Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

dina,

Sai da ya kammala wayar sannan ya lura da kayan dake gefensa kan kujera nan ya dudduba cike da mamaki dan ya san bani na siya masa ba da nice ba ta haka zan bashi ba to amma waye ya kawo? Ganin baida wanda zai bashi amsa yasa shi tashi yabini cikin bedroom,amma bani ba hatta shi yayi mamakin ta yadda aka yi koma wacece wannan ta san yau birthday dinshi kuma duk yadda akayi tayi bincike sosai akansa.

Ina kwance ina wani sabon kukan ya shigo, zama yayi gefena yana kamoni zuwa jikinsa, "baby meke faruwa? What's wrong with you?"

Jajayen idanuwana na daga ina kallonsa raina a bace,

"baka ga kaya a falo ba?"

"na gani, waye ya kawo?"

"kafini sanin wanda ya kawo ai tunda ga dukkan alamu soyayya kake yi da ita saboda gashi nan har ta san yau birthday dinka ta aiko maka da gift har gida....."

"Baby wai ya kike magana kamar irin na san komai dinnan.... I know nothing about what you are saying...... I don't know who's behind this..... Trust me...."

Ido na tsura masa ina son gano gaskiyar abinda yake fada min nan naga shima ya saka nasa cikin nawa hakan ya tabbatar min da duk abinda yake fada gaskiyane domin da ba gaskiya bane bazai iya hada idonsa da nawa ba, rungumeshi nayi ina kuka duk da hakan na kasa saukowa daga fushin da nayi, shikuma dama ya jima yana receiving massages na wata yarinya wai Suhaila amma bai taba daukar abin serious ba bare har ya kulata to ko itace ta aiko masa wannan kayan? Wannan shine tunanin da yaketa yi amma baya son in gane shiyasa yayi saurin katse tunanin, dakyar da rarrashi ya lallabani na sauko dan tsabar yana son in saki raina shine ya shiga kitchen ya dafa mana noodles duk da ni nake fada masa wasu abubuwan gudun kar ayi kwaba, ina zaune ina kallonsa ya gama dafawa ya soya kwai sannan muka koma falo. Tamkar wata baby koda yake yace ni din baby ce a gareshi haka ya zaunar dani ya rinka bani a baki duk da girkin nasa ya danyi yaji kadan amma haka na daure naci yau dai na sha soyayya kamar wata sabuwar amarya ni kaina na san nayi dacen samun miji mai sona sosai wanda baida wani buri sai na ganin farin cikina,

"baby ina ta sauri in dawo gida kuma shikenan sai in zo in sameki kinata kuka...."

"wancan kayan fa ka san yadda zaka yi dasu dan wallahi ba zasu zauna min a gida ba..."

"au ba zaki barni in saka ba...?" ya bukata cikin tsokana ai yunkurawa nayi zan tashi yayi saurin danneni da gefe daya na jikinshi, ina shirin fara yi masa tsiwa ya rufe min baki da nashi dan dole nayi shiru na hadiye maganganun da nayi niyyar fadi ada,

Washe gari ban san ya yayi da kayan ba na dai ga ya fita dasu kuma ni dai tun daga wannan lokacin hankalina yaki kwanciya dan na fahimci koma wacece wannan to da gaske take kuma a shiryenta tazo, duk da na yarda da irin soyayyar da mijina yake nuna min amma nidai ina tsoro ina tsoron kar yarinyar nan tayi tasiri acikin zuciyarsa har ya raba soyayyar da yake yimin ya sammata,wannan al'amari shi yake sake tayar min da hankali har yake ɗarsar min da tsoro mai girma cikin zuciyata, gashi dan jaraba kullum sai ta turo masa massage ko gajiya bata yi, ita tana yi Felicia tana yi sun sakani a tsakiya suna kokarin kwatar min miji ta kowanne hali,

Anty na kira ina kuka na zayyane mata dukkan damuwata nan ta kwantar min da hankali kuma ta babbani shawarwari akan yanda zan rike mijina da kyau sannan in sake bada himma wurin kyautata shi da bashi farin ciki haka kuma in manta da duk wata mace dake kawo masa hari in rage wannan zafin kishin nawa in kula da mijina, haka kuma in kula da hakkinsa sosai na shimfida in daina wannan ragwantar dan na fada mata ni yanzu tunda na rabu da wannan cikin na daina daukar dawainiyarshi yadda ya kamata dan yanzu a sati baifi sau biyu ba nake iyawa shima dakyar sai da rarrashi da lallabawa amma lokacin da ina da ciki duk lokacin da yazo ina maraba, faɗa tayi min sosai tace in rinka daurewa kuma inyi hakuri a kowanne lokaci kowa haka yake hakuri, mun jima sosai da anty tana bani shawarwari kafin muka yi sallama, dan aikace aikace na nagama na kwanta dan in dan rage bacci kafin lokacin girki yayi, ina kwanciya naga ya kirani video call dauka nayi ina lumshe idanuwana........

*Garin dadi littafin kudi ne ga mai bukatar cigaban labarin sai ya tura 500 ta 0774712835 Aisha Ibrahim Access Bank sai a tura evidence of payment ta wannan no 07044644433 ko a tura katin waya da shaidar biya wannan no 07044644433*

*_Ummi Shatu_*👌🏻
[1/5, 12:43] Maman K: {50}


*Ina kuke manyan mata ƴan ƙwalisa ma'abota son gyara da kece raini, maza ku garzayo ku nemi maman Maryam domin samun lafiyayyu kuma haɗaɗɗun Lagos lace wanda zaku iya samun ɗinkakku da kuma sabbi a ledarsu, kaya iya zaɓinki, gefe ɗaya muna da GHT product, zaku samu,*

~MAI DA TSOHUWA YARINYA

~FEMALE CARE

~REODEO

~VIGOR MAX

~ LONGZIT

~B CLEAR

*DUK ZAKU SAMU WADANNAN KAYA CIKIN SAUKI DA RAHUSA MAZA KU NEMI MAMAN MARYAM AKAN WANNAN NO 07080222187, SIYAN NA GARI MAIDA KUƊI GIDA.....*

~~Shima lumshe idanuwan yayi kamar yadda ya ga nayi sannan cikin sanyin murya yace,

"Hey baby....."

"hey boo.....Ya aiki?"

"we thank God, am just wanna check you.... Yakike"

"awwwwn..... Ina lafiya but am missing you"

"zan dawo soon, me za a bani idan na dawo anything for me?"

Idanuwana na sake lumshe masa sannan na shagwabe murya,

"I kept something special for you darling......"

"are you serious?"

"yes dear...."

"ok zan zo da wuri baby, i love you"

"I love you too"

Sallama muka yi na ajiye wayar ina dariya saboda maganar da ya fada ta karshe wadda cikin raɗa ya fada kamar baya son kowa yaji,

Ina cikin baccina mai daɗi naji wani ƙaddararren bugun kofa wanda ya tadani dan dole, nan na zira hijabi na fita fuskata babu yabo babu fallasa tunda daga bacci na tashi, lokacin da na bude wasu fararen yanmata na gani guda biyu amma daya tafi daya tsayi dukkansu sun sha abaya sai kamshi suke, sannu da zuwa nayi musu kafi na basu hanya suka shiga ciki nikuma na tsaya a kitchen na dauko musu ruwa da lemo nabi bayan su dashi,

"Ina yini..." suka ce dani atare fuskokinsu duk dauke da murmushi,

"lafiya lau, yagida"

"lafiya lau...." suka sake amsawa a tare,

Ɗan shiru falon yayi kafin na katse shirun ta hanyar cewa "kusha ruwa mana sannan ban gane ku ba...."

"ehh gaskiya ba zaki ganemu ba saboda baki sanmu ba in fact ma baki taba ganinmu ba"

"ehh hakane gaskiya" na fada ina sake kallon su daya bayan daya dan na kasa ganewa shin ƙawaye ne ko kuma yaya da ƙanwa ne,

"ni dai sunana Malika wannan kuma kawata ce sunanta Suhaila....."

"ayya Allah sarki" na fada ina murmushi dan wacce tayi maganar itace babbar wato doguwar ciki,

"Maimunatu kamar yadda Malika ta sanar dake sunana Suhaila kuma nazo wurinki ne da wata babbar buƙata wadda ƙarama ce ta wani bangaren bata da girma..... Amma dan Allah ki fahimceni"

Gyara zamana nayi sosai ina fuskantarsu dan jin meke tafe dasu,

"ina sauraronki...."

"Da farko dai ina yi miki albishir da cewa mun zo miki da alkhairi har gadon barcinki.... Kamar yadda na fada miki wata yar bukata ce ba mai girma ba sai dai amma ta yuyu ke ki dauketa da girma, Maimunatu idan har kin amince da bukatata to zan mallaka miki abubuwa da yawa na more rayuwa, haka kuma zan fitar dake duk Kasar da kike so banda sauran kayan alatun rayuwa da zan mallaka miki.... "

" baiwar Allah har yanzu baki fadi bukatar taki ba sai wasu maganganu kike yi daban.... "

" calm down.... Zan fada miki amma ina so muyi yarjejeniya ne ta yadda ni dake zamu saka hannu da shaidu da komai.... Tun ranar da Allah yasa idanuwana suka sauka kan mijin ki naji bani da wani abu da nake so sama dashi, ban farga da cewa yana da aure ba har sai bayan da na nutsa cikin kogin sonshi, nabi duk wata hanya da ta dace dan ganin nasamu attention ɗinsa but all in vain, daga ƙarshe naga bani da wata hanya wacce zan iya bi har ta kai ni ga nasara face ke... Ke kadai ce zaki iya taimaka min wurin samun soyayyar mijin ki domin a yanda labari yazo min bashida wani abu da yake mutuntawa da martabawa sama dake, ke kaɗaice MACE GUDA ƊAYA TILO dake mulkin birnin zuciyarsa, dan haka shiyasa nazo da ƙoƙon barata duk da nasan KISHI KUMALLON MATA ba lallai ya bari zuciyarki ta amince da bukatata ba..... "

Ai gaba daya daskarewa nayi awurin ina jina tamkar cikin mafarki wannan kuma wacce irin masifa ce take sake tunkaro ni? Sai yanzu na gane ta ashe itace wadda taketa bibiyar mijina babu dare babu rana yanzu kuma dan rashin kunya shine zata zo har gida ta ruɗeni da abin duniya ta shiga tsakanina da mijina, to ai ba abin duniya ba ko ita duniyar zata bani akan in siyar mata soyayyar mijina bana jin zata yi nasara domin nafi sonsa fiye da komai, kuma zan iya yadda in rasa komai da na mallaka dan kawai in cigaba da zama tare dashi,

"Maimunatu baki ce komai ba....." inji kawarta Malika,

Ajiyar zuciya na sauke sannan na kallesu nace "duk naji abubuwan da kuka zo dasu sai dai ina so in tunatar daku abu daya da kuka manta, bani ke iko da zuciyarsa ba haka kuma ba nice zan zaba masa dukkan abinda yake so ba shiyasa sai nake ganin kamar zuwanku wurina baida wani alfanu tunda nidai bazan sa ba kuma bazan hana ba.... "

" kamar baki fahimci abin da nake nufi ba...... " inji Suhaila, hannu na ɗaga mata alamar dakatarwa,

" ya isa haka dan Allah, idan har wannan ne ya kawoku to dan Allah kuna iya tashi ku tafi domin bazan taba fahimtarku ba..... "

" nazo har gidan ki da bukatata amma kin wulakanta ni ba tare da kin san koni wacece ba, to shikenan zan nuna miki indai kudi da mulki suna siyan soyayya sai na siyi soyayyar mijinki.....

Mikewa tsaye nayi kamar yadda naga sun mike tana zubar da hawaye" wallahi karya kike, ko wacece ke baki isa kin siyi soyayyar mijina ba kuma mijina yafi karfinki....... "

Bata sake tankawa ba kawarta ta jata suka fita tana kuka, suna fita Samha tana shigowa duk da bana wani sake mata amma hakan bai hanata shigowa ba a duk sanda taga damar hakan ta samu,

" widat wadanne bakine wadannan kika yi suka fita da kuka? "

" nima ban san su ba, wani gida suke nema sai aka kwatanta musu nan...."

"ayya to ubangiji Allah ya rufa asiri"

"amin"

Sama sama nake amsa mata dan ni gaba daya zuciyata zafi take yi da zata taimaka min ma da ta kwashi kafafuwanta ta kara gaba dan bana bukatar wannan zaman nata, fahimtar hakan ina jin tayi shiyasa ta tashi ta tafi,

Nidai gaba daya na rasa abinda yake yimin dadi ji nake kamar idan yazo in bayyana masa amma wata zuciyar kuma tana cemin bai kamata in sanar dashi ba kawai in bar abin a raina ni daya, tunawa nayi da shawarwarin anty nan na danni zuciyata duk da abin yana damuna amma haka na daure na maida komai kamar ba komai ba, ganin yamma tana kokarin yi yasani fara dukkan aikace aikacen da na saba gabatarwa kafin ya dawo daga karshe nayi wanka na caba ado ina zaman jiransa. Koda ya dawo kokarin danne abinda ke raina nayi ban bari ya gane ba bare har yazo yana explaining, sakar masa fuska nayi da jiki muka sha soyayya kamar yadda muka saba sai dai fa lamarin suhaila sam yaki bacewa daga cikin zuciyata dan mutane yanzu ba abin yarda bane especially ma ita da har ALWASHI tayi akan mijina, daga karshe dai kin fadawa kowa nayi na barwa Allah yayi min maganin koma menene da kansa domin shine masani akan komai,

Kwana biyu dai baya samun zama yadda ya kamata saboda bikin abokinsa Ahmad da ya sako kai, yadda ahmad ya tsaya tsayin daka lokacin bikinmu shiyasa shima yanzu yake son ramawa kura aniyarta dan shine a sahun gaba akan komai, kasancewar a Kano za ayi bikin shiyasa da satin bikin yazo muka tattara muka tafi amma wannan karon agidanmu muka sauka kuma tare zamu dawo ranar da za a raka amarya, wannan zuwan banyi yawo ba sosai dan wasu ma basu san nazo ba gidan ƙawalli kawai na leka naga Irfan sai ko gidanmu da naje shima ban ko wuni ba, daga nan na dan shiga kasuwa itama sama sama, nayi attending duka events din kuma tun anan muka yi sabo da amaryar mai suna Nihal haka koda aka rakota Abuja ni na zauna tare da ita har zuwa lokacin da angwaye suka karaso sannan muka yi musu sallama muka tafi, tun muna hanya yake cemin wai yau bikin Ahmad ya tuna masa namu bikin muma,

"me ka tuna daga ciki?" na bukata ina kwanciya a gefen jikinshi,

"everything baby..... Babu abinda na manta"

"wow....." na fada cikin tsokana, "ke baki tuna komai ba"

'na tuna mana... "

" me kika tuna? "

" ranar dinner..... "

Dariya yayi ya ja hancina saboda ya san tunda na fadi haka to kuma tsokanace zata biyo baya, har muka je gida maganar muke yi,

A falo na barshi suna waya da mommy nikuma na wuce bedroom waist bit din da na siyo na ɗaura da niyyar burgeshi dama normal one din na siya ba mai hadi ba kamar yadda naji masu siyarwar suna tambayata lokacin da naje siya wai mai hadi ko marar hadi nace marar hadi dan bana son garin burge miji inje kuma in sabawa Mahalicci na, riga na saka iya cibiya da mini skirt wadda mazaunai na kadai ta rufe na fito, ai tun yana wayar da ya hango ni daga nesa naga ya tashi zaune daga kishingiden da yake yana miko min hannu amma sai na makale kafada naki zuwa, nafi son har sai ya gama yadda zamu fi sakewa da juna amma yanzu idan na kusanceshi ai akwai matsala, kasa hakuri yayi yace ma mommy bari yana zuwa zai kirata back ya ajiye wayar ya juyo yana kallona sosai,

"zo mana baby...." a hankali nake takowa zuwa inda yake, ina karasowa ya damƙi waist dina yana cewa,

"baby what's this?"

"kwalliya nayi maka"

"I see, yayi kyau saura nan....." ya fada yana taɓa cibiyata,

"kana so?"

"yes baby....."

Tunda ya samu jigidar nan ai ya samu abin yi lallai ada nayi sake da ban saka tunda wuri ba sai yanzu ashe bawan Allah yana so kuma yana ra'ayi kuma da yake mai different colors na saka sai hakan yafi daukar hankalinsa tunda na gane haka nima yanzu sai na daina saka kayan da zasu rufe ta, koda yaushe kananun riguna nake sakawa iya cibiya inyita juyi yana kallo na wani lokacin ma har a bani tukwici.
*** *** ***

Shalele shine sunan da kowa na gidan ke kiranta dashi saboda tsabar shagwaba da gata kasancewarta mace guda daya a cikin gidan, duk sauran yan uwanta maza ne sannan kuma itace yar auta, wannan dalilin yasa kowa ya tashi abu Shalele duk wata kulawa tana samu gashi ta fito daga tsatson mulki da masu gidan rana saboda mahaifinta mai fada aji ne ne gaba da baya, duk abinda take so shi ake yi mata haka wanda bata so kuma an barshi har abada. Cikakken sunanta Suhaila Umar Lemu, mahaifinta ɗaya daga cikin ƙososhin gwamnatin tarayya ne suna zaune garin Abuja amma asalinsu yan jihar Bauchi ne,

Tana kan hanyarta ta zuwa airport da sanyin safiyar Laraba idanuwanta suka yi tozali gami da arba da samz wanda ke hanyarsa ta zuwa office, masha Allah kawai take furtawa acikin ranta saboda tsabar haduwarsa komai nashi yaja hankalinta nan tayi ta binsa har zuwa office ɗin su,

Parking tayi ta kira daya daga cikin securities din office din, karon farko wasu sabbin kudi yan dubu ta zaro guda goma ciss ta mika kafin ta fara tambayarsa,

"dan Allah taimako zaka yimin, naga wani guy baƙi giant ya shiga nan yanzu shi nake so ka bani phone no dinsa...."

Dan jimm security din yayi kafin yace "ehh madam na gane shi amma sai dai bani da no dinsa...."

"babu matsala na baka assignment kaje ka nemo min komai da ya shafe shi please and am going to pay...."

"ok ma, i shall..."

Exchanging contacts suka yi sannan ta juya kan motarta ta fita tana jan dan siririn tsaki sakamakon kiran da Jalil keta faman yi mata dan ya jima da sauka...........


*Garin dadi littafin kudi ne ga mai bukatar cigaban labarin sai ya tura 500 ta 0774712835 Aisha Ibrahim Access Bank sai a tura evidence of payment ta wannan no 07044644433 ko a tura katin waya da shaidar biya wannan no 07044644433*

_*Ummi Shatu*_👌🏻
[1/5, 12:43] Maman K: {46}


*Ina kuke manyan mata ƴan ƙwalisa ma'abota son gyara da kece raini, maza ku garzayo ku nemi maman Maryam domin samun lafiyayyu kuma haɗaɗɗun Lagos lace wanda zaku iya samun ɗinkakku da kuma sabbi a ledarsu, kaya iya zaɓinki, gefe ɗaya muna da GHT product, zaku samu,*

~MAI DA TSOHUWA YARINYA

~FEMALE CARE

~REODEO

~VIGOR MAX

~ LONGZIT

~B CLEAR

*DUK ZAKU SAMU WADANNAN KAYA CIKIN SAUKI DA RAHUSA MAZA KU NEMI MAMAN MARYAM AKAN WANNAN NO 07080222187, SIYAN NA GARI MAIDA KUƊI GIDA.....*


~~~Ina shiga cikin bedroom din ko zama banyi ba naji shigowarsa shima alamar biyoni yayi, ina kokarin zama ya rikoni tare da zaunar dani cikin jikinsa,

"am very sorry my love..... Kiyi hakuri zan ci, zo muje in ci a gabanki ki gani....."

Shiru nayi ina sauraren ban bakin da yake yimin tare da share min hawayena,

"ban san cewa ranki zai baci ba amma kiyi hakuri bazan sake ba...."

Duk da cewa a ƙoshe yake amma haka yaketa cakular abincin bayan mun koma falo ya samu nasarar shawo kaina, ɗauke abincin nayi na saka cikin fridge tunda na riga da na huce na koma normal kamar babu wani abu da ya faru,

Tun dab da lokacin kwanciyata na fara jin cikina da marata suna ciwo amma sai na daure ban fada masa ba, wanka nayi na kwanta ina jin ciwon yana ƙaruwa ahaka na samu bacci ya daukeni bayan nagama azkhar din kwanciya bacci, cikin dare ciwo ya sake tashi yace muje zuwa yayinda bacci kuma ya ƙaurace min dan azaba, zaune na tashi na zauna na zubawa sarautar Allah ido shikuma yana kwance yana ta baccinsa wanda na san bawai ya wani jima da ɗaukarsa bane, na jima zaune kafin na samu ya dan lafa min na sake komawa bacci zuwa asubah na sake tashi,

Bathroom na shiga domin kama ruwa nan naga ashe ma bleeding nake ban sani ba ga wani irin murdawa da marata keyi abin ba sauki, ganin jinin da nayine ya firgita ni shiyasa na koma na tashe shi. Sai lokacin ya san halin da nake ciki cikin firgici ya riƙeni yana cewa,

"Baby yi sauri muje hospital.... Bana son wani abu ya sameki ko cikin dake jikinki....."

Kai na ɗaga masa ina cije lips ɗina duka biyu a haka dai ya taimaka min na cire rigar baccin jikina na saka doguwar riga da hijabi muka yi salla sannan muka tafi,

Muna zuwa likita ya shiga dubani nan ya tabbatarwa da samz cikin jikina ya lalace sai dai ni bai fada min ba dan kada hankalina ya tashi saboda ko yanzun ma cikin tashin hankali nake, faɗin irin baƙar azabar da na sha kuwa ɓata lokaci ne kuma har lokacin babu wanda ya sani daga ni sai shi sai zuwa azahar bayan cikin ya gama faduwa sannan samz ya kira yaya Abdul hakim ya sanar dashi nan shima yaje gida ya fada musu shiyasa kafin kace me asibiti ya cika da ƴan gidanmu nikam ina can ina bacci banma san wacce wainar ake toyawa ba. Zuwa la'asar na tashi daga baccin wahalar da na sha nan naga Anty, mama,Bishra, anty salaha ganin na farka duk suka yo kaina suna yimin sannu, tea anty ta hada min sannan ta zubo min abinci, da ido naketa neman samz amma da dukkan alamu baya cikin ɗakin dan da ace yana nan ai da na ganshi may be yaje gida ko kuma yana waje, nan dai duk suka shiga jajanta min ɓarin da nayi, ni dai a ɓoye na keta kuka na ban bari wani ya gani ba, zuwa magriba su Annie suka ƙaraso ita da Abba da yaya Abdul hakim wanda shine ya kawo su, basu jima da zuwa ba samz ya dawo dauke da fruits cikin leda da drinks harda balangu, kaya dai kaca kaca na ciye ciye haka ya kawo, bamu samu kebewa dashi ba saboda mutane har sai bayan ishah lokacin da duk ƴan gidanmu suka tafi sai iya Bishra kadai da aka bar min wanda zamu kwana tare

Misalin ƙarfe 9 ya shigo ya zauna kusa dani yana yimin sannu, ai kamar dama jira nake nan na fara kuka shikuma ya shiga rarrashi na yana bani baki,

"yanzu duk yadda muka ƙwallafa rai akan cikin nan ashe ba zai ma zo duniya ba...." na fada cikin kuka, hannuwana ya rike cikin nasa yana sake rarrashi na da kalamai masu dadi,

"babu komai baby haka Allah ya so kuma insha Allah zai sake bamu wani mai albarka.... Ki kwantar da hankalinki Kinji...."

Kai na ɗaga masa ina sauraren kalaman da yake yimin na kwantar da hankali da samar da nutsuwa cikin zuciya, muna nan tare dashi har wurin 10 sai da yaga na ware na sake sosai sannan yayi mana saida safe ya tafi,

Kwana na biyu a asibitin kafin aka bamu sallama, kai tsaye gidanmu aka wuce dani dan su anty sunce sai an kula dani sosai, a ranar shikuma ya koma Abuja saboda aiki, kamar yadda yake ta cewa in kwantar da hankali na kar in saka damuwa acikin raina kwantar da hankalin nawa nayi shiyasa nayi fes dani ban wani lalace ba.

A ɓangaren mommy kuwa bayan sun gama ƙulle ƙullensu da shirye shiryensu ita da aminiyar tata daga ƙarshe taji labari mai daɗi daga bakin samz dan shine da bakinsa ya sanar mata da wai na samu miscarriage lokacin da abun ya faru kuma yakara da cemata ina asibiti ma lokacin ko sallamata ba ayi ba, ko da wasa bata nuna masa tayi farin ciki ko bakin ciki ba dama kuma ya riga da yasan duk wani lamari wanda ya shafeni to bata damu dashi ba shiyasa abin bai wani dameshi ko bashi mamaki ba amma acan ƙasan zuciyarta taji dadin labarin da yaje mata dashi dan dama bata da wani buri wanda ya wuce taga wannan cikin nawa ya lalace dan tace ba zata taba hada jini damu ba shiyasa babu ɓata lokaci ta sanarwa da aminiyar tata wadda bafa hakura suka yiba a'a sun sake ɗaura ɗamarar cigaba da yaƙar zaman lafiyarmu dashi.

Bayan tafiyar shi kullum muna tare a waya tun daga safe har zuwa lokacin kwanciya bacci shi kansa ya yaba da irin yadda yaga na saki raina kuma na kwantar da hankalina nayi Kumari ban bari na lalace ba, satinshi biyu da tafiya yazo kuma tun kafin yazo yake cewa wai a gida zai sameni?

"Gidanmu....." na bashi amsa dan na fahimci inda zancen nasa yake son zuwa,

"Gidanmu nida ke?"

"gidan iyayena...."

Dariya yayi ya kwantar da murya yace "baby ba zamu hadu agidanmu ba inyaso after na tafi sai ki koma"

"lallai ma sannunka..... A'a gaskiya"

"to shikenan sai nazo"

"tom, me zan dafa maka?"

"ni ke kadai nake bukata, you are the real meal...."


"yen yen yen....."


"yen yen yen yen...." shima ya fada cikin kwaikwayon muryata, dariya muka yi gaba daya kafin muka yi sallama na ajiye wayar,

Girki nayi masa

Please Login or Register in order to submit comment