Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kina da gata kuma muna sonki babu inda akace taje gidanki ta saki a gaba dan kawai kina auren danta ita kuma bata sonki, wai dama irin wannan zaman kike yi da dangin mijinki amma shine baki taɓa fada ba?"

" anty ai ba tare muke da ita ba sai lokacin da ta zo amma shi lafiya lau muke zama sai dai itace matsalar..... "

" ni dama na san bata sonki amma ban taɓa zaton abin ya kai har haka ba, ko zaki koma gidansa to tabbas sai mahaifiyarsa ta fita sabgarku, sai ta gane darajarki da kimarki, sai ta san kema yar so ce kamar kowa "

Shiru nayi ina sauraren fadan da anty keyi wanda tamkar yanzu abin ke faruwa nidai cigaba da saurarenta kawai nayi banyi magana ba domin na jima da fahimtar abin yayi mata ciwo.

Shi kam bayan tahowarmu da anty ciki ya koma ransa a bace sosai, a falo ya samu mommy tsaye tana huci, zama yayi ya dafe kansa yana jin zuciyarsa na tafarfasa,

"mommy dan Allah laifin me mata ta tayi miki da bakya kaunarta? Wanne irin laifi tayi miki da ta cancanci wannan kiyayyar? Mommy ni me nayi miki da bakya kaunata? Kiga yadda kika rabani da mata ta bayan tana sona ina sonta, mommy mata ta soyayya ta cancanci samu daga gareki ba kiyayya ba domin ta mayar dani mutumin kirki nagari abin kwatance, ada ina cikin duhu amma gashi ta fito dani haske ta soni tsakani da Allah ba dan abin duniya ba, duk abinda na sakata shi take yi wanda bana so tun kafin na hanata take nisantarsa amma mommy duk wannan bai sa kinga farinta ba har sai da kika zama sanadiyyar tafiyarta, to mommy yanzu burinki ya cika kin koreta amma ki sani wallahi tallahi bazan auri Felicia ba haka kuma bazan auri duk wata wacce zaki kawo min ba... " daga haka ya wuce cikin bedroom idanuwansa sunyi jajur, binsa da kallo mommy tayi tana taba baki, yana shiga daki ya dauki waya yai dialing no ta amma bata shiga dan wayar tawa tana kashe daga karshe ya ajiye ba wai dan ya hakura ba, har dare wayata tana kashe nan ransa ya sake jagula gashi ya kasa cin abinci dama kuma wanda ya dora har aka samu matsala saboda shi bai karasa ba kashewa yayi sai mommyn ce ta karasa.

Nima duk yadda naso daurewa naso mantawa da halin bakin cikin da zuciyata ke ciki abin ya faskara sannan ya gagara ni ina ganin wannan matakin da anty ta dauka akan samz tamkar yayi tsauri da yawa duk da nasan tana yi ne domin ni, sai da na jima na bata lokaci a falo inda su Aslam ke kallo wai duk dan in samu sauki wurin damuwata amma abin haushi lokacin da nazo kwanciya sai na kasa bacci kai kamar ma lokacin ne damuwar tawa tafi sako min kai nan na rasa abinda yake yimin dadi na nemi farin ciki sama da kasa na rasa acikin raina gashi anty tayi min gargadin da kar in yarda in kuskura in bude wayata bare har ya samu damar magana dani a yanzu shiyasa nake ji araina kamar damuwarsa zata fi tawa, juyi nayi ta yi har daga karshe na tashi zaune ganin kamar baccin baida niyyar daukata saboda kewar mijina ta gama mamaye duk wani ilahirin fili dake cikin zuciyata,bathroom na shiga na dauro alwala na fito dan acikin nasihar da anty tayi min harda in daure kuma in dage inyita fadawa Allah damuwata ina kai masa kuka na insha Allah duk wata matsalata zata kau, salla nayi raka'a biyu amma na tsawaita tsaiwa da sujjada ta domin duk bukatuna da damuwata sai da na fadawa Allah daga karshe nayi addu'a na shafa na tashi bayan na idar na koma na sake kwanciya ina jin tausayinsa yana kai komo acikin raina,

"Allah sarki bawan Allah ko yanzu wanne hali yake ciki? Ko ya samu ya iya bacci ko shima ya kasa kamar ni oho" abinda nake ta nanatawa kenan acikin zuciyata idanuwana suna zubar da hawaye amma a zuciyata dai nayi yakinin Insha Allah tunda na fawwalawa Allah lamurana zai yi min magani kuma zai bani mafita cikin yardarsa. Haka na kusan kwana ina saƙawa da kwacewa har asubah ta kawo jiki wanda sai lokacin ne kuma wani nannauyan bacci ya daukeni wanda ya haddasa min makara sosai dan sai karfe 7 saura sannan na farka, Islam har tayi shirin makaranta ta fita, a gurguje nayi alwala nayi salla na sake komawa na kwanta.

Sassafe ya tashi kasancewar shima baiyi wani baccin kirki ba kamar yadda nima banyi ba, shirin office yayi ya fito amma yana so sai ya fara biyawa ta gidan anty ya bata hakuri, lokacin da ya zo ta fita kai yara school nikuma ina ciki ina bacci dan haka ya nemi wuri ya jira ta har ta dawo,

"A'a Muhammad Kaine kuma shine ka tsaya a nan maimakon ka shiga ciki" anty ta fada bayan ta fito daga cikin motar ta,

"babu komai anty nan dinma yayi dama ke nake jira ai"

"sannu da zuwa, bismillah karaso ciki"

A falo suka zauna bayan sun gaisa ya dan sunkuyar da kai yana shafa kan nashi da yake shi mutum ne mai kunya,

"anty nazo ne in baki hakuri kan abinda ya faru dan Allah kiyi hakuri"

Murmushi anty tayi ta dube shi cikin tausayawa tace "Muhammad bafa abune na laifi ko wani abu mai kama da haka ba, ni ba raba aurenku zanyi da widat ba but ina so ne tayi rayuwa cikin farin ciki kamar yadda kowacce mace ya cancanci tayi rayuwar farin ciki da ƴanci a gidan mijinta, kayi hakuri ka fahimceni, widat ba yaji ta iyo ba kawai na dauko tane ta huta sannan mahaifiyarka ta san darajarta..... "

" to shikenan anty na fahimceki kuma na gane amma dan Allah zan iya ganinta? "

Girgiza masa kai anty tayi tace" bata tashi daga bacci ba kuma ko idonta biyu ma bana jin zan barka ka ganta domin hakan kamar fama mata ciwon dake ranta ne.... "

Mikewa yayi yai mata sallama ya tafi yana jin zuciyar sa kamar zata fashe dan bakin ciki kuma har cikin ransa bai ga laifin anty ba ko shine yake irin matsayinta yaje ya samu ana tozarta yar uwarsa irin matakin da zai dauka kenan tunda tana da gata. Tunda na koma bacci bani na tashi ba sai wurin 11 wanka nayi na fito kuma ina dosowa naji kamshin turaren samz amma dai banyi magana ba na zuba breakfast naci na koma daki saboda anty ta fita ta tafi chamber din su, rasa abinda zanyi nayi dole sai kallo na kunna,

Samz kuwa kasa aikinma yayi da yaje office din daga karshe yaje ya samu Ahmad abokinsa, bai boye masa komai ba ya zayyane masa dukkan abinda ya faru daga farko har kawo yanzu,

"Hmmmmm gaskiya mommy itace mai laifi kuma ita ta janyo duk wadannan matsalolin sai dai babu yadda za muyi sai hakuri dole mu bita ahakan da take muci gaba da yi mata addu'a har ta gane gaskiya, sannan ni ina ganin idan har zai yuyu to muje mu samu mommy muyi mata bayani har ta sauko taje ta iyo bikon Widat dan bana tunanin itama Antyn nata zata dawo maka da ita cikin sauki haka siddan batare da taga alamar anyi wa tufkar hanci ba, ai ma sunyi kokari ko ince ita widat din tayi kokari da bata taba nuna maka bacin ranta ko ta mayarwa da mommy ba, yaran yanzu da idanuwan su yake a tsaye ba kowa ke dagawa uwar miji kafa ba, widat gaskiya tana kaunar ka kuma kana da kima da daraja a idonta shiyasa ta kasa nuna damuwarta akan abinda mommy ke yi mata "

Tare suka nufi gidan bayan sun tashi daga aiki mommy suka je suka samu sai dai duk yadda ahmad ya so ta fahimcesu bata fahimcesu ba maimakon haka ma sai fada da ta rinka yi ta inda take shiga bata nan take fita ba,

" wai shin da me auren yarinyar nan ya amfane shi da kuke son sai an je an dawo da ita? Tunda ya aureta ya tare a karkashinta kamar wata yar sarki, sai abinda take so yake yi, duk yabi ya susuce saboda ita ta mayar dashi kamar bawa, dan haka in dai ni na haife shi to ba zata dawo ba ya saketa, yanda yar uwarta ta wulakantani nima sai na wulakantasu, dan haka aurensu ya kare sai dai yayi wani sabon auren.... "

" mommy kiyi hakuri, bawai muna ja'inja ko jayayya da umarnin ki bane, amma mommy ki gane wani abu guda ɗaya, idan har yanzu kika rabashi da wannan yarinyar kika sa ya auri wata to watan ai bamu san yaya halinta da tarbiyarta yake ba, duk wanda kake zaune dashi lafiya ta yuyu saboda kuna zaune nesa da juna ne baza ka san ainihin wanene shi ba har sai kun zauna tare..... Mommy kinga ita wannan yarinyar ke da kanki zaki shaideta bata taba yi miki rashin kunya ko gardama ko mayar miki da martani ba amma bana jin za asamu wata wacce zata iya wannan hakurin nata kiyi nazarin maganata.... "

" Babu wani hakuri da tayi ko take yi dani, tunda tana auren ɗana yazama dole tayi min biyayya, sannan dama ta san hakan zata faru saboda juyar da tunaninsa tayi ta aure shi batare da son raina ba wannan kadai ya isa ya hanata zaman lafiya a gidan aure kuma ya isa ya hana auren yayi albarka, dan haka ku tashi ku bani wuri tun kafin raina yagama baci "

" Allah ya huci zuciyarki mommy, Allah ya baki hakuri " Ahmad ya fada yana tashi domin fita, bin bayansa samz yayi dama yasan zai yi wahala ai a samo kan mommy lokaci guda.........



_*Ummi Shatu*_👌🏻
[1/18, 09:48] Maman K: 66

*Ina kuke manyan mata ƴan ƙwalisa ma'abota son gyara da kece raini, maza ku garzayo ku nemi maman Maryam domin samun lafiyayyu kuma haɗaɗɗun Lagos lace wanda zaku iya samun ɗinkakku da kuma sabbi a ledarsu, kaya iya zaɓinki, gefe ɗaya muna da GHT product, zaku samu,*

~MAI DA TSOHUWA YARINYA

~FEMALE CARE

~REODEO

~VIGOR MAX

~ LONGZIT

~B CLEAR

*DUK ZAKU SAMU WADANNAN KAYA CIKIN SAUKI DA RAHUSA MAZA KU NEMI MAMAN MARYAM AKAN WANNAN NO 07080222187, SIYAN NA GARI MAIDA KUƊI GIDA.....*


~~~Cike da damuwa yake kallon Ahmad bayan sun fito daga wurin mommy,

"Samz..... Ka kara hakuri kasan ita rayuwa kowa da irin ta yadda Allah yake jarrabarsa, to mu dauka wannan abubuwan da suke faruwa jarrabawa ce daga Allah idan kayi hakuri ka Mika masa lamuranka sai kaga Kaci riba biyu ka samu lada kuma bukatarka ta biya damuwarka ta gushe, na san ba abune mai sauƙi ba a raba mutum da partner dinshi bayan suna kaunar junansu.... Babu yadda zaka yi mommy uwa ce dole haka za abita kuma a lallabata har zuwa lokacin da zata sauko kuma zata gane har ta gyara, ko da wasa kar kace zaka fada mata abinda zai harzukata ko ya bata mata rai, su iyaye magana mai dadi ake faɗa musu koda kuwa kai bazai yi maka dadin ba haka Allah yayi umarni kuma haka manzon Allah yai umarni musamman ma uwa dan haka kayi hakuri ka cigaba da lallabata har muga abinda Allah zai yi "

Ji yake kamar ya fashe da kuka dan ciwon da yake ji a cikin zuciyarsa,

" Ahmad mommy daban take, halinta gaba daya daban yake, yanzu dan Allah laifin me widat tayi mata da ta saka mata wannan karan tsanar? A matsayin ta na mahaifiyata yadace ace tana son duk wani abu wanda nake so, yadace ace tana kaunar duk wani abu wanda nake kauna bawai tana nuna kyama da tsana ba.... "

" kai dai kayi hakuri kawai kasan halin iyayenmu mata, wannan kishin bafa iya akan mijinsu yake tsayawa ba wasu har matan ƴaƴayensu da matan yan uwan mijinsu.... Shiyasa nace maka sai dai mubi abin a hankali har Allah yayi maganin komai, ka kwantar da hankalinka ka samu kaci abinci"

"Insha Allah, an jima zan zo ka rakani wurin antyn nasu"

"babu problem sai kazo"

Sallama suka yi shi ahmad ya fita shikuma ya juya ya koma ciki, zama yayi ya rafka tagumi dan gaba daya ya rasa abinda yake yi masa dadi, sai bayan da yayi sallar magriba sannan ya tafi gidan ahmad ta can suka wuce gidan anty,

Muna falo gaba daya nida yaran suna homework nikuma ina kallo yayin da ita kuma anty ke can wurin daddy wato mijinta wanda bai jima da shigowa ba yazo ya same mu har yana tsokanata, na san jimawarta yana da nasaba da sanar dashi matsalata shiyasa har yanzu bata shigo ba ta yuyu tattaunawa suke yi kan maganar. Ni sam ban san sun zo ba saboda a falon daddy aka sauke su, hakuri suka fara bayarwa amma anty ta dakatar dasu,

"Muhammad ai na fada maka baka da laifi a cikin wannan lamarin kuma ba yaji widat ta iyo ba nice nan na taho da ita kuma gaskiya ba zata koma ba har sai an samu daidaito da gyara"

"Anty tunda har kin san Muhammad baida laifi ko wata matsala ai ba ayi masa hukunci da laifin mommy ba domin wannan matakin da kika dauka shi zai shafa"

"haka kuke gani ahmad amma ni na san abinda nake nufi kuma sannan inada nawa dalilan na yin haka"

Duk yadda suka matsa ma anty da magiya akan tayi hakuri ta basu ni su tafi dani anty ƙi tayi kuma ko mijinta bai goyi bayan ta basu ni mu tafi tare ba, sun jima a gidan daga karshe suka tafi batare da munga juna ba kuma sam anty bata fada min ba cewa sun zo, wayata na kunna bayan nayi shirin bacci, massages ne guda biyu suka shigo wanda na Hashim ne yana ta rokona akan yana so zamuyi magana wai in daure in bashi dama, ban bi ta kai ba naci gaba da tunanin abinda ya dameni kawai, kiran samz ne ya katse min tunanin nawa wanda dama na san zai kira dan ta yuyu ya jima yana kirana amma baya samu,

"Baby...." naji ya fada cikin sanyin murya,

"Sweet...."

"Kin kasa bacci ko?"

"Hmm baccin nan da sauki sweet"

"wallahi baby ni bama baccine matsalata ba, matsalar komai baya yimin dadi ne bana jin dadin gaba daya, dan Allah baby karki bari a rabamu"

"sweet muyi hakuri Insha Allah ba zamu rabu ba, ka kwantar da hankalinka anty tayi min bayanin komai kuma na fahimceta, kaima ka fahimceta amma ka sani idan har ban fika shiga damuwa ba to bana jin kai zaka fini.... Mu kara hakuri sweet muci gaba da addu'a Insha Allah komai zai daidaita.... Kaci abinci?"

" hakane baby amma har yanzu ni dai hankalina ya kasa kwanciya"

"sweet Kaci abinci?"

"uhmmm" tunda naji amsar da ya bani na gane bai ci ba,

"sweet baka ci abinci ba.... Meyasa?"

"baby bana jin dadin komai"

"to kuma shine zaka yiwa kanka horon yunwa sweet? Nifa naci abinci sosai, dan Allah Kaci abinci..... Idan ba haka ba zan kashe wayata ba zaka sake samuna ba"

"kiyi hakuri zan ci, amma matsalar ban san me zan ci ba, ko in hada tea"

"gaskiya banda tea saboda ba abinci bane, shiga kitchen ka dafa noodles Ina jinka..."

"baby yanzun?"

"eh mana, bana son zaman ka da yunwa, ko in kashe wayata?"

"no no baby kar ki kashe bari naje"

Ina jinsa ya fita daga cikin bedroom din ya shiga kitchen, murmushi nayi acikin raina ban bari yaji ba, gas ya kunna ya dora noodles din Ina jinsa yana yi muna hira har ya gama ya zuba a flate yakoma cikin bedroom ya fara ci,

"wow... Baby Kin san dadin da noodles dinnan tayi kuwa?"

"Kaci har dani please..." na fada ina turo baki, haka nayita rarrashinsa har ya gama cin abincin yayi shirin bacci daga nan muka yi sallama bayan na sake kwantar masa da hankali.

Washe gari mommy ta tattara ta koma Kaduna bayan ta yiwa samz kashedin kar ya kuskura ya dawo dani idan kuma hakan ta faru to Allah yasa bata yafe ba dan a cewarta anty tayi mata cin mutuncin da babu wanda ya taba yi mata shi a duniya, ita kuma anty tace bazan koma ba har sai mahaifiyarsa ta sauko daga kan dokin zuciyar da ta hau wannan lamari gaba daya shine ya haifar da matsalar da muke ci nida shi, gashi muna son juna muna kaunar junanmu amma kaddara na neman rabamu, duk da ban rasa komai ba a gidan anty amma zaman hakuri nake yi domin bana jin dadin komai haka kuma babu abinda za ayi min naji dadi, duk yadda naso in daure kar damuwa ta dameni amma na kasa duk da muna gaisawa dashi a waya,

Yau kam tun bayan asuba ya kirani wai baida lafiya zaro ido nayi kamar yana ganina nace,

"sweet me ke damunka? Kasa damuwa a ranka ko?"

"baby wani zazzabi nake yi tun last 2 days, nigh fever ne kuma...."

"ayya sorry sweetheart"

"ba zaki zo ki dubani ba baby?" ya fada bayan yaja wani gwauron numfashi,

"Haba sweet ta yaya zan zo duba ka? Kaima ka san nafi kowa son kasancewa kusa da kai amma babu yanda zanyi..."

"baby kinada yadda zakiyi mana, ada ma muka hadu bare yanzu da muke matsayin mata da miji"

"sweet kayi hakuri Insha Allah zaka samu lafiya amma dan Allah kaje asibiti anjima ayi maka test sai a baka magani"

"uhmmm...." shine kadai amsar da ya bani ya kashe wayar nan naji tausayinsa kuma ya kama ni, da son samune ace yanzu ina can tare dashi ina bashi kulawar da ta dace don zazzabi na mugun wahalar dashi, to ko dai anty zanje in samu in tambayeta ko zata barni inje in duba shi inyaso sai in raka shi asibitin, bari nayi har zuwa lokacin da zata tashi sai inje inyi mata bayani ko zata amince amma gaba daya banda nutsuwa kasa komawa baccin nayi ma har zuwa lokacin da naji fitowar anty,

Tashi nayi na fita nabita cikin kitchen inda take hadawa daddy breakfast,

"Anty ina kwana?"

"lafiya lau widat yakike, Kin tashi lafiya?"

"lafiya lau alhamdulillah.... Dama anty.... Muhammad ne ya kirani yake fada min baida lafiya ko bacci haka ya kwana bai yi ba shine nace ko inje in duboshi...." murmushi naga anty tayi kafin naji tace,

"hmmm yaro kenan, yaro yarone, yaro man kaza, kedai widat ba zaki taba hango abinda nake hango miki ba, Muhammad ai ba karamin yaro bane da har sai an je an kula dashi idan bashi da lafiya, ki kyaleshi insha Allah zai samu lafiya basai kinje ba..."

"to anty" na fada ina kokarin juyawa dan fita, duk wannan bayanin da anty tayi min baisa hankalina ya kwanta ba maimakon haka ma sai tashi da ya kara yi dan inata kiran wayarsa a kashe, kwanciya nayi lamo ina tunani ahaka anty ta shigo ta sameni tayi shirinta tsaf na fita,

"widat bari naje chamber.... Wallahi wani case mai sarkakiya gareni, zanje inyi duba na tsanaki akai dan mun kusa shiga court...."

"to shikenan anty Allah ya dawo dake lafiya ya bada sa'a"

"amin, idan da wani abu ki kirani"

"to shikenan sai kin dawo"

Bayan fitar anty zuciyata shawara tayi ta bani kan inje inga halin da samz yake ciki saboda har yanzu wayar shi a kashe, a gurguje nayi wanka na shirya banyi wata doguwar kwalliya ba na fita dan gidan babu kowa sai iya mai aiki duk yaran sun tafi makaranta kuma basa tasowa sai 6 dan hade da islamiyya ce,

Door bell nayita danna masa kamar babu gobe har yasamu ya taso yazo ya bude min ganin nice sai ya ware ya fara murmushi, "baby.... Please come in" tare muka shiga ina tambayarsa ya saukin jikin nasa ya yake ji a yanzu? "

" baby da sauki amma ba sosai ba "

" kaje hospital din? "

" no "

" to ai kaji problem dinka, dan Allah kaje asibiti "

Daukata yayi cancak ya ajiyeni kan cinyarsa bayan ya zauna kan kujera,

" Nifa ka bari, ko anty bata san na fito ba kawai duba ka zanyi in tafi.... "

" hakanma na gode baby " ya fada yana kissing wuyana,

" Kaci abinci? "

" baby babu abinda naci.... "

"to ba dole kayi rashin lafiya ba sweet, kaki zuwa hospital and kana ta zama da yunwa so kake ulcer ta kamaka kuma?"

"to baby ya zanyi, ana neman raba ni dake"

"babu wanda zai rabamu sweet kama daina fadin haka"

Kitchen na shiga na dafa masa noodles na soya masa ƙwai na kawo masa nice na tayashi ci har ya koshi sannan na yi niyyar tafiya, rike hannuna yayi idanuwansa a narke ni kaina sai da nayi dagaske wurin iya rike hawayen da suka taru a idona nan na fita na barshi na koma, ina zuwa gidan naga motar anty alamar ta dawo,a falo na sameta tana cin abinci,

"Anty ashe kin dawo"

"ehh na shigo aka ce min kin fita, ina kika je?"

Shiru nayi nai tsuru tsuru saboda ban san ƙaryar da zan yi mata ba sannan kuma fadin gaskiyar shima wata matsalar ce,

"widat sai da kika je wurinsa ko? To shikenan tunda kin fi son zaman da kike yi din bari in mayar dake, ki shirya kayanki zuwa anjima sai ki koma..." daga haka ta dauki wayoyinta ta nufi cikin bedroom dinta, hawaye na fara nabi bayanta amma sai bata saurareni ba daga karshe ma tace in fita kar in dameta dan bacci zata yi haka na tashi na fito ina share hawayena kuma har yamma bata fito ba jin alamar dawowar daddy na tashi na fita daga kwancen da nake a dakin islam, wurin daddyn naje nayi masa sannu da zuwa sannna na tsara masa duk yadda muka yi da anty ban boye laifina ba nace dan Allah ya bata hakuri, cewa yayi inje zasuyi magana insha Allah duk yadda suka yi za a kirani, tashi nayi na fita na koma daki na zauna...........



*_Ummi Shatu_*👌🏻
[1/19, 09:54] Maman K: 67


*Ina kuke manyan mata ƴan ƙwalisa ma'abota son gyara da kece raini, maza ku garzayo ku nemi maman Maryam domin samun lafiyayyu kuma haɗaɗɗun Lagos lace wanda zaku iya samun ɗinkakku da kuma sabbi a ledarsu, kaya iya zaɓinki, gefe ɗaya muna da GHT product, zaku samu,*

~MAI DA TSOHUWA YARINYA

~FEMALE CARE

~REODEO

~VIGOR MAX

~ LONGZIT

~B CLEAR

*DUK ZAKU SAMU WADANNAN KAYA CIKIN SAUKI DA RAHUSA MAZA KU NEMI MAMAN MARYAM AKAN WANNAN NO 07080222187, SIYAN NA GARI MAIDA KUƊI GIDA.....*


~~~Bayan fita ta babu jimawa anty ta shiga sashen daddy dauke da abincinsa,

"khadija me ya faru ne ke da ƴar taki?"

"daddy wani abu tace nayi mata?"

"ehh to kusan haka dai gaskiya, dan yanzun nan tabar nan ta fada min duk abinda ya faru.... Tace da alama ranki ya ɓaci"

"to ai dole raina ya baci daddy, duk fa wannan abun da nake yi dan in gyara komai ne a daina kyararta da tsangwamarta amma shine ta debi kafafuwa ta tafi wurinsa....."

"kin san tsakanin mata da miji fa, ni ina ganin kawai idan har gyaran zai zo da tangarda kawai ta koma dakinta"

"dan dai idanuwanka basu gane maka irin tijarar da matar nan tayi bane shiyasa amma da Allah yasa ka gani to da kai da kanka zaka ce widat bata cancanci zama sirikarta ba...."

"haka za ayi hakuri har Allah ya gyara"

Ni dai ina can daki ban san me ake ciki ba sai damuna da Hashim keta faman yi da kira da massages duk da naki kula shi, gajiya nayi da kiran da yake yimin na ɗauka,

"Maimuna dan Allah ki yi hakuri ki saurare ni"

"to wai tayaya zan saurare ka? Na fada maka ni matar aure ce wannan wanne irin jaraba ce?"

"kiyi hakuri ko mintuna biyar ki bani zan zo har inda kike..."

"sai na nemi permission awurin mijina" katse wayar nayi na kira samz, jin ta shiga yasa nayi murmushi araina ina cewa ya bude wayar kenan, ta dan jima tana ringing kafin naji ya dauka,

"Hey baby....."

"Hello boo.... Ya jikin?"

"am feeling better"

"Allah yabaka lafiya"

"amin sweetheart,thank you"

"am dama wani ne wai ke son ganina akwai maganar da zamuyi shine yake son in bashi time zai ganni shine nace sai na nemi permission

Please Login or Register in order to submit comment