Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

wankan sassafe amma ranar na asuba nayi gashi dama ina fashin salla jikina na mulke da madarar turare sannan na shirya cikin doguwar riga kamar yadda na saba dan tashin wuri zamu yi.

Ƙarfe goma daidai na sauka garin Abuja, kamar koda yaushe Anty ce tazo ta ɗaukeni zuwa gidan ta, gidan babu kowa sai mai yi mata aiki da yarinyar dake tayata renon Fawas wacce ake kira da Labiba, tun bayan sauka ta a garin hankalina ya tafi ga Samz domin ban san a wanne hali yake ciki ba, so nake kawai in ganshi inga yanda ya koma, magana nayi wa Anty nace zan tafi duboshi nan ta fara yimin faɗa wai ni na cika gaggawa da rashin ta ido idan nayi haƙuri ma ai nan da ƴan kwanaki ne za a aura min shi in zauna tare dashi a inuwa ɗaya, shiru nayi ban ƙara maganar ba har sai da ta kirani da kanta tace in fito mu tafi bayan ta kammala shirya masa abinci, ina riƙe da Fawas muka tafi me renonshi kuma tana baya,

A Wani ƙaramin asibiti muka tsaya ina biye da anty a baya har cikin asibitin, ɗakin da aka kwantar dashi muka shiga babu kowa awurinsa sai abokinshi kaɗai Ahmad wanda shima bamu sameshi ba ya ɗan fita zai je ya dawo, shi kaɗai ne kwance yana bacci, ganin bacci yake yasa anty juyawa suka koma gida suka barni ni kaɗai, ɗakin nake bi da kallo wanda dama na zaman mutum ɗaya ne saboda bashi da wani girma sai toilet aciki, gefenshi naje na zauna na ɗauko wayata ina dubawa dan rabona da hawa online tun jiya, status ɗin Hashim na buɗe kamar yadda shima yake buɗe nawa duk lokacin da na saka kawai dai magana ce bama yi amma muna ganin status ɗin juna, hotonshi na gani shida wannan farar matar Hajja Sharif a Sharifa wadda a ƙasan hoton nasu ya rubuta Hajjaju nah, murmushi nayi dan ni abin nasu ma dariya yake bani ba haushi ba, kallon gefe na nayi na kalli Samz dake kwance idsnuwanshi lumshe yana bacci araina nace "Ga inda namiji yake...."

Kashe wayar tawa nayi na zuba masa ido ina kallonsa kamar yau ne nafara ganinsa, ya ɗanyi rama kaɗan amma ba wani caan ba sai haske da yayi wanda kana gani ka san ba na daɗi bane, ina nan zaune in kalli can in kalli can naji ya riƙo hannuna, juyawa nayi na kalleshi shi ɗinma ni yake kallo yana yimin murmushi,

"Ka tashi.... Sorry"

"Baby...." ya faɗa yana murza hannuna dake cikin nashi,

"ya jikin"

"Da sauƙi..... Yasu Abba"

"Suna gaishe ka.... Tashi ka ci abinci"

Tashi nayi na zuba masa white rice & stew ɗin da anty ta dafa masa sannan na koma gefen gadon na zauna duk da naga ɗakin ɗauke yake da abubuwa na nau'in kayan ciye ciye da shaye shaye amma hakan bai sa na zubo masa abincin kaɗan ba, filet na ciko masa na zubo masa nama sosai sannan na koma kusa dashi inda yake zaune yana kallo na sanye cikin jeans da t shirt, zama nayi kusa dashi nafara bashi abincin a baki yana ci muna hira a haka har abokinshi ya shigo nan muka gaisa bayan Samz ya gabatar dani a wurin sa, sake fita yayi ya bamu wuri muka cigaba da hira, wayar shi ya kunna ya nuna min hoton gidanmu wanda ya siya mana, suman zaune nayi ina kallon gidan da irin yanda ya haɗu,

"Ni kaɗai zan zauna acan ko?" na tambayeshi cikin tsokana ina gefen jikinshi na kwantar da kaina kan kafaɗarshi shi kuma ya ɗora kansa bisa nawa muna kallon hoton,

"Duk yadda kika ce... Idan ma kince bayan an ɗaura auren baki buƙatar ganina a gidan zan iya dawowa Abuja a ranar in barki Kisha zamanki......"

"uhmm kai ɗin?" na faɗa kaina a ƙasa,

"Ehh ni mana, bazan iya bane?"

"zaka iya...."

Murmushi yayi ya shafi kumatu na batare da yace wani abu ba, har magriba muna tare sai bayan salla sannan anty tazo muka tafi, bayan na koma gidan ma sai da muka yi waya dashi kuma muka jima muna hira yana sanar dani wai irin ɓacin ran da yake shiga duk lokacin da ya ganni da mayafi wai in koma saka hijabi har ƙasa, cike da farin ciki muka yi sallama na kwanta bacci washe gari kam tunda safe na tafi wurin sa dan ni na bashi breakfast ma yaci ganin na zo yasa Ahmad abokinsa ya tafi, tare muka wuni dashi har dare,dan sauƙi kam ya fara samun sauƙi sai dai har yanzu asibitin basu sallameshi ba. Ina da kwana biyar da zuwa aka bashi sallama ya tattara ya koma gida, har gidan muka je tun daga nan kuma bamu sake komawa ba sai dai a waya muke gaisa wa dashi, acan Kano kuwa shirye shiryen karɓar lefe na akeyi dan anty ma har ta tafi tunda safe, zuwa yamma ƙawalli ta kirani a waya ina ɗauka naji tace,

"Amaryar Samz.... Irin wannan uban kaya haka, gaskiya samz ya kashe miki kuɗi"

Video ɗin kayan tayi ta turo min ta WhatsApp nan naga akwati na goma har kit na sha ɗaya su kansu akwatinan sun haɗu ballantana uban kayan da suke ciki, waya yamin yana tambaya ta wai idan akwai abin da bai yimin ba in faɗa sai a canjo min, murmushi nayi nace ni ya rabani da wani maganar kaya yanzu ta lafiyar sa nake, gidan uncle ɗin shi sune suka haɗa komai sannan sune suka kawo kayan da matar uncle ɗin shi Anty siyama da sauran dangin mahaifinshi amma babu dangin mommy ko ƙawayenta ko mutum ɗaya dan gaba ɗaya ta tsame hannunta daga al'amuran da suka shafe shi ga uban rashin arziƙi da take tatawa daddy kullum masifar safe daban ta rana daban ta dare daban abu kaɗan sai tace wai shi ne ya rabata da ɗan ta ya janyeshi kuma wallahi ta ɗauki alwashi ba zata taɓa yafewa ba sai ta ɗauki fansa dan da ta cigaba da ganin irin wannan tashin hankali da ɓacin ran gara Samz ɗin ya mutu kowa ma ya rasa, irin waɗannan kalaman nata sune suke tayarwa da daddy hankali, alla alla yake a ɗaura auren nan a huta dan a yanda yake ganin take taken mommy zata iya aikata komai wurin ganin ta rusa auren nan musamman ma yanzu da ta sake haɗe kai da Madam comfort wanda kullum suke sa ƙafa su fita ba zasu dawo ba sai dare,

Samz kuwa shi da kansa ya gane ƙarfin addu'ace da ikon Allah kawai suka ceceshi shiyasa abun ya tsaya a iya jinya wannan dalilin ne yasa ya sake riƙe addu'a da kyau kullum cikin sake ɗora masa wata nake yi amma ta waya dan tunda aka fara yimin gyaran jiki anty ta ƙi yarda ya ganni ta hanamu haɗuwa dashi kwata kwata duk da ƙishin ruwan ganin juna da muke yi gyara ake yimin na kece raini nabi nayi ɓulɓul dani duk da fargaba bata barina ina cin abinci ina ƙoshi, gashi taƙi barina in koma kano wai sai ana saura kwana uku biki da nayi magana kuma saboda ƴan shirye shirye na sai tace ai ni ƴar gata ce ga ƙawalli na can da Bishra suna yimin komai, a daddafe dai duk na iya zama har kwanakin da ta ɗiba min suka cika, samz kuwa har lokacin bamu haɗu ba sai dai ta waya, gida sun gama duk wani shirye shirye, ranar Litinin muka bar garin Abuja muka nufi Kanon dabo tumbin giwa nida anty da yaran ta gaba daya harda masu yi mata aiki dan ba zata dawo kwana kusa ba sai angama komai na biki ta huta sannan, su a mota suka tafi ni kuma jirgi nabi dan haka na riga su sauka...........✍🏻

*Garin dadi littafin kudi ne ga mai bukatar cigaban labarin sai ya tura 500 ta 0774712835 Aisha Ibrahim Access Bank sai a tura evidence of payment ta wannan no 07044644433 ko a tura katin waya da shaidar biya wannan no 07044644433*



_*Ummi Shatu*_👌🏻
[1/5, 12:43] Maman K: ©️ *HASKE WRITERS ASSOCIATION*
_(Home of expert & perfect Writers)_



*GARIN DAƊI.....!*💍💍



*_NA_*

_*UMMI A'ISHA*_


PAID BOOK #500


*Wattpad:ummishatu*

29

*Ina kuke manyan mata ƴan ƙwalisa ma'abota son gyara da kece raini, maza ku garzayo ku nemi maman Maryam domin samun lafiyayyu kuma haɗaɗɗun Lagos lace wanda zaku iya samun ɗinkakku da kuma sabbi a ledarsu, kaya iya zaɓinki, gefe ɗaya muna da GHT product, zaku samu,*

~MAI DA TSOHUWA YARINYA

~FEMALE CARE

~REODEO

~VIGOR MAX

~ LONGZIT

~B CLEAR

*DUK ZAKU SAMU WADANNAN KAYA CIKIN SAUKI DA RAHUSA MAZA KU NEMI MAMAN MARYAM AKAN WANNAN NO 07080222187, SIYAN NA GARI MAIDA KUƊI GIDA.....*

~~~Cikin farin ciki da ɗoki nake shaƙar iskar garina kuma tushena wato Kanon dabo tarin Allah, sai murna nake yi wadda ban san ko ta mecece ba amma ni dai na san ba murnar aure bace,

Lokacin da naje gida tun daga ƙofar gida na san anyi gyara na musamman a gidan domin gashi nan ya sha sabon fenti ko ina an gyareshi tsaf, ƙawalli tana gidan dan haka rungume juna muka yi muna tsalle yaya Abdul Hakim da fitowarsa kenan daga sashen Annie ya bimu da harara wadda ba mu san ma yana yi ba, sakina tayi tana ƙare min kallo sakamakon canjawar da nayi nai ƙiba da haske saboda supplements din da Anty ke bani na gyaran jiki da sauran abubuwa ita kanta bata san yawan kuɗin da ta kashe ba wurin gyara ni tun daga kan su dilke, magungunan infection, na gyara fata da dai sauran su,

"Tabdijam...... Samz zai kwashi lagwada...." ta faɗa a hankali ta yadda wani ba zai jiyo ta ba, harararta nayi nace "ya ranki"


"Wataƙila daren ranar da aka kaiki ki samu ciki ƙawalli....."

"Ta Allah ba taki ba ƙawalli......insha Allah sai bayan shekara biyu zan haihu"

"a wannan samz ɗin naki zaki kai shekara biyu baki haihu ba?"

Kallon yanda ta riƙe haɓa kamar wata tsohuwa nayi dariya nayi nai gaba abina ta biyo baya na, gani nayi gaba ɗaya ƴan gidanmu sun zama busy dan ban samu mama agida ba wai sun fita kasuwa ita da Anty Salaha sai iya Annie kaɗai da sauran abokan arziƙi wadanda suka zo ganin kaya dan har yau ba agama zuwa kallo ba, ni dai ko ta kan kayan ban bi ba sai wadanda aka dinko min su na dudduba ciki harda wanda zanyi fitar biki dasu na kamu da dinner, ƙawalli ke tsara yanda shigar tawa zata kasance, ni dai duk jikina yayi la'asar da ganin dagaske gidan zan bari in tafi gidan samz ada babu abin da nake so irin maganar aure na dashi amma ahalin yanzu idan ƙawalli tayi min faɗa ma muke yi ita kuma tunda ta gane shikenan bata da aiki sai tsokana ta, gaba ɗaya ji nake auren ya fice min arai kamar a sake ƙara watanni amma na san hakan ba zata taɓa faruwa ba, ƙawalli na kalla dake ta haɗa min kaya na wuri ɗaya ina daure da towel da hijabi a jikina fitowata kenan daga wanka,

"yaushe angon zai shigo ne?"

"oho masa ni na sani ne" na bata amsa ina ƙokarin zama gefen gado, dariya naji ta fashe da ita,

"ohh Allah me iko wai ashe dama zanga widat haka? Ashe wannan ranar zata zo da zata rinƙa jin tsoron Samz"

"Wallahi ji nake inama a ɗaga....." na faɗa ƙwalla na taruwa acikin idanuwa na dan duk da ina sonsa yanzu ji nake bana son haɗuwarmu kwana kusa balle har mu zauna inuwa ɗaya,

"ai idan aka ɗaga ina jin sai an baki gado a asibiti.... Mutumin da kike ta jinya a kansa yanzu kuma kice wai so kike a ɗaga...."

Ban sake tanka mata ba kawai na fara kuka, lallashi na ta fara tana cemin to kuma menene abin kuka har itama ta fara a haka anty ta shigo ta same mu,

" kin jimin yara da shashanci kunzo kun zauna kun ƙule a ɗaki kuna kuka kamar waɗanda aka yiwa mutuwa.... Dan Allah ni karku ɓata min lokaci ungo ku zaɓa....."

Wayarta ta miƙo mana, decorations ne kala kala take son mu zaɓi kalar wanda za ayi, ƙawalli ce ta zaɓi wani kamar na gargajiya gargajiya amma yayi bala'in kyau, karɓa anty tayi tana cewa,

" Ranar kamun wanne kaya ma zata saka? Ungo ku zaɓi na dinner "

"Golden ne Anty" ƙawalli ta bata amsa, sake zaɓar na dinner ɗin tayi ta miƙa mata wayarta ta fice ta barmu kamar yadda tazo ta same mu, kafin kace mi har magriba tayi wanda hakan ke sake tada min da hankali,

Bayan tafiyar ƙawalli ɗakin mama naje muka zauna tana ta haɗa kan kayan da ta siyo na amfanin kitchen wanda za a tafi dasu jere gobe laraba ranar Alhamis za ayi kamu juma'a dinner asabar kuma za a ɗaura aure ayi yini akai amarya ɗakinta, duk ji nake kamar inyita kuka har sai an fasa bikin nan yanzu Ala basshi nan gaba sai ayi, shi kansa samz ɗin yanzu bana doguwar hira dashi dan gaba ɗaya haushinsa nake ji daga ya kirani zan tambayi menene sannan ina gama bashi amsa zan kashe wayata, ba wai laifi yayi min ko daina sonshi nayi ba a'a haka kawai nake jin bana son kusancinmu dashi, duk da hakan da nake yi masa shi baya zuciya ya kan kirani kamar yadda ya saba, dan ko yanzu da na zo kwanciya saida ya kirani amma nace bacci nake ji, cewa yayi to shikenan in kwanta in yi, kashe wayar nayi gaba ɗaya ina ta juye juye nama kasa baccin gaba ɗaya, daga ƙarshe hijabi na nasa na fita, sashen Annie na shiga na buɗe ɗakin bishra wacce ke kwance tana bacci sakamakon zirga zirgar da itama tasha yau, kusa da ita naje na kwanta naja bargo na lulluɓa sai hawaye, na jima ina zubar da hawaye kafin bacci ya ɗauke ni wanda bani na tashi ba sai bayan asuba irin ƙarfe 6 ɗin nan wannan ɗinma anty ce ta shigo da ban san ranar tashin mu ba daga ni har Bishran, ɗakina na koma nayi wanka a gurguje bayan nayi salla, sama sama nayi breakfast sannan na tafi gidan ƙunshi nida Anty wadda tayi dropping ɗina sannan ta wuce kasuwa ta can kuma zata wuce gidana, sai bayan da aka gama min ƙunshin sannan ƙawalli ta sameni a gidan,

"Rangaɗi.... Amarya komai naki na dabanne... Gidanki mai kyau wallahi...."

Shiru nayi mata dan bana son jin zancen gidan nan hankalina tashi yake idan naji an ambaceshi, ƙunshin aka yi mata itama amma iya baƙi saɓanin nawa da aka haɗa harda ja na seletif, bayan azahar muka bar gidan ƙunshin muka koma gida yau dai nafi ganin gudun yinin fiye da na kowacce rana dan kafin ƙiftawa da bismillah har magriba sunyi kuma sai lokacin ƴan jere suka dawo kowa yana santin gidana, daren ranar kasa bacci nayi dan haka na tashi na koma cikin su Anty waɗanda ke falon mama suna aiki, kan dugowar kujera na kwanta anan nai bacci dandanan kuma naji gari ya waye kuma a ranar aka fara gudanar da biki, shi dai ango bai zo ba yace sai ranar Juma'a zai dira wanda ni hakan ma yafi min.

Tunda garin Allah ya waye bayan na dawo daga gyaran gashi ake kwaskware ni ana sake kwatalle ni dan wata me gyaran jiki ta musamman Anty ta kirawo wacce tazo ta sake gyara min fatata gyaran da yafi na baya sannan ta turare min jikina da wani turare wanda ya sha haɗi na musamman nan take fatata ta kama ƙamshin gam ta riƙe sai zuwa yamma na samu kaina hannun matar nan bayan ta sakani nayi wanka da wani ruwan turare, me kwalliya ce ta zo itama ta fara nata aikin babu jimawa kamanni na suka canja na tashi daga widat ɗin da aka sani na koma kamar wata balarabiya ko ƴar India, kayana milk colour ne amma an sirka da golden haka takalmi da yar jakar da na riƙe da gwaggoro na duk golden, sai bayan da aka gama ɗaukata hotuna sannan aka sakani a mota muka nufi wurin kamu dan Anty sai waya take iyowa wai mutane suna jirana, faɗin irin kyawun da nayi da irin kuɗin da aka kashe ɓata bakine da ɓata lokaci, anci an sha haka kuma an sha hotuna, dangin ango suma sun zo matar uncle ɗinshi Anty Amina da wasu mata su biyar sai bayan da aka gama kamu sannan suka tafi, duk na gama gajiya da zaman nan da tashi, bamu muka bar hall ɗinnan ba sai 8 saura shiyasa a mutuƙar gajiye na koma gida, ranar kam da wuri nayi bacci. Washe gari ango ya baƙunci Kano dan tun 1 ya kirani yake sanar dani ya sauka shida abokinsa Ahmad dan anan ma suka yi sallar juma'a, kamar jiya yauma wuni aka yi ana hidimtawa fatata har tsawon wani lokaci ga uban ƙamshi da ake manna mata babu ƙaƙƙautawa, tun kafin magriba na isa gidan kwalliya nida ƙawalli amma can ta tafi ta barni, har bayan ishah aka kai ana yimin kwalliya salla ce kaɗai ke tadani, kwalliyar yau ai har tafi ta jiya kyau da matsayi domin yau ne na fito a asalin bride, ƙamshi kuwa ai ba a ma magana dan ta ko ina tashi yake, misalin ƙarfe 8 daidai suka zo ɗaukata, babu kowa atare dasu daga shi sai abokinsa, komai nawa blue sai ɗan ratsin silver kaɗan saboda takalmi na da pose ɗina duk silver colour ne da sarka da earrings harda zobuna da agogo duk silver, a hankali nake tafiya saboda tsinin takalmin ƙafata gashi rigar ta baya tana jan ƙasa, ganin ina ƙoƙarin fitowa ya buɗe motar ya fito sai lokacin na ganshi bayan tsawon kwanaki rabona da shi, shima blue ɗin shadda ya saka mai kyau da tsada harda hula itama blue dama ba ƙaramin kyau manyan kayan ke yi masa ba to kyawun yau har yafi na kullum,

"Baby...." yace dani bayan ya ƙaraso kusa dani,

"zo ka riƙe min rigata ta baya dan Allah"

Matsowa yayi dab dani nan muka shaƙi ƙamshin juna,

"why not in ɗauke ki maimakon riƙe miki riga ai kamar zai fi ko...."

Tun kafin in bashi amsa naji ya tarairaye ni ya ɗaukenin zuwa inda motar su take, bani da zaɓi illa in lafe cikin jikinsa,

"Ya biki? Kin gaji ko?"

Kai na ɗaga masa cikin shagwaɓa ina ɓata fuska kamar zanyi kuka,

"Ayya... Am soo sorry baby"


"Ahmad buɗe mana ƙofar nan pls"

Sai lokacin naji kunya ta kama ni da naga abokin shi ya fito ya buɗe mana ƙofar baya, ji nayi kamar inye me dan kunya, sakani yayi ya rufe ƙofar sannan ya zagayo ta ɗaya ɓarin shima ya shigo, hannuwana ya kamo cikin nasa masu mutuƙar ɗumi da laushi wannan dalilinne yasa sau tari idan ya riƙe hannuna bana iya ƙwacewa hannunshi is very soft and warm, jana jikinshi yayi yana raɗa min,

"matso muyi sirri kar Ahmad yaji mu..."

Banyi magana ba illa kallon fuskar shi da nayi wadda tasha gyara tun daga sajenshi zuwa gemunsa, rungume ni yayi sosai a jikinsa yana yimin raɗa,

"kinyi kyau baby.... You look... Just amazing..... Let me snap u" ya faɗa yana ciro iPhone ɗinshi daga aljihu ya ɗaukeni sannan yayi mana nida shi,

"kaima kayi kyau" na faɗa murya ta na rawa, hannunnshi ɗaya na riƙe da nawa ɗayan kuma na gadon bayana yana wasa da zip ɗin rigata cikin wayo da dabara yake sauke zip ɗin bai san duk ina ankare dashi ba, wuya na zai yiwa kiss na yi saurin toshe bakin sa da hannu na, da ido yake tambaya ta wai why? Raɗa masa nayi,

"Zaka karya alƙawarinmu.... We promised ourselves sai bayan munyi aure"

Kanshi ya ɗaga sama sannan ya ƙwace bakin sa daga tsohewar da hannu na yayi masa,

"amma ai ba zaki hanani wannan ba...." ya faɗa yana sauke zip ɗin rigata a hankali ta yadda Ahmad ba zai ji mu ba,

"ni dai a'a wallahi... Is part of our promised" na faɗa ina riƙe hannunsa,

"Oh my God..." ya faɗa yana kallo na da shanyanyun idanuwansa wanda yau suka fi kullum shanyewa, saukar da nawa nayi ƙasa daga cikin nasa, gadon baya na yake shafawa yana faɗin,

"please baby....."

"Naƙi wayon" na faɗa cikin raina ina maƙale masa kafaɗa, duk yadda yaso ya min wayo ƙin yarda nayi sai wani marairaicewa yake yi yana lumshe min ido amma naƙi furr tunda har yanzu ba a ɗaura mana aure ba sai zuwa gobe, ƙyaleni yayi kuma yayi shiru ya daina roƙo na may be fushi yayi wanda sam hakan bai ɗaɗani da ƙasa ba, kuma duk da ya daina kulani hakan bai sa na bar jikinsa ba dan kamar mage haka nake idan na samu jikinsa, kaina kan kafaɗarsa na zagayeshi da hannuwana duka biyu na maƙale, bai ƙara kulani ba sai hirarsu da suke yi shida abokinsa da kuma waya da yake amsawa jifa jifa a haka har muka ƙarasa event center ɗin da dandazon ƴan uwa da abokan arziƙi keta dakon zuwan mu..........✍🏻


*Garin dadi littafin kudi ne ga mai bukatar cigaban labarin sai ya tura 500 ta 0774712835 Aisha Ibrahim Access Bank sai a tura evidence of payment ta wannan no 07044644433 ko a tura katin waya da shaidar biya wannan no 07044644433*


_*Ummi Shatu*_👌🏻
[1/5, 12:43] Maman K: ©️ *HASKE WRITERS ASSOCIATION*
_(Home of expert & perfect Writers)_


*GARIN DAƊI.....!*💍💍


*_NA_*

*_UMMI A'ISHA_*


PAID BOOK #500


*Wattpad:ummishatu*

30

*Ina kuke manyan mata ƴan ƙwalisa ma'abota son gyara da kece raini, maza ku garzayo ku nemi maman Maryam domin samun lafiyayyu kuma haɗaɗɗun Lagos lace wanda zaku iya samun ɗinkakku da kuma sabbi a ledarsu, kaya iya zaɓinki, gefe ɗaya muna da GHT product, zaku samu,*

~MAI DA TSOHUWA YARINYA

~FEMALE CARE

~REODEO

~VIGOR MAX

~ LONGZIT

~B CLEAR

*DUK ZAKU SAMU WADANNAN KAYA CIKIN SAUKI DA RAHUSA MAZA KU NEMI MAMAN MARYAM AKAN WANNAN NO 07080222187, SIYAN NA GARI MAIDA KUƊI GIDA.....*

~~~Wani farin ciki ne ke faman ɗawainiya dani ina jin rayuwata da gangar jikina kamar tana tafiya akan iska, da zarar na tuna cewa nida samz gobe zamu zama ma'aurata kuma mallakin juna sai inji ƙafafuwana tamkar baza su iya ɗaukana ba saboda tsantsar shauƙi da tsananin ɗoki,

Hannayena na saka na sake maƙale shi bayan na ɗaga idanuwana ina kallon fuskarsa, zaune nake gefenshi amma ina cikin jikinsa nasa hannaye na zagaye shi kaina bisa kafaɗarsa, wata irin zazzafar soyayyarsa nake ji wadda ban taɓa jiba dan ji nake kamar zan koma cikin cikinsa dan so, kallo na shima yayi muka haɗa ido,

"ni kika yima rowa ko?" ya faɗa yana ɗan cije lips ɗin shi na ƙasa, farrr nayi masa da idanuwa na kafin nayi masa gwalo, goshinsa ya haɗa da nawa sannan ya bani amsa da,

"zan rama ne.... Ki gama naki iya yau kaɗai gareki.... Ni kuwa daga gobe nawa turn ɗin zai fara..... Zaki yi bayani"

Shagwaɓe fuska nayi na sake narkewa acikin jikinsa,

"nidai a'a"

"nima a'a" ya faɗa cikin kwaikwayon muryata, dariya muka yi gaba ɗaya daga ni har shi,

"ɗan gyara min zip ɗin rigata...." nace dashi jin alamun mun ƙaraso event center ɗin,saida ya turo baki kamar yadda nake yi masa sannan ya zuge min zip ɗin yana hararata cikin shauƙin so,ƴar pose ɗita ya buɗe ya ƙara min kuɗi ƴan ɗari biyar biyar sabbi fil wanda ya ciro daga cikin aljihunsa.

A tare muka jera bayan mun fito daga cikin hall ɗin muna riƙe da hannun juna kuma tun daga nan aka fara haskamu da camera, haske kake gani ko ta ina an zagaye mu ana yimana hotuna,

"Masha Allah.... My favorite couple" ƙawalli ta faɗa bayan ta tsaya kusa dani dan a ɗauke mu tare, mun jima awaje kafin aka yi mana jagora zuwa ciki kuma har lokacin hannuna yana saƙale cikin nasa, har wurin zaman mu aka rakamu sannan aka fara gabatar da abubuwan, addu'a aka fara yi daga nan aka yi

Please Login or Register in order to submit comment