Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

mafita, bashi kuma dame bashi hakuri dan haka ya miqe ciki a sanyaye ya tafi masallacin dake cikin asibitin ya fara salloli. Ya Dade yana mikawa Allah kukansa tareda Neman yafiya akan abinda ya aikata har besan tsahon lokacin daya dauka ba. Agogon masallacin ya kalla karfe 6:30am almost 3hours kenan da aka shigar da ita theatre room din. Wayarsa ce ta shiga ringing sunan Mum daya gani yasaka shi dagawa da Sauri yana tunanin abinda ya faru kuma a can gidan take kiransa da wannan safiyar.

"Abdurrahman kana ina ne tuntuni gamu cikin asibitin a wanne ward kuke ne" ta fada cikin muryar dake nuna tsantsar tashin hankalin da take ciki.
Dakyar ya iya amsa mata da "Hajiya ina Masallaci yanzu ku din kuna Ina" a zuciyarsa yana tunanin waya gaya mata ma suna asibitin ma. Kwatanta masa inda suke ba bata lokaci ya tashi ya fita zuciyarsa na bugawa da taraddadin abinda zeje ya tarar. A harabar aaibitin suka hadu, kallon sa tayi yanda lokaci daya ya fita hayyacinsa sai ta rikoshi tana cewa

"Oh ni Maimunatu wai me ya sami yarinyar mutane ne Hajara ce ta kira fa take gayamin wai kun kawota asibiti ita ma bata san meya sameta ba" shi sai a lokacin ma ya tuna da wata Hajara suka zo dan tun dasu ka zo asibitin besan inda tayi ba. Haka suka yi zaune jugum jugum kowa da kalar tunanin da yakeyi. Awa hudu sannan aka bude kofar theatre room din. Gaba dayansu suka mike suka nufi Dr Huzaifa, cikin rawar murya ya tareshi yana cewa
"Huzaifa how is she? how is my wife".
Kallon banza Dr yabishi dashi kafin ya mayar da hankalinsa kan Hajiya dake tambayar sa itama akan abinda ya samu Hamdah.
"I can't say anything now sedai kawai mujira ta tashi tukunna muga abinda Allah zeyi and......." Se kuma yayi shiru.
"And what fadi mana" Bashir Kanin Abdurrahman din ya tambayeshi, se yayi Jim sannan yace
"the babies are no more" yayi gaba abinsa.

Gaba daya wutar kan Abdurrahman din ce ta dauke komai ya tsaya masa "Babies" Kalmar ke taci gaba dayi masa yawo akai, kallonsa yakai kan nurses guda biyu dake tsaye a gurin kowacce rike da baby a hannunta se kawai ya zama kamar wani kurma he couldn't say a single word sai kallonsu Hajia yake da suka karbi yaran
"Look at them Yaya wlh just like you" Bashir ya fada in between tears saboda tausayin yaran dake hannunsu masu kyau da aka ce wai sun rasu ya mikawa yayan nasa 7month old baby da girmansu masha Allah zaka iya cewa bacci yake in baka sani ba. Dukka biyun ya hada a hannunsa wasu hawaye na zubo masa, muryar rada rasa yace "I killed my sons, I killed my own boys" hawaye na ci gaba da zubar masa. Wani mugun kallon banza Hajiya ta bishi dashi jin abin dayake fadi, bashiri cikin daga murya tace "Abdurrahman what did you just said ka maimaitamin banji sosai ba". Zuwan Alhajinsu da shima saukarsa Kaduna kenan ya tarar bata nan se sauran yaran suka gaya musu Amaryar Yayansu ce ta haihu twins amma sun rasu shine ya tafi asibitin shima. Duk yanda taso ta yi fada Alhaji Ibrahim hanata yayi
"Ki bari Maimunatu ko ma menene muje gida ba a asbibiti ba"
"Alhaji kaji me yaron nan yake fada kuwa kisa fa naji yana ambata kabarshi yamin bayanin abind yake nufi tun anan" Hajiaya ta fada tana sauke numfashi tsabar yanda ranta ya baci. Lallabata suka shigayi sannan ta hakura amma bata sake yarda ko da ido ta kalli inda Abdurrahman din yake tsaye ba, kofar resting room din da aka shiga da Hamdah ta tafi ta tsaya tana jin likacin da Alhajin yake cewa zasuje da Yaran ayi musu sutura kai kawai ta daga masa batare da ta juyo ba.

Karfe 11am tayiwa Iyalan gidan Prof Ahmad Ammani a asibitin Dan tun lokacin da Hajiya Maimuna ta sanar da Mumcy halin da ake ciki hankalinta ta ya ki kwanciya, dole ba shiri suka nufo kadunan kuma har zuwa lokacin bata farka ba. Suna zazzaune a kofar dakin Dr huzaifa ya fito bayan ya shiga dubata, kallonsu yayi sannan yace
"Zaku iya shiga ku ganta amma please kar Ku tasheta". Gaba daya suka mike suka nufi dakin dan kuwa kowa yana dokin zuwa yaga halin da Hamdahn take ciki harda Abdurrahman se yayi saurin dakatar dashi yace
"Malam dakata mana bamu bukatarka Shiga". kallonsa yayi kaman yanda shima yake kallonsa sai kuma ya gyada kai yayi gaba da niyyar shiga dakin.
"Bakaji me yace maka bane ko kuwa" Hajia ta katseshi cikin tsawa, haka jiki a sanyaye ya koma yana kallonta tacikin glass din da akayiwa dakin Katanga dashi. Batada maraba da gawa in banda computer dake Nina tafiyar numfashinta. Tayi wata fayau da ita ta kara haske sosai kallo daya zaka mata ka hango ramar da tayi lokaci daya.
****************************
A hankali ta fara motsa yatsun hannunta lokaci daya kuma tana qoqarin bude idanunta datakeji kamar an saka gum an liqe mata su. Bin dakin takeyi da kallo tana kokarin tuna musabbabin zuwanta da kuma ina ne nan din amma ta kasa gano ko daya daga ciki. Abu daya ta ke tunowa CIWO, ciwo kadai ta tuno da ta ringaji a daren jiya cikin bacci to kodama mafarki takeyi? cikin hanzari takai hannunta kan cikinta sedai tayi wurin wayam babu tudun sa babu alamarsa lokaci daya wani azababben ciwon ciki da Mara suka taso mata at once ba shiri ta bude dukka muryar da Allah ya bata ta fasa kuka. Gaba daya suka rufa kanta Mumcy ta shiga qoqarin riqeta saboda yanda take jijjiga kamar wadda Ta hau Aljanu har tana qoqarin cire allurar Hannunta, ganin bazata iya ba ya saka Farouk janyeta ya rungumeta gaba daya a jikinsa duk dauriyarsa yau seda ya zubda mata da hawayen tausayi. Dr Huzaifa da Nurse din da ta tafi kiransa ne suka dawo nan da nan ya hada allurai suka taru suka riqeta kafin yayi mata allurar lokaci daya jikinta ya saki ta koma ragwab ta kwanta.

Kuka babu me cewa wani yayi hauri sukeyi hatta mazan basuda courage din rarrashinsu, bayanin da Dr Huzaifa yayi musu wai magani aka bata na zubda ciki tasha kuma over dose shi yafi daga musu hankali to wayayi mata wannan danyen aikin dan sun san dai da saninta bazata sha ba. Kallonsa ya maida kan Abdurrahman dayai saurin miqewa jin Farouk yana qara maimaita wa Huzaifa tambayar Uban waye ya bata maganin a me ma tasha se kawai ya girgiza kai cikin jin dacin abun har ransa yace
"Gashi can mijinta ne se ku tambayeshi dalili" kafin ya gama rufe baki tuni Abdurrahman din har ya bace daga ward din ko kalar rigarsa ba'a hangowa.






🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

*RUBUTACCIYAR QADDARAH*

🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

*By Maryamah* 💞💞
©2020

*PAGE* 3⃣7⃣


Salati Hajiya Maimuna ta rafka tana tafa hannayenta kafin ta fashe da kuka "Ni Maimuna na shiga uku me Abdurrahman ya dauki kansa me yake so ya zama Alhaji kaga irin abinda nake gaya maka tun farko irin haka na guda gashi yanzu ta faru ta qare nidai Hasiya ta cuceni tsakani na sa ita se dai Ubangiji yai mana Hisabi kawai" ta fada tana sake rushewa da Kuka. Senator Ibrahim Khalil da Kunya da Nauyin Iyayen Hamdah ya hanashi kwakwkwaran motsi ya kalleta, tabbas shi kansa ayau yayi danasanin Yancin daya bawa Yayansa Maza musamman Abdurrahman daya fi so duk cikin yayansa. Shi kansa dabi'ar masu jajayen kunnuwa ta hudashi sosai hakan ta sakashi dora yayansa akan turba irin tasu, dukda yana iya qoqarinsa gurin ilmantar dasu ta fuskar Addini domin ko sanda Abdurrahman yake a London akwai malami daya ajiye masa a gida yana karantar dashi amma kuskurensa daya na bashi cikakkiyar damar aiwatar da duk abinda yayi niyya.

A farkon zaman Abdurrahman a London din a hannunsa yake a lokacin suna tareda Hajia Hasiya matarsa ta biyu ita kuma Hajia Maimuna tana Nigeria da sauran yaranta mata. Hajiya Hasiya ita ta bada gudummowa gurin tabbatar tabarbarewar tarbiyyar Abdurrahman din har seda ta samu nasarar cusa masa mugayen dabi'un da suke dawainiya dashi a yanzu. Ita ta tilastawa Baban siya masa gida na kansa dan ya zauna lokacin daya fara University ya kuma mallaka masa duk wasu abubuwa najin dadin rayuwa. Tun shekarunsa basu kai ba yake riqe manyan kudade dan ko be bashi ba ita zata bashi saboda ita Allah be bata Haihuwa ba seta dauki Abdurrahman din ta riqe kamar danta.

"Alhaji kana tsaye yaron nan ya tafi haka zaka barshi kana kallon halin da yar mutane take ciki" Hajia Maimuna ta katse masa tunanin daya tafi, gaba daya ya diririce ya kasa kallon Dr Maryam data harde hannuwanta biyu a qirji Allah kadai yasan me take saqawa a ranta. Tun dazu take ayyana dauke yarta kawai ta tafi da ita amma ta dakata sabida Abubakar daya ce ta Jira Prof Ammani daya taho daga Abuja ya qaraso dan bayaso kanwar tasa ta koma gida da sauran nauyin Abdurrahman akanta dole ayi wadda za'ayi kawai. Shigowar Zahra da Mijinta se Amrah da Afra da sukayo kama kaman basket din data jero kayan abinci a ciki. Idanuwanta kawai zaka kalla kasan tasha kuka hatta da Baban su Amrah taqi koda yadda tayi magana dashi gani take kaman shi ya jawowa Hamdah wannan wahalar, badan shiba kila da batayi wannan qaddararren auran da be qareta da komai ba se wahala da ciwo. Tunda Mumcy ta kirata addu'arta daya Ubangiji Allah yasa maganin be mata wani lahani da ze cutar da ita a gaba ba aure dai an gama shi bi jahi rasulullah bazata koma wannan gidan ba. Kusada Momcy ta zauna ta dage kanta sama dan ko Hajiyar Abdul din bata ji zata iya gaisarwa, haka suka ci gaba da zaman shiru a gurin babu me magana a cikinsu.

Se wurin qarfe biyu Prof Ammani ya qaraso asibitin, kallo daya yayi wa Hamdah ta cikin glass din ya dauke kai zuciyarsa tana masa wata irin quna wai yarsa ce haka kwance cikin mawuyacin hali. Zuwa yanzu kam yaje bango baya tunanin ze iya ci gaba da zuba ido akan abubuwan da suke faruwa seya kalli Farouk daya kame a coner daya yana ta muzurai tun dazun yace

"Umar kaje Near by police station kayi Filing case akansa Abdurrahaman Ibrahim Khalil yayi attempting kisan kai ka kuma tsayawa yar uwarka a kotu ka tabbatar ka kwato mata haqqinta saboda haifarta mukayi kamar kowacce ya bawai siyota nayi a kanti ba amma kafin sannan Alhaji inaso Takardar sakinta ta rigani isa Kano Dan Allah" ya qarasa magana idonsa akan Senator Ibrahim Khalil daya waro idanuwa jin zancen Kotu, se ya mike jiki na rawa ya isa inda Prof yake tsaye, magana ya shiga yi masa yana cewa
"Prof ba haka za'ayi ba inaga wannan duk ba wata babbar matsala bace gaba daya bata fi mu sasantata a cikin gida ba ba lallai se hukuma ta shigo ciki ba saboda qarshe ni abin ze shafa ze bata min siyasata ne kaga ace Dana na cikina ana tuhumarsa da laifin yunqurin kisan matarsa...."

"Ka qara da ya kashe Yayansa guda biyu kaga yanda abinda zefi tafiya daidai, siyasa kuma da kake magana kai ta shafa inda ka lura da tarbiyyar danka da bata kawo mu da haka ba tun farkon hasashen nagarta nayi masa ashe ni ban hango daidai ba to nagodewa Allah daya taqaita samuwar zuri'a a tsakani kaga babu sauran wani abinda ya rage mana mu daku sedai mu ce wanda ya cuci wani Allah ya saka masa, kai Abubakar nemo likitan nan ya rubuta mata sallama Maryam kuje can gidan keda Su Hamidah ku hada mata abinda zaku iya ni kuma zan wuce da Mamana ina da rai bazan bari ta wukaqanta ba" yanda yake maganar kadai ya isa ya nuna maka tsantsar bacin ran dayake ciki. Hatta da fuskarsa ta chanza kamar ba Professor Ammani ba wannan me yawan fara'a da sakin fuska. Zuciyar Mumcy qal ta miqe ko ba komai mijin nata ya yanke hukunci daidai da yanda take ra'ayi dan haka babu bata lokaci suka nufi gidan Abdurrahman din kamar yanda Abba yace ita da Zahra da Inteesar Matar Baffa da suka taho da ita. Hatta da Zahra me tsohon ciki haka ta zage seda suka hade mata kayanta tsaf wadanda za'a kwance kawai suka bari kafin su gama tuni Farouk ya nemo Mota da masu kwance Gadajen suka shiga loda kaya baji ba gani. Babu irin roko da Kukan da Hajia Maimuna batayi ba akan suyi hakuri dan tuni suka baro asibitin bayan Abbah ya dauki Hamdah a Ambulance suka wuce Kano dukda irin magiyar da Dr Huzaifa yaringayi masa shima akan ya barta suga yanayin lafiyar ta amma yace Aa, bazata qara koda minti a qarqashin kulawarsu ba kuma su tabbata duk inda Abdurrahman yake ya sakar masa yarsa dan baya su su shiga kotu da sauran wata alaqa a tsakaninsu bare har ayi tunanin ze dubi alaqar auratayya ya raga masa.

Tun kafin su Isa Kano yagama booking komai na Asibiti dan haka straight AKTH suka tafi da ita. Matsayinsa da kuma Mamanta yasa kusan likitoci biyar suka rufu akanta duk dan sake tabbatar da lafiyarta Alhamdulillah kuwa babu abinda ya sameta se dan abinda ba'a rasa ba Operation dinma na plaster yayi mata ba dinki bane dan haka baze wani dauki dogon lokaci ba ze warke. A Amenity aka kwantar da ita, Abbah da kansa ya zauna har seda su Mumcy suka iso Kano yace taje gida ta huta se da daddare tazo ta karbeshi babu wanda ya musa masa dan sun san tunda har ta kaishi ga haka to kuwa ransa ya baci bilhaqqi.

Cikin ikon Allah washe garin ranar wurin 12pm ta farka kuma cikin hayyacinta. Kallon Mumcy dake zaune akan Farar kujera a gefen gadon suna yar hira da wasu qawayenta likitoci da suka zo duba Hamdan se kuma Hamidah na tsaye tana jijjiga little Maryam da suke cewa Miimi yarinyar Yaya Baffa mamanta taje gida ta dawo. Dan yunqurawa tayi tana cije baki saboda zafin da gurin yankan yake yi mata tace "wash Allah" abinda ya janyo hankalinsu suka shiga yi mata sannu,

"Sannu Hamdah kin auna arziqi ina keyi miki ciwo yanzu" Dr Zuhra ta fada tana tallafota dan ta gyara mata zama ita ke handling case din Hamdah a yanzu. Seta nuna mata cikinta kawai dan batajin zata iya magana.
"Zaki iya tashi" Dr Zuhra ta kuma tambayarta nan ma kai ta gyada mata alamar Eh, seta kamota ta sauka daga kan gadon tana mata sannu,

"Daure ki taka qafarki don't be lazy kinji in 3 days time zakijiki garas insha Allah kinji Daughter" haka Dr Zuhra keta fada har suka shige Toilet din dake manne da dakin, Mumcy dake binsu da kallo tundazun tausayin yar tata fal zuciyarta ta sauke ajiyar zuciya a hankali. Allah kenan meyin yadda yaso ba kuma ka isa ka tambayeshi dalili ba, ji a yadda Hamdah ta taso da rayuwarta amma Aure ya chanza mata komai, ita kuma tata rashin sa'ar a aure take, Allah kadai yasan meya sa yake jarabtarta ta haka koma mene tana fatan ya bata ikon cinye wannan jarabawar. Tana zaune har suka fito daga toilet din Hamdah daure da Babban Towel Fari a jikinta sannan ta lulluba mata wani akanta dake digar ruwa da alama wanke shi akayi.

"Aa Dr wanka kika wa yar taki kenan" Mumcy ta fada cikin murmushi tana gyara mata inda zata zauna.

"Wanka na mata data ci abinci tasha magani zakiga qarfinta ya dawo Allah na tuba me zamu jira kuma, shi dai wannan yaro kansa ya cuta na ma gayamata ta sakawa zuciyarta salama in so samu ne ta share babinsa a rayuwarta kamar ma bata yi wannan auran ba insha Allahu tana gama jego Allah ze kawo mata mafi alkhairinsa ke se tayi auran da kowa zeyi alfahari dashi ai Aisha ba qaramar mace bace bakuma ta boranci muna nan dadin nan ita ma seta ji shi bi'iznillah".

Kalamnta sunyiwa Mumcy dadi matuqa take yaba kulawar da Dr Zuhra take bawa Hamdah tunda aka kawota asibitin a tsaye take akanta. Haka ta zuba mata lafiyayyen abincin da Intee ta kawo dukda bakinta babu dadi amma ta daure taci sosai kuma taji dadin jikinta dan harda Yunwa data qara kashe mata jiki. Kan gadon ta koma bayan ta gama duk a qoqarin ganin ta hana zuciyarta tuna abinda ya farun take kamar yanda Mama Zuhra take ta qara mata Nasiha akai. Wunin ranar haka tayi shi dangi da abokanan arziqi da suka samu labari nata zuwa dubata ciki kuwa harda Hajjan Abdulmalik.

Kallon Zainab ta ringayi data lalace kamar ba ita ba ta jeme tayi baqiqqirin a ranta tana mamakin meya sami Zainab din haka? Ga Khausar ita ma ta zama abin tausayi da alama zaman gidan ya isheta kuma babu tsayayye ita kanta Hajjan Abin tausayi a yanda take gayawa Mumcy wai Hawan Jini ne yai mata mugun kamu har likitoci sunce in ya ci gaba da hawa stroke ze iya kamata to ya zakayi Matsaloli sun saka ka a gaba sedai Addu'a kawai. Haka suka qaraci zamansu sukayi musu Sallama suka tafi. Bayan sun fita ne Hajia Amina Maman Maryam take cewa Mumcy
"Maryam kinga ishara ba ita rayuwa yanzu tun a duniya bawa yake kwashe abinda ya shuka kiga dai Matar nan wai tana maganar Hawan jini dana Allah ya taimaketa ciwon zuciya be kamata ba ai tayi a hankali kawai" "Hmm" kawai Mumcy ta fada dan ita ba wannan bane ma a gabanta yanzu lafiyar yarta tafi mata komai.

Satinta daya aka sallameta cikin ikon Allah ta warware se abinda ba'a rasa ba, harzuwa lokacin babu Abdurrahman babu dalilinsa hatta da wayoyinsa a kashe suke ba bu kuma wanda yasan inda yake. Tsaf ta ware take sabgoginta dukda wasu lokutan idan ta tuna yaranta data rasa seta shiga daki tayi kuka gashi ko kalar fuskarsu bata gani ba, ta dai riga tabar Abdurrahman da Allah shi ze bi mata haqqinta. Lokaci lokaci Hajara tana kiranta a waya suna gaisawa a bakinta ma takejin batan dabon da Abdurrahman din yayi wai ba'a san inda ya tafi ba a ranta tace shi yaga duhu ita kam Haske ta gani ya gama boye boyensa ya fito ya bata takardarta shi kadai ya rage musu a tsakani yanzu.

***************************
Two month leap
Batasan ya akayi ba meya faru ita dai wata safiyar litinin Yaya Farouk ya shigo mata da well printed farar takadda da sunan takaddar sakinta. Dukda haushinsa da takeji amma seta tsinci kanta da rashin jin dadin sakin, shikenan fa yanzu zata shiga zawarci na biyu yanzu za'a fara lissafa mata aure Allah kadai yasan kuma ina zata fada se kawai ta zauna a gefen gadon Mumcy inda ya tarar da ita ta saka kuka.

"Kiyi haquri Maman muma ba'a son ranmu ba amma wannan ita kadai ce hanyar da zamu inganta rayuwarki, Abdurrahman ba miji bane kura ce da fatar Akuya ya yaudare mu ne kawai dukda bawa baya taba kaucewa Qaddaar sa ki godewa Allah daya kawo sanadiyyar rabuwar ku dan na tabbata idan kika san ainihin shidin waye se kinyi dana sanin Faruwar ranar da kika hadu dashi ma a rayuwarki gaba daya dan haka kiyi saurin share hawayenki kuma ki godewa Allah kiyi fatan hakan yazama alkhairi a gareki insha Allahu qarshen wahalarki kenan kinji" kalaman Abba da suka sanyaya mata zuciya kenan da daddare bayan data same shi da takaddar da Yah Farouk ya bata. Haka ta koma dakinta jiki a sanyaye sedai koda sau dayane tana so ta qara ganin Abdurrahman din, tana so ta tambayeshi wane laifi ta aikata masa haka da har ya mata irin wannan danyan hukuncin, so take ta tuna masa da romon bakin soyayyar dayai mata alqawari da tarin kulawa kafin ta yadda ta aureshi ya manta lokacin daya ce ze wa marigayin mijinta takwara in har ta haifi Da namiji lokacin da yake cewa he can't wait to have cute kids with her amma ya qare da yi wa yayansa kisan wulaqanci amma babu komai akwai Allah ze kuma yi musu hisabi dan dai bazata iya yafe wannan cutar da yayi mata ba.

Cuku cukun neman Admission ta shigayi dan tana so ta fadada iliminta. A kaf yaran gidansu Goma ita kadaice ta dauke bangaren Abbah wato lecturing, ita ma tana so ta taka matsayi irin nasa wata rana a kirata da Professor Hamdah Ahmad Ammani dan haka ta shiga neman makaranta inda zata dora Phd dinta akan Genetics Engineering, cikin ikon Allah ta samu admission a Wata makaranta dake birnin London ta kuwa fara shirye shiryen tafiya cikin sati biyu komai ya kammalar mata hatta da gidan da zata zauna ta kama an kuma gama shirya mata komai seda ya rage saura kwana uku ta fara lectures jirginta ya daga zuwa qasar ta London ta bar gida da tarin kewar mutanen cikinsa.

Bata wani sha wahalar gane kan garin da kuma makarantar ba saboda Islaha Yayar Afeeya dake aure take kuma zaune a kasar ta London kuma makaranta daya suke karatu, ita ta nuna mata komai da ko ina kasancewarta me saurin fahimta in few days ta zama yar gari.

Unguwar da take zaune duk yawanci gidajen dalibai ne dukda akwai ma'aikata wasu single wasu kuma masu aure da suke zaune a gurin. Tayi Sa'ar samun makotanta biyu da suke jere da juna dukka musulmai ne dayar Bahaushiyace ma amma yar Ghana me suna Zuhaihat se kuma Darussalam Balarabiyar qasar Saudiyya da Allah ya hada jininsu haduwar farko kuma sukayi sa'a ashe course daya suke karanta. Darussalam ma Bazawara ce kamar Hamdah tana da Da guda daya Ashrab ta rabu da mijinta saboda yayi Ridda sakamakon wata baturiya daya fada soyayya da ita lokacin suna zaune ne a kasar Canada dalilin dayasa suka rabu kenan ta dakko danta ta dawo nan London take karatu tana kuma some part time Job. Kofar dake jingine da tata ta gefen hagu ce suka ce mata wani dan Nigeria ne a ciki amma ya dade baya garin kuma dai Landlord din ya ce musu be saki gidan ba har yanzu tsahon shekara biyu yana ci gaba da biyan kudi shi dinne dai Allah be sa ya dawo qasarba.

Karatunta takeyi bilhaqqi dan dama shi ya kaita, ta dade da siyan katon kwado ta garqame kofar zuciyarta dashi ta kumayi cilli dashi a tsakiyar Teku ta yanda babu wanda ze bincikoshi ballantana ya har ya qara yi mata kutse zuwa cikinta. Kasar ta London ta karbeta matuqa, tayi kyau na birgewa fatarta tamkar ta wani jariri sabuwar haihuwa tsabar laushi haka jikinta ya murje ta zama wata babbar mace ta kwatance.

Hamdah Ahmad Ammani Mace yar kimanin shekara 27 a yanzu ta amsa sunanta na qasaitacciyar Mace da take juya duniya a hannunta. Nata sirrin kyan shekaru ne suke qara fiddo dashi domin yanda jikinta ya qarasa cikewa a yanzu da kuma chanje chanjen da ta samu na halitta seya qara fito da ainihin kyawun sura da Fuskar da Allah yayi mata. Diri da kirar jikinta tamkar irin matan Ethopia da suka amsa sunansu Mata haka fuskart kamar Balarabiyar qasar sudan Amma ita fara ce tas koma ince Yellow.

Kwayar idanunta su suke qara mata kyau se kuma hakoranta da suke a jere kamar wadda aka sakawa a kanti, Tabbas Hamdah Me kyau ce tabarakalla masha Allah cikinta da wajenta kamar yadda Zuciyarta take me kyau, taskun rayuwa data shiga wani al'amari ne daga rabbil izzati da babu bawan daya zarce a jarrabashi. Kowanne dan adam da tasa kalar _Rubutacciyar Qaddarar_ sedai kawai ta wani tafi ta wani zafi kamar yadda Examination take a makarantu anan duniya sedai muyi fatan Allah ya hadamu da abinda zamu iya.

Watanninta biyu a London tuni ta zama yar gari, ranar Friday da wuri take fitowa daga school saboda presentation ne kawai sukeyi. Bayan ta fito ne ta biya ta super market tunowa da yau birthday din Ashrab yaron Darussalam dan haka ta shiga nemo masa abinda zata bashi as gift.

Hannunta riqe da manyan ledojin data ciko da tarkacen kayan wasan yara su motoci jirage da sauransu saboda tasab abinda Ashrab din yafi so kenan, dole seta tsallaka titi kafin

Please Login or Register in order to submit comment