Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

jawabin maraba da ɗan taƙaitaccen tarihin kowannenmu daga bisani aka fara cashewa bayan an kira amarya da ango,

Anci an sha an raƙashe haka kuma an zubar da kuɗi babu laifi, misalin ƙarfe 10:30 aka tashi, yanzu kam ba tare dashi zamu koma ba, ina katarin anty wanda hakan ba ƙaramin daɗi yayi min ba dan nasan wataƙila idan dashi zamu koma ya nemi yimin abun neman magana daga ƙarshe muyi faɗa idan na bijire,

Muna komawa gida nayi wanka nabi lafiyar gado duk da ina ɗan jin yunwa dan yanzu bana cin abinci sosai. Kasancewar na gaji bacci na nayi haiƙan har sai da gari ya waye sannan na tashi, tunda na tashi kuma da zarar na tuna yau za a ɗaura min aure a kaini gidan miji sai inji gabana ya tsinke ya faɗi haka dai nake ta daurewa nayi wanka aka yimin kwalliya nayi shiga ta cikin wani tsadadden leshi wanda anty ta ɗinka min dark purple, da yake yau ake wuni shiyasa gidan namu cike yake taf da ƴan uwa da abokan arziƙi a nata cashewa da masu kiɗan ƙwaryar da aka ɗauko, wayata a kashe take banma san inda take ba, anty ce ta sakani a ɗaki ta bani wani farfesun kaza kuma ta sakani a gaba sai na cinye, idan ban manta ba irin wannan naman naci yafi sau uku kuma duk babu daɗi dan har ji na nake kamar zan amayo dashi, abubuwan da anty ta ɗura min acikin cikin nan nawa sun fi gaban lissafawa duk da sunan maganin infection da na gyaran jiki, haka dai na rinƙa yaga ina ci ina yatsine fuska da haka har na cinye sannan ta haɗa min maltina da madara na sha ƙawalli sai gwalo take yimin idan ta faki idon anty, bayan na gama ci mun fito muka ji alamun dawowar ƴan ɗaurin aure nan na sake jin jikina yayi sanyi shikenan aure ya ɗauru, ban sake gaskata hakan ba sai da yayuna suka shigo suna bada labarin an ɗaura akan sadaki naira dubu ɗari, kamar zanyi kuka amma anty tace idan na kuskura nayi hawaye nida ita ne, sake shiryani aka yi muka fita wurin angwaye, ya sha farar shadda ƙal da baƙin glasses a idonshi yayi kyau har ya gaji, hotuna aka yiyyi mana sannan suka tafi mu kuma muka koma gida kafin kace me har anfara maganar tafiya kaini, ji nayi kamar in gudu wani wurin in ɓoye amma babu dama domin duk inda nayi ƙawalli na biye dani, ita ta rakani wurin Abba ma yayi min nasiha irinta uba da ƴa sannan su mama, faɗan da suka yimin shine ya saka ni kuka kamar zanyi hauka, itama Anty nata faɗan tayi min kamar haka,

"To widat gashi dai Allah ya kawo mu ya nuna mana, rana bata ƙarya, yau zaki tafi gidan mijin ki, to wallahi kar naji labarin ƙazanta da rashin gyara, sannan banda raina miji banda rashin kunya, haka ƴan uwansa kisa aranki baza su taɓa sonki ba... Hakan shi zai sa ki zauna lafiya kuma zuciyar ki ta huta, dan duk tsanar da zasu nuna miki dama kin san hakan zai biyo baya, amma idan kika sawa ranki dole sai sun soki to zaki tabbata cikin damuwa dan baza su soki ba saboda kullum kallon wadda ta raba su da ɗan uwansu ta fitar dashi daga addininsu zasu yi ta yi miki amma Hakan kar ya hanaki kyautata musu idan sun zo gareki, kiyi musu dukkan wani nau'i na kyautatawa musamman ma mahaifiyarsa karki yarda ki wulakantata dan ta nuna bata sonki, ki tuna itace ta kawo mijin ki duniya tayi ɗawainiya dashi har ya zama abin da ya zama yanzu, kiyi mata biyayya iya iyawarki kuma ki girmama ta ki bata matsayin uwa.... Allah ya baku zaman lafiya "

Duk faɗan da iyaye suka yi min na anty ne yafi tsaya min arai da naji tayi maganar ƴan uwan samz ba zasu soni ba, tabbas nima na fahimci hakan domin babu wadda ya taɓa nemana acikin ƴan uwansa ko danginsa, anty Amina ce kaɗai matar uncle ɗinsa da wasu dangin su ke fafutukar zuwa neman aure na dan yanzun ma sune suka zo ɗaukar amarya,

A can gidan su samz kuwa mahaifiyarsa bata san abin da ke gudana ba dan daddy baya shiga shirginta kuma baya sanar da ita komai akan batun auren mu da Samz, sai yau ta sani da taga Abdullahi ƙaninsa yayi shiga da manyan kaya nan take tambayarsa ina zai je? Amsa ya bata da wai ɗaurin auren Samz ai tunda taji haka ta yanke jiki ta faɗi bata sake sanin inda kanta yake ba saboda dama tana da lalurar hawan jini, asibiti aka kai ta aka bata gado amma samz kwata kwata bai san hakan yana faruwa ba dan babu wanda ya faɗa masa kuma ko auren nasa ma daddy ne ya gargaɗeshi akan ya ɓoye mata karya kuskura ya sanar da ita idan ba haka ba hanawa zata yi zata bi bokaye a ɓata lamarin wannan dalilin ne yasa bai sanar da ita ba.

Bayan sallar magriba aka kaini gidana dake unguwar hotoro, kuma ana kaini kowa ya kama gabansa aka watse aka barni inata shaƙar kuka na, ƙawalli kuwa saida ta gama yimin rashin mutuncinta kafin ta tafi daga baya kuma itama kukan tayi sannan ta tafi, ganin zaman shiru yana neman damuna yasa nayi alwala nayi sallolin dake kaina wato magriba da isha, bayan na idar na koma kan gado na takure ina kallon uban dukiyar da aka kashe min acikin ɗakina wanda komai silver colour, shi kuwa ango bai shigo ba sai bayan sallar ishah kuma shi kaɗai babu ɗan rakiya dama iya Ahmad ne abokin nasa to shi kuma tun bayan ɗaurin aure ya koma Abuja,

A kusa dani ya zauna yana ƙoƙarin buɗe fuskata,

"Kuka kike yi ne?" ya buƙata cikin tsokana, shiru nayi na sunkuyar da kaina,

"Ahmad yace akwai salla da zamuyi ta nafila raka'a biyu ko? Muyi sai ki ci abinci ki kwanta.... Zan bar ki ki huta yau"

Shiru nayi nai tsit kamar ruwa ya cinye ni, hannuna ya kama cikin nashi,

"Kin jima kina tambayar wacce irin rashin lafiya nake yi idan banda lafiya amma bana faɗa miki ko? To yau zan faɗa miki dan kece maganin.... Ciwon ciki ne kuma Dr ya tabbatar min da maganin yana wurin ki soo sau nawa zaki rinƙa bani? Da safe da yamma, ko da safe da rana da yamma da kuma dare? " ai ban san lokacin da na kalleshi ba a tsorace, shi ɗinma ni yake kallo, murmushi naga yayi ya miƙe tsaye, nikam ji nayi kunyar duniya ta taru ta lulluɓeni kamar ƙasa ta buɗe in shige, gaskiya sai yau na yarda namiji bai da kunya, alwala ya ɗauro muka yi salla raka'a biyu muka karanta abin da ya sawwaƙa cikin Littafi mai tsarki muka yi addu'a, abin da ya shigo dashi ya ɗauko mana, gasasshiyar kaza ce sai fresh milk da fruits, kan cinyarsa ya ɗora ni yayi ta yimin ɗura har sai da ya cika min ciki dan wai ya fahimci ban ci abinci ba, wanka yace in je inyi nace nayi, bai takura min ba shi ya rage kayan jikinsa ya shiga daga shi sai boxer, sai bayan da ya shiga sannan nayi hanzarin saka kayan bacci riga da wando na shige cikin bargo, shima bai wani jima sosai ba ya fito ɗaure da towel, leƙensa nake yi ta yadda ba zai gane ba ina kallonsa ya shafa turare yasa kayan baccin sa baccin sa wando iya rabin cinyarsa da riga armless, kan gadon ya nufo nan nayi gaggawar rufe idanuwa na, gaba ɗaya a sanyaye yake sakamakon wayar da ƙanwarshi Mary tayi masa ɗazu ɗazun nan tana sanar dashi rashin lafiyar mommy wadda ke kwance a asibiti wannan abun da yaji shine musabbabin tashin hankalinsa kawai yana dannewa ne yana nuna min he's ok. A hankali ya hawo kan gadon ya kwanta gefena wanda hakan sai da naji gabana ya faɗi, wayarshi ya kashe sannan ya ajiyeta kan bedside drawer kusa da tawa,

"Baby.... Yau rowa ta ƙare ko?" yace dani yana ƙoƙarin jawoni jikinsa da hannayensa masu taushi, ban ƙiba na shige cikin jikinsa nayi pillow da ƙirjinsa,

"kina jin bacci?"

"uhmm" na bashi amsa,

"yau baki ya mutu Babu magana? "Ya faɗa yana shafa gadon bayana a hankali zuwa can naji yana ɓalle botiran jikin rigar tawa,

"zaki fi jin daɗin bacci a haka" ya raɗa min bayan ya saɓule rigar daga jikina, manna ni yayi a jikinsa bayan shima ya cire tashi rigar, duk da ina cikin kiɗima tare da ɗimuwa hakan bai hanani jin daɗin ɗumin jikinsa ba dan kamar me zazzabi haka naji jikinsa,

"baka da lafiya ne?" na tambayeshi bayan na ɗaga kaina na kalleshi acikin duhun da muke kwance,

"a'a lafiya nake..... Me ya faru?"

"naji jikin ka ne kamar da zafi"

"a'a haka temperature ɗin jikina yake normally....."

"kuma kaje hospital?"

"me zai kaini hospital alhali lafiya ta ƙalau"

Murmushi nayi na mayar da kaina na kwantar araina ina tunanin dalilin da yasa ya iya barina daren yau, tuno tsokanar da Ƙawalli ta rinƙa yimin ɗazu kafin ta tafi nayi, sake maƙaleshi nayi tsam ina shaƙar ƙamshin jikinsa, ina jinsa hannunsa yaƙi tsayawa wuri guda a jikina ya taɓa can ya taɓa can da haka har ya isa inda ya jima yana kwaɗayin zuwa, na san dalilinsa na auna ƙirjina saboda dab da lokacin bikin mu yake cemin wai matar uncle ɗinsa ta haɗo lefenmu yaje gani wai yaga ta saka manyan braziers wanda ko haihuwa nayi ba lallai su yi min daidai ba nikuma nace wallahi in dai wanda na ganine zasu yimin amma yace ƙarya nake wai ni ɗin nawa nake shi so yake ma ya samomin cream in rinƙa shafawa ko zan ciko, tsokana iri iri babu wadda bai yimin ba sai rabuwa nayi dashi, sai da yagama ganin ƙwaƙwaf ɗin shi sannan muka yi addu'a tare, wani bacci mai daɗi ne yayi awon gaba dani jina a alƙayyar da ban taɓa samun kaina aciki ba.............✍🏻

Asuba ta gari Widsamz 🥰


*Garin dadi littafin kudi ne ga mai bukatar cigaban labarin sai ya tura 500 ta 0774712835 Aisha Ibrahim Access Bank sai a tura evidence of payment ta wannan no 07044644433 ko a tura katin waya da shaidar biya wannan no 07044644433*



*_Ummi Shatu_*👌🏻

[1/5, 12:43] Maman K: ©️ *HASKE WRITERS ASSOCIATION*
_(Home of experts & perfect Writers)_



*GARIN DAƊI....!*💍💍


_*NA*_

_*UMMI A'ISHA*_


*Wattpad:ummishatu*


{33}


PAID Book #500


*Ina kuke manyan mata ƴan ƙwalisa ma'abota son gyara da kece raini, maza ku garzayo ku nemi maman Maryam domin samun lafiyayyu kuma haɗaɗɗun Lagos lace wanda zaku iya samun ɗinkakku da kuma sabbi a ledarsu, kaya iya zaɓinki, gefe ɗaya muna da GHT product, zaku samu,*

~MAI DA TSOHUWA YARINYA

~FEMALE CARE

~REODEO

~VIGOR MAX

~ LONGZIT

~B CLEAR

*DUK ZAKU SAMU WADANNAN KAYA CIKIN SAUKI DA RAHUSA MAZA KU NEMI MAMAN MARYAM AKAN WANNAN NO 07080222187, SIYAN NA GARI MAIDA KUƊI GIDA.....*

~~~Koda na koma ciki samu nayi wayata na rangajin neman ɗauki na, cikin hanzari na ɗauka nan naga shine yake kira, cikin bedroom ɗina na wuce ina ɗaga wayar kuma har lokacin hawaye basu bar fita daga idanuwana ba,

"my baby...... Pls stop crying mana... Haba" ya faɗa cikin lanƙwasa murya, kwanciya nayi nai lamo ina sauraren tausashasshiyar muryarsa mai kama da zuma wurin zaƙi,

"uhmm na manta before in tafi.... Koda yake ma bari za muyi video call anjima"

"Allah ya kiyaye hanya, I love you"

"I love you too baby"

Sai da ya tabbatar da ya kwantar min da hankali na daina kuka sannan muka yi sallama lokacin har ya isa tasha ya samu mota, falo na koma wurin Bishra bayan na tura masa text massage kuma ina gama tura masa na kashe wayata dan tsokana nayi kuma na san zai kira.
***
Bayan sallar magriba ya isa gida, bai samu kowa a gidan ba sai iya daddy domin su mommy sun tafi church, zama yayi suka gaisa da daddy suka ɗan taɓa hira wadda mafi yawan hirar akan halayyar mommy ne wacce har yanzu ta kasa saduda kullum cikin rikici take da neman tashin hankali,

"Daddy dan Allah ka cigaba da haƙuri da halin mommy kar ka ɗauki mataki akan ta.... Daddy bazan so a kaina mommy ta samu matsala da kai ba" Samz ya faɗa kansa a ƙasa fuskarsa ɗauke da damuwa,

"Ka kwantar da hankalinka babu abin da zai faru insha Allah, ai na saba da halin mahaifiyarku...... A gaskiya ba kuyi sa'ar uwa ba, ku yafe min ban samar muku uwa ta gari ba Muhammad"

Jin maganar daddy yayi batai masa daɗi ba duk da yasan mommy ba uwa ta gari bace amma da daddy ya kira ta da wannan sunan sai da yaji wani iri, har lokacin sallar ishah suna tare da daddy yana sake yi masa nasiha akan ya kula dani kuma ya riƙeni amana saboda iyayena dani kaina mun cancanci halacci, bayan sun dawo daga salla ya wuce ɗakinsa, wanka ya fara yi bayan ya fito ya kira wayata wadda nima ɗin tun ɗazu nake kiran sa dan inji ko ya sauka gida lafiya amma network bai barni na sameshi ba wai is not reachable,

Muna zaune a falo nida Bishra muna kallon wani Indian film a tashar zee world naga kiransa, tashi nayi na shige cikin bedroom sannan na ɗauki kiran da yake video call ne,

"Baby.... What are you doing?"

Shagwaɓe fuska nayi kafin nace dashi,

"tun ɗazu nake kiranka amma ban same ka ba, me ya faru?"

"sorry baby.... Nima i wanted to call you, muna tare da daddy ne"

"Ya ka samu mutanen gida?"

"Duk suna lafiya" ya faɗa cikin harshen hausa,

"ya jikin mommy?" na sake tambayarsa,

"Ta samu sauƙi sosai"

"A gaida ta"

"zata ji....., me kika ce ɗazu?"

Fuskata na rufe ina dariya, dariyar shima yayi sannan naga ya gyara zamanshi ya jingina bayanshi da gado,

"Ki bari anjima zan kiraki muyi hira, yanzu zan je wurin su mommy...... Kin ci abinci ko?"

"Naci.... Shikenan ka gaishe su"

Katse kiran nayi na koma falo shi kuma ya ƙarasa shiryawarshi cikin kayan shan iska boxer da ƙaramar t shirt ya fita saboda yaji motsin dawowarsu mommy daga church,

Dukkansu suna zaune a falo banda Hadiza wacce ke cikin kitchen tana dafa musu abin da zasu ci, gaba ɗaya ƙannen nashi sunyi murna da ganin sa amma banda mommy wacce tayi kicin kicin da fuska tun bayan da taga shigowarshi, sama sama ma ta amsa gaisuwarshi wanda sam bai ma yi tunanin zata amsa ba, zama yayi cikin su duk da mommyn bata sakar masa fuska ba, abinci Hadiza ta kawo masa jalop ɗin taliya da ɗanyen kifi, da yake dama shi ba mai yawan magana bane har suka gama cin abincin bai yi magana ba,

"Samuel abin da kayi yayi daidai kenan ko? Ka kyauta abin da kayi ko? Ni mahaifiyarka ni ka juyawa baya ka zaɓi wasu fiye dani...." mommy tace dashi bayan su Mary sun fita daga falon ya rage daga ita sai shi,

"mommy wallahi ba juya miki baya nayi ba har yanzu kina nan matsayin ki na mahaifiyata wadda bani da wani sama dake...."

"shikenan" ta faɗa tana tashi daga inda take zaune zuwa cikin bedroom ɗin ta, ta ɗan ji sanyi kaɗan a ranta da jin abin da ya faɗa mata amma duk da haka wannan bazai canja mata ƙudurin da ta jima dashi a cikin ranta ba, sam ba zata fasa ba daga abin da tayi niyya dan a yanzu ba musuluntar da yayi ne tashin hankalinta ba babban tashin hankalinta wannan auren da yayi wanda take ji ajikinta kamar shine zai raba ta da ɗanta wanda ita kuma ba zata taɓa lamuntar hakan ba.
***
A ɓangaren Hashim kuwa abubuwa sun ci uban na da, fantamawa yake yi ba kaɗan ba shida hajiyarshi hajja Sharifa wadda ke sakar masa kuɗi ko ta ina, gaba ɗaya ya sallama gidan su tun daga ranar da Iya tayi masa korar kare bai sake waiwayar unguwar ba kai ko hanya bata bida shi haka ya bar su Iya cikin ƙuncin rayuwa da halin ƙaƙa na kayi shi bai taimaka musu ba bai kuma bar mai taimakonsu ya taimaka musu ba, ko bikina bai ji ba kuma bai san nayi ba dan shi yanzu ba ta ni yake yi ba ta hajja Sharifa yake yi wacce ta zamo fitilarsa acewarsa ta dalilin ta ne ya soma riƙe manyan kuɗaɗe, duk inda manyan yara suke to zaka samu da Hashim aciki, kullum yana hanyar zuwa party da sauran wuraren shaƙatawa ga uban tarin ƴanmata masu aji da marassa aji duk nasa ne, duniya tana gara masa fiye da yadda yake so, ni kuwa dama ya jima da mantawa dani acikin tarihin rayuwarsa,

Gidan hajja Sharifa yake zaune kuma anan yake tara abokai da ƴanmata suke sharholiyarsu babu mai kwaɓarsu.
***
Shirin bacci nayi cikin kayan bacci na masu taushi, ina kammalawa na haye gado araina ina cewa "Bishra uwar son kallo" dan tana can falo tana kallon wani film, wayata na ɗauka da zummar kiran samz sai ga kiran shi ya shigo, murmushi nayi na ɗauka,

"Hubbi baka yi bacci ba?" na faɗa cikin tsokana,

"Taya zanyi bacci banji voice dinki ba baby...."

"Ni bama zan iya bacci ba saboda baka nan..." na faɗa ina fashewa da kuka a hankali,

"Am soo sorry baby.... Bari kuka mana, ranar Friday zan dawo...... Ba ɗazu kince min idan na dawo zaki bani maganina sau 3 a rana ba?"

"uhmm uhmm" na faɗa ina maƙale kafaɗa kamar yana kallona, murmushi naji yayi kafin ya soma jero min kisses ta cikin wayar, ɗan tsagaitawa yayi kafin yace,

"Idan na dawo ai za a bani ko?"

"Ni ko yanzu ka dawo ma...." na faɗa nima ina kissing ɗin shi ta cikin wayar,

"I love you baby... I don't know how to describe irin yanayin da na samu kaina that night...."

"Kai ba zaka iya describing ba amma ni zan iya" na bashi amsa ina turo baki kamar yana kallo na,

"ok, how did you feel? Tell me"

Gyara kwanciyata nayi sannan nayi gyaran murya nace,

"Zafi, raɗaɗi, zugi etc, sai da naji kamar ansa sabuwar razor blade an yanyaka wurin sannan aka kawo ruwan barkwano aka watsa a wurin, ta hakane kawai zan iya describing maka abin da naji ranar...."

"oh my God...." naji ya faɗa cikin murmushi,

"Ayya sorry baby, ni kuma ranar naji zaƙi fiye da sugar fiye da zuma, and naji zaƙi fiye da Maggi fiye da komai a duniyar nan.... Kuma tun daga ranar na samu nutsuwar da har yau ban sake jin buƙatar wata mace ba.... Thank you for that"

Turo baki na sake yi ina yi masa shagwaɓa shi kuma yana ta lallashi na a haka har na samu nayi bacci,asubar fari kuwa bayan na idar da salla da massage ɗin shi na fara cin karo,

_Mornings would be better if I woke up next to you. Good Morning my love_

Reply na tura masa ko 5 seconds ba ayiba sai ga kiran shi ya kirani video call, ɗayan bedroom ɗin na koma nabar Bishra a ɗayan, saida na fara gasheshi sannan muka yi karatun Alqur'ani tare sannan na ɗora masa Al'azkar ɗin da nake koya masa, ina faɗa yana faɗa da haka na koyar dashi addu'o'i guda biyar,

"Baby cire hijab ɗin mana" naji yace bayan ya rufe littafin dake hannunsa ya ajiye kan bedside drawer,

"Saboda me?" na tambaye shi ina kallon fuskarshi,

"I want to see your chest please...." kunya naji ta kamani jin amsar da ya bani, cire hijabin nayi ina ɓoɓɓoye fuskata,

"please cire night gown ɗin mana"

Turo baki nayi inata noƙe noƙe amma saida na cire, kissing ɗina yake ta yi ta cikin wayar kamar zai cinye ni daga ƙarshe nace ya kwanta yayi bacci muka yi sallama, nima baccin na koma bayan na maida rigata kuma na kashe wayata. Yau dai wuni nayi ina yin baƙi, Anty Salma tazo ƙawar Anty wadda muka je training Lagos tare, bayan ta tafi su Annie suka zo ganin ɗaki su ɗinma basu wani jima ba, lokacin da zasu tafi kamar inbisu haka naji, har yamma inata baƙi washe gari kuma Anty ta kawo min yaranta su Islam suka wunar min saboda jibi zasu koma Abuja, a ranar shima Daddyn samz da uncle ɗinsa suka zo, girki nayi musu musamman duk da su ɗinma basu wani jima ba shi kansa samz ɗin bai san zasu zo ba bare ni, Albarka daddy yayi ta saka min sannan suka tafi,

Da daddare da ya kirani nake sanar dashi zuwansu daddy duk da yayi mamakin zuwan nasu amma yaji daɗi sosai saboda ko babu komai ai naga wani nasa yazo matsugunninmu, da yake yanayi ne na sanyi takure nake cikin bargo nasha uban kayan sanyi harda socks a ƙafata, kuka na fara yi masa babu gaira ba dalili shi kuma dandanan ya ruɗe,

"Baby menene?"

"Ni ka dawo haka"

"2 days remaining insha Allah baby.... But it seems like you are feeling cool ko?"

Kai na ɗaga masa ina ƙaƙalo hawayen shagwaɓa,

"Same here sweetheart nima sanyin nake ji amma na kusa dawowa kinji, ki daina kuka"

Ya jima yana kissing da rarrashi na kafin na yarda nayi bacci, kullum nida shi muna maƙale akan waya inyita zuba masa shagwaɓa yana lallashina da haka har Friday tayi, ai ranar da farin ciki na tashi, tunda wuri na soma shirin karɓarsa, girki nayi masa sannan na gyara jikina dama tuni Bishra ta tafi dan tun safe ta tafi gida wai zata yi baƙi, kwalliya nayi cikin wata maroon ɗin doguwar riga amma irin ta zaman gidan nance bata fita ba saboda bata da nauyi kuma shara shara ce sannan ƙirjin rigar a buɗe yake, turare nasha kota ina sannan na zauna zaman jiransa ina game a system ɗina dan rage lokaci, ƙarfe 3 daidai na yamma ya ƙaraso, tashi nayi naje na buɗe masa gate ya shigo yana sanye da baƙin jeans da green ɗin t shirt an rubuta fresh agaban rigar da baƙin combos a ƙafarshi yana goye da jakar shi kan shi da baƙar p cap, sai baƙin glasses a idonshi kamar yadda ya saba yin shigar shi tun a lagos da na fara ganinshi, tsalle nayi na ɗaleshi lokacin da ya shigo nan ya riƙe ni muna dariya.......... ✍🏻



*Garin dadi littafin kudi ne ga mai bukatar cigaban labarin sai ya tura 500 ta 0774712835 Aisha Ibrahim Access Bank sai a tura evidence of payment ta wannan no 07044644433 ko a tura katin waya da shaidar biya wannan no 07044644433*



_*Ummi Shatu *_👌🏻
[1/5, 12:43] Maman K: ©️ *HASKE WRITERS ASSOCIATION*
_(Home of experts & perfect Writers)_


*GARIN DAƊI.....!*💍💍


*_NA_*

_*UMMI A'ISHA*_


*Wattpad:ummishatu*


{31}


PAID BOOK #500



*Ina kuke manyan mata ƴan ƙwalisa ma'abota son gyara da kece raini, maza ku garzayo ku nemi maman Maryam domin samun lafiyayyu kuma haɗaɗɗun Lagos lace wanda zaku iya samun ɗinkakku da kuma sabbi a ledarsu, kaya iya zaɓinki, gefe ɗaya muna da GHT product, zaku samu,*

~MAI DA TSOHUWA YARINYA

~FEMALE CARE

~REODEO

~VIGOR MAX

~ LONGZIT

~B CLEAR

*DUK ZAKU SAMU WADANNAN KAYA CIKIN SAUKI DA RAHUSA MAZA KU NEMI MAMAN MARYAM AKAN WANNAN NO 07080222187, SIYAN NA GARI MAIDA KUƊI GIDA.....*

~~~Cikin barcina naji wasu lafiyayyun tagwayen kisses bisa kumatuna zuwa kan lips ɗina waɗanda suka yi sanadiyyar katsewar daddaɗan baccin da nake yi cikin nutsuwa da kwanciyar hankali, a hankali na buɗe idanuwa na dake cike da tarin baccin gajiya nan idanuwan nawa suka sauka kan fuskarsa inda yake durƙushe gaban gadon yana kallo na,take ƙwaƙwalwata tayi hanzarin tuno min da a inda nake da kuma halin da nake, cikin azama na sake jan duvet na tuƙunƙune, kau da kansa yayi,

"ki tashi kiyi salla.... We are late" ya faɗa yana ƙoƙarin tashi daga gaban gadon, kai tsaye wurin da aka keɓance domin yin salla ya nufa sai lokacin na kula da yayi alwala tun tuni ashe, cikin rashin sakin jiki na lalubo rigar bacci na nasaka sannan na sauko daga kan gadon ina mamakin irin baccin da

Please Login or Register in order to submit comment