Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

washe gari aka yi yini kuma a ranar aka raka amarya gidanta dake unguwar Kwandila, nikam bayan bikin nan sai da nafi sati ɗaya ina baccin gajiya sakamakon gajiyar da na kwasa, ƴan biki kuwa tuni sun baje sai ƴan gida sune basu tattafi ba,sai bayan bikin sannan nake jin ana maganar bikina wai nan da wata biyu anty harda cewa wai dan Allah in dai daure in yi ƙiba kafin bikin kuma zata haɗo min wani haɗi mai kamar garin kunu in rinƙa damawa ina sha,sai ranar na tabbatar da dagaske nima anfara lissafin aure na, washe gari da naje gidan ƙawalli muke ƙara maganar danni sai naga kamar ansa lokacin yayi kusa sosai maimakon ma ace irin wata huɗun nan ko biyar zuwa shida, dariya ƙawalli tayi tace,

"Keda wannan samz ɗin naki ai gara dai ayi ayi a miƙaku ɗakinku tun kafin haƙurinku ya ƙare"

"me kike nufi?" na faɗa ina harararta,

"Ni babu abin da nake nufi kawai gaskiya na faɗa"

Ban bata amsa ba na ɗauki wayata na yi gefe ina amsa kiran da Samz keyi min, har dare ina gidan ƙawalli sai da nayi sallar ishah sannan yaya Abdul hakim ya maida ni gida, yanzu kam kusan kwana muke yi muna waya yau ma tun 9 muke waya yana bani labarin ta yadda yasan gidanmu har suka zo shida uncle ɗinsa wai gidan anty yaje dayake lokacin da ina Abuja ya taɓa rakani yaga gidan, itace ta bashi phone no ɗin Abba kuma tayi masa kwatancen gidanmu a Kano kuma tun kafin su zo uncle ɗinsa ya sanar da Abba buƙatarsu ta ayi bikin kwana kusa, cikin bargo na shige sosai sannan nace,

"Amma dai kasan bana son barin Kano ko?"

"kina nufin in barki a Kano?"

"Ehh mana"

"OK babu problem zan barki a Kano, duk lokacin da kike son zama dani sai ki zo Abuja lokacin da kika ji bakya son ganina kuma sai ki dawo gidanki na Kano"

"dagaske zaka barni a Kano?"

"Dagaske Allah, zan sama miki gida anan"

"Nagode sweetheart"

"Don't mention it dear"

Kusan kwana muka yi muna hira a waya yana bani labarin irin tanadin da yayi min idan munyi aure nima ina faɗa masa nawa da haka har bacci ya kwashe ni na barshi nan kan waya yana magana shi daya saida yaji shirun yayi yawa babu amsa sannan ya farga.........✍🏻


*Garin dadi littafin kudi ne ga mai bukatar cigaban labarin sai ya tura 500 ta 0774712835 Aisha Ibrahim Access Bank sai a tura evidence of payment ta wannan no 07044644433 ko a tura katin waya da shaidar biya wannan no 07044644433*



_*Ummi Shatu*_👌🏻

[1/5, 12:43] Maman K: ©️ *HASKE WRITERS ASSOCIATION*
_(Home of experts & perfect Writers)_




*GARIN DAƊI.....!*💍💍




*_NA_*

_*UMMI A'ISHA*_


PAID BOOK #500


*Wattpad:ummishatu*



26

*Ina kuke manyan mata ƴan ƙwalisa ma'abota son gyara da kece raini, maza ku garzayo ku nemi maman Maryam domin samun lafiyayyu kuma haɗaɗɗun Lagos lace wanda zaku iya samun ɗinkakku da kuma sabbi a ledarsu, kaya iya zaɓinki, gefe ɗaya muna da GHT product, zaku samu,*

~MAI DA TSOHUWA YARINYA

~FEMALE CARE

~REODEO

~VIGOR MAX

~ LONGZIT

~B CLEAR

*DUK ZAKU SAMU WADANNAN KAYA CIKIN SAUKI DA RAHUSA MAZA KU NEMI MAMAN MARYAM AKAN WANNAN NO 07080222187, SIYAN NA GARI MAIDA KUƊI GIDA.....*

~~~Abu kamar wasa shirye shiryen biki sun kankama gadan gadan a gidan mu kuma sai lokacin na fara jin fargabar auren da za ayi min, ada bani da magana ko buri sai na in ganni a gidan Samz amma yanzu da zarar na tuna sai inji gabana ya faɗi sannan ga wata irin kewa da nake ji ta ƴan gidanmu gaba ɗaya tun kafin in bar gidan sai dai duk da fargabar da nake ciki hakan bai hanani yin kumari ba saboda yanzu bani da wata sauran damuwa ko matsala, kullum muna tare da shi awaya duk da tun zuwanshi bikin Yaya Abdul Hakim bai ƙara dawowa ba sai dai ta waya wannan kam yakan ɓata lokutansa da dukiyarsa wurin hira dani, lokacinsa yake bani sosai kamar bai da sauran wani abu mai muhimmanci a rayuwar sa sama dani, duk wani abu da ya shige masa duhu dangane da addini ni yake fara tambaya ni kuma in bashi amsa gwargwadon sanina da fahimtata wanda kuma ilmi na bai kai ba sai in tambayi Abba, sosai ya dage wurin neman ilmin addini dan duk bayan sallar magriba yake zuwa wurin wani alaramma ɗaukar karatu, ni dai a lokuta da dama ina zama in yi shiru in yi ta tunani dan har yau ban san kowa nashi ba duk da ya sanar dani yana da ƙanne Hadiza, Maryam da Abdallah saboda mahaifinsu dama can sunan musulmai yake saka musu duk da mommy bata so,

A yanda na fahimta samz yana tare da damuwa duk da bai fito fili ya sanar dani ba ya barwa ransa domin damuwar tana da nasaba da mahaifiiyarsa dan gaba ɗaya ta fita sabgarsa ko gaisuwarsa bata amsawa tun daga ranar da yaje mata da maganar yana son zai musulunta, tun daga lokacin idan yayi mata waya bata ɗauka idan ya kira ƙannenshi sun bata wayar bata karɓa fushi take yi dashi sosai kuma wannan abun shine yafi komai damunsa ahalin yanzu, duk da tana fushi dashi hakan bai hana shi sake shiryawa ba ya nufi Kaduna ranar Juma'a, saida yayi mata tsaraba da kayan fruits domin tana mutuwar son kankana da gwanda da abarba da kuma apple, duk ya siya mata harda ƙarin ayaba da lemo, bayan sallar la'asar ya shiga gidan sanye da farin yadi riƙe da kayan da ya siya, tana zaune tsakar gida tare da ƙanwarshi Mary tana yi mata kitso, Mary ce kaɗai tayi masa magana ta hanyar gaida shi amma ita mommy yi tayi kamar bata san dashi ba a wurin,

"Mommy.... Zuwa nayi in baki haƙuri akan abin da nayi miki, pls forgive me mommy..... Dan Allah ki daina fushi dani, fushinki zai iya cutar da rsyuwata"

"Ai Samuel baka ga komai ba, ba dai kace ni zaka watsawa ƙasa a ido ba? Ni da na haife ka na reneka na kula da rayuwar ka ni kayiwa haka ko? To hanya ɗaya ce kuma ita kaɗai zata sa in daina fushi da kai, kayi gaggawar barin wannan addinin ka dawo kiristanci "

" Mommy kiyi haƙuri "

" ka tashi kaje na gama magana "

Tashi yayi bayan ya ajiye mata kayan duk da baida tabbacin zata ci, bedroom ɗinsa ya shiga ya ajiye jakar laptop ɗin shi sannan ya kwanta kan gadonshi, gaba ɗaya ya rasa abin da yake yi masa daɗi, shi dai ya san ba zai iya barin musulunci ba ahalin yanzu haka kuma baya son fushin da mommy keyi dashi, wayar shi ya ciro daga aljihun gaban rigarsa ya lalubo no beloved ya kira,

Ina falon mama ina kallon wani Indian series a tashar zee world naga kiran sa, kallon na kashe na miƙe na koma cikin ɗakina na zauna bakin gado ina yi masa sallama,

"Baby yakike......."

"lafiya lau Honey... Ya juma'a"

"Lafiya lau"

"Lafiya kuwa? Naji kamar akwai abin da yake damunka" na faɗa ina kishingiɗa a jikin gado na, shiru yayi na ɗan wani lokaci yana sake jinjina kulawa ta a gareshi domin ina saurin gane yanayinsa na farin ciki ko baƙin ciki koda kuwa iya muryarsa naji,

"Babu abin da ke damuna kawai na kwanta ne kaina na ciwo kaɗan"

"ayya sorry ko dai fargabar aurence?" na faɗa cikin tsokana, dariya naji yayi kamar yadda na tsammata,

"Fargaba kamar wata ke.... Ni da nake alla alla lokacin yazo in samu abokiyar hirar dare... Kamar in janyo lokacin fa haka nake ji"

"Wacece abokiyar hirar daren taka? Ai na faɗa maka ni bacci zan yi in barka"

"Haba baby..... Ba zaki tausaya min ba"

"Ka san me ƙawalli tace kwanaki?"

"a'a... Me tace?"

"wai in fara koya maka baccin tun daga yanzu, dan haka har baccin rana zaka rinƙa yi"

"zan so haka nima.... May be dama rashinki ne yasa nake kasa baccin amma idan kina nan na san zanyi"

"ai dolenka ma ka koyi bacci...."

"Haba baby...." ya sake faɗa yana murmushi,

"Ehh, da bacci da abinci zan rinƙa baka da yawa"

"kina son na ƙara ƙiba kenan"

"ohh yeah"

"OK babu problem amma ni bana son nayi ƙiba baby..... Haka ya isa"

"amma shine ni kake so in yi" na faɗa cikin shagwaɓa,

"kema kaɗan nake so kiyi amma idan kin yi da yawa babu matsala ina sonki a duk yanda kike"

"thank you Dear, I love you"

"I love you too"

A taƙaice dai mun jima muna hira sannan muka yi sallama. Har Samz ya gama weekend ɗinshi ya koma mommy bata saurare shi ba sai Daddynshi ke kwantar masa da hankali cewar wata rana zata sauko shi dai kawai ya cigaba da yi mata biyayya, ya san zai yi wuya ta sauko musamman ma idan ta ji maganar aurenshi da ni wanda har yanzu ba a faɗa mata ba, sai da aka gama haɗa komai sannan Daddy ke sanar da ita wai next month bikin Muhammad Mu'allim, suma ne kawai bata yi ba nan ta shiga zage zage da yiwa daddy Allah ya isa wai ya raba ta da yaronta kuma ita ɗanta bazai auri musulmi ba,

Kwana tayi tana bala'i ta hana Daddy bacci sai masifa take,

"yaro na... My beloved son shine yau zai auri Muslim ehhhhhh...... Over my dead body...... Samz zai auri Muslim ya fasa auren Felicia.... Impossible... This will not be possible... Allah ya isa tsakanina da ku..... An yiwa yaro na asiri"

Duk maganganun da take yi daddy yana jin ta amma ya rabu da ita da yake shi mutum ne mai haƙurin gaske sai dai ka cuce shi ba dai ya cuce ka ba, har asuba bata yi bacci ba gari yana wayewa ta shirya ta fita duk a tunaninsa church ta tafi, gidan aminiyarta mahaifiyar Felicia ta tafi wato madam comfort, tana zuwa ta fashe da kuka tana zayyana mata abunda ke faruwa,

"Maman Mary inada solution.... Dole na san ba a banza Samz ya zama haka ba, dan haka shawara ta shine muje inda za a raba shi da tsafin da aka yi masa a juya tunaninsa da ƙwaƙwalwarsa ya manta da kowacce mace sai Felicia, nan da next month ɗin sai ayi wedding ceremony ɗinsu " na'am maman Mary tayi da shawarar madam comfort nan suka bazama suka rankaya suka tafi wurin bokansu wanda saida suka yi doguwar tafiya dan sai da suka manta da barin cikin gari tun suna wuce ƴan ƙauyuka da gidaje tsilla tsilla har ya zamana sai sai jeji, tun wayewar gari suke tafiya akan babur amma basu isa ga wannan boka ba sai la'asar sakaliya,

Madam comfort ce ta fara shiga cikin ƴar bukkar bayan ta jima tana yi wa boka bayani ta fito ta kira Maman Mary, tambayar ta boka yayi,

"Duk naji matsalolinki da damuwarki dama dalilin zuwanki nan.... Yanzu me kike so ayi masa?"

"Yawwa boka so nake a juya tunanin sa ya bar wannan sabon addinin da ya shiga ya dawo namu.... Sannan akwai wata yarinya da yake so zai aura amma ni ban san ta ba itama ina so a nisanta ta dashi a mantar dashi ita gaba ɗaya yaji ta fita a ransa ya daina tunawa da ita ya dawo ya auri ƴar aminiyata Felicia....... "

Wata ƙara boka yayi da kuwwa mai tsoratarwa ya shafa ƙoƙon dake gaban sa cike da ruwan tsafi sai ga hoton samz nan ya bayyana raɗau,

" Wannan ne? "

" Ehh shine " inji Madam comfort,

" To angama" boka ya basu tabbaci,

"Boka kar a cutar dashi kawai iya abin da na faɗa maka za ayi masa", "babu matsala zuwa cikin dare zamu gama aikin mu lokacin aiki yafi tafiya daidai" kuɗi ta ajiye masa suka tashi suka sake kama hanyar gida.

Nidai yau tunda na tashi nake faɗuwar gaba barin ma lokacin sallar azahar amma koda na gayawa Anty wadda ta zo gida bayan ta haihu sai take cemin wai dama in dai biki ya kusa haka kowacce mace ke ji kawai dai in tsananta addu'a, addu'ar naketa yi acikin zuciya ta kome nake ina yin wannan addu'ar har magriba inda Samz ya kirani video call ganin sa nayi kamar marar lafiya shima yana zaune gefen titi.........✍🏻


*Garin dadi littafin kudi ne ga mai bukatar cigaban labarin sai ya tura 500 ta 0774712835 Aisha Ibrahim Access Bank sai a tura evidence of payment ta wannan no 07044644433 ko a tura katin waya da shaidar biya wannan no 07044644433*


*_Ummi Shatu_*👌🏻
[1/5, 12:43] Maman K: ©️ *HASKE WRITERS ASSOCIATION*
_(Home of expert & perfect writers)_



*GARIN DAƊI.....!*💍
PAID BOOK #500


_*NA*_


_*UMMI A'ISHA*_


*Wattpad:ummishatu*



27

*Ina kuke manyan mata ƴan ƙwalisa ma'abota son gyara da kece raini, maza ku garzayo ku nemi maman Maryam domin samun lafiyayyu kuma haɗaɗɗun Lagos lace wanda zaku iya samun ɗinkakku da kuma sabbi a ledarsu, kaya iya zaɓinki, gefe ɗaya muna da GHT product, zaku samu,*

~MAI DA TSOHUWA YARINYA

~FEMALE CARE

~REODEO

~VIGOR MAX

~ LONGZIT

~B CLEAR

*DUK ZAKU SAMU WADANNAN KAYA CIKIN SAUKI DA RAHUSA MAZA KU NEMI MAMAN MARYAM AKAN WANNAN NO 07080222187, SIYAN NA GARI MAIDA KUƊI GIDA.....*

~~~Ƙurawa juna ido muka yi kamar yau ne muka fara ganin juna sai dai amma ni ba cikin idanuwansa nake kallo ba kunya bata barina in iya saka nawa idon cikin nasa,

"Mr man..... Ya kake?" na faɗa cikin tsokana,

"Baby..... Lafiya lau nake, kefa?" ya buƙata yana sake kallo na,

"nima lafiya nake"

"ok naji daɗin jin hakan.... Yau saura kwana nawa ma bikinmu?"

"ni ban san saura kwana nawa ba, bana counting" na faɗa cikin shagwaɓata da na saba yi masa ina turo baki,

"ni ina counting ɗin ai, sai anyi magana kice kina sona bayan gashi nan bama kya ɗokin zuwa kusa dani" shima ya faɗa cikin shagwaɓar, dariya na ƙyalƙyale da ita kafin nace,

"ashe dai kaima ɗin shagwaɓaɓɓe ne ban sani ba...."

"Ehh kin koya min" ya faɗa yana lumshe idanuwansa,

"ni ɗin na iya shagwaɓa ne?" na buƙata nima ina gyara kwanciya ta a gefen gado na,

"Baby ai kin iya shagwaɓa..... Yanzu ki bani labarin yau me kika yi dan ban ganki ba throughout sai yanzu......."

"yau babu abin da nayi sannan babu inda naje kawai kusan a kwance na wuni"

"Baki da lafiya?" ya buƙata yana kallona,

"lafiya ta Lau kawai dai bana jin hayaniya ne yau ɗinnan...."

"same here my dear..... Nima yau ɗinnan ina jin jikina very weak..... I don't know what's happening to me..."

"Sorry...."

"Amma baby meyasa gaba ɗaya ni dake muke jin yanayi iri ɗaya?" jin tambayar da yayi min naji gabana ya tsinke ya faɗi domin nima abin da ke kai kawo araina kenan dan kamar ya shiga zuciya ta ya gani,duk da haka ban nuna masa ba sai nayi murmushin jan hankali nace,

" ni da kai ai abu ɗayane ko ka manta ne? Hatta jinin dake gudana ajikinmu iri ɗaya ne, haka zuciyar dake bugawa a ƙirjina kai ma itace ke bugawa a naka ƙirjin... Kaga kuwa idan haka ne to ya zama dole mu rinƙa tsintar kanmu cikin yanayi guda" murmushi naga yayi tare da lumshe idanuwansa, a hankali naji ya furta,

"my clever baby..... You know what? Am eager naga munyi aure ina ganin ki kusa dani kina yimin irin waɗannan sweet sweet words ɗin"

Rufe fuska ta nayi da hannuna guda ɗaya cike da kunya,

"Yaushe zaka zo?" na tambaye shi bayan na buɗe fuskar tawa,

"kina nemana ne?"

"Ehh mana"

"to yaushe kike son ganina?" ya sake tambayata bayan ya miƙe daga zaunen da yake yana tafiya gefen titi,

"ko gobe ma...."

Ɗan shiru yayi alamar tunani zuwa caan naji yace,

"banda gobe..... I have a lot of things da zanyi gobe but insha Allah next tomorrow zan zo Kano...."

"Me zan dafa maka?"

"komai ma baby...."

"zaka sake zuwa idan ka tafi?"

"no, sai munyi aure sannan zan zo"

"baka da zance sai na aure..... Aure dai aure dai"

"to me kike so in ambata wanda ya wuce wannan? Shine a raina yanzu"

Har ya ƙarasa masallacin unguwar su muna hira kuma wani abun mamaki yau gaba ɗaya daga ni har shi kamar bama son yin sallama da juna dan sai munyi sallama sai mu sake ɗauko wata sabuwar hirar, da haka har aka kira sallar isha nan ya shiga salla, nima tashi nayi nai sallar har lokacin jikina a wani sanyaye yake kamar an aiko min da saƙon mutuwa,

Sake kirana yayi misalin ƙarfe 9 na dare yana sanar da ni ciwon kan dake damunsa addu'ar samun lafiya nayi masa sannan na ƙara da,

"wannan Hisnul Muslim ɗin da na faɗa maka wanda ka ɗauko a Play store ka duba shi da kyau duk wata addu'a da kake buƙata insha Allah zaka samu aciki...."

"Baby ai ban iyaba.... Ki koya min"

"Babu matsala bari mu fara tun daga addu'ar farko..."

Hannu nasa na buɗe bed drawer ɗina na ciro littafin Hisnul Muslim ɗina na buɗe muka fara tun daga addu'ar farko, ina faɗa yana faɗa sannan kowacce addu'a sai nayi masa cikakken bayani akanta, har 12 muka kai sannan nace yayi bacci haka ya ɗan huta, sallama muka yi yace zai yi baccin wai amma idan 3 tayi na tashe shi tunda nace ni ba bacci zanyi ba karatu zanyi, saida na fara yin salloli na nayi raka'a takwas sannan na fara karatun littafi mai tsarki, har 3 na kai idona biyu bayan na idar ina shirin kwanciya sai ga kiran Samz,

"Yanzu nake shirin kiran ka fa"

"Na tashi..... Nayi wani mafarki ne"

"Kayi addu'a?"

"Nayi"

"Allah yasa ya zama alkhairi"

Baccina na kwanta na shaƙa cikin kwanciyar hankali shi kuma samz ya kwana yana salla har asuba, washe gari da matsanancin zazzabi ya tashi da ciwon kai, tun yana iya amsa waya har yazo baya iyawa, ai hankali na idan yayi dubu sai da ya tashi, ji nayi kamar in yi tsuntsuwa in tafi Abuja in je in kula dashi, sai yau naji da ace zan iya janyo ranar bikin mu da na janyota ko dan in bashi cikakkiyar kulawa domin tun ina iya samun wayar tashi har ta kai ta kawo idan na kira sai injita akashe, sai zuwa dare sannan naji ta shiga kuma nan ɗinma ba shine ya ɗaga wayar ba wani friend ɗin shi ne Ahmad wanda suke yin aiki tare, shine yake yimin bayanin wai dama Samz ɗin yana da typhoid soo yanzun ma typhoid ɗin nasa ne ya tashi, nidai ban samu jin muryarsa ba sai da gari ya waye har lokacin yana asibiti ba a sallameshi ba, babu abin da ya sauya ko ya canja daga kulawar da muke baiwa junanmu sai dai zuwa Kanon da bai yi ba kenan kamar yadda yaci buri rashin lafiya yayi ta yi har tsawon wasu kwanaki, a ɓangare ɗaya kuma ya ware maƙudan kuɗi ya bawa matar uncle ɗinsa wadda ita ce ke haɗa lefe na ba lefe kaɗai ba kusan duk wani shirye shirye ma wanda ya shafi bikinmu a gidan uncle ɗinsa ake yi dan hatta gidan da zamu zauna ma uncle ɗinsa ya bawa wakilci akan ya samo mana gida mai daraja a Kano acikin manyan unguwanni wai tunda nace a Kano zan zauna, cikin lokaci ƙanƙani aka samu wani lafiyayyen gida a unguwar hotoro, gidane flat mai mutuƙar kyau da aji sabo fil ban san adadin miliyoyin da ya salwantar ba wurin mallakar gidan amma bai sanar dani ba har yanzu saboda yana cikin hali na rashin lafiya, ganin rashin lafiyar tasa ta tsananta ya sanya mahaifinsu da ƙannenshi tafiya wurinsa amma banda mommy wadda tace ko mutuwa zai yi yaje yaita mutuwar ita babu ruwanta, nima na so in je in duba shi amma ƴan gidanmu basu barni ba sai iya su kaɗai ne suka je, anty kuwa kullum daga gidan ta ake kai musu abinci asibitin da suke, ga biki nata ƙaratowa ga ango na kwance yana fama da kansa, ni kaina ni ɗinma bani da maraba da marar lafiyar domin kullum cikin damuwa da tunani nake gashi kullum addu'a ta kar Allah yasa in yi mafarki da ya warke saboda ance idan kayi mafarki marar lafiya ya warke to mutuwa yayi, duk abin da baka so sau da yawa shine yake faruwa, ina cikin bacci wanda ya ɗauke ni mintuna kaɗan da suka wuce nayi mafarki wai Samz ya rasu ai a wani hargitse na tashi hankalina a dugunzume, fuskata sharkaf hawaye sakamakon kukan da nasha cikin mafarkin, wayata na ɗauka jikina na rawa na soma kiran wayarsa........✍🏻



*Garin dadi littafin kudi ne ga mai bukatar cigaban labarin sai ya tura 500 ta 0774712835 Aisha Ibrahim Access Bank sai a tura evidence of payment ta wannan no 07044644433 ko a tura katin waya da shaidar biya wannan no 07044644433*


_*Ummi Shatu*_👌🏻
[1/5, 12:43] Maman K: ©️ *HASKE WRITERS ASSOCIATION*
_(Home of expert & perfect writers)_


*GARIN DAƊI.....!*💍💍
PAID BOOK #500


*_NA_*

*_UMMI A'ISHA_*

FROM THE WRITER OF

SO DA ALAƘA
MIJIN MATACCIYA
KUMALLON MATA
KAMAR DA WASA & REST...

*wattpad:ummishatu*



28

*Ina kuke manyan mata ƴan ƙwalisa ma'abota son gyara da kece raini, maza ku garzayo ku nemi maman Maryam domin samun lafiyayyu kuma haɗaɗɗun Lagos lace wanda zaku iya samun ɗinkakku da kuma sabbi a ledarsu, kaya iya zaɓinki, gefe ɗaya muna da GHT product, zaku samu,*

~MAI DA TSOHUWA YARINYA

~FEMALE CARE

~REODEO

~VIGOR MAX

~ LONGZIT

~B CLEAR

*DUK ZAKU SAMU WADANNAN KAYA CIKIN SAUKI DA RAHUSA MAZA KU NEMI MAMAN MARYAM AKAN WANNAN NO 07080222187, SIYAN NA GARI MAIDA KUƊI GIDA.....*

~~~Ji nayi tamkar in shiga cikin wayar in gano me ke faruwa dashi a daidai wannan lokaci, cikin raina kuwa addu'a nake yi,

"ya Allah ka bawa bawan nan naka lafiya..... Ya Allah ka tsawaita rayuwar sa, ya Allah ka bashi nisan kwana kada ka ɗauki rayuwarsa yanzu ko dan halin da zan shiga.... Ya baki farin ciki a lokacin da na yanke ƙauna da sake samun sa cikin rayuwa ta..... Ya mallaka min komai dan ganin na dawwama cikin farin ciki..... Ya bani lokacinsa da duk wani abu da yake da iko dashi dan kawai in yi farin ciki, ya soni a lokacin da wani ya ƙini.... Yana burin zama dani tun a lokacin da wani ya guje ni.... Ya Allah ka tausaya min kada ka sake yanke min wannan farin ciki..... " na faɗa hawaye na sauka kan kumatu na,

" Baby.... " naji muryarsa ta daki dodon kunnuwa na duk da a hankali yayi maganar sannan kana ji ka san baida cikakkiyar lafiya,

" Dear... Sannu ya jikin naka? " na faɗa cikin hawayen farin ciki, ashe dai bai mutun ba yana nan a raye,

"Da sauƙi..... Amma ina fushi dake"

"kayi hakuri dear.... Menene laifi na?"

"Ba ki zo kin dubani ba"

"zan zo gobe goben nan insha Allah, dama kara nayi da alkunya amma tunda har yanzu kana kwance dole in zo..."

"A'a kiyi zamanki.... Na samu sauƙi"

"nidai duk da haka sai na zo.... Dama burina ka samu sauƙi kayi lafiya sosai"

"ba kya son ayi bikinmu ina kwance....."

"Akan me zan so ayi biki angona yana kwance"

"Kar na kasa baki kulawa ko?"

Share hawayen fuskata na shiga yi ina murmushi ohh wannan mutum ya iya jan magana, daga faɗin abin da ke raina shikenan shine har an juya min magana,

"Kuka kika yi ko?" ya sake tambaya ta,

"A'a...."

"Ga voice ɗinki nan ya sauya.... Waye ya saki kuka? Faɗa min"

"Babu kowa.... Kawai nayi missing ɗinka ne"

"I miss you more baby..... Zaki zo goben in turo miki kudin flight?"

"uhmm uhmm nidai karka turo" na faɗa cikin shagwaɓa,

"no zan turo miki"

Sallama muka yi nan na shiga haɗa kayana cikin traveling bag duk wani abu da zan buƙata na haɗa kayana saboda dama anty nata son in je a fara gyara ni tun kwanakin baya amma naƙi sai aiko min da kayan take amma babu wanda na taɓa amfani dashi dan ƙawalli ta gama tsoratar dani wai wallahi idan na yi wa waɗannan abubuwan shan hauka Samz kashe ni zai yi gara ma in yi sama sama,

A ranar na siyi ticket online nagama komai kuma daga wannan lokacin bamu ƙara magana da shi ba sai kuɗin flight da ya turo min kamar yadda ya alƙawarta daga nan ya kashe wayarsa, ko bacci rabi da rabi nayi asubar fari na yi wanka duk da bana

Please Login or Register in order to submit comment