Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
*RUBUTACCIYAR QADDARAH*
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
*By Maryamah* 💞💞
©2020

PAGE 01
Qarar wayarta ceta ta yarda ita daga daddadan baccin safen da ta koma tunbayan data idar da sallar asubah. Idonta arufe ta laluba bedside drower din tareda daukan wayan, akunnenta kawai tasaka Kaman yanda tayi tunani muryar kawarta taji Afeeya. Cike da karadi take cewa "ah this girl so u dey even sleep u forget say na Guru lecture we get today koh?" ae tun Afeeya bata karasaba tai tsalle ta diro daga kan gadon tareda kallon agogo.9:10am yanuna lecture dazasu shiga 10:00am sanin halin Guru Kaman yanda suke kiran lecturan medaukansu Biol315 dabaya tolerating late coming koda karin minti daya yasa dasauri sauri tai wanka kasancewarta ba ma'abociyar kwalliya ba yasa doguwar riga kadai ta zira tareda daukan jakanta tayi waje bata ko saurari Mama Uwani daketa faman kwala mata kira Akan ta tsaya ko Tea ne tasha tayi waje.
Kiris ya rage ta fasa kuka ganin parking space din babu ko mota daya. Se alokacin ta tunada motarta na wurin gyara sannan kowa na gidan yafita bata da zabi illa ta taka da kafa zuwa titi ko Allah zesa ta samu abin hawa. Tafiya kawai takeyi tanajin wayarta na kara alaman kira Amma taki kulata abin haushi har seda tazo kabuga daga cikin unguwar tasu ta Tudun yola sannan tasamu adaidaita sahu. BUK old site yakaita, Sanda ta isa kofar Lecture Hall din a gajiye take liqis, tsayawa tayi sannan ta duba agogon wayarta karfe 10:20am ta gani ido ta zaro dan ko giyar wake tasha bata isa ta ratsa masa class ba, rashin mafita ya sakata kawai ta nemi guri akan varander dake wurin ta zauna tana sauraron yanda yake gabatar da lecture din tashi cikeda kwarewa dasanin abinda yakeyi. Tabbas ya amsa sunan nasa na Guru Dan da ka yake bada lecture batareda ya duba littafi ba haka idan yana dictation baya manta ko full stop akan abinda yafada. Tayi nisa cikin tunanin tajiyo muryarsa yana fadin "Tear a sheet of paper and write your name".
Ko ba afadaba tasan short gun zebayar nan sauran daliban yan uwanta da suka yi latti suka hau hayaniya suna fadin "we are sorry sir" Dan sunsan tabbas inhar akayi test dinnan babu kae tokuwa rubutacciyar carryover ce Dan shi baya fixing date na test haka in kayi missing baya make up . Banzan kallon daya watsa musune yasasu yin shirun dole se asannan idonsa ya sauka akanta, hankaki kwance tana danna wayarta kamar ma batasan abinda yake faruwa ba. Murmushin da iyakarsa lebe yayi Idonsa still akan ta yafurta "You can come in but indicate on ur papers as late comers I'm going to subtract 5 marks from ur score" dasauri suka ringa shiga dukda sunsan balallai suyi wani abin kirkiba Dan inkai missing lecture dinsa sau daya ba lallai kagane class din gaba ba.
Yi tayi Kaman bata batajiba seda wata yarinya dake kusada ita ta kara maimaita mata dacewa "kitashi tun bechanza ra'ayiba". Tura bakinta daya zame mata dabi'a tayi tana kunkuni tareda harar Afeeya dake mata dariya kasa kasa sannan ta shiga, duk abinda takeyi akan idon Guru Dan murmushi kawai yayi Sannan yashiga dictating musu test question din daya basu minti 20 kachal. Kamar yanda ka'idar sa take kuwa ko minti daya be kara musuba ya tattara takaddunsa yayi waje dan shi haka yake baya shiga lokacin wani shima ba'a shigar masa nasa.
Bayan da suka fito Afeeya na mata tsiyar wae me ta tsaya yi harta makara yanzu da bebarsu sun shigaba yaya kenan, ita dae bata tankataba har suka shiga wata lecture. Kasancewar chain classes ne dasu yasaka basu samu break ba se karfe daya. Suna zaune a cafteria suna cin abinci ita Afeeya, Maryam se Aysha,hira sukeyi jefi jefi har ta gama, ganin basu gama ba kuma da dan sauran lokaci ya sakata ciro wayarta dake cikin jaka tafara duba missed calls din kai murmushi tayi ganin kiran sahibinta har 5 missed call batareda bata lokaciba tae dialing number kaman dama yana jiranta yae saurin katsewa ya kirata.
" HAMDAH" ya kira sunanta cikin wata irin murya datake sakata manta kowanne saurayi inbashiba."na'am ABDUL" ta amsa masa.
"I missed you so badly babe wallahi i feel like flaying to Nigeria to come and see that beautiful face of yours". wani killer smile ta saki kamar yana gabanta tareda cewa "I missed you too My Jaan can't wait to see you". Tuni ta manta da wanzuwar su Aysha dake kallonta, ko ba'a fada ba sunsan Abdulmalik ne Dan aduniya in kanaso kaga fara'ar HAMDAH to kakira sunan ABDULMALIK.
Abin har mamaki yake basu insuka tuna haduwar HAMDAH da ABDULMALIK din lokacin suna 100l alokacin shikuma yana service dinsa a Chemical engineering department nan BUK. Ba irin wulakancin da beganiba a wurin HAMDAH Amma ya jure Dan acewarsa samun mace kamarta she an sha wahala. Naci da kuma iya soyayyah irin nasa ne ya ribato masa zuciyarta dukda daga baya sun yita samun sabani lokacin data fuskanci tarin yammata daya ke dasu, hakan ba wani Abu bane musamman awurin samari irin Abdulmalik da ya mallaki abubuwa da damage inkayi la'akari da kyau, gayu, ilimi ga uwa uba kuma kudi daya ke dashi Dan haka mata kebinsa ako ina.
A haka dae sukayi sabo tun abin yana kamar wasa harya zama da gaske yakeyi dan zancen Abdulmalik a wurin Hamdah hatta dame bawa flowers ruwa a gidansu ya sanshi. "To Juliet se kitashi mu tafi in kuma anan zakiyi taki lecture din se mu barki muyi gaba". Seda ta hararesu sannan sukayi sallama tana ta zuba masa shagwabarta dake kara masa sonta, se wurin karfe biyar suka tashi gaba daya sukae sallama inda suka fita tareda Maryam daya ke unguwar su daya.
A Get 4 sukayi sallama da Maryam din tashiga gida. Tun daga get take aikawa Khaleefa kaninta da sakon harara dan shi yaja Mata da motarta na nan da duk bata makara har hakaba. "Yi hakuri auntyna wallahi tun 7am nake gurin mechanic dinnan ashe beyiba seda na tasashi agaba tukunna". Se kuma tadan saki fusaka ganin motar tata fes Dan har wankewa yasa akayi "Allah ya taimakeka dayau nida Kaine agidannan" ta fada tana cilla masa bandir na 100N,cafkewa yayi Dan yasan metake nufi tareda cewa "Se Aunty Allah yasa kifi haka "murmushi tayi tareda amsawa da "Amin" takarasa cikin palour.
Zaune ta tarar da mahaifiyarsu wadda base angaya makaba saboda tsananin kama da sukayi, kwalliya tayi ta alfarma cikin wani danyan Boyel dayasha stone work me kyau da tsari yayinda palour ya bade da kanshin turarenta da kuma air freshener da akasaka. "Se Mumcy duk wannan kwalliyar taron Abbah ce haka" cikin sigar tsokana tayi maganar.
"Ungo wannan ja'ira wato kun mayarda ni kamar kakarku ko yanzu su khaleefa suka gama shine kema zaki dora naki". Seda ta kwankwadi ruwan da kareema me aikinsu tamiko mata kafin tace "Ai Mummy kwalliyar yau dince tafi takullum wae duk dan ki hana Abbah karo mana Aunty to tunda tsoranki yakeyi bari muzamu hada kae munemo masa sedai kiji yan kawo Amarya". Pillow dake gefenta ta chilla mata tana cewa "Dan gidanku sedai Abdilmalik yai miki badai Abbah ba nikadice ba kari" dariya ragowar yan uwannata ke kwasa Dan dramer mummy da Hamdah ba fashi kullum se anyi.
Seda tayi sallar magriba sannan ta suko kasan ta tarar da gaba daya yan gidannasu a palour in kacire Anty Zahra datayi aure da Yaya Abubakar da ke aiki a Lagos. Kallonsu tayi tsaf sannan tace"Tab lallai Abbah anmaka wayo kalli wadannan zaratan samarin Duk yayan tane Amma taringa kwaskwarima da powder Duk dan karkaga ta tsufa kayo Amarya".
Harararta Mumcy tayi sannan tace "Wlh Hamdah zanci gidanku haka kawai zakibi kidamu mutane" ta hade rae.kallonta Abbah yayi yaga yanda ta kule yai murmushi yace "Haba An Maririna aikinsan kekadaice ki kyale Hamdah" she a sannan ta saki ranta Dan tasan tsakanin Hamdah da Abbah tana iya sakashi yayi auran ma kuma yayi.
Cin abincinsu sukeyi cike da kauna sam babu wani takura a tsarin rayuwarsu inkaga yanda iyayen ke wasa da yayansu haka babba da karami Amma kuma hakan besa wani ya raina nagaba dashiba komai nasu yanada limit.
Zuri'ar Professor Ahmad Muhammad Ammani kenan da Dr Maryam Aliyu yola. Aurene na soyayya tsakanin jikakken Dan Bokon dakuma farar bafillatanar ta yola, sun hadune lokacin da aka turashi bautar kasa Yola yana koyarwa a makarantarsu har Allah ya kaddarah aure a tsakaninsu alokacin Maryam din nada shekaru 13 ya taho da ita nan kano inda iyayensa suke. Auransu ba dadewa suka koma kasar Germany dazama inda yaci gaba da karatunsa na Masters asannane kuma tayi Haihuwar farko ta haifi Yah Abubakar, bayanshi sannan ta haifi yah Muhammad me sunan kakanmu da muke cewa Baffah, se Aunty Zahra sannan Yah Farouk. Alokacin Abba na matsayin Dr a fannin daya karanta wato Physics kuma yana koyarwa a Jami'ar Al-azhar dake Birnin Cairo sai yanemi data koma makaranta yanema mata admission kamar wasa tafara karantar MBBS, dukda karatunta hakan besa ta dakatar da haihuwa ba acewarta su uku iyayensu suka Haifa yayarta Adda Halima Allah beyi zatayi nisan kwanaba ta rasu wurin haihuwarta ta fari daga ita se yayanta daya Kawu Mahmud.
Tana 2nd year dinta ta haifeni shekara biyu tsakani ta haifi khaleefa, a lokacin Abbah yakarbi kwalin kasancewa Professor daganan kuma ya dawo Nigeria domin kasarsa ta amfana dashi.
Bayan khaleefa ta haifi Ahmad Wanda muke kira junior se Hamida, Muhsin da Aliyu muna kiransa Annur Auta mu 10 kenan.
Ayanzu haka babbar gynea doctor ce anan Asibitin mal Aminu Kano yayin da Abbah ke rikeda matsayin VC a wata jami'a. wannan kenan.
Kamar kullum da wuri tashirya dukda yau ba lecture dinsa garesu a farkoba sedan gudun bata lokaci musamman da Malamin daya kama ta yadaukesu bayanan Dan haka batasan wa aka chanzaba. Shigar atamfa tayi Holland me ruwan Ash da dakuma navy blue dinkin riga da skirt ne dukda ba wani heavy make up tayiba Amma tayi kyau sosai.
Tafito domin yin breakfast ganin Mummy bazata fita da wuri ba yasata daukan motarta kirar Toyota _Venza_ sannan tai musu sallama ta fita makaranta. Tafe take tana sauron wakar Eidsheren me taken shape of you harta isa inda tasaba yin parking ta ajiye motan sannan tashiga class.
2:00pm tai closing suka fito suna hira akan bikin Aysha daya ke karatowa "kunga wannan hirar tamu ba karewa zatayiba kuma aron mota nayo kar ayi fushi gobe a hanani "Afeeya ce ta amsa mata da cewa "Ai kedai kin banu wallahi Ina taki motar duk nacinki dai Mumcy bazata hakura tabar miki tata ba" "kamar kuwa kinsan plan dina So nake Abbah ya gaji da rabon fada yasiyamin irinta" daidai Sanda suka karasa gurin motar sedai me wani yayi parking bayanta in a way that bazata iya fita ba seya janye tasa motar.
Baba tsoho kamar yanda suke kiran tsohon dake zama agurin yana Dan kular musu da motocine ya taso yana cewa"yarinya ta an tashi ko?"
"Eh wlh Baba ko kaga Wanda ya ajiye wannan motar?" Tanuna masa latest BMW din dake pake bayan ta ta.
"Eh aikuwa me wancan office dinne Dan ina sallah yazo kafin kuma in idar yabar gurin".
Jitayi ranta ya baci ta tsani abin haushi "inba shirme ba how can you block some ones car ko angaya masa zama nazoyi makaranatar".fuu ta nufi office din da Baban ya kwatanta mata bata ko saurari Maryam dake sanar mata da office din waye ba.
A cukule ta karasa kallon kofar tayi taga an rubuta Dr AA Galadima. Knocking tayi Amma taji shiru kuma dae dae zuwanta taga wani yafito daga ciki harta tambaye shi ya shaida mata da mutum a ciki hakan yasa ta saka kai kawai tashiga.

Yana zaune akan kujera ya juya baya da waya akunnansa, yanda yake maganarne ya tabbatar mata da mace yake sedai kalaman daya ke amfani dasu sam basu yi kama da na soyayya ba hasalaima sun fi kama da cin fuska ko wulakanci duk da muryarsa a kasa take. Gashin kansa takalla tayasha gyara style din askin yafita sosai aranta tace "Kaman Abdul dina".
Tunda ta Shiga Kallo daya yai mata ya ci gaba wayarsa, ganin abinnasa harda rainin wayo yasa ta cewa "Sir wurinka fa nazo" akalla yakara kusan minti 5 sannan ya kashe lokacin Hamdah tagama cika fam.
"Yes inajinki" ya amsa mata cike da izza. seda ta harareshi ta gefen ido Wanda sarai yana lura da duk wani cuna baki datakeyi sannan tace "Nazo zan dauka mota nane..."se akacemiki tana gurina" yai saurin katseta. Wannan karon harda murguda baki tace sannan race "Niba haka naceba nadaiga Mota a gurin kuma ance taka ce".
Gefen table din yanuna mata tareda cewa "You can take the key ki matsar da ita seki kawomin "kallon sa kawai tayi tana jinjina rainin hankali irinna Guru kamar zatayi magana sedai kome ta tuna oho ta saki murmushi mai ma'anoni dayawa tareda cewa "Ok Sir" tadauka tafice.
Tana tafe tana murmushi harta karasa inda tabarsu Maryam, kallonta suke da mamaki ganin dadewar datayi gashi kuma tafito da fara'a. Maryam ta cillawa key din motar Mumcy tace "drive it home please "lokacin da take kokarin kunna motar Guru.
Tsabar mamaki kasa magana sukayi Afeeya data gama hango abinda ke shirin faruwa tai saurin tareta ta hanyar cewa "Aa Hamdah karki haka wata rigimar tafi gaban wasa"
"Naki kallo daga kaina baze kara rainawa wani hankali haka ba" taja mota fuu tayi gaba abinta, basuda zabi illah suka bita a daya motar Dan tuni Hamdah tafice daga cikin makarantar.
*****************************************

🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
*RUBUTACCIYAR QADDARAH*
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
*By Maryamah* 💞💞
©2020

Shaf Guru ya manta da lamarin wata Hamdah harya gama abubuwan da zeyi yai shirin tafiya gida. Mukullin motarsa ya shiga nema Amma yace daukeni inda ka ajiye, wani abokin aikinsa ne ya leka office din jin motsin mutum "Dr ashe kadawo dazu naga fitarka Ina ta daga maka hannu baka ganiba".
Kallonsa yayi da mamaki aransa yana tunanin yaushe ne ma ya fita "So she took my car" ya fada a fili sedai instead yaji haushi se kawai yaji ta birgeshi kawae, gaskiya tana da liver shi kuma yana son mutum mara tsoro.
Wayarsa yadauka kawai yakira drivernsa akan yazo yadaukeshi aransa yace "let see if she will return it". Akan kwanar layinsu suka hadu da Mumcy data gaji da zaman jiranta "su Hamdah kuma yau wa aka tsokano Nidai babu ruwana wlh karma ki lossafani cikin rigimarki. Me tsaya miki kiyi rashin jin baya nan ga kuma yayanku can Baffa yazo".
Baki ta cuna takarawa motar wuta aranta tana cewa "ita Mumcy kullum nice mara gaskiya bayan batasan me mutuminnan Dan rainin hankali Yayi min ba ai dai shiya fara tsokanata" guri me kyau ta samarwa motar ta ajiye sannan ta shiga sabgoginta. Duk wanda ya shigo gidan seya kalli motar dan dae sunsan babu me irinta a gidan, sanin Hali yasa Babu Wanda yabi takan ta bare motar da ta shigo da ita Dan in da sabo Halin Hamdah ne tada zaune tsaye.
Seda aka Kwana biyu a tsakani Yah Baffa ya tasata agaba da tambayar Inda ta samo mota. Rasa abin ce mata yayi illa Kallon ta kawae da yake, amsar da tabashi tayi bala'in daure masa kai Wae "Motar Malamin muce"
"Shine yabaki aro ko yaya?"
"Aa"
"Se akayi yaya?"
Tiryan tiryan ta labarta masa yanda abin ya faru Tundaga farko.
"kyaci ubanki ranar da kika dauko fadan dazesa adaureki shashasha me kalar salahai se masifar fitina azuciya".
Cuna baki tayi abinda yazame mata jiki tana kunkuni "Mutum kullum bashida aiki seyiwa mutane fada wae ma meya kawo shi gidan oho".
"Ki fada afili mana karamar mara kunya wlh duk Abbah ne ya lalataki inba haka ba tsabar tsaurin ido kidaukowa mutum mota". ita dai ko ajikinta Dan ko ba komai ta koyawa guru hankali" ya taka da kafa ko ya hau lift" ta fada a zuciyarta. Ranar baccin ta tayi harda minshari cike da kwanciyar hankali. Washe garin ranar kasan cewar bata da lecture yasa ta wuni a gida, ido kawai Mumcy ta zuba mata tun tana jiran taga anzo daukar mota har dare yayi taji shiru, gajiya tayi ta tambayeta "Wai Hamdah yaushe zaki mayar musu da motarsu ne?"
"In mayar ko suzo su karba?" tabawa Mumcy amsa hakan yasa takama bakinta tayi shiru aranta ko addu'a take Allah ya kawo Abubakar a gobe juma'a Dan shi kadai ke taka mata birki kan duk iskancin da takeyi. fatanta Allah ya shirya mata Hamdahnta Dan fitinar yarinyar tayi yawa kwata kwata bata da tsoro.
Ranar Monday 8:00am tai mata a class Dan bata so tabar wata kofa da abu ze hadasu bare ya wulakantata tunda Akwai jikakkiya a tsakaninsu. kamar kullum be kara ko minti daya ba yashiga ajin, idonsa akan ta yafara sauka yadan kalleta for some seconds Wanda har mayun yammata masu kallonsa suka hankalta da inda yake kallo nan fa kishin Hamdan ya kamasu Dan asaninsu babu wata mace data ishi Guru kallo Amma se gashi yana kallon wannan fitsararriyar yarinyar da bata ganin kan kowa da gashi.
Ammani Kaman yanda suke kiranta zan iya cewa babu Wanda besantaba afadin BUK both new nd old site. Kasancewarta kyakykyawar mace ajin farko. Fara ce tas koma mu kirata yellow Dan hasken Hamdah har kashe ido yake.bata da tsaho can haka ba gajeriya bace tana dai tsakiya haka girman jikinta sam bata da kiba Amma Allah ya mata kira mai kyau domin saman ta da kasan ta acike yake dam. Babbab abinda ke daukar hankalin Maza akan ta shine kalar kwayar idonta data kasance Grey colour da wani irin sparks Kaman na gold dole in ka kalleta kasake kallo gata da shiru shiru a fuska. Kyanta ya tarar da gayu dukda Hamdah bata kwalliya a fuska amma tana shiga ta burgewa da komai hassadarka dole ta burgeka dan kusan duk wani abin gayu ko kyalekyale na mata a kaf campus din a wurinta ake fara koya. Mutane da dama nayi mata kallon me girman kai kodan rashin shiga sabgar mutane da batayi sefa wadanda suka Santa ko wadanda suke good time ba. ZAHIRIN HAMDAH kenan
A badini kuwa sunan da Ake kiranta a gida shine Fitilar sharri Dan Idan kanason siyan balai da kudinka to ka takali Hamdah. Bata da tsoro ko kadan sannan bata san wani abu rufa rufa ba. Gaba gadi take komai nata. Tana tsananin son abinda take so hakanan tana tsananta kiyayyah ga abinda bata so hakanan bata da Wuyar sabo ko kadan in har jininku ya hadu.Wannan itace HAMDAH AHMAD AMMANI a takaice.
Awa biyu (2hrs) lecture ta daukesu Kaman kullum bayan yagama ya basu short gun test tareda Assignment. Sit by sit yake bi yana tattara takaddun "Meet me in my office" kunnanta yajiyo mata dai-dai lokacin da yazare ta ta takardar Wanda kafin ta dago har ya wuce illah kamshin turarensa dana mouth fresh dinsa daya barmata. Da harara tabi bayansa ta murguda baki sannan tace "se kazo ka daukeni ae kamar wata yarka kana commanding dina" kasa kasa tayi maganar dan ko Afeeya dake kusa da ita be zama lallai taji me tace ba amma yanda yake watching moves dinta bakinta kawae ya kalla ya gane abinda tafada tsaf, se yai murmushi, da ido ya mata alama da "karkizo zakiga abinda zanyi". Yana fita kuwa ta dane kan desk tana tsarawa kawayenta irin dinki da shigar da zasuyi ranar Dinner Aysha.
Agogo ya kalla for the second time kimanin 1hour kenan da barinsa class din. bayan fitarsa sarai yasan basuda wata lecture Dan haka yayi qwafa sannan ya miki ya nufin ajin, Clique members dinta ne zaune Dukkansu Maza da Mata sun zagayeta Banda dariya Babu abinda sukeyi. Labarin wani Bayeraben Professor Abokin Aikin Abbanta a University take basu Dayake sonta. yanda take kwatanta fuskar mutumin Wai dayaga picture dinta seka rantse da Allah tana gurin "I'm telling you Prof Balogun yafi mutuminnan kyau kai A swear ko Obasanjo albarka munin mutuminnan ze iya saka meciki tayi miscarriage Wae shi be yadda ba sona yakeyi" yanda take exergirating Abun ne yake qara basu dariya Shigowarsa tasa kasu yin shiru Dif kaman ruwa ya cinyesu banda Oga Hamda dake kokarin nemo picture din Prof Monkey Tana ci gaba da cewa "wae fa da Abba ya hadamu a waya mugaisa harda wani Babe yake cemin niko dariya nake kaman kaina ya kwance..." daga kanta tayi da niyyar mika musu wayar su gani se ganin mutum tayi akanta kamar gunki. "Ke wato bakiji me nace miki ba ko".
Seka rantse bashi yayi maganar ba. Dukda yanda zuciyarta ke bugu hakan be hanata dauke kai tayi Kaman ba ta jishi ba. "Wai bada ke nake magana ba ne ehe".. "Toh ai ganinayi sunana HAMDAH ba keba.......Wata gigitacciyar tsawa ya daka mata da ta sakata kasa qarasa abinda tayi niyyar fada "I give just 2 minutes to come to my office if not (ya murda hannunsa) wlh nida ke ne yau a makarantar nan".
Sosai ta tsorata, zata iya cewa ba'a taba mata tsawa kamar haka ba. Babu shiri Ta mike jikinta na rawa tabi bayansa. A tare suka shiga office Din Dan har suna kusan cin karo. Kallonta kawae yakeyi Wanda har seda ta tsargu. Seyanzu ya gano zallar yarinta a tareda ita in ya rantse beyi karyaba bazata haura shekaru 17 zuwa 18 ba.
"How old are you?"
Kallonsa kawai tayi irin karaina min hankali tareda dauke kai.
"I'm I not talking to you?"
Ya fada cike da hargagi Dan yarinyar tafara

Please Login or Register in order to submit comment