Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

 ©️ HASKE WRITERS ASSOCIATION
_(Home of expert & perfect writers)_


*GARIN DAƊI.........!*
(Based on a true life story)




*_NA_*

_*UMMI A'ISHA*_


*Wattpad:ummishatu*



بسم الله الرحمن الرحيم، رب اشرح لي صدري ويسر لي أمري، لا إله إلا الله وحده لا شريك له، اشهد ان لا اله الا الله محمد رسول الله.



_Gaisuwa mai tarin yawa gareku masoya masu karanta littattafan na,labarin garin daɗi labari ne da ya faru a gaske wanda tun lokacin da naji labarin ya tsaya min rai, ya zauna cikin zuciya ta daga ƙarshe naga ya dace in raba wannan labari ga masoya na suma su ji abinda naji duk da na fara sabon littafina a wattpad mai suna baƙo ayi min afuwa na ajiye rubuta baƙo har sai na kammala wannan da yardar Allah, asha karatu lafiya._



1


~~~Alhaji Mukhtar Garzali shine cikakken sunan mahaifinmu, mahaifinmu alƙali ne kuma mai shari'a a wata babbar kotu dake cikin garin Kanon dabo tarin Allah, mu bakwai mahaifinmu ya haifa hudu mata uku maza, yaya Abdallah shine babba sai mai bimasa yaya Abdurrahman, daga nan sai Anty khadija sai yaya Abdul hakim dake bi mata, sai Anty Salaha daga nan sai ni Maimunatu wadda ake kira da (widat) sai ƴar autar mu Bishra. Mahaifinmu sanannen mutum ne kuma ana ganin girman sa da mutuncinsa a ko ina, matansa na aure guda biyu hajiya Aisha (mama) da hajiya Fatima wadda muke kira da Annie, dukkaninsu haifaffun cikin garin Kano ne, shi Abba ɗan asalin garin takai ne wanda aikine ya kai kakansa wato mahaifin babansa zama kasancewarsa alƙali, itama mama ƴar asalin garin takai ce Annie ce kaɗai haifaffiyar garin wudil. Hajiya Aisha itace uwar gida kuma duk hannunta muka taso kasancewar Allah bai bata haihuwa ba, zaman lafiyar da suke yi yasa baƙo baya iya gane ko ƴayan waye mu, duka mazan gidanmu lauyoyi ne domin gaba ɗaya ra'ayinsu kenan na son gadar babanmu, haka a mata ma babbar yayar mu anty khadija lawyer ce, anty salaha ce kaɗai ma'aikaciyar jinya sai bishra dake da irin nata ra'ayin na karantar fannin lafiya domin a yanzu haka tana can makarantar koyon ungozoma da aikin jinya dake garin azare. Nikam dama tun ina ƴar ƙarama nake da sha'awar kutse cikin na'ura mai ƙwaƙwalwa wato (computer) a turance, tun ban iyaba nake shiga ɗakin mazan gidanmu duk wadda naga yayi wasarere da tasa ko ya saka a charge haka zan buɗe inyita yi masa bincike a ciki, duka kam na shashi babu iyaka banda punishment kala kala da suke sakani musamman yaya Abdurrahman da yaƙi jinin ya ajiye abunsa yazo ya iskeshi ba daidai ba ancanja masa matsugunni ko an taɓa masa, duk da irin duka da punishment ɗin da ake sakani hakan bai hanani cigaba da tattaɓa musu laptop ɗinsu ba har saida ta kai ta kawo sun daina ajiyewa acikin ɗakinsu kowa ya canja maɓoya, cikin haka kwatsam sai muka yi baƙo yaron aminin abbanmu wanda yasamu gurbin karatu a jami'ar bayero dake cikin garin kano, sunansa faisal kuma shima harda laptop ɗinshi yazo nan fa na samu aikin yi dan hatta makarantar islamiyya sai su Annie sunyi dagaske nake tafiya lokacin ina aji biyar a makarantar secondary ta jeka ka dawo, shi yaya faisal baida matsala koda yaushe barmin laptop ɗinshi yake yi inyita bincike na da games har sai idan abu mai muhimmanci zai yi sannan zai karɓa shi ɗinma yana gamawa zai dawo min da ita shiyasa laptop ɗin ta zama kamar wata tawa, cikin ƙirƙire ƙirƙire na wata rana na ƙirƙiri wata manhaja ta makarantar mu wadda kowanne ɗalibi za asaka bayanansa da suka shafe shi kama tun daga sunansa, jinsi, aji, report sheet da sauransu harda tambarin makarantar mu a tsakiya, wannan abu da nayi shi ya sake fito da baiwata a fili dan har gobe da wannan tsarin makarantar mu suke amfani dashi kuma lokacin har karramani aka yi domin na faɗawa principal cewa saboda asamu sauƙin fitar da sakamakon jarrabawa na ƙirƙiri application ɗin duba da yadda naga malaman mu na shan wahala wurin marking da harhaɗa marks har su fitar da position sannan ga yawan kuskure da ake samu duk da muna taya su da recording amma daga ƙarshe sai kaga anyi ba daidai ba, wannan abu da nayi shi ya kawo sauƙin aikin da class masters ke sha shiyasa nima darajata ta ɗagu a idon kowa ranar da aka karrama ni kuwa harda sabuwar laptop mai tsada ƴar ƙarama mai kyau principal ta bani lokacin ina zango farko a aji 6,tun daga nan na goge kuma na ƙware a harkar computer ba tare da wani ya koya min ba karambani nane kawai yasa na iya, dan tsabar karambani ni na tsara invitation cards ɗin bikin anty salaha kuma kowa ya yaba domin na ɓata lokaci akansa ina yi masa ado. Bayan na kammala makarantar secondary sakamako ya fito na tafi makarantar koyon ilmin na'ura mai ƙwaƙwalwa a garin kazaure nan na sake gwanancewa dama abune da nake so, shekara biyu na gama nadawo gida ɗauke da sakamako mai kyau, babu ɓata lokaci na faɗa jami'ar bayero dan karantar computer science, nan ɗinma nayi na gama cikin nasara nayi service na gama, lokacin ne na fara tunanin abinda yadace nayi domin samun ƴan canji duk da Annie kullum maganar aurena ce a bakinta acewarta lokaci yayi wanda yadace in fitar da miji inyi aure duk da ni har lokacin ban samu wanda hankalina ya kwanta dashi ba domin Allah ma ya sani ni ina da choice acikin maza, akwai irin mijin da najima ina yi wa kaina fata da kwaɗayin samu sai dai yawancin samarin da nake haɗuwa dasu su kuma ba hakan suke ba shiyasa soyayyar tamu bata ɗorewa sosai, a gefe ɗaya kuma yaya faisal ɗan aminin Abba wanda yayi karatu a gidanmu shima sona yake dan ayanzu haka ya jima da kammala karatunsa kuma yana aiki da wata ma'aikata ƙarƙashin gwamnatin tarayya a garin Abuja. Nidai sama sama nake kula yaya faisal bafa wai dan yayi min ba a'a sai dan kawai bana son wulaƙantashi, cikin haka naga wata sanarwa online wai wani kamfani yana buƙatar waɗanda suka iya computer zai ɗaukesu aiki, kamar wasa nayi applying cikin kwanaki biyu suka kirani interview kuma tun awurin suka ce sun ɗaukeni Monday zan fara fita aiki, wannan abu ba ƙaramin daɗi yayi min ba domin kamar irin a mazaunin trainers aka ɗaukemu mune zamu rinƙa koyar da ɗalibansu computer lokaci ƙanƙani na faso gari yanzu babu ruwana da tambayar su Annie kuɗin pads ko kuɗin powder domin albashi ake bamu mai tsoka banda allowances da muke samu, gaba ɗaya yanzu na zama wata busy kullum cikin bincike nake saboda koyarwa sai da research gudun kada students su tsuyeka ko su ƙureka, yaya faisal kuwa yau ina dawowa gida daga aiki naga saƙonsa ta kafar sadarwar Instagram wai gobe insha Allah zai shigo Kano anan ma zai yi weekend ya kira wayata bai same ni ba, shiru nayi ban amsa masa ba domin nidai bana farin ciki da wannan zuwan nasa haka kuma bana baƙin ciki, ƙawata tun ta ƙuruciya wato childhood friend mai suna Maryam ita na yi wa text massage na sanar da ita halin da ake ciki cewar ina da baƙo gobe, reply ta dawo min dashi cewa zata zo anjima inyaso sai mu san abin da zamu shirya domin tarɓarsa, kashe wayata nayi na jonata a charge sannan na saka kayan shan iska na fita, babu kowa a falon mama sai tv dake ta faman aiki ita kaɗai kai tsaye sashen Annie na wuce can na iske su suna girkin abincin dare tare da mai taimaka musu wurin aikace aikacen gida madina, zama nayi ina kallon Annie dake gyara gyaɗar miya,

"Annie bishra bata dawo bane daga gidan anty salahan?"

"ke dai ba baki son zuwa ba? Tunda ita ta tafi ai sai kibarta ta kwana biyu" mama ta bani amsa tana yankan alayyahu, hannu na kai na ɗauki alayyahun na fara tayata gyarashi ina miƙa mata tana yankawa,

"ai ni ban taɓa ganin yarinya mai ƙulafucin gida irin widat ba, duk inda zata je hankalinta baya kwanciya in dai ba a gida ta ganta ba" Annie ta faɗa tana ƙoƙarin tashi daga kan kujerar da take zaune,

"a'a widat kam akwai ƙulafuci, lokacin da tana ƙarama bata ɗaukuwa" inji mama,

"to ai yanzu gashi sai labari" madina ta amsawa mama,

"ai har yanzun ma haka take bata iya tafiyar kwana biyu tabar gida in dai ba makaranta taje ba"

Ina jin su ban ce komai ba domin wani tunanin nake yi acikin raina kawai tunanin aure nake, wato duk ranar da aka raba ni da gidan mu aka kai ni wani garin tofa angama dani dan nasan zan jima ban daina kewar gidan mu ba wannan dalilinne ma yasa ban fiya son inyi saurayi wanda ba ɗan Kano ba saboda bana son yin nisa da gida shi kansa yaya faisal sai munyi ta da wajewa idan har Allah yayi shine mijina to sai dai ya nema min gida a Kano ya ajiyeni inyaso shi sai ya rinƙa zuwa duk lokacin da ya samu dama amma gaskiya bana jin zan iya binsa Abuja ɗinnan, sallamar Maryam ce ta katseni daga tunanin da nake yi, miƙewa nayi tsaye lokacin da suke gaggaisawa dasu mama bayan sun gama muka nufi ɗakina dake can cikin sashen mama domin acan duk aka yi mana ɗakuna yaran gidan, bishra ce kaɗai take ɓangaren Annie, ɗakin dake mazaunin nawa muka shiga Maryam ta zauna bakin gado tana kallo na yayin da nake duba wayata wacce ke jone jikin sucket tana charge,

"yan mata ya aka yi ne?" na fada cikin murmushi batare da na kalleta ba, itama murmushin tayi sannan cikin tsokana tace,

"saurayinmu me yafi so acikin nau'in abinci da abin sha? So nake mu burgeshi ƙarshen burgewa sannan ya koma gida yana santin girkin mu..."

Ɗan taɓe baki nayi kafin na ajiye wayata na koma gefen gado na zauna ina tattare ƙasan dogon wandon cotton din da yake jikina,

" ƙawalli nifa wallahi bana wani ɗokin zuwan bawan Allahn nan saboda kawai ina kulashi ne sakamakon akwai alaƙa mai ƙarfi tsakanin iyayenmu amma ni ba shine zaɓina ba......"

Numfashi taja sannan ta kalleni bayan ta ɗan yi tagumi kamar wata sabuwar marainiya,

" ƙawalli kenan, sau da yawa kalamanki na bani mamaki kuma na kan rasa a gurbin da zan ajiye su, wai menene laifin yaya faisal? Kin san asalin sa, kin san halayansa da ɗabi'unsa, yana da iliminsa yana da aikin sa sannan ko halittar da Allah yayi masa bashida muni to me kike nema? "

Lumshe idanuwa nayi ina sakin ajiyar zuciya nasan duk yanda zan kai da kwatanta mata abinda ke kai komo acikin raina ba zata fahimceni ba, kai bama ita kaɗai ba kusan kowa ba zai gane abinda ke raina ba,

" ni babu abinda nake nema ƙawalli, kawai dai ina son in auri mijin da nake jin sonsa da ƙaunarsa har cikin jinin jikina wanda zai zauna a zuciyata, wanda ko laifi yayi min idan na kalle shi zan ji na huce saboda tsabar son da nake yi masa..... Wallahi idan na auri yaya faisal ba fa lallai in iya faranta masa yadda yakamata ba saboda bana jin ina yi masa irin wannan mahaukacin son da nake ji a jikina zan yi wa mijina..... "

Dariya Maryam ta sheƙe da ita kafin ta dafa kafaɗa ta tana kallo na,

" wannan yarinyar akwai motsi akanki, to waye ya faɗa miki yanayin yanda muke jin so ɗaya ne? Kowanne ɗan adam da irin yadda yake jin soyayya, ƙiyayya, kwaɗayi, wasu suna zurfafa soyayya ko ƙiyayya yayin da wasu kuma ƴan i don't care ne, kuma kema kina daga cikinsu saboda baki taɓa yin saurayi kinji kina tsananin sonsa ba ko Kiji kin damu dashi irin totally ɗinnan, dan haka kima cire wannan batun a ranki, nasan insha Allah daga ranar da kuka zama ma'aurata zaki so shi kuma zaki ƙaunaceshi"

"gaskiya ƙawalli bana jin hakan zai iya zama gaskiya acikin rayuwata domin ni kaɗai nasan abinda ke kai komo acikin raina, sannan ni ban yarda da kalamanki ba da ki kace wai mutane suna da bambanci wurin jin raɗaɗin so ko soyayya, duk wani mahaluƙi yana jin so acikin ransa mutuƙar yasamu wanda yake so haka kuma yana jin ƙiyayya acikin ransa idan har aka yi rashin dace jini bai haɗu ba ko kuma idan an ɓata masa"

Mayafin jikinta ta cire ta ajiye gefe sannan tayi gyaran murya ta dube ni,

"wai baki yarda da maganata ba kenan da na ce miki akwai mutanen da sam kwata kwata basu jin son kowa acikin ransu haka kuma basa jin tsanarsa? To bari na baki misali da jin ƙamshi, a duniyar nan tamu akwai mutanen da su gaba ɗaya basa jin ƙamshi haka kuma basa jin wari, su awurinsu da ki saka turare da kar ki saka duk ɗaya ne domin basa bambance ƙamshinsa da warinsa, yayin da wasu mutanen ke masifar jin ƙamshi ko yaya kika saka turare sai sun ji ƙamshinsa to haka so yake ko ince zuciya, wata zuciyar tana da ƙulafucin so sannan babu wahala ta faɗa so yayin da wata zuciyar babu ruwanta komai kyautatawa da kulawa bata zarmewa cikin soyayya to ke taki zuciyar irin wannan ce shiyasa kowanne saurayi sai kiga bai yimika ba komai girman haɗuwarsa kuwa"

Ɗan damm nayi batare da nayi magana ba face jujjuya maganganunta da na keta faman yi acikin raina, ina sake tambayar zuciyata wai dama ana samun irin haka kamar yadda ƙawallita ta faɗa??............................ ✍🏻





*_Ummi Shatu_*👌🏻
[1/5, 12:43] Maman K: ©️ HASKE WRITERS ASSOCIATION.
_(Home of expert & perpect writers)_



*GARIN DAƊI.......!*💍💍


*_NA_*


*_UMMI A'ISHA_*


*Wattpad:ummishatu*



*2*



~~~Ganin na zurfafa wurin tunanin da baida wani alfanu ya sanya Maryam zungurata tare da faɗin,

"tunanin me kike yi ne kuma? Wai dan Allah menene damuwarki ƙawalli?"

Numfashi na ajiye ahankali kafin na kalleta ina sake gyara zamana bayan na jingina bayana da jikin gadona,

"kawai mamakin kalamanki nake ta faman yi, ta yaya ma zaki kwatanta zuciya ta da misalin mutanen da basa jin ƙamshi ko wari? Ni dai ina ji acikin raina kawai dan yaya faisal ba type ɗina bane shiyasa bana jin sonshi acikin zuciya ta"

"dan girman Allah kibar maganar nan ƙawalli, kawai muyi maganar abinda yadace muyi wurin karɓarsa, me kike ganin za mu shirya masa?"

Na san dan kawai abar maganar yasa ta faɗin haka, share maganar nima nayi nai tsam da raina sannan na bata amsa da cewa,

" nifa da snacks ma kaɗai zan haɗa masa ai ya isheshi kuma bamu wahalar da kanmu ba "

Hararata tayi tare da jan ɗan ƙaramin tsaki,

"mtswww kina da damuwa wallahi, ta yaya zamu bashi snacks kaɗai? Gaskiya koda zamu bashi snacks ɗin to ya zama dole mu yi masa girki"

"nifa gaskiya agajiye nake kema kin sani, dama weekend ne kaɗai ranar hutuna to shima weekend ɗin gashi yazo min babu hutu"

"wallahi ko zakiyi me sai mun yi masa girkin nan, mutum zai taso tun gari igari ya Abuja yazo takanas saboda ke kice wai iya snacks za a bashi? Wannan ma ba zai yuyu ba"

"to naji, yanzu ke aganinki me da me yadace muyi masa?"

"yawwa yanzu kika yi magana, fried rice ma kaɗai ta isa da ɗan pepe chicken ɗinsa sai cream cocumber and apple salad inyaso sai ayi snacks ɗin da lemon kwakwa"

"shikenan to babu matsala zuwa goben da safe sai muyi"

"haka nake son ji, ko kefa, bari in tashi in je gida sai goben"

Mayafina na ɗauka na bi bayanta domin yi mata rakiya, muna tafe muna sake tattaunawa har muka zo daidai sashen samarin gidan mu wanda a halin yanzu iya yaya Abdul hakim ne kaɗai aciki domin yaya Abdallah yayi aure shi kuma yaya Abdurrahman ya tafi bauchi wani aiki, muryar yaya Abdul hakim muka tsinkayo yana cewa,

"idan kika sake kika fita ahaka sai jikin ki ya faɗa miki...."

Jikina na shiga dubawa amma banga aibun shigata ba sam domin kuwa riga da wandone ajikina masu taushi sai mayafi da na yafa,haushin hakanne yasani juyawa na koma ban ƙara bi ta kan Maryam ba dake tsaye suna gaisawa dashi, ina komawa ɗakina nayi salla bayan na idar na sake komawa wurin su Annie waɗanda ke zaune cikin wata runfa dake cikin farfajiyar gidan mu, zama nima nayi bayan na zubo abinci, nan na ɓata lokaci har zuwa lokacin da Abba ya shigo nan kuma muka rankaya muka bishi sashensa, Abba yana mutuƙar ji dani domin sunan mahaifiyarsa gareni haka kuma shine da kansa ya saka min sunan da ake yi min alkunya dashi wato widat. Ganin ƙarfe goma saura ya sani yi wa su Abba sallama na wuce ɗakina, miss called nagani guda biyu na yaya faisal, shirin bacci nayi ina tsaka da addu'a naji wani kiran yana shigowa, ɗauka nayi bayan na kwanta na nutsu ina saurarensa,

"Ko gimbiyar ta fara bacci ne na tasheta? Ni ɗinne akwai ni da rashin haƙuri in dai akanki ne...."

Danne abinda nake ji nayi na ƙirƙiro murmushin dole nayi wanda har shi saida ya jiyo sautin fitarsa, sau da yawa bana jin daɗin hirar da yake yi min kawai dai ina daurewa ne in danne in saurareshi amma ba wai dan yana burgeni ba,

" ba bacci nayi ba, ina wurin Abba ne kuma na bar wayar a ɗaki sai yanzu na shigo"

"ƴar gatan Abba, ai najima da sanin dama Abba ya naji dake, duk gidan nan babu wanda ya kai mu gata"

"har da kai a tsokanar?"

"a'a ba tsokana bace, na san bacci kike ji kin dawo daga aiki kin gaji, dan haka bari na barki kiyi bacci kafin mu haɗu gobe"

"shikenan nagode"

"kiyi bacci lafiya, bye bye"

Kashe wayar nayi na turata can ƙasan ɗaya pillow na dake gefen kaina domin dama baccin nake ji kamar ya sani shiyasa lokaci ƙanƙani bacci yayi awon gaba dani. Misalin ƙarfe 11 saura na tashi daga baccin da na koma bayan sallar asuba ganin yanda lokaci ya tafi ya sani zaro ido a raina ina cewa,

"har yanzu ƙawalli bata zo mun ɗora girkin nan ba"

Brush kaɗai nayi na fita amma sai dai me? Tun bayan fitowata nake jiyo wani lafiyayyen ƙamshi wanda ya tsinkar min da yawu, kitchen ɗin mama na shiga wanda daga can ne nake jiyo tashin ƙamshin, ina shiga na iske ƙawalli tanata cin uban aiki kuma ita kaɗai, ta sauke fried rice tana kwashewa cikin warmer sannan ga samosa tana soyawa gefe ɗaya kuma tana yin chicken pepe, sakin baki kawai nayi na tsaya ina kallonta gaba ɗaya ma na rasa abinda zan furta,

"yan mata sai yanzu aka tashi? Barka da fitowa"

"haba dan Allah ƙawalli, yanzu maimakon ki tasheni muyi aikin tare sai ki zo kiyi ta wahala ke ɗaya? Oya tashi in ƙarasa"

Murmushi tayi sannan ta miƙa hannu ta ɗauko plate guda ɗaya na tangaran ta soma zuba fried rice ɗin aciki,

"na san kina jin yunwa to ga taɓi kije kici idan kin gama kiyi wanka ki shirya dan babu mamaki ya taho.... Ki duba cikin fridge salad ɗin da na haɗa na ciki sai ki ɗan ɗibi kaɗan dan na baƙo ne kawai dai na sanmiki ne...."

"dan Allah kibar shi in ƙarasa kema kije ki huta" na faɗa ina marairaicewa,

"zancen kike so, nifa na gama aikina malama, idan ma zaki karɓa kije kici gara ki karɓa idan kuma baki karɓa in mayar abuna in juye dama albarkacin yaya faisal kika ci...."

Murmushi nayi na karɓa ina harararta,

"har wani ma albarkacin sa naci? Shi awa"

Bata kulani ba ta maida hankali wurin soye soyen da take yi ganin haka ya sani wucewa falon mama na ɗebi salad ɗin kamar yadda tace sannan na zauna na fara ci ina sake jinjina halacci da mutunci irin na Maryam duk da na san nima ɗin idan nice zanyi mata fiye da haka to amma a ƙawayen yanzu a wannan zamanin ba lallai asamu waɗanda suke ƙawance tsakani da Allah kamar yadda muke yi ba, ina ci ina duba lokaci ta agogon bangon dake kafe cikin falon ahaka na kammala na wuce ɗakina, saida na buɗe wayata sannan na fara shirin shiga wanka, massage ɗin yaya faisal ne ya shigo nan na buɗe naga yace min ya taho yana hanya harma ya wuce Kaduna, reply na mayar masa cewa Allah ya kawo shi lafiya, daga nan na shiga wanka a raina ina cewa gara inyi inyi in fito dan nasan yanzu zan ganshi ya ƙaraso saboda bala'in gudu gareshi a mota sam bai iya driving a hankali ba. Bayan na fito daga wanka ina shiryawa ƙawalli ta shigo riƙe da plate tana cin fried rice,

"sannu da aiki, nagode madalla Allah ya bar zumunci..."

"wannan yarinyar.... Kina abu kamar wata tsohuwa wadda ta shekara ɗari a duniya, shegen manyance"

"daga godiya shine manyance? Ai shikenan, ya kusa ƙarasowa"

"Allah ya kawoshi lafiya..."

"amin" na amsa ina ƙoƙarin ciro wata doguwar riga ta wani yadin material milk colour dama kusan irin shigar da nafi yi kenan doguwar riga dan zai yi wahala ka ganni da riga da skirt ko zani, daga doguwar riga sai riga da wando, turaren Arabian oud nayi amfani dasu sannan na saka kayan na yafa baƙin sirrin gyale, ina zaune kusa

Please Login or Register in order to submit comment