Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ba amma gaskiya ta iya kulawa da rayuwar mutum.
*
Saɓe yake da jakarshi ya tare napep ya shiga kai tsaye hotel ɗin da take ya nufa, a bakin ɗakin da take ya tsaya yayi knocking tsawon mintuna 5 ta zo ta buɗe,

"Hashim Kaine? Come in" ta faɗa tana bashi hanya tare da yi masa alama da hannun ta cewa ya shiga ciki,wuri ya samu ya zauna yana gaida ta cike da ladabi,

"any problem?" ta faɗa tana kallon yanayinsa wanda damuwa ta bayyana ƙarara,

"Ranki ya daɗe bani da wurin zama yanzu, an kore ni daga inda nake zaune...."

Shiru tayi na ƴan wasu mintuna kafin ta kalle shi, shi ma itan yake kallo yana kallon shigar da tayi cikin doguwar jar riga mai adon duwatsu kanta ta dan yafa ƙaramin mayafi,

"tashi muje...."

Babu musu ya miƙe suka fita daga ɗakin bayan ta rufe, hotel ɗin suka bari cikin rantsattsiyar motar ta baƙa wadda ke ɗauke da gilasai masu duhun gaske,

Wata sabuwar unguwa suka shiga mai ɗauke da manya manyan gine gine masu aji da matsayi, wani katafaren gida yaga sun dosa wanda ya sha ginin zamani da dashe dashe na manyan shokoki haɗeda flowers waɗanda suka taru suka yiwa gidan ƙawanya, horn tayi wani ɗan dattijon mutum ya leƙo ganin motar ta ya sashi hanzarin buɗe gate ɗin nan ta danna motar ta ciki, shi dai Hashim bin ko ina yake da kallo ba tare da yayi magana ba har zuwa lokacin da ta umarce shi da ya fito bayan tayi parking, cikin ɗaya daga cikin parts ɗin gidan suka shiga nan ya ganshi tamkar aljannar duniya domin komai yaji, falo ne ƙaton gaske ya sha kayan alatu sai bedrooms guda biyu kowanne da royal bed aciki,

"zaka iya zama anan... Daga nan har zuwa lokacin da ka so tashi"

Lumshe idanuwansa yayi gaba ɗaya ma ya rasa irin godiyar da zai yiwa hajja sharifa domin ta sauya rayuwar sa daga haɗuwarsu ta mayar dashi babban yaro abin kwatance agari...........


*Garin dadi littafin kudi ne ga mai bukatar cigaban labarin sai ya tura 500 ta 0774712835 Aisha Ibrahim Access Bank sai a tura evidence of payment ta wannan no 07044644433 ko a tura katin waya da shaidar biya wannan no 07044644433*


*_Ummi Shatu_*👌🏻
[1/5, 12:43] Maman K: ©️ *HASKE WRITERS ASSOCIATION*
_(Home of experts & perfect writers)_



*GARIN DAƊI......!*💍💍



_*NA*_


_*UMMI A'ISHA*_


*Wattpad:ummishatu*



PAID BOOK


*15*




~~~Buɗe kyawawan idanuwansa yayi a kanta bakinsa ɗauke da kalaman godiya,

"zan iya mallaka maka gidan nan gaba ɗayanshi Hashim........ Ka saki jikinka dani kawai"

"nagode Ranki ya daɗe tabbas haɗuwata dake alkhairi ne, ban ma san irin godiyar da zan yi miki ba, haƙiƙa kin sauya rayuwa ta cikin ɗan ƙanƙanin lokaci kin mayar dani mai daraja a idon duniya......"

Lumshe idanuwanta tayi ta buɗesu cikin muryar hutu da rangwaɗa tace,

" Don't mention it..... "

Bin bayanta yayi suka ciga da zagaya gidan tana sake nuna masa sauran ɓangarorin gidan, bayan sun gama tare suka rankaya suka koma cikin gari bayan ya ajiye jakar kayanshi.
**

Kamar yadda muka shirya da anty washe gari da naje wurin aiki hutu na rubuta ina dawowa gida na sanar mata cewa na ɗauki hutun, a ranar ta turo min kuɗin jirgi na biya online,

Har lokacin a cikin damuwa da ƙuncin rayuwa nake babu abin da ya canja, addu'a ta a kullum dai Allah ya tafiyar min da ɓacin ran nan ya sanya farin ciki ko bai kai na da ba,

Ranar Friday na tafi Abuja wurin anty bayan nayi sallama da su Annie da ƙawalli, Anty da kanta taje ta taho dani saboda ban wani san gari ba, dan in banda Anty ta dawo nan ni banda kowa a Abuja yaya Faisal ne ma da yake cewa zamu zauna anan lokacin da ana maganar auren mu. Tun a hanya anty ta fara nuna min rashin jin daɗinta duba da irin yadda na rame na lalace na fiffige, kallo na ta sake yi a karo na ba adadi sannan ta mayar da hankalinta kan driving ɗin da take yi,

"Gaskiya ban ji daɗin yanda na ganki ba Widat.... Meke damunki haka?"

Murmushi nayi mai kama da yaƙe,

"Anty babu komai fa...."

"Haba Widat..... Ai ko ɗan ƙaramin yaro ya ganki ya san akwai abin da yake damunki sai dai idan ba zaki faɗa ba"

Murmushi nayi kawai ba tare da nace wani abu ba da haka har muka ƙarasa gida, baza ido kawai nayi ina kallon gidan anty mai kama da aljannar duniya, komai yaji ko ina gwanin sha'awa,

"Anty kice a aljannar duniya kike.... Wannan ƙaton gida"

"Naki ai sai yafi wannan Widat.... Nima tsohuwa na samu wannan bare ke"

Dariya nayi na bi bayanta ina sake bin gidan da kallo,bedroom ɗin ta tace in saka kayana amma naƙi na saka a ɗakin yaranta wato Islam, Aslam da Sultan. Da daddare muna zaune muna hira anty take ƙara tambaya ta dangane da damuwata sake cemata nayi babu komai,

"Amma babu komai Munatu kika bi kika lalace haka? Barin damuwa a rai dai baya magani bari in faɗa miki, problem shared problem solved"

Ajiyar zuciya na saki sannan nace,

"Anty ai aikin gama ya gama abin da ya faru ya riga da ya faru harma ya wuce sai dai labari........" abinda ya faru tsakanina da Hashim tun farkon haɗuwarmu na kwashe na faɗawa anty, har na gama bata ce komai ba sai bayan da na gama sannan naji tayi ajiyar zuciya,

" Hmm to in banda abin ki Widat menene abin damuwa anan har da zaki bari ɓacin rai yayi tasiri akan ki? Godewa Allah fa ya kamata kiyi da yasa kika gane tun yanzu akan sai bayan kunyi aure sannan ya fito miki da halinsa kinga time ɗin is too late to cry.... Amma yanzu kina da options kina da damar da zaki fita daga rayuwar sa fita ta har abada.... Ke in banda abin ki ma wannan abin da Hashim yayi miki ai minor abune compared to butulcin da maza ke yi wa matayensu...... Widat zaki sha mamaki idan na fara baki irin cases da mata ke kawo mana akan mazajensu wallahi ke sai ki godewa Allah domin naki da sauƙi...... Sauƙin naki shine bai riga da ya zama mijin ki ba amma su yawanci mazajensu ne wasu harda yara biyar shida ko bakwai..... Ki godewa Allah kawai ki mance dashi dama taimako dan Allah kika yi to ladan ki yana gareshi, kuma insha Allah zaki samu mai sonki so na gaskiya wanda zai iya sadaukar da nasa farin cikin akan naki,wanda zai ƙaunaceki ya kula dake sannan ya baki dukkanin gata "

" Hmmmmm to anty insha Allah zan manta da komai " na faɗa bayan naja doguwar ajiyar zuciya dan gani nake kamar wannan lokacin ba zai zo ba, gani nake kamar farin cikina ya tafi kenan har abada zai yi wahala kuma ya sake dawowa. Har 12 muka kai muna hira da anty tana bani labarai kala kala dangane da butulci irin na ɗa namiji wanda ita ganau ce ba wai jiyau ba dan wasu cases ɗinma itace tayi handling ɗin su, ni kam na cika fam da mamaki domin wasu labaran tamkar a shirin wasan kwaikwayo wasu kuma kamar a littafin hausa lallai in dai hakane to wannan duniyar tamu cike take da butulu masu manta alkhairi, ganin 12 na neman wucewa yasa nayi wa anty sallama na shiga ɗaki, ɗakin yaran da girman sa yana ɗauke da ƙananan gadajensu guda uku sai wardrobe da mirror da toilet ɗin su, dama tun kafin zuwa na sultan a wurin anty yake kwana dan haka gadon dake girke da sunan nashi na maye, bayan nayi addu'a na fara tuna labaran da anty ta babbani ɗazu, lallai anty tayi gaskiya da tace ni kamata yayi in godewa Allah da ya nuna min ainihin halayyar Hashim ba wai sai after munyi aure ba, insha Allah zanyi ƙokari in cire kowacce damuwa daga raina kamar yadda anty ta faɗa, da waɗannan tunane tunanen dai na samu nayi bacci na zuciya ta wasai babu damuwar komai.

Rayuwa ta a gidan Anty sai sam barka da godiyar ubangiji domin har na ɗan canja duk da cewa har yanzu akwai ɗan abun da ba a rasa ba amma yanzun dai an samu ci gaba ba kaɗan ba gashi anty babu takura duk abin da nake so shi zanyi haka idan tana gida zama za muyi mu wuni muna hira a haka har na samu kimanin sati uku lokacinne muka yi waya da yaya Faisal yace min zai kawo matar shi gidan anty mu gaisa, a ranar kuwa bayan sallar magrib sai gasu,

Abun mamaki da dariya matar sai taƙi amsa gaisuwa ta sai iya ta anty kaɗai, ko a jikina daga ƙarshe na shigewata ɗaki naje ina chaten da ƙawalli ta wadda take tsegunta min wai yaya Hakim ya tafi Ilorin zai yi wani aiki ita kuma shine har da kuka lokacin da zai tafi wai da cewa ma yayi zai fasa tafiyar, dariya nayi nace mata ai da ya fasa ɗin, ina nan kwance ina ta shan dariyar labarin ƙawalli anty ta leƙo take cemin wai baƙi zasu tafi,

"su gaida gida anty" na faɗa ina daga kwance,

"a'a Widat ba a haka, ki fito kiyi musu sallama ai saboda ke suka zo, ni tun yaushe nake garin amma kinga sun taɓa zuwa?"

Ajiye waya ta nayi na miƙe nabi bayan anty, iskesu nayi suna sallama da anty, nima nace su gaida gida na ɗan taka musu na juyowa ta cikin gida. Bayan kamar zuwan su da kwana biyar kawai ranar a WhatsApp sai naga dogon massage daga yaya Faisal wai dan Allah duk wata hanya ko kafa da chaten ko waya a tsakanin mu in yi haƙuri ya yanketa saboda hakan na neman haifar masa da matsala a gidan sa shi kuma yana son matarshi da zaman lafiyar su sannan bashi da niyyar ƙara aure yanzu, yana yimin fatan samun miji nagari wanda ya fi shi da komai kuma zai yi blocking ɗina, wannan abu yayi mutuƙar yimin ciwo dan har saida na zubar da hawaye, nan take nayi blocking ɗina nima na goge no ɗinsa raina na ƙuna, bayan anty ta dawo daga aiki nake faɗa mata, dariya naga tayi kafin tace,

"hmm ai dama nasan za arina, ai tunda naga wannan matar tashi tana shasshan ƙamshi na san za ayi haka"

"to amma Anty ni nake kiran yaya Faisal ko ni nake yi masa magana online? Wallahi shine yake kirana kuma shi yake yimin magana, daɗin abin ma nice na ƙishi tun farko ba shine ya ƙi ba bare su goranta min, idan ma shine yayi min wannan massage ɗin ko ita ce tayi duk damuwarsu kuma su ta matsewa.... "

" Kowa dai yayi abinsa yagama insha Allah mijin ki na nan yana jiran ki wanda yasan darajarki da muhimmancinki, karma wannan abun ya dameki "

Shiru nayi domin damuwa kuwa ta nawa, ƙarewar damuwa har kuka ma nayi. Sati na huɗu a gidan anty tace min in shirya zamu tafi Lagos tare da aminiyarta anty Salma wacce zata jagorance mu zuwa wannan training ɗin da tace min zamuyi na wani aiki wanda za muyi wanda ya shafi na'ura mai ƙwaƙwalwa, aikin ita ya dace tayi amma ganin yanda nake da naci da ƙoƙari akan computer yasanya tace ni inje in yi ta san zan iya, tare da ƙawarta Anty Salma zamu tafi zamu je muyi 1 month, kayana duk na gama shiryawa ranar Lahadi muka wuce Lagos domin ranar Monday za a fara training ɗin, wannan shine mafarin sauyawar rayuwa ta domin acanne labarin zai fara wanda yake cike da ƙalubale masu tarin yawa............ ✍🏻



*Garin dadi littafin kudi ne ga mai bukatar cigaban labarin sai ya tura 500 ta 0774712835 Aisha Ibrahim Access Bank sai a tura evidence of payment ta wannan no 07044644433 ko a tura katin waya da shaidar biya wannan no 07044644433*


*Ina mata ƴan ƙwalisa ƴan kwalliya masu son burge mazajensu da gyara kansu cikin sauƙi rahusa ga dama ta samu ku garzaya ko nemi maman Maryam domin huce takaici, zaku samu haɗaɗɗun ɗinkakkun Lagos lace cikin farashi mai sauƙi gefe guda kuma ga GHT product domin gyara ku, zaku iya tuntuɓarta ta wannan no 07047034063 kada ku manta nima Ummi Shatu da bazarta nake rawa dan siyan na gari maida kuɗi gida*

_*Ummi Shatu*_👌🏻

[1/5, 12:43] Maman K: ©️ *HASKE WRITERS ASSOCIATION*
_(Home of experts & perfect writers)_



*GARIN DAƊI.......!*💍💍



*_NA_*

_*UMMI A'ISHA*_



*Wattpad:ummishtau*


_Kina raina a har kullum ƙawata Khadija Sidi, fatan alkhairi agareki a duk inda kike._



16



~~~Misalin ƙarfe 3 da wasu ƴan mintuna muka isa cikin garin Iko cunkus ɗakin tsumma, awani katafaren haɗaɗɗen hotel muka sauka mai suna MORNING STAR HOTEL wanda acikine za a gabatar da training ɗin kuma nan suka namu masauki, bedroom guda ɗaya muka kama nida Anty Salma domin na faɗa mata nidai tsoro nake ji bazan iya zama ni ɗaya a ɗaki ba,

Abinci Anty Salma tayi mana order bayan mun ci munyi wanka na ɗan kwanta domin huce gajiya, ina kwance ina tunanin rayuwa ta da irin yanda komai na rayuwa ya juya min baya kuma yayi min atishawar tsaki, komai ya tsaya min cak bana jin daɗinsa kullum cikin tunani da damuwa nake na kasa dainawa, ƙarar wayata ce ta katse min tunanin da nake yi nan na ɗauka ina murmushi saboda ganin Anty ce,

"Matafiya an sauka lafiya?"

"Lafiya Lau anty yasu Aslam"

"Alhamdulilah, to Allah ya huta gajiya"

"amin Anty sai munyi waya"

Katse wayar nayi ina sake shiga cikin sabon tunani domin shine aikina ahalin yanzu, daren ranar tun 8:30 nayi bacci saboda tsabar uwar gajiyar da nake tattare da ita, zuwa asuba ni nafara tashi sannan na tada Anty Salma, zama nayi nai karatun alqur'ani har zuwa lokacin da rana ta soma ɓullowa lokacin tuni anty Salma ta shirya, nima wanka nayi na shirya tsaf cikin doguwar gown dark purple banyi wata doguwar kwalliya ba in banda powder da lipstick da na shafa ko kwalli ban saka ba nayi rolling da squeeze veil baƙi na saka takalmi toms baƙi, face mask na saka a fuska ta kamar yadda dokar training ɗin take dole asaka mask sannan a bayar da tazara, side hand bag ɗina na rataya light purple bayan na fesa turaren black oud,

Anty Salma dai tsayawa tayi tana kallona tare da sakin murmushi nima kallonta nayi kuma naji shigar ta ta burge ni domin doguwar riga ta atamfa ta saka tayi rolling da babban mayafi da ganin ta Kaga matar aure kamila,

"Widat ƴar gayu, karfa muje ki haɗa mana go slow awurin training ɗin"

Dariya nayi na wuce gaba tana biye dani a baya,

"Lallai anty Salma abinma harda tsokana"

"tsokana ko gaskiya? Kinga yanda kika sha kyau?"

Murmushi nayi bance komai ba muka jera har cikin babban hall ɗin da zamu gudanar da training ɗin wanda tuni har mutane sun fara zuwa a nata registration, kujera muka samu muka zauna kusa da wasu mata suma su biyu, ido na shiga tsittsillawa ina kallon cikin hall ɗin da mutanen dake cikin sa, bayan kamar mintuna biyar da zaman mu wani farin guy yazo saitinmu ya sha ƙananan kaya,

"kunyi signing?" ya tambaye mu cikin turanci, bashi amsa muka yi da cewa "a'a" mu ɗinma cikin harshen turanci,

Wani ya ɗagawa hannu wanda nidai banga ko wanene ba domin kaina yana ƙasa ina duba wayata ina kallon status ɗin yaya Abdurrashid babban yayanmu wanda ke bin Anty shima lawyer ne amma na gwamnati ba irin sauranba yana can Federal University dake Enugu yana lecturing inda yake koyar da Administrative law, jin anty Salma ta taɓani ya sani karɓar pen ɗin hannunta na rubuta sunana da phone no da state sannan nayi signature nasa date, duk yana tsaye yana kallo na ko ince suna kallo na domin bashi kaɗai ke kallo na ba har da wannan farin guy ɗin na farko wato wanda ya fara zuwa wurin mu. Saida aka gama registration sannan aka buɗe da addu'a aka ɗan yi jawabai jawabai na maraba tare da maƙasudin wannan training wato aiki ne da zamu bi mu lissafe tare da ƙidaya dukkanin kamfanoni da masana'antu haɗida shaguna dake kowacce jaha, daga nan akace za ayi breakfast sai a fara training dama already an shirya wurin cin abinci,

Ko a gida ni ba kasafai nake cin abubuwa ba barkatai musamman masu maiƙo domin sukan sanyani rashin lafiya irin ciwon ciki, ulcer da sauran su, ganin pepper chicken da donuts sai kayan tea ya sani yatsina fuska, iya naman kaɗai na samu na ci sai ruwan tea, na tattara kayan fulawar na mayar musu abin su, bayan an gama breakfast aka fara training wanda saida aka fara raba mana manual ɗin da zamu yi amfani dasu, tunda muka zauna ba mu tashi ba sai da lokacin salla yayi awurin salla ne muka rinka haɗuwa da mutane sosai waɗanda suka zo daga Kano amma kuma ba mu san su ba suma basu sanmu ba, bayan an dawo daga salla aka yi lunch wanda wannan ɗinma dai ɗan tabawa nayi kawai saboda yanzu bana iya cin abinci komai daɗinsa, Anty Salma dake kusa dani tashi tayi dan zuwa bathroom, kamar jira yake sai gashi yazo kusa dani,

"Me ke damunki? Naga bakya cin abinci da yawa ko baki da lafiya?"

Juyawa nayi na kalle shi, wannan ɗan farin ne wanda ɗazu naji a kira shi da Samir, murmushin ƙarfin hali nayi na kalle shi,

"lafiya ta Lau, naci abinci mana, dama iya cina kenan bana iya cin fiye da haka...."

Murmushi shima naga yayi kafin yace, "anya kuwa? Idan baki iya cin abinci a cikin mutane ba ki faɗa min sai in yi miki take away ki tafi dashi" girgiza masa kai nayi alamar nagode kuma bana buƙata duk waɗannan maganganun muna yin su ne cikin turanci domin Bayer Abe ne baya jin hausa kwata kwata, godiya nayi masa ya miƙe ya tafi ba wai dan ya so ba, haka da yamma lokacin da za a tashi da aka zo rabon snacks wanda zamu tafi dashi as dinner saida yayi min doubling lokacin da yazo kaina wai yana lura dani yaga ban wani ci abinci da yawa ba dan haka ga guda biyu nan in tabbatar na cinye da daddare da yake shine yake kula da ɓangaren abincin da zamu rinƙa ci awurin har agama,

Godiya nayi masa na wuce nabi bayan anty Salma, tsokana ta ta fara yi wai daga zuwa kuma shine har nayi saurayi dariya nayi nace "Anty rufa min asiri ina ni ina yaren da ba nawa ba". Washe gari kamar jiya yauma doguwar riga na saka dama kuma ni koda yaushe shiga ta kenan sam bana jin daɗin wasu kaya idan ba dogayen riguna ba, yau rigata royal blue ne colour ɗinta sai nayi amfani da farin mayafi na saka takalmi toms blue, kamar jiya yauma banci abinci sosai ba gashi na tashi da ɓacin ciki sakamakon pepper chicken ɗin da naci jiya da daddare mai uban yaji wanda aka saka mana cikin take away ɗin da aka ba mu, duk dai zaune nake gashi zaman ma babu daɗi, lokacin da naje yin signing Samir sai sannu yake yimin kamar yasan bani da lafiyar, a ranar aka yi mana test dangane da abubuwan da aka koya mana jiya da yau through online, zuwa 5:30 aka tashi dama haka ƙa'idar take, muna fita daga hall ɗin Samir ya boyoni nan ya karɓi no wayata, kuma a ranar ya fara kirana abu kaɗan sai ya kirani, ko test ma idan anyi shi yake faɗa min score ɗina haka idan ana yi sai yazo yaga abin da nake yi amma ni dai duk ban wani ɗauke shi serious ba dan na san relationship dashi matsala ne tunda ba yarenmu ɗaya ba,

Yau kam kaina wani irin ciwo yake yi wanda daƙyar nake buɗe idanuna amma haka na daure naje training ɗinnan, miƙewa nayi na wuce bathroom ina hawa step muka yi karo dashi, cikin azabar ciwo na ɗago na kalle shi, dama na saba ganin shi a hall ɗin domin yana ɗaya daga cikin trainers ɗin amma ban taɓa yi masa kallon tsaf ba sai yau, dogo ne mai ɗan jiki irin su ne ake kira da giant, wankan tarwaɗa, idanuwansa manya ne round, ƙwayar idonsa fara ce sol hakanne yasa baƙin ɗison dake ciki yin kyau na musamman, magana ta gaskiya gayen yana da kyau ƙarshen kyau domin komai yaji a halittarsa, gemun da ya tara shi ya sake ƙawata kyawun fuskar tashi mai haɗe da saje, kallon farko idan kayi masa ba zaka taɓa zargin wai ba musulmi bane domin shigarsa da siffarsa tamkar musulmi yake dan ko yanzun ma sanye yake da manyan kaya riga da wando na wani light brown ɗin yadi wanda yayi mutuƙar amsar sa harda hula zannabukar, idanuwana ne suka sauka kan abin hannunsa wanda ke ɗauke da wani ɗan ƙaramin cross a jiki,

"Sorry..." ya faɗa yana ƙoƙarin matsawa daga gaba na, kai na ɗaga masa na wuce cikin bathroom ɗin domin duk a jere suke na maza can gaba na matan daga farko, sharrin shaiɗan da zuciya sai naji duk duniya babu wani namiji da ya taɓa yimin kuma ya burge ni kamar wannan bawan Allahn, ji nayi duk duniya shine namiji na farko da yayi nasarar tafiya da tunanina lokaci guda, abin da zan yi nayi na lallaɓa na fito, ada ban damu da kallon wurin da trainers ke zama ba amma yau gaba ɗaya hankalina wurin ya tattara ya koma kuma ba kowa idanuwana ke son gani ba face wannan guy ɗin wanda naji ana kira da Samz,

"Ya Allah..... Karka ɗora min abin da bazan iya ba, ya Allah kaji tausayina, kaji tausayin zuciya ta" na faɗa ina ɗauke idona daga kansa inda yake can nesa yana zaune da earpiece a kunnen shi yana latsa wayar hannunshi, ni kam yau kamar wata doluwa haka na koma dan har aka gama aka tashi yau bana fahimtar komai sai aikin satar kallon samz wanda inada tabbacin shi bai ma san ina yi ba.

Na ɗauka abin na wasa ne amma koda muka koma masauki sai naji abin na neman ta'azzara domin wasa wasa tunanin wannan bawan Allah yana neman wuce gona da iri cikin zuciya ta, ada ina ganin kamar duk mazan duniya babu tamkar Hashim sai a yau na ƙaryata kaina domin abin da nake ji dangane da samz ya ninka abin da naji akan Hashim da riɓi dubu, da ƙyar na samu nayi bacci ina muradi tare da ɗokin gari ya waye inje in sake ganin sa, washe gari ko anty Salma sai da tayi mamakin shiryawa ta domin sammako nayi haka kusan mune farkon zuwa bai fi mutane biyar muka tarar sun riga mu ba, shiyasa akan idon mu kusan kowa yazo, nifa? Ai ina nan zaune na zubawa ƙofofin shigowa ido gaba ɗaya in kalli nan side ɗin in kalli ɗayan side ɗin ina son inga ta inda zai shigo, a bisa dukkan alamu yau ya makara ne dan duk trainers ɗin sun riga shi zuwa shine na ƙarshe, wani sanyi naji acikin raina lokacin da na ga yayi slizing ƙofar yana shigowa, sanye yake da baƙin jeans da t shirt mai dogon hannu da botira a gaba red & blue colour yasha p cap da baƙin takalmi combos, idanuwansa sanye cikin baƙin glasses da earpiece a kunnenshi, shagala nayi da kallon sa gaba ɗaya amma a ɓoye babu wanda ya sani, ada ni mai ƙoƙari ce dan har tashi nake yi in bada amsa ko in yi explaining ɗin wani abu amma yau da aka tasheni in yi bayani kasawa nayi, abin da ya bawa kusan kowa mamaki, kamar kar a tashi nake ji domin Friday dai ce na san bazan sake ganin sa ba sai ranar Monday, Samir kuwa harda biyoni da wani abincin kamar yadda ya saba wai in tafi dashi, jikina a sanyaye na koma masauki, nayi wanka na shirya bayan na ɗan huta, ina yin sallar magriba na hau online, ina hawa naga sabuwar special no tayi min magana, buɗewa nayi araina ina tunanin waye kuma wannan,

"Maimunatu me ke damunki? Yau kamar kina cikin damuwa...." shine abin da naga an rubuta da harshen turanci, komawa nayi

Please Login or Register in order to submit comment