Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

[8/30, 9:32 AM] Mhizz Jiddherr❤️: *Z E E Y A D*
```(The Abandoned Prince)```





*NA*
*JIDDAH BINT MUHAMMAD*






*MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION*





*Note:*
_Banyi alƙawarin Posting kullum ba😁, sannan kuma labari na ƙagagge, ne banyi shi dan cin zarafin wani koh wata ba, kowa dai yasan da cewa ɗan Adam ajizi ne, dan haka duk wani kuskure da aka samu cikin labarin nan toh a bisa rashin sani ne, ba zan kar6i cin mutunci koh wasu ƙananun maganganu ba, MHIZZ JIDDHERR batada abokin faɗa, kowa nawa ne, dan haka idan kin zage ni koh a 6oye ne na yafe miki😁_




_Bismillahi_Rahmanin_Rahim_




_*YAA WAHHABU,KAMAR YADDA NA FARA WANNAN LITTAFI LAFIYA,KASA NAGA ƘARSHEN SA LAFIYA BA TARE DA AN SAMU WATA MATSALA BA,Aameen Yaa Hayyu Yaa Qayyum🤲🏽*_





*001...*




*Cairo [Egypt]*




..............."My life my rules, nobody has the audacity to interfere in my life, and nobody has the gut to decide what is good or better for me...this is my life so let me live it the way i want it, Your highness ni ba yaro bane why then duk abinda zanyi sai wani ne zai yanke hukuncin hakan,why ba za'a barni nayi rayuwa ta cike da ƴanci ba kamar yadda akasan kowane cikakken ɗan sarki mai ragamar mulki a ƙasa ba?, am tired, am fed up with all this shit, so let me be, i need freedom...so freed me from all this...Please" ya ƙarashe cikin cize haƙora yana kallon farin dattijon dake kishingiɗe kan kujerar alfarma inda fuskar sa ke fitar da tsantsar 6acin rai.



A fusace ya juya ya fara tafiya, daidai isowar sa bakin ƙofa ya tsinkayo muryar dattijon nan.


"ZEEYAD!" ya ƙira shi cikin kakkausar murya.



Runtse idanu yayi yana dakatawa ba tare da ya juyo ba.


Miƙewa dattijon nan yayi daga kan Kujerar sa yayin da fadawan da suka zagaye shi suka shiga gyara masa doguwar alkyabar dake jikin sa.


"How dare you hun?, babu wani mahaluƙi da ya ta6a karya koh ƙetare dokar da na gindaya a wannan masarautar, yau kai ɗan da na haifa baka isa ka karya min doka kuma na kyaleka ba, dan kana gudan jini na ba hakan na nufin zakayi dukkanin abinda kaga dama kuma na barka ba, dole ne kabi doka kamar yadda kowane mahaluƙi keyi a masarautar nan, idan kuwa ba haka ba lallai zaka fuskanci hukunci mai tsanani."



A fusace ya juyo yana fuskantar Uban nasa yace "I know it,I know you will never change,your mind has already been poisoned, but sooner or later zaka gane cewa what you're doing is totally wrong Father, am your Son your own flesh and blood, but you never gave me a Fathers love..."


"ZEEYAD!, Enough of this Nonsense...."


"You better keep your mouth shut,save your words it maybe useful for you next time, this is between me and my Father, so you better not interfere in it, understand?" ya faɗa cikin katse ta yana aika mata da mugun kallo.


"ZEEYAD!" ya Faɗa yana mai wanke sa da wani irin zazzafan mari.


"Ashe bakada kunƴa har haka bansaniba?, a matsayin uwa take a wurin ka."


"Ba uwata bace, Mahaifiya ta ta daɗe da mutuwa kowa yasan da hakan,wannan matar ba mahaifiya ta bace, this selfish and disgusting woman here is nothing but a mess to our Family" ya faɗa yana nuna ta da yatsa,inda kuma idanun sa suke daɗa canza launi zuwa jaa.



"ZEEYAD!" ya faɗa a zafafe yana sake ɗaukesa da wani marin.


Hannun mahaifin nasa ya ruƙo kafin ya shiga dukan kansa dashi yana faɗin "Beat me, beat me as hard as you can, you enjoyed it right, you enjoyed beating your Only lovely son don't you, ka tsane ni koh, then why don't you just kill me Dad?."



Sosai ran Mahaifin nasa yayi mugun 6aci,wanda kallo ɗaya zakayi masa ka firgice tsabar zallar kwarjini dama kuma jinin sarautar dake yawo a jijiyoyin jikin sa.



Wani marin ya sake ɗauke ɗan nasa dashi kafin yace "Kuje ku ɗauke sa,sannan ku tabbatar da kunyi masa hukunci mai tsanani wanda koh da kuɗi aka basa nangaba ba zai sake sha'awar aikata abinda yayi ba yanzun" ya ƙarashe faɗa yana kauda kansa daga kallon da ɗan nasa keyi masa.


Da umarnin Sarki suka ƙaraso wurin tare da kamasa sukayi waje dashi,ba tare da yayi gardama ba yabi su,kasancewar hakan ya rigada ya zame masa jiki.


Kallon Juna itada ɗan saurayin dake kusada ita sukayi kafin duk su saki wani irin murmushi mai cikeda zallar ma'anoni iri-iri.



Wani irin ɗaki da ya kasance kamar Kurkutu aka jefa sa kafin a garƙame kwaɗo a ƙofar sukayi gaba suka barsa.


Bakin ƙofar ya matso yana kama ƙarafunan ƙofar, kallo ɗaya zakayi masa ka fahimci irin tsantsar 6acin ran dayake ciki.



Kansa ya ɗaga sama yana kallon yadda hadari ya haɗu wanda ƙiris take ruwa ya sauƙo.


Sam bai damu ba,sai ma samun ƴar ƙarfen gadon dake ajiye a ɗakin da yayi ya kwanta fuskar sa na fuskantar sama.



Sama da shekaru goma na cikin rayuwar sa yana tafiyar da ita ne cike da ƙunci da wahala tun bayan mutuwar mahaifiyar sa,inda ya kasance bashida kowa face mahaifin nasa wanda yake tunanin zai zame masa gatan sa,sai dai kash! akasin hakan ta kasance wanda tun bayan mutuwar mahaifiyar tasa ya rasa gane kan mahaifin nasa kwata-kwata,balle ma dayake ƙarƙashin kishiyoyin uwa har uku wanda tunda ya taso bai ta6a samun wata kulawa ta musamman daga gare su ba sa6anin ƴaƴan cikin su da suka haifa.



ZEEYAD,matashin yaro mai kwazo da kaifin basira,Dukda mulki da ƙarfin iko irinta mahaifin sa hakan bai sanƴa shi fita daga cikin ƙangin rayuwa mai cike da ƙunci da rashin ƴanci ba.



A kaf cikin yara Shida da mahaifin sa ya mallaka babu marar gata kamar sa,Makaranta mai tsada,Tsadaddun sutura irinta ƴaƴan manƴan sarakuna,tsantsar ƙauna daga wurin mahaifa,rayuwa mai cike da jindaɗi da ababen more rayuwa iri daban-daban kowane yaro dama kuma ƴaƴan ruƙon gidan sun mallake sa sa6anin shi da koh almajirin cikin gida ya fisa gata.



ZEEYAD yaro ne mai ƙoƙari sosai dukda kasancewar yana cikin ɗaya daga cikin makarantu masu sauƙin kuɗi a ƙasar hakan bai sanƴa guiwar sa ta sace ya kasa yin abinda zai fice shi a rayuwa ba.



Dukda cewa dukkanin yaran gidan ba a ƙasar suke karatu ba hakan bai sanƴa shi jin baƙin cikin da zai hana sa cigaba ba,burin sa shine ya samu ya jona makarantar gaba tunda ya kammala karatun secondary ɗinsa,ya jona Jami'a kasancewar sa na son zama hamshaƙin ɗan kasuwar da duniya keji dasu.



ZEEYAD yaro ne mai tarin baiwa,6oyayyiyar baiwar da babu wani mahaluƙi da yasan sa dashi.



Dukda kasancewar sa ɗa namiji babba a wurin mahaifin nasa hakan bai hana sa nuna masa *TSANTSAR ƘIYAYYA* da warayya a tsakanin sauran ƴaƴan nasa ba.



Koh dan ya kasance mai rauni ne a cikin su wanda ba komai bane ya dame sa,bai kuma damu da shiga harkar da bata shafe sa ba yasa hakan ke faruwa dashi kokuwa tsantsar son zuciya ce kawai dama kuma makirci irin ta kishiyoyin mahaifiyar sa yasa hakan ke faruwa dashi.



Ya taso ne a rayuwa ba tare da yasan mecece soyayya ba sai akasin ta wato tsantsar ƙiyayya.



Tun bayan mutuwar mahaifiyar sa bai sake dariyar farin ciki ba,yau shekaru goma kenan,laifi kaɗan ne zaiyiwa mahaifin sa ya sanƴa a hukunta shi,hukunci mai tsanani,wanda koh a cikin bayi sai wanda ya aikata babban laifi akeyiwa hakan.



Dayawa daga cikin bayi sun fisa gata,wanda hakan yawancin su ke ɗaukar alhaƙin hakan wurin yi masa dukkanin abinda suka so domin kuwa dasu dashi ɗin babu wani bambamci tsakanin su,kamar yadda suke faɗa.



A yau yanada shekaru Ashirin a duniya sai dai koh da da wasa bai baryin addu'a wurin neman taimako daga wurin wanda ya dace kuma maji roƙon bayin sa ba.



Da akwai lokacin da ya gindaya wa kansa na zama cikin wannan ƙunci da wahalar da zaran lokacin nan ta cika kuwa,tabbas ba zai saurarawa koma waye ba,kama daga kan Mahaifin nasa dama kowa dake cikin Masarautar nan,amma kafin burin sa ya cika dole ne ya samu damar tseratar da rayuwar sa daga wannan kangin wuyar da yake ciki,ta haka ne kaɗai burin sa dama kuma mafarkin sa zai zamto gaskiya,da zaran kuma hakan ta faruwa toh tabbas kowa zaiji *A JIKIN SA..............*






*Share Fisabillah👏🏽*





*MHIZZ JIDDHERR........✍🏽*
[8/30, 9:32 AM] Mhizz Jiddherr❤️: *Z E E Y A D*
```(The Abandoned Prince)```




*NA*
*JIDDAH BINT MUHAMMAD*




*MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION*





*Note:*
_Banyi alƙawarin Posting kullum ba😁, sannan kuma labari na ƙagagge, ne banyi shi dan cin zarafin wani koh wata ba, kowa dai yasan da cewa ɗan Adam ajizi ne, dan haka duk wani kuskure da aka samu cikin labarin nan toh a bisa rashin sani ne, ba zan kar6i cin mutunci koh wasu ƙananun maganganu ba, MHIZZ JIDDHERR batada abokin faɗa, kowa nawa ne, dan haka idan kin zage ni koh a 6oye ne na yafe miki😁_




_Bismillahi_Rahmanin_Rahim_





_*YAA WAHHABU,KAMAR YADDA NA FARA WANNAN LITTAFI LAFIYA,KASA NAGA ƘARSHEN SA LAFIYA BA TARE DA AN SAMU WATA MATSALA BA,Aameen Yaa Hayyu Yaa Qayyum🤲🏽*_





*002...*




................A firgice ya tashi sakamakon sauƙar ruwan sanƴin da yaji an kwara masa a jiki.



"Kai ƙasƙantacce marar galihu, gari ya rigada ya waye gara ka fito ka kama ayyukan da kasan kana yi tun kafin ran sarki ya sake 6aci ya sanƴa ayi maka horor da tafi wannan" cewar bawan dake gadin gidan kurkukun.



Wiping fuskar sa yayi da hannun sa yana aikawa wannan bawa wani irin kallo da shi kaɗai yasan ma'anar sa.



"Ba zaka tashi bane ka tsare ni da wadannan firgitattun idanun naka yawa na Aljanu, ka sani sa'a ɗaya kaci na matsayin ka ɗan sarki da babu abinda zai sanƴa na hukunta ka da wannan kallon da kakeyi min."



Dariya sauran masu gadin suka sanƴa kafin ɗaya daga ciki yace "Toh ai koh ka hukunta shi ba laifi bane, ubansa ma yakeyi masa wannan horor balle kuma kai da kake matsayin mai kula da dukkanin abinda yakeyi, ai daɗin yin maganin sa kenan dan kuwa koh ya kai ƙara babu wani matakin da za'a ɗauka."



Dariya suka sake sanƴawa kafin na farkon yace "Ai kawai ina raga masa ne, amma lokaci na zuwa da nima zan aiwatar da nawa hukuncin akansa hahaha."



Sunkuyar da kai yayi yana jinsu, kafin kuma daga bisani ya buɗe masa ƙofar ya fito bayan sun gama ci masa mutunci.



Ƙafa ya sanƴa masa take yaci tuntu6e ya faɗi, nan take suka sake sanƴa wata dariyar kuma.



"Lalatacce kawai, tashi" ya faɗa yana bugun sa da ƙafar sa.



Miƙewa yayi ya karkaɗe jikin sa kafin ya nufi tsakiyar Ƙaton gidan yarin inda wata ƙatuwar rijiya take.



Ruwa ya fara janƴowa kafin ya kwara a jikin sa yana sauƙe nannauyar ajiyar zuciya, dan kuwa sosai zuciyar sa ke tafarfasa.



ƙara janƴo wani ruwan yayi kafin ya shiga gabatar da alwala, ganin haka yasa wannan arrogant mutumin nan ƙarasowa wurin sa.



Ball yayi da gugar kafin ya finciko shi ya tsayar dashi yana faɗin "Naga rashin kunƴar ka ƙara gaba take, aiki ne birjik a gaban ka,amma kazo nan kana wani shashancin kuma daban."



Kallon sa yayi da gajiyayyun idanun sa kafin kuma ya furzar da hannun sa daga riƙon da yayi masa yace "Sallah zanyi, ba zan iya ta6uka komai ba ba tare da nayi sallah ba, ba shashanci bane,haske ne babba a cikin rayuwa ta."


Sunkuyawa yayi ya ɗauko gugar ya shiga jan wani ruwan,shaƙo wuyar sa yayi ta baya kafin ya kifar da kansa zuwa saitin rijiyar kamar wanda zai jefa shi ciki yace "Kai ƙasƙantacce baka isa ina baka umarni kuma kaƙi bi ba, lallai naga kana wasa da rayuwar ka,babu abinda zai hana ni jefa ka cikin rijiyar nan muddin ka sake yunƙurin yin jayayya dani."


"Mai ke faruwa ne anan?" Suka tsinkayo wani murya ya faɗi hakan.


Da sauri ya sauƙo da ZEEYAD ɗin yana ture sa gefe kafin ya juyo zuwa ga wanda yayi maganar,inda yayi saurin rissinawa yana faɗin "Yallabai nayi dashi akan yaje ya gabatar da aikin da sarki ya sanƴa sa amma kuma yanayi min gardama."


Ƙarasowa wannan mutumin yayi wanda ke sanƴe da kayan fatar damusa kamar yadda sauran dakarun wurin ke dashi duka,sai dai nasa ya ɗan bambamta da nasu.



Kallon ZEEYAD dake ta faman huci yayi yace "Ku kyale shi yayi abinda yaga dama, zaku iya komawa bakin aikin ku."


"Amma Yallabai..."


"Banason jin wata magana" ya faɗa cikin katse shi.


Wani irin mugun kallo ya watsawa ZEEYAD kafin yace dashi "Ka kammala duk abinda zakayi kazo ka same ni."


Juyawa ZEEYAD ɗin yayi da niyar barin wurin kafin ya tsinkayo muryar mutumin nan na faɗin "Yarima ZEEYAD kada ka kula abinda Mulah yake faɗa maka a kullum..."


"Babu ruwanka dani, ka tsaya a matsayin ka na sarkin Dakaru, furucin ka babu abinda zai ƙaramin sai ƙunar zuciya da 6acin rai" yana faɗin haka ya bar shi nan tsaye a wurin.



Da kallo sarkin Dakaru ya bishi dashi kafin ya saki murmushi ya juya ya bar wurin.



Hanƴar Babbar Masarautar ya nufa, sosai yake a galabaice ga kuma ƴunwa da take nuƙurƙusar sa,a haka ya daure ya ƙarasa bakin ƙofar shiga farfajiyar masarautar.



Wucewa yayi niyar yi sai dai yaga masu tsaron wurin sun sanƴa dogin takoban su masu bakin kibiya sun toshe hanƴar shigan.



Ɗagowa yayi ya kallesu yace "Mai hakan ke nufi?."


"Mai kake buƙatar ji kuwa?, saƙo bai zo mana cewa ka aiwatar da umarnin sarki ba, ba kai babu shiga ciki muddin baka kammala aikin da aka sanƴa ka ba" cewar ɗaya daga cikin dakarun.



"Babu inda zanje sannan ba zanyi wani aiki ba muddin ba'a barni na shiga ciki ba, wannan gidan namu ne ba na kowa ba a cikin ku, dan haka bakuda damar hana ni shiga."



Dariya sukayi kafin ɗaya yace "Gidan ku ne, amma kuma ai ba'a girmama ka kamar ɗan gidan."


"Wannan ba damuwar ku bace, ku buɗamin yanzun nan" ya faɗa a tsawace.


Ƙin kulasa sukayi hakan yasa shi bangaje su ya tsallaka ya wuce.


"Ka dakata anan Yarima ZEEYAD kokuma na harbe ka" faɗin ɗaya daga cikin su yana saita masa kibiyar kwari da baka.



Tsayawa yayi yana lumshe gajiyayyun idanun sa tare da cize haƙora ya juyo yana kallon su, dawowa yayi ya wuce su ba tare da yabi ta kansu ba ya bar wurin.



Da Kallo suka bisa kafin ɗaya yace "Haƙiƙa yana bani tausayi."


Kallon sa ɗayan yayi yace "Rayuwar sa abar tausayi ce,sai dai fah ka kiyaye yin magana akan tausayin da kake yi masa a koh ina,dan kuwa wannan Masarautar cike take da munafukai" yana faɗin haka ya tsuke bakin sa tare da yin shiru,hakan yasa shima na farkon yin shiru suna kallo ZEEYAD ɗin har ya 6acewa ganin su...........



__________________




"ZEEYAD,ZEEYAD ka tsaya mana" ya faɗa yana shan gaban sa.



"ZEEYAD maiyasa kake haka?, kazo muje gidan mu kayi wanka kaci abinci mana idan yaso sai ka wuce wurin aikin naka."



Kallon ɗan saurayin dake tsaye gaban sa wanda ba zai wuce sa'an sa ba yayi yace "Nagode Sadeeq da wurin sallahr da ka bani,amma ba zan iya zuwa gidan ku ba gudun kada na sanƴa ku cikin matsala."



"Wane irin matsala kuma ZEEYAD, ka manta abinda Baba yace ne?, duk ranar da aka kore ka daga gidan ku zaka iya zuwa gidan mu ka huta kayi duk abinda kake so, ZEEYAD ni fah abokin ka ne dan Allah kazo muje mana."



"Sadeeq da akwai idon mutane a kaina, muddin na bika gidan ku har na aiwatar da wani abin toh fah ka sani sarki ba zai ta6a kyale Mahaifin ka ba, ka rabu dani Sadeeq banason wani abu ya same ku sabida ni."



"Dan Allah ZEEYAD."



"Just leave me alone, please!" ya faɗa a tsawace yana yarfar da hannun Sadeeq ɗin daga jikin shi kafin ya wuce a fusace zuwa inda zasa.



Saurin mara masa baya Sadeeq yayi yana faɗin "Ba zan jure ganin ka cikin wannan halin ba ZEEYAD muje ni zan tayaka da aikin koma menene."



Babu wanda ya kula ɗan uwansa haka suka ƙaraso filin da aka ke6anta kawai dan horar da bayi.



"Sabida kai ka kawo taurin kai duniya sai yanzu kake zuwa?" cewar Mulah yana aika masa da kallo mai cike da tsantsar mugunta.



"Kai kuma fah daga ina?" ya faɗa yana kallon Sadeeq.



"Ni...na...nazo ne taya shi yin aikin."


"Iyeh, wato kai har lalacin naka ta kai haka,sai ka kawo mai taimaka maka?."



"A'a wallahi ba shi ne ya gayyato ni ba nine na kawo kaina" cewar Sadeeq ɗin.


"Kai yimin shiru munafuki kawai" ya faɗa yana ture shi.


"Sadeeq" cewar ZEEYAD ɗin yana ɗago sa tsaye.


"Duk abinda zakayi kayi shi a kaina Mulah,ba sai ka ta6a wani koh kaji wa wani rauni a kaina ba" ya faɗa yana kallon Mulah ɗin.



"Au haba, bari mu gani koh zaka iyayin aikin kai kaɗai kokuma murɗaɗɗen jikin duk na banza ne babu ƙarfin, kai kuma maza ka 6ace daga nan wurin yanzun nan idan ba so kake nayi maka 6alli-6alli a maƙogoro ba" ya faɗa yana ciro wata ƴar ƙaramar wuƙa daga bakin takalmin sa.



Juyawa ZEEYAD yayi zuwa ga Sadeeq yace "Sadeeq ka bar nan wurin yanzun nan."



Girgiza kai Sadeeq yayi yace "Zan tafi amma ka sani ina nan ina jiran ka a mahaɗar mu, dan Allah kayi a hankali."



Kai ya jinjina masa kafin Sadeeq ɗin ya juya ya bar wurin, cakumo rigar sa ta baya Mulah yayi har zuwa cikin inda jibgin ayyukan suke yace "Buɗe idanun ka ka gani da kyau ya kai ƙasƙantaccen Yarima, wadannan ayyukan duk gabaɗaya kai zakayi su, sannan awa uku kawai aka baka, ka sani ka rigada ka cinƴe awa ɗaya a yawace-yawacen banzan da ka gama yi, yanzu awa biyu ya rage maka kayi clearing nan wurin baki ɗaya."



Tunda Mulah ya fara magana ZEEYAD ke kallon uban Karar ƙaiƙayin dake jibge a wuri ɗaya, ga kuma manƴa-manƴan ƙayoyin masu kama da kibiya a jikin su, uwa uba kuma da hannun sa zai yaye su baki ɗaya ya kai chan ƙololuwa ya zubar.



"Wannan aikin ba na hannu bane, ina shovel da wheelbarrow?."


"A gidan uwarka, kaje ka tashi uwarka dake kwance cikin kabari tazo ta baka."



Iya ƙololuwa ran ZEEYAD yayi mummunar 6aci wanda bai san sadda yayi kukan kura ya kaiwa Mulah uban naushi a baki ba, take ya zube ƙasa inda kuma baiyi ƙasa a guiwa ba ya haye kansa ya cigaba da basa wasu irin azabbabun naushi a fuska, kai kace ba ƙarfin sa bane yake aikata wannan aika-aikar.



"How dare you?, she is my mother, she is a queen, the greatest queen among all, ba zan ta6a kyale duk wanda yace zai zage ta ba, zan iya yafe komai amma ba zan ta6a yafewa wanda yaso cin mutuncin mahaifiya ta ba,babu abinda tayi maka, dukkanin ku kun kasance butulallu ne,babu irin kyautatawar da mahaifiya ta batayi muku ba sadda take raye,why then zaka zage ta bayan mutuwar ta?, ba zan ta6a kyaleka ba yau ɗinnan, sai na kashe ka, sai na kashe ka Mulahhh" yana faɗin hakan ne cikin azababbiyar 6acin rai yayin da hannun sa bai gushe daga kaiwa Mulah duka ba, yayin da ake ta kiciniyar ɗaga sa amma an kasa yin hakan.



Babu wanda yayi nasarar ɗaga ZEEYAD daga kan Mulah har sai da ya tabbatar da Mulah baya motsi tukun kafin ya barshi yana sauƙe wata iriyar azababbiyar huci, yayin da fuskar Mulah ba'a cewa komai wurin muni dama chan ba kyan gani ne dashi ba, balle yanzu da yasha uban bugu.



Hayaniya ce ta ƙecere a wurin inda kowa ke mamakin yadda akayi kamar ZEEYAD ya kai Mulah ƙasa yake bugu harda sumar dashi.



Hannayen sa ya shiga dubawa kafin ya kalli fuskar Mulah ganin abinda ya aikata ne yasa shi saurin sauƙa daga kansa, kafin kuma yayi hanƴar fita daga wurin cikin gudu.



Wurin haɗuwar su da Sadeeq yaje inda ya same sa zaune gindin wata ƙatuwar bishiya yana zaman jiran sa.



Hango sa da Sadeeq yayi ne yasa shi saurin miƙewa yana taro sa da faɗin "Har ka gama?, i know you can do it abinda yafi aikin nan ma zaka iya" ya faɗa cikin murmushi yana bubbuga kafaɗar shi.



"Zeeyaaaddd" sukaji an ƙira da ƙarfi, juyawar da sukayi suka hango tawagar abokan Mulah ne ke tunkaro su, ba tare da ya tsaya yin wata-wata ba yace da Sadeeq "Run" ya faɗa yana fita da gudu ganin haka yasa Sadeeq da bai fahimci komai ba mara masa baya shi ma cikin gudu...........





*Share Fisabillah*




*MHIZZ JIDDHERR.........✍🏽*
[8/30, 9:32 AM] Mhizz Jiddherr❤️: *Z E E YA D*
```(The Abandoned Prince)```


*NA*
*JIDDAH BINT MUHAMMAD*





*MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION*






*004...*





_Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah._





.............Kujera aka ja masa ya zauna kafin ya shiga ƙare musu kallo ɗaya bayan ɗaya.


Idanun sa ne suka sauƙa kan ZEEYAD da kansa ke sunkuye

Please Login or Register in order to submit comment