Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

amma har nayi na gama bata kulani ba, tashi nayi na fita na koma ɗakina na cigaba da zaman ƙunci.

Har weekend ɗinnan yaci ya cinye cikin damuwa nayi shi ranar Monday kuwa ban iya fita aiki ba nidai duk gani nan ne damuwa ta taru tayi min yawa, daren ranar ban san me ya faru ba kawai dai naga mama ta shigo tace in je abba na kirana, hijabi na nasaka na fita, yana zaune falonsa yana cin tuwon dare, tuwon biskin masara miyar taushe zama nayi gabansa na fara gaishe shi, ɗagowa yayi ya kalleni,

"maimunatu..... Har yanzu wannan maganar tana ranki tana damunki?"

Girgiza kai nayi alamar a'a sannan cikin sanyin murya nace "a'a abba na yarda da duk zaɓin da kayi min"

Murmushi naga yayi ya cigaba da cin tuwonsa kafin daga bisani ya sake ɗagowa ya kalleni,

"maimunatu kina son faisal? Ma'ana zaki iya zama dashi a matsayin miji agareki ko zuciyar ki bata aminta da shiba?"

Girgiza kaina nayi alamar zuciya ta bata aminta dashi ba, abba bai ƙara magana ba har sai da ya kammala cin abincinsa sannan yace dani,

"maimunatu bazan yi miki auren dole ba, domin mune a koda yaushe muke yi wa mutane nasiha akan kar su aurar da yaransu ga wanda basa so, mu alƙalai mune muka fi kowa sanin haɗarin dake tattare da wannan al'amari domin mune ake kawowa ƙara muke ganin cases kala kala sanadiyyar auren dole, ko yau ɗinnan sai da nayi shari'a makamanciyar wannan, tunda bakya son faisal to bazan tilastaki ba, kije Allah yayi miki zaɓin miji na gari ki kawo duk wanda kike so in dai mutumin kirki ne zan aura miki shi..... Allah yayi miki albarka "

Wani sanyi naji yana ratsa zuciya ta cikin farin ciki na sunkuyar da kaina nace" nagode abba, Allah ya ƙara lafiya da tsawon kwana "

" amin tashi kije "

Tashi nayi ina fita na ruga a guje zuwa cikin ɗakina ina shiga na dungura akan gado na sake dungurawa haka nayi ta yi dan tsananin farin ciki, yau kam faɗar irin halin murnar da nake ciki ɓata baki ne,bacci kuwa harda minshari dan har makara nayi.

Washe gari kamar koda yaushe lokacin da naje gaida Annie bata amsa ba dama kwana biyu bata amsa ni, har na juya zan fita naji tace "zo nan"

Dawowa nayi na tsugunna,

"widat haka kika ga ya fiye miki ko? Kin fi so kiyi ta zama agabanmu babu aure ko, yanzu menene laifin yaron nan faisal, inane zai je neman aure a hana shi? Baida wata makusa sai awurinki da kikace bai yi miki ba"

"Annie kiyi haƙuri, ki cigaba da yi min addu'a insha Allah zan kawo wanda yayi min"

"Allah ya zaɓa miki mafi alkhairi ya baki nagari mai sonki da gaskiya"

Tashi nayi na fita naje na ƙarasa shiryawa domin tafiya aiki, yau ma ta gidan su hashim na fara biyawa na kuwa iske shi yana nan bai fita ba,

"yau ma na zaci ba zaki zo ba ai, gashi ban san inda zan je in nemoki ba, lafiya kuwa jiya naji shiru?" ya faɗa bayan mun fito daga gidan domin tafiya,

"lafiya Lau hashim, jiya dai ban ji daɗi bane sosai shiyasa"

"ayya shiyasa ashe naji jikina nima babu daɗin, ashe ƴar kyakkyawata ce bata jin daɗi"

"hashim kenan, wai waye ya faɗa maka ni kyakkyawa ce? Kama cire wannan tunanin daga cikin ranka dan bana so ranar da idonka ya buɗe ka ganni ba yanda ka zata ba"

"hmm maimunatu kenan.... Wallahi a duk yanda kike kin yi min, ko yaya kike ina son ki kuma bazan taɓa dainawa ba, ko duk matan duniya kinfi su muni to ni awurina kinfi kowacce mace kyau... Bana jin zanga wata mace wadda tafi ki kyau a idanu na"

Irin waɗannan kalaman na hashim sune ke ƙara min ƙwarin gwiwa wurin ganin na cimma ƙudurina na taimakawa rayuwar sa musamman ma yanzu da maganar aurena da yaya faisal ta gama rushewa, so da ƙaunar da muke nunawa junanmu abin ba a cewa komai, koda yaushe muna tare, sau da yawa na kan gayyaceshi muje film house cinema duk da ba idanu gareshi ba amma hakan na lura yana saka shi farin ciki sosai, duk inda na san zai ɗebe masa kewa ya sanyashi farin ciki ina kai shi, wuraren shaƙatawa da tanɗe tanɗe gami da lashe lashe duk mukan je kuma babu wanda zai ganshi yace makaho ne dama kuma na siya mana wasu glasses masu kyau ta jumia iri ɗaya baƙaƙe koda yaushe shi yake sakawa.

Yau dai na shirya tsaf domin aiwatar da ƙudurina da na jima ina shiryawa akan hashim, sai da nayi musu siyayyar kayan abinci kamar yadda na saba duk ƙarshen wata sannan naje gidan, kamar koda yaushe godiya da albarka iya keta faman saka min bayan ta tsagaita na kalleta cike da kunya nace,

"iya dan Allah zan ɗan yi miki wata tambaya, wai dama hashim da wannan lalurar aka haife shi ko daga baya ya haɗu da ita?"

Shiru naga tayi kafin ta nisa tace dani,

"a'a lafiya lau ras aka haife shi da idanuwansa... Saida ya fara girma ma ya kai kimanin shekaru takwas sannan wani al'amari ya faru dashi wanda shine kamar silar makancewarsa..... Wani mafarki yayi wani abu adunƙule mai duhu yazo ya daki idanuwansa shikenan ya tashi babu ido... Magani mun yi har mun gaji tun mahaifinsa yana raye, kuɗin da muka kashe ba zasu lissafu ba dan kayan ɗakina duk anan suka ƙare wurin nema masa magani amma ba ayi dace ba, sai lokacin da mahaifinsa yana kwance yana jinyar ajali wani amininsa ya iyo masa aike daga ƙasar chadi cewa an samu mai magani acan wanda insha Allah ana saka ran wai idan aka kai hashimu wurinsa to zai samu waraka amma mu dai har yau ba mu samu zuwa ba domin kuɗin da aka yanka sunyi yawa ba kaɗanba. "


Ajiyar zuciya na sauke ina godiya ga Allah acikin raina domin insha Allah komai yawan kuɗin a shirye nake in nemo inbada in dai idanuwan masoyina zasu buɗe zai ganni kamar yadda yake mafarki kullum maganarsa yana son yayi tozali da kyakkyawar fuskata koda sau ɗayane a tarihin rayuwarsa..............


*Garin dadi littafin kudi ne ga mai bukatar cigaban labarin sai ya tura 500 ta 0774712835 Aisha Ibrahim Access Bank sai a tura evidence of payment ta wannan no 07044644433 ko a tura katin waya da shaidar biya wannan no 07044644433*

*_Ummi Shatu_*👌🏻
[1/5, 12:43] Maman K: ©️ *HASKE WRITERS ASSOCIATION.*
_(Home of experts & perfect writers)_



*GARIN DAƊI......!*💍💍



*_NA_*


_*UMMI A'ISHA*_


*Wattpad:ummishatu*




From the writer of

KAMAR DA WASA
KUMALLON MATA
MIJIN MATACCIYA
SO DA ALAƘA & Rest.....


*8*



~~~Sai da na ɗan nisa kaɗan sannan na kalli iya zuciya ta cike fal da farin ciki nace,

"iya ban tari numfashinki ba kuɗin zasu kai har naira nawa...."

Jugum naga tayi kuma ta rafka tagumi alamar tunani, zuwa can ta ɗago ta kalleni,

"ƴarnan kuɗin nan fa da yawa dan tun a lokacin malam ɗan bahago aminin mahaifinsu cewa yayi muddin wannan malamin zai yi mana aiki to sai mun bada kuɗi sama da dubu dari biyar a lokacin, tun lokacin haka yace bare yanzu da komai ya sake tsananta abubuwa duk suka sake yin tashin gwauron zabi..... "

" hakane, amma iya a ina za asamu shi aminin baban domin a sake jin dahir ɗin inda za asamu shi mai maganin? "

" ehh to, a gaskiya yanzu ba nace ga takamaimai wurin da za a samu ɗan bahago ba domin mafatauci ne, yawo yake yi ƙasashen duniya, wuri daban daban yake zuwa yau yana nan gobe yana can, ko lokacin da mahaifin su hashimu ya rasu da iyalinsa tazo gaisuwa cewa tayi shi ɗin yana can ƙasar Mali, sanin takamaiman inda yake sai an dangano da iyalinsa.... "

" to iya a ina iyalin nasa suke? Ai sai aje a tambayo su inyaso sai su haɗamu dashi yayi mana bayani..... "

" to shikenan sai inje, suna can wajen Kano daidai wannan ɗan dajin dake tsakankanin kano da Katsina.... "

" yawwa iya sai ki daure kije"

"zan je in Allah ya yarda"

Tashi tayi taje taci gaba da ƴan aikace aikacenta domin Amira bata nan, shirun da muka yi gaba ɗayanmu nida shi na katse ta hanyar faɗin,

"wai lafiya kuwa naga kayi shiru ranka ya daɗe?"

Ɗan kawar da kansa yayi kafin ya bani amsa da,

"gaskiya maimunatu ɗawainiyar da kike yi dani tayi yawa...... Tunda muka haɗu ban taɓa yi miki wani abu na kyautatawa koda sau ɗaya ba amma ke kullum cikin yi min wahala kike, anya wannan tarayyar tamu babu ƙwara aciki?"

Tamke fuska nayi nasha kunu kamar yana kallona cikin ɓacin rai nace,

" ohhh kulawar da nake yi da kai ashe dama wahala ce ban sani ba? Ashe dama tsakaninmu akwai ƙwara ni ban sani ba? Hmm to ai gara da ka tunatar dani abin da na manta" daga haka na ɗauki handbag ɗina na zira takalmi na nayi gaba dama sai da na hanga na hango na tabbatar iya bata kusa,

A bakin ƙofa na tsaya daga waje domin nasan dole zai biyo baya na, ban kai ga gama tunanina ba kuwa sai gashi ya fito, baya na juya masa,

"Haba maimunatu menene kuma abin yin fushi daga magana? Kiyi haƙuri ban san cewa hakan zai ɓata miki rai ba"

Sai lokacin na juyo na kalleshi, ƙura masa ido nayi duk da nasan shi ba ganina yake yi ba, "baki haƙura bane? Ki sani duk punishment ɗin da kika ga yayi daidai da laifin da na aikata"

Dariya nayi na ɗan rausaya "ta yaya zan baka punishment? Ka rufa min asiri ban isa yin wannan ɗanyen aikin ba"

"waye ya faɗa miki cewa ɗanyen aiki ne? Karma ki ƙara faɗa"

"to shikenan bazan sake ba, nidai yanzu daga nan gida zan wuce, ka faɗawa iya na tafi"

"zan faɗa mata kin yi fushi shiyasa ko sallama baki yi mata ba"

"nayi fushi abaya amma yanzu na huce, kuma dama ai kaine ka saka nayi fushin"

"to ina neman afuwa"

"kin wuce wannan matsayin agareni, duk laifin da za kiyi min komai girmansa na yafe miki tun kafin kiyi"

"ka jika ko, so kake ka shagwaɓani kenan inyita cin kare na babu babbaka tunda an ce an yafe min"

"ki yi min duk abin da kike so in dai nine na yafe miki"

"nagode da wannan karamcin da karramawar, ubangiji Allah ya baka lafiya....."

"amin mai tagwayen suna, nagode, Allah ya kai min ke gida lafiya, agaida min su mamana"

"basa cin miƙe" na faɗa daidai lokacin da muka fara tafiya zamu bar ƙofar gidansu,

"to ai ba laifina bane laifin maimunatu ne da bata rakani na gaishe su ba"

"hmmm wato har ka samo hanyar da zaka kare kanka ko"

"to ba gaskiya na faɗa ba?"

Kafin ya bani amsa Amira ta ƙaraso tare da ƙawayenta guda biyu, gaishemu suka yi sannan suka wuce suna bin mu da kallon sha'awa, kai bama su ba ku san duk wanda ya ganmu sai yaji mun burgeshi domin munyi mutuƙar dacewa da juna ta ko ina. Daƙyar muka rabu na shiga napep na tafi, ina sauka na hangi yaya Abdul hakim tsaye shida ƙawalli ko me suke cewa oho na raya hakan acikin raina, tun kafin inƙarasa yaya Abdul hakim ke faman bina da harara dama can bama shiri to bare yanzu da yake jin haushina naƙi auren yaya faisal,

Wuce su nayi zan shiga gida, muryar ƙawalli naji tana cewa "ba faɗa meya kawo gaba ƙawalli"

"au dama kune? Ai ban ganku ba" daga haka nayi ciki, murmushi tayi ta kalli yaya Abdul hakim,

"me kayiwa ƙawata da har laifinka ya shafeni?"

"wannan ƙawar taki ai bata da kunya" daga haka ya wuce masallaci ita kuma ta shigo ciki, ina rage doguwar rigar jikina ta shigo ta iskeni,

"gaskiya baki da mutunci ƙawalli, yanzu mu kike cewa wai baki ganmu ba?"

"ai yaya Abdul hakim ɗinne sai ana yi masa haka, haba mutum yabi ya takura min sai faman haushina yake ji dan kawai ban auri abokinsa ba, to ana dole ne?"

"dan Allah wannan maganar ta wuce, a fuskanci gaba kawai, dan yanzu shima maganar da yake yimin wai yaya faisal ɗinma har ya samu mata, ya ma tura gidansu"

"dama can wataƙila suna tare, kawai yaudara ce irinta maza"

"ba lallai suna tarenba, ta yuyu dai yanzu suka haɗu kuma Allah yayi abin cikin gaggawa"

"koma dai yaya ne su ya dama, nima ai na samu nawa masoyin"

"nidai yanzu kinga tafiya ta, sai an jima dan tun ɗazu na fito daga gida na zo muka sha hirarmu da su Annie har yaya Abdul hakim ya dawo, na wuce gida sai kin shigo"

"to shikenan bari nayi wanka sai in shigo"

Fita tayi nikuma na ɗauki wayata na soma duba number din farida wadda aka ɗaukemu aiki tare, ada dai sanin da nayi suna yin adashe amma ni ban taɓa yiba, jin ta ɗauka yasa nayi saurin mayar da hankali na kan sallamar da take yi min,

"yawwa farida dan Allah har yanzu kuna yin wannan adashen ne?" na buƙata bayan mun gaisa, shiru naji ta ɗanyi kafin ta bani amsa da cewa,

"ehh gaskiya mun kwana biyu ba muyi ba amma muna son mu fara daga this month, za kiyi ne? "

"ehh ina son yi amma na nawa nawa za ayi?"

"last time dai da muka yi na 20k muka yi mu 10 Kinga 200k kenan.... Yanzu kuma da zamu daure sai muyi na 30k amma sai yadda aka tsara dai"

"yawwa farida dan Allah ayi hakan kuma ina buƙatar alfarma a bani ɗaukar farko saboda wata matsala ce ta taso min kuma inada buƙatar kuɗi wallahi cikin gaggawa"

"to shikenan zan tuntuɓesu inji, duk yadda aka tsayar da magana zaki jini, Allah ya wuce mana gaba"

"amin ya Allah nagode farida"

Daga haka muka yi sallama na ajiye wayar ina jin farin ciki yana shiga kowanne lungu da saƙo dake cikin zuciya ta domin hashim ya kusa ganin fuskata, ya kusa ya daina hasashe ko in ce laluben kamannina, madalla da ubangiji mafi tsarki fiye da komai.

Daren ranar duk na ƙarar dashi ne wurin tunani tare da ƙulla ƙullar ta yadda zan samu tsabar kuɗi kuma zunzurutunsa har sama da naira dubu ɗari biyar daga ƙarshe naga bani da wata mafita illa guda ɗaya, mafitar kuwa itace inci bashi daga bankin da nake hulɗa dasu ma'ana salary account ɗina kuma dama anan ne nake ajiyar kuɗaɗe na, kwata kwata zuciya ta bata gamsu ko ta amintu da in sanarwa wani ko in nemi shawarar wani ba koda kuwa acikin gidan mu ne domin ta yuyu a iya sace min gwiwa daga wannan kyakkyawan ƙudurin nawa wanda na san zan samu tagomashin lada har a wurin ubangiji na,

Dole ta sa nayi amanna da shawarar da zuciya ta tabani na in ciyo bashi daga banki sannan gefe ɗaya in fara zuba adashen da su farida zasu yi wato ƴan office ɗinmu,

Ban sanarwa da kowa ba washe gari kafin naje office na biya ta banki domin gudanar da buƙatata, har wurin manager aka kaini, ɗan kyakkyawa dashi matashi dan bana tunanin ma ko auren fari yayi duba da irin yadda yake wani lallaɓani yana yi min kirki dan abun bai wani ɗauki dogon lokaci ba daga ƙarshe yace wai inbashi no ɗina duk yadda ake ciki zai kirani ya sanar dani, godiya nayi masa na tafi domin har na ɗan makara akan time ɗin da na saba zuwa office, ina zuwa office na iske su farida har sun haɗu sun gama tatraunawa kan maganar adashen da za muyi kuma kowa ya amince saboda dama su sun saba yi lokaci zuwa lokaci dan har na 50k suke yi yadai danganta da halin da aka samu kai, daƙyar suka amince zasu bani ɗaukar farko saboda kusan kowa yana son ɗaukar farkon, ajiyar zuciya na sauke domin insha Allah ina sa ran na gama da wannan matsalar yanzu saura ƙiris, da yardar ubangiji sai na zamo silar murmushin hashim sai na zame masa sanyin idaniya na har abada......... ✍🏻



*Garin dadi littafin kudi ne ga mai bukatar cigaban labarin sai ya tura 500 ta 0774712835 Aisha Ibrahim Access Bank sai a tura evidence of payment ta wannan no 07044644433 ko a tura katin waya da shaidar biya wannan no 07044644433*


*_Ummi Shatu_*👌🏻
[1/5, 12:43] Maman K: ©️ *HASKE WRITERS ASSOCIATION.*
_(Home of experts & perfect writers)_




*GARIN DAƊI.....!*💍💍



_*NA*_

*_UMMI A'ISHA_*



10


~~~Na jima goshina a ƙasa ina tasbihi ga ubangiji na, ina ji Hashim na faman yi min karin bayani kan yadda al'amarin ya kasance amma ban iya amsa masa ba har sai da na ɗago daga doguwar sujjadar da nayi,

"Ya naji kin yi shiru ne Abar sona?"

Wasu hawayen farin ciki ne suka sake zubo min fuska ta kuma ɗauke da murmushi,

"Farin cikin halin da na tsinci kaina shi ne ya hana ni furta koda kalma ɗaya...."

"haƙiƙa ke wani sashe ne mai mutuƙar muhimmanci a rayuwa ta, Sam bani da bakin gode miki....."

"Ka daina yi min wannan godiyar Hashim.... Allah shi ya ƙaddara hakan zata kasance ni kawai dai ɗan taimako nayi dan haka give thanks to Allah"

"Maimuna kenan..... Ba zaki gane ƙarfin sonki acikin zuciya ta ba har sai ranar da na aure ki da yardar Allah, zan kula dake kamar yadda uwa take kula da jaririnta, zan lallaɓaki tamkar yadda ake lallaɓa ƙwai akan tire....."

Dariya nayi na koma na jingina da jikin gado na cikin farin ciki,

" Allah ya baka ikon kula dani fiye da hakan, ka san me yasa nake farin ciki da buɗewar idonka? "

" a'a sai kin faɗa "

" Ranar da muka fara haɗuwa ka sanar dani koda kana cikin damuwa mutane basa ganewa saboda ba idanuwanka suke gani ba, yanzu kuwa Kaga zaka ga idon kowa sannan kowa zai ga idonka.... "

" hakane amma ni dalilina ya sha baban da naki...."

" kai menene naka dalilin? "

" ni saboda zan rinƙa kallon kyakkyawar fuskarki.... Sannan a duk lokacin da kika yi min kwalliya zan gani kuma zan bada tukwici"

Wani ƙarin farin cikinne naji yana sake lulluɓeni. Mun jima muna hira dashi kafin daga bisani muka yi sallama domin lokacin sallar ishah yayi tuni aka jima da kira, sai da na jima ina addu'a tare da yi wa Allah godiya sannan na tashi daga kan abin salla ta, tsabar farin ciki yau kasa bacci nayi sai juye juye har garin Allah ya waye, duk wanda ya ganni ya san ina cikin farin ciki saboda annurin dake kwance kan fuska ta,

Lokacin da na fita domin zuwa aiki kuwa saida na tsaya nayi sadaka sannan na wuce office, wuni muka yi muna waya da Hashim wanda ke sanar dani wai zuwa gobe insha Allah zasu kamo hanyar gida, nidai kam bakina gaba ɗaya ya kasa rufuwa kawai jiran dawowarsu nake yi inyi ido huɗu da abin sona.
***

Kamar yadda masu iya magana ke faɗi wai rana bata ƙarya sai dai uwar ɗiya taji kunya tabbas kuwa hakanne domin tun daren jiya su Hashim suka sauka amma ban samu zuwa ba kasancewar basu dawo da wuri ba, yau dai insha Allah nake son zuwa,

Ƙawalli na kira domin ta taya ni yi masa abubuwan da zan tarɓeshi dasu, ada dai inata nuƙu nuƙu da ɓoye ɓoye kamar ban son kowa yasan tarayya ta dashi but now nafi to fili dan bana shayin nuna shi gaban kowa a Matsayin wanda nake so kuma nake da burin aure,

Farfesun kaji muka yi masa wanda ya sha kayan ƙamshi sai ƙamshin daddawa yake, sai jallop ɗin macaroni, bayan mun kammala na shiga wanka na fito, caɓa ado nayi cikin wata doguwar riga pink mai adon stones nasa milk colour ɗin takalmi da jaka na ɗebi kayan na tafi domin itama Ƙawalli tuni ta jima da tafiya dan tun bayan da muka gama,

Napep na shiga muka nufi unguwarsu Hashim sai ƙamshin black oud nake zubawa sam dama ban sanar dashi cewa na taho ba, misalin ƙarfe 11 harda wasu ƴan mintuna na isa gidan ina riƙe da babban basket ɗin da na zuba masa abubuwan da na girka masa na shiga bakina ɗauke da sallama, da gudun tsiya Amira ta zo ta rungume ni wanda na san ba komai ke ɗawainiya da ita ba face tsantsar farin ciki wanda nima acikinsa nake. Kayan hannuna ta karɓa muka ƙarasa ciki inda Iya keta faman lale marhabun dani, gabana ne naji ya yanke ya faɗi lokacin da muka yi ido huɗu da Hashim daidai lokacin da yake ƙokarin fitowa daga cikin ɗaki nikuma zan zauna kan tabarma,

"Tabarakallah, masha Allah" na faɗa a hankali sakamakon wani irin mashahurin kyau da naga ya bayyana a gareshi, duk da dama nasan kyakkyawa ne amma wannan kyawun na yau ya zarce na kullum lallai idanu ba ƙaramin kyau da kwarjini suke sake ƙarawa mutum ba, sunkuyar da kaina ƙasa nayi ina gaida Iya yayin da shi kuma yazo kusa dani ya zauna wanda hakan ya sani jin kunya mutuƙa,

"Sarauniya...... Me yasa zaki wahalar min da kanki ki fito, ai ni ya dace in zo har gida in gaida ki sannan in yi godiya, Maimunatu nagode, nagode da alkhairin da kika yi min, haƙiƙa bani da kalmomin da zan gode miki"

Ɗan ɓata face nayi ina gyara veil ɗin dake kaina, "Zaka fara maganar godiyar ko? Wai kai godiyar nan bata ƙarewa ne? Kullum sai kayi min godiya hakan bai isa ba? Bari na tashi na tafi...."

Cikin sauri yace "A'a dan Allah karki tafi, kiyi haƙuri bazan sake ba" ya faɗa yana riƙe gefen rigata, su Iya nayi saurin kalla amma sai naga babu kowa a wurin da alama sun tashi sun bar mana wurin tun lokacin da ban san ko yaushe bane,

"To gaskiya idan baka so raina ya ɓaci ka daina yi min godiyar nan haka..... Da wannan godiyar gara kayi min addu'a zai fi faranta min rai"


"Ina yi miki a koda yaushe, amma wacce iri kike so in yi miki nikuma nayi miki alƙwari kullum bazan manta ba zanyi miki"

"Kawai kace Allah ya cikawa Maimunatu burinta...."

Tun kafin in ƙarasa ya katse ni, "Menene burin nata?"

Ɗan kallon sa nayi amma ban iya tsayawa na kalleshin ba nayi gaggawar kawar da kaina gefe,

"Kasancewa da farin cikin ta har ƙarshen rayuwarta"

Murmushi yayi ya kalleni,

"Nikuma kin san addu'ar da nake buƙata a gare ki?"

"A'a" na faɗa ina maida hankali na gaba ɗaya kansa,

"Allah ya makantar da idanuwa na kar inga kowacce mace sai Maimunatu ita kaɗai har tsawon rayuwa ta...."

"Hmmm bana fatan haka, a har kullum abin da bana ku ƙauna shine inga idanuwanka basa gani.... Wannan shine babban tashin hankali agareni"

"Nagode Widat.... Haƙiƙa...."

Kallon sa da nayi shine sanadiyyar da yasa shi yin shiru yana murmushi, bakinsa ya kama da hannunsa alamar ba zai ƙara ba, abincin da na kawo masa na tura masa gabansa nan ya langaɓar da kai yana kallona,

"Inyi magana kuma ace za ayi fushi dani...." ya faɗa cikin muryar tsokana,

"Hmm baka taɓa ganin fuskata ba sai yau, ada murya ta kake ji yau kuma gashi ka ganni, Jina yafi ganina ko?" na faɗa nima cikin tsokana,kafe ni yayi da ido nikuma nayi saurin saukar da idanuwa ƙasa,

"Ai ko hasidin iza hasada ya ganki ya san jinki bai fi ganin ki ba... Tsarin halittar da ubangiji Allah yayi miki ya kyautata ta, madalla da ubangijin tsara halitta..."

Wani sanyi naji yana shigata ta ko ina saboda daɗaɗan kalaman da Hashim ke faɗa min, farin ciki biyu ne ya taru ya haɗar min ayau, farin cikin kalaman dake fitowa daga gareshi da kuma farin cikin yau gashi zaune gabana yana kallon kowanne irin motsi nawa................ ✍🏻


*Garin dadi littafin kudi ne ga mai bukatar cigaban labarin sai ya tura 500 ta 0774712835 Aisha Ibrahim Access Bank sai a tura evidence of payment ta wannan no 07044644433 ko a tura katin waya da shaidar biya wannan no 07044644433*



_*Ummi Shatu*_👌🏻
[1/5, 12:43] Maman K: ©️ *HASKE WRITERS ASSOCIATION.*
_(Home of experts & perfect Writers)_




*GARIN DAƊI.....!*💍💍

Free Book


*_NA_*

_*UMMI A'ISHA*_



*Wattpad:ummishatu*




*9*



~~~Yau da wuri na tashi daga office ban zame ko ina ba sai makarantar makafi, can na iskesu suna yin wasanni abun gwanin burgewa, an ɗaure zakara ansakeshi a tsakiyar fili sun bazu kowa yana yunƙurin kamawa, wuri na samu na zauna ina murmushi ni ɗaya duk da babu hashim

Please Login or Register in order to submit comment