Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da kaina farfesun kifi sai sakwara da miyar dage dage kuma da wuri yazo dan lokacin da yazo ba afi 12 ba,

Farar shadda ya saka da hula dara baƙa, nikam ban yi wata kwalliya ba dan yadda naga take takensa tun kafin yazo yasa na shiga taitayina, powder kadai na shafa sai kwalli sai ko dan lipstick da na goga ta wuri ɗaya nayi kuskure da na daddage nasha turare kamar anyi ɓarinsa bayan kuma na san yana daya daga cikin abubuwan dake jan ra'ayinsa, baƙar doguwar riga na saka na yafa dan siririn mayafinta na fita na sameshi falon saukar baƙi yana waya da daddynsu, ganin shigowa ta ya mika min hannu na maƙale kafada naƙi zuwa murmushi yayi ganin na zauna can nesa dashi,

"Ehh daddy ina Kano yanzu haka naje duba jikin Maimunatu kasan tun last tafiyan da nayi ban dawo ba sai yanzu.... Gata...."

"Gashi daddy zai yi magana dake...."

Dama na san ba zai barni nesa dashi ba kuma da biyu yacewa daddy bari ya bani wayar wato dai dole sai nazo kusa dashi, ai kuwa ina zuwa ya zaunar ni kusa dashi ya riƙeni, gaisawa muka yi da daddy ya sake duba ni dama kuma muna gaisawa a wayata lokaci zuwa lokaci, bayan munyi sallama ina kokarin tashi ya riƙeni yana kokarin saka idanuwansa cikin nawa amma naki,a gurguje yayi sallama da daddy sannan ya ɗago kaina,

"baby yakike?"

"am fine dear..."

"bakya missing dina? Nifa i have been missing you a lot"

"Same here...." na fada ina kissing ɗinsa a kumatunsa guda ɗaya,

"to yaushe zaki dawo? Ko zamu tafi tare?"

"a'a ba tare zamu tafi ba"

"sai yaushe?"

"nan da 2 weeks"

"Haba baby.... 2 weeks yayi yawa"

"zo Kaci abinci inyaso sai muyi maganar tafiyar daga baya"

Yana manne dani yaci abinci duk ya hanani sakat ya hanani motsawa nan da can, a takaice dai a gidan ya wuni, duk sai da muka bi sashen su mama da Annie na kai shi ya gaida su daya bayan daya, koda muka fito cemin yayi wai to in rakashi gidanmu last time yayi mantuwa dan Allah in rakashi ya ɗauko, dariya nayi na sake maƙale hannunshi dake cikin nawa,

"wai dan Allah menene matsalarka? Idan kayi hakuri ma ai na kusa dawowa"

"ba zaki raka ni ba?"

"ka bari idan ka tashi tafiya sai ka biya ka dauka daga can sai ka wuce"

"baby wayonki yayi yawa" ya fada yana lakuce min hanci, "kaima haka" dariya yayi kawai bai sake maganar ba, zuwa yamma yayi mana sallama ya tafi kuma a ranar da daddare Abba yake cewa su mama ai yadace nima in tattara in koma tunda dai lafiya nake babu wata matsala amma sai mama tace adai kara barina in warware in kara koda sati biyu ne inyaso sai in tafi,

Ai ina fada masa abinda gida suka ce ya fara murna wai da ya zaci baza a barni in dawo yanzu ba sai nayi irin wata biyun nan zuwa biyar dariya nayi nace haba sai kace ana hauka. Lokacin da na fara lissafin tafiya ziyara na kakkaiwa yan uwa da abokan arziki kafin in koma dan idan na tafi ban san lokacin dawowata ba sai Allah shiyasa wannan karon kayana na kwasa rankatakaf kaɗan na bari, naje gidan ƙawalli na wuni Irfan ɗinta har yayi wayo sosai ya girma kai kace yayi wata uku, ƙunshi nayi da kitso da duk wani gyara wanda na san ya dace inyi, washe gari na koma, lokacin da naje bai taso daga office ba amma ya kusa, duk da bana nan amma gidan babu wani datti mai yawa da alama yana kula da gidan kuma yana gyarawa.

Tun kafin ya dawo na shiga kitchen na dora mana girki inata dariyar zumundinsa ni kadai dan sai murna yake yana cewa wai shi yau ango yake, noodles na dafa mana jallop nasa kifi da vegetables dan ita kadai ce mai sauƙin dafawa,bayan na gama na sake gyara jikina na caba kwalliya nasa wani leshi fited gown ɗaya daga cikin wanda na ɗinka zuwa na Kano a sunan ƙawalli,

Ƙarfe 6 ya shigo, da gudu na ƙarasa na rungumeshi tare da daleshi, rungumeni shima yayi yana sinsinar jikina cikin farin ciki da tsantsar soyayya,

"welcome back my baby love...."

Ya yaba da kwalliyata sosai dan sai farin ciki yake yana saka min albarka, kai gaskiya munyi missing juna ba kaɗan ba, haka dai muka kwana cikin farin ciki bayan mun raba dare muna shan soyayya kamar waɗanda suka shekara basa tare, cike da farin ciki da ƙaunar juna muka yi bacci nidai saboda tsabar gajiyar da na kwasa washe gari ko tashi banyi ba ina bacci ya shirya ya tafi office bai tasheni ba, sai 10 sannan na tashi wannan dinma yunwa ce ta tadani, mamaki ne ya kama ni lokacin da na kunna wayata naga time wai har 10, kamar dama jirana yake in kunna wayar sai ga kiransa, da murnata na daga kiran ina kokarin sauka daga kan gado,

"Ina kwana...." na fada cikin shagwaba,

"morning my love.... Kin tashi"

"na tashi yanzu, shine ka tafi baka tasheni na ganka ba"

"am very sorry, bari in kiraki video call sai ki ganni"

Brush naje nayi sannan na wuce kitchen muna yin vedio call din ina kallonsa yana kallona, kwai kadai na soya sai tea da na hada nasha, sai bayan da na kammala sannan muka yi sallama saboda shima zai shiga meeting, muna yin sallama na yunkura zan tashi dan inje inyi wanka na soma jin kukan mage da na kare duk lokaci guda........


*Garin dadi littafin kudi ne ga mai bukatar cigaban labarin sai ya tura 500 ta 0774712835 Aisha Ibrahim Access Bank sai a tura evidence of payment ta wannan no 07044644433 ko a tura katin waya da shaidar biya wannan no 07044644433*


*_Ummi Shatu_*👌🏻
[1/5, 12:43] Maman K: {47}

*Ina kuke manyan mata ƴan ƙwalisa ma'abota son gyara da kece raini, maza ku garzayo ku nemi maman Maryam domin samun lafiyayyu kuma haɗaɗɗun Lagos lace wanda zaku iya samun ɗinkakku da kuma sabbi a ledarsu, kaya iya zaɓinki, gefe ɗaya muna da GHT product, zaku samu,*

~MAI DA TSOHUWA YARINYA

~FEMALE CARE

~REODEO

~VIGOR MAX

~ LONGZIT

~B CLEAR

*DUK ZAKU SAMU WADANNAN KAYA CIKIN SAUKI DA RAHUSA MAZA KU NEMI MAMAN MARYAM AKAN WANNAN NO 07080222187, SIYAN NA GARI MAIDA KUƊI GIDA.....*


~~~Bazan iya kwatanta yanayin tsoro da firgici da na shiga a lokacin ba domin gaba daya komai ya kwance min haka na nemi addu'a a bakina ko daya na rasa, jikina kuwa tamkar mazari dan tsabar rawa da kakkarwa, tamkar zan suma dan tsabar tsorata to abune da baka san dashi ba kuma baka kwana dashi ba sannan na tabbata a gidan babu kare kuma babu mage to idan da akwai ma tayaya zasu shigo har cikin part dinmu? Koda na bude idanuwana baƙake na gansu sidik gwanin ban tsoro kowanne ya bude baki babu kyan gani sai lokacin na samu addu'a tazo bakina na fara ƙwallawa da ƙarfi cikin rawar murya da rawar jiki, da rarrafe da jan jiki na samu na shige cikin bedroom har lokacin cikin tsananin tashin hankali nake, ina shiga na sakawa ƙofar key wayata ma ashe can na barota,

Da wannan tashin hankalin na wuni ranar ina cikin bedroom kunshe na kasa koda bude kofar ne bare in iya fita falo duk da ina jiyo karar wayata anata kirana tun jimawa, har cikin bedroom ɗin ma tsoronsa nake dan ko toilet na kasa shiga saboda gani nake kamar zan gansu aciki gashi sai gizo suke yimin acikin idanuwana, addu'a naketa yi ina karawa amma har lokacin a firgice nake, zuwa yamma ya dawo ko time din tashinsa bai bari yayi ba ya taho saboda yanata kirana amma wayar nata ringing ba a dauka shiyasa ya taho da wuri dan ya dubani yaga ko lafiya,

Ina bude ƙofar bedroom din bayan yayi knocking na tabbatar shine na fada jikinsa ina kuka daga ni sai rigar bacci wadda ko wanka ban samu damar yiba haka na wuni cikin tsoro da fargaba,

"baby.... What's happening??"

"Wallahi wani baƙin kare ne da bakar mage acikin gidan nan, muna gama waya da kai na gansu kamar zasu cinyeni...."

"what? Acikin gidan nan?"

Tare muka koma falo ina makalkale dashi muka je ya shiga duba ko ina har su kitchen amma babu alamar komai aciki daga karshe ya tisani da tambayar wai anya ba mafarki nayi ba ko kuma kawai firgita nayi ba?

"baby are you sure ba mafarki bane?"

"wallahi sweet ba mafarki bane da idona na gansu"

"ok am sorry"

Har bathroom sai da ya rakani sannan nayi wanka na fito ga uwar yunwa dake ciciyata, sama sama na shirya ban bata lokaci wurin kwalliya ba muka wuce kitchen na dora mana abinci. Tun daga wannan rana na kasa sakewa acikin gidan kullum cikin fargaba nake saboda zan iya ganinsu kowanne lokaci kamar yadda suke yimin gizo ba dare ba rana amma sunfi yimin a lokacin da baya nan, idan yana nan koda weekend bana ganin komai kuma bana jin kukan komai amma da zarar baya nan shikenan nikuma zaman lafiyata ya kare sai gane gane da jin koke koken mage da haushin kare gaba daya duk sai zaman gidan naji ya isheni ya fita a kaina kamar in tattara in gudu haka nake ji duk nabi nayi fiki fiki dani shi da kansa sai ya fara tausaya min yace bari mu kira anty mu sanar mata, da kansa ya kirata ranar bayan ya dawo daga aiki da daddare bani wayar yayi na zayyane mata komai da nake ji kuma nake gani nan anty tace to in dage da addu'a sannan in kiyaye duka azkhar haka kuma in yawaita karatun alqur'ani mai girma da saurarensa daga karshe tace mu samo ƴayan habbatussauda in rinka zubawa a garwashi ina turara gidan dashi kamar yadda ake saka turaren wuta,

Bani ba shi kansa gidan ya fita masa akai saboda gaba daya yaga a takure nake wannan dalilin yasa ya fara neman gida babu shiri dan yace gara mu tashi mu canja gida sai dai baya son nesa da wurin aiki yafi son inda yake dan kurkusa da wurin aikinsa, cikin sa'a ranar yazo min da labarin an samu wani estate kamar wannan wanda muke ciki kuma wani dan office din su ne ma ya sama masa saboda shima aciki yake tare da matarsa wadda basu wuce 4 months da aure ba wai itama kuma daga Kano ya aurota amma shi asalinsa dan zaria ne,

Cikin lokaci kanakani yabiya kudin gida yayi komai muka fara harhada kayanmu nidai farin ciki ai kamar zanyi tsalle akan kaya saboda na fishi matsuwa da mubar gidan daman,

Compound ne mai kyau upstairs kuma kowanne akwai mutane aciki ma'aikata, mu dai muna sama kuma opposite muke da wannan ɗan office din su samz mai suna Kabir kamar yadda naji yana faɗa sai dai ban taɓa ganinsa ba har zuwa lokacin da muka tare, bayan mun tare da kwana biyu sai gasu sun zo mana bayan sallar magriba, muna zaune muna kallon series a tashar zee world suka yi mana knocking, dogon hijabina na saka saboda daga ni sai riga armless iya cibiya da dan wando rigar iya cinyata shikuma boxer ne kadai a jikinsa ma ko riga babu, ciki ya shiga ya sako farar jallabiya sannan ya wuce ya bude ƙofar, ganin Kabir yasa shi fadada fara'arsa tare da mika masa hannu bayan yabawa Samha hanya alamar ta shiga ciki,

Ina zaune kan kujera na nutsu ina kallo dan bana son kallon ya wuceni naji sallamarta, fuska ta da fara'a na amsa mata duk da ban santa ba kuma banma taba ganinta ba sai yau, tasha turare babu laifi dan sai da yafara yimin sallama kafin ita tayi,

Harga Allah tun daga shigarta da yanayinya nasha jinin jikina dan tamkar yar duniya haka na ganta saboda yanzu rayuwa ta canja duk yadda mutum yake yanayinsa kadai zai fassara maka wanene shi, kuma ko ada dinma hakane,

"sannu da zuwa..." nace da ita ina karema shigarta kallo dan duk da bani nayi shigar ba amma ji nayi kunya ta rufeni,

"yawwa sannu, yakike"

"lafiya lau" nace lokacin da nake tashi na wuce kitchen, wanda shi zaka fara wucewa kafin ka shigo falo daga nan sai wani dan corridor wanda aciki bedrooms dinmu suke guda biyu daya da toilet aciki dayan kuma toilet dinshi awaje yake ta kusa dashi, duka dai komai a wadace yake dan har yafi wancan gidan da muka baro wadata a girma da komai koda yake lokacin yana shi kadai may be shiyasa ya kamashi a haka, juice na dauko mata da ruwa sai dambun naman kaza wanda dama dashi na taho tun daga Kano cikin wani madaidaicin bokiti wannan mama ce tayi min na taho dashi shikuma samz bai dameshi ba sosai yana ci amma kadan kadan nice ma dai kusan kullum sai na dan damka nasa a bakina,

Komawa nayi wurin ta muka gaisa bayan na gabatar mata da kayan motsa bakin da na kawo mata,

"sunana Samha, nice matar abokin mijinki Kabir kuma makociyarki wanda gidanmu ke opposite"

"ayya Allah sarki ashe matar Kabir ce, ina jin labarinku ai amma bamu taba haduwa ba"

"ehh nayi tunanin zanga kun shigar mana sai muka ji shiru"

"wallahi riga mu kuka yi kin san har yanzu bamu kammala gyara kayanmu bane amma Muma muna da niyyar shiga, bama gidan ki kadai ba ai duk gidajen zamu shiga Insha Allah"

Allah sarki, to ai yanzun ma ina zuba ido "

" Insha Allah zaki ganni da rana ma ni zan zo muku ko yamma ba zuwan dare ba"

"to shikenan ina nan ina zuba ido"

Mun dan sha hira sosai duk da bamu san juna ba kuma naji mutukar mamaki da naji cewa wai matar aure ce, ya ilahi wannan wanne irin zamani wai muke ciki? Nidai gaba daya ji nayi bata wani yimin ba dan kamar bata da kamun kai amma zan bata lokaci dai in karanceta dan lokaci shi ke sanar dakai wanene ainihin mutum. Munata hira har lokacin sallar ishah yayi nace mu tashi muyi salla amma bata maida hankali ba saboda kallo ya dauki hankalinta sosai sai bayan da na idar sannan itama ta samu tayi, tana idarwa kuma samz yana shigowa kiran ta inji kabir nan na tashi na rakata har waje nida shi yana rike da hannuna muka gaisa da mijin nata sannan muka yi sallama ina ce musu Insha Allah Muma zamu shigo musamman ma tunda muna kusa,

Ƙofa na jirashi ya rufe yana juyowa na dage kafata daya ina yamutsa fuska,

"what?" ya bukata yana kama hannuna,

"na taka kaya bazan iya tafiya ba ka goyeni...."

"you want to stress me dai...." ya fada tare da sunkuyawa, da tsallena na haye bayansa muka karasa ciki ina makale wuyansa da hannayena,

"baby Kin sake nauyi fa....."

"haba sweet ni din har nawa ma nake"

Dariya yayi ya kwanto dani kan cinyarsa yana cire min hijabin,

"my sweet 16 baby...."

"ai bazan fi hakan ba love"

"I know..." yace dani yana dariya sau tari haka dama yake biye min muyita shirme kamar wasu kananun yara to yau dinma hakan akayi dan har fin 11 muna ta shiririta afalo daga bisani muka yi shirin bacci nan dinma bamu hakura ba sai dariya yaketa sakani yana yimin cakulkul, alhamdulillah dai yanzu na daina wannan gane ganen da jin kukan abubuwa tun bayan da muka baro tsohon gidan da muke,cikin farin ciki da nutsuwa nayi bacci na barshi yana yimin tausa a kafafuwa na..........

*Garin dadi littafin kudi ne ga mai bukatar cigaban labarin sai ya tura 500 ta 0774712835 Aisha Ibrahim Access Bank sai a tura evidence of payment ta wannan no 07044644433 ko a tura katin waya da shaidar biya wannan no 07044644433*


*_Ummi Shatu_*👌🏻
[1/5, 12:43] Maman K: {48}

*Ina kuke manyan mata ƴan ƙwalisa ma'abota son gyara da kece raini, maza ku garzayo ku nemi maman Maryam domin samun lafiyayyu kuma haɗaɗɗun Lagos lace wanda zaku iya samun ɗinkakku da kuma sabbi a ledarsu, kaya iya zaɓinki, gefe ɗaya muna da GHT product, zaku samu,*

~MAI DA TSOHUWA YARINYA

~FEMALE CARE

~REODEO

~VIGOR MAX

~ LONGZIT

~B CLEAR

*DUK ZAKU SAMU WADANNAN KAYA CIKIN SAUKI DA RAHUSA MAZA KU NEMI MAMAN MARYAM AKAN WANNAN NO 07080222187, SIYAN NA GARI MAIDA KUƊI GIDA.....*


~~~Yau da wuri na tashi na shiga kitchen na shiryawa samz breakfast saboda shima da wuri zai fita office domin acewarsa akwai baƙi da zasu zo musu saboda wani gagarumin aiki da zasuyi,

Duk da yana sauri dankali na soya masa sannan nayi masa sos din kwai na haɗa masa tea na kai masa lokacin har ya fito daga wanka yana shiryawa, kayan breakfast din na ajiye sannan na karasa na taimaka masa ya gama shiryawa na dauki turare na fesa masa ina kallonsa cikin yaba shigarsa ta yau domin suit ya saka blue black amma rigar ta ciki fara ce sai necktie da ya saka,

"kayi kyau sosai sweet.... Kamar in hanaka fita" na karasa maganar cikin shagwaba,

"tnx darling but kar ki hanani fita i beg...."

"to zauna kayi breakfast sai ka tafi...."

"duk yadda kika ce haka za ayi my love"

Sosai yaci abincin kafin yayi min sallama ya tafi wanda sai da na raka shi har ƙofa sannan na dawo na kwanta bayan na rufe ko ina saboda bacci nake son in koma in dan yi,

Ban fi 20 minutes da kwanciya ba naji knocking, jin knocking din ba mai karewa bane ya sani tashi ina mamakin waye kuma yanzu? To ko shine yayi mantuwa ya dawo? Da waɗannan tunane tunanen dai na karasa, ina budewa naga Samha matar Kabir, murmushi nayi nace,

"Hajiya Samha kece, sannu da zuwa"

"yawwa sannu, ga baƙuwar sassafe" ta faɗa tana kokarin shigowa nan na bata hanya ta shiga nabi bayanta, daga ita sai rigar bacci sai hijabi, hira muka dan fara yi tun 9 da tazo har kusan azahar nan kuma naji abin yafara damuna domin inada aikace aikace na da nake son inyi, ina son in gyara gidana in wankewa mijina inner wears dinsa da kayan baccinsa kuma ina son in danyi bacci kafin ya dawo ko dan in bashi lakacina sosai amma taki fahimtar hakan bare ta tafi nikuma bana son in fito in fada mata ko in shiga ciki in barta taga kamar kora da hali nake yi mata amma duk mace mai hankali tunda kika zo tun safe anan kika karya ai ya dace ki tafi gidan ki kuma tun ana marmarinki ba afito ance ki tafi ba,

"Hajiya Samha naga azahar ta kusa bari na tashi akwai yan ayyukana suna nan jingim banyi ba suna jirana...."

"har wani aiki gareki widat? Aikin nawa yake? Ni kin ganni nan wallahi tunda na tashi ko tsinke ban dauke ba daga gidana na fito, ke ko gadon da muka kwana ma haka na fito na barshi kuma bana jin zan iya gyarawa"

"to ai ke amarya ce, har yanzu kina cikin dokin amarci nikuwa fa?"


"a'a wallahi kawai dai abinda na lura dashi shi namiji zuma ne sai da wuta dan daga lokacin da ka nuna masa kai wahalalle ne tofa a wahala zaka kare amma idan ka nuna masa kai ma dan hau ne sai kiga kun daidaita..... Wasu matan fa dan wahala har wanki suke yiwa miji wai, ni hauka nake zan yiwa namiji wanki, wallahi sai dai kar yasaka kayan "

Tunda naji irin kalamanta sai na sha jinin jikina bance komai ba sai murmushi da nayi nan taci gaba da mitarta akan wai ita ba zata zauna ta bautawa namiji ba bata son wahala bla blah blah daga karshe dai ta tashi ta fita kuma shi dinma da tayi min sallmar ba gidanta ta shigaba ina hangota ta window din bedroom dinmu lokacin da na shiga ina tattara kayan da zan wanke, can kasa ta sauka ta shiga wani apartment din, nidai ko kadan kalamanta basuyi tasiri a gareni ba domin kowa da irin fahimtar sa da kuma tarbiyarsa har gobe mazan gidanmu sune suke kaiwa Abbanmu wanki su biya kuma before su fara aiki su yi aure sune suke yi masa wanki tas yayin da sukuma su Annie sune suke wanke masa kananan kaya kuma har gobe basu daina ba shiyasa ni a ganina wannan ba wai wahala bace kyautatawa ce, nima kuma tunda nayi aure nake wannan hidimar amma dukka kayana samz ke hadawa da nashi ya bayar wanki,

Ina kokarin shiga bathroom inyi wankin naji yana kirana a waya nan yake sanar dani sun gama meeting din may be ma yau da wuri zai dawo gida, sallama muka yi na shiga nayi aikina na gama na wanke toilet din nazo na gyara gidan sannan nayi wanka na dora girki,zuwa ƙarfe uku na fita na ɗan shiga maƙota kamar yadda naga dacewar hakan kowanne gida na shiga kuma dukkansu ba wasu manya bane wasu zasuyi sa'anni na wasu kuma koda zasu girmeni to da kadan ne dan dukkansu babu wadda tayi haihuwa uku daga biyu sai mai ɗaya, mace daya ce na ganta da dan girmanta dan yaran ta ma sun kai biyar kuma duk ciki tafi nutsuwa ko dan dama bama za a hada hankalinta da na sauran ba tunda tafisu shekaru kuma a gidanta ma na dan fi jimawa saboda tana ta bani shawarwarin in iya takuna kuma in iya bakina a compound dinnan domin akwai matsala, idan har baka iya bakinka ba yanzu zaka ji sirrin ka da duk wani abu da ya shafeka awaje haka kuma inyi takatsantsan, to ni dai ta barni a duhu dan bata fito fili ta fayyace min meyake faruwa acikin compound dinba amma duk da haka na dan fahimci wani abu kadan, sallama nayi mata na tafi inata mamaki da tunani kala kala saboda tace min duk ciki itace ta fara zuwa kowa anan yazo ya sameta ita asali daga jihar Borno suka dawo ita da mai gidanta wanda ya samu canjin aiki ana kiran ta da Hajja Gana,amma wannan hannunka mai sandar da tayi min yasa naji bana sha'awar yin mu'amala da kowa a cikin compound din sai dai kawai hakkin musulunci amma bazan shiga jikin kowa ba kuma bazan bari kowa ya shiga jikina ba zan zauna da kowa nesa nesa dan naga kamar dukkansu kansu yana rawa ciki harda Samha. Ina komawa sallar la' asar nayi na sake gyare jikina na sauya shigata daga wacce naje da ita unguwa nasake wata sabuwa inda na saka wata fitinanniyar riga three quarter purple color mai ƙaramin hannu, wuyan rigar a bude yake gaba ɗaya shiyasa kusan rabin ƙirjina awaje yake, sarka da dan kunne na saka masu jan hankali domin sarkar ta shige har tsakiyar ƙirjina da yake doguwa ce haka dan kunnayen sun sauko har kan kafaduna suma, turarena wanda nake amfani dashi musamman idan ina gida shi nabi na shasshafa har cikin cibiyata da bayan kunnena da sauransu fuska ta ban yi mata wani havy makeup ba light nayi yanda zan fi daukar hankalinsa, ƙarfe shida daidai ya dawo, ina falo ina kallo dama aikin kenan kallon series sai ko karatun novel, kiransa da ya shigo cikin wayata shine ya katse min kallon da nake yi na dauka ina yanga tamkar yana kallona,

"Sweet ya....?"

"Baby am back....."

"Awwwwn.... Am coming dear"

Da gudu naje na buɗe ƙofar ina budewa na koma ciki na labe yana shigowa bayan ya rufe ƙofar na ɗale shi duk kuwa da cewa yana riƙe da jakar computer ɗin shi da baƙar leda wadda ban san me ya siyo mana ba aciki,

"Baby....." na ji ya kirani cikin shagwaba alamar a gajiye yake, kayan na karba muka karasa ciki yana ta aikin kallona kamar yau yafara ganina, ai muna zuwa ya janyoni jikinsa ya soma sinsinata yana wasa da sarkar da nasa,

"wow... baby kinyi kyau, come closer please....."

"nayi kyau a hakan?" na bukata cikin shagwaba,


"yes nah..." ya bani amsa yana murmushi, yana ta santin kwalliyata na samu na rage masa kayan jikinsa na cire masa socks da rigar jikinsa daidai lokacin kuma kiran mahaifiyarsa ya shigo ya ɗauka ina jin alamun itace na kwashi kayan na basu wuri na wuce bedroom na kai sannan nazo na wuce kitchen naje na kwaso warmers ɗin abinci na kawo, ledar da ya shigo

Please Login or Register in order to submit comment