Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

saboda Bishra ta haihu baby girl nan muka sha suna kuma duk kayan da na rinka siya ina ajiyewa wanda dama na rabar da fin rabi sauran duka na kwashe na kai mata dan yarinyar sunana aka saka mata amma za a kirata da Iman, saboda tsabar gajiyar da nayi kwana biyu na diba ina bacci har sai da na wartsake sannan muka dawo amma tare muka taho da cousins dinsa yaran uncle dinsa su biyu Ummussalma da Ummulkhair wanda zasu yi mana hutun 2 weeks kuma sosai naji dadin zama da yaran dan tunda suka zo sune suke yimin komai girki ne kadai nake yi da kaina shiyasa lokacin da zasu tafi na hada musu sha tara ta arziki dan kayan kwalliya da turaruka da atamfofi na siyo musu sannan na dora musu da kudi, shima kudin ya basu ya hadasu da Ahmad suka tafi tare saboda zai kai matarsa Kano suna da biki. Haka rayuwa taci gaba da tafiyar mana cikin farin ciki da kwanciyar hankali duk da wani lokacin ina shiga tashin hankali da damuwa saboda rashin samun cikin da banyi ba amma yanzu na kwantar da hankalina kuma na fawwalawa Allah komai tun bayan da a kwanakin baya na shiga kunci na daina walwala kullum sai tunani hakan ya tashi hankalinsa sosai shine yaje ya fadawa anty ta zo ta yimin fada sosai tace inbarwa Allah ikon sa sannan in kyautata masa zato to da dadi da babu dadi dai a haka nake daurewa kuma cikin Ikon Allah yanzu na bar damuwa,

A bangaren samz kuwa a yanzu abubuwa sun bude masa fiye da baya yasamu cigaban da karramawa fiyeda yadda yake ada dan ahalin yanzu shine na biyu awurin aikinsu, wannan damar da ya samu ni kaina na canja bama shi ba saboda wani katafaren makeken gida ya siya mana anan mai tama gidan upstairs ne kamar ba a Nigeria ba gashi an zuba furnitures masu tsada, duk wanda yaga gidan sai ya yaba, walima muka yi kafin muka koma, bedrooms a gidan ba a cewa komai ni kaina nawa guda biyu ne shima haka dan ina dashi a sama ina dashi a kasa haka shima baya ga dakunan yara da na baki amma duk da yawan bedrooms ɗin daki daya muke shearing, ga babban kitchen sama da kasa abin dai sai wanda ya gani, kowa sai fatan alkhairi yake yi mana ana sanya mana albarka, ban gama dokin wannan gidan ba ya bude min babban restaurant wanda shima ya kashe kudi sosai, gayya muka yi sosai wannan karon dan bude restaurant din wanda ya tsaru sosai, yan uwa duk an zo ana igobe za ayi bikin budewar har mama da Annie wannan karon duk sun zo gida na, wani irin dadi na rinka ji da naga taron yan uwa agidana wanda hakan bai taba faruwa ba shekara biyar kenan da aurena,

A cikin bedroom dina na sama ƙawalli ta sauka ita da yaranta nan ta kalleni ta kara tace,

"ƙawalli ke kam kin samu duniya sai ki dukufa kuma ki nemi lahira amma duniya kin gama samu"

Dariya nayi nace mata "Allah ya bamu gaba daya ƙawalli"

Washe gari aka bude kuma duk abinda aka dafa ranar kyauta ne dan yan uwa da abokan arziki, nan aka yiyyi addu'o'i aka sanya albarka aka watse, kowa a ranar ya tafi iya ƙawalli ce kadai bata tafi ba saboda yaya Abdul hakim zai zo to idan yazo sai su tafi tare,

"ƙawalli baki gani ba harda yaya Faisal na gani kamar ko? Ko ya aka yi yasan da wannan bikin bude restaurant din saboda nidai rabona dashi kamar fa tun ina amarya"

Kallona ƙawalli tayi kafin naji tace "ai ba kama bace shi dinne kika gani, shi ai dan gidane masu sanar dashi suna da yawa"

"hakane, ko ina wannan matar tashi mai bakin kishin tsiya..."

"au wai baki da labari?"

"me ya faru?"

"tun yaushe suka rabu da ita, Abbansu Irfan ne ma ya shiga case din, ai in fada miki yarinyar nan bin maza ta fara bai sani ba, shi baya bata kudi amma irin yanda take kashe kashen kudi sai abin ya fara damunsa nan fa ya fara bibiyarta daga karshe ya gane mu'amala take da wasu mazan da aurenta gashi ta zuzzubar masa da ciki duk bai sani ba kefa case iri iri tun daga wannan lokacin da suka rabu bai sake aure ba har yau, yace shi yanzu aure ya fice masa daga rai.... "

" innalillahi..... Kinji wata masifa kuma, Allah ya karemu ni wallahi ƙawalli ina ganin kokarin matan dake bin wasu mazan wannan ai jefa kai cikin masifa ne"

"kibari kawai ƙawalli, Allah ya karemu daga mummunar kaddara kedai amma abin dai ya ƙazanta"

Nidai na jima ina jajanta wannan maganar har samz ya dawo nan na tafi na bar ƙawalli bayan mun gama hawa sama da ita saboda nace mata yau jikin mijina zanje inyi bacci jiya shi kadai yayi bacci bawan Allah shine muka fara fada da ita wai idan naje gidanta ita ai bata barina ni daya har inje in dawo tare muke kwana,

Koda naje wurin samz sai da na bashi labarin matar yaya Faisal dinnan dan abin ya bani mamaki sosai, dorani yayi kan cinyarsa yace min,

"kin gaji ko?"

"sosai ma..."

"to me kika zo yi?"

"me mata take zuwa yi dakin mijinta?"

"samun lada...." ya fada yana wasa da hannuna idonsa kan fuskata,

"to ni bacci nazo yi"

"bakya son ladan?"

"Nidai bacci nake ji..."

"ok to am very sorry, zo kiyi bacci" yace dani yana kwantar dani gefensa, washe gari ban koma wurin ƙawalli da wuri ba shiyasa naje na sameta ta cika fam ina zuwa ta soma masifa harda cewa itama mijinta yana hanya zai zo su tafi inyaso mu cinye junanmu jarababbu, dariya ta bani ba kadanba haka dai na lallabata har muka shirya muka sha hira kafin yaya ya karaso, tare da shi muka je restaurant din ya gani sannan suka tafi,

Sosai yanzu na zama busy saboda restaurant dinnan duk da bani kadai ke kula dashi ba, Abdullah kaninsa da yazo gidana yayi service na dora akai bayan ya gama service din, kai bama shi kadai ba na samarwa mutane sunfi 20 ta bangarensa aiki haka har gobe duk wanda yazo bana rasa aikin da zan bashi.

Yau ban dawo gida da wuri ba saboda akwai wata order da akayi ta bikin wani dan senator kuma mune zamu ciyar da bakin abinci wannan dalilinne yasa na tsaya aka yi komai akan idona na tabbatar da komai yayi yanda za a fita kunya kafin na koma gida, zaune na iskeshi a falon kasa yana shan cornflakes,

"ayya my love na barka kai daya, ga abinci na taho maka dashi"

Hannu ya mika min na kama yajani zuwa jikinsa yafara bani cornflakes din,

"karki damu baby, ai kina kula dani yadda ya kamata"

"nagode da fahimta sweet"

"you are welcome my dear"

Sai da ya barni na gama komai nayi wanka sannan ya ja hannuna muka fita harabar gidan inda naga wasu galla gallan motoci sabbi guda biyu iri daya blue black da black color,

"baby ki zabi daya acikin wadannan..."

"innalillahi... Sweet.... Wata motar ka siya min? Wayyo Allah dadi.... Thank you darling.....Allah yakara buda maka" na fada ina tsalle tare da rungumeshi"

"anything for you my love" yace dani cikin kulawa, blue black din na zaba shikuma ya dauki black one din, ranar nidai ji nayi kamar mafarki nake dan gani nake kowanne lokaci zan iya farkawa daga wannan daddadan mafarkin kamar lokacin da muka tare a wannan gidan shima haka na rinka jin kamar mafarki saboda gidane da ada sai a tv nake gani ban taba tunanin zan zauna a irinsa ba, ban sake tsinkewa ba sai da yace min zamu tafi umarah nan da 2 weeks saboda an gama yi mana komai kai jama'a nifa ta fashe min bana kamar yadda naji yan gidanmu na fada a group wai bana ni ta fashewa alkhairai tako ina,

Ni dai lokacin da muka je kasa mai tsarki dukufa nayi naita addu'a ina fadawa Allah dukkan bukatuna da burikana, satinmu uku muka dawo inda na kwasowa mijina kaya kamar me musamman ma kayan bacci da jallabiya sai turaruka da agogo, yan sannu da zuwa kam kowa yazo da abinda zan bashi har aka gama zuwa. Bayan dawowarmu da sati biyu ina gida ban fita ba sai ga anty, nayi mamakin ganinta dan bata ce min zata zo ba bayan kuma kullum sai munyi waya, falon sama muka haura dan dama shiryawa nake zan fita kuma da niyyata ma zan biya ta gidan nata sai kuma gata,

"Anty sannu da zuwa, ina kwana yasu Aslam"

"lafiya lau widat, duk suna nan lafiya"

"anty me zan kawo miki"

"babu komai widat, zauna magana na zo muyi, widat rayuwa gaba ɗayanta tsari ce daga ubangiji kuma duk abinda kaga ya faru to haka Allah ya so kuma ya kaddara, bawa bai isa ya canja kaddarar sa ba, mijin ki yaje ya sameni har gida jiya yace in zo in baki hakuri sannan in sanar dake abinda yake faruwa wanda ke baki saniba.... "

" anty me zaki sanar dani? Me yake faruwa? " na fada cikin tashin hankali dan a iya sanina nida shi lafiya lau muke zaune ba wata matsala,

" ki kwantar da hankalinki..... Shi ya rasa ta yanda zai yi confronting dinki ya sanar da ke zai kara aure nan da 3 months..... Amma yace ba wai dan kin gaza ko ya daina sonki bane, haka kuma ba wai dan baku samu haihuwa bane......"

Nidai iya abinda na iya fahimta kenan amma duk sauran maganganun na anty bana iya jinsu bare har na gane me take son cewa dan tunda ta ambaci kamar zai kara aure shikenan komai nawa ya tsaya cak.........


_*Ummi Shatu*_👌🏻
[1/24, 16:58] Maman K: 70

*Ina kuke manyan mata ƴan ƙwalisa ma'abota son gyara da kece raini, maza ku garzayo ku nemi maman Maryam domin samun lafiyayyu kuma haɗaɗɗun Lagos lace wanda zaku iya samun ɗinkakku da kuma sabbi a ledarsu, kaya iya zaɓinki, gefe ɗaya muna da GHT product, zaku samu*,

~MAI DA TSOHUWA YARINYA

~FEMALE CARE

~REODEO

~VIGOR MAX

~ LONGZIT

~B CLEAR

*DUK ZAKU SAMU WADANNAN KAYA CIKIN SAUKI DA RAHUSA MAZA KU NEMI MAMAN MARYAM AKAN WANNAN NO 07080222187, SIYAN NA GARI MAIDA KUƊI GIDA....*


~~~Gaba ɗaya ba zan iya kwatanta halin da nake ciki ba musamman ma zuciyata wadda take wani irin bugawa kamar zata fashe ko kuma zata faso kirjina ta iyo tsalle ta fito waje,

"Anty..... Kika ce zai kara aure nan da 3 months?"

"Ehh haka na fada miki widat kuma hakanne amma ina so ki kwantar da hankalinki sannan ki kori duk wani shaidan daga cikin zuciyarki wanda zai zuga ki ko kuma yayi miki mummunar huduba har ya hanaki zaman lafiya da mijinki ko kuma yasa ki fara adawa ko yaki da wannan kudurin na mijinki..... Ki sani shi aure ko ince karin aure awurin na miji lokaci ne kuma samun dama ne da sukuni..... Sannan ki tsarkake zuciyarki ki kuma kyautata zato sai kiga kishiyar ta zamar miki alkhairi, ita kishiya zuwanta ba wai sharrine ko shi yake nuna miji baya yin ka ba, kiyi hakuri ki bawa zuciyarki hakuri ki karɓi wannan lamarin da zuciya ɗaya..... Kuma ke sai ki godewa Allah ma saboda mijinki yana sonki kuma yana ji dake ki duba kiga irin kyautatawar da yake miki yanda ya mayar dake tamkar wata tauraruwa, ki duba kiga irin daular da ya zuba miki a gidan nan, kiga yadda yake riritaki kamar wata sarauniya "

Shiru nayi ina faman kukan zuci dan ni banga wannan gatan da anty ke ikirarin yayi min ba idan dai har dan gidan da ya sake mana ne da motar da ya siya min da umarar da ya kai ni to gara ace babu ko ɗaya aciki akan ya kara min kishiya,

" Na san da ciwo widat amma kiyi hakuri ki daure karki daga hankalinki, Allah yana sane dake kuma yana tare dake..... Insha Allah mijinki bazai taɓa juya miki baya ko ya sauya miki ba saboda soyayyar da yake yi miki daga Allah ce, kedai kawai abinda zan fada miki shine kiyi hakuri kar ki fasa daga kyautatawar da kike yi masa sannan kar ki daina duk wani abu da kika san ada kina yi dan faranta masa, ki sake zage dantse fiye da yanda kike yi ada, kar dan zai kara aure ki tada bore da fushi ki daina kulawa dashi irin wannan kuskuren shine kuskure mafi girma da mata keyi a lokacin da miji zai kara aure wanda sai daga baya kuma kiga an zo ana cizon yatsa...... "

Duk yadda naso in zubar da hawaye ko dan in samu saukin tafarfasar da zuciyata keyi kasawa nayi haka nayita kallon anty tana sake bani shawarwari na yadda zan cigaba da kulawa dashi daga karshe tace komai zai zo da sauki insha Allah dan yace ba tare zamu zauna ba da amaryar wai ita a Kano zai ajiyeta nikuma ina nan tare dashi, har tayi ta gama ta tafi bani da nutsuwa sai bayan tafiyar ta da na shiga bedroom dina na ƙasa ina zama naji wasu hawaye masu dumi sun fara zuba daga idanuwana, kasa aikata komai nayi hatta wayata ina kallonta anata kirana amma na gagara dauka kai duk cikin kiranma babu wanda na kula sai kiran Abdallah kadai shima text message na tura masa cewa bazan samu fitowa ba yau bana jin dadi daga haka na rufe wayar gaba daya na cigaba da kukana, wani irin daci nake ji yana mamaye harshena kuma tsabar hankalina ba a kwance yake ba ko yunwa bana ji haka na zauna wuni guda ina daki na gagara ko fitowa,

Cikin wannan hali ya dawo ya sameni lokacin ƙarfe 9 na dare saura, dama tunda ya san anty tazo to dole ya san akwai damuwa, ni gaba ɗaya abin mamaki yake bani wai shine zai kara aure sam babu wannan alamar dan babu abinda ya canja na daga kulawar da nake samu daga gareshi haka baya fita waje bayan ya dawo to duk yaushe aka kitsa maganar aure ban gane ko naga alama ba? Lallai bayan Allah to wanda ya dace kaji tsoro shine namiji dan munafuki ne lamba 1, wato duk abubuwan da yayi min na farin ciki ashe ba dan Allah yayi su ba dan zai kara aure ne,

"Babe......" naji yace dani bayan ya zauna dab dani,juyawa nayi na kalleshi daga nan ban sake ba har naji ya riko hannuna,

"Babe dan Allah kar ki sakama ranki damuwa, kiyi hakuri, wallahi ba dan na daina sonki ne zanyi wannan auren ba...."

"dagaske auren zaka yi?" na katse shi da wannan tambayar bayan na kalleshi da jajayen idanuwana wadanda suka fada tamkar wacce tayi kashin haƙori,

"baby kiyi hakuri kuma ki fahimceni, dan na kara aure ba wai yana nufin kin gaza bane..."

Fincike hannuna nayi na juya ina fuskantarshi cikin masifa da tsananin bacin,

"Dama mana.... Dama haka zaka fada, ina duk alkawarirrikan da kayi min abaya? Ina duk dadin bakin da kayi abaya kake cewa ba zaka taba yimin kishiya ba saboda ka san bazaka yin adalci ba..... Oh yanzu duk ka manta ko kuwa adalcin zaka yi? Saboda ban haihu ba shiyasa zaka auro wata ta haifa maka ƴaya? Ashe duk waɗannan kudaden da kake ta faman yimin barin su kana kashe min toshiyar baki ne saboda zaka kara aure? To wallahi da ace na san kudurinka kenan da babu abinda zan karɓa daga ciki.... Kafi kowa sanin irin yarda da amincin da zuciyata ta baka amma da yake namiji ba dan goyo bane shine yanzu zaka yimin wannan sakayyar...... " shiru yayi yana saurarata har sai da na dasa aya ina numfarfashi cikin masifa sannan ya sake kama hannaye na ya tausasa murya yace,

" baby kiyi hakuri na san ban kyauta miki ba amma nima babu yadda zanyi ne...... Uncle Ahmad ne ya bani ƴarsa kuma bada ni yayi magana ba da daddy suka yi, ban san yadda zan tunkareshi ince bazan auri ƴarsa ba bayan ya taka rawar gani acikin rayuwata, da taimakonsa na zama abinda na zama yanzu.... "

" wato babu yadda za kayi, lallai kam babu yadda zaka yi tunda kai mace ne dole ayi maka auren dole,dama ai haka kuke yi idan kuka so cin amana da yaudara sai ku ce baku yarinya akayi aka ce ku aura, duk duniya ko kuma duk cikin dangi arasa wanda za abawa sadakar auren sai kai saboda kai kadai ne mutum?.... "

" bani kadai bane amma ni yaga zai bawa kuma kinga da kunya ince A'a musamman ma da ya sanar dani cewa tunda munirat ta kammala karatu ta kammala service bata samu mijin aure ba shi kuma baya son yaci gaba da ganinta a haka shiyasa ya yanke wannan shawarar..... "

" yanzu ai gashi ta samu mijin ko? To na rantse maka da girman Allah sai dai ka zabi ɗaya ko ni ko ita.... " daga haka na tashi na fita ina kuka batare da na saurari kiran da yake yimin ba, da gudu na haura sama na shige dakina na mayar da kofa na datse, duk da cewa kowa da dakunanshi amma a guda daya muke cakuda mu zauna bama wani raba daki sai dai a baki, a bakine kawai, kuka na sake zama nayi iya yina ina jinsa yana ta buga kofar akan in bude amma naki budewa, kyale ni yayi ya wuce bedroom dinshi yayi wanka ya sake dawowa wurina shima gaba daya baida nutsuwa kamar yadda bani da ita,

"baby bude muyi magana please and please...."

Gajiya nayi da magiyar da yake yimin na taso nazo bakin kofar nace,

"ka san me? Wallahi bazan iya cigaba da zama da kai ba, ka sallame ni kawai a yau din nan in tafi gidanmu....... Maci amana kawai..."

"am very sorry babe...."

"wallahi ba zan zauna ba kaji dai na rantse, ni ban hanaka aure ba na barka kayi aurenka amma ni ka sawwake min tunda dama ba haihuwa nayi ba bare kace inyi zaman ƴaya ni ban haihu ba shiyasa zaka auro wacce zata haifa maka taron arfa"

Shi kansa ya san zuciyata acikin zafi take duba da irin kalaman dake fitowa daga bakina, kirjina in banda suya babu abinda yake yi ji nake na tsani komai a duniya lallai duk matar da ba ayiwa kishiya ba to bata san yanda zafin kishi yake ba,

"kiyi hakuri....."

Ina jinsa na rabu dashi na wuce kan makeken gadona na kwanta naci gaba da kuka a haka na kwana banyi wani baccin kirki ba shima haka dan haka ya rinka zarya daga dakin da yake zuwa wanda nake ciki ina shasshekar kuka na wanda yana iya juyowa daga bakin kofa inda yake tsaye, sai zuwa asubah sannan zazzabi ya rufe ni dama kaina tun bayan da anty ta fada min dalilin zuwanta ya sara ya fara ciwo har yanzu bai daina ba a haka na kwana cikin matsanancin ciwo duk da ina kwance jiri nake ji yana daukana,

Gari yana wayewa ya kira anty a waya ya sanar da ita wai tun daren jiya na shiga daki na rufe kaina inata kuka naki kula shi, bayan ta kai yara school sai gata ta zo ina kwance jikina yagama yin laushi na jiyo muryarta,

"widat.... Bude min kofar nan ko ranki ya baci..."

Kasa tafiya nayi sai da rarrafe naje na bude mata ina budewa na karasa zubewa awurin, sama sama naji ya dauke ni yayi kan gado dani anty tana faman salati daga karshe dai suka nufi asibiti dani wanda take aka daura min drip sai da na sha ruwa leda takwas kafin na farfado har nake iya bude ido in kalli kowa, tsakanina da kowa ido ne naki yiwa kowa magana ciki kuwa har da ita antyn bare shi uban gayyar da ko kallo baya samu daga gareni. Hatta abinci sai anty ta tisani a gaba tayi min wuka wuka tayi dagaske sannan nake yarda inci, kwanana biyu na dan fara dawowa hayyacina, zaunar dani anty tayi ta sake yimin fada tun tana yi da zafi har ta dawo yimin cikin ruwan sanyi da rarrashi,

"widat bafa kece mace ta farko da za a fara yiwa kishiya ba sannan ko gidanmu mata biyu kika taso kika gani haka kuma ke kanki shaida ce suna zaune lafiya suna burge kowa har gobe sittura iri daya suke dinkawa babu bambanci, ke kanki har kika bar gidan kika yi aure baki taba sanin wacece take da girki ba saboda tsabar hadin kansu.... Kema ina so kiyi koyi da iyayenmu, ki nutsu ki kwantar da hankalinki Insha Allah komai zai zo miki da sauki kuma Insha Allah bazaki kunyata ba.... "

Duk bayanin nan da anty take yi baya shiga kaina saboda zuciyata ta riga da ta gama karyewa ni kawai gani nake samz baiyi min adalci ba kuma yaci amanata tunda har zai iya auren wata ya hadani da ita, duk da anty tayi min fada ban sauko ba bare har in kula shi, sai da nayi sati biyu a asibiti sannan aka sallameni a ranar da muka koma gida aka sake komawa gidan jiya washe gari ya sake mayar dani asibiti ya kira anty, wannan karon kam kwana biyu kadai nayi muka wuce gidan anty bayan an sallameni, sai da nayi kwana biyar a gidanta kafin ta mayar dani gidana, tunda na koma kuma naki hakuri duk nabi na saka damuwa araina dan ni kawai so nake ya sawwake min in bar masa gidansa amma yaki, kowa hakuri yake bani babu wanda ke goyon bayana dama irin wannan lokacin gani kake kamar kowa ya tsaneka gashi ko gidanmu sun ce in dai banyi hakuri na zauna ba kar na dawo musu gida, shi kuwa yaya Abdurahman zagina yayi son ranshi wai gidanmu ba mata biyu na gani ba to wallahi idan na kashe aurena in san inda zan je shima Abba haka ya fada, waya muka yi da kawalli ina kuka ina faɗa mata nan ta babbani hakuri muka yi sallama,

Yin duniya nayi akan ya sakeni amma yaki ni kuma ko ganinsa bana son yi gashi bikin kullum sake matsowa yake dan yau ya shigo min da akwatuna na irin wanda yayiwa amaryar set biyu babu abinda ya bambanta ai tun da naga haka na fara nemarwa kaina mafita ba tare da sanin kowa ba, ranar Litinin da safe yana fita aiki nima naja akwatina babba wanda na kwashi kayana wanda zan bukata sai Airport domin jirgin karfe 10 zan bi zuwa Paris.........



_*Ummi Shatu*_👌🏻

71


*Ina kuke manyan mata ƴan ƙwalisa ma'abota son gyara da kece raini, maza ku garzayo ku nemi maman Maryam domin samun lafiyayyu kuma haɗaɗɗun Lagos lace wanda zaku iya samun ɗinkakku da kuma sabbi a ledarsu, kaya iya zaɓinki, gefe ɗaya muna da GHT product, zaku samu*,

~MAI DA TSOHUWA YARINYA

~FEMALE CARE

~REODEO

~VIGOR MAX

~ LONGZIT

~B CLEAR

*DUK ZAKU SAMU WADANNAN KAYA CIKIN SAUKI DA RAHUSA MAZA KU NEMI MAMAN MARYAM AKAN WANNAN NO 07080222187, SIYAN NA GARI MAIDA KUƊI GIDA.....*


~~~A wani ƙayatacce kuma lafiyayyen hotel na sauka wanda ni kaina ban san adadin kwanakin da zan kwashe aciki ba domin ba yanzu zan koma gida ba har sai an yi bikinsa an gama kai sai ma naji araina zan iya cigaba da zama tare dashi, sabon sim card na siya na saka cikin wayata saboda wancan wanda nake amfani dasu na cire na zubar nan cikin bedroom dina lokacin da zan taho saboda bama na son ya samu damar bibiyata bare har ya samu nasarar gano inda nake, duk da barin gida babu dadi amma naji sauki a cikin zuciyata da na nesanta dashi kuma ina kokarin tirsasa zuciyata dan ta manta dashi duk da nasan hakan abune mai wuya.

Lokacin da samz ya dawo gida misalin karfe 9 ne saura na dare nan yaga bai ganni ba kuma ko ina a bude bare ko yayi tunanin na shiga na rufe kaina kamar yadda na saba nan hankalinsa ya tashi, anty ya fara tuntuba ko naje gidanta tace a'a sai dai ko idan Kano na tafi bari ta kira su Annie, nan fa hankula suka tashi jin duk inda aka kira sai ace ban je

Please Login or Register in order to submit comment