You Cannot Download this book untill you login but you can read it .
Login Register
ko ba zaki dawo bane?" hakan da naji sai kawai na ajiye kayan sai iya abinda zan buƙata acan kawai na ɗauka sai kuma kayan baby da na diddiba dama kusan komai guda biyu nake siya saboda ita, shi kam kudi yasaka min a account ɗina wai idan naje na ƙara siyama baby kaya before yazo,
Sai da aka yi haihuwar da kwana biyu za a shiga na uku sannan ya sama min ticket saboda yanzu ba a fiya zirga zirga sosai ba saboda canje canje da aka samu na yanayin rayuwa, kullum sai munyi video call da ƙawalli naga babyn wanda har anyi masa huɗuba da sunan Abbanmu amma za a ringa kiran shi da Irfan wannan sunan dama tun kafin ƙawalli tayi aure take riƙe dashi a ranta wai shi zata sakawa ɗanta shiyasa tana faɗa min nace to Alhamdulillah su ƙawalli buri ya cika,
Tamkar idan na tafi bazan dawo ba haka samz ya zame min duk yabi ya hanani sukuni sai jagwalgwala ni yake saboda gobe jirgin safe zan bi kusan bai barni nayi baccin kirki ba yanzu naga wani tashen jaraba yake koda yake dama tun farko kusan hakan yake kuma da haka ya horani nima, yau dai sai da ya gama tara min gajiya sannan ya barni shiyasa da bacci a idona sosai na isa Kano,
Kai tsaye gidana na wuce na sauka ai kam gida kamar na shekara bana nan dan ko ina ya haɗa datti ya fita kamanninsa, mai gadi na yana nan yana kula da duk inda ya kamata kuma duk karshen wata samz yana biyansa albashinsa, iya inda zan iya gyarawa kawai na dan karkade na goge sauran na bari sai an nutsu, wayata na kunna na kirashi video call,
"baby, i miss you..."
"I miss you too my love, kaga gidana yadda yayi datti?"
"haka zaki zauna cikin datti?"
"a'a zanje gidan ƙawalli acan zan kwana sai bayan suna sai in koma gida inyi kwana biyu sannan sai in dawo kaga kafin lokacin na turo an gyara min..."
"to shikenan baby.... Allah ya kiyaye, i love you"
"I love you too...."
Sallama muka yi na tashi na tattara duk abinda zan tattara cikin madaidaicin akwati sannan na kai motata wadda ke rufe sai yanzu nasa aka bude min aka gyara, gidan ƙawalli na nufa batare na sanar mata ba nafi son kawai sai dai ta ganni, ai kuwa lokacin da na isa gidan cike yake da dangi yan gidanmu da yan gidansu wai har su bishra da suka fini nisa sun rigani zuwa ganina yasa gidan ya rude da murna kowa sai tsiya yake yimin saboda ba kowa ya san inada ciki ba. Ai tsokana na shata awurin yan gidanmu dan har maza ba iya mata ba shi yaya Abdul hakim lokacin da ya ganni ma cewa yayi wai,
"wa nake gani wannan kamar zata fashe?" kowa sai da yayi dariya banda ni wacce ta turo baki kamar zanyi kuka, bamu samu keɓewa da ƙawalli ba sai bayan sallar ishah lokacin kusan kowa ya tafi sai iya bishra da kanwar ƙawalli Kubrah sai kakarsu gwaggo, nidai ina ɗakin mai jego acan na sauka sai lokacin take bani labarin haihuwa duk sai na ji na tsure dan tace min anyi mata ɗinki yafi a ƙirga shiyasa naga tana ta tafiya daƙyar, har 9 ta wuce hirar da muketa yi kenan wato ita mace dai komai sai ta sha wahala ko an haihu lafiya rainon ɗan ma babu sauƙi sai dai Allah yasa mu dace kawai, kasancewar akwai bacci a idona wanka nayi nazo na saka rigar bacci ina shirin kwanciya kiran samz yana shigowa dariya naji ƙawalli tana yi tare da faɗin "ashe dai har yanzu kuna nan da wannan shegen ƙulafucin junan keda wannan mijin naki"
Ban kulata ba na ɗauki wayar ina ce masa "am sorry Bae ban manta da kai ba yanzu nake son in kiraka nima, bacci nake ji..."
"bacci tun yanzu baby...."
"ba jiya ka hanani bacci ba...." na fada ina turo baki, dariya naji yayi kafin ya fara rarrashi na nikam na samu abinda nake so nan nayita zuba masa shagwaba bayan na hadasu da ƙawalli sun gaisa yayi mata barka ita kuma tayi godiyar kayayyakin da muka kawo, wallahi dakyar na iya bacci daren yau saboda na saba koda yaushe sai yayi min tausa ya matsa min jikina kafin nayi bacci..........
*Garin dadi littafin kudi ne ga mai bukatar cigaban labarin sai ya tura 500 ta 0774712835 Aisha Ibrahim Access Bank sai a tura evidence of payment ta wannan no 07044644433 ko a tura katin waya da shaidar biya wannan no 07044644433*
*_Ummi Shatu_*👌🏻
[1/5, 12:43] Maman K: G*D
*Ina kuke manyan mata ƴan ƙwalisa ma'abota son gyara da kece raini, maza ku garzayo ku nemi maman Maryam domin samun lafiyayyu kuma haɗaɗɗun Lagos lace wanda zaku iya samun ɗinkakku da kuma sabbi a ledarsu, kaya iya zaɓinki, gefe ɗaya muna da GHT product, zaku samu,*
~MAI DA TSOHUWA YARINYA
~FEMALE CARE
~REODEO
~VIGOR MAX
~ LONGZIT
~B CLEAR
*DUK ZAKU SAMU WADANNAN KAYA CIKIN SAUKI DA RAHUSA MAZA KU NEMI MAMAN MARYAM AKAN WANNAN NO 07080222187, SIYAN NA GARI MAIDA KUƊI GIDA.....*
{42}
~~~Lafiya lau na kwanta amma tun cikin dare nake jin ciwon kai da zazzabi sama sama yana rufeni banda uban tashin zuciya da ya sarƙafemin zuciya dan kadan kadan nake jin amai yana taso min amma dai ban tashi ba, juyawa nayi na kalleshi inda yake bayana a kwance sai dai amma ya kanainaye ni gaba ɗaya cikin jikinsa, a hankali na soma ƙoƙarin zamewa daga jikin nasa ina son tashi dan bakina ya soma cika da yawu,motsin hakan da yaji shine ya tashe shi daga baccin da yayi nisa aciki,
"Baby menene?"
Yamutsa fuska nayi kafin nace "babu komai ina son shiga toilet ne..."
"baby jikinki da zafi..... Fever ne?"
"ehh.... Harda ciwon kai"
"ayya sorry, muje idan kin dawo sai Kisha paracetamol"
Shine ya taimaka min na shiga bathroom din amma kuma na kasa yin aman sai yunkuri dai nake ta yi daga karshe dole haka ya daukoni ya dawo dani ya kwantar dani tare da lullubata dan sanyi nake ji sosai gashi kaina kamar zai fashe dan ciwo haka bakina jinsa nake kwata kwata babu dandano har wani ɗaci ɗaci yake yi. Da wannan zazzabin na kwana dan bai sakeni ba sai bayan asubah kuma sai lokacin na iya tashi nayi salla sannan na sake kwanciya shi kam sai faman sannu yake yi min yana tambayar ya nake ji,
"jiri nake ji sosai kamar zan fadi kuma bakina ɗaci sannan duk jikina babu ƙarfi"
"am sorry baby.... Allah ya baki lafiya,za muje hospital anjima" ɗaga masa kai kawai nayi kafin na lumshe idanuwana, duk da a bukace yake dani amma sai ya hakura zuwa 11 muka shirya bayan ya kira abokinsa ahmad wanda shine yazo ya kai mu a motarshi, duk yanda nake ji da abubuwan dake damuna na zayyanewa Dr nan aka rubuta min drugs bayan tests da na yiyyi, tun a hanya nake fada masa abinda nake sha'awar ci wato alalan gwangwani kuma wanda aka saka manja ba man gyada ba, murmushi yayi yana rungume dani muna zaune abaya yace,
"baby yau kuma yar moimoi ce.... An bar maganar waina?" kai na ɗaga masa ina sake shinshinarsa saboda dadin da turarensa ke yi min, hannuna daya dake cikin nasa ya murza yai kissing yace da Ahmad dan Allah ya fara biyawa restaurant kafin ya saukemu a gida, take away ya iyo min na alalan sannan ya dawo, daurewa nayi har muka isa gida sannan ya bude abincin ya bani naci sai da na gama sannan ya fita office, yana hanyar office din baima karasa ba naji yana kirana a waya, dakyar na daga saboda baccin da nake ji, ina ajiye wayarshi itama anty salaha ta kirani nan na daga bayan mun gaisa nace mata zan kirata an jima dan yanzu baccin dake idona bazai barni in fahimci komai.
Wuni nayi ina bacci dan ko sallar azahar ban yiba sai 3 da na tashi bayan na idar da salla wanka nayi duk da har lokacin bana jin karfin jikina sosai, cire wayata daga flight mood nayi na kira anty salaha muka gaisa muka dan taba hira sannan muka yi sallama, ahakan na daure na shiga kitchen saboda Dr yace in dan rinka motsa jikina,
White rice na dafa mana sai stew din kifi duk da na san ba wai lallai ni din inci ba, ina cikin kitchen Ina soya miyar ya dawo, ganina a kitchen Ina aiki ya sakashi ɗan bata face ya kalleni yana hararata cikin wasa,
"baby bakya jin magana ko? Why all this?"
"sweet ba kana ji dr yace kar in rinka zama wuri daya ba, irinka yin aiki ko babu yawa ba...."
Matsowa yayi ta bayana ya rungume ni yana shafa cikina,
"to amma baby you should wait until you recovered...."
"no.... Na fada maka na gaji da ganinka kana cin abincin restaurant...."
"You no want peace baby...." yace dani yana kissing wuyana da kuncina,
Tare muka karasa girkin sannan muka tarkata muka koma falo kuma tun bayan dawowarsa bai sake fita ba muna tare manne da juna musamman ma ni dan yanda nake manne masa kamar wata cingam haka zan ta lafe masa a jiki kamar wata mage amma bawan Allah bai taɓa gajiyawa ba ko ya nuna alamar yana son in dan bashi space, Felicia kuwa duk da baya daukar kiran nata bata hakura ba maimakon haka ma ai sai canja no da tayi ta kirashi kwata kwata bai kawo cewa ita bace dan ko true caller bata nuna masa sunanta ba,
Ina kwance na bararraje a jikinsa ina kallon cartoon a MBC 3 ta kirashi, bana jiyo abinda take cewa amma shi ina jin amsar da yake bata, da farko ma kashewa yaso yayi amma sai ta tayi saurin fara rokonshi hakan yasa ya tsaya yana jiran yaji gudun ruwanta,
"Samz am very sorry for what I did...... Am very sorry pls, na san na ɓata maka rai kuma na batawa matarka but hakan bazai sake faruwa ba, I promise you"
"look Felicia, wannan kiran da kike yimin bana sonshi, kin san ina da mata, akan me zaki rinka kirana cikin dare? Duk abubuwan da kika yi abaya bai isheki ba? Kin yi niyyar batawa matata rayuwa, kin hadani da mahaifiyata tayaya kike expecting zan so ki?"
"Haba samz..... I said am sorry, please and please"
"Is ok, shikenan?"
"ina son ganinka..."
"wannan kuma bazan yi miki alkawari ba saboda bama zai yuyu ba"
"please samz..."
Jin magiyar bata ƙare ba yasa shi kashe wayar yana kallona, duk da ina jin duk abinda ya fada amma sai nayi kamar hankali na ba akan shi yake ba saboda karma ya zargi ko raina ya ɓaci,
"baby...."
"sweet...." na amsa ina sake shigewa cikin jikinsa tare da kokarin kai bakina kan nashi, karɓa yayi yana goga hancinsa kan nawa muna yiwa juna murmushi,
"hope dai ban bata miki rai ba..... Felicia ce take ta damuna da kir....."
"dan Allah kabar wannan maganar ni raina bai baci ba.... Bama na son maganar please...." na fada ina lasar lips ɗinsa da harshena, shima biye min yayi yana ramawa idan na lasar masa lips shima sai ya lashi nawa, idan na cijeshi a lips dinsa na sama ko na kasa sai shima ya rama haka muka yita yi har sai da lokacin sallar ishah ya so kure mana dan dama duk lokacin da muke yin irin wasannin nan bama ji bare gani.
Tsawon kwanaki biyu na shafe ina fama da wannan nacaccen zazzabin mai nacin tsiya wanda kusan duk dare dashi nake kwana ga jiri da ciwon kai gefe daya kuma gaba daya bakina baba jin dandanon komai haka yake salam duk da ina fama da kwadayi kwadayi banda tashin zuciya da yake saka yawu yaita taruwar min a baki nida shi yanzu bamu da wani abunyi sai shafe shafen cikina ko fita zai yi ba zai yi min sallama ni kadai ba sai ya hada da cikin shima yayi masa tasa sallamar ta musamman ta hanyar shafa shi wani lokacin harda sunbatarsa yake yi,
Ni dai yau tun bayan fitarsa ma a kwance na wuni sai zuwa yamma bayan mun gama waya dasu mama naji babu abinda nake sha'awar ci irin wainar fulawa to amma matsalar idan ni nayi bafa lallai in iya ciba shiyasa na bari sai ya dawo, wurin ƙarfe 5 da wani abu ya dawo ina zaune falo nasha kwalliyata cikin milk color din riga iya gwiwa mai siririn hannu marar kauri haka kuma ta ɗan kamani kadan saboda kumarin da na kara yi,
"my love...." ya fada yana hadani da jikinsa,
"sannu da zuwa sweet...."
Ni da kaina na hada masa komai bayan na sanar dashi wainar fulawar da zai yi min, tare muka shiga kitchen din ina nuna masa yadda zai yi da haka dai ya soya wata ta dagargaje wata kuma tayi min yadda nake so, bayan ya gama muka dawo falo na haye cinyarsa muka ci tare,
"sweet ya maganar da muka yi na zuwanka Kaduna?"
"baby ai gani nayi baki da lafiya and kuma bana son tafiya ma na barki ke daya...."
"nifa naji sauki my love, goben dai kaje ko dan ka bawa mommy hakuri..."
Shuru ya ɗanyi na wani lokaci kafin yace "baby ki bari ki kara samun lafiya sai inje"
"ni na samu lafiya, kaje tunda bawai kwana zaka yi ba"
"akan me ba zan kwana ba?" ya fada kamar gaske amma na san kawai tsokana ta yake yi,
"saboda muna bukatarka mana"
"ban yarda ba, bayan kwana biyu rowa kike yi min...."
"Nifa bani da lafiya" na fada cikin shagwaba ina turo masa baki,
"ina binki bashi ai, zaki biya one by one..."
Haka dai na samu na lallaɓashi washe gari yayi sammakon tafiya kadunan bayan na sha dogon hugging kamar babu gobe dan ya jima manne dani kafin ya hakura ya tafi ni dai ni kaina ban san wanne irin so muke yiwa juna nida mijina ba gashi sam bama gajiya da juna idan yana gida muna manne da juna idan baya nan muna manne awaya kuma tun ada ahaka muke har yanzu babu abinda ya canja maimakon ya ragu ma abin ƙara gaba yake.
Lokacin da ya isa Kaduna sun jima tare da daddy suna tattaunawa amma bawai akan mommy bane duk da dai daga baya daddyn sai da yayi complain akanta kamar yadda ya saba dan gaba daya zaman hakuri yake da ita gashi shi damuwarsa yaranta mata ne baya son ta ɗorasu kan wannan halayyar tata suje gidan mazaje ana samun matsala amma ita sam taki fahimtarsa bare ta gyara, hakuri kawai samz yake bashi dan idan ba hakurin ba babu yadda za ayi da mommy, ina kitchen ya kirani ya hadani da daddy muka gaisa sannan muka yi sallama wannan karon babu kisses babu i love you saboda daddy yana nan, daga wurin daddy ciki yakarasa wurinsu mommy daga mommy sai mary saboda Hadiza ta koma school shima Abdallah haka, yanda mommyn ke fushi dashi suma su Mary haka wannan dalilin ne ma yasa ko gaishe shi bata yi ba tana zaune tana kallonsa abinda ya bata masa rai kenan har yayi mata kaca kaca yace kuma tsaf zai zaneta idan ta kawo masa raini hakuri ta bashi kafin ta tashi ta basu wuri, kujerar dake kallon mommy anan ya zauna ya gaidata ta amsa babu yabo babu fallasa dan duk da ɓacin ran da take ciki da fushin da take yi dashi zuwansa yasa taji dan sauki har ta dan sauko,
"mommy na zo ne in baki hakuri akan abunda ya faru, kiyi hakuri ki yafe min sannan kiyi hakuri ki karbi matata a matsayin surukarki saboda wallahi bata da wata matsala, duk abinda ake nema wurin macen kwarai tana dashi.... Tana kyautata min tana kulawa da duk wasu hakkoki nawa..... "
" kai din dai da kazo in yafe maka to na yafe maka amma kar ka sake sako min zancen matarka anan Samuel.... Bana kaunarta kuma bana jin zan ƙaunace ta har abada, ai dama tun farko saida na gargadeka amma ka toshe kunnuwanka, kaje kayi gaban kanka, to wallahi mutukar kana son farin cikina da albarkata sai ka rabu da wannan yarinyar, ka saketa ta koma gidan iyayenta..... "
" mommy wallahi bana son inji kina irin wannan maganar, saboda me zan saki matata? "
" saboda bata dace da kai ba, ni na haifeka kuma ni nafi kowa sanin abinda ya dace da kai....."
Duk yadda yaso ya fahimtar da mommy ta rufe idanuwanta taki fahimta ganin haka ya sanyashi tashi domin tafiya saboda yaga bambamin fadan da take ta faman yi ba mai karewa bane, cikin bacin rai tace,
" Samuel what are you trying to do? Ni mahaifiyarka ina yi maka magana zaka tashi ka fita? Nima har ta kai ta nuna maka bani da muhimmanci agareka?"
"mommy ba haka bane kawai naga maganar taki karewa ne kullum magana daya...." daga haka ya ajiye mata kudi yan dari biyar sabbi fil ya fita tana tsaye tana kallonsa cikin takaici, kafin ta koma ta zauna kan kujera cikin rashin sanin takamaimai abin yi...............
*Garin dadi littafin kudi ne ga mai bukatar cigaban labarin sai ya tura 500 ta 0774712835 Aisha Ibrahim Access Bank sai a tura evidence of payment ta wannan no 07044644433 ko a tura katin waya da shaidar biya wannan no 07044644433*
*_Ummi Shatu_*👌🏻
[1/5, 12:43] Maman K: {45}
*Ina kuke manyan mata ƴan ƙwalisa ma'abota son gyara da kece raini, maza ku garzayo ku nemi maman Maryam domin samun lafiyayyu kuma haɗaɗɗun Lagos lace wanda zaku iya samun ɗinkakku da kuma sabbi a ledarsu, kaya iya zaɓinki, gefe ɗaya muna da GHT product, zaku samu,*
~MAI DA TSOHUWA YARINYA
~FEMALE CARE
~REODEO
~VIGOR MAX
~ LONGZIT
~B CLEAR
*DUK ZAKU SAMU WADANNAN KAYA CIKIN SAUKI DA RAHUSA MAZA KU NEMI MAMAN MARYAM AKAN WANNAN NO 07080222187, SIYAN NA GARI MAIDA KUƊI GIDA.....*
~~~Tunda nazo Kano sai naji kamar kada na koma Abuja saboda yadda na shiga na sake cikin ƴan uwana kullum gidan ƙawalli cika yake da ƴan uwa da abokan arziƙi masu zuwa barka, ayi ta shan hira ana tsokanar juna wannan dalilin yasa naji kamar aware nake idan na koma Abuja, su mama dai tunda suka zo suka ga baby lokacin banma zo ba har yau basu dawo ba,
Kullum wuni ake ana kai kawo a gidan har suna ya ƙarato, kaya na ɗauko acikin kayan lefe na guda hudu leshi biyu atamfa biyu na bawa Bishra taje ta kai min dinki emergency, ranar da za ayiwa ƙawalli kunshi da kitso kuwa har dani duk da bana jure zaman amma wannan kam na jure tsaf nan nima na fito fes dani, bayan da aka gama yimin samz ya kirani yana ganin ƙunshin ya soma santi yana cewa,
"baby yaushe zaki dawo? Ko ni in zo?"
"da naji daɗi kuma nayi farin ciki...."
"ok zan zo Insha Allah, dama ina so in zo inga baby....."
"Allah ya baka iko ya kawo ka lafiya"
A lokacin yake faɗa min cewa sunyi magana da matar uncle ɗinshi wato Anty Amina kuma zata zo Insha Allah, ai kuwa naji daɗi sosai dan babu dadi ace ana abu agidanmu dangin mijin kowa yana zuwa banda nawa, mun jima muna hira wadda duk rabi shiririta ce amma haka ya biye ni ya koma kamar wani mate dina, sallama muka yi sai lokacin na samu na koma cikin mutane inda aketa aikace aikace saboda taron sunan da za ayi duk da dai ɗagawa dama akayi saboda mai jegon ta ɗan sake jin ƙarfin jikin ta. Ai ranar suna nima zama nayi tamkar mai jegon saboda irin yadda nake ta shiga ina fita, taro yayi taro jama'a sun cika ko dan dayake sunan fari ne oho, gajiya kam na gaji liss harda su ciwon jiki, wanka nayi da ruwan dumi na zo nabi lafiyar gado sai kuma me? Kiran samz nagani ya shigo cikin wayata, cikin kasala na ɗauka ina lumshe idanuwa duk da lokacin ba a fi ƙarfe 8:30 ba dan wasu ma basu tafi ba har lokacin,
"sweet yakake..."
'baby zan zo mu tafi yanzu" jin abinda ya fada sai kawai nayi murmushi dan duk tunanina tsokanata yake dan haka na amsa masa da,
"toh sai kazo..." na katse wayar tare da gyara kwanciyata, zuwa 9 na dan fara bacci naji ƙawalli na cemin "ƙawalli ki tashi ga jelarki can yazo.... Wai kije ku tafi"
Tashin nayi cike da mamaki nasa hijabi na fita falo nan na samesu shida angon ƙarnin ya wani kama jaririn ya riƙe kamar wanda zai tafi dashi, zama nayi na gaida su sannan na zuba masa ido ina kallon sa bance komai ba saboda naga hankalinsa yana kan hirar da suke yi shida yaya Abdul hakim, shi bai tashi mun tafi ba haka kuma bai ce in koma inje inyi kwanciyata ba haka na sasu gaba ina kallo ina saurare har 10 saura sannan na shiga na debo kayana ƙawalli ta rakoni, da yake dare ne shi ya ja motar, muna fita daga gidan na kwanta ajikinsa dan a mutukar gajiye nake gefe daya kuma nayi missing dinshi,
"Baby ko bakya son zuwa na? Banga kina murna ba"
"Ba haka bane kawai dai na gaji ne sweet" murmushi yayi ya kama hannuna guda daya ya rike tare da kissing ɗinsa yana shafa kunshina,
"zamu fara biyawa in siyo suya...... Ina jin yunwa sama sama"
"zan sha ice cream...."
"no baby.... Baki ganin situation dinke ne? Idan kika sha ice cream sanyi zai iya kama babynmu fa"
"yanzu ta baby ma kake yi ba tani ba ko?"
"am sorry baby, ba haka nake nufi ba"
Daru na tayar masa saboda ina sha'awar shan ice cream din harga Allah amma sai cemin yayi wai ko zan sha sai idan zan barshi ya narke ya huce nikuma jin hakan yasa nace ni na hakura amma da naga dagaske zamu bar wurin bai siya min ba sai nace na amince nan ya sake fita ya siyo min roba ɗaya ya dawo kuma ina ji ina gani ya hanani sha wai sai ya huce, har muka je gida ina turo masa baki ban huce ba,amma da yake yafi kowa sanina sannan ya san ta inda zai sauko dani jikinsa yajani ya sabule rigar baccina ya soma yimin tausa duka jikina abinka da gajiyayya ai lokaci ƙanƙani na fara bacci,
"baby nikuma fa? Zaki fara baccin nan naki kibarni ko?" ai ni ina nasan ma yana yi dan tuni na fara nisa cikin baccina, ban san lokacin da yaje ya gyara bedroom dinba ya goggoge sannan yazo ya dauke ni ya mayar dani ciki ya kwantar akan gado, wanka yaje yayi kafin shima yazo ya kwanta gefe na.
Washe gari shi ya taimaka min muka gyara ko ina muka tsaftace sannan ya fita ya iyo mana cefane nayi mana girki zuwa yamma muka fita kuma bawai wani wuri zamuje ba kawai zaga gari sai magariba sannan muka wuce gidan uncle dinsa duk da matar tashi mun hadu a sunan ƙawalli,
Dukkansu suna zaune cikin babban falon gidan suna kallon wani ƙayataccen series a tauraron ɗan adam, da murna duk suka tare dani daga anty Aminan har yaran sai dai banda mutum ɗaya wato Munira wacce itace babbar ƴar Anty Amina wadda a haife na san bazata girmema ƙanwata Bishra ba, tamkar bata ganni ko bata san da wata halitta ba awurin haka tayi duk kuwa da tana jin mahaifiyarta da sauran ƴan uwanta sunata lale marhabun dani, idonta yana kan tv tun bayan zuwana sai ko kan wayarta wacce ke ajiye kan cinyarta,
"Anty banyi salla ba a hanya ta samemu.... Shima sallar ya tsaya yi shiyasa bai shigo ba"
"Ah to shigo ki fara salla tukunna sai ki zo kici tuwo gashi nan...."
"wallahi kuwa kamar kin san shi nake so yanzu anty Amina"
"to kuwa gashi nan zaki ci har ki tafi dashi idan kina so"
"ai kuwa nagode" na fada ina murmushi ina biye da ita har cikin bedroom ɗin ta duk da inata ce mata ta nuna min ɗakin yaran sai inyi acan amma tace a'a a ɗakinta zanyi, sallata nayi a nutse bayan na idar na shiga mamakin wannan yarinyar tata Munira lallai kowa da halinsa sannan albasa bata yi
Book Chapters
Chapter 21
Chapter 22Chapter 23Chapter 24Chapter 25Chapter 26Chapter 27Chapter 28Chapter 29Chapter 30Chapter 31Chapter 32Chapter 33Chapter 34Chapter 35Chapter 36Chapter 37Chapter 38