Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tayi mata,

Wani ɗan mitsitsin garin magani boka ya basu yace a zubawa samz a abinci ko lemo, da zarar yaci shikenan magana ta ƙare, washe garin ranar suka kamo hanya suka nufo gida, kuma tun a hanya ta kira samz tace masa lallai lallai gobe yazo gida tana son ganinsa inyaso ya koma, da yake yanzu baya son ɓacin ranta saboda lalurar hawan jinin da take fama dashi ya amsa mata da to shi kansa daddy lalurarta ce tasa yake ɗaga mata ƙafar da har take cin karenta babu babbaka, ni dai ranar munyi waya dashi mun sha soyayyar mu kuma mun rabu cikin farin ciki yana tsokanata wai wannan weekend ɗin idan yazo sai ya yiwa maganinshi over dose, zai sha babu adadi ni kuma nace to wallahi ashe kuwa zan gudu gida,

Babu wani ɓoye ɓoye lokacin da yaje mommy tace magani ta karɓo masa na neman tsari daga miyagun mutane da shaiɗanu, gashi nan yaci, ba dan ransa na so ba sai dan kawai kar ya ɓata mata rai har hawan jininta ya tashi ya zuba yaci, sam baya son ya sake zama sanadiyyar kwanciyarta a asibiti shiyasa yake kaffa kaffa da tskatsantsan da duk wani umarninta................


*Garin dadi littafin kudi ne ga mai bukatar cigaban labarin sai ya tura 500 ta 0774712835 Aisha Ibrahim Access Bank sai a tura evidence of payment ta wannan no 07044644433 ko a tura katin waya da shaidar biya wannan no 07044644433*





*_Ummi Shatu_*👌🏻
[1/5, 12:43] Maman K: ©️ *HASKE WRITERS ASSOCIATION*
( _Home of experts & perfect Writers_)



*GARIN DAƊI....*💍💍


_*NA*_

_*UMMI A'ISHA*_


*Wattpad:ummishatu*


PAID BOOK #500



{37}


*Ina kuke manyan mata ƴan ƙwalisa ma'abota son gyara da kece raini, maza ku garzayo ku nemi maman Maryam domin samun lafiyayyu kuma haɗaɗɗun Lagos lace wanda zaku iya samun ɗinkakku da kuma sabbi a ledarsu, kaya iya zaɓinki, gefe ɗaya muna da GHT product, zaku samu,*

~MAI DA TSOHUWA YARINYA

~FEMALE CARE

~REODEO

~VIGOR MAX

~ LONGZIT

~B CLEAR

*DUK ZAKU SAMU WADANNAN KAYA CIKIN SAUKI DA RAHUSA MAZA KU NEMI MAMAN MARYAM AKAN WANNAN NO 07080222187, SIYAN NA GARI MAIDA KUƊI GIDA.....*

~~~Ko kallonsa banyi ba bare yasa ran zan kula shi ma, yana kwanciya akan gadon na sauka na bar masa gadon gaba ɗaya, ina turo baki, can kan sofa na koma na yi zamana inata faman harare harare, jin yunwa na neman illatani ya sanyani ɗaukar abincin da ya yi mana order daren jiya,shinkafar sanyi ƙarara amma haka na cuccusa sannan na ci shawarmar dake ajiye gefe,

Ban sake bi ta kan Samz bawan Allah ba dake kwance zazzabi yayi masa kamun kazar kuku domin ruf ya rufeshi irin rufewar da ko numfashi ya fitar to hucin zafi yake, ni duk a tunanina lafiyarshi ƙalau shiyasa nake ta sabgar gabana ban kula shi ba, har azahar, lokacin ne na farga da irin rawar ɗarin da jikinsa keyi, ɗan matsawa nayi dab dashi,

"Baby lulluɓeni....." yace dani jikinsa na karkarwa, hannu na kai jikinsa nan naji zafi sosai,

"sorry....." na faɗa ina lulluɓarsa, duk da ina cikin fushin abin da yayi min amma ajiye fushin nayi a gefe a raina ina cewa sai ya warke zan ɗora daga inda na tsaya, abubuwa nake ta lulluɓa masa amma cewa yake wai inƙara lulluɓarsa dan ji yake kamar ban lulluɓa masa komai ba,

Irin halin da naga yana ciki ai tuni na fara kuka ina yi masa sannu tare da cemasa ya tashi mu tafi asibiti, hannu naga ya miƙo min, ina kamawa yajani jikinsa wanda ya ɗau zafi,

"Sannu.... Dan Allah ka tashi mu tafi asibiti kaji"

"shhh....." yace min tare da sake matse ni, shiru nayi ina sauraren bugun da zuciyoyinmu keyi domin kaina yana ta saitin ƙirjinsa ne, a haka naji ya samu bacci, buɗe idanuwa na nayi ina kallonsa, sai kakkame jikinsa yake yi kamar wanda yake razana cikin baccin, addu'a na soma tofa masa zuwa wani lokaci, can naga ya buɗe idonsa, yunƙurawa yayi ya ɗau wayarsa ya kira Ahmad,

"Dan Allah ka kawo min maganin zazzaɓi mana......, ina hotel bana gida"

Sai da ya sanar dashi hotel ɗin da muke sannan ya ajiye wayar, kallona yayi yace,

"ki buɗe ƙofa Ahmad yana nan zuwa yanzu"

Tashi nayi naje na buɗe sannan na dawo na zauna gefen sa,

"sanyi fa nake ji....." naji ya faɗa yana sake curewa wuri ɗaya na gane nufinsa so yake insake komawa jikinsa, babu yadda na iya jikinsa nasake zuwa na shiga nan ya rufeni ruf haɓarsa bisa kaina. Koda naji motsin shigowar Ahmad lumshe idanuwana nayi nai luf kamar me bacci, har ciki ya ƙaraso bayan Samz yayi masa izini,

"Sorry.... Ya jikin? Wai tun yaushe ne zazzaɓin?"

"Da shi na kwana wallahi.... Gashi ni matsala ta magani bai fiya zama a cikina ba"

"Daurewa zaka yi, Allah ya baka lafiya"

"Amin, dan Allah ka samoma baby abinci"

"ok to ina zuwa"

Saida naji fitar sa sannan na bude idona na kai kallo na kan kyakkyawar fuskarsa,

"Kaga kasa abokinka yazo ya samemu ahaka.... Ko kunya baka ji...."

Turo baki naga shima yayi sannan cikin zafin zazzabi naji yace,

"Dama ai ya san abunda muke yi, soo dan ya ganmu ahaka babu wani abu....."

"Ni dai babu ruwana... Babu abin da muke yi" na bashi amsa ina ɓoye kai na a ƙirjinsa,

"uhmmm" shine abin da yace kawai ya sake matse ni, ahaka Ahmad ya dawo ya same mu inda ya kawo mana abinci cikin take away daga nan yayi masa sallama ya fita, ƙofar naje na rufe bayan fitarsa sannan na dawo wurin samz abincin na taimaka masa yaci kafin ya sha maganin ya koma ya kwanta babu ɓata lokaci bacci ya ɗaukeshi. Nima ɗan taɓa abincin nayi sannan na shiga wanka nayi na fito ɗaure da towel har lokacin bacci yake zama nayi gefensa na kai hannuna ɗaya na taɓa jikinsa, akwai zazzabin sai dai zafin ya ɗan ragu,

Ban ɓata lokaci sosai wurin yin kwalliya ba dan cream kawai na shafa sai turarena na touch na saka doguwar riga marar nauyi onion pink dan gaba ɗaya kayan nawa dama waɗanda na taho dasu na hutawa ne da shan iska dan duk ƙananan kaya ne amma kuma abun haushi sai ga abin da na tarar wata ƙatuwa tare da mijina, wallahi har bana son tunowa wannan abun dan da zarar na tuna sai inji kamar in shaƙe kaina dan ko yawu da ƙyar nake iya haɗiyewa tsabar zafin da zuciya ta keyi,

Salla nayi bayan na idar na zauna nayi addu'o'ina sannan na tashi na koma bayanshi na kwanta tare da rungumeshi ta baya duk da har lokacin bai farka ba, ni na san ina masifar son mijina amma duk da hakan ba zai hana in nuna masa ɓacin raina akan cin amanar da yayi min ba, son da nake yi masa bana jin zan iya rayuwa da wani namijin wanda bashi ba kamar yadda shima ya jima yana sanar dani wai ba zai iya zama da wata mace ba indai bani bace shine lokacin nace masa to kuma idan na mutu fa? Wai wallahi idan na mutu to shi ma haka zai yi ta zama har tashi mutuwar ta zo ta iske shi amma ni dai koda ya mutu kar in zauna haka in yi aure, haɗe rai nayi nace saboda nice baya kishi ko shiyasa zai faɗi haka wai ba rashin kishi bane shi yana baƙin cikin wani ya shiga gonar nan tasa dan dai kawai dan kar yace in zauna kar in yi aure wani yaga sirrinsa inga kamar ya fiya son kai shiyasa yace in yi kuma ni mace ce wata rana ta yuyu inji kewarsa shi kuma gashi ya mutu ai sai asamu matsala, turo baki nayi nace ni babu wani kewa da zanyi saboda azumi zan yi ta yi, dariya yayi yace ashe dai ana yinshi,

Kwantar da kaina nayi a bayansa ina mai lumshe idanuwana, hannuna naji ya riƙe da nashi tashi nayi shima ya tashi, bathroom ya shiga yayi alwala ya fito yayi salla sannan ya sake kwanciya gefe na yana shafa ƙunshin hannuna da tun zuwansa yake ta faman kallo, jikinsa ya jani har lokacin da zazzabi a jikinsa amma tsabar ƙarfin hali haka ya fara kissing ɗina nima ina ramawa, salon soyayyar yau da ya nuna min ta dabance daga ƙarshe ya rungume ni yana mayar da numfashi a hankali zuwa can naji yace,

"Am very sorry baby.... Wallahi banci amanarki ba.... Ban taɓa sanin wata ƴa mace ba bayan ke....."

Saurin rufe masa baki nayi da hannun na domin yanzu bana buƙatar jin komai daga gareshi saboda yanayin da muka tsinci kanmu kaɗai ya isa gamsar dani hakan, kan shi na ɗora bisa ƙirjina na rungume ina shafawa, shima a nasa ɓangaren godiya yake yi wa Allah da ya tsare shi bai biye wa sharrin zuciya da na shaiɗan ya tafka saɓon Allah da Felicia ba da tuni ƙila yanzu ita zai bawa abin da ya jima yana buri,

Ni kaina naji a jikina kamar yanayin na yau ya banbanta da na baya,kallona yayi cikin sanyin murya yace "Gashi bana son taɓa ruwa ya za ayi kenan?", rufe idanuwana nayi ban bashi amsa ba, a daren ranar muka tattara muka bar hotel ɗin muka koma gidansa muka sake buɗe shafin soyayya,zazzabin a yanzu ya sauka gaba ɗaya, ina kwance jikinsa sanye da rigar bacci na naji yace,

" Kamar mun samu baby yau ko?" kafaɗa na maƙale nace, "Ba yanzu ba sai nan da 2 years lokacin mutane sun manta lokacin da muka yi aure, amma yanzu kunya zan ji kowa ya san abin da muka yi"

Dariya yayi ya sumbaci goshina yace "To menene solution?"

"Planning..." na bashi amsa kai tsaye, murmushi naga ya sake yi sannan yace "Da wanne method zaki yi amfani?"

"I don't even know..."

Wayarshi ya ɗauka yana ce min "Ok let us check and see......" ya faɗa kamar gaske nikuma ban san wayo yake yi min ba harda ƙara shigewa jikinsa ina kallo nima,

"Kina son Pills?" kafaɗa na maƙale, murmushi yayi yawuce yace,

"Implan?" kafaɗa na sake maƙalewa alamar bana so,

"ok Injection?"

"No"

"Withdrawal method?"

"uhmmm uhmmm"

"To wanne zaki yi? Kowanne kince a'a"

"ni bana son period ɗina ya rikice.... Kai kayi mana"

Ware ido yayi kafin yayi murmushi yace "ni idan kin yarda withdrawal method zanyi"

Shure shure na fara na shagwaɓe fuska nace ni ban yarda ba sai dai ya je asa masa irin wanda ake sakawa maza shi kuma ya kafe akan lallai ga wanda zai yi saboda kawai ya san ba zan yarda ba.

Bayan sati biyu da zuwana na fara fama da tashin zuciya da amai haka kawai ko babu abin da naci sai inji amai yana taso min gashi kwata kwata na kasa gane abin da nake sha'awa takamaimai dan gaba ɗaya abincin duniya ji nayi na tsanesu duk wanda na sani da ma wanda ban sani ba, shi kansa tun da na fara aman nan ban sake yi masa girki ba sai dai idan ya fita yaci nikuma maltina kaɗai nake iya sha itama tunda nayi amai shikenan naji ta fita a kaina,

Kasancewar yau weekend ne yana gida yana bacci, zuwa 11 ya tashi yayi wanka ya fito ina zaune falo sanye da farar riga iya cinya mai ɗan siririn hannu dama shi nake jira ya tashi, zama yayi kusa dani ya dafa kafaɗa ta yajani jikinsa yana shafa cinyata, kallonsa nayi yana sanye da milk colour din trouser da brown ɗin riga a gaban rigar an rubuta _Beyond Reality_ "nifa yunwa nake ji" na faɗa kamar zanyi kuka,

"Me zaki ci?" ya tambaye ni cikin kulawa, shiru na ɗan yi zuwa can nace,

"Waina da kunun tsamiya"

"Wainar shinkafa?" yatsina fuska nayi nace "Wainar gero da ƙuli ƙuli"

"To shikenan bari in fita in samo miki...." ya faɗa cikin kulawa duk da can cikin ransa tunani yake ta inda zai fara neman wainar gero a garin Abuja dama dama da a ce wainar shinkafa ne ma da dasauki,

"wannan kwaɗayin da kike yi 2 days baby anya na lafiya ne?" ya fada cikin zolaya,

"kai ma ka sani ai.... Ni wallahi bazan koma kano ba sai na haihu"

Kissing ɗina yayi a goshi sannan naji yace "I love both of you"

"We love you too..." na bashi amsa ina kissing lips ɗinsa, fita yayi ina jin sa yana tambayar Ahmad a waya inda zai samo waina da kunun tsamiya Ahmad yace sai dai yaje Zubah kuma ina sa ran can ɗin ya tafi, murmushi nayi na zame hular kaina na soma tsefe kitson kaina dan tuni ya fara damuna amma kuma da zarar na tuna inada ciki sai inji wata mummunar faɗuwar gaba irin wadda ban taɓa jiba.................


*Garin dadi littafin kudi ne ga mai bukatar cigaban labarin sai ya tura 500 ta 0774712835 Aisha Ibrahim Access Bank sai a tura evidence of payment ta wannan no 07044644433 ko a tura katin waya da shaidar biya wannan no 07044644433*



_*Ummi Shatu*_👌🏻
[1/5, 12:43] Maman K: ©️ *HASKE WRITERS ASSOCIATION*
_(Home of experts & perfect Writers)_




*GARIN DAƊI.....!*💍💍


*_NA_*

*_UMMI A'ISHA_*

*Wattpad:ummishatu*


PAID BOOK #500


{36}


*Ina kuke manyan mata ƴan ƙwalisa ma'abota son gyara da kece raini, maza ku garzayo ku nemi maman Maryam domin samun lafiyayyu kuma haɗaɗɗun Lagos lace wanda zaku iya samun ɗinkakku da kuma sabbi a ledarsu, kaya iya zaɓinki, gefe ɗaya muna da GHT product, zaku samu,*

~MAI DA TSOHUWA YARINYA

~FEMALE CARE

~REODEO

~VIGOR MAX

~ LONGZIT

~B CLEAR

*DUK ZAKU SAMU WADANNAN KAYA CIKIN SAUKI DA RAHUSA MAZA KU NEMI MAMAN MARYAM AKAN WANNAN NO 07080222187, SIYAN NA GARI MAIDA KUƊI GIDA.....*

~~~Sai da nayi dagaske kuma nayi ta maza sannan na samu na tattaro ƴar ragowar juriyar da ta rage min duk da can cikin raina tashin hankali ne danƙare, ɗakin na soma bida kallo sannan na dire kallona kan kyakkyawar matashiyar dake kwance kan gadon da nake kyautata zaton na miji nane, fara ce sol mai ƙiba, babu komai ajikinta haka take kwance tsirara haihuwar uwarta sai ko wani matsiyacin pant wanda dashi gara babu saboda baida maraba da babu ɗin, hannunta riƙe da waya tana latsawa, jin motsina ya sanya ta jan blanket ta ɗan rufe jikinta kaɗan tana kallona sama da ƙasa, ni kuwa uwar kishi tuni naji wani abu ya tokare min maƙoshi haka idanuwana sun kaɗa sun yi jajur kamar gauta,

"Wacece ke kuma wa kike nema?" ta faɗa cikin kallon raini da ƙasƙanci cikin harshen turanci,

"Ke ya dace in yi wa tambayar wacece ke, wanda nake nema kuma wurin mijina na zo" na mayar mata da amsa nima cikin harshen turanci domin duk ƙaryar turancinta nima ina taƙama da nawa,

Wani kallo tayi min kafin ta tashi zaune tana sake kallona,

"Ok you mean kece matar Samz? Wannan jaririyar "

"Naji daɗin da kika gane hakan tun lokaci bai ƙure miki ba....."

"Hmmmm...... To ai baki da wani muhimmanci a gareshi, dan da kina dashi da bai ƙyaleki tsawon 2 months yazo yana sheƙe aya dani ba anan... Ohhh wato kin kasa haƙuri kin biyoshi?"

Zazzafan yawu na haɗiye domin zuciyata tafarfasa take yi kamar in je in shaƙeta,

" Kece kike ganin bani da muhimmanci awurinsa amma shi ya san muhimmanci na, zaman sheƙe aya kuma da kika ce kinayi tare da mijina bai dameni ba tun da dama ya jima da bani labarin ki cewa ke ƴar akuya ce kowa ma bi kike, sannan dan na zo wurin mijina ai sai naga kamar banyi laifi ba ko? Sai a tattara a ƙara gaba saboda me wuri yazo, kowanne addini ya girmama mata kuma ya daraja aure sannan ya ƙyamaci fasiƙai...... Ki gaggauta barin gidan nan tun kafin in je in dawo in wulaƙanta ki "

Ina kaiwa nan na fita, jakata dake falo na fincika na bar gidan zuciyata na wani irin zafi da raɗaɗi, ina fitowa naga mai taxi ɗin da ya kawoni yana ƙoƙarin rufe gaban motarsa da alama gyara ya ɗan yi,

" Ahh hajiya ko dai ba a dace ba? Kar dai ba ayi miki kwatancen daidai ba?"

"Ehh ba nan bane, muje ka sauke ni"

Jakata ya ɗauka yasa aciki sannan nima na shiga yaja muka tafi, gaba ɗaya duhu nake gani bana iya ganin komai, samz ya raina min wayo da hankali ko ɗazu da safe da muka yi waya sai da yayi min daɗin bakin da sai da naji kamar na fi kowacce mace muhimmanci acikin rayuwarsa, harda ce min,

"Gwauruwa..... Ni Kinga ina da mata"

Dariya nayi kafin nace masa "Kaine gwauro nima ina da miji, mijina kuma yafi na kowacce mace, gashi kyakkyawa gashi mai hankali, ma'abocin tsafta da iya kwalliya, ya iya saka kaya, ƙamshinsa kaɗai yana sanyaya raina.... Ina missing ɗinshi over"

Murmushi naji yayi sannan naji yace,

"Kina da miji but you are still virgin....."

"No, am not" na faɗa cikin shagwaɓa ina turo masa baki,

"Seriously baby......."

"To kaima saurayi ne sabo fil"

"No, ai ni kin riga da kinyi disvirgin ɗina...." rufe fuskata nayi kamar yana ganina,

"ta yaya? Nida babu ruwana"

"Ohh so kike in faɗa miki?"

"Hajiya ina muka nufa? A ina zan ajiye ki?" muryar mai taxi ce ta katse min dogon tunanin da na faɗa,

"ka kai ni hotel..."

"wanne hajiya?"

"koma wannene kawai kai ni" na bashi amsa kaina na jikin window ina kallon yanda rayuwa ke gudana agarin,

Gaba ɗaya bana cikin hayyacina, hankalina duk baya tare dani danma inata karanta addu'a acikin raina shine sauƙin da na ɗan samu. Ba zan iya gane hotel ɗin da ya ajiye ni ba nan na bashi kuɗinsa duk da banma san ko nawa na bashi ba nayi gaba ina jin sa yana cewa ga canji amma na wuce kawai,

Ɗaki na kama na biya kuɗi sannan aka kaini, ina shiga na zame na zauna a ƙasa jikin gado, gaskiya samz yayi mugun yaudarata dan ko a first night ɗinmu haka ya rinƙa nuna min kamar bai taɓa sanin wata mace ba sai ni, ashe duk salon yaudara ne, wayata na ɗauka ina hawaye na rubuta masa saƙo kamar haka,

_Ka jima kana cin amanata ban sani ba, ashe dama karuwa ka ajiye agidanka shiyasa kayi watsi dani ka ƙi zuwa inda nake to yau Allah ya nuna min da idona na gani, Allah ya isa tsakanina da kai, kuma sai Allah ya saka min, sannan ko Kaine autan maza to na haƙura da kai, ka aiko min da sakina ko ta waya ne._

Ina gama rubutawa na tura masa na kashe wayata zuciyata na cigaba da yi min zafi, wannan sirrin bai cancanci in sanar da kowa ba dan duniya sai tayi min dariya, idan na fallasa wannan sirrin to fa kamar na ɗauki wuƙa na burmawa kaina ne, ko ƴan gidan mu da ƙawalli ba zan iya faɗawa ba, kuka na fara yi cikin ƙunar zuci.

Ina fita daga ɗakin Felicia ta lashi lips ɗinta abin ka da ƴar neman mata take ta ji sha'awata ta yi mata dirar mikiya,

"Wow.... This beb is beautiful..... Shege samz dama wannan Fulani girl ɗin ya samu, ya samu fine girl yana ta morewa abin shi..... To wallahi nima sai na ɗana, i most taste that girl, ko Samz yana so ko baya so sai munyi shearing ɗinta tare"

"Haba no wonder naji yana faɗawa friend ɗinshi wai he's eager yaje wurinta dan rabonshi da ita it's almost 2 months"

Kwanciya tayi ta rungume pillow tana lasar baki a idon zucinta tana hangoni tare da ita muna aikata masha'a amma cikin ranta alƙawari take yi wa kanta na dole sai tayi amfani dani koma me zai faru sai dai ya faru dan ita bata ganin macen da tayi mata ta ƙyale.

A ɓangaren samz kuwa yana bacci lokacin da saƙona ya shiga wayarsa, misalin ƙarfe biyu da wani abu ya farka kuma da tunani na ya farka dan alla alla yake yayi salla sai ya kirani amma me? Koda yazo kirana bayan ya idar da sallar sai yaga saƙon da na tura masa, dafe goshinsa yayi hankalinsa a tashe dan duk tashin hankalin da nake ciki nasa ya ninka nawa, tunawa yayi da zuwan Felicia jiya da yamma wai tazo yi masa weekend kuma tana da interview da zata yi da wani company sun yi magana da mommynshi tace ya bata Accomodation, babu yadda zai yi shiyasa ya bar mata gidan shi kuma ya koma gidan Ahmad ya kwana dan shi dai ba zai kwana wuri ɗaya da ita ba kuma tunda ya baro gidan bai koma ba har yanzun nan, ko ɗazu sai da ya gama yi wa Ahmad hira ta wai so yake yaje ya ganni ya ganni a video call na ƙara girma kuma nace banda ciki, dariya Ahmad yayi yace,

"Allah sarki ni wallahi tausayi ma take bani, haka kawai kana tarawa ƴar mutane gajiya, akan ka auro babbar budurwa ka tashi ka ɗauko ƴar yarinya wacce zaka yi ta cin zalinta..... Wai dan Allah tana iyawa da kai?"

Dariya yayi ya kwanta harda jan blanket ya rufe jikinsa,

" Idan tazo ka tambayeta... Da ina cin zalinta ai da ba zata rinƙa kuka idan zan taho ba..... "

Tashi yayi domin zama bai kamashi ba ya san duk yanda aka yi na zo Abuja ne idan ba haka ba ta yaya zan san cewa Felicia tana gidansa? Yanzu dole yaje ya nemoni duk inda nake sannan ya zama dole yaje ya kori Felicia daga gidansa korar kare koda hakan na nufin fushin mommy akansa,

"Wai in saketa.... Am sorry baby, ai babu saki a auren mu insha Allah.... In sakeki ki auri wani kenan? Ohh my God idan hakan ta faru zan samu heart attack..... No my sweet baby" ya faɗa yana sauya kayan jikinsa, ko rufewa Ahmad gidan bai yi ba ya fita nemana, shine har su tasha, airport kasuwa da duk inda ya san zai iya samu na yasan da ace Anty na gari da gidanta zan nufa kai tsaye, waya ya kikkira Kano amma daga yanda suke gaisawa da ƴan gidan mu ya fahimci cewa ban sanarwa da kowa abin da yake faruwa ba, har magariba tayi yana nemana amma shiru ga waya a kashe wanda ya kira yafi sau ɗari,

Gidanshi ya koma yayi wa Felicia kaca kaca amma taƙi tafiya sai da taga dagaske haukansa yafi nata sannan ta tattara ta fita, shi kam rasa inda zai sa kansa yaji daɗi yayi daga ƙarshe shaiɗan ya fara raya masa ya ɗanje night club ya ɗan sha abin da zai kwantar masa da hankali, girgiza kai yayi domin ko ada lokacin da yake Christian baya shan giya bare yanzu da ya musulunta, giya da neman mata tun asali dama bai san daɗinshi ba bare yanzu,

Yanda na kwana banyi bacci ba haka shima ya kwana cikin damuwa da tunanin inda zai samoni, washe gari har asibiti yaje ya dudduba amma babu labari, gida ya koma ya zauna yayi tagumi yana saƙawa da warwarewa kan inda ya dace yaje, to ko Kano zai koma? Ji yayi gabansa ya faɗi kansa ya fara ciwo, zuwa can ya tuna da wani abu cikin sauri ya tashi ya ɗauko system ɗinsa ya buɗe text massage ɗin da nayi masa ya soma bin diddigi zuwa wani lokaci yaga daga inda na tura masa text ɗin, kai samz jaraba ne a harkar na'ura, kai tsaye hotel ɗin da nake ya nufa, har ɗakin da nake lokacin naci kukana na ƙoshi har hawayen sun ƙafe. Ina yashe ƙasan tiles kamar wata gawa dan ko ruwa da ƙyar na iya sha, abinci kuwa rabona dashi tun jiya, tabbas naji alamun shigowar mutum amma sai nayi zaton ma'aikatan hotel ɗinne sam ban kawo a raina cewa shine ba saboda ban taɓa zaton zai gano nan har yazo ba saboda wayata a kashe take, da yake acikin duhu nake ban kunna wuta ba amma duk da haka ƙamshin turaren black oud da naji sai da na ji ƙirjina ya rirriƙe domin sak irin ƙamshin da mijina keyi wanda nice da kaina na zaɓa masa wannan turaren kuma ni na fara siya masa,

Kamar acikin mafarki naji muryarsa,

"Baby" ai tuni naji wani gagarumin ƙarfi ya zo min, kishin da ya lafa ya motsa nan na rufe ido na fara zazzaga masa masifar da ta jima tana ciciyar raina,

"Mayaudari me ya kawo ka? Ka zo ka sake yi min

Please Login or Register in order to submit comment