Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

zatai tayi tana jiranka sai kace dan kai aka halicce ta? Wallahi tun wuri ka maida hankalinka, baka da aiki sai yawo, wuni zaka yi kana yawo na ba gaira bare ɗan dalili, ba zaka dawo gidan nan ba sai dare kuma daren ma ba na kusa ba, to wallahi ka san inda yake yi maka ciwo.... "

" Iya nifa ba ko ina nake zuwa ba wurin abokaina nake zuwa muke zama muyi hira "

" Kunci gidanku kai da abokan naka, abokan da sai yanzu ka same su asama ta kumfa bayan da duk basa tare da kai lokacin da kana makahon ka, wato yanzu ido ya buɗe har ka samu wanda suka fi mu, ada babu mai zuwa gidan nan da sunan yazo wurinka sai Yarinyar nan Maimunatu ita kaɗai amma yanzu wuni za ayi ana yi min sallama a gidan nan mata da maza da sunan an zo wurinka.... To wallahi ba a gidan nan ba, bazan yarda da wannan ba "

Jin Iya ta isheshi da faɗa ya sake komawa ɗaki yayi kwanciyarsa ya cigaba da chaten ɗinsa ya barta nan tana ta kumfar baki.

Ni kam idan nace bana cikin damuwa ƙarya nake yi, dagaske bada wasa ba naji haushin abin da Hashim yayi min, wai kamar ni intaka ƙafa da ƙafa inje har gidansu wurinsa amma ya watsa min ƙasa a ido yaƙi fitowa ya bar ni nan har in gaji da zama in tashi, ai ko faɗa muka yi ko kuma wani laifin nayi masa bai dace yayi min irin wannan wulaƙancin ba,

Raina aɓace zuciya ta cike da damuwa na hango farida da alama daga masallaci take domin lokacin sallar azahar yayi tun tuni, waving ɗinta nayi nan ta taho wurina tana latsa wayar ta, zama tayi tana faɗin,

"Widat ya ne, you looked some how today, what's happening?"

Murmushin yaƙe nayi wanda yafi kuka ciwo kafin na kalle ta,

"Wallahi babu komai, kawai dai wata friend ɗina ce ke neman shawara nikuma na rasa abin da zan faɗa mata shine duk abin ya dameni, wai saurayinta ne da suke tare yayi mata wulaƙanci....." kwashe duk abin da ya faru tsakanina yau da Hashim a gidan su nayi na faɗawa farida amma na ɓoye cewar nice nace ƙawata ce, ajiyar zuciya farida ta sauke ta kalleni,

" wallahi maza basu da kirki wasun su..... Allah dai ya kyauta amma bai kyauta mata ba sam, wataƙila yanzu ya daina son ta ko kuma wani laifin tayi masa yake fushi, shi dai yasan abin da yake going soo it's better kawai ta tuntuɓeshi taji abin da tayi masa "

" hakane kam, bari infaɗa mata hakan " na faɗa ina ɗaukar wayata, cikin sa'a kuwa na ganshi online, saƙo na tura masa kamar haka,


_Hashim kenan, sanin kanka ne ba wai maula na zo wurinka ba balle ka ajiye ni zaune ina faman jiranka, ai ko laifi nayi maka bai kamata kayi min haka ba gara ka fito fili ka sanar dani abin da ke cikin ranka._

Duk da yana online bai buɗe saƙona ba bare ya bani amsa hakan ya sake ƙular dani amma na danni zuciya ta ban sake ce masa komai ba, har zuwa lokacin da ya buɗe ɗin ya karanta nan ma bai tanka ba duk da naga alamar ya karanta ɗin saboda saƙon ya nuna min blue akan layika biyun dake ƙasanshi, sauka nayi daga online damuwa cunkushe fal raina ɓacin rai danƙare cikin zuciya ta, yau dan takaici wuni guda ban sha koda ruwa ba bare inci abinci, rabona da abinci tun breakfast ɗin da nayi a gida shi ɗinma iya ruwan tea ne sai soyayyen ƙwai ko bread ban ci ba, haka na wuni cikin damuwa duk raina babu daɗi har 5 tayi lokacin na tashi daga aiki na fito na hau napep don komawa gida,

Cikin napep ɗinma cikin ƙunci nake dan abubuwan dake ta faman kai kawo acikin raina masu nauyi da sanyawa zuciya damuwa, ina zaune nayi tagumi da wayata a hannuna danger ta tsayar damu muna tsayawa naji an daki bayan napep ɗin da ƙarfin gaske wanda yayi sanadiyyar da muka tafi muka daki na gaban mu, nidai abin da zan iya tunawa kenan sai buɗe idona nayi na ganni kwance kan gadon asibiti ƴan gidanmu na kewaye dani, kan anty Khadija na fara sauke idona wato babbar yayarmu sai Bishra tana zaune kusa da ita sai Anty Salaha gefe ɗaya kuma Yaya Abdul Hakim ne sai ƙawalli na zaune kusa dani,

"Sannu Widat..... An auna arziƙi" Anty Khadija ta faɗa tana tsotsar farar ƙasa dama duk lokacin da take laulayin ciki ba a raba ta da shan farar ƙasa,

"Sannu ya kike jin jikin?" anty Salaha ta tambayeni tana tasowa zuwa kusa dani,

"Da sauƙi" na faɗa ina riƙe kaina wanda ke yi min azababben ciwo, duk sannu suke ta faman yi min, jikina in banda ciwo babu abin da yake yi min domin na kukkuje na daddauje amma anyi sa'a babu karaya ko ɗaya, ganin ƴan gidanmu da irin hirar da ake yi ta sani na ɗan ware dan har wayata na ɗauka nima na hau online,

"Ohh ni Dije waya ta shiga ran bayin Allah ba kaɗan ba ana gadon asibiti ma chaten ake" Anty khadija ta faɗa tana kallo na,

"Ai abun ba a cewa komai, kin san har a maƙabarta ana chaten? Wai mutum yaje maƙabarta kai mamaci amma ya ɗauko waya yana chaten ko amsa kira...." Yaya Abdul Hakim ya faɗa,

"Last time da naje umarah abin ya bani mamaki Hakim wai har a ɗakin Allah sai ka ga mutane da waya a hannu ana chaten ko wani abu me kama da haka, wanda ya je ibada dan Allah me ya haɗa shi da wannan?" Anty khadija ta faɗa tana jijjiga kai alamar ɓacin rai,

" Anty kin manta yanda rayuwar duk ta taɓarɓare ne? Ai abin sai addu'a kawai " Anty Salaha ta faɗa tana duba takardar dake maƙale a jikin gado na,

Nikam status nayi da cewar ina gadon asibiti na samu accident jiya da yamma ina buƙatar addu'ar ƴan uwa da abokan arziƙi, nan take aka fara yi min fatan samun lafiya tare da kyakkyawar addu'a, gaba ɗaya contacts ɗina kowa yayi min addu'a da sannu wasu ƙafa da ƙafa ma suka zo suka dubani musamman ƴan office ɗinmu da friends waɗanda ke kusa amma banda Hashim duk da ya duba status ɗin nawa ya gani amma ko uffan bai ce ba, hatta Yaya Faisal sai da ya kirani ya dubani dan har yanzu muna ganin status ɗin juna duk da yayi aure watanni huɗu baya da suka wuce amma har gobe muna ɗan gaisawa ko ta chat ne dan har yana ce min so yake ya samu leave zai kawo mana matarshi gida mu gaisa,

Wannan abu da Hashim yayi min shi ya sake ɓata min rai dan confirm yaga status ɗina amma ko sannu maimakon haka ma shi sai status yake ta sakawa a wani katafaren boutique na zamani wanda ya haɗu ƙarshen haɗuwa ya sha decoration shi kansa Hashim ɗin ya haɗu cikin wasu arnan jeans da t shirt baƙaƙe abin ka da farin mutum ya haska sosai idanuwansa sakaye cikin baƙin glass, gefensa wata farar mata ce kyakkyawa itama idanuwanta rufe ruf da baƙin glass wanda ya amsheta sosai da wasu mutane zagaye suna yanka cake da gani bikin buɗe wannan boutique ɗin ake yi kuma ko tantama babu wannan matar itace mamallakiyar wurin domin naga wani hoton nata na daban Hashim ɗin ya ɗora yana cewa "the C. E. O", shiru nayi na gama kallon status ɗinsa tsab sannan na ajiye wayata acikin raina ina saƙa abubuwa da dama........

*Garin dadi littafin kudi ne ga mai bukatar cigaban labarin sai ya tura 500 ta 0774712835 Aisha Ibrahim Access Bank sai a tura evidence of payment ta wannan no 07044644433 ko a tura katin waya da shaidar biya wannan no 07044644433*


_*Ummi Shatu*_👌🏻
[1/5, 12:43] Maman K: ©️ *HASKE WRITERS ASSOCIATION*
_(Home of experts & perfect Writers)_




*GARIN DAƊI.......!*💍💍



*_NA_*


*_UMMI A'ISHA_*



*Wattpad:ummishatu*



*13*



~~~Duk irin yadda na so in ɓoye damuwata kasawa nayi dan gaba ɗaya nayi wani irin muzu muzu dani duk na fiffige kana ganina ka san akwai abin da yake damuna, ada na tsammani zan iya yin pretending in danne ba tare da wani ya gane ba amma kash labarin zuciya a tambayi fuska,

Zaune nake tsakiyar gadon da aka kwantar dani hannu na riƙe da wayata ba komai nake kallo ba illa pictures ɗinmu nida Hashim waɗanda muka yi a lokacin da bai samu lafiya ba a lokacin yana makahonsa sai dai duk da baya gani a lokacin rayuwa tafi yimin daɗi dashi saboda ko babu komai yana da lokacina sosai kuma muna baiwa junanmu kulawa cikin so da ƙauna tare da ririta juna saɓanin yanzu da abubuwa suka rincaɓe suka tsananta komai babu daɗi,

Shigowar ƴan gidanmu ce ta sani ajiye wayar ina kallon su ɗaya bayan ɗaya mama ce kan gaba sai anty Khadija, Bishra da yaya Abdul Hakim shine ƙarshen shigowa,

"ya na ganki ke kadai ina ƙawar taki?" anty Khadija ta buƙata tana ƙoƙarin zama kusa dani,

"Tana zuwa anty abu ta fita siyowa"

Anty bata ƙara magana ba muka fara gaisawa dasu mama suna yi min ya jiki gefe ɗaya ga abincin da suka zo da shi da su fruits da dai sauran su ahaka har ƙawalli ta dawo daga siyan pad ɗin da ta tafi shagunan waje domin taje na cikin asibitin wai ya ƙare.

Har na ƙaraci zamana a asibiti nagama tsawon sati biyu Hashim bai yimin ko sannu ba bare har in sa ran zai zo ya duba ni haƙiƙa wannan abu yayi min ciwo mutuƙa, ranar da aka sallame ni muka tattara muka koma gida nida ƴan uwa na domin na warke sumul sai dai ɗan abin da ba a rasa ba dan har yanzu wani ciwon bai gama warkewa ba caan gida na cigaba da kula dashi.

Sai da na warke tass sannan na koma aiki washe garin ranar da na koma na shiga kasuwa nayiwa su Iya siyayyar kayan abinci kamar yadda na saba, duk da Hashim ya nuna bai damu da rayuwata ba yanzu to ni ba saboda shi zanyi ba dan Allah zanyi,

Napep na samu ya zuba min kayan muka tafi, muna shiga unguwar shima Hashim yana shigowa nan mai Napep ya sauke min kayan ina ƙoƙarin sallamarsa Hashim ya ƙaraso, ƙananan kaya ne a jikinsa fuskarsa ɗauke da baƙin tabarau,wani irin kallo na wulaƙanci da ƙasƙanci yake bin kayan dasu kafin naga ya tare ƙofar gidan alamun baza a wuce a shiga ciki ba,

"lafiya? Wannan kayan fa?"

Zuciya ta na danna sannan na danne fushi na nace,

"Hashim baka gane ni bane??"

"To idan ma ban gane ki ba menene? Ki kwashi tarkacenki kiyi gaba ba a buƙata anan"

Da mamaki nake kallonsa kafin nima in murtuke fuska kamar yadda yayi,

"Idan kana tsammanin saboda kai na kawo kayan nan to kayi kuskure, ni har na manta da wata aba wai rayuwar ka ma dan ni mutanen kirki ne a gaba na bana banza ba, kuma taimakawa mai buƙatar taimako ba kanka na fara ba,bare ingama a kanka...."

"To ki kwashe kayan ki ki ƙara gaba dan ba zaki shiga gidan nan ba, kin zama tauraruwa mai wutsiya ganin ki ba alkhairi ba, tunda nake da tsohuwa ta bata taɓa yin fushi dani ba sai ta dalilin ki yanzu ko gaishe ta nayi bata amsawa duk saboda ke.... Wallahi Maimunatu na tsane ki kuma nayi dana sanin sanin ki, tir da kasancewarki a cikin rayuwa..... "

" Tabbas Bahaushe yayi gaskiya da yace Tsintacciyar mage bata mage...... Dole kace kayi dana sani tunda ada acikin duhu kake rayuwa yanzu kuma Allah ya kawo maka WANI HASKE wanda ya yaye maka wannan duhun har kake iya ganin gabanka sannan kake iya bambance tsakanin ƙasa da gari, to ka sani dan kayi dana sanin sanina a rayuwa ba laifi bane dan dama wannan ɗabi'a ce ta dabbobi mayar da masoyi ya koma maƙiyi sannan dan ka tsaneni ai ba kai ka halicce ni ba bare hakan ya dameni..... Daga ƙarshe karka yi tir da kasancewata acikin rayuwar ka domin already na fita, kaje kayi rayuwa da duk wanda kake so kuma ka zaɓa..... Sannan gida da kake maganar bazan shiga ba sam banga laifin ka ba amma kaje ka bincika gidan Alƙali Mukhtar Garzali na tabbata zaka samu gidan ubana ya ɗara wannan sau dubu dan ko B/Q ɗin gidanmu tafi wannan akurkin daraja sau dubu.......Mtswwww " tun kafin in ƙarasa naji saukar mari tauuu, cikin zafin rai na ɗaga ido na kalleshi, kafin na ankara shima gani nayi an ɗauke shi da mari wanda ba kowa bane face mahaifiyarsa,

" Hashimu rashin mutuncin da butulcin har ya kai haka? "

" Hajiya zo mu tafi, ba girman ki bane sannan kuma ba mutunci ki bane ki zauna akan layi ana irin wannan dake ba, tunda yace ba zaki shiga gidan nan ba ki rabu dashi muje kawai...." Juyawa nayi ina kallon mai Napep ɗin da ya saukeni ashe bai tafi ba duk wannan dramar akan idonsa ta faru, sai lokacin naga mutanen da Hashim ya tara min wanda sam da ban san dasu ba, sai kace ana ɗaukar film saboda irin yanda mutane suka taru suna kallonmu, ban jira komai ba na wuce na shiga Napep na bar Hashim da mahaifiyarsa tana yi masa faɗa kamar zata dafashi ta cinye, idanuwa na jajur ina shafa marin da Hashim yayi min kamar acikin mafarki nake kallon lamarin wai yau nice Hashim ya mara,

"Ai hajiya kin burgeni da kika mayar masa da maganar da ya faɗa miki, na san maganganun da kika jefe shi dasu su zasu hana shi bacci a daren yau.... Irin waɗannan samarin basu da mutunci ko iyayen su ma basu ɗauke su a bakin komai ba to kinga kuwa wa zasu gani da mutunci? Ke kuwa ƴar gidan masu mutunci ce daga gidan mutunci kika fito, mahaifinki ubane a wurin kowa a cikin garin nan babu wanda bai san shi ba...... Ni kaina nan wallahi kallon uba nake yi masa domin uban ne "

Jin abin da mai Napep ɗin nan ke faɗa ya tuna min da karamci da kuma ƙoƙari na mahaifinmu bawai iya musulmi kaɗai ba har waɗanda ba musulmai ba dan da kunnena naji wata Christian tana cewa" wannan mutumin uba ne " bata ma san ina da alaƙa dashi ba, har muka isa unguwar mu mai Napep yana yabon mahaifina da irin taimakon da yake yi wanda hakan ne ya rage min kaso mai yawa na ɓacin ran da nake ciki, a ƙofar gidansu ƙawalli na sauka har zan shiga naji mai napep yana tambaya ta,

"Hajiya kayan naki fa......"

"kaje dashi na bar maka"

"Allah yayi miki albarka ya yi miki sakayya da gidan aljanna...."

"Amin" na faɗa ina ƙoƙarin shiga gidansu ƙawalli zuciya ta na faman tafarfasa kamar zata tarwatse,

Tana cikin bathroom tana wanka zama nayi kan gadonta ina jiran fitowarta dan ji nake kamar idan ban amayar da abin da ke damuna yana yimin yawo a cikin zuciya ba yau ɗin nan komai na iya faruwa.

Can gidansu Hashim kuwa bayan tahowata Iya cigaba da balbala masa faɗa tayi ta inda take shiga ba ta nan take fita ba,

"Marar mutunci butulu, yarinyar da ta ɗaukoka daga rana ta saka a inuwa yau ita kake ƙoƙarin turawa rana.... Ita kake tozartawa a gaban mutane saboda baka gaji mutunci ba...."

"To wai Iya nan gidan ubanta ne da dole sai ta shiga?"

"Kaima ai ba gidan ubanka bane.... Koda ubanka ya mutu bai bar min gida ba nan gidan ɗan uwanane dan haka kaima ka tattara ka bar min gidana tunda kai ba ɗan goyo da zani bane"

"akan waccan yarinyar kike cewa inbar gidan nan"

"ehh akanta, maza ka tattara naka ya naka kaje duk inda zaka je"

Ɗakinsa ya shiga bayan kamar mintuna biyu ya fito riƙe da jaka ƴar goyawa,

"Wallahi idona idon Maimunatu sai na wulaƙanta rayuwar ta tunda ta zama silar rabuwa ta da mahaifiya ta"

"kaje kayi mata duk abin da zaka yi karka fasa amma kar ka manta itama da gatanta dan gatanta ma yafi naka, ubanta Alƙali ne kuma yayunta ma haka dan haka kamaka zasu yi su ɗaure har sai igiya tayi rara karka ce ban baka labari ba......"

Bai tsaya ba bare ya tanka kawai saka kai yayi ya fice daga gidan har lokacin iya na faman faɗa kamar zata ari baki, Amira ce ta shigo tana sanye da kayan makarantar islamiyya,

" Iya... Iya yanzu naga yaya Hashim da jaka, korarsa kika yi? "

" korarsa nayi Amira yaje can ya samu wata uwar...."


*Garin dadi littafin kudi ne ga mai bukatar cigaban labarin sai ya tura 500 ta 0774712835 Aisha Ibrahim Access Bank sai a tura evidence of payment ta wannan no 07044644433 ko a tura katin waya da shaidar biya wannan no 07044644433*



_*Ummi Shatu*_👌🏻
[1/5, 12:43] Maman K: ©️ *HASKE WRITERS ASSOCIATION*




*GARIN DAƊI.....!*



*_NA_*

*_UMMI A'ISHA_*



PAID BOOK



14


~~~Lokacin da ƙawalli ta fito nayi zurfi cikin tunani har sai da ta taɓa ni sannan na dawo cikin hayyacina na kalle ta da idanuwa na waɗanda suka yi jajur kamar gauta,

"ƙawalli lafiya kuwa? Me ke damunki?" ta tambayeni tana ƙokarin zama kusa da ni tare da dafa kafaɗa ta,

"ƙawalli ban san ta yaya zan kwatanta miki irin halin da zuciya ta take ciki ba..... Ina cikin matsananciyar damuwar da ni kaina ban san adadinta ba....... Gaba ɗaya jina nake a wata duniya ta daban ba wannan tamu wadda na sani kuma na saba da ita ba...... " Gaba ɗaya abin da ya faru tsakanina da Hashim na kwashe na sanar da ita tun daga farkon haɗuwar mu har kawo yau da abin da ya faru babu abin da na ɓoye mata,

Tunda ta gama sauraren labarin da na bata wanda yafi kama da tatsuniya tayi shiru tana kallo na kamar ruwa ya ci ta, ni kuma sai lokacin na samu damar zubar da hawaye na waɗanda suka jima suna suna ƙona zuciya ta,

"Haƙiƙa widat kin yi kuskure babba ba ƙarami ba..... A wannan zamanin da muke ciki yanzu ai ba kowane zaka yi masa alkhairi bai butulce maka ba daga ƙarshe shiyasa alkhairinma ake tsoron yinsa, kuskure na farko da kika yi shine ƙin sanar da kowa ko kuma rashin neman shawarar kowa cikin wannan al'amari, da ace kin nemi shawara da duk hakan bata faru ba saboda me shawara aikinsa baya ɓaci..... Amma babu komai tunda dai aikin gama ya gama, yanzu kawai karki sa damuwa acikin ranki ki manta komai kuma ki ɗauka kamar ba ayiba, shi ma Hashim ki sa aranki kamar baki taɓa haɗuwa dashi ba a cikin tarihin rayuwar ki "

Hawayen dake zuba a idanuwa na ta share tana ci gaba da rarrashina, ni kam sai da na ci kukana na more sannan nayi shiru amma nasa araina sannan na yiwa kaina alƙawarin mantawa da Hashim da dukkan rayuwarsa gaba ɗaya koda kuwa shi ne autan maza duk na san ba abu ne mai sauƙi ba manta butulci musamman ga mutumin da ada ba komai ba ta sanadiyyarka ya zama komai sannan daga baya yazo ya ɗauke ka babban maƙiyinka.

Tare da ƙawalli muka tafi gidanmu tana sake kwantar min da hankali, mun jima muna hira kafin ta tafi, ni kam ko abincin dare yau ban ci ba haka bacci shima na kasa sai juyi kawai nake yi raina cike da damuwa, tunda na zo duniya ba a taɓa cimin mutunci irin wannan ba, babu wanda ya taɓa wulaƙantani kamar yanda Hashim ya wulaƙantani yau, kwata kwata kasa runtsawa nayi sai bayan asuba sannan bacci ɓarawo ya samu nasarar yin awon gaba dani.

Tsawon kwana da kwanaki na ɗauka cikin hali na damuwa da rashin walwala dan hatta abinci wannan daƙyar nake daurewa ina ci amma ba wai dan ina jin daɗinsa ba, kuka kuwa kusan kowanne dare sai na yishi dan har ya zame min sabo saboda da rana zan ɗan yi al'amura na zan fita aiki zan haɗu da abokan aiki na zamu tattauna za ayi hira ayita dariya ina jin su kuma ina zaune ina kallon kowa amma da zarar na dawo gida sai inji ƙuncin duniya da damuwa sun taru sun lulluɓeni wani lokacin ma inji duniyar gaba ɗaya ta isheni gashi in nemi bacci a idona inji na rasa, gaba ɗaya dai rayuwar ina yin ta ne cikin ƙunci da damuwa sam bani da wata walwala gaba ɗaya na rasa farin ciki abinci wannan wani sa'ilin kasa ci nake yi shiyasa duk na rame na lalace sai uban ƙashin wuya da nake ta fama dashi,

Kowa ya ganni yasan ina cikin damuwa kuma akwai abin da ke damuna amma duk wanda ya tambayeni cikin yayuna ko su Annie sai ince babu komai, daga ƙarshe da Annie taga abun ya isheta anty khadija ta kira babbar yayarmu tace ita ta kasa gane kaina kullum ina cikin damuwa kuma ganina cikin wannan hali itama nata hankalin tashi yake dan Allah ta kirani in je wajen ta in yi kwana biyu ko zan ɗan warware dan tayi min juyin duniyar nan tana tambaya ta amma naƙi na sanar da ita damuwa ta,

Sam ban san sunyi haka ba, bayan na dawo daga aiki ina ɗaki kamar yanda na saba zama ni ɗaya cikin ƙunci tare da tunani marar amfani ba wai tunanin Hashim ba a'a asalima tun daga ranar da yayi min wannan wulakancin ban ƙara tuna shi ba cikin raina kawai dai ta dalilin abin da yayi min ne na rasa farin ciki da walwala kuma na shiga ƙunci da damuwa, shiyasa kullum cikin tunanin makomar rayuwa ta nake, ƙarar waya ta ne ya cika ɗakin amma har tayi ta tsinke ban ji ba saboda hankali na baya wurin, sai akaro na biyu sannan naji shi ɗinma yana dab da tsinkewa, ganin anty ce ya sani hanzarin ɗauka,

"hello anty...."

"uhmm..... Widat bacci kike yi ne?"

"a'a anty, idona biyu"

"to ya aiki, an dawo an gaji ko"

"wallahi anty kamar kin sani"

"ato ba nace ki zama lawyer Irina ba mu baki aiki a chamber ɗinmu ba kin ƙi...."

"kai ai anty wannan aikin naku sai ku, haba taya zan iya zuwa tsakiyar mutane in tashi ina bayani kowa na kallo na"

Dariya anty tayi kafin naji tace,

"ni kuwa kinga ko yau sai da na shiga court can ma naga yayanki, shi ya je kare wanda ake ƙara nikuma ina kare masu ƙara...."

Cike da mamaki na gyara zama na dan jin wannan abun al'ajabi,

"Anty.... Kuma ya aka yi? Dama ana yin haka? Wanne daga ciki ma tukunna? Yaya Abdul Hakim ko yaya Abdul Majid?"

"Abdurrahman dai....."

"kuma anty yaya kuka yi? Baku nuna kun san juna ba?"

Dariya ta sake yi sannan naji tace,

"ina ruwana dashi, kowa aikinsa yayi, yayi nasa nayi nawa ko gaisawa ma ba muyi ba, to ke in banda abin ki sau nawa ina zuwa kotun Abba amma ai ba sani ba sabo, ita shari'a haka take, kuma da kike cewa ba zaki iya tsayawa gaban mutane ba naga kema inda kike aikin gaban students kike tsayawa "

" Anty ai wannan ba irin naku bane..... "

" menene bambanci munatu? Yanzu dai nan da friday ina so ki shirya ki taho nan Abuja wurina, akwai wani aiki da zan saki ankusa fara training...... "

" Anty zan iya kuwa.... " tun kafin in ƙarasa ta katse ni,

"Na san zaki iya ɗin ne ai yasa nace kizo, ki rubuta leave a wurin aikin naku"

"to shikenan Anty, yaushe zan taho?"

"ki taho Friday, bari zan turo miki kuɗin abin hawa"

"Anty na jirgi fa zaki turo"

"bakida matsala tawan"

Sallama muka yi na kashe wayar ina murmushi jin muryar anty har yasa na ɗan ji sanyi araina, ita dama tana da kula kuma ta iya tafi da damu dan mun fi shiri da ita fiye da anty salaha, ita anty salaha bata da yawan magana sannan ba kasafai ake zama da ita ayi hira ta ji matsalar ka ko damuwarka ba saɓanin Anty wanda ita da kanta zata kiraka tana tambayar ka babu wata damuwa ai ko? Ko dan kasancewarta lawyer ne ban sani

Please Login or Register in order to submit comment