Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da Maryam muna hira naga kiran yaya faisal ya shigo,

"Kinga har ya ƙaraso ba" na faɗa ina ɗaga wayar ai kuwa ina karata a kunnena naji yace "madam gani na zo"

"ok to ina zuwa" na bashi amsa kafin na cire wayar daga kunnena na miƙe tsaye ina sake duba fuskata a mirror, ni na fara yin gaba ita kuma ƙawalli zata biyoni daga baya.

Kamar koda yaushe a sashen su yaya Abdurrahman na iskeshi ɗakin yaya Abdul hakim, ya sha gayunsa cikin wani sabon lallausan yadi fari kansa sanye da hula, ganina na shigo yasashi yin murmushi yana kallona,

Zama nayi ɗan nesa dashi na fara gaidashi fuskata a sake duk da saida nayi namijin gaske kafin hakan ta kasance. Muna zaune muna ɗan taɓa hira wacce mafi yawanta ta aikina ce ƙawalli ta shigo hannunta ɗauke da babban faranti wanda ta ajiye agabansa itama suka shiga gaisawa, ta ɗan jima sannan ta fita ta tafi, nikam har saida lokacin sallar azahar yayi sannan na samu na fito na nufi sashen mama tun daga nan ban sake komawa wurin sa ba har sai bayan da aka yi sallar magrib duk da massage ɗin da naga ya tutturo min akan wai in zo in ɗauki kayana da ya kawo min, sai da na bari ƙawalli ta dawo sannan muka je tare bayan na sake caɓa ado cikin wata doguwar riga ƴar kanti mai santsi, nan ta kwashi kayan ta fita dasu ta kai cikin gida, tare dashi muka shiga gidan suka gaggaisa dasu mama sannan ya shiga wurin Abba, tun daga nan nikam nayi sallama dashi na wuce ɗakina, kayan da yaya faisal ya kawo min nagani saman gadona ƙawalli ta ajiye min su nan na zauna na soma dubawa, turaruka ne yan ubansu designers sai kayan ciye ciye su chocolate kala daban daban sannan sai kwalin sabuwar waya ƴar yayi mai shegen tsada. Kinkimar kayan nayi na nufi wurin mama dasu domin nuna musu amma koda naje sai naji tace ai tuni Maryam ta kawo musu sun gani dan itace ma ta umarceta da ta kai min kayan ɗakina suma ga irin tsarabar da ya kawo musu, fruits nagani kaya guda tun daga kan lemo, ayaba, abarba da apple, apple ɗin na ɗauka guda ɗaya na wuce ɗakina na ajiye kayan na soma shirin bacci bayan na gabatar da sallar ishah lokacin misalin ƙarfe tara da rabi (9:30) na dare, kishingida nayi akan gado na na ɗauki apple ɗin da na shigo dashi na fara gutsira ina ci, wayata na hannuna ina duba posting ɗin da aka yi a Instagram dan yau gaba ɗaya ban hauba sai yanzu, kiran da ya shigo cikin wayar tawa ne ya katse min kallon da nake yi, "yanzu zai katse min jin daɗi" na ayyana hakan acikin raina ina ƙoƙarin ɗaga kiran,

"albishirinki..... Abba yace in turo magabata na......" iya abinda na iya ji kenan sakamakon silmiyewar da wayar tayi ta faɗi................... ✍🏼






*_Ummi Shatu_*👌🏻
[1/5, 12:43] Maman K: ©️ *HASKE WRITERS ASSOCIATION.*
_(Home of expert & perfect writers)_



*GARIN DAƊI.....!*💍💍



*_NA_*

*_UMMI A'ISHA_*


*Wattpad:ummishatu*



*3*



~~~Ban bari naji ƙarashen abin da yake faɗi ba na runtse idanuwa na ina jin wani yanayi yana lulluɓeni wanda shi ba farin ciki ba haka kuma ba baƙin ciki ba, jin kamar bana tare dashi ya sanyashi katse kiran ya sake kirana cikin ɗoki da shauƙi, ɗagawa nayi jikina a mutuƙar sanyaye,

"Ranki ya daɗe ya na jiki shiru? Ko dai duk farin cikinne ya hanaki magana?"

"uhmmm" na faɗa cikin murmushin da bai kai zuci ba, murmushin shima naji yayi kafin yace,

"to shikenan zan bar ki ki cigaba da murnar ki zuwa gobe zamu haɗu"

Sallama muka yi ya katse wayar murna fal ransa amma ni dai banji wata murna ko saɓaninta ba, kashe wayar tawa nayi gaba ɗaya nayi addu'a na shafa, inata saƙe saƙe acikin raina da haka har bacci ya ɗaukeni. Yau ma kamar jiya ƙawalli ce ta haɗawa yaya faisal kayan karyawa ni babu abin da nayi in banda wanka na shirya cikin blue ɗin doguwar riga nayi rolling muka wuce sashen su yaya Abdulhakim bayan mun karya, yaya faisal na zaune yana karyawa sai faman fara'a yake tayi kamar gonar auduga gaba ɗaya bakinsa yaƙi rufuwa, gaishe shi muka yi daga nan na kama bakina nayi shiru sai shida ƙawalli ne kawai keta hirarsu cikin barkwanci daga bisani ta tashi ta fita ya rage daga ni sai shi, kallona yayi cikin murmushi yace,

"kinji yadda muka yi da abba ko? Insha Allah gobe ina komawa zan sanarwa da gida yanda muka yi dashi...."

"wai gaggawar me kake yi ne har haka?"

Wani murmushin ya sake yi kafin ya bani amsa da,

"babu maganar gaggawa acikin wannan lamari widat.... Insha Allah ma acikin month ɗinnan zan gama haɗa lefenki sannan zan samu gidan da zamu zauna a Abuja"

Murmushi nayi tare da faɗin, "wa yaga ganɗoki"

"naji, dama abin da nake nema ne kuma ya samu to me zan jira? Any delay is dangerous"

Dariya na ɗan yi bance komai ba, yau dai babu laifi na ɗan saki jiki dashi mun ɗan taɓa hira har azahar, da rana abincin da aka dafa a gida na kai masa shinkafa da miya da salad zuwa yamma muka fita tare dashi da ƙawalli tayi mana rakiya zuwa unguwar jan bulo gidan anty salaha, a can muka tarar da bishra wacce ta sake dan bata ma da ranar komawa gida da alama,

"wai ke sai yaushe zaki dawo gida ne?" na faɗa ina kallonta domin harga Allah bana jin daɗin gidan sosai da bata nan,

"babu ruwan ki, tun da ke baki zoba to ki ƙale ita da ta zo, kuma nan ɗin a jeji take da zaki wani ce yaushe zata koma gida" anty salaha ta faɗa cikin faɗa tana hararata,

"Allah ya baki haƙuri" na faɗa ina ɗan ɓata rai,

"haƙuri kaya ne, ai wallahi zaki yi auren kema kuma nima zan rama duk wannan rashin ziyarar da kike yi min"

"a'a anty tuba muke kar ayi mana haka" yaya faisal ya faɗa yana dariya, har magrib muka kai a gidan anty salaha daga bisani muka yi musu sallama muka tafi nan ya ajiyewa bishra kuɗi wanda ban san ko naira dubu nawa bane. Bayan da muka koma gida wata hirar muka ɗora daga ni sai shi a farfajiyar gidanmu sashen su yaya Abdurrahman lokacin ƙawallita ta tafi, har 10 muna tare kuma sai lokacinne muka yi sallama na wuce cikin gida shi kuma suka cigaba da zama da yaya abdulhakim wanda shigowarshi kenan cikin gidan,

Washe gari daurewa nayi ban koma bacci ba tun bayan sallar asubah saboda ina son in taya ƙawalli aiki yau, ƙarfe 6 naji shigowarta, bata zaci idona biyu ba tasa wayarta a charge domin har lokacin da akwai wutar nepa, tana shirin fita daga cikin ɗakin nayi magana,

"barka da zuwa, ina kwana?"

Fasa fitar tayi ta dawo baya tana dariya "yau sammako aka yi kenan? Kiyi baccinki wallahi"

Ƙoƙarin tashi zaune nayi ina gyara baƙar hular baccin dake kaina,

"muje in tayaki dan Allah"

Ba dan taso ba muka fita tare muka fara aikin, dankali da ƙwai muka haɗa masa da ƴar sos wacce ta ƙawatu sai tashin ƙamshi take, kafin 8 mun kammala komai, baccina na sake komawa a karo na biyu wadda bani na tashi ba sai 10:30 kuma wannan ɗinma mama ce ta tadani wai intashi in je muyi sallama da yaya faisal zai tafi domin yafi so ya tafi da wuri, wanka nayi a gurguje na fito, ina cikin shiryawa ina tambayar kaina wai ƙawalli itama tun da ta tafi bata dawo ba? Riga da wando na Pakistan na saka na yafa mayafi na fita, cikin shirinsa tsaf na tafiya na sameshi, ga breakfast ɗin da muka haɗa masa nan ya gama ci sai santi yake yi min, mun ɗan taɓa hira kaɗan muka fito na rakoshi domin tafiya, muna tsaye gaban motarsa ƙawalli ta shigo,

"ah me zan gani? Ba dai har ya fito ba?"

"ehh na fito Maryam, ai dama da ace baki zo ba da sai na nemoki kafin na tafi"

Ina jin su bance komai ba sai murmushi da nake yi, gaisawa suka yi kafin ya buɗe motarsa ya shiga,sabbin kuɗi ya miƙo min wai gashi mai yawan nawa ɗayan kuma na maryam, godiya muka yi ya ja motarsa ya tafi muka wuce cikin gida. Kuɗin da yabamu na bawa ƙawalli nata 5k nikuma 10k sannan na haɗa mata da biyu daga cikin turarukan da ya kawo min sannan na ɗiba mata chocolate ɗin, bayan tafiyarta wuni nayi ina bacci har yamma bayan na tashi ne na kira yaya faisal nan yace min ya isa gida, ayau na buɗe wayar da ya bani na fara amfani da ita har 11 na dare na kai ina transferring kayana dake cikin tsohuwar wayata saida na gama tura komai sannan na kwanta bacci domin gobe da aiki.

Kamar yadda yaya faisal ya faɗa yana komawa gida ya sanarwa da magabatansa maganarmu tare da damar da abba ya bashi na yaturo a tsaida maganar aure, satinshi biyu da zuwa yace min suma ƴan gidan su zasu zo nan shiri ya tashi agidanmu cikin weekend suka zo, mazane guda shida, mahaifinshi da yan uwansa guda biyu sai ƴan uwan mamanshi da aminin babanshi guda ɗaya, faɗin irin girmamawa da karramawar da aka yi musu ɓata bakine, haka suma sun yi bajinta sosai sun kawo Kuɗin aure na naira dubu hamsin da goro da alawa kaya guda wanda ya kasance na saka rana kuma sun bar ranar a matsayin nan da watanni shida masu zuwa. Yaya faisal ganɗoki tuni ya fara shiri nikam babu abin da nake shiryawa tun da gani nake bikin ma da saura.

Kamar koda yaushe yau na taso daga aiki ina cikin napep zai maidani gida, sanye nake da doguwar riga baƙa na saka baƙar hula a kaina na ɗora baƙin mayafi a kai, hankalina gaba ɗaya na kan wayata inda nake duba wani posting da A&U kitchen tools suka yi inda suke tallata wata blender mai kai huɗu wadda har dambun nama tana yi haka kuma tana yin sakwara, birki naji mai napep ya taka da ƙarfi sannan ya ɗauke napep ɗin mun yi gefe guda tamkar zamu hantsila, cike da masifa da ɓacin rai naga ya fita, sai lokacin hankalina ya kai kan wani matashin saurayi dake tsaye sanye cikin ƙananan kaya, fuskarshi sanye da baƙin gilashi wanda ya rufe idanuwansa rikif bana jin abin da suke cewa, dawowa mai napep ɗin yayi yana cigaba da masifa,

"haba mutane sai kace dabbobi, salon ka buge su kuma su goga maka masifa su zame maka jidali..."

"bawan Allah kayi hakuri makaho ne fa, baya gani"

Gaba ɗayanmu juyawa muka yi muna kallon wanda yayi maganar, wani ɗan dattijo ne jikinsa sanye da kaya irin na ƴan ƙungiyar direbobi, bai jira cewar mai napep ɗinba yaƙara gaba ya koma wurin wannan saurayin ya kama hannunsa wanda inada yaƙinin cewa napep ko mota zai tare masa, ƙura masa ido nayi ina kallonsa kyakkyawa ne masha Allah kuma idan ba sani kayiba ba zaka taɓa dangantashi da makanta ba, jin mai napep ya fincikemu da ƙarfi ya sani gaggawar dakatar dashi wanda ni kaina ban san dalili ba, cikin hanzari na fita na nufi inda suke tsaye dattijon nan na Ƙoƙarin tare masa abin hawa, rasa abin da zance musu nayi daga ƙarshe nayi sallama dattijon nan ya amsa tare da kallona bayan ya maido da hankalinsa gaba ɗaya kaina dan jin abin da yake tafe dani,

"am baba dama zuwa nayi in bashi haƙuri akan abin da ya faru, wallahi mai napep ɗin bai san cewa baya gani bane, ya zaci ko da gangan yayi mana haka amma dan Allah yayi haƙuri.... Bawan Allah dan Allah kayi haƙuri"

"babu komai yarinya irin hakan ta jima tana faruwa, duk wanda yaganshi sai ya zaci yana da idanu shiyasa abu ƙanƙani sai mutane suyita kyararsa suna ganin kamar da ganganci yake shan gabansu idan suna tuƙi, makarantar makafi yake zuwa kuma kusan kullum nan yake zuwa ni nake tare masa abin hawan da zai mayar dashi gida"

Sake duban saurayin nayi da kyau sai naji duk tausayinsa ya ɗarsu a raina sannan kuma ya mamaye zuciyata gaba ɗaya,

"baba to mu tafi dashi sai mu saukeshi tun da naga bai samu abin hawa ba"

"a'a kuje kawai, ba drop kika ɗauka ba?"

"babu komai baba sai mu ajiyeshi koma ina zai je"

"gyaɗi gyaɗi ƴan dusa zai je"

"OK nima court road zanje, mu tafi babu matsala"


"Hashim zo ku tafi, Allah ya kiyaye hanya"

Kama hannunsa yayi yasakashi cikin napep ɗin yana yi mana Allah ya kiyaye hanya sai gobe idan yazo, shi dai har muka fara tafiya bai yi magana ba sai kai da yake ɗaga masa alamun to, ni kuwa tamkar na samu wani mirror domin kafeshi nayi da idanuwa ina kallonsa, farine sol dogo haka kuma bashida jiki yana dai sahun sirara, in banda makantar dake tare dashi sam bashida wata makusa,

"hajiya ina zamu kai shi?" naji muryar mai napep yana tambayata,

"gyaɗi gyaɗi ƴan dusa, idan muka saukeshi sai ka kai ni"

"to shikenan Allah ya saukemu lafiya"

Cigaba da kallonsa nayi acikin raina ina tunanin ko yaya wannan bawan Allah yake ji, gashi saurayi matashi wanda a yayi shekaru da yawa ace shekararsa 32,sai dai gashi nan tsaf tsaf dashi babu ƙazanta ko rashin gyara atare dashi, har mukaje gyaɗi gyaɗi ƴan dusa bai yi ko tari ba saida mai napep ya tambayeshi a ina zai saukeshi sannan yayi magana,

"kusa da sabuwar transformer....."

Muna zuwa wurin kuwa yace ya isa ga gidan nan, Allah mai iko shi ne abin da naketa nanatawa acikin raina, aljihun wandonsa ya fara lalubawa zai ciro kuɗi, ɗari biyar guda ɗaya da dubu ɗaya itama guda ɗaya sai ɗari biyu, ɗari biyun naga ya ɗauka yana cewa mai napep,

"ga ɗari biyu ka ɗauki kuɗinka"

"barshi zan bashi Kuɗin" na faɗa ina kallonsa,

Sai lokacin ya ɗan jiyo ya kalli gefen da nake sannan naji yace "nagode Allah ya saka da alkhairi"

Daga haka ya juya ya nufi gidan su wanda yake dab da inda muka tsaya, ni dai har ya shige cikin gidan ban daina kallonsa ba har saida na daina hango shi................. ✍🏼





*_Ummi Shatu_*👌🏻
[1/5, 12:43] Maman K: ©️ *HASKE WRITERS ASSOCIATION.*
_(Home of expert & perfect writers)_




*GARIN DAƊI.......!*💍💍



*_NA_*


_*UMMI A'ISHA*_



*Wattpad:ummishatu*



*4*



~~~Nidai har naje gida ban daina tunanin wannan bawan Allahn ba domin dagaske al'amarinsa naji ya tsaya min acikin raina amma ban iya faɗawa kowa ba duk da cewa ƙawalli tazo munsha hira domin har bayan mgriba muna tare amma ban sanar da ita ba sai hirar bikina da take ta faman yi tana cewa gaba ɗaya ma ta rasa irin shigar da zata yi ranar, kasancewar tunanin wannan guy ɗin da naji ankira da suna hashim yana ƙoƙon raina shiyasa ban sake nayita yi mata kauɗi kamar koda yaushe ba daga ƙarshe har taso ta fahimta,

"ƙawalli wai ko dai wani abu yana damunki ne?" naji ta faɗa bayan ta zuba min ido, murmushi na ɗan yi cikin ƙarfin hali sannan nima na dubeta ina wasa da igiyar dake gaban doguwar rigar dake jikina mai gajeren hannu,

"me kika gani ƙawalli?"

"to ai na ganki ne gaba ɗaya kamar kinyi sanyi"

"wallahi lafiya lau nake kawai tsabar gajiya ce, yau tunda naje office ban samu kaina ba har lokacin tashi"

"to ya kamata ki kwanta da wuri ki huta, nima bari na tashi na wuce gida, idan yaya faisal yakira a miƙa min gaisuwa"

Harararta nayi na ɗauke kaina ina cewa,

"idan dagaske gaisheshin kike son yi ga no ɗinsa nan ki ɗauka sai ki kirashi"

"kya dai ji dashi"

"ko kuma ke kiji dashi ba"

Hijabinta ta saka tana dariya tare da ficewa daga ɗakin. Ni dai yau gaba ɗaya na kasa mantawa da tunanin wannan makahon saurayin dan hatta yaya faisal ma sai da ya fahimci yau bana jin hira shiyasa ba mu wani jima ba muka yi sallama nikam sai bacci ɓarawo, washe gari da wuri na tashi na shirya domin tafiya aiki, kamar koda yaushe doguwar riga na saka ta atamfa dark purple na yafa purple ɗin mayafi sai zuba ƙamshin turaren blue nake yi wanda ya haɗu da ƙamshin Arabian oud, ina ƙoƙarin fita daga gida bayan na yiwa su Annie sallama naji ƙarar wayata, ganin yaya faisal ne ya sani yin murmushi kafin na ɗaga wayar,

"ko har kin fita?"

"a'a sai dai niyya ka ganni nan zan fita yanzu"

"to shikenan Allah ya kiyaye hanya, idan kika je office za muyi waya"

"babu matsala" na faɗa ina zare wayar daga kunnena tare da mitar kiran da yaya faisal yayi min dan gashi nan sanadiyyar hakan ban samu damar gabatar da addu'ar fita daga cikin gida ba.

Lokaci zuwa lokaci nake duba agogon dake ɗaure a hannuna domin bana son yin latti so nake na fita kamar jiya ko Allah zai sa insake gamo da hashim wanda tausayinsa da son sanin halin da yake ciki ya gama addabar ruhi na da zuciyata gaba ɗaya, misalin ƙarfe 5 dai dai na yamma na fito daga office na ɗauki drop ɗin napep muka nufi hanyar da nabi jiya, sai tsittsilla ido nake yi ai kuwa cikin ikon Allah na hangosu tsaye da wannan dattijon na jiya wanda yace shine yake tare masa abun hawa kullum, agabansu muka yi parking ina kallonsu cikin fara'a na fito ina gaida wannan dattijon,

"yarinya sai dai kuma ban ganeki ba daga ina?"


"Baba Jinjiri itace fa budurwar jiya baka gane ta ba? Wadda muka tafi tare...." jin abin da ya fito daga bakin saurayin ya sakani sakin baki ina kallon ikon Allah,

"eh an yi haka, sai yanzu na shaidata, yarinya ya aka yi?"

"baba na zone mu tafi tare dashi"

"Allah sarki to Allah ya saka miki da alkhairi kinji"

"amin" na amsa ina mai juyawa domin shiga cikin napep ɗin, kamar jiya yau ma baba jinjiri ne ya taimaka masa ya shiga cikin napep ɗin muka tafi, bayan mun fara tafiya naji yace,

"ina yini?"

"lafiya lau, ya makaranta?"

"alhamdulillah" daga haka muka ɗanyi shiru kafin na katse shirun da cewa,

"amma ya aka yi ka ganeni?"

Murmushi Naga yayi wanda ya sake bayyana kyawunsa,

"na ganeki ne ta hanyar jin muryar ki, dama kuma jiya da tunanin ki na kwana, kiyi haƙuri da rashin sakin fuska da nayi miki.... Wallahi jiyan ne raina gaba ɗaya aɓace yake shiyasa"

"ayya babu komai karka damu, amma ai na baka haƙuri dangane da abin da ya faru soo bai kamata ka ɓata ranka ba"

"ba zaki gane halin da nake ji ba a duk lokacin da mutane suka yi min irin abin da mai napep ɗinnan yayi min, makanta tafi komai yawan ƙalubale, kowanne mutum ana iya gane halin da yake ciki idan har aka kalli ƙwayar idonshi to mu ba aga namu idonba bare a fahimce mu.... "

" babu komai Allah shi ya san dalilin da yasa ya iyo ku a haka "

Kasancewar muna ta hira dashi kafin na farga sai na ga har mun kawo ƙofar gidan nasu, yana ƙoƙarin ciro kuɗin da zai biya mai napep nace yabarshi sannan na ɗora da cewa,

" idan har babu damuwa kuma babu matsala ka rinƙa jirana kullum zan rinƙa zuwa muna tahowa tare"

Gyaɗa min kai yayi alamun babu matsalar sannan naji yace,

"amma menene sunan malamar?"

"maimunatu (widat)"

"mai tagwayen suna"

Daga haka yawuce nikuma nabi bayan sa da kallo ina murmushin da ni kaina ban san ma'anarsa ba. Yau ma kamar jiya da tunaninsa a raina naje gida haka kuma ban sanarwa da kowa ba sannan tun daga wannan rana muke dawowa tare dashi domin kullum sai na biya ta wurin da yake tsayawa mun ɗaukeshi, yau kam ban tashi da wuri ba har 6 na kai a wurin aiki shiyasa duk nabi na shiga damuwa saboda nasan hashim yana can ta yuyu har ya gaji da jirana, sannan gashi shi ba waya gareshi ba da na taɓa yi masa maganar waya ce min yayi wai waya ta masu ido ce shi bashi da buƙata,da damuwa acikin raina muka doshi inda muka saba ɗaukarsa kamar koda yaushe, can na hango shi zaune ƙasan wata bishiyar maina hannunshi riƙe da wani ganye yana wasa dashi, a hankali na sauka na ƙarasa batare da na bari yaji takun sawayena ba domin saɗaf saɗaf nake tafiya har naje dab dashi, tsayawa nayi akusa dashi ko rabin minti banyi ba da tsayawa naga ya dakata da wasan da yake yi da wannan ganyen ya ɗan karkato da kanshi kafin yayi murmushi yace,

"barka da zuwa, gaskiya yau da alama kinsha aiki dan kin makara sosai...... Har na fara yanke tsammani da zuwanki...." duk da ba wannan ne karo na farko da hakan ta faru ba amma na cika da al'ajabi mutuƙa,

"assalamu alaikum" na faɗa ina kallonsa, sanye yake da jeans da t shirt dukansu blue colour sai dai jeans ɗin yafi rigar turuwa sosai,

"wa'alaikumussalam da maimunatu"

"kayi haƙuri da zaman da na barka kayi kana jirana, tashi mu tafi"

Miƙewa yayi yana murmushi na wuce yana biye dani,

"karki damu dama naji ajikina zaki zo shiyasa zaman bai wani dameni ba"

"to yau kuma ta yaya ka gane zuwa na duk da banyi magana ba?" na faɗa yayin da muka soma tafiya,

Murmushi yayi ya ɗan juyo saitina kamar mai kallona,

"yau da gobe ai tafi ƙarfin wasa, ƙamshin turarenki kaɗai naji sai kuma naji alamar bugun numfashinki...."

"ta haka kake gane mutane kenan?"

"eh wasu ba, amma mafi yawa ta muryoyinsu nake gane su"

"gaskiya kana da basira sosai"

"a'a daga Allah ne"

Har muka je ƙofar gidan su muna hira kuma daƙyar muka rabu zuciyar kowa cike da tunanin ɗan uwansa domin a ƴan kwanakin da muka yi muna dawowa tare tuni har mun fara shaƙuwa da juna.

Yau da na tsaya ɗaukarsa ban ganshi ba kuma koda na tambayi baba jinjiri sai yace dani wai yau kwata kwata hashim bai zo ba abin da ya tayar min da hankali kenan har nakasa jurewa sai da na bishi gidan su, ginin gida ne irin na talakawa, ɗakuna guda biyu ne babu ko siminti sai ƴar baranda, suna zaune a barandar shi kuma yana kwance ga tukunyar da aka dafa masa ruwan maina nan agefe, sallama ta ya sanya duka hankalinsu dawowa gare ni, wata ƴar dattijuwa ce wadda daga gani itace mahaifiyarsa sai wata ƴar budurwa baƙa,

"maimunatu ce wadda nake baki labarinta, dama nace miki zata zo" na jiyo muryarsa cikin alamun ciwo yana sanarwa da mahaifiyar tashi, cikin girmamawa aka shinfiɗa min tabarma, muka gaggaisa anan suke sanar min da rashin lafiyar tashi wai tun daren jiya bayan ya dawo da zazzaɓi ya kwana har yau ɗinnan,

"sannu hashim..... Allah ya baka lafiya ai dama tun da naga shiru kuma naji an ce baka zo ba nayi tunanin ko ba lafiya ba, amma ya sha magani kuwa?" na ƙarashe maganar ina kallon mahaifiyar tashi, dukkansu shiru suka yi babu wanda ya amsa min, sai wannan yar budurwar ce naji tace,

" a'a bai sha magani ba, ba a samu kuɗin siyowa ba... "

" amma yaci abinci? "

" a'a, yau ba mu dafa komai ba, dama iya ke yin waina ta siyarwa kullum da safe to yau da asuba ta tattara min kuɗin dan inje in yi mata cefane wasu suka ƙwace....."

"subhanallahi ubangiji Allah ya rufa asiri, bari ina zuwa"

Wayata na ciro daga cikin jaka na kira bishra amma har tayi ta katse bata ɗauka ba, anty salaha na kira ina jan tsaki sakamakon rashin ɗaukar da bishra bata yi ba, itama anty salahan sai dab da zata katse sannan ta ɗauka tana cewa "widat ya aka yi?"

"anty dan Allah magani nake so ki tura min zan siyo, na zazzaɓi da ciwon kai"

"akwai amai ne ko kasala haka?" ta tambayeni, kallon iya nayi na tambaye ta ko akwai amai tace min babu dan baima ci komai ba nan na faɗawa anty tace to bari ta turo min amma babba ne ko yaro marar lafiyar nace mata babba ne, sallama muka yi sannan na miƙe ina cewa su iya bari naje ina dawowa

Please Login or Register in order to submit comment