Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

koma menene da kansa domin shine masani akan komai,

Kwana biyu dai baya samun zama yadda ya kamata saboda bikin abokinsa Ahmad da ya sako kai, yadda ahmad ya tsaya tsayin daka lokacin bikinmu shiyasa shima yanzu yake son ramawa kura aniyarta dan shine a sahun gaba akan komai, kasancewar a Kano za ayi bikin shiyasa da satin bikin yazo muka tattara muka tafi amma wannan karon agidanmu muka sauka kuma tare zamu dawo ranar da za a raka amarya, wannan zuwan banyi yawo ba sosai dan wasu ma basu san nazo ba gidan ƙawalli kawai na leka naga Irfan sai ko gidanmu da naje shima ban ko wuni ba, daga nan na dan shiga kasuwa itama sama sama, nayi attending duka events din kuma tun anan muka yi sabo da amaryar mai suna Nihal haka koda aka rakota Abuja ni na zauna tare da ita har zuwa lokacin da angwaye suka karaso sannan muka yi musu sallama muka tafi, tun muna hanya yake cemin wai yau bikin Ahmad ya tuna masa namu bikin muma,

"me ka tuna daga ciki?" na bukata ina kwanciya a gefen jikinshi,

"everything baby..... Babu abinda na manta"

"wow....." na fada cikin tsokana, "ke baki tuna komai ba"

'na tuna mana... "

" me kika tuna? "

" ranar dinner..... "

Dariya yayi ya ja hancina saboda ya san tunda na fadi haka to kuma tsokanace zata biyo baya, har muka je gida maganar muke yi,

A falo na barshi suna waya da mommy nikuma na wuce bedroom waist bit din da na siyo na ɗaura da niyyar burgeshi dama normal one din na siya ba mai hadi ba kamar yadda naji masu siyarwar suna tambayata lokacin da naje siya wai mai hadi ko marar hadi nace marar hadi dan bana son garin burge miji inje kuma in sabawa Mahalicci na, riga na saka iya cibiya da mini skirt wadda mazaunai na kadai ta rufe na fito, ai tun yana wayar da ya hango ni daga nesa naga ya tashi zaune daga kishingiden da yake yana miko min hannu amma sai na makale kafada naki zuwa, nafi son har sai ya gama yadda zamu fi sakewa da juna amma yanzu idan na kusanceshi ai akwai matsala, kasa hakuri yayi yace ma mommy bari yana zuwa zai kirata back ya ajiye wayar ya juyo yana kallona sosai,

"zo mana baby...." a hankali nake takowa zuwa inda yake, ina karasowa ya damƙi waist dina yana cewa,

"baby what's this?"

"kwalliya nayi maka"

"I see, yayi kyau saura nan....." ya fada yana taɓa cibiyata,

"kana so?"

"yes baby....."

Tunda ya samu jigidar nan ai ya samu abin yi lallai ada nayi sake da ban saka tunda wuri ba sai yanzu ashe bawan Allah yana so kuma yana ra'ayi kuma da yake mai different colors na saka sai hakan yafi daukar hankalinsa tunda na gane haka nima yanzu sai na daina saka kayan da zasu rufe ta, koda yaushe kananun riguna nake sakawa iya cibiya inyita juyi yana kallo na wani lokacin ma har a bani tukwici.
*** *** ***

Shalele shine sunan da kowa na gidan ke kiranta dashi saboda tsabar shagwaba da gata kasancewarta mace guda daya a cikin gidan, duk sauran yan uwanta maza ne sannan kuma itace yar auta, wannan dalilin yasa kowa ya tashi abu Shalele duk wata kulawa tana samu gashi ta fito daga tsatson mulki da masu gidan rana saboda mahaifinta mai fada aji ne ne gaba da baya, duk abinda take so shi ake yi mata haka wanda bata so kuma an barshi har abada. Cikakken sunanta Suhaila Umar Lemu, mahaifinta ɗaya daga cikin ƙososhin gwamnatin tarayya ne suna zaune garin Abuja amma asalinsu yan jihar Bauchi ne,

Tana kan hanyarta ta zuwa airport da sanyin safiyar Laraba idanuwanta suka yi tozali gami da arba da samz wanda ke hanyarsa ta zuwa office, masha Allah kawai take furtawa acikin ranta saboda tsabar haduwarsa komai nashi yaja hankalinta nan tayi ta binsa har zuwa office ɗin su,

Parking tayi ta kira daya daga cikin securities din office din, karon farko wasu sabbin kudi yan dubu ta zaro guda goma ciss ta mika kafin ta fara tambayarsa,

"dan Allah taimako zaka yimin, naga wani guy baƙi giant ya shiga nan yanzu shi nake so ka bani phone no dinsa...."

Dan jimm security din yayi kafin yace "ehh madam na gane shi amma sai dai bani da no dinsa...."

"babu matsala na baka assignment kaje ka nemo min komai da ya shafe shi please and am going to pay...."

"ok ma, i shall..."

Exchanging contacts suka yi sannan ta juya kan motarta ta fita tana jan dan siririn tsaki sakamakon kiran da Jalil keta faman yi mata dan ya jima da sauka...........


*Garin dadi littafin kudi ne ga mai bukatar cigaban labarin sai ya tura 500 ta 0774712835 Aisha Ibrahim Access Bank sai a tura evidence of payment ta wannan no 07044644433 ko a tura katin waya da shaidar biya wannan no 07044644433*

_*Ummi Shatu*_👌🏻

[1/5, 12:43] Maman K: {53}


*Ina kuke manyan mata ƴan ƙwalisa ma'abota son gyara da kece raini, maza ku garzayo ku nemi maman Maryam domin samun lafiyayyu kuma haɗaɗɗun Lagos lace wanda zaku iya samun ɗinkakku da kuma sabbi a ledarsu, kaya iya zaɓinki, gefe ɗaya muna da GHT product, zaku samu,*

~MAI DA TSOHUWA YARINYA

~FEMALE CARE

~REODEO

~VIGOR MAX

~ LONGZIT

~B CLEAR

*DUK ZAKU SAMU WADANNAN KAYA CIKIN SAUKI DA RAHUSA MAZA KU NEMI MAMAN MARYAM AKAN WANNAN NO 07080222187, SIYAN NA GARI MAIDA KUƊI GIDA.....*


~~~Wannan karon gida na wuce kuma acan na sauka, kowa yayi murnar ganina domin nayi kyau na canja nayi ƙiba, wuni muke muna waya da shi dama kuma can haka ya sabar min dashi, kwana biyu da zuwana na fita na yiyyi ziyara har gidan uncle dinsa naje wato gidan anty Amina, duka yaran nata suna nan iya munira ce kadai ban gani ba akace tana school, washe gari gidan yaya Abdurahman naje daga nan na wuce gidan ƙawalli, nasha mamaki sosai ganin Irfan yana takawa sai dai ba sosai ba dan tafiyar bata gama nuna ba,

"yanmatan Abuja me samz din naki yake baki ne kiketa habaka haka?"

"ƙawalli wai har yanzu sunan nan bazai fita daga bakin ki ba? Idan ba zaki kirashi da Muhammad ba ki hakura"

Dariya ƙawalli tayi tare da ajiye min uban tiren da ta jibgo min kayan dadi akai danginsu kwalam da makulashe,

"Allah ya baki hakuri na daina, a gafurceni..."

"to dai ya fi miki" na fada ina ajiye Irfan kusa dani,sai da muka sha hira muka koshi na gama cika cikina sannan na fara sanar da ita damuwata,

"ƙawalli nifa rashin samun cikin nan nawa yafara damuna, tun abun baya daga min hankali yanzu yafara daga min, abun yayi min jinkiri...."

"kar ki fadi haka ƙawalli, ki daina irin wannan maganar domin Allah yana sane da komai sannan kuma shine zai magance ma kowa damuwarsa, ki daina daga hankalinki akan batun ciki Insha Allah ubangiji Allah zai baki masu albarka nan bada jimawa ba, komai fa lokaci gareshi.... "

" haka shima yake cewa amma ni damuwata kinga mahaifiyarsa da ƴan uwansa ba kaunata suke yiba to rashin haihuwata da wuri zai sake kawo wata damuwar tsakaninmu.... "

" hakane amma kuma ai komai daga Allah yake sannan shine mai badawa kuma naga haihuwar nan kin taba samun ciki bawai baki taba samu bane bare ace bakya haihuwa, wallahi karma ki daga hankalinki "

" ƙawalli ba zaki fahimceni ba kamar yadda shima nasan ba zai taba fahimtata ba, ni kadai na san damuwata da irin yadda nake ji, ni yanzu ma kafin na koma zanje asibitin Dr Aziza in ganta ko da akwai shawarwarin da zata bani bayan ta dubani saboda shi naga kamar abin bai dameshi ba duk lokacin da nayi masa maganar muje asibiti a duba mu ko da matsala sai yaki yace babu wani matsala "

" to ai da gaskiyarsa ni banga laifin sa ba akan me zaki dage sai kunje anyiwa Allah shishhigi? "

" ƙawalli zuwanmu asibiti yana da nasa advantage dinfa, kinga idan akwai wani abu zasu fada mana idan ma lafiyarmu ƙalau sai in samu peace of mind in kwantar da hankalina..."

"hakane ƙawalli kuma na fahimceki tabbas kin zo da magana, to ki samu kije kiga Dr din before ki tafi"

"Insha Allah zanje, ke ai naga kamar harma kin kusa juye na biyu"

Dariya tayi ta kai min duka na goce, kamar koda yaushe wuni nayi ciss gidan ƙawalli sai bayan da nayi sallar magriba sannan suka mayar dani gida, dama tun a hanya yake kirana bana dauka saboda yaya Abdul Hakeem yana wurin shiyasa ina zuwa gida na wuce dakina na bararraje sannan na kirashi,shagwaba naji yafara yimin kamar yadda ya saba,

"baby what have i done to deserve this punishment??"

"am very sorry sweet, you did nothing, yanzu gashi na dawo bazan sake tafiya ba har sai lokacin da ka sallameni..."

"thank you baby...." mun raba dare muna yin waya dashi kafin bacci ya daukeni ban ma san lokacin da na ajiye wayar ba,

Da yake anty salaha tana dab da haihuwa ana igobe zan koma Abuja ta haihu wannan dalilinne yasa ban koma ba na kirashi ina fada masa haihuwar da akayi kuma gara in zauna ayi suna agama akan ace sai na koma sannan in kara dawowa, ba dan ya so ba ya kyaleni ya hakura akan hakan.

***

Tun bayan tafiyata shalele ta cigaba da uzzura masa tare da matsa masa duk da shi bai santa ba kai baima taɓa ganinta ba, ranar da na cika 1 week da tafiya sai gata ita da Malika a gidanmu da yamma da yake shi baya fita ko ina kwata kwata bai iya yawo ba daga gida sai office sai ko yan bukatun da ba arasa ba, ranar a gida ya wuni yana bacci wurin 3 ya tashi ya kirani vedio call wai yunwa yake ji so yake yayi girki in koya masa,

Murmushi nayi ina kallonsa dan a bisa dukkan alamu ya sha bacci babu laifi,

"to yanzu me zaka dafa?"

"jallop rice baby...."

"Ok tom shiga kitchen"

Tashi yayi ya shiga, inata faɗa masa yadda zai yi ina nunnuna masa da haka har yayi jallop din wadda ya wadata ta da kayan lambu dan tasha carrot da cabbage babu laifi, zubawa yayi a flate ya koma falo yana tsokanata wai banji yadda jallop dinshi tayi dadi ba, shagwabe masa fuska nayi kamar zanyi kuka ina cewa,

"nima ta ban sha'awa ina so sweet"

"don't worry baby idan kika dawo zan dafa miki wanda tafi wannan dadi...."

"awwwwn that's my favorite person..."

Sai da aka fara kiran sallar la'asar sannan muka yi sallama. Wanka ya shiga yayi ya fito ya feshe jikinsa da turare sannan ya saka kananan kaya yayi salla, tun yana yin sallar yaji ana buga door bell, yana sallama ya tashi ya nufi kofa dan ganin waye zuciyarsa fal tunani iri iri dan yasan babu mai zuwa mana a daidai wannan lokaci, yana budewa idonsa suka yi tozali da yanmata guda biyu, duk a tunaninsa wurina suka zo shiyasa ya dan saki fuska kadan ya amsa gaisuwarsu,

"am bata nan fa.... Ta dan yi tafiya"

"ayya Allah ya dawo da ita lafiya, sai dai amma dama ba wurin ta muka zo ba kai muka zo nema" Malika tayi magana cikin karfin hali,

"ok but ban ganeku ba"

"dama ai baka sanmu ba"

"meya faru?"

"wannan itace suhaila wadda ta jima tana tura maka da text massage kana ignoring..."

"to me kuma ya kawoku gidana?"

"gani muka yi idan hagu ta ƙi zai a koma dama...."

"I don't understand this..... But inada mata, am married soo pls stay away from me"

Sosai maganarsa ta yiwa Malika ciwo kuma ta kona mata rai, in banda sharrin so da kaddarar so ya za ayi har su zo wurin namiji ya nemi raina musu hankali, Shiru tayi saboda ta gama kuluwa da kalamansa, ita kuwa suhaila da yake ance abinda zuciya ke so ai sam hakan bai bata mata rai ba sai ma sake burgeta da yayi, ji tayi kamar ta durkusa kasa ta soma rokon soyayyarsa amma sai ta dan fuske, yana kokarin maida kofa ya rufe samha na fitowa daga gidanta nan ta tsaya tana kallonsu har Malika wacce ke kule tace "baiwar Allah da magana ne?"

"to ai na ganku kuna fitowa daga cikin gidan nan ne kuma ni a iya sanina matar gidan tayi tafiya tun last week..."

"to ai dama ba wurin ta muka zo ba wurin mai gidan muka zo" daga haka suka wuce ta suka kama gabansu,

Wannan lamari ya daurewa samha kai kuma ya bata mamaki, kwafa tayi ta sheke da dariya kafin tace "wayyoni Allah dama ai dadina da gobe saurin zuwa, wanda bai ji bari ba zai ji hoho, maganin ki widat ba kince namiji dan goyo bane, ai wallahi sai na fesa miki wannan labarin kin ji shi, gashi nan ke da kike tattalin mijin hakan bai sa yaji tausayinki yaki bibiyar matan banza ba, mu da kike yiwa kallon bamu iya ba sai gashi namu mazajen basa bin yanmata bare har su kawo su har cikin gida... "

Ban san me yake faruwa ba ina can gidanmu hankalina kwance inata sabgogina har akayi sunan anty salaha inda jaririya taci sunan mama amma zamu rinka kiranta da Ammah, ana gama suna na fara tarkata nawa i nawa dan komawa Abuja duk da acikin Satin za a kawo kudin auren Bishra daga Bauchi amma Abba yace tafiya zanyi wai ai na jima kuma ba tarone na mata ba mazane zasu kawo gara in koma gidana wurin mijina, lokacin da nake bawa samz labari dariya ya rinka yimin yana cewa Abba yafi sonsa akaina nikuma harda su kukan shagwaba kamar gaske, cikin kwanakin na kammala na koma. Ni na kawo kaina gida ban jira yaje ya taho dani ba kawai dai ya san cewa yau zan dawo but bai san time dinba ni kuwa tunda safe na shirya na biyo jirgin rana saboda nima nayi missing mijina kamar yadda shima yayi,

A bakin kofa na tsaya na danna door bell ina shirin sake dannawa sai gashi yazo ya bude banyi wata wata ba nayi hugging dinsa shima rungume ni yayi yana yimin sannu da zuwa,

"welcome back my baby love...."

Traveling bag ɗina ya dauka muka shiga ciki har lokacin muna manne kamar wani mayen ƙarfe da ya hadu da dan uwansa, daga shi sai t shirt da short nicker da yake weekend ɗin, a falo muka yada zango ya dorani bisa cinyarsa yana rike da hannuwana wadanda suka sha lalle,

"baby kika tafi kika barni ni kaɗai....." ya fada cikin shagwaba yana sinsina kirjina,

"am sorry boo, bazan sake ba, Kaci abinci?"

"nayi mana girki ina jiranki ki dawo muci...."

"awwwwn..... Me ka dafa?"

"let's go and see..." yace dani yana daukata har zuwa kan dining din, jallop din shinkafa irin wadda yayi rannan sai chicken pepe, murmushi nayi ina yaba yadda naga girkin yayi kyau a ido domin komai shar shar,

Da kansa yayi saving dina kafin muka fara ciyar da junanmu kamar yadda muka saba, ai fa tunda na dawo shikenan fita ko zuwa kofa sai ta gagareshi dama kuma weekend ne nanfa muka yi kamar zamu cinye juna tsabar soyayya kuma bashi ya fita ba sai ranar Monday da ya fita office, baccina na shaka kamar yadda na saba bayan azahar na tashi nayi wanka nayi salla na shiga kitchen kenan babu jimawa naji an danna door bell nan na fita na bude, Samha ce shiyasa sai da nayi tsaki cikin raina haka ta biyoni muka shigo tare tana zuba kamar kanyar da bata da zaƙi, zama tayi muka gaisa tayi min sannu da zuwa sannan ta kada baki ta fara fadar abinda ya kawota.

"Widat ban san yanda zaki dauki maganata ba sannan ban san wacce irin fahimta zaki yi mata ba amma koma dai yayane ya zama dole in sanar dake abubuwan da baki sani ba kodan ki san ta yadda zaki kare kanki......"

"ban fahimceki ba Samha, kawai ki tafi straight forward ki fada min abinda kike son fada kibar wani kwana kwana.... Me ya faru?"

"dama na sha fada miki maza ba abin yarda bane kuma duk macen da tace namiji ubane to wallahi sai ta mutu marainiya, namiji rigar ƙaya ne kuma tabarmar ƙashi, namiji ƙanin ajali ne sannan duk abinda zakayi dan ka tarairayeshi ka burgeshi hakan bazai hanashi ya watsa maka ƙasa a cikin idanuwanka ba, mijinki duk yadda kike kyautata masa da wahalta masa da bakya nan wallahi tallahi mata yake kawowa cikin gidan nan.... "

Ras Ras naji gabana ya fadi a karon farko amma sai na daure kuma na danni zuciyata,

" wannan shine abinda kika zo ki fada min? Indai shine bana bukata dan fada min din baida amfani "

" dama na san ranki zai baci amma ni a matsayina na makociyarki wacce tafi kusa dake dole in sauke wannan hakkin makotakar, sannan yanzu cututtuka sunyi yawa na zamani kar kije kina zaune akwaso miki cutar da zata illata ki "

" duk na fahimceki amma sai nake ganin dani dake duk muji da matsalar da ta damemu ya fiye mana akan mu sakawa mazajen wasu ido muna gano laifunsu dan muma namu mazajen baza arasa irin nasu laifin ba wanda suke boye mana suna aikatawa a bayan idon mu..."

"ohh widat abinda zaki fada min kenan akan na kawo miki laifin mijinki? Wannan bakaken maganganun zaki jefeni dasu?"

"ba bakar magana na fada miki ba abinda ke raina na fada miki kuma mijina mutum ne kamar kowa ba ma'asumi bane bare ace dole bazai aikata laifi ba, dukkanmu masu laifi ne musamman mazajenmu to amma ni kazantar da ban gani ba na dauketa a tsafta, tunda yana respecting dina yana tattalina wannan labarin da kika zo min dashi bazai sa in juyawa mijina baya ba mutukar ba wai canja min yayi ba... "

" to shikenan Allah ya gani na sauke duk wani hakki na zaman tare da ya rataya kuma ya wajaba a kaina... "

" idan kin gama zaki iya tafiya saboda aiki nake yi " nace da ita cikin jin haushi dan ita da ta kawo min labarin tafi bani haushi fiye da shi samz din da ya aikata laifin......


*_Ummi Shatu_*👌🏻
[1/5, 12:43] Maman K: {52}



*Ina kuke manyan mata ƴan ƙwalisa ma'abota son gyara da kece raini, maza ku garzayo ku nemi maman Maryam domin samun lafiyayyu kuma haɗaɗɗun Lagos lace wanda zaku iya samun ɗinkakku da kuma sabbi a ledarsu, kaya iya zaɓinki, gefe ɗaya muna da GHT product, zaku samu,*

~MAI DA TSOHUWA YARINYA

~FEMALE CARE

~REODEO

~VIGOR MAX

~ LONGZIT

~B CLEAR

*DUK ZAKU SAMU WADANNAN KAYA CIKIN SAUKI DA RAHUSA MAZA KU NEMI MAMAN MARYAM AKAN WANNAN NO 07080222187, SIYAN NA GARI MAIDA KUƊI GIDA.....*


~~~Sake maimaita abinda na gani naketa faman yi acikin raina gashi abun ya tsaya min cikin rai kamar me shiyasa duk yadda naso in daure na kasa daurewa zuciyata banda tafarfasa babu abinda take yi jira kawai nake ya fito in amayar masa da ta cikina ko zanji saukin abinda yake ta sukar ƙahon zuciyata,

Bai jima ba sai gashi ya fito, "baby haɗa min tea, yau bana son cin abu mai nauyi...."

Shiru nayi masa kamar banji ba har sai da ya sake maimaitawa, faɗar irin kunar da zuciyata keyi bata lokaci ne shiyasa na miƙa masa wayar nace "Gashi nan budurwarka da ka turama kudi ta turo maka massage tana godiya..... Wallahi wannan rainin hankalin ya isa haka kuma na gaji dashi, kaima idan gajiya kayi kawai ka sallame ni in koma gidanmu, koda yaushe nuna min kake yi ni kadai kake so bayan alhali ba haka bane acikin zuciyarka..... "

" Baby wai me ke faruwa?"

" gashi nan ka duba wayarka.... " daga haka na juya na fita naje falo na zauna na hada kai da gwiwa ai sai kuka, ina jin motsin fitowa rasa amma ban ko dago kai na ba bare yasa ran zan saurare shi,

" baby.... Am very sorry...... Let me explain this to you clearly.... "

" wallahi ni babu abinda zaka fada min saboda duk abinda zaka fada min karya ne, last time wata har aiko maka da gift tayi kace min baka Santa ba na yarda yanzu kuma again ka turawa wata kudi sannan yanzu kazo kana cemin zaka yimin explaining, i don't want your explanation, i don't want to hear it.... "

" please baby, please..... " ban barshi ya karasa ba na tada bori da rikici nan duk na burkice masa naƙi saurararsa kwata kwata, duk da yadda yaso yayi min bayani ban bashi dama ba sai ma baƙaken maganganu da nake ta fada masa kishi ya rufe min ido duk maganar da ta fito daga bakina kawai faɗa nake ai banma san lokacin da na kirashi da maci amana ba, kallona kawai ya tsaya yana yi bai ce min komai ba,

Koda nazo bacci banma je bedroom dinba kan doguwar kujera na kwanta, biyoni falcon yayi ganin ba zan kwana acikin dakin ba,

"baby Meyasa ba zaki kwanta acikin bedroom ba? Ki shiga ni sai in kwana anan tunda bakya son kwana tare dani..."

Ban kula shi ba haka ya gaji da tsayuwarshi ya koma ciki, da yake na saba da kwanciya a jikinshi yana yi yana yimin tausa yau duk sai na kasa baccin sai juyi amma taurin kai da zafin kishi sun ki barina inje gareshi ni kawai kiransa da darling da naga wata tayi shine ya tsaya min arai har nake tunanin akwai wata alaƙa a tsakani. Da ƙyar na iya bacci shima baccin babu wani dadi haka nayi shi, washe gari ma kin kula shi nayi gaba daya naki yi masa magana har ya gama shirinsa ya tafi wurin aiki, wanka nayi na shirya fuskata duk ta kumbura saboda kuka da rashin isasshen bacci, duk da ban kula shi ba acan wurin aikinma bai hakura ba sai kirana yake amma bana dauka, WhatsApp yaje ya turo min massage da yaga ina online,

"Am very sorry my sugar baby" budawa nayi nagani amma banyi reply ba, sake turo min yayi please say something my dear nan dinma ban tanka ba daga karshe sai na sauka, ina sauka ya turo min da text massage wanda ko bi ta kai banyi ba. Karfe 6 saura ya dawo ciki ciki na amsa masa ya shige ciki yayi wanka ya fito, zama yayi kusa dani yana kokarin zama nayi niyyar tashi ya rikoni ai sai na fashe masa da kuka, waya yafara kira ya saka a hands free nan naji muryar yaya Abdul hakeem,

"ke....... Widat kina jina?" ya fada cikin tsawa wadda ta sani tsorata dan da mugun bacin rai yayi maganar dama kuma shi babu wasa cikin tsarinsa shiyasa muka fi tsoronsa fiye da kowa cikin yayyenmu,

"ba magana nake yi miki ba?" ya sake fada cikin tsawa,

"Ah ah, Abdul hakeem..... You na calm down please, nifa ban kira ka akan ka ɓatawa matata rai ba, i just call you dan ka bata hakuri....." samz ya fada yana jawoni jikinsa saboda na fara zubar da hawaye, wannan ai shine a dakeka a hanaka kuka,

"wanne irin a bata hakuri sai kace itace gaba da mutane, ka barni da ita inci ƙaniyarta tunda bata da mutunci, mijinki kike kin yima magana dan kawai yana sakar miki fuska? To wallahi ki bude kunnenki da kyau ki jini idan kika bari kika sake ya kara kawo min kararki sai naci mutuncinki marar kunya kawai..... " ni dama a rayuwata na tsani faɗa bana son a sakani a gaba ana yimin fada ana daga min murya yanzun nan zai sakani kuka, wannan fadan na yaya Abdul hakeem ai kamar an yi min mugun duka haka naketa tsiyayar da hawaye,shima da yaji fadan na yaya Abdul hakeem yayi yawa kashe wayar yayi yaci gaba da rarrashi na kamar yadda ya saba dan shi baya yimin fada bare tsawa rarrashina yake da lallaba ni a koda yaushe,

"am very sorry baby, kiyi hakuri Kinji......"

"yanzu abinda kayi min kayi min adalci? Kaje kana mu'amala da wata awaje har kana tura

Please Login or Register in order to submit comment