Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

na duba no ɗin nan naga muna the same group na wannan training ɗin da muke yi ina duba jikin sunan naga an rubuta ~Samz~ zumbur na miƙe daga kwancen da nake kamar wadda aka tsikara............. ✍🏻



*Garin dadi littafin kudi ne ga mai bukatar cigaban labarin sai ya tura 500 ta 0774712835 Aisha Ibrahim Access Bank sai a tura evidence of payment ta wannan no 07044644433 ko a tura katin waya da shaidar biya wannan no 07044644433*


*Ina mata ƴan ƙwalisa ƴan kwalliya masu son burge mazajensu da gyara kansu cikin sauƙi rahusa ga dama ta samu ku garzaya ko nemi maman Maryam domin huce takaici, zaku samu haɗaɗɗun ɗinkakkun Lagos lace cikin farashi mai sauƙi gefe guda kuma ga GHT product domin gyara ku, zaku iya tuntuɓarta ta wannan no 07047034063 kada ku manta nima Ummi Shatu da bazarta nake rawa dan siyan na gari maida kuɗi gida.*

_*Ummi Shatu*_👌🏻
[1/5, 12:43] Maman K: ©️ *HASKE WRITERS ASSOCIATION*




*GARIN DAƊI.....!*



*_NA_*


*_UMMI A'ISHA_*


PAID BOOK


17


*Ina kuke manyan mata ƴan ƙwalisa ma'abota son gyara da kece raini, maza ku garzayo ku nemi maman Maryam domin samun lafiyayyu kuma haɗaɗɗun Lagos lace wanda zaku iya samun ɗinkakku da kuma sabbi a ledarsu, kaya iya zaɓinki, gefe ɗaya muna da GHT product, zaku samu,*

*MAI DA TSOHUWA YARINYA

*FEMALE CARE

*REODEO

*VIGOR MAX

* LONGZIT

*B CLEAR

*DUK ZAKU SAMU WADANNAN KAYA CIKIN SAUKI DA RAHUSA MAZA KU NEMI MAMAN MARYAM AKAN WANNAN NO 07080222187, SIYAN NA GARI MAIDA KUƊI GIDA....*


~~~Hannu na sa ina murza idanuwa dan samun tabbacin shin dagaske ne ko kuma sune suke yimin gizo? Tabbas da gaske ne hakan ya sanya naji jikina ya fara rawa wadda ban san ko ta mecece ba,

"uhmm....... Kin yi shiru" ya sake turo min, cikin kasala na koma na kwanta sannan na bashi amsa da,

"Babu abin da ke damuna kawai dai na gaji ne...."

"Gajiya? Wacce irin gajiya?"

Murmushi nayi araina ina jinjina ƙwaƙwarsa da gani zai yi tambaya,

"Na gaji da zama ne wuri ɗaya kuma ina fama da ciwon kai" na bashi amsa ina murmushi ni kaɗai,

"ayya sorry....."

Murmushi kaɗai nayi kafin na buɗe saƙon da ya sake turo min,

"Zan iya zuwa in duba ki yanzu?" ɗan jimm nayi na kalli gefen da anty Salma ke zaune tana duba manual,

"Kar ka zo pls....."

"Why?" ya sake tambaya ta,

"Idan ka zo za ayi min faɗa"

"OK na gane, amma ina buƙatar wata alfarma daga gareki"

"Allah yasa zan iya"

"Ki turo min pics ɗin ki ina son ganin ki ban taɓa ganin fuskarki ba"

Ajiyar zuciya na sauke araina ina cewa idan wannan ne babu matsala abune mai sauƙi, pics ɗina na tura masa guda biyu nace shima ya turo min nashi, turo min yayi sama da guda biyar a ƙasan ya rubuta wai shi bai iya rowar pics ba, murmushi nayi na fara buɗesu ɗaya bayan ɗaya ina kalla, gaba ɗaya hotunan yayi bala'in kyau kamar ka sace shi ka gudu,

"Zan iya kiran ki yanzu?"

Shiru nayi kafin na bashi amsa da "ehh" yana buɗe saƙona sai ga kiran sa, nan naji gabana ya shiga faɗuwa, to ni yanzu me zan ce masa ni Maimunatu? Na shiga tambayar kaina ba tare da na ɗauki wayar ba har sai da na jiyo muryar anty Salma tana cewa ba kirana ake yiba? Cikin sanyin murya da tsoro wanda ban san ko na menene ba na ɗaga kiran,

"Hello...." na faɗa ina lumshe idanuwa na,

"Hello........ Ya jikin?" ya tambaya cikin harshen turanci,

"Da sauƙi....." na amsa ina sake gyara kwanciya ta,

"Kin sha magani?" kai na girgiza masa kamar yana kallo na,

"Meyasa baki sha magani ba?"

"Babu komai...."

"kin ci abinci?? “

" Ehh "

" Ban yarda ba..... Duk da baki son in zo dole zan zo zan kawo miki maganin headache ɗin"

"ka bar shi kawai.... Na gode" tun kafin in ƙarasa naji ya katseni da cewa,

"Zamu fara faɗa ba daga fara wayarmu yau, ki jirani nan da 5 minutes"

Katse wayar yayi nikuma na sake mirginawa ɗaya ɓangaren ina mamakin wannan al'amari, har 5 minutes ɗin tayi ta gota ban sani ba saboda ina can ina tunani, mamaki da al'ajabi sun taru sunyi min rubdugu har sai da naji ƙarar wayata alamar kira sannan na tuna,

"Zo ki karɓa....."

"kana ina?"

"Ina harabar hotel ɗin"

Tashi nayi zaune na kalli anty Salma nace mata ankawo min magani zan karɓo, ita duk tunanin ta Samir ne saboda taji muna hira da turanci nikuma bance mata ba shi bane na barta ahaka, a yadda nake haka na fita babu abin da na sauya ina sanye da dogon hijabi mai hannu har ƙasa. Irin faɗuwa da bugawar da gabana ke yi ba zata kwatantu ba, haka dai na daure na fita harabar hotel ɗin, caan na hango shi tsaye shi kaɗai dan haka cikin sassarfa na ƙarasa jikina yana ɗan rawa,ko da naje dab dashi sai na rasa me zanyi, shin zanyi masa sallama ne ko yaya?

"Princess......" naji ya faɗa cikin husky voice ɗinsa, ɗan murmushi nayi na sadda kaina ƙasa,

"ya jikin?"

"da sauƙi"

"ina yi miki fatan samun sauƙi cikin gaggawa"

"na gode"

Shiru ne ya ɗan biyo baya dan na lura shi ɗinma ba wai mutum ne mai surutu ba sau da yawa shi kaɗai zaka ganshi zaune shiru sai ko wayar shi da zaita latsawa ko laptop ɗin shi,

"Ga maganin kije ki kwanta ki huta...."

"nagode"

"nima haka"

Karɓar ledar nayi duk da na ganta ƙatuwa haka kuma naji ta da ɗan nauyi wannan ke tabbatar da ba wai iya maganin ne kaɗai aciki ba, sallama yayi min ya tafi nabi bayan sa da kallo yanzu ma ƙananan kaya ne a jikinsa jeans da t shirt, ciki na koma ina jin wani al'amari yana ratsa birnin zuciya ta,

Fruits ne cikin leda sai ko maganin ciwon kai, apple kaɗai naci nasha magani na kwanta bayan nayi sallar isha, bargo na shige na cigaba da chaten ɗina dan itama anty Salma na jiyo ta tana waya da mai gidanta da yaranta, samz ne ke tambaya ta wai waye saurayi na, murmushi nayi nace masa babu, cewa yayi wai bai yarda ba ya za ayi ince ba ni da saurayi, wani murmushin na sake yi nace masa ban samu type ɗina bane, tambaya ta ya sake yi wai shi type ɗina ne? Shiru nayi na rasa amsar da zan bashi dan a zahirin gaskiya shine type ɗin nawa, duk yanda nake son mijina ya kasance haka samz yake sai dai akwai ƙatuwar matsala dan ko mun fara soyayya tofa babu inda zata je tunda shi ba musulmi bane, sake tambaya ta yayi, bani da zaɓi wanda ya wuce in faɗa masa gaskiyar lamari nan nace masa ehh dariya naga ya yi sannan yace wai in kara tura masa pics ɗina guda biyun da na tura sunyi kaɗan, tsokanarshi nayi nace to dai idan matarshi ta gani kar ya kira sunana dariya yayi kafin yace min ai bai da aure, zaro ido nayi nace dagaske?

"Dagaske mana, ko dan kin ganni na fara tsufa?"

"a'a ni bance ba...... Kawai na tambaya ne"

Hira muka cigaba da yi har ƙarfe 9, shi da kansa yace wai in ajiye wayata haka in kwanta in yi bacci amma kafin in yi baccin bari ya kirani yaji jikina, sallama muka yi na kashe wayata gaba ɗaya na yi addu'ar bacci, da tunaninsa nayi bacci da asuba kuwa ina buɗe wayata da message ɗinsa na fara yin tozali kuma hakan ba ƙaramin daɗi yayi min ba, sake komawa bacci nayi wanda bani na tashi ba sai wurin 9, wanka nayi naci abinci na sake komawa na kwanta na faɗa yanar gizo,ina shiga WhatsApp da massage ɗinshi nayi arba, murmushi nayi na fara karanta saƙon kamar haka, _As you rest and heal, know that you are thought of warmly and wished a quick recovery._, reply nayi masa ina tura masa sai gashi online, hira muka fara yi wadda tayi mutuƙar ɗebe min kewa ta sani na manta komai da duk wata damuwa wacce nake tare da ita sai dariya kawai nake yi wanda hakan yasa Anty Salma tsokana ta, har azahar tayi muna hira da shi sai lokacin nace masa zan yi salla sannan muka yi sallama. A cikin weekend ɗin mun ɗan saba da juna saboda kullum sai ya kirani da safe da rana da yamma da kuma dare ga chaten da muke yi wuni za muyi muna abu ɗaya shiyasa har na matsu Monday tayi in ganshi dan tun lokacin da yazo ya kawo min magani bai sake zuwa ba sai dai waya, shima a nasa ɓangaren kamar ya fini matsuwa da Monday tayi ya ganni duba da irin yadda yake ta maganar yana cewa weekend ɗin wai baya sauri yaƙi ya ƙare kuma shi babu inda yake zuwa kullum yana gida sai ko wani lokacin ya kan je filin ƙwallo, murmushi nayi araina nace "ai saida exercise ɗin kai kam ko ka ɗan rage nauyi.......".

Asubar farko ta ranar Litinin na tashi na shirya cikin ɗoki da farin ciki, babu komai araina face murna da tarin farin ciki haka fuskata ƙunshe take da annurin zallar farin ciki, nasha kyau har na gaji cikin simple makeup ɗin da nayi dan dama daga powder sai kwalli da lip glow shikenan kwalliya ta amma duk da haka na haɗu iya haɗuwa cikin doguwar rigar atamfar da na saka ash colour mai ratsin green coour, mayafi nasa green nasa baƙin takalmi, ni kaina na san weather ɗin garin Lagos ta karɓi fatar jikina duba da irin yadda nayi wani fresh dani kamar me shafa mai, nayi kyau nayi haske fatata sai sheƙi da ƙyalli take, yau kama kaina nayi naja class ɗina sosai dan ko inda trainers suke ban kalla ba tun bayan da muka yi signing lokacin da muka shigo,

Kaina yana ƙasa ban ɗago ba naji wani shegen ƙamshi yana ratsa ƙofofin hancina duk da cewa akwai face mask a fuskata,

"Good morning....." naji daga bayana saitin kunne na, juyowar da zan yi na jini cikin jikinsa domin dab dani ya duƙo ya dafa kujerar da nake kai, kamar wani mayen ƙarfe wanda ya haɗu da ɗan uwansa mayen ƙarfen daƙyar na iya janyewa,

"Good morning...." na fada murya ta can ƙasa,

"Morning..... How was your night and how do you feel now?" ya faɗa saitin kunnena cikin raɗa,

"I feel much better....."

Bai ƙara cewa komai ba ya juya ya tafi, Nana dake kusa da ni ta juyo ta kalle ni dan yanzu ba sosai muke zama tare da Anty Salma ba cikin Aunties take shiga nikuma nake shiga cikin sa'annina, duk ƙwaƙwar Nana na son jin me ke tsakanina da Samir da kuma Samz ƙin faɗa mata nayi,

Lokacin breakfast da lunch duk sai da ya kirani awaya wai yana kallo na inci abinci da yawa, ga mamaki na muna hira awaya ina cin abinci sai gashi na cinye da inata mitar an zuba min da yawa dan shinkafa ce jalop da fried rice itama a gefe sai alala guda ɗaya da farfesun kayan ciki sannan ga pepper chicken akai, muna hira inata nishaɗi ban san lokacin da na cinye ba gaba ɗaya sai guntu na bari,

"Kaga yadda naci abinci yau? Rabon da na ci abinci irin haka har  na manta"

"Tunda hakane na gane logic ɗin yanzu duk lokacin da zaki ci abinci zan rinka kiranki har sai nasa kin ci da yawa" dariya nayi na tashi na mayar da flates ɗin sannan na wuce toilet ina jin cikina dam kamar zai fashe, bayan na fito kuma sai ban ganshi ba wurin zaman su, har kusan lokacin tashi baya nan text massage na tura masa _Where are you?_ babu reply har kamar 5 minutes zuwa can sai gashi ya shigo kai tsaye wurina yataho, ɗan ranƙwafowa yayi yace min,

"Gani na dawo.... Lafiya Lau nake"

Murmushi nayi na ɗaga masa kai, juyawa yayi ya wuce wurin zamansa, har aka tashi ba mu sake magana ba sai bayan da na koma masauki, lokacin da zan ci abinci kamar da rana cemin yayi wai in cika flate hakan kuma nayi ina ci muna hira na cinye, waje na fita dan nayi bala'in ƙoshi, wurin 9 muka yi sallama da shi na kwanta raina fari tas babu damuwar komai, tun daga lokacin kusan kullum muna waya dashi nake cin abinci yanzu abinci nake ci sosai dagaske bada wasa ba, yau dai tunda yashigo naga he looks somehow, after kamar 30 minutes ya ɗauki jakar shi ya fita, wayarshi nayi ta kira amma a kashe, abincin ma yau ban wani iya ci da yawa ba, bayan an dawo daga lunch trainers ɗin ke sanar damu wai muyi haƙuri  training da za ayi mana yanzu Samuel ne kuma bai da lafiya sai zuwa gobe idan yazo,

Bayan mun tashi na sake gwada kiran sa sai lokacin naji da ta shiga, muryarshi sanyi ƙalau muka gaisa sannan na tambayeshi address ɗin inda ya sauka zan je in duba shi, sallama muka yi bayan ya faɗa min, faɗa ma Aunty Salma nayi zan je cikin gari, bata hanani ba amma tace dai kar in jima in tabbatar na dawo before dare, side handbag ɗina na ɗauka na fita.............



*Garin dadi littafin kudi ne ga mai bukatar cigaban labarin sai ya tura 500 ta 0774712835 Aisha Ibrahim Access Bank sai a tura evidence of payment ta wannan no 07044644433 ko a tura katin waya da shaidar biya wannan no 07044644433*


*_Ummi Shatu_*👌🏻
[1/5, 12:43] Maman K: ©️ *HASKE WRITERS ASSOCIATION*




*GARIN DAƊI.....!*




*_NA_*

*_UMMI A'ISHA_*



PAID BOOK



18


*Ina kuke manyan mata ƴan ƙwalisa ma'abota son gyara da kece raini, maza ku garzayo ku nemi maman Maryam domin samun lafiyayyu kuma haɗaɗɗun Lagos lace wanda zaku iya samun ɗinkakku da kuma sabbi a ledarsu, kaya iya zaɓinki, gefe ɗaya muna da GHT product, zaku samu,*

~MAI DA TSOHUWA YARINYA

~FEMALE CARE

~REODEO

~VIGOR MAX

~ LONGZIT

~B CLEAR

*DUK ZAKU SAMU WADANNAN KAYA CIKIN SAUKI DA RAHUSA MAZA KU NEMI MAMAN MARYAM AKAN WANNAN NO 07080222187, SIYAN NA GARI MAIDA KUƊI GIDA.....*

~~Drop na ɗauka har masaukin da samz ya sauka kuma ban wani sha wahalar gane wurin ba saboda sanannen wuri ne, har ɗakin da yake na shiga bayan nayi knocking naji shiru, yana kwance cikin blanket, a hankali na ƙarasa shiga na zauna gefen gadon, zaune ya tashi fuskarsa ɗauke da murmushi duk da fuskar ta ɗan faɗa kaɗan haka bakinsa lips ɗinsa duk sun bushe sunyi fari alamun bai ci abinci ba,

"Sannu..... Ya jiki?" na tambayeshi ina kallon cikin ɗakin,

"Da sauƙi...... Me yasa kika wahalar da kanki kika zo?"

"Na zo inga yanda kake ne kuma in duba ka"

"Na gode, ya training?"

"Babu daɗi" na faɗa cikin shagwaɓa ina ɗan turo baki,

"Me yasa?" ya tambaye ni yana kallon cikin idanuwa na amma ban bari mun haɗa ido ba,

"Saboda baka nan...."

"Ayya sorry.... Gobe zan zo in dai naji sauƙi"

"Allah ya baka lafiya...... Amma me ke damunka?"

"Amin.... Nagode"

"Me ke damunka?" na sake tambayarshi ina kallon gefen da yake zaune sanye cikin fararen jersey,

"Karki damu naji sauƙi...." jin abin da ya faɗa ya sani ɗan ɓata fuska kaɗan ina gyara handbag ɗina,

"Shikenan tunda ba zaka faɗa min ba"

"Am sorry..... Kaina ne ke ciwo" ya faɗa yana murmushi, na san ba hakan bane kawai dai ya faɗa ne dan a wuce wurin,

"shikenan Allah ya baka lafiya..... Bari na wuce"

Langaɓar da kai naga yayi yana kallona,

"amma dai ba fushi kika yi ba ko?"

"uhmm ni ba fushi nayi ba" na faɗa ina miƙewa tsaye,

"OK bari na zo na rakaki masaukinku" cikin sauri na juya ina kallonsa yana ƙoƙarin saukowa daga kan gadon,

"a'a ni bana buƙata dan Allah ba sai ka fita ba kayi zaman ka"

"kina ganin babu matsala zaki iya zuwa ke daya?"

"insha Allah zan je lafiya kawai kayi zaman ka Allah ya kara sauƙi amma idan baka warke ba Allah nima zan kwanta" daga haka na fita daga cikin ɗakin ina murmushi ni kaɗai, murmushin shima yayi bayan fita ta yana mai shaƙar ƙamshin turare na da na bar masa shi kansa bai san wanne irin al'amari ne wannan ba amma yana jina acikin ransa fiye da komai da ya mallaka ahalin yanzu sannan bai taɓa ganin yarinyar da ta burgeshi yaji jininsa ya haɗu da nata tun akaron farko ba kamata, sai dai jikinsa da tunaninsa na bashi cewa akwai tarin ƙalubale a tarayyarmu wanda nima sau da dama ina tuna hakan.

Kamar ɗazu yanzu ma drop na ɗauka ina kallon yanda cikin garin yake wanda ya amsa sunansa birni, wayata na ciro cikin handbag dan ganin wanda ke kirana, Anty na gani nan na ɗaga bakina ɗauke da sallama,

"Salma tace min kin fita, ina kika je?"

"Anty bafa nisa nayi ba, kinma ganni a hanya na kusa komawa hotel ɗin da muka sauka"

"Har yanzu fa baki amsa min tambaya ta ba nace ina kika je?"

"Dubiya naje...."

"waye bashida lafiya?"

"Tare muke training"

"to daga yau karki sake fita dab da magriba, kin ji abin da nace?"

"To anty, agaida su Sultan"

"Zasu ji"

Kiranta na katsewa na Samz na shigowa, cikin sanyin muryarsa naji yace,

"Inata kira kina waya..."

"ehh, anty ce, elder sister ɗina"

"Ayya, ya hanya?"

"Mun kusa mu ƙarasa....."

"kuna ta ina yanzu?"

Ɗaga idona nayi na kalli waje nan naga wani symbol na wani restaurant,

"Perfect kitchen restaurant....."

"ok to Allah ya kai ku lafiya"

"amin, ya jiki?"

"ai na warke, tun da na ganki naji na samu lafiya"

Murmushi nayi nace, "da gaske?"

"Da gaske mana"

"Ba dai ka ƙi ka faɗa min abin da yake damunka ba?"

"No baby.... Ba ƙin faɗa miki nayi ba ai na samu sauƙi"

"to Allah ya baka lafiya"

Har na koma masauki muna waya dashi sai da nace masa na shiga ɗaki sannan muka yi sallama.

Washe gari  tun sassafe naga kiransa video call ta Imo, murmushi nayi na ɗauka ina kallonsa, yana kwance cikin bargo da rigar sanyi a jikinsa,nima ƙudundune nake cikin bargo da hijab a jikina saboda sanyin Lagos,

"Good morning baby....."

"morning..... Ya jikinka?"

"Naji sauƙi...... Just want to see your beautiful face"

"Na gode, zaka zo?"

"yeah, zan zo in ganki cutie"

"Ka daina faɗa min haka, kar kasa in fara ɗaukar kaina sahun masu kyau"

"Ni awurina kinfi kowacce mace kyau....."

Lumshe idanuwa na nayi ina murmushi kafin na buɗesu akan shi, "nima awurina kafi kowanne namiji kyau....."

"are you serious baby?"

"Am serious"

"Thank you queen"

"you are welcome king" na faɗa cikin tsokana,

"Kamar dai kinfi sakewa dani a waya ko?"

"uhmm kusan haka ne gaskiya" na bashi amsa ina rufe fuskata,

"shy girl"

Sallama muka yi na ɗan sake komawa bacci zuwa wani lokaci naji anty Salma na tashi na wai inyi sauri dan har mun so mu makara saboda itama baccin ta koma, cikin hanzari na shirya muka fita, koda muka je mune kusan na ƙarshen zuwa dan sai da aka tare mu ma, ina zama ya taso yazo kusa dani ya zauna juyawa nayi na kalle shi yana sanye da blue black ɗin wani yadi yasha hula itama kalar yadin nasa,

"you are late....." naji ya faɗa bayan ya zauna,

"Good morning....." na ce dashi ina ƙokarin saka wayata a silent,yana nan zaune kusa dani har aka tafi break, yinin ranar gaba ɗaya a kusa dani yayi shi idan nayi magana nace ya tashi sai yace wai gadina yake,haka lamarin ya cigaba da gudana tsakanina dashi sai dai har yau babu wanda na sanarwa cewa muna soyayya da samz dan ko ƙawalli ban faɗawa ba haka kuma har yau muma ajunanmu nida shi ba mu furtawa juna kalmar so ba amma dai duka alamomi sun gama bayyana, kulawa muke da juna yana riritani kamar wani ƙwai, duk abin da zai saka ni farin ciki ya sanshi kuma ya iya shi ina jin wannan shi ne dalilin da yasa bai wani sha wuya ba wurin samun zuciya ta. A kwana a tashi ba wuya a wurin Allah domin har mun fara lissafin tafiya gida nan da kwana shida, text massage samz ya turo min wai in shirya mu fita hang out wannan weekend ɗin, da yake da yamma zamu fita shiyasa banji wata fargaba ba na faɗawa anty Salma na shirya na fita inda yake jira na, sanye nake cikin gown maroon colour na yane kaina da farin gyalen rigar, shi kuma ƙananan kaya ne ajikinsa jeans da t shirt sai p cap, daga ni har shi munyi kyau ajin ƙarshe, wurin shaƙatawa ya kaimu can kusa da wani ruwa kai idan kaga wurin kamar ba a Nigeria ba dan haɗuwarsa da tsarinsa ga mutane nan tsilla tsilla masu yawon buɗe ido da shaƙatawa wasu har ɗan cikin ruwan suke shiga daga baki baki ana yi musu hoto yayin da wasu suke shiga jirgin ruwa wurin dai gwanin sha'awa, zama muka yi nida shi muna fuskantar juna,

"Maimunatu......." ya faɗa bayan ya riƙo hannu na guda ɗaya wanda har sai da naji wani yarrr saboda rashin sabo,

"Na'am..." na amsa ina kallon hannayenmu dake maƙale wuri ɗaya,

"ki faɗa min gaskiya karki yaudare ni..... Dagaske baki da saurayi?"

Kai na ɗaga masa alamar ehh, ajiyar zuciya naji ya sauke kafin ya sake ɗora ɗaya hannun nasa kan nawa ya haɗe,

"Ni inada budurwa...... Harma relationship ɗinmu yaje gida wurin iyayen mu...."

Wani ras ras naji gabana ya fara faɗuwa babu ƙaƙƙautawa,

"Amma yanzu lokacin da na haɗu dake sai na ji ra'ayina ya sauya, naji a yanzu babu wadda ta dace dani sai ke..... Maimunatu na faɗa kogin sonki....."

Shiru nayi na rasa amsar da zan bashi, abin ka da Lagos kowa harkar gabansa yake babu wanda ya ko kallemu,

" Nima ina son ka..... Amma ita budurwar taka ya zaka yi da ita? "

Murmushi yayi ya ɗan sunkuyar da kansa alamun tunani,

" amma bakya ganin akwai matsala tunda ni ba musulmi ba ne?"

"Banda matsala da addininka... A yanzu dai kayi naka in yi nawa" na faɗa ina yi masa murmushi saboda ba abu ne mai sauƙi karon farko ka faɗawa mutum ba akan daidai yake ba musamman irin su samz da sunfi shekara 30 cikin abun dole sai a hankali cikin hikima da dabara duk da nasan zai yi wahala muyi aure amma har ga Allah nidai zuciya ta a yanzu shi take so kuma take muradi.............


*Garin dadi littafin kudi ne ga mai bukatar cigaban labarin sai ya tura 500 ta 0774712835 Aisha Ibrahim Access Bank sai a tura evidence of payment ta wannan no 07044644433 ko a tura katin waya da shaidar biya wannan no 07044644433*


_*Ummi Shatu*_👌🏻
[1/5, 12:43] Maman K: ©️ *HASKE WRITERS ASSOCIATION*
_(Home of expert & perfect Writers)_



*GARIN DAƊI.......!*💍💍



*_NA_*

*_UMMI A'ISHA_*


*Wattpad:ummishatu*


_If an egg is broken by outside force, life ends, if broken by inside force, life begins. Great things always begin from inside_



20


*Ina kuke manyan mata ƴan ƙwalisa ma'abota son gyara da kece raini, maza ku garzayo ku nemi maman Maryam domin samun lafiyayyu kuma haɗaɗɗun Lagos lace wanda zaku iya samun ɗinkakku da kuma sabbi a ledarsu, kaya iya zaɓinki, gefe ɗaya muna da GHT product, zaku samu,*

~MAI DA TSOHUWA YARINYA

~FEMALE CARE

~REODEO

~VIGOR MAX

~ LONGZIT

~B CLEAR

*DUK ZAKU SAMU WADANNAN KAYA CIKIN SAUKI DA RAHUSA MAZA KU NEMI MAMAN MARYAM AKAN WANNAN NO 07080222187, SIYAN NA GARI MAIDA KUƊI GIDA.....*


~~~Ni kaina inada yaƙinin cewa zanyi missing Samz duba da irin yadda zuciyata ta shaƙu dashi ƙwarai dagaske, duk da baida yawan hayaniya amma ni idan yana tare dani mai surutu yake zama tare da barkwanci dan haka zai yi ta tsokana ta yana zolaya ta, da tunaninsa a ƙoƙon raina muka sauka garin Abuja, Anty da kanta itace ta ɗauko ni zuwa gidanta,

"Widat da alama Lagos ɗin nan ta karɓeki....." Anty ta faɗa cikin wasa akan hanyar mu ta zuwa gidanta fuskarta ƙunshe da fara'a, juyawa nayi na kalle ta,

"Anty me kika gani?" na buƙata ina kallonta,

"Na ganine ai kin narka uwar ƙiba..." ta bani amsa idanuwanta na kan titi,

"wai dagaske Anty?"

"Allah dagaske kin yi ƙiba Widat, babu wanda ya faɗa miki? Salma bata faɗa miki ba?"

Please Login or Register in order to submit comment