Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tura mata maganin ta gani kaga ita ma zata qara taimaka mana da duk abinda ya dace. Seda suka biya gidan Afeeya da shekara daya data wuce ta Auri wani Abokin Abdulmalik din. Sun sameta tana jan Katon cikinta haihuwa ko yau ko gobe. Tausayinta ya kama Hamdah duk ta kumbura tayi baqi haka suka baro gidan lokacin har 11pm tayi.




🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

*RUBUTACCIYAR QADDARAH*

🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

*By Maryamah* 💞💞
©2020

*PAGE* 2⃣1⃣

Some days later.
Bayan sauraron sanarwa daga sarkin musulmi a safiyar ranar ta Juma'a aka tashi dashirin yin Idin karamar sallah. kamar kowanne gari kuma alada ta dukkan musulmi duk inda ka shiga zaka tarar ana girke girke saboda wannan biki mai girma haka take a gidan Abdulmaleek ma karfe 8:00am na safiyar ranar uwargida Hamdah ta gama shirya mijin nata cikin wani rantsatstsen yadi kalar coffee daya kara haska farar fatarsa, zaman hularsa kansa take gyara masa tana bashi wani labari wayarsa tayi kara alamar kira. Daga wayar yayi ya kara a kunnensa yana doka mata murmushi kamar wawa daga daya bangaren akace "To Tattabara kai muke jira" inji Umar. "Gani nan fitowa yaya" ya fada tareda kashewa wayar. Kaman yanda yake aladar su tare suke tafiya sallar idi gaba dayan mazan gidan in har kana Kano kuma anan Family house din suke haduwa ire iren wadannan abubuwan suke saka mutane ganin kamar kansu a hade yake dukda a bangaren mazan basu da wata matsala sosai. Cikin sauri yai pecking goshinta yana cewa "Babe labarin nan baze kare ba bari in muka dawo se a qarasa take care kinji" yai waje.

Kitchen ta koma inda twins ke tayata girke girken sallah. Kafin wani lokaci sun gama, ta zuzzuba na ko ina sannan suka kara gyara gidan tsaf sukayi mata sallama ita kuma tashiga wanka. Seda ta gama sille jikinta sosai sannan ta zauna ta shiga zana hadaddiyar kwalliya a kan fuskarta Wanda rabon da tayi irinta har ta manta. Cikin dinkunan dayayi mata na sallah ta dauko wata Gezner kalar Army green datasha swovriskey stones daga sama har qasa dinkin doguwar riga se walwali takeyi. Sosai ta fidda mata da shape dan rigar ta shawu sosai dukda ramar da tayi hakan be hana rigar zauna mata ba tayi kyau Kaman ka sace ka gudu. Daurin data san yana so tayi wato ture kaga tsiya ta saki dogon gashinta daya sauka har rabin bayanta. Seda tabi dukkanin ilahirin jikinta ta feshe da turaruka masu sanyi da dadin kamshi sannan da zura cogen takalmin daya dace da kwalliyarta. Babban palour ta fito dan tasan duk inda yake yanzu yana hanyar dawowa gida.

Tana kitchen tana qara goge Warmers din data zuba musu abinci tajiyo sallamar khalifa tareda abokanansa guda biyu. Seda ta yafa mayafin data dakko saboda hakan sannan ta fita har sun zazzauna. Seta kalleshi fuskarta dauke da murmushi tace "Oh su leefa yaushe a gari dawowa ba sanarwa" . Murmushin yakeyi shima yace "Wlh jiya na dawo da dare fa Mumcy take cemin kinzo baku dade da tafiya bama shiyasa yanzu ana sakkowa na taho kinsan I missed you is so much dinnan". " Kaji dashi" ta fada tana qoqarin mikewa bayan sun gaisa da friends din nasa.
Abinchi ta kawo musu da drinks suka kuwa zage suna ci suna yar hira jefi jefi yana mata labarin Cyprus in da yake karatu. Har suka gama cin Abincin Abdulmalik be dawoba Dan haka ta hadashi da abinchin su Mumcy harda na Maryam tace dan Allah ya biya ya kaimata.

sai kusan goma da rabi ya shiga gidan hakuri ya shiga bata kan dadewar wai sun biya gaishe gaishene Se santin kwalliyar tata yakeyi ita kuwa wani dadi takeji bakinta ya ki rufuwa. Bayan sun gama cin abincine yace ta dauko gyalenta su shiga cikin gida dukda bata so hakan ba Amma bata da zabi gudun kar ayimata abinda aka saba musamman yau da gidan yake cike da jama'a shiyasa ma ko abinci tundazu ta bawa Isma'il Babban Jikan gidan daya shigo gaisheta tace ya kai musu. A babban falo suka tarar da yawancinsu Banda Hamshakiya Hajia babba dan haka cikin girmamawa ta shiga gaida kowa. Ta dai samu amsawar kirki daga gurin sirikinnata da kuma sauran yayyan mijinnata maza sai Hajia Shuwa da ke mata sannu da aiki da cewa abinci yayi dadi daga nan ta wuce domin gaida surukar tata tun batayi sabin laifiba.

Tana zaune kaman yanda ta saba ta caba ado irin na manyan mata Gwala gwalai kaman zasuyi magana a jikinta, dama bata zaci amsawar gaisuwa daga daga Hajjan ba dan haka abin be wani dameta ba se kawai ta nemi gefe ta zauna, gajia tayi da zama gashi har lokacin be shigo ba yana can sun tsaya da su Ahmad Bestfriend dinsa daya zo se kawai ta mike da niyyar komawa gidanta daidai lokacin da Abdul da Ahmad se wani da bata san sunansa ba amma taga suna Yanayi da yan gidan suka shigo. "Zo ki kwashe gayyar tsiyar da kika kawo Dan ni baza'a shanyeni yanda aka shanyemin da ba" Hajja ta fada tana nuni da hadaddun food warmers din dake ajiye a gefe wanda ta zubo mata abinci da alama yanda aka ajiyesu haka suke ba'a taba ba. Seta kasa tsayawa dan ta fara gajia da irin wannan cin fuskar. Idan su mutanen gidan an gama zubda mata da kima a gabansu Ahmad fa da wannan bakon da bata ma san matsayinsa a gurinsu ba. Tana jin lokacin da take cewa "Oh ga yar iska tana miki magana kinyi gaba ko Idan uwarki Maryam ce zaki shareta ne ki wuce".

Duk yanda taso ta danne hawayenta ta gagara Dan haka tabarsu suka fara zarya akan fuskarta, ta kofar kitchen ta fita dan tafi mata saurin komawa part dinsu dan a lokacin bata burin ta hadu da kowa. Durkusawa yayi ya hada kayan cikin basket din da aka kawo su cikin sanyin jiki ya miki da niyyar binta "Ina zakaje shanyayye wato an jika an baka kasha duk ka susuce yar gwal na kuka ko shine ga bita zaizai zaka wani kwashi kaya ka bita a baya toh tayi kukan jini ma bana hawayeba Dan abinci dai bazanciba wanda akayi a bayama Allah ya tsare ehe". Dolensa ya koma ya zauna Amma zuciyarsa na gurinta gaba daya tana gurinta Allah Allah yake su gama gaisawa dasu Ahmad su fita amma kamar ta shiga ransa se cewa tayi ma akawo musu abinci ta tasa su dole se sunci.
A bangaren Hamdah kuwa kukanta tasha ta gode Allah dan abin ya zame mata jiki. Wayarta ta dakko ta shiga kiran yan uwa da abokan arziki tanayi musu bark da sallah. Wayar Afeeya takira tana dagawa cikin karadi tace mata "Uwar gidan Abdulmalik tun dazu nake trying wayarki bata shiga to ki taho ganin baby na haihu". Cike da karadi Afeeya ke maganar Dan haka tace mata "Toh uwar azakwai Nidai Allah ya kawo randa zan ganki a Labour room ko bakinki ze mutu haba ayi mutum da dan banzan surutu. "Wallahi dagaske nake nama tura miki pic din babyn tun jiya da daren nasan baki budeba shiyasa baki kiraniba".
Ai lokaci daya duk wata bacin rai da damuwarta ya bace, sosai take murna lokaci daya tausayin kanta ya kamata. Cikin clique dinsu su hudu Maryam nada yara biyu Ga Afeeya ma tayi daya haka nan Aysha ma tana hanya ko yau ko gobe ita ce dai shiru haryanzu, bata san lokaci da hawaye ya shiga zubo mata "Allah ya raya Afeee me kika rokamin da kina labour?" Ta tambayi Afeeya muryarta na rawa alaman san yin kuka. Sai kuma jikin Afeeya yayi sanyi, dukda basu tabayin wata magana akan haihuwa ba amma tasan dole ita ma tana so. Kokari tayi na ganin ta kwantar mata da hankali karshema ta janye hankalinta da wata hirar. Sanda ya shigo yaji dadin yanda ya sameta tana walwala cikin doki take nuna masa picture din yaron Afeeya me kyau dashi. Seya dafe kansa sannan yace "Afwan wallahi tun cikin dare Habib ya kirani suna aaibiti gaba daya ke kika mantar dani kin tuna". Seta rufe fuskarta ai kuwa ya shiga mata dariya kamar tababbe. Ce mata yayi ta bari da daddare zasuje, hakan kuwa akayi yana dawowa daga Sallar Isha suka tafi ganin babyn da har suka dawo tana santin babyn.


Kwanci tashi asarar me rai hakanan kwanakinmu suna ta karewa se gashi ana lissafin shekaru hudu da Auran Abdulmalik da Hamdah. A cikin shekarun zamu iya cewa babu abunda ya sauya tun shekaru biyu da suka gabata gidan aurannata dai se godiyar Allah. Cin mutunchi da wulakanci sedai in basuyi niyya ba a gurin wanda ya ajiyeta kadai take samun sauqi. Iya kacin kokari yan uwanta nayi dan ganin sun kwantar mata da hankali banda Yaya Baffa da yace shi sedai ma a raba auran baze zuba ido yana ji yana kallo yarinya qarama ta hadu da taskun Uwar miji ba. Abbah ne ya ke nuna masa da cewa kowacce mace da irin qalubaleb rayuwarta sannan in har sukayi haka sunyi Abdulmalik butulci. Iyakar qoqari yanayi akanta sautari yana ketare umarnin mahaifiyarsa akan farin cikinta dukda ita Hajja ita ce akan gaba kafin Hamdah a gurinsa dan haka su dai nasu su bita da Addu'a. Maryam aminiyarta data zamar mata tamkar yar uwa kusan kullum tana kan hanyar zuwa wurin ta kodan debe mata kewa kasancewar Yusuf ba mazauni bane uwa uba kuma Abdulmalik da bashida sauran sukuni indai ba yaganta cikin walwala ba.
A koda yaushe tana kokari gurin toshe duk wata ka fa datasan zata hadata da mutanen gidan ko Sabga indai ba suje tare su tafi ba bata zuwa hakan kuwa kullum qara wutar tsanarta a zuciyar Hajja da yan korarta yakeyi. Sosai ta mayarda hankalinta kan aikinta wanda a da ta jingine yanzu Shi yake debe mata kewa Dan koba komai inta fita tana samu tayi walwala da mutane.

Su hudu ne zaune cikin office din Malama Hadiza, Malama Ramlah, Malama Sa'adiya sai ita Hamdah magana suke tayi akan zaman takewar aure inda maganar duk akan Takurawa ce irin ta iyayen miji, labarai suketa kawo wa akan irin incidence din ita dai Hamdah nata ji gani dake Kaman da ita suke musamman lokacin da Sa'adiya take basu labarin wata makociyarta da uwar miji ta takura mata akan rashin haihuwa. "Ai kedai Hamdah ki godewa Allah da kika samu soyayyar dangin miji" cewar Ramlah. "Uhm" kawai ta iya cewa tareda murmushin yake Wanda akace yafi kuka ciwo Dan ita kadai tasan abinda yake damunta. "Yadai Malama Hamdah ni se nake ganin kaman kina cikin damuwa kuma bakiso ki sanar mana bayan anan dukkan mu babu wadda bata fadan matsalarta mukuma taya ta da shawarwari ko ba haka ba" cewar Hadiza "Kwarai kuwa wallahi nikaina na fahimci haka sedai nayi shiru ne tunda naga bata bukatar musani" Sa'adiya ta kara nata. Tasani dukkansu matane masu nutsuwa da sanin ya kamata Dan tun fara aikinta acikin department din kaf dasu kadai take hulda dukda dukkansu sun girme mata dan Malama Hadiza wacce suke kira da Anty ta kusa haifarta kuma Kaman yanda suka fada kowacce takan kawo matsalarta sukuma tayata warwarewa. zuciyarta ce ta bata shawara da ta gaya musu kilan ta samu mafita Dan haka cikin sanyin murya tashiga labarta musu salon zaman nata da surukannata.
"Tab dijan lallai Hamdah kina cikin damuwa Amma ba komai Allah daya hukunta faruwar komai yana sane dake" Ramlah ta fada bayan data janye tagumin da tayi "Kwarai kuwa toh Amma shin wai meyake damun mutanenmu ne wai me aka dauki haihuwa ne? shin a tunanin su a san kanka zaka ki kaso ka haihune? Kodan gujewa irin wadannan gorin ai kaima ka ajiye Dan kanka Amma ba komai ki ci gaba da godewa Allah akan duk abin da kikaga ya sameki a rayuwa, ki kuma dauki hakan a matsayin wata _*RUBUTACCIYAR KADDARAH _* da baki isa ki kauce mata ba. Idan kika yi hakuri se kiga Allah ya saka miki da rabo mai girma kidauka hakan duk cikin bauta ne wani izgilanci da wulakanci na mutane karya raunata miki zuciya ki kuma dage da kyautatawa mijinki tunda shi be kyamaceki ba ahakan".Kuka ne ya kwace mata Dan maganganun na Anty Hadiza sun shigeta tabbas gaskiya ta fada kuma zata kara dagewa akan adduar da takeyi Allah ya bata ikon cinye Wannan Jarrabawa. Har suka tashi suna jimanta wannan alamari tareda bata shawarwari dasuka kara karfafa mata gwuiwa ita dai aranta godewa Allah takeyi daya hadata zama da mutane dasuka san ciwon kansu da haka ta karasa gida.

Cikeda mamaki take kallon kofar part din nata da yake a bude, a iya saninta dai ta rufe ko ina da zata fita kuma bataga motar Abdulmalik ba alamar be dawo ba kenan, to kodai bada motar ya shigoba? Ta tambayi kanta, da wannan tunanin ta karasa cikin parlour sedai abinda ta gani ne yai bala'in daure mata kai. Matane zazzaune a falon sun baje abinci sunaci ko ina na falon yayi kaca kaca. kallonta takai kan kofar da zata sada ka da part din Abdulmalik din Wanda basu taba koda budeshi ba saboda da nata suke amfani wasu Maza maza ta gani suna fito da kwalaye datake tsammanin na kayan gado ne, bata karasa tsinkewa da Al'amarin ba seda taji daya daga cikinsu yana cewa "Hajia wannan fa dayan dakin baze dauki set ba sedai iya gado da Mirrow ne suka samu shiga". "Ba matsala Ina ce dai wancan Babban saitin dakin ya dauka ko?" Wata mace daga cikin matan me kama da kilaki ta bashi amsa. "Kwarai kuwa Hajia sema kin shiga dakin kin gani wallahi" shewa matan suka dauka gaba daya suna cewa "Se mu na gaske ba abinda za'a nunawa yarmu dai wallahi se farar fata da dogon hanci (niko nace ashe dai da abinda za'a nuna mukun😏).

Wani Jiri ne taji yana neman kada ita babu shiri ta nemi bango ta dafa, bata ko ganin gabanta ta nufi dakinta da sauri dan buri ta be wuce ta samu guri ta kwanta ba. Har ta shiga dakin ta nemi guri ta zauna cikin ta na wani irin hautsinawa kamar zatayi amai in banda kalmar "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" babu abinda take nanatwa. Addu'a take kar Allah yasa hasashenta ya zama gaskiya Dan kuwa in haka ne Ina zata saka kanta?. Maganar Mumcy ce ta fado mata a rai zuwan da tayi ranar Sunday inda take ce mata "Ashe kuma mijinki aure zeyi shine baki fadamin ba". "Haba dai kiji Mumcyn nan kilan dai mafarki kikayi Abbah yayo miki Amarya Amma badai niba " tabawa Mumcy amsa.Tausayin diyar ta tane ya kama dan da alama bata sani ba itama dai bata da tabbas kishin kishin taji a gurin Mamansu Maryam da take kawar Kanwar Hajia Shuwa kishiyar Babar Abdulmalik din. Se kawai ta barwa ranta maganar tunda taga alamar bata da masaniya akai Amma tasan tunda Har taji kishin kishin din abin to Akwai kanshin gaskiya a ciki.
Mikewa tsaye tayi cikin kidima tana qara tuna maganar da Sumayya ta fada mata wadda har fada tayi mata akan bata son irin haka karinga yiwa mutum fatan Alkahiri. Tunawa tayi lokacin da take ce mata "Nidai Anty Hamdah kome zaki fada sedai ki fada amma wallahi sekin tashi tsaye Dan wannan Hajia Hauwan da kike gani babu Allah aranta ko ita Hajja da kika ganinsu tare ba haka tabarta ba Dan haka inma zaki mike ki kwatarwa kanki yanci to tun da wuri kiyi in ba haka ba ina school zaki kirani ki bani labari" Hannunta ta dora akai ta fasa ihu iya karfi ta.

"Nashiga uku ni Hamdah Allah ka kawomin dauki, kishiyi? Ni Abdul zeyiwa kishiya. lallai yau nayarda Namiji bashida tabbas Namiji badan goyo bane Abdumalik ka cuceni" ta qarasa tana fashe da wani irin kuka me ban tausayi.



















🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

*RUBUTACCIYAR QADDARAH*

🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

*By Maryamah* 💞💞
©2020

*PAGE* 2⃣2⃣


A gurguje ya shigo gidan duk a kokarin sa nason yarigata komawa dan shi dai kwakwalwar sa tagama kullewa tunda Hajja ta kirashi wai yau masu jeren Amarya zasuzo. Bai yarda da gaske take ba se a lokacin da Usman ya kirashi wai ga wasu mutane Hajja tace a bude musu gidab zasu zuba kaya kuma dai ba yan uwan Anty Hamdah bane. Wannan wace irin rayuwa ce ace wai namiji za'ayiwa auran dole wai shi wane irin iyaye Allah ya bashi ne? Shi dama Alhaji Ba'a maganarsa Dan tunda magana ce ta kudi tuni an wuce gurin a bangarensa. Wani irin buguwa zuciyarsa tayi ganin motarta ajiye a harabar gidan yasan yau karyarsa ta kare bashida wata kalmar daze iya kare kansa a gurin Hamdah. Se yau yake Dana sanin boye mata da yayi tunda farko daya sanar da ita abinda yake faruwa kilan da abin yazo masa da sauki.

Be ko bi takan matan dake palour ba duk da yanda suka shiga tsokanarsa wai ga Ango. Shidai ya dade bega marasa zuciya irinsu ba, har gida yaje ya kaftawa Ita Amaryar da uwarta warning akansa amma basuji ba to zega ubanda ze shigo masa da ita cikin gida a matsayin mata. Badan akwai abinda yafisu muhimmanci a gurinsa yanzu ba da babu abinda ze hanashi tsayawa ya musu rashin mutunchi se sun kwashe duk abinda suka kawo. A corridor suka ci karo da ita tana kokarin fitowa shi kuma ze shiga yanayinta kadai ya tabbatar masa da cewa aikin gama ya gama. Da dakyar ya lalubo miyau ya jika makoshinsa sannan ya nufeta da niyyar yarike ya lallasheta yanda ya saba amma ina yau kam ya makaro. Cikin wani irin zafin nama taja da baya tana masa mugun kallo har lokacin hawaye basu dena fita daga idonta ba. Kara kusantarta yayi cikin muryar tsawa ta dakatar dashi "Don't you dare lay your filthy hands on my body". Se ya tsaya cak zuciyar sa tashiga double flipping, wani irin tashin hankali da fitina ya hango a cikin kwayar idanunta Wanda be taba saninta dasu ba. Yasan za'ayi haka se yayi saurin ja da baya ya sakawa kofar key tayanda ba yanda zata iya fita sannan ya nufota cikin kasa da murya yace "Please Hamdah kisaurareni kiji wallahi ki yarda bansan komai akan maganar auran nan ba yanda kika gansu nima haka nagansu......" "Kai dallah rufe min baki munafukin Allah ni zaka yaudara da roman baki? To wanda kayu a baya ma Allah ya sakamin a tunaninka har Akwai wata kalma taka da zata kuma yin tasiri akaina ne? Never" Ta katseshi.

Ko kadan beji haushin maganar ta ba dan yasan he deserve morethan that kokarin sa kawai ya isa gareta ya rike ta ajikinsa ya rarrasheta Amma taki bashi damar hakan. Gaba daya ta birkice masa ta tashi daga Hamdah daya sani takoma wata daban, jifan sa ta shigayi da duk abinda yazo hannunta bakinta be gaji da fadin Allah ya saka mata ba abinda yake qara dugunzuma hankalinsa kenan dan yasan tabbas ya zalinceta. Hamdah nada zafin kishi amma tana da fahimta. Bakowacce mace bace zata iya saurararka a wannan yanayi dan haka kawai ya kai zuciyarsa nesa yana jin yanda take jifansa da kalmomin da ya tabbatar in a hayyacinta take bazata kirashi ko da makamantansu ba. Kokarinta kawai ta kai ga kofa ta fita Dan Ta rantse bata kara kwana cikin gidansa. Dambe suka shiga yi ganin zata bata masa lokaci yasa mata karfi ya riqeta kam a jikinsa sedai fa a banza dan ayau duk wata dabara tasa da wani salo baiyi tasiri akan ta ba dan taki responding in banda duka da yakushi ba abinda take kai masa tana kuka kamar ranta zefita."Ka sakeni Abdul ko in kashe ka in kuma kashe kaina".
Babu shiri ya saketa ta zube a gurin tana ci gaba da kukan. "Nace maka ka budeni na tafi wallahi gidan mu zani na gama auranka" ta qara fada cikin muryarta data dashe tsabar kuka. Gefen gadon ya zauna ya rike kansa dake barazanar tarwatsewa, wannan shi ake kira da goma da ashirin wai shin Ina ze saka kansa? Yabarta ta tafi gida tace me? Kawai ta dawo ta tarar ana jerwa Amarya kaya acikin gidanta? Me yan uwanta zasu daukeshi ya gaza sauke amanar daya karba kenan.
Kallonta yayi yanda ta hada kai da guiwa tana kuka mai ban tausayi, tabbas yasan be kyauta mata ba Amma yaya zeyi? Haka nan ko a tunani be taba kawo zuwan irin wannan rana a cikin rayuwarsu ba Amma yaya zeyi da *_RUBUTACCIYAR KADDARAH_*? Wayarsa dake aljihuce ta shiga ringing amma ya shareta dan ayanzu bayajin ze iya magana da kowa ganin me kiran ya nace ya sakashi zaro wayar abin haushima unknown number ne dan haka ya danna kawai ya dora akunnansa batareda yayi magana ba

"Hello dear ya zakayimin haka Dan Allah gashi ance ko kayan dakinma basu gama samun guri ba bayan ita Matar ka dakuna nawa ne da ita agidan da ni zaka bani wannan Dan akurkin meyasa bazaka sakani a upstairs din ba aini Amarya ce.." Wani tuquqin bakin ciki ne ya taso masa, wato duk kashedin daya mata be shiga kunnenta ba kenan shine zata kirashi. "Se kizo ki fitar da ita ai kisaka naki kayan Idan ubanki ne ya gina min gidan mahaukaciya kawai" kit ya kashe wayar tareda yin cilli da ita ta fashe.

Sororo tayi da waya a hannu Hajia Hauwa dake gefenta kuma duk taji maganar tasa tayi saurin tareta da cewa "Karki damu kidai bari a daura daga shi har Matar tasa se sunyi bayani Dan bakida bukatar wata mai aiki ita kadaima ta isheki shiyas nace mubarta a gidan kar a fidda ita daganan kinga bakin ciki seya yi ajalinta.
"Amma Momy kina ganin abun nan ze yuwu kuwa kiga fa uban aikin da akayi akan mutumin nan amma kullum kamar dada ingizashi akeyi" ta tambayi uwar tata. "Kiji ki da shirme in aiki be ci shi ba ai yaci Uwarsa ko bagashi ta daga hankali an saka lokaci ba, ai takanta zamubi tunda yaba mata biyayya ayita ingizata tana sakashi yayi ita kuma kinsanni zan iya yin komai Dan ganin nasiyo miki mutunchi a gidan aure" shewa suka dauka kamar wasu kawaye daga nan suka cigaba da shirye shiryensu.
****************************

Duk yanda Abdulmalik yayi zaton lamarin nata ya zarce haka Dan yanda sukaga rana haka suka ga dare a gidan haka nan suka kwana tana surfa masa tsiya duk kuwa da irin nasiha da fadan da Mumcy da Abbah suka ringa mata ta waya sannan suka ce ahir dinta suga qafarta a gida. Tayi kuka har ta gaji tayi alqawarin shida zaman lafiya kuwa sedai a labari haka ta ringa caza masa kwakwalwa hatta da gadon da ze kwanta yayi bacci ruwa ta debo bokiti guda ta juye masa aka yana kwance, dole ya koma cikin mota yabarta bayan ya kulleta ta waje.

Bayan ya dawo daga masallaci ya lallaba ya shiga gidan, tana kwance daidai kofar idanuwanta sunyi fada ta rame lokaci daya. Kokarin dagata ya shigayi a hankali dan karya tasheta sedai ya makara karaf ta bude ido ta kalleshi. Bude baki tayi daniyyar yi masa rashin kunyar data saba yai saurin matse mata bakin yana aro duk wata jarumtarsa ya bata fuskafa. " Wallahi kika kuskura kikamin shirme sekinga abinda zanyi miki ke bar wannan ma kika qara magana ban yafe ba". Se kawai ta saki kuka, muguntar har ta kai haka ya cuceta ya kuma hadata da Allah. Har suka isa toilet ya direta sannan ya shiga hada mata ruwan wanka. "Kiyi maza kiyi wanka ki yo alwala na baki minti goma ki qara akan hakan ki gani" ya fada fuskarsa babu alamar wasa. Haka tayi wankan ta fito tana sallah tana kuka a wurin sujjadar karshe kuwa tafi minti goma yanajin yanda shashsheqarta take qara karfi, hankalinsa ya qara tashi kardai Yarinyar nan qararsa take kaiwa Allah? Se ya mike ya isa inda take, cikin wata raunanniyar murya yace "Hamdah dan girman Allah kiyi hakuri abun zeyimin yawa in kika kaini gaban Allah. Ki bani dana na kare kaina Dan Allah". Durqusawa yayi a gabanta tamkar me neman gafara. Harta Sallame sallarta ta

Please Login or Register in order to submit comment