikin nadama da kunya wacce tunda yazo cikinta yake yace,

"Hakika ban san da bakin da zanyi muku godiya ba, nagode madalla Allah ya saka muku da alkhairi, rabon da inci abinci irin wannan kai koma ba irin wannan dinba rabon da inci abinci in koshi har na manta, ubangiji Allah ya saka muku da mafificin alkhairi, Allah ya baku duk abinda kuke nema duniya da lahira, wato maimunatu dalilin da yasa kika ga na matsa kuma na dage akan sai nazo inda kike na ganki shine, tun shekarar da ta wuce nake ta fafutukar nemanki amma na gagara kuma na gaza samun ki, na jima ina nemanki tun bayan fitowa ta daga gidan yari.... "

" subhanallahi..... Gidan yari kuma? Me ya faru haka? " na fada ina kallonsa, sunkuyar da kansa yayi kafin yace,

" labarin mai tsawo ne amma zan gajarta muku shi ta yadda zamu samu mu gama da wuri, maimunatu na shiga tashin hankali irin wanda ban taba sanin cewar akwai shi ba sai da ya riskeni, hakika duk wanda yaci amana to sai yaga sakayya tun a duniya, na san naci amanar ki sannan na yaudareki shiyasa alhaki yake ta bibiyata har gobe bai barni ba, a lokacin da na rabu dake na koma wajen hajiya sharifa na tare banda matsalar komai duk da wani lokacin ina fuskantar wulakanci da tozarci daga gareta musamman idan tayi bakon da yafini kyau ko kuruciya amma duk haka nake hadiyewa kuma daga karshe sai na zama bani da amfanin komai a wurinta sai tukata a mota dan ta kwace mukullan shagonta dake wajena kaf, kwatsam sai wata rana tace in shirya in kawo ta Abuja kuma zamuyi kwana biyu nan na shirya muka kamo hanya amma da yake bamu taso da wuri ba dare ya riskemu a hanya, muna dab da shigowa garin Abuja wata mota tasha gaban mu dole na taka burki ashe barayi ne nan suka shigo cikin motar tamu suka umarce ni da inbi wata kwana nan nabi jikina yana rawa yayinda ita kuma suke dukanta suna jona mata iron ga bindiga sun saitata sunce tana ihu zasu harbeta, nan take suka kwace wayarta suka kwashe duk kudadenta dake banki bayan sun umarceta ta bude musu wayar, daga karshe suka daddaureta suka jefata waje ba tare da na sani ba dan na gama gigicewa, ni kaina sai da suka sumar dani kafin suka jefar dani suka tafi da motar, wallahi tallahi iya abinda na sani kenan bayan shi ban san wani abu ba sai kawai bude idona nayi na ganni agadon asibiti na jijji ciwo amma dan rashin imani ban kai ga gama warkewa ba naga zugar jami'an tsaro mota guda an zo tafiya dani.."

" innalillahi wa inna ilaihir rajiun" muka fada atare nida samz,

"Ashe bayan da suka jefar damu sun je sunci gaba da amfani da wayar hajja sharifa har suna ta karbar kudade a hannun mutane da sunan itace yayin da ita kuma take can kwance a gadon asibiti, sai da ta ji sauki sannan maganganu suka yi ta fitowa nan fa taje tayi report wurin yan sanda kuma koda suka tambayeta first suspect dinta cewa tayi nine nan aka je aka taho dani aka kaini cell aka rufe daga nan ban san hawa ba ban san sauka ba aka tura ni gidan maza bayan an tura mu kotu nasha bakar wahala, babu irin bayani da rokon da ban yiwa hajja sharifa ba amma taki yarda haka kuma taki fitar dani daga masifar da ta sakani haka na kwashe tsawon lokaci a gidan maza har zuwa lokacin da Allah ya hadani da wani bawan Allah mutumin kirki wanda shi barrister ne neman wani yaje dan ya tattauna dashi sai nikuma aka fito dani saboda case dinmu iri dayane an zata shine,

Nan muka tattauna dashi har ya fahimci dai bani ne wanda yake nema ba amma duk da haka sai yace zai taimaka min da iya damar da Allah ya hore masa kuma cikin ikon Allah cikin kankanin lokaci aka fito da file din shari'armu da hajja sharifa aka mayar wata kotun ta daban kuma anan ne muka samu nasara har Allah ya fito dani kuma sai bayan fitowa ta sannan na fahimci cewa ɗaya daga cikin yayyenki maza shine yayi min wannan taimakon tare da taimakon mahaifinku..... Maimuna babu abinda zance miki sai dai Allah ya saka miki da gidan aljanna keda mijinki da duk zur'arku gaba daya.... "

" ikon Allah, to yanzu wannan ciwon da na gani a hannunka kamar baya aiki sosai me ya faru? "

Ajiyar zuciya ya sauke tare da jujjuya hannun nasa kafin naji yace" bayan fitowa ta daga gidan gyaran hali sai naga ya dace in nemi aiki ko wata sana'a koda kuwa ta hannu ce domin zamana haka bazai yuyu ba tunda dole inada bukatu nan na samu wani kamfanin sarrafa robobi suka daukeni, ban jima da fara zuwa aikin ba na hadu da wannan iftila'in inda injin da nake aiki dashi ya kufce yayi min wannan lahanin a sanadiyyar haka dole na bar aiki kuma na kashe kudin da ni kaina ban san yawansu ba daga karshe ma sai bara na fara dan gaba daya yan yatsuna sun cire, ni yanzu damuwata ma na rasa matar aure, dukkan macen da ta ganni sai kiga kamar guduna take, na zama abun gudu awurin mata Maimunatu "

" Ina su Iya da walida? " na bukata cikin tausayawa,

" Allah yayi wa iya rasuwa ita kuma walida tayi aure acan wani kauye dake Gwarzo... "

" Allah sarki ubangiji Allah ya jikan iya da rahama... "

" amin ya Allah " ya fada cikin tsantsar nadama da damuwa, nidai gaba daya na rasa ta inda zan taimaka masa,

"To ni zanje in koma amma dan Allah ki yafe min widat"

"karka damu Hashim ai wannan maganar ta wuce ubangiji Allah ya yafe mana gaba daya dama ni ban rike ka acikin raina ba wallahi saboda duk abinda kaga ubangiji yayi to shine daidai fata dai Allah yasa mu fi karfin zuciyoyinmu sannan mu dauki darasin dake cikin wannan abun da ya faru... "

" nagode Allah yasaka da alkhairi, na gode sosai "

Ciki samz ya shiga ya dauko masa kudin da nidai ban san ko nawa bane ya bashi nan muka yi sallama dashi muka rakashi ya tafi mu kuma muka dawo ciki ga mamakina sai naga samz ya canja fuska ya bata rai haka dai muka yi sallar ishah muka idar duk baida walwala kai har muka je kwanciya bacci bai sakar min fuska ba, shareshi nayi har sai da na kammala shirina na bacci sannan na zo na kwanta acikin jikinsa, farar night gown na saka mai santsi mai siririn hannu iya gwiwa na sha humra da madarar turare kamar babu gobe,

"sweet hannuna yana ciwo" na fada cikin shagwaba da kuma jan hankali,

"me ya samu hannun?" ya bukata bayan ya kunna bedside lamp,

"nima ban sani ba... Kawai ciwo yake yimin"

"ok sorry..." ya fada yana kokarin matsa min hannun,

"wai fushin me kake yi boo?" nace dashi ina karkato da fuskarshi zuwa gareni dan ya wani dauke kai kamar irin muna gabar nan,

"what?" ya fada yana kallona,

"why all this vexed?" nace dashi ina kissing kumatunsa, Shiru yayi min yaki tankawa, girgiza shi nayi sannan cikin shagwaba nace,

"sweet..." kallona kadai yayi bai amsa ba,

"sweet" na sake faɗa ina jijjigashi, kallona naga ya sake yi

"wai laifin me nayi maka?" nace dashi ina kallonsa bayan na turo masa baki, Shiru yayi ya juyar da kai, kansa na hau na mika fuskata saitin da fuskarshi take nan ya sake juyar da ita daya saitin na sake binsa haka muka yi ta yi har ya gaji ya tsaya wuri daya ya zuba min ido kawai,

"sweet are we fighting?" na fada ina rakwarkwabe fuska, kai ya daga min wai ehh,

"am very sorry...."

Kai naga ya girgiza min alamar bai hakura ba, kunnuwana na rike ina sake ce masa "am very sorry" amma sai ya girgiza kai wai bai hakura ba daga karshe sauka nayi daga kan gadon na rike kunnena zan fara tsallen kwado ai ban kai ga farawa ba naga yayi sauri ya diro daga kan gadon ya dagani yana bude baki alamar mamaki,

"baby what's this? What are you trying to do? Menene hakan?"

"to ba Kaine kake fushi ba kaki kulani kuma na baka hakuri amma kaki hakura..."

"shine kuma zakiyi tsallen kwado?" kai na daga masa,

"no banda wannan, kar kiyi punishing kanki da wannan"

"to ka hakura?" na tambayeshi muna kokarin hawa saman gadon wanda ya sha farin bedsheet mai tarin pillows da yawa sama da guda goma daya daga cikin gifts din da anty ta hada min ne tun lokacin bikina dan ta siya min bedsheets sunfi kala biyar,

Kwanciya naga yayi ya juya min baya ya dauki pillow guda daya ya runguma ai take na matsa na kwace pillow din Ina turo masa baki akan me zai rungumi pillow, wani ya sake dauka shima na kwace, ya sake daukar wani shi dinma na kwace, kallona yayi na wasu sakanni kafin naga ya janyo wani pillown mai design din heart ya rungume nan nayi nayi in kwace na kasa dan ya kankameshi sosai kuma ya rufe idanuwanshi, pillow na dauka na daki kafadarshi yai burus kamar bai ji ba haka nayita dukanshi da pillow amma yaki motsi daga karshe na ja masa hancinsa sai lokacin ya bude idonsa, juyawa nima nayi na ja baya zan matsa in bashi wuri ashe ina dab da bakin gadon nan nayi baya zan fada yayi saurin riƙoni ya dawo dani tsakiyar gadon,

"ba zaka fada min laifin da nayi maka ba ko?" na fada ina kokarin kakalo kuka,

"dama baƙon naki ex dinki ne? Yazo yayi ta wani kallonki kema kina kallonsa"

Goshina na dafe ina kallonsa, "yanzu dama wai akan wannan ne? Dan Allah yanzu ko ce maka akayi wannan bawan Allahn zai burgeni ko ya ja hankalina sai ka yarda? Kaga fa halin da yake ciki shi kansa tausayin kansa yake ji saboda irin hisabin da yake karɓa......"

"daga yau babu ke babu shi...."

"ko baka faɗa ba dama sweet bare kuma ka fada, wallahi babu wani namiji dake burgeni yake tafiya da tunani na sai kai kadai, kai nifa ban taɓa ganin mai irin kirarka ko halittarka ba sai a irin Turkish dramas dinnan.... Kai one in town ne" na fada ina hayewa jikinsa tare da hada fuskata da tashi,

"saboda me?"

"saboda kai na musamman ne.... Nifa ban taba tunanin zan iya da kai ba" dariya naga yayi har sai da haƙoransa suka bayyana ya sake matseni sosai a kirjinsa yana shakar kamshina.........




_*Ummi Shatu*_👌🏻
[1/23, 15:39] Maman K: 69


*Ina kuke manyan mata ƴan ƙwalisa ma'abota son gyara da kece raini, maza ku garzayo ku nemi maman Maryam domin samun lafiyayyu kuma haɗaɗɗun Lagos lace wanda zaku iya samun ɗinkakku da kuma sabbi a ledarsu, kaya iya zaɓinki, gefe ɗaya muna da GHT product, zaku samu*,

~MAI DA TSOHUWA YARINYA

~FEMALE CARE

~REODEO

~VIGOR MAX

~ LONGZIT

~B CLEAR

*DUK ZAKU SAMU WADANNAN KAYA CIKIN SAUKI DA RAHUSA MAZA KU NEMI MAMAN MARYAM AKAN WANNAN NO 07080222187, SIYAN NA GARI MAIDA KUƊI GIDA.....,*

~~Tsawon kwana biyu ya ɗauka yana yimin rigima tun bayan da Hashim yazo, nidai a koda yaushe kuma a kowanne lokaci nuna masa nake zuciyata bata da wani gurbi da zata ajiye wani bayan shi amma duk da haka yaki daina wannan rikicin,

"wai yaushe ka koyi rigima ne sweet?" na fada ina jan hancinsa kasancewar tsaye nake gabansa inda shi kuma yake zaune kan stoll ɗin mudubina bayan ya fito daga wanka ina shirya shi,

"babu wani rigima da na koya..."

"to inba rigima ba yaushe zaka rinka tunanin zan kara saurarar wani namiji alhali ka zuba min zumar sonka na lashe...."

Hannuna ya rike guda daya bayan na gama taje masa sumar kansa,

"kika ce me?"

"na kurbi zumar kauna...kuma na lashe....."

Dariya yayi ya sumbaci hannun nawa nan na kammala shirya shi nima na shirya cikin wata onion pink din doguwar riga nayi rolling da farin veil dama nace masa unguwa zai rakani, hannuna ya rike muka fita, koda muka kusa zuwa inda nake da niyyar zuwa idonshi na rufe masa da dan kwalin rigata shiyasa dama na taho dashi saboda baida wani girma, hannunsa na kama har muka shiga wurin,

"baby..... Ina muka zo ne?"

"nazo in siyar da kai mana..." na fada daidai lokacin da muka shiga cikin wurin kuma sai lokacin na bude masa fuskar tashi me zai gani? Wani dan karamin wurin cin abinci ne na kama ya sha decoration sai babban cake da akayi banda sauran snacks ko ina an rubuta HBD Sweet,

" happy birthday to you.... Happy birthday to you...." yaji daga bayan shi yana juyawa yaga Ahmad da matarshi harda babynsu, gaba daya mamaki ya cika shi ya rasa ma me zai ce kawai sai ya rungume ni yana kissing goshina, nima rungumeshi nayi ina dariya,

Wurin ya kayatu saboda babu hayaniya kuma babu idanuwan mutane da yawa, kida aka dan saka mana yana tashi kasa kasa nan muka ɗan taka sannan muka yanka cake muka yiyyi pictures bayan munci mun sha muka koma gida,

"baby wai yaushe duk kika shirya wannan abun?"

"Haba sweet ai ka cancanci fiye da haka, you deserve more than this my love...." na fada ina hugging dinsa,

"thank you alot my dear... Allah yayi miki albarka"

"amin honey...."

Yanzu dai zamanmu yafi daɗi fiye da baya saboda bamu da matsalar kowa kuma babu damuwar komai, na maida hankali kan business dina da nake yi na snacks wanda ya karbeni dari bisa dari sannan ga riba da nake samu, duk da kudin da nake samu samz bai taba saka ido akai ba ko yaki yimin abubuwan da ya saba shiyasa nima ban bari idanuwana sun rufe ba bare kaina ya kulle, abubuwa nake siya masa kamar ban san zafin kudina ba nima, inner wears, turaruka, kayan bacci agoguna, takalma duka siya masa nake kuma masu tsada, haka dai muketa lallaba rayuwarmu cikin farin ciki da kaunar juna,

Hutu muka dauka nida shi gaba ɗaya muka tafi Kano

Please Login or Register in order to submit comment