Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya sake faruwa..... Ki dauki wannan kudin kibar min gidana kafin na dawo idan kuma har kika bari na dawo na sameki zaki kuka da kanki..... " kudin dake hannunsa ya wurga mata kan kujera ya zagayeta ya wuce yabarta tsaye bakinta a bude saboda mamaki, duk wannan farin cikin da suka sha amma yanzu yazo yana cemata wai it was a mistake? Tsaki taja ta wuce cikin bedroom din da ta sauka babu shiri ta shiga harhada kayanta bayan ta gama ta canja kaya ta saka jeans da t shirt ta wuce bedroom dinmu nanma ta bincike daga karshe ta kwashe masa duk wani kudi nasa dake ajiye cikin beside drawer ta fito taja akwatinta ta fita, lokacin da ta fito tsaye ta ganshi fuskarsa a daure ita fa abinma mamaki yake bata irin wannan daure fuska kamar wadda tayi masa dole alhali ba tirsasa shi tayi ya aikata wannan abun da ita ba ra'ayinsa ne har me afkuwa ta afku amma shine zai zo yana yi mata kurarin banza da na wofi,

"Karki kara dawowa inda nake daga rana mai kamar ta yau, ki dauki abinda ya faru a matsayin kuskure wanda nake dana sanin faruwarsa gami da tarin bakin ciki da kuma nadama..... Sannan idan har kika bari mata ta tasan wannan maganar wallahi sai na illataki...... "

Tsayawa tayi tana saurarensa daidai lokacin da tazo wucewa ta gefensa har yayi ya gama ya diga aya bata ce masa uffan ba har sai da ya gama, a zuciye ta juya ta kalle shi saboda duk cikin kalamansa babu wanda yafi bata haushi irin matarsa da taji ya ambata dama ta dade da sanin babu wanda yake so yake gudun bacin ransa sama da matarsa duk kuwa da ta san tafi matar tasa zama mace dan ta girmeni nesa ba kusa ba,

"wai dole nayi maka ka kwanta dani? Kana magana kamar wanda na yiwa dole bayan kaine da kanka ka kawo kanka har kana yimin sumbatu... Ita matar taka da kake magana a kanta idan har baka son ta sani Meyasa kayi? Mtsww Excuse me..."

Wucewa tayi ta barshi cike da bacin rai yana kallon ta, sai da yaga fitar ta daga cikin gidan sannan ya koma ciki ya zauna ya dafe kansa wanda keta faman yi masa ciwo tun bayan da ya tashi, gashi sam yaki kunna wayarsa dan bai san me zai fada min ba.

Ni kam tun bayan da na tashi naji shiru bai kirani ba naketa kiran wayar shi amma a kashe sannan rabonshi da online tun jiya bayan mun gama chaten, kawai sai naji abun ya fara damuna saboda na san shi baya kashe waya sai da dalili to amma yanzu wanne dalilin ne zai sa ya kashe wayarshi? Haka na wuni duk banda wani kuzari, yanda na wuni haka shima ya wuni gashi ya rasa wanda zai fadawa damuwarshi har abashi shawara dama kuma nice to ni yasan idan har ya fada min to fa burkice masa zanyi dan abanza ma nake kishi idan wata ta kula shi koda shi din bai kulata ba bare kuma ace yayi mu'amala da wata ai mutuwa ne kawai bazan yiba dan bakin ciki da bacin rai shiyasa bazai sanar min ba, haka ya wuni baida lafiya har sai da dare yayi sannan ya kunna wayarshi,

Bayan na idar da sallar ishah na sake gwada kiran layinsa nan naji ta shiga hamdala nayi na sauke wani gwauron numfashi,

"boo....."

"baby..."

Muryarshi kadai da naji ya isa sanar dani cewa akwai matsala nan da nan na rikice na fara tambayarsa damuwarsa,

"Sweet.... Meke faruwa ne wayarka a kashe kuma muryarka kamar da wani abu...."

"Banda lafiya...."

"amma sweet shine baka fada min ba tunda wuri na dawo...."

"ai ba wani abu bane mai girma baby, is just a headache kuma nasha magani kiyi zamanki idan kika gama sai ki dawo...."

"no boo Insha Allah gobe zan dawo.... Am very sorry"

"Kun gama komai?"

"babu abinda ba a gama ba, gara in dawo saboda karatuna"

"ok baby, I love you"

"I love you too..."

Daga haka muka yi sallama kuma a daren nagama hada kayana dan dagaske naji hankalina bai kwanta ba da yanayin da na ji shi. Shi kuma kokarin warwarewa yake yi kafin in dawo, so yake ya koma kamar yadda yake ta yadda bazan fahimci komai ba shi dai Allah yasani bai taba sanin wata ya mace bayana ba sai wannan wadda kaddara ta fada masa Allah shine shaidarsa amma yana tsoron in san wannan maganar dan yasan za asamu matsala babba ma kuwa ba karama ba,

Washe gari da shirina na tafiya na tashi su anty sai tsiya suke yimin wai daga ji mijina baida lafiya shine duk nabi na rikice aka kasa gane kaina, ƙawalli kuwa lokacin da na fada mata cewa tayi,

"ohh wannan kauna wannan kauna ya Rabbi ka dawwamar da ita har gaban abada, ya kamata kam a hanzarta a tafi aje a bashi magani" banza nayi da ita dan na fahimci abin da take son cewa.

A gurguje na shirya na yi wanka su anty suka kaini airport sai Abuja, lokacin da na isa azahar ta wuce babu jimawa, inata kiran wayar shi amma a kashe, koda na isa gidan ma sai da na jima ina danna masa door bell sannan yazo ya bude, daga shi sai farar t shirt da wando iya gwiwa,

"baby..... Welcome home" ya fada yana jana cikin kirjinshi, hugging dinshi nima nayi sosai ina kallon fuskarshi wadda idanuwanshi suka dan yi ja sannan suka kumbura,

"sannu sweet.... Ya jikin?" nace dashi ina daga kafafuwana dan in tabo bakinshi da nawa, ya gane abinda nake son yi shiyasa ya sunkuyo nan na hade bakina da nashi naki saki saboda nayi missing dinshi da yawa, mun jima ahaka kafin ya dauki bag din muka shiga ciki, ai muna zuwa falo na sake makaleshi na haye jikinsa bakina cikin nasa sai dai yau na lura sam baida kuzari,

"sweet wai me ke damunka?"

"fever ne...."

"sorry, kasha maganin?"

Kai ya daga min yana kasa da zip din rigata,

"baby push up kika saka ko...."

"Meka ke nufi?"

"a cuci kika saka anan" ya fada yana taɓa chest dina,

"to wa zan cuta?"

"ni mana...."

"yes" na fada ina fara idanuwana, kissing dina yayi a goshina yana karasa zame rigar tawa, a haka ya barni kuma yake son ganina daga ni sai bra sai underwear, sai da na gama shan dumin jikinsa sannan na shiga kitchen na dora mana girki, shi dai duk inda nayi bina yake da kallo dan tausayina yake ji sannan ya kasa yanke shawara akan ya fada min ko kuma kada ya fada min,

Har dare a sanyaye yake amma sai ni ban kawo komai acikin raina ba duk zatona rashin lafiyarce, tare muka kwanta amma har nayi bacci na farka shi bai runtsa ba,

"sweet..... Me ke damunka?"

"baby me kika gani?"

"Sweet kamar akwai abinda ke damunka, dan Allah ka fada min gaskiya karka boye min...."

Shiru naji yayi hakan yasa na mika hannu na kunna bedside lamp ina kallon sa,

"sweet baka ɓoye min komai idan da wata damuwa ko matsala dan Allah ka sanar dani, ina tare dake dakai bazan taba juya maka baya ba, damuwarka damuwata ce, duk abinda ya shafeka ya shafeni....." na fada ina shafa kansa bayan na rungume kan nasa cikin tsakiyar kirjina kamar yadda na jima da fahimtar hakan yana yi masa dadi kuma yana samar masa da nutsuwa, shi dai idan ina son in samo kansa to yaji shi cikin kirjina yana juya kansa duk inda yaso, lumshe idanuwanshi naga yayi sannan ya lalubo hannuna guda daya ya matse cikin nasa,

"baby dan Allah ki yafe min kuma kiyi hakuri sannan kar ki guje min wallahi ina mutukar sonki, ke kadai nake so...."

Sake matseshi nayi na shafo sumar kanshi zuwa fuskarshi cikin kwantar da hankali nace masa,

"sweet na sani.... Na yafe maka amma dan Allah ka fada min menene dan hankalina ya kwanta"

"zan fada miki baby but dan Allah ki nutsu kuma ki fahimceni...."

"Insha Allah sweet..."

"baby lokacin da bakya nan...... Lokacin da kika tafi Kano mommy sun zo ita da Hadiza da Felicia......"

Ni dai ji nayi duk na ƙosa ya fada min me ya faru dan tunda naji ya ambaci Felicia naji gabana ya fadi da mugun karfin da bai taba yi ba cikin zaƙuwa nace,

" sweet ina jinka sai me ya faru.....? "

" baby.... Before I tell you, you have to promise me to be calm and forgive me.... Please don't leave me...."

Shiru nayi ina nazarin maganganun da ya fada min, ni dai ina tsoron abinda zanji daga gareshi tunda yace min mommy ta zo tunda kuwa tazo to nasan akwai abinda ya faru marar daɗi, nan na daga masa kai har lokacin ina rungume dashi kamar wani jariri wanda ke bukatar jin dumin jikin mahaifiyarsa...............



_*Ummi Shatu*_👌🏻
[1/12, 11:21] Maman K: 62

*Ina kuke manyan mata ƴan ƙwalisa ma'abota son gyara da kece raini, maza ku garzayo ku nemi maman Maryam domin samun lafiyayyu kuma haɗaɗɗun Lagos lace wanda zaku iya samun ɗinkakku da kuma sabbi a ledarsu, kaya iya zaɓinki, gefe ɗaya muna da GHT product, zaku samu,*

~MAI DA TSOHUWA YARINYA

~FEMALE CARE

~REODEO

~VIGOR MAX

~ LONGZIT

~B CLEAR

*DUK ZAKU SAMU WADANNAN KAYA CIKIN SAUKI DA RAHUSA MAZA KU NEMI MAMAN MARYAM AKAN WANNAN NO 07080222187, SIYAN NA GARI MAIDA KUƊI GIDA.....*

~~~Yanda ya rokeni akan kar in daga hankalina kuma kada na juya masa baya bayan ya sanar dani abinda ya faru hakan na kuduri niyyar yi har acikin zuciyata, sake rungumeshi nayi na sumbaci goshinsa har lokacin yana makale da hannuna guda daya acikin nasa,

"baby bayan kan tafi Kano su mommy sun zo..... Mommy ta matsa min akan lallai sai na kara aure na auri Felicia....."

Ai yadda naji maganar tasa ji nayi tamkar saukar aradu shiyasa nayi zumbur na mike zaune daga kwancen da nake kallonsa hankalina a mugun tashe jikina har rawa yake, idanuwana awaje nake kallonsa,

" sai me ya faru? Kai kuma me kace? Ka yarda ka amince zaka yimin kishiyar?" duk wadannan tambayoyin lokaci guda na jera masa su raina a jagule,

"calm down baby..... Ban amince ba na fada mata bazan iya yi miki kishiya ba, ki kwantar da hankalinki...."

Ya fada yana jana jikinsa, wata ajiyar zuciya na sauke ina kallonsa zuciyata na bugawa da mugun karfi gaba daya ma na kasa magana sai ajiyar zuciya,

" baby take it easy please..... Ba abun fushi ko daga hankali bane Kinji " yace dani bayan ya kwantar dani, hancina yana gogar nashi ya lakuce min kumatu ya kashe bedside lamp din da na kunna yabini ya kwanta a jikina yayi pillow da kirjina kamar koda yaushe,

"baby.... Kinyi shiru ba kice komai ba, nace miki ki kwantar da hankalinki babu maganar yi miki kishiya.... Amma na san da mata suna yiwa maza kishiya zakiyi min ko? Da guda nawa zaki yi min?"

Ai babu shiri dariya ta subuce min jin abinda yace, "Meyasa kace haka?"

"kawai na tambaya ne...."

"da mata nayiwa maza kishiya ai kaima ka san bazan iya yi maka ba saboda ina sonka fiye da komai.... Sannan kana kyautata min koda yaushe"

"baby are you kidding me?"

"am not kidding you sweet..... Bazan taba yi maka kishiya ba, ko rabuwa muka yi bazan kara aure ba"

"baby idan kuma mutuwa nayi fa?"

Saurin rufe masa baki nayi da hannuna guda daya,

"dan Allah ka daina wannan maganar dan ko ita din ce to zan kare rayuwata a haka har karshen rayuwata"

"A'a baby ai wata rana zaki bukaceni...."

"to ai zan bukace ka kace ba zan bukaci wani ba.... Sweet kasan wani abu?"

Kai ya girgiza min kafin yace "no"

"ni wallahi ban taɓa sha'awar wani namiji ba sai kai, kai kadai ke bani sha'awa" na karasa fada ina boye fuskata a jikin tasa,

"come... Wai dama kina sha'awata shine ban taba sani ba?" ya fada yana juya ni na koma samansa,

"ehh mana sweet...."

"to me yake baki sha'awa atare dani?"

"gaba dayanka....... Tun daga sama har kasa" na fada ina hada fuskata da tashi, biye min yayi muka bata lokaci muna wasanni amma ga mamakina sai naga bai nemeni ba amma sai na danganta hakan da rashin lafiyar da yake yi.

***

Wasa wasa Malika tayiwa shalele layar zana dan gaba daya ta bace taje har gidansu neman ta ance tafi 3 weeks da tafiya Kano, gashi bata daukar wayarta haka ko tayi mata massage bata reply daga karshe dai ta fahimci kawai 419 tayi mata sannan gefe daya tana yi mata zagon ƙasa dama tun jimawa wannan damar ashe take ta nema amma bata samu ba sai yanzu, kyaleta suhaila tayi sannan tayi kokarin tursasa zuciyarta da ta manta da samz saboda taga kamar ba zata sameshi ba sai wani kadari na Allah, haka kuma gefe daya ga Affan wanda yanzu ya matsa akan ta bashi damar ya turo iyayensa duk da zuwansa gidansu biyu kacal haka ko waya ba wani shakuwa suka yiba ahakan dai ta bashi damar bayan ta sanarwa da gida, sati yana zagayowa magabatansa suka zo ai suna zuwa abbanta yaga yasan mahaifin Affan dinma ashe dan tare suka yi jami'a nan fa kowa ya cika da mamaki daga karshe suka yanke hukuncin to me zai hana ma a daura auren kawai anan take inyaso sauran abubuwa sai su biyo baya, ai kuwa hakan akayi tunda dama akwai shaidu anan aka daura auren aka bada sadaki, Abu kamar wasa kowa sai jin labarin yayi nan kuma shirye shiryen biki ya tashi dan nan da sati biyu amaryar zata tare kuma sai a lokacin ne hajiya taji babban kuskuren da shalele ta tafka,

"yanzu tsabar rashin hankali shalele sai kawai kawa ta zugaki kiyi gaban kanki batare da kin sanar dani ba? Ashe ba dan Allah ya takaita ba haka zakiyita bata har sai sun kare.... To yanzu sai kiyi karatun ta nutsu ki san da irin kawayen da zaki rinka mu'amala dan wasu ba dan Allah suke sonka ba haka kuma ba dan Allah suke zaune dakai ba kina dai ganin duk irin kyautatawar da kika yiwa Malika amma cin dunduniyarki take bata son cigaban ki bata sonki da alkhairi... " ta san duk abinda hajiya ta fada gaskiya ne ita dai kawai tabar Malika da Allah dan ta jima tana cutar ta kuma dama ta jima da gane cewa ita yar rigima ce, haka dai ta daure ta manta da batunta ta cigaba da shirye shiryen bikinta kuma cikin lokaci kankani ta manta da batun samz ta rungumi Affan dinta wanda yake nuna mata soyayya fiye da komai da ya mallaka, ita kadai tayi hidimar bikinta babu kawaye sai yan uwa da suka tayata komai nan aka sha biki wanda ya kayata aka mikata gidan mijinta, Malika kuwa sai a Instagram taga hotunan bikin kawar tata wai ta auri Affan Umar faruk nan hankalinta ya tashi sosai amma babu yadda ta iya duk yadda taso ta dakile wannan auren abun yafi karfinta.
***
Tun bayan da na dawo na fuskanci baya son kusantata kamar yadda ya saba ada wanda idan son samunsa ne kowanne dare ya kasance dani haka ma da asubah kawai tausayina ne yake hanashi hakan da kuma raunin da nake dashi dan shima kansa ya san bana son wannan yawan bukatar tasa kawai ina daurewa ne ahakanma, to yanzu tunda na dawo yaki kusantata tsakanina dashi sai yan wasanni wanda muka saba yi irin na ma'aurata, shi kuma a zuciyar sa ya kudurce wai bazai kusanceni ba har sai yaje hospital yayi tests kala kala an tabbatar bai dauki wani disease ko infection daga jikin Felicia ba gudun kada ya shafa min nima ni kuma ban saniba shikuma bai samu time ba har yanzu saboda aiki, daren jiya haka ya gama jagwalgwalani daga karshe yaki kusantata wannan abun ya bata min rai kuma ya bani haushi,shiyasa na kwanta na juya masa baya naki kulashi duk da har lokacin kokarin samar min da nutsuwa yake,

"baby menene abin fushin? Kiyi hakuri please ki saurare ni...."

"ba dole nayi fushi ba na nuna maka ni ga abinda nake so amma ka tsaya sai wani wahalar dani kake....."

Burkitoni yayi bai barni naci gaba da masifar ba ya hada bakina da nashi haka dai ya lallabani har ya bani farin cikin da ya dace, sharewa nayi ban cigaba da mitar ba tunda yace min wai inyi hakuri ya gaji ne kaza da kaza, a haka dai na samu bacci bayan ya gama kalamunceni da maganganu masu dadi. Washe gari ma haka muka yi dashi da safe sai da yagama kunna ni sannan ya fara kokarin yimin wayo, kuka na fara yi masa nan hankalinsa ya tashi dan nace ni wallahi gida zan tafi,

"Baby dan Allah ki saurare ni inyi miki bayani..."

"babu wani bayani da zaka yimin..... Tunda na dawo kaki kusantata ban san me ka gani ba atare dani sai kace wadda take dauke da wata cutar...... Ni wallahi gida zan tafi"

"haba baby, kin san me? Toilet dina na office ne ruwa baya zuwa shine na shiga na general staffs dinmu to tun daga lokacin nake ganin kamar na dauki infection.... Bana son in shafa miki ne that's why but I promise you yau zanje inga Dr idan har ya tabbatar min da zan iya kusantarki babu matsala shikenan idan kuma sai na warke.... " tun kafin ya karasa na fara turje turje da buge buge ina rera kuka,

" ni wallahi ban yarda ba, kawai koma me kake dauke dashi ka bani hakkina a haka inyaso muyi jinyar tare...... "

" baby ki bari naga Dr first..."

"ni wallahi a'a" na fada cikin kuka, ganin kuka nake yi dagaske da turje turje ya sashi rungumeni tare da kissing bakina, ba dan yaso ba a haka ya raya sunnah dani kuma sai lokacin ya samu kaina,

"baby ko kunya kika ce sai na baki hakkin ki ko?" ya fada yana rungume dani cikin kirjinsa yana shafa bayana,

"to tun yaushe rabonka da ka bani.... Tunfa ina Kano da kaje"

"to ai kece kike hanani kice wai ba tuwo bane..... Baby rigima"

"shine kaima zaka fara yimin rowar?"

"A'a ni ba zan yi miki rowa ba duk time din da kike so zan baki my love....."

Kaina na daga nayi kissing dinsa kafin nace "yau baza kaje office ba?"

"zanje..... Ina jira ne ki sallameni"

Mikewa nayi da sauri naje na hada mana ruwan wanka wanda ina cikin hadawa ya shigo, a gurguje muka yi muka fito nidai ko kaya ban saka ba daga ni sai towel na shiga kitchen na dafa masa tea na soya masa kwai na biyo shi har cikin bedroom din inda yake shiryawa shima, a bakin gado na ajiye masa na karasa shirya shi na fesa masa turare ya zauna ya karya, kissing din goshinsa nayi sai lips dinsa sannan yayi hugging dina shima yai kissing dina ya tafi.

Ranar gaba daya bai wani zauna a office yajima ba ya tafi wani private hospital bai ɓoyewa Dr dinba ya fada masa gaskiyar ya hada shimfida da wadda ba matarsa ba kuma ta yuyu tana bin wasu mazan shine yake tsoron ko ya dauki wani infection din ajikinta nan aka yiyyi masa tests aka ce ya jira result,

Nikam bayan tafiyarsa riga nasa na shiga kitchen na gyara ko ina nayi wanke wanke nazo na gyara falon da bedroom na wanke toilet sannan na kwanta na janyo wayata na kirashi, lokacin yana asibitin yana jiran result,

"hello baby...."

"hey boo.... Ya aiki?"

"alhamdulillah but bana office ina hospital... Ina jiran result"

"sweet wai sai da kaje asibitin nan, babu komai fa"

"no baby, saboda ke naje bana son in shafa miki ne..."

"Insha Allah babu abinda zai faru boo, sai ka dawo, I love you"

"I love you too"

Wayata na katsewa kiran Felicia na shigowa sai da ya ja tsaki a ransa yana tambayar kanta wannan kuma yanzu me take nema dan shi gaba daya yanzu ya gama tsanarta,

"hello....."

"hello samz.... Na kiraka ne inyi maka albishir...."

"albishir? Na me kuma?"

"very soon zaka zama daddy...." ai gaba daya maganar tata sai yaji ta kamar kwarankwatsa wannan kuma wacce sabuwar masifar ce?

"very soon zan zama daddy? A ina?"

"zan haifa maka baby nan bada jimawa ba samz saboda lokacin da muka yi having sex I was ovulating ....."

Innalillahi wa inna ilaihir rajiun shine abinda yaketa maimaitatawa bayan ya dafe kansa ya zauna daga tsayen da yake a da,bai iya sake magana ba har sai da yaji Felicia ta sake maimaita abinda ta fada nan ya rufeta da masifa kamar zai daketa,

" look Felicia bana son shirmen banza da na wofi, karki sake kirana akan wannan maganar, menene nawa da ovulation dinki ko wani abu mai kama da haka..... Am not ready for this nonsense kin gane..." daga haka ya tsinke wayar yana sake jan tsaki.........



_*Ummi Shatu*_👌🏻
[1/15, 09:26] Maman K: 63

*Ina kuke manyan mata ƴan ƙwalisa ma'abota son gyara da kece raini, maza ku garzayo ku nemi maman Maryam domin samun lafiyayyu kuma haɗaɗɗun Lagos lace wanda zaku iya samun ɗinkakku da kuma sabbi a ledarsu, kaya iya zaɓinki, gefe ɗaya muna da GHT product, zaku samu,*

~MAI DA TSOHUWA YARINYA

~FEMALE CARE

~REODEO

~VIGOR MAX

~ LONGZIT

~B CLEAR

*DUK ZAKU SAMU WADANNAN KAYA CIKIN SAUKI DA RAHUSA MAZA KU NEMI MAMAN MARYAM AKAN WANNAN NO 07080222187, SIYAN NA GARI MAIDA KUƊI GIDA.....*

~~~Gaba ɗaya rasa abinda yake yi masa dadi yayi saboda jikinsa da tunaninsa yana bashi wannan sabuwar hanyar da su Felicia suka dauko indai ba wani ƙadari na Allah ba to zasu iya cin nasara su tarwatsa masa farin cikinsa dan yasan muddin maganar cikin nan ta tabbata tofa zamana dashi da yuyuwar ya kare,

"innalillahi wa inna ilaihir rajiun...... Ya Rabb see me through....." ya fada idanuwansa na juyewa izuwa launin ja, a haka ya samu yaje ya karbi result din wanda ya nuna komai lafiya lafiya wato baya dauke da kowacce irin kwayar cuta ko wani abu mai kama da haka,

Yana komawa office bai zauna ba ya dauko laptop dinshi ya nufo gida, a ransa yana ta tunanin ko dai ya sanar dani abinda yake faruwa ne ta yadda zan fahimce shi kar sai nan gaba magana ta fito sannan in kasa fahimtarsa gaba daya, nikam lokacin da ya dawo ma baje ya sameni inata rubuce rubuce dan wani assignment nake kokarin yi kuma yau a kansa na wuni ko abinci ban girka ba,

"welcome back boo....." na fada lokacin da naje taro shi, hannuna ya riko yana kokarin boye min damuwarsa,

"baby..... What are you doing?"

"Assignment..."

"Allah ya bada sa'a"

"amin sweet"

Cewa yayi in cigaba da abinda nake yi ya yafe ba sai na rakashi yayi wankan ba, ina nan zaune ina ta fama ya shigo daga shi sai gajeren wando iya gwiwa,

"sweet bari na tashi in dafa mana noodles...."

"ba naga akwai abinci ba a fridge?"

"ehh da akwai"

"bari nayi mana warming dinshi kawai muci, kici gaba da aikin ki"

"thank you sweet"

Kitchen ya shiga ya dumama mana abincin duk yana cikin tunani da neman mafita amma bai bari tunanin yayi yawa ba ta yadda zan gane,

Muna cin abincin ya kama hannuna ya rike,

"baby.... Dan Allah kiyi min alkwari duk rintsi ba zaki rabu dani ba"

Kalamansa mamaki suka bani har hakan yasa na tsaya daga cin abincin da nake yi na kalleshi,

"sweet me kuma ya kawo wannan maganar?"

"baby don't ask me why just promise me....."

"sweet ko ban yi maka alkawari ba yakamata kai da kanka kasan ina tsananin sonka kuma ba zan taba barin ka ba har abada.... Ba zan taba juya maka baya ba saboda ka Soni kamar ni kadai ce abinda na rage a duniya, ka kaunaceni fiye da kowacce mace, ka mayar dani kamar sarauniya bani da wata damuwa domin kana bani dukkan gata da kulawa.... Irinka acikin maza basu da yawa, sai da Allah ya zabo min kai sannan ya bani, ta yaya kake tunanin har zan iya barinka boo? To idan na barka wurin wa zanje? Ni wallahi ka bata min rai ma da har kake zaton zan iya barinka.... " na karasa maganar ina fincike hannuna tare da yunkurin tashi, saurin rikoni yayi ya jani jikinsa,

" am very sorry baby.... Yi hakuri kar kiyi fushi"

"ni nayi fushi abincin ma na fasa ci"

"yi hakuri...."

Shi da kansa ya karasa bani abincin bayan mun gama yayi sallah yazo ya zauna ya karasa min

Please Login or Register in order to submit comment