Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

dinma hakane,

"sannu da zuwa..." nace da ita ina karema shigarta kallo dan duk da bani nayi shigar ba amma ji nayi kunya ta rufeni,

"yawwa sannu, yakike"

"lafiya lau" nace lokacin da nake tashi na wuce kitchen, wanda shi zaka fara wucewa kafin ka shigo falo daga nan sai wani dan corridor wanda aciki bedrooms dinmu suke guda biyu daya da toilet aciki dayan kuma toilet dinshi awaje yake ta kusa dashi, duka dai komai a wadace yake dan har yafi wancan gidan da muka baro wadata a girma da komai koda yake lokacin yana shi kadai may be shiyasa ya kamashi a haka, juice na dauko mata da ruwa sai dambun naman kaza wanda dama dashi na taho tun daga Kano cikin wani madaidaicin bokiti wannan mama ce tayi min na taho dashi shikuma samz bai dameshi ba sosai yana ci amma kadan kadan nice ma dai kusan kullum sai na dan damka nasa a bakina,

Komawa nayi wurin ta muka gaisa bayan na gabatar mata da kayan motsa bakin da na kawo mata,

"sunana Samha, nice matar abokin mijinki Kabir kuma makociyarki wanda gidanmu ke opposite"

"ayya Allah sarki ashe matar Kabir ce, ina jin labarinku ai amma bamu taba haduwa ba"

"ehh nayi tunanin zanga kun shigar mana sai muka ji shiru"

"wallahi riga mu kuka yi kin san har yanzu bamu kammala gyara kayanmu bane amma Muma muna da niyyar shiga, bama gidan ki kadai ba ai duk gidajen zamu shiga Insha Allah"

Allah sarki, to ai yanzun ma ina zuba ido "

" Insha Allah zaki ganni da rana ma ni zan zo muku ko yamma ba zuwan dare ba"

"to shikenan ina nan ina zuba ido"

Mun dan sha hira sosai duk da bamu san juna ba kuma naji mutukar mamaki da naji cewa wai matar aure ce, ya ilahi wannan wanne irin zamani wai muke ciki? Nidai gaba daya ji nayi bata wani yimin ba dan kamar bata da kamun kai amma zan bata lokaci dai in karanceta dan lokaci shi ke sanar dakai wanene ainihin mutum. Munata hira har lokacin sallar ishah yayi nace mu tashi muyi salla amma bata maida hankali ba saboda kallo ya dauki hankalinta sosai sai bayan da na idar sannan itama ta samu tayi, tana idarwa kuma samz yana shigowa kiran ta inji kabir nan na tashi na rakata har waje nida shi yana rike da hannuna muka gaisa da mijin nata sannan muka yi sallama ina ce musu Insha Allah Muma zamu shigo musamman ma tunda muna kusa,

Ƙofa na jirashi ya rufe yana juyowa na dage kafata daya ina yamutsa fuska,

"what?" ya bukata yana kama hannuna,

"na taka kaya bazan iya tafiya ba ka goyeni...."

"you want to stress me dai...." ya fada tare da sunkuyawa, da tsallena na haye bayansa muka karasa ciki ina makale wuyansa da hannayena,

"baby Kin sake nauyi fa....."

"haba sweet ni din har nawa ma nake"

Dariya yayi ya kwanto dani kan cinyarsa yana cire min hijabin,

"my sweet 16 baby...."

"ai bazan fi hakan ba love"

"I know..." yace dani yana dariya sau tari haka dama yake biye min muyita shirme kamar wasu kananun yara to yau dinma hakan akayi dan har fin 11 muna ta shiririta afalo daga bisani muka yi shirin bacci nan dinma bamu hakura ba sai dariya yaketa sakani yana yimin cakulkul, alhamdulillah dai yanzu na daina wannan gane ganen da jin kukan abubuwa tun bayan da muka baro tsohon gidan da muke,cikin farin ciki da nutsuwa nayi bacci na barshi yana yimin tausa a kafafuwa na..........

*Garin dadi littafin kudi ne ga mai bukatar cigaban labarin sai ya tura 500 ta 0774712835 Aisha Ibrahim Access Bank sai a tura evidence of payment ta wannan no 07044644433 ko a tura katin waya da shaidar biya wannan no 07044644433*


*_Ummi Shatu_*👌🏻
[1/5, 12:43] Maman K: {48}

*Ina kuke manyan mata ƴan ƙwalisa ma'abota son gyara da kece raini, maza ku garzayo ku nemi maman Maryam domin samun lafiyayyu kuma haɗaɗɗun Lagos lace wanda zaku iya samun ɗinkakku da kuma sabbi a ledarsu, kaya iya zaɓinki, gefe ɗaya muna da GHT product, zaku samu,*

~MAI DA TSOHUWA YARINYA

~FEMALE CARE

~REODEO

~VIGOR MAX

~ LONGZIT

~B CLEAR

*DUK ZAKU SAMU WADANNAN KAYA CIKIN SAUKI DA RAHUSA MAZA KU NEMI MAMAN MARYAM AKAN WANNAN NO 07080222187, SIYAN NA GARI MAIDA KUƊI GIDA.....*


~~~Yau da wuri na tashi na shiga kitchen na shiryawa samz breakfast saboda shima da wuri zai fita office domin acewarsa akwai baƙi da zasu zo musu saboda wani gagarumin aiki da zasuyi,

Duk da yana sauri dankali na soya masa sannan nayi masa sos din kwai na haɗa masa tea na kai masa lokacin har ya fito daga wanka yana shiryawa, kayan breakfast din na ajiye sannan na karasa na taimaka masa ya gama shiryawa na dauki turare na fesa masa ina kallonsa cikin yaba shigarsa ta yau domin suit ya saka blue black amma rigar ta ciki fara ce sai necktie da ya saka,

"kayi kyau sosai sweet.... Kamar in hanaka fita" na karasa maganar cikin shagwaba,

"tnx darling but kar ki hanani fita i beg...."

"to zauna kayi breakfast sai ka tafi...."

"duk yadda kika ce haka za ayi my love"

Sosai yaci abincin kafin yayi min sallama ya tafi wanda sai da na raka shi har ƙofa sannan na dawo na kwanta bayan na rufe ko ina saboda bacci nake son in koma in dan yi,

Ban fi 20 minutes da kwanciya ba naji knocking, jin knocking din ba mai karewa bane ya sani tashi ina mamakin waye kuma yanzu? To ko shine yayi mantuwa ya dawo? Da waɗannan tunane tunanen dai na karasa, ina budewa naga Samha matar Kabir, murmushi nayi nace,

"Hajiya Samha kece, sannu da zuwa"

"yawwa sannu, ga baƙuwar sassafe" ta faɗa tana kokarin shigowa nan na bata hanya ta shiga nabi bayanta, daga ita sai rigar bacci sai hijabi, hira muka dan fara yi tun 9 da tazo har kusan azahar nan kuma naji abin yafara damuna domin inada aikace aikace na da nake son inyi, ina son in gyara gidana in wankewa mijina inner wears dinsa da kayan baccinsa kuma ina son in danyi bacci kafin ya dawo ko dan in bashi lakacina sosai amma taki fahimtar hakan bare ta tafi nikuma bana son in fito in fada mata ko in shiga ciki in barta taga kamar kora da hali nake yi mata amma duk mace mai hankali tunda kika zo tun safe anan kika karya ai ya dace ki tafi gidan ki kuma tun ana marmarinki ba afito ance ki tafi ba,

"Hajiya Samha naga azahar ta kusa bari na tashi akwai yan ayyukana suna nan jingim banyi ba suna jirana...."

"har wani aiki gareki widat? Aikin nawa yake? Ni kin ganni nan wallahi tunda na tashi ko tsinke ban dauke ba daga gidana na fito, ke ko gadon da muka kwana ma haka na fito na barshi kuma bana jin zan iya gyarawa"

"to ai ke amarya ce, har yanzu kina cikin dokin amarci nikuwa fa?"


"a'a wallahi kawai dai abinda na lura dashi shi namiji zuma ne sai da wuta dan daga lokacin da ka nuna masa kai wahalalle ne tofa a wahala zaka kare amma idan ka nuna masa kai ma dan hau ne sai kiga kun daidaita..... Wasu matan fa dan wahala har wanki suke yiwa miji wai, ni hauka nake zan yiwa namiji wanki, wallahi sai dai kar yasaka kayan "

Tunda naji irin kalamanta sai na sha jinin jikina bance komai ba sai murmushi da nayi nan taci gaba da mitarta akan wai ita ba zata zauna ta bautawa namiji ba bata son wahala bla blah blah daga karshe dai ta tashi ta fita kuma shi dinma da tayi min sallmar ba gidanta ta shigaba ina hangota ta window din bedroom dinmu lokacin da na shiga ina tattara kayan da zan wanke, can kasa ta sauka ta shiga wani apartment din, nidai ko kadan kalamanta basuyi tasiri a gareni ba domin kowa da irin fahimtar sa da kuma tarbiyarsa har gobe mazan gidanmu sune suke kaiwa Abbanmu wanki su biya kuma before su fara aiki su yi aure sune suke yi masa wanki tas yayin da sukuma su Annie sune suke wanke masa kananan kaya kuma har gobe basu daina ba shiyasa ni a ganina wannan ba wai wahala bace kyautatawa ce, nima kuma tunda nayi aure nake wannan hidimar amma dukka kayana samz ke hadawa da nashi ya bayar wanki,

Ina kokarin shiga bathroom inyi wankin naji yana kirana a waya nan yake sanar dani sun gama meeting din may be ma yau da wuri zai dawo gida, sallama muka yi na shiga nayi aikina na gama na wanke toilet din nazo na gyara gidan sannan nayi wanka na dora girki,zuwa ƙarfe uku na fita na ɗan shiga maƙota kamar yadda naga dacewar hakan kowanne gida na shiga kuma dukkansu ba wasu manya bane wasu zasuyi sa'anni na wasu kuma koda zasu girmeni to da kadan ne dan dukkansu babu wadda tayi haihuwa uku daga biyu sai mai ɗaya, mace daya ce na ganta da dan girmanta dan yaran ta ma sun kai biyar kuma duk ciki tafi nutsuwa ko dan dama bama za a hada hankalinta da na sauran ba tunda tafisu shekaru kuma a gidanta ma na dan fi jimawa saboda tana ta bani shawarwarin in iya takuna kuma in iya bakina a compound dinnan domin akwai matsala, idan har baka iya bakinka ba yanzu zaka ji sirrin ka da duk wani abu da ya shafeka awaje haka kuma inyi takatsantsan, to ni dai ta barni a duhu dan bata fito fili ta fayyace min meyake faruwa acikin compound dinba amma duk da haka na dan fahimci wani abu kadan, sallama nayi mata na tafi inata mamaki da tunani kala kala saboda tace min duk ciki itace ta fara zuwa kowa anan yazo ya sameta ita asali daga jihar Borno suka dawo ita da mai gidanta wanda ya samu canjin aiki ana kiran ta da Hajja Gana,amma wannan hannunka mai sandar da tayi min yasa naji bana sha'awar yin mu'amala da kowa a cikin compound din sai dai kawai hakkin musulunci amma bazan shiga jikin kowa ba kuma bazan bari kowa ya shiga jikina ba zan zauna da kowa nesa nesa dan naga kamar dukkansu kansu yana rawa ciki harda Samha. Ina komawa sallar la' asar nayi na sake gyare jikina na sauya shigata daga wacce naje da ita unguwa nasake wata sabuwa inda na saka wata fitinanniyar riga three quarter purple color mai ƙaramin hannu, wuyan rigar a bude yake gaba ɗaya shiyasa kusan rabin ƙirjina awaje yake, sarka da dan kunne na saka masu jan hankali domin sarkar ta shige har tsakiyar ƙirjina da yake doguwa ce haka dan kunnayen sun sauko har kan kafaduna suma, turarena wanda nake amfani dashi musamman idan ina gida shi nabi na shasshafa har cikin cibiyata da bayan kunnena da sauransu fuska ta ban yi mata wani havy makeup ba light nayi yanda zan fi daukar hankalinsa, ƙarfe shida daidai ya dawo, ina falo ina kallo dama aikin kenan kallon series sai ko karatun novel, kiransa da ya shigo cikin wayata shine ya katse min kallon da nake yi na dauka ina yanga tamkar yana kallona,

"Sweet ya....?"

"Baby am back....."

"Awwwwn.... Am coming dear"

Da gudu naje na buɗe ƙofar ina budewa na koma ciki na labe yana shigowa bayan ya rufe ƙofar na ɗale shi duk kuwa da cewa yana riƙe da jakar computer ɗin shi da baƙar leda wadda ban san me ya siyo mana ba aciki,

"Baby....." na ji ya kirani cikin shagwaba alamar a gajiye yake, kayan na karba muka karasa ciki yana ta aikin kallona kamar yau yafara ganina, ai muna zuwa ya janyoni jikinsa ya soma sinsinata yana wasa da sarkar da nasa,

"wow... baby kinyi kyau, come closer please....."

"nayi kyau a hakan?" na bukata cikin shagwaba,


"yes nah..." ya bani amsa yana murmushi, yana ta santin kwalliyata na samu na rage masa kayan jikinsa na cire masa socks da rigar jikinsa daidai lokacin kuma kiran mahaifiyarsa ya shigo ya ɗauka ina jin alamun itace na kwashi kayan na basu wuri na wuce bedroom na kai sannan nazo na wuce kitchen naje na kwaso warmers ɗin abinci na kawo, ledar da ya shigo mana da ita na dauka fruits ne aciki sai kilishi duk da shi baya ci amma ya kan siyo min saboda ya fahimci ina so,

Fruits din na yanyanka na hada masa komai yadda ya dace kafin na koma bedroom din na wuce bathroom na hada masa ruwan wanka na fito na nemi wuri na zauna ina jiran sa yagama ya shigo dan bana son in zauna inji abinda suke tattaunawa tunda kowa da muhallinsa. A can falo kuwa samz ya sake sosai yana shan hira da mommy domin yau ta sigar da tazo masa daban babu fada babu complain babu komai sai bincikar lafiyarsa da kuma halin da yake ciki nan ya zauna yake sanar da ita dukkan abubuwan dake faruwa a office da kuma canjin gidan da muka yi amma bai sanar da ita dalili ba nan take ce masa to ya kamata dai ya dage yayi saving kudinsa har yasamu ya mallaki gida a Abuja ya huta wannan gidan hayar, hira suka yi mai dadi sosai wacce rabon da su yi irin ta har ya manta yau ya sake yayi hira da mahaifiyarsa wacce yajima bai samu wannan damar ba, har aka kira salla aka idar yana kan waya nidai har na kosa na gaji da saurarensa har nayi salla na idar na zauna dan karanta alqur'ani, sai can naji shigowarsa, karasa rage masa kayan jikin nasa nayi ya shiga wanka nikuma na fito masa da kananun kaya wanda zai sha iska babu takura, jiransa nayi har ya fito ya shirya sannan muka koma falo bayan yayi salla, ina kwance jikinsa yana tambaya ta yau me da me nayi nake bashi labarin zuwan matar abokinsa wato abokin aikin sa Kabir, dariya yayita yimin jin nace ita ta hanani bacci dan muna tare har azahar. Hmm kamar da wasa sai Samha ta mayar da zuwa gidana kamar wani ibada dan kullum sai tazo sannan gashi bata la'akari da ko mijina yana nan ko baya nan, idan yana nan sai dai ya koma bedroom yabar mana falo sannan kuma hakan bazai sa ta tafi da wuri ba, koda cikin weekend ne haka take zuwar mana ta baro nata mijin ni wannan abu yana daure min kai kuma yana bani haushi dan gaskiya ni wannan zuwan nata yana takura min kuma ma sai naga kamar tafi zuwa idan samz yana nan wannan dalilin yasa na fara gajiya na daina bude mata ƙofa koda yaushe amma hakan fa baisa ta daina zuwa ba,

Yau muna baje falo muna kallo nayi ɗai ɗai kan jikinsa kamar yadda na saba kwanciya jikinsa kamar wata mage, wayar shi ce tayi kara ya dauka, ji nayi yace,

"ehh muna tare gata..." kara min wayar yayi a kunne ni wallahi duk tunanina ma ko acikin yan gidanmu ne wani ya kira wayata bai samu ba shine ya kira wayar sa amma me ina magana naji muryar makociyata Samha...........


*Garin dadi littafin kudi ne ga mai bukatar cigaban labarin sai ya tura 500 ta 0774712835 Aisha Ibrahim Access Bank sai a tura evidence of payment ta wannan no 07044644433 ko a tura katin waya da shaidar biya wannan no 07044644433*


*_Ummi Shatu_*👌🏻
[1/5, 12:43] Maman K: {49}

*Ina kuke manyan mata ƴan ƙwalisa ma'abota son gyara da kece raini, maza ku garzayo ku nemi maman Maryam domin samun lafiyayyu kuma haɗaɗɗun Lagos lace wanda zaku iya samun ɗinkakku da kuma sabbi a ledarsu, kaya iya zaɓinki, gefe ɗaya muna da GHT product, zaku samu,*

~MAI DA TSOHUWA YARINYA

~FEMALE CARE

~REODEO

~VIGOR MAX

~ LONGZIT

~B CLEAR

*DUK ZAKU SAMU WADANNAN KAYA CIKIN SAUKI DA RAHUSA MAZA KU NEMI MAMAN MARYAM AKAN WANNAN NO 07080222187, SIYAN NA GARI MAIDA KUƊI GIDA.....*


~~~Cike da mamaki gami da hasashe kala kala da tunani iri iri nama kasa magana dan tambayoyin dake kai komo cunkushe cikin raina sun hanani lalubo ko kalma kwaya daya da zan tarbeta da ita, shin meya hadata da mijina? A ina ta samu no dinsa? Wanne dalili yasa ta kira no dinsa? To dama ta taɓa kiran sa ne ko kuma wannan ne karo na farko? Duka wadannan tambayoyin fa ina bukatar amsarsu sai dai a wurin wa zan samu?

"hello neighbor kina jina?" naji ta bukata daga cikin wayar, wani gwauron numfashi na sauke kafin na amsa mata a dakile,

"ina jinki, amma lafiya?"

"lafiya lau wallahi, ai kinga yau ban leko ba bana ɗan jin dadine kuma wallahi na wuni ban iya cin komai ba shiyasa nace bari na kiraki ko zan samu wani abu in ci....."

"ba zaki samu ba dan nima yau banyi girki ba" daga haka ban jira cewarta ba na katse wayar duk da haka ban hakura ba sai da naje na danna mata block sannan nayi delete no din shi dai yana zaune yana kallo na baice komai saboda shima din yayi mamakin yadda aka yi ta dauki no dinsa a wayar mijinta ta kirashi dan ko tantama ba yayi wannan ita kadai ce hanya daya da zata iya samun no dinsa,

"baby...." naji ya kirani yana wasa da zanen dake gaban rigata wanda aka rubuta _Hello Kitty_ shiru nayi masa ban amsa ba saboda matar nan ba ƙaramin ɓata min rai tayi ba, ya za ayi ta wani kirawo mijina dan kawai tana nemana akan buƙatarta?

"Hello kitty....." ya fada cikin tsokana, "what?" na bukata bayan nayi kicin kicin da fuska alamar ina sama,

"sweetheart nikuma menene laifi na? Me nayi?"

Shuru nan dinma nayi tunda idan zanyi masa adalci kam shi ai bashida da laifin komai tunda yana zaune ta kira shi, ban kai ga lalubo amsar da zan bashi ba sai ga wani kiran daga Felicia wannan kam kin ɗauka yayi kamar yadda ya saba ƙin ɗaga wayarta ita kuma gata da shegen naci nan ta kafa kira hakan ya sake kular dani,

"dan Allah ko ka ɗaga kiran nan ko ka saka wayarka a silent dan wallahi nidai an dameni....."

Ɗaukar wayar tashi yayi yabar falon ya wuce cikin bedroom hakan ya sake tunzurani gashi ya tafi ya barni cikin tunani shin zai dauki wayar ne ko kuma me ya tafi yi cikin dakin? Wata zuciyar ce ta rinka zugani akan in bishi inga me yake yi, nan dai na kasa hakura na tashi na bishi, akan gado naga wayar tashi a ajiye shikuma ya shiga bathroom, to nikam yau dai ko inje in dauki wayar nan tashi ne inyi abinda ban taba yiba wato bincike? Kul wallahi ahir dinki Maimunata kina zaune da mijinki lafiya kuna kaffa kaffa da juna kar ki kuskura ki ganowa kanki abinda zai hana ki zaman lafiya da mijinki domin duk dadinka da miji to ka nisanci wayarshi,

Wannan shawarar ta daya zuciyar tawa nabi na koma falo jiki a sanyaye na nemi wuri na zauna duk kallon da nake yi ya fita daga kaina ma, amma fa ya zama dole in takawa wannan yarinyar samha burki kar ta kuskura ta sake kirar min wayar mijina duk da ma dai nayi blocking dinta,

Ina nan zaune ni ba kallon nake ba ban kuma tashi ba ya fito, "baby lets hang out....."

"Awwwwn....." na fada ina tashi tare da rungumeshi, a gurguje naje na shirya na saka bakar abaya na fito ba tare da nayi kwalliya ko na shafa turare ba, ba wani nisa muka yi sosai ba amma dai duk da haka fitar ta sakani farin ciki dan har video call muka yi da kawalli na nuna mata inda muka je, Irfan ta hasko min wanda yake kwance yana bacci yayi bulbul dashi kai bama shi kadai ba gaba dayansu sunyi bulbul dasu saboda yanzu suna wata na biyu ne,

"ƙawalli dan Allah nima ki sakani acikin addu'a in samu cikin nan in haihu....."

"oh Allah gaggawar me kike? Wato har kin manta ko? To kar kiyi mamakin yanzu haka ma kina dashi...."

"yanzun dai babu sai dai Allah ya kawo....."

"Allah yakawo mai albarka kawata"

"amin" na fada a marairaice, daga nan muka yi sallama, zuwa 9 muka koma gida. Bayan kwana biyu da samha ta shigo ban sakar mata fuska ba kamar yadda na saba sakar mata dan har ga Allah ni na gaji da lamarinta so nake ta daina shigo min gida dan soki burutsunta yayi yawa sai tazo tana yi min wasu maganganu na rashin hankali wai dan Allah ina gamsuwa da mijina, ido na zuba mata fuskata babu walwala nace,

"samha wai meke damunki? Menene naki na yimin wannan maganar? Wannan fa sirrinane tsakanina da mijina idan har na fada miki wacce riba zaki samu?"

"ehh gaskiya sirrin ki ne kam amma abunne yake bani mamaki, ni wallahi mijina bana wani samun abunda nake so, kamar ba namiji ba dan tunda muka yi aure nidai banji abinda ake ta kozozozon ana ji ba...."

"to wannan ai kuma keda mijinki ya kamata ku zauna ku tattauna har ku samu mafita bawai ki zo kina fadawa duniya ba...."

"Wallahi sis abunne yake damuna shiyasa, kuma mafita nake nema shiyasa....."

"ki samu mijinki ku tattauna shine mafita....."

"ai bama lallai ya tsaya ya saurareni ba...."

"Allah ya kyauta" abinda nace kenan saboda bana son mu tsawaita maganar ma bare ta kaini gaba nan muka bar maganar duk da haka ban sake mata ba,

A halin yanzu dai ƴan mata biyu ke bibiyar samz bayan Felicia akwai wata wadda shima kansa bai san wacece ita ba sai dai yana mamakin ta yadda ta san abubuwa da dama game dashi ciki kuwa harda ni matarsa ta sani kuma tana ikirarin sai ya sakeni ya aureta bai taba fada min ba nima kuma ban bincika ba dan na san bin diddigin miji bai da amfani, ita Felicia kam dama na san da zamanta kuma na san zabin mahaifiyarsa ce shiyasa abin ban saka shi araina ba amma ita wannan dake bibiyarsa itace tashin hankali na a yanzu kuma na fuskanci hakanne a yau din nan da misalin ƙarfe 11 aka danna min doorbell har kusan sau biyar da yake na shiga wanka, ina fitowa da na buɗe banga kowa ba sai wata babbar paper bag fara nan na kinkima na shiga da ita ciki tunda banga kowa ba ta yuyu wanda ya kawo din shine ya ajiye bayan ya jira yaji shiru,

Zama nayi na soma fito da kayan ciki, wani ɗan ƙaramin box na fara cin karo dashi ina budewa naga zoben azurfa mai kyau, sannan sai wani turare oad na maza shima acikin gidansa sai agogo mai masifar kyau shima acikin gidansa sai kuma greeting cards guda biyu irin wanda masoya ke turawa masoyansu a lokacin bikin wani shagali dan tayasu murna, a jiki ba a rubuta komai ba amma an nuna ana taya shi murnar zagayowar ranar haihuwarshi,ai ji nayi kamar inyi me dan baƙin ciki kuma ban taba sanin inada zafin kishi ba sai yau dan wuni nayi cikin baƙin ciki da damuwa, yana ta kirana normal call da video call kamar yadda ya saba duk lokacin da yake office wuni muke muna waya indai bawai aiki ne yayi masa yawa ba amma yau naki ɗauka haka kuma babu abinda nayi a gidan sai aikin kuka da nasha wannan kam nayi na kara kamar babu gobe dan har sai da idanuwana suka kumbura, haka na wuni naki ci naki shan komai kamar wata mai azumi shi dai yana can baima san abinda yake faruwa ba duk tunaninsa bana tare da wayar ne ko kuma ina ta baccin nawa na sabo, sai da naji yunwa na neman illata ni sannan na hada tea na sha,

Ƙarfe 6 da yan wasu mintuna ya dawo kuma yana waya da mommy ya shigo kamar yadda hakan yazama al'adarsu yanzu, ban wani saurareshi ba yau babu hugging babu kisses babu magana haka na bude masa kofa ina budewa na juya na wuce cikin bedroom, bin bayana yayi da kallo ya zauna a falo a gajiye kuma a kasalance ya ajiye jakar laptop ɗin shi dama yau bai shigo da komai ba saboda jiya ya sissiyo min duk wasu kayan tande tande da makulashe suna nan cike a fridge

Please Login or Register in order to submit comment