Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

acikinsu amma hakan ya sanyaya raina ganin suna rayuwa cikin farin ciki, suma kenan da halittarsu ta samu tawaya sun fawwalawa Allah komai suna rayuwa cikin godiyar ubangiji da farin ciki ina ga mu da Allah bai tauye mana komai na halitta ba ya zama dole mu kasance cikin hali na godiya da kuma takatsantsan akan duk wani abu da ya haramta,

Neman hashim na shiga yi ina yi ina tambayar ma'aikatan wurin da haka har aka kai ni wani wuri mai kama da office inda yake zaune kan kujera da wata na'ura gabansa yana yin typing sai dai tasu na'urar ba irin tamu bace masu idanu akwai bambance bambance masu tarin yawa, jin motsin shigowa ta yasa shi saurarawa daga abin da yake yi yayin da ni kuma nayi shiru ina takowa a hankali har na zo dab dashi ɗan karkato da kanshi yayi kafin naga yayi murmushi ya cigaba da aikin sa, zuwa can yace,

"munatu na ya aka yi kika san cewa ina nan? waye ya kawo ki?"

Murmushi nayi na nemi wuri na zauna kan wata kujerar roba koriya,

"kayi mamakin ganina ne a wannan lokaci?"

"a'a banyi mamaki ba, kawai dai na tambaya ne"

"Rakoni aka yi"

"to barka da zuwa, bari yanzu zan ƙarasa sai mu tafi"

"to shikenan"

Wayata na ciro daga cikin handbag ɗina ina yi masa hotona shi kuma yana cigaba da aikin sa har ya kammala. Gidansu muka wuce direct dan ina so inji ko iya ta samu zuwa gidan ɗan bahago, ita kaɗai muka tarar a gidan tana zaune ta kunna radio tana saurara maganin zaman kaɗaici, shigowarmu ya sanya ta kashe radion tana yi mana sannu da zuwa, nidai a tsattsaye muka gaisa na soma tambayarta ya maganar zuwanta wurin iyalan ɗan bahago?

"insha Allah dama gobe nake son zuwa, sammako ma zanyi da yardar Allah kan azahar na dawo"

"to shikenan iya ubangiji Allah ya kiyaye hanya sai kin dawo ɗin"

Sallama muka yi dasu na tashi na tafi kuma tun ina cikin napep naga manager na kirana amma ban ɗauka ba har sai da na sauka sannan na kira shi nan yake faɗa min komai ya zama daidai insha Allah zasu bani loan ɗin da na buƙata godiya nayi masa muka yi sallama na shiga gida.

Kamar yadda na tsara hakance ta kasance ba tare da wani kuskure ba domin na samu duk kuɗaɗen da nake buƙata, sannan cikin Ikon Allah lokacin da Iya taje gidan Malam Ɗan bahago ta iskeshi ya dawo daga doguwar tafiyar da yayi shekara da shekara a ƙasar Mali nan suka shirya maganar yadda zasu tafi Chadi domin shine zai yi musu jagora har zuwa gidan mutumin da yace shine zai baiwa Hashim maganin lalurarsa da izinin ubangiji,a ranar da na ɗauki adashena na haɗa da kuɗin wurina wanda na karɓi loan na kai musu domin cikin satin nan zasu yi tafiyar, ban tsaya iya nan ba har sai da na siyo musu wayar hannu mai sauƙin kuɗi wacce zasu iya sarrafawa domin jin halin da suke ciki domin tafiya ce zasu yi ta mota ba wai jirgi ba sannan hanyar cike take da ƙalubale kala kala kamar yadda Malam Ɗan bahago ya faɗa.

Tamkar zanyi kuka lokacin da naje yi musu sallama saboda da asuba zasu kama hanya gobe, duk nabi na shiga damuwa jikina yayi sanyi, tafiyar nan da Hashim zai yi ina ji ajikina kamar zan rasa wani ɓangare ajikina mai muhimmanci sai yanzu ne na gane irin ƙarfin girman shaƙuwar da muka yi dan na kasa ɓoye damuwata ji nake kamar inbisu mu tafi tare ayi komai akan idona in gani, shi da kansa sai da ya fahimci ina cikin matsananciyar damuwa daga ƙarshe yace to ko dai a fasa tafiyar tunda hakan na neman sakani cikin damuwa?,

Hawayen dake tsere akan kumatuna na goge sannan cikin raunin zuciya nace,

"A'a dan Allah karku fasa Hashim, lafiyarka itace gaba da komai awurina, kuje Allah ya kiyaye hanya ya dawo daku lafiya"

Shima ɗin dai cikin damuwar yake sai dai yafini dauriya, na gane hakanne ta dalilin yanda muryarsa tayi sanyi kana ji kasan akwai wani raɗaɗi dake nuƙurƙursar can ƙasan ransa, haka dai muka rabu zuciyoyinmu duk babu daɗi kowa yana jin zafi da raɗaɗin rabuwar da za muyi na tsawon lokaci domin Allah kaɗai yasan ranar dawowarsu,nidai har naje gida ina kukan zuci, hawayen ne dai nayi ta maza wurin dakatar dasu da hanasu zubowa sai dai suna nan suna kwaranya cikin zuciya ta wanda hakan shi yafi komai illa ga zuciyar tawa,hatta bacci daren ranar gagarata yayi sai dab da asuba sannan na samu ya saceni.

Misalin ƙarfe 10 na safe na tashi daga nannauyan baccin da na jima inayi mai cike da mafarkai kala kala wanda duk basa rasa nasaba da tafiyar Hashim wanda na san dan dai na saka abun a raina ne shiyasa nake ta yin mafarkai iri iri, wanka nayi na fito na shirya cikin doguwar riga milk colour, wayata na ɗauka ina duba miss calls ɗin da aka yi min lokacin da ina bacci, Bishra ce da Manager sai su Hashim, su Hashim ɗin na fara kira amma wayar bata shiga har na gaji na daina ma kiran na haƙura na ajiye wayar na fita, haka dai yau na wuni nidai gani nan gani nan ne dai gashi wannan Manager ɗin ya takura min da kira daga ƙarshe da na gaji na ɗaga,

"Ranki ya daɗe na dameki ko? Kiyi haƙuri na kasa jurewa ne wallahi, tun ranar da na ganki naji kin shiga raina lokaci guda, to ina ta so in sanar dake amma baki bani lokaci ba, kamar dai yadda kika sani sunana Ahmad Idris, ni haifaffen garin Kano ne amma asalinmu ƴan Albasu local Government ne, mu biyu ne a wurin iyayen mu daga ni sai ƙanwata zarah, nidai yanzu babu abin da nake buƙata wanda ya wuce in samu matar aure, mahaifiyata itama kullum maganarta in samo matar aure..... To kin san ba wai matan ne babu ba a'a nagari masu mutunci da halin ƙwarai sune ba afiya samu ba amma ke dai insha Allah ina kyautata miki zato kuma na san insha Allah ba zanyi dana sani ba...... Maimuna ki bani dama in aure ki... "

Ajiyar zuciya na sauke bayan gama jin duk waɗannan uban bayanan da ya rattaɓo min, cikin sanyin muryata wadda ta haɗu da damuwar da nake ciki nace,

" Nagode sosai da soyayyarka, sai dai zan baka haƙuri saboda akwai wanda muka yi alƙawarin aure tare dashi kuma duk mun yi amanna muna son junanmu,da ace babu alƙawarin wani a kaina da babu abin da zai hanani baka damar neman aure na"

Shiru naji yayi irin shirun da yaya Faisal yayi lokacin da na sanar dashi na fasa aurensa, bayan wasu mintuna naji yace,

"Shi wanda kuka yi alƙawarin auren dashi ya tura gidanku ne an amince anbashi ke?"

"Ehh.." na faɗa aƙule domin na fara ƙosawa da waɗannan maganganun nasa masu kama da ƴaƴan barkono tsabar zafin su a cikin raina,

"To shikenan Allah ya tabbatar da alkhairi ya sanya albarka, ina yi miki fatan alkhairi"

"Amin, nagode"

Ajiye wayar yayi daidai da shigowar ƙanwata Bishra wacce take bina,

"Yaya Widat inata kiran wayarki baki ɗauka ba"

"Ban tashi daga bacci ba lokacin, ya aka yi?"

"Lafiya Lau.... Ashe wai bikin Yaya Faisal next 2 months ko"

"Allah yasanya alkhairi" na faɗa adaƙile dan yau ɗinnan sai a hankali sam bana son hayaniya.
***
Yau kimanin watanni uku kenan da tafiyar su Hashim kullum muna waya dasu kuma muna gaisawa suna sanar dani irin cigaban da ake samu wurin maganin da ake yi masa wanda insha Allah ana sa ran samun nasara. A ɓangaren Hashim yafi kowa farin ciki domin ya jima yana burin tozali da kyakkyawar fuskar masoyiyarsa kuma abar ƙaunarsa wadda bashi da kamarta duk duniya kuma ko gaba baya jin zai samu kamarta balle wacce ta fita, shi kansa yanzu yasan yana samun sauƙi domin duhun da yake gani yana yayewa sannu sannu amma har yau dai bai fara gani ba sai dai yana ganin wannan duhun yana raguwa lokaci zuwa lokaci wanda insha Allah da haka da haka zai gushe gaba ɗaya kamar yadda mai maganin ya faɗa musu.

Yau dai itace rana ta ƙarshe da Hashim zai gama amfani da maganin da aka bashi wanda yake wanke fuskar shi dashi, tunda ya faɗa min daren jiya banyi bacci ba kwana nayi ina sallar nafila da karatun Alqur'ani inata yi masa addu'a akan Allah yasa adace kuma ya bashi cikakkiyar lafiya mai ɗorewa,

Tun asussuba nake ta kiran su amma ban samesu ba haka na haƙura na shirya na tafi wurin aiki, har na taso daga aiki ban samesu ba su kuma basu kirani ba, haƙura nayi na yada zuciya ta kuma na kwantar da hankali na,daga ƙarshe gidan su ƙawalli ma na shiga dan kawar wa da kaina tunani muka kuwa sha hirarmu zuwa magariba na dawo gida,

Ina zaune kan abin salla bayan na idar da salla kamar yadda ƙa'idata take duk bayan sallar magariba na kan zauna in yi tasbihi da karatun Alqur'ani har zuwa lokacin sallar ishah, wayata ce ta katseni daga karatun da nake yi inda nake karanta suratul Ibrahim, ganin su Hashim ne sai da naji gabana ya faɗi da wani irin matsanancin ƙarfi,nan nayi sallama duk a duburce,

"Amincin Allah ya tabbata ga ma'abociyar kyau da cikar halitta, Sarauniya wacce babu kamarta, ma'abociyar kwarjini da kuma kyautatawa..... Tabbas kece bugun numfashi na, idan har babu ke rayuwa ta bata da sauran amfani domin idanuwa na ke kaɗai suka cancanci suyita kallo har ranar da zan koma ga Mahalicci na wanda ya buɗe min idanuwa na ta silarki tare da taimakonki da kuma jajurcewarki..... Dan Allah ki bani dukkan umarnin da kike so zana bi, ki buƙaci dukkan abin da kike buƙata daga gareni nayi miki alƙawarin zanyi.... Wai dama haka duniyar nan tamu take? Ashe haka duniya ke cike da abubuwan kyawu gami da ban mamaki.... "

Kasa motsi nayi sai hawayen farin ciki dake kaiwa da komowa daga idanuwa jin wai idanuwan Hashim sun buɗe, ban san lokacin da nakai goshina ƙasa ba dan yin sujjadar godiya ga ubangiji na......... ✍🏻


*Garin dadi littafin kudi ne ga mai bukatar cigaban labarin sai ya tura 500 ta 0774712835 Aisha Ibrahim Access Bank sai a tura evidence of payment ta wannan no 07044644433 ko a tura katin waya da shaidar biya wannan no 07044644433*

*_Ummi Shatu_*👌🏻
[1/5, 12:43] Maman K: ©️ *HASKE WRITERS ASSOCIATION.*
( _Home of experts & perfect writers_)



*GARIN DAƊI.......!*💍💍


PAID BOOK


*_NA_*


*_UMMI A'ISHA_*


*Wattpad:ummishatu*



*11*


~~~Wuni guda cur nayi a gidan su Hashim sai zuwa yamma nayi sallama da Iya, tare muka jera dashi ya rakani wanda har sai da muka yi tafiya mai nisa muna tafe muna hirarmu, kallo ɗaya zaka yi mana ka gane masoya na waɗanda basa son rabuwa da juna, daƙyar muka rabu na hau napep don ya ƙarasa dani gida shi kuma ya juya, ni kaina saida nayi mamakin doguwar tafiyar da muka yi da Hashim a ƙafa wanda idan ni kaɗai ce nasan koda kuɗi ban isa nayi wannan tafiyar ba,

Gidan su ƙawalli na fara tsayawa na shiga bakina har kunne murna fal ciki na kuwa yi sa'a yau bata je islamiyya ba, cikin farin ciki na zauna kusa da ita ina zame ɗan gyalen dake kaina,

"Albishirinki....... Ƙawalli idon Hashim ya buɗe kuma kin san wani abu?"

"a'a ban sani ba sai kin faɗa" ta faɗa tana kallo na kamar yau ta fara ganina,

"Daga ni har shi mun yi wa juna, wallahi ada inata jin tsoro da fargaba kar ya ganni ban yi masa ba amma koda na ɗan bugi cikin sa sai naji ba haka bane nayi masa 100%"

"Allah sarki, to Allah ya bar ƙauna yasa ta ɗore..."

Kasaƙe nayi ina kallonta tare da jin haushin kalamanta musamman na ƙarshe wai wani nan Allah yasa ta ɗore,

"to me kike nufi?" na faɗa cikin gimtse fuska,

"ah kinga ni kar kiyi min fassara babu abin da nake nufi sai alkhairi....."

"to ai naji ne kamar baki ɗauki maganar tawa serious ba"

"ni kinga duk ba wannan ba, kin san me? Nima nayi saurayi kuma insha Allah nanda ɗan wani lokaci zai fito neman aure na"

Duka na ɗaka mata cike da mamaki nace "shegiya ƙawalli dama kin yi kamu shine baki faɗa min ba sai yanzu?"

"uhmm ba haka bane ƙawalli, ada bai bayyanar min da kansa bane sai yanzu, kuma ma dai na gida ne"

"kamar ya? Ban gane na gida ba, waye?"

Bata amsa min ba ta janyo wayar ta dake ajiye kusa da ita ta buɗe sannan ta miƙo min, cike da mamaki na ɗago na kalleta bayan na gama kallon pic ɗin,

"Yaya Abdul hakim....."

Murmushi tayi ta ɗaga min kai tana kallona,

"Wallahi ƙawalli ku munafukai ne daga ke har yaya Abdul hakim ɗin..... Tun yaushe kuka fara soyayya?"

Dariya ta fashe da ita sannan ta jingina tana kallo na,

"Mun kai 4 years muna soyayya amma babu wanda ya sani, sometimes muna tare dake zaki ji an kirani to dashi nake waya bada kowa ba, dan ke kanki shaida ce banda saurayi, shi kaɗai ne"

"amma kuna soyayya shine daga ke har shi baku taɓa nunawa ba ƙawalli? Ni kaina ban taɓa ganewa ba fa"

"iya takune kawai na yayanki"

"uhmm lallai, ai kuwa ba kiyi dacen miji mai haƙuri ba ga shegen muguntar tsiya"

Dariya ta sake yi kafin tace "ya isheki haka kibar zagar min miji"

Tashi nayi na haɗa nawa inawa na tattara na tafi tana biye dani har zuwa gidanmu, muna zuwa bakin gate yaya Abdul hakim na fitowa, basarwa yayi saboda azatonsa har lokacin ban san suna soyayya da Maryam ba, dariya kawai nayi zan wuce naji yace,

"Ke, dariyar me kike yi?"

"babu komai yaya kawai dai wani abu na tuno" daga haka na wuce na barsu shida ita tsaye, sai bayan da na jima da shiga gida sai gata ni duk tunanina ma ta koma gida ashe tana wurin mutumin.
***
BAYAN WATA TAKWAS
**
Tun bayan samun lafiyar Hashim babu wata matsala da zance munci karo da ita a soyayyar mu, mun shaƙu iya shaƙuwa dan koda yaushe muna tare sannan har yau nice ke yi musu siyayyar kayan abinci duk ƙarshen wata duk da uban tulin bashin dake kaina wanda ban gama biya ba, me zai faru? Kwatsam sai na fara ganin canji a wurin Hashim duk da babu wani abu na saɓani da ya haɗamu,

Yanzu ba sosai ma muke haɗuwa ba saboda baya zama agida kullum yana da wurin zuwa musamman yanzu da yayi friends maza da mata, kullum sune yawon zuwa birthday party, picnic da sauran bukukuwa na manyan yara, ƴanmata kuwa abun ba acewa komai saboda Hashim na da kyau irin kyawun da yake ɗaukar hankalin kowacce mace, a yawon zuwa party ɗinsu ya haɗu da wata sugar mommy hamshaƙiyar mai kuɗi wadda mijinta ya rasu ya bar mata dukiya kaca kaca, gashi bata taɓa haihuwa ba, a haife zata kai kimanin shekaru 50,tana zaune harabar hotel ɗin New Era su Hashim suka shigo yana sanye da ƙananan kaya, duk wani motsinsa akan idon hajiya Sharifa, wani daga cikin ma'aikatan hotel ɗin ta tura domin ya kira mata Hashim, bai yi musu ba yaje, kujera ta nuna masa ya zauna yana mamakin kiran da tayi masa,

"ƴan samari yakake? Ina zaune anan naga shigowarku, idan ba zaka damu ba ina son za muyi wani business da kai?"

"Business? Wanne irin business?"

"firstly we have to introduce ourselves.... Am Sharifa Mukhtar, and you?"

"Hashim Musa" ya faɗa yana kallon wani waje,

"Nice name..... Wato Hashim akwai wani business ɗina da ake kula min dashi anan cikin garin Kano amma sai na dakatar dashi saboda ana ha'intata tare da cutar dani amma kai kallon farko da nayi maka na san cewa you can make it...."

Ajiyar zuciya ya sauke har lokacin bai ce komai ba,

" if you are not ready now don't worry yourself zuwa gobe sai muyi magana, bari na baka room no ɗina da phone no ɗina "

Wayar hannunshi ya miƙa mata nan ta tsaya tana kallon wayar tare da jujjuya ta saboda ganin tecno p3 duk da touch screen ce, girgiza kai tayi,

" yaya classic guy like you zai rinƙa amfani da wannan wayar? No, no, this phone doesn't deserve you, am soo surprise, bari insa a kawo maka waya latest one"

Cike da mamaki yake kallonta, fara ce sol kamar balarabiya ga kyau ga kuɗi ga hutu wannan dalilin ne yasa tsufanta baya bayyana saboda ya samu gyara gashi ba taɓa haihuwa tayi ba sannan bata da girman jiki caan, jin wayar da take yi yasa shi dakatar da tunaninsa ya maida hankali kanta yana sauraro,

"Ina hotel ɗin yanzu haka.... Wacce irin waya da wacce kuke da ita?..." ɗan jim tayi sannan yaji tace,

"No, kawo iPhone ɗin dai, classic guy ne zai yi using da ita not me and am very sure bazai so sauran kamar wannan ba tunda kusan itace yanzu latest phone and it will suit him"

Cigaba da kallonta yayi har zuwa lokacin da ta kammala wayar ta kalle shi tana murmushi,

"yi haƙuri ka ɗan jira for some minutes nasa za a kawo maka new phone ka daina using wannan wayar mai araha, haba big guy kamarka da wannan.... Beside gaka handsome"

Rasa abin da zai ce yayi domin acikin ransa cike yake da tsananin mamaki, wannan wacce irin mace ce daga haɗuwa sai kyautar waya mai shegen tsada? Sunkuyar da kansa yayi ƙasa yana ɗan nazari wanda nazarin nasa yana da alaƙa da yanayin yanda ya samu kansa a yanzu saboda tun bayan da idonsa ya samu lafiya ya buɗe ƴanmata ke rububi a kansa sunata rushing na introducing kansu a wurin sa,

"uhmmm ya kayi shiru? Ko da akwai wani problem ne?"

Girgiza kai yayi domin bai da amsar da zai bata a wannan lokaci, kawai kallon tsananin kyaun da Allah yayi mata yake, gaskiya tana cikin sahun gaba na mata masu kyau da ganin ta shuwah Arab ce dan daga nan inda yake yana iya jiyo ƙamshinta wanda ya cika masa hanci ga uban tulin gashi yalo yalo da ta tufke kamar gammo yana hangowa ta cikin mayafin da ke kanta,

"shakka babu irin waɗannan matan sune suka dace dani.... Irin matan da idan na kalle su komai girman damuwata da ɓacin ran dake tare dani zan ji ya gushe....... To amma ya zanyi da Maimunatu?" wani ɓangare na zuciyar sa ya tambaye shi,

"A gaskiya Maimunatu bata daga cikin jerin mata irin wanda nake so sannan suka dace dani..... Saboda bata da kyau na azo agani, idan har na cigaba da kasancewa da ita har ta kaimu ga aure to tamkar wata alfarma nayi mata saboda kwata kwata ba ajina bace..... " duk waɗannan maganganun yana yin su ne cikin ransa babu wanda yaji. Zama suka cigaba da yi tana ɗan jansa da hira har zuwa lokacin da wanda zai kawo wayar ya ƙaraso, nan ta karɓa kuma a take tayi transfer ɗin kuɗin wayar wanda ke neman hauka ta Hashim dan bai taɓa tsammanin zai iya riƙe waya mai tsadar wannan ba a tarihin rayuwarsa,

"lucky is by my side" ya faɗa cikin zuciyar sa, miƙa masa wayar tayi sannan ta karɓi no ɗinshi tasa cikin wayarta, wayar hannuta yake bi da kallo wadda kusan irin tashi ce babu bambanci sai ko na colour, yatsun hannunta sunsha jan ƙunshi rangaɗaɗau sannan ga rings na gold jere a yatsunta,

"masha Allah....." ya faɗa can ƙasan maƙoshinsa, gaba ɗaya ya rasa wacce irin godiya zai yi mata, hannu ta ɗaga masa alamar bata son godiya, sallama yayi mata ko ta kan friends ɗinsa bai bi ba waɗanda suka zo tare yayi gaba abinsa,

Tun a daren ranar suka fara chaten da Hajja Sharifa, ni sam ban san abin da ke faruwa ba na dai ganshi online amma baya amsa magana ta sai kamar after 20 minutes har daga ƙarshe na kashe data ta na kwanta domin har 11 tayi, shi kuwa Hashim hajja Sharifa ta gama kwaɗaita masa business ɗin da zasu yi inda tace gobe yazo ya same ta zata kai shi ta nuna masa boutique ɗinta wanda ta jima da rufewa amma zata dake buɗeshi kuma zata sabunta shi zata je Dubai ta kawo kaya ta zuba gaba ɗaya shagon zai zama ƙarƙashin kulawarsa sannan akwai barbing saloon aciki, ni duk ban san abin da ke faruwa ba haka nayi bacci na hankali kwance amma na tashi da niyyar tunkarar Hashim da maganar aurenmu kamar yadda ƙawalli ta bani shawara kan yakamata inyi masa magana dan mu san inda muka sa gaba ita kam already an gama maganar bikin su da yaya Abdul hakim.............✍🏻


*Garin dadi littafin kudi ne ga mai bukatar cigaban labarin sai ya tura 500 ta 0774712835 Aisha Ibrahim Access Bank sai a tura evidence of payment ta wannan no 07044644433 ko a tura katin waya da shaidar biya wannan no 07044644433*



*_Ummi Shatu_*👌🏻
[1/5, 12:43] Maman K: ©️ *HASKE WRITERS ASSOCIATION*
_(Home of experts & perfect writers)_




*GARIN DAƊI....!*💍💍



_*NA*_


_*UMMI A'ISHA*_


From the writer of

KAMAR DA WASA
KUMALLON MATA
MIJIN MATACCIYA
SO DA ALAƘA & Rest.....


*Wattpad:ummishatu*



*12*



~~~Kamar kullum cikin shiga ta alfarma na shirya nasha turare nayi breakfast sama sama sannan na fita, wayar Hashim nake ta kira amma no answer baya ɗauka hakan yayi mutuƙar bani mamaki domin a iya sanina baya ƙin ɗaukar waya inda yana kusa, canja shawara nayi nace da mai napep ya sauya akalar napep ɗin a maimakon hanyar office mu kama hanyar gidan su Hashim,


Da fara'a tare da sakin fuska Iya ta tarbeni muka gaisa banji motsin kowa ba sai nata ita kaɗai da alama gidan babu kowa,

"Iya su Amiran basa nanne?" na buƙata kaina na ƙasa,

"Amira ta tafi makaranta Maimunatu...... Shi kuma Hashimu yana ɗaki ina jin bai tashi ba bare in duba shi in yi masa magana kin zo"

Wani ɗan ƙaramin ɗaki mai ɗauke da wani tsohon koɗaɗɗen labule ta shiga, yana kwance yana lallatsa sabuwar wayar iPhone ɗin sa yana hira da hajja Sharifa wacce ke sanar dashi wai da kwaɗayin wainar gero ta tashi irin wadda ake saka garin ƙuli ƙuli aciki a ina zai samo mata?

"Au Hashim dama idonka biyu? Ai na ɗauka bacci kake yi?"

"wallahi idona biyu Iya...."

"ehh ai gashi na gani, baka ji shigowar Maimunatu ba?"

"naji mana"

"Haka fa, to amma kaji zuwan nata shine ba zaka fito ku gaisa ba?"

"Iya ai ke ta zo gaisarwa, ba fa danni ta zo ba"

"Eh lallai, to wai tsaya wannan dalleliyar wayar ita kuma daga ina? A ina ka samota?"

"Iya wani abokin kasuwanci nane ya bani, yanzu ma muna sake tattaunawa ne game da yanda kasuwancin zai gudana, dan Allah kice kawai ta tafi idan na samu lokaci zan nemeta yanzu inada abun yi"

"Yayi maka kyau Hashim, yau kuma Maimunatun za a cewa ta tafi? Ashe baka da kirki ban sani ba? Yarinyar ta tsallake gida fiye da dubu tazo namu amma kake furta irin waɗannan maganganun? To idan ka gadama ka fito, idan kuma baka gadama ba karka fito kayi zamanka "

Daga haka ta fito daga cikin ɗakin cike da ɓacin rai, duk abubuwan dake faruwa a kunnena ne kuma naji komai domin ɗakin bai da wani tazara da inda nake zaune,

Iya ƙokarin ɓoye ɓacin ranta tayi ta ce min wai yana zuwa amma abun takaici saida ya shafe mintuna 15 bai fito ba, miƙewa nayi ina sake duba agogon hannu na saboda lokaci yaja,

"Iya zan ƙarasa wurin aiki na makara sosai kar makarar tayi yawa" cike da damuwa da ɓacin rai naji tace,

"to shikenan Allah ya bada sa'a ta tsare sai kin dawo"

"amin Iya" na faɗa ina ɓoye damuwa ta dan har ga Allah naji haushi sosai ba kaɗan ba.

Sai bayan da na fita sannan Hashim ya fito daga cikin ɗaki daga shi sai singileti da gajeren wando,

"Da kyau butulu, ai na zaci ko zaka yi butulci bai kamata ka yi wa wannan Yarinyar ba haka bai kamata ka yi wa Allah butulci ba.... Tunda ka samu ido ka daina zuwa makaranta, ka daina zuwa majilissin ɗaukar karatu, ka daina zuwa masallaci, ka daina tashin asubah, anya Hashimu ka ɗauko hanya mai ɓullewa? Yanzu abin da ka yi wa Yarinyar nan kayi daidai kenan? "

" Iya nifa banyi komai ba, ba gashi na fito ba, tana ina? "

"Zama

Please Login or Register in order to submit comment