Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ninke sallayar ko kallon inda yake batayi ba. Bude baki yayi da niyyar sake magana yaji ana dukan kofa kΓ mar za'a karyata.

Hajja ce ta doko musu uban sammako Dan tun a daren jiya Hajia Hauwa ta shaida mata abinda Abdul din yayi da karin gishirin yan jere. Jin bugun bana hankali ba ya sakashi fita ya bude kofar yana addu'ar Allah yasa wanda ze iya duka ne.
"Toh shanyayye wato Har ka isa in kiraka a waya kaki dagawa sannan kazo ma kaji dalilin kiran ban isa ba koh, kai har kayi tsaurin idon da zaka cewa Haula bada kudin ubanta ka Gina gida ba to ita wannan kodaddiyar data barbaza kayanta a ko ina nawa nata uban ya baka lokacin da kake ginin eye to wallahi ka fita daga idona in rufe tun wuri Idan ba baki kake so in maka ba toh kashiga hankalinka tunda wuri kasanni sarai". Bakinta har kumfa yake tsabar bala'i. Wani irin suya ranta yakeyi tana kara tsanar Hamdah a kowacce dakika. Cikin palour ta shiga tana karewa ko ina kallo dan bata san sanda aka qara gyarashi ba ko nata Albarka, seta tabe baki sannan tace "Ina ita isashshiyar sabuwar uwar taka take.."

"Gani nan dena bata bakinki kina daga murya Hajja ki kuma kwantar da hankalinki base kinyi wa dan ki baki ba dan ke zakiyi asara yanzu zaki ga filin gidan nan dan zan bar masa abinsa in yaso ki auro masa Haula da uwarta da wadannan kannen nata guda biyu su cike masa hudubi". Se ta bude baki cike da mamaki tana kallonta, yanda take gaya mata Magana kai tsaye batareda tsoro ko shakka ba kamar ba wannan surukar tata ba me mata biyayya tamkar zata bauta masa. A bangarenshi kuwa beyi wani mamaki ba Dan dama yasan irin wannan ranar na nan tafe kuma ya kwana da sanin halin mutuniyar tasa. Lokaci da yawa har mamaki yake ina tsiwa da rashin kunyar ta suka tafi take bari suna takata a gidan. Abu daya ne ya daure masa kai d jin cewa wai ita Hajja ce zatayi asara kuma ita gidansu zata tafi to kodai Hamdah tadena sonsa ne?

Innalillahi ya shiga nanatawa a cikin ransa in kuwa haka ta kasance ya jefa rayuwarsa a Ina? Ta ina ma ze fara rayuwa babu ita? Ba shiri ya nufeta cikin tashin hankali dan se lokacin yaga akwatin da take ja, se ya riko hannunta cikin di mauta ya ce "Ki taimakeni Hamdah karki tafi wallahi kece rayuwata saboda ke nake numfashi a doron kasa. Barinki gidana tamkar barin numfashine daga gangar jikina kiyimin rai karki rabu dani". Duk yanda zuciyarta tayi rauni amma seta dake taqi koda kallon bangaren da yake. " Hamdah mutuwa zanyi wallahi in kika tafi" seta kalleshi da sauri zuciyarta cike da son sa da kaunarsa ga kuma kishinsa dake azalzalar ta duk a lokaci daya. Taci alwashin daga masa hankali ko kadan bata so yaga gazawarta Dan haka ta dauke kanta kawai tayi waje tana share kwallar dake zubo mata shima ya rufa mata baya yanajin yanda Hajja ke kwada masa tana dura masa duk ashar din data zo bakinta. Tun lokacin da suka fara drama ta zama hoto mamaki ya kusan kasheta wai dama wannan yarinyar tana magana, wato ta aura masa uwar Haula ma ba Haulan lallai seta tashi tsaye akanta taga alama ba gurin karamin boka suka kai mata Da ba acewarta gurin masu shan jini aka kai shi.


Sanda ya fita tuni tayiwa motar ta key me gadi ya wangale mata Gate se kawai ya shiga gidan da sauri ya dakko mukulli batare da ya tanka Hajja dake karamin hauka ba tana buge bugen waya ko ita da waye oho.

A kusan tare suka shiga gidan tana fita ya bita suka tasa tsere tana Kuka kamar wacce akacewa Mumcy ta mutu a haka tashiga palour yana take mata baya. A tsaye ta tarar da Mumcy da jaka a hannunta alamar fita zatayi se yaya Farouk dake gyara zaman hularsa shima batayi wata wata ba ta fada jikin Mumcy tareda fashewa da sabon kuka gaba daya seta kashe mata jiki har bata san lokacin da hawayen suka fara sauko mata ba itama ta shiga cewa "Kiyi shiru Hamdah na Dan Allah kiyi hakuri babu wanda ze miki dole in har ina raye". Seya sunkuyar da kansa wata irin kunyar matar ta kamshi, ji yayi Kaman an daure masa jijiyoyin jikinsa ganin Ya da uwar suna kuka ashe har cutarwar tayi yawan da ta shafi Mumcy itama? Ya tambayi kansa. Amsar a bayyane take sanin irin tarin kaunar dake tsakaninsu Dan ze iya cewa kaf yayanta tafi son Hamdah. Shi kansa Yaya Farouk jikinsa ne yayi sanyi ganin hawayen mahaifiyar tasu gaba daya sukayi zugum zugum suna kallonsu. Abbah dake sakkowa palour ne ya shiga cewa "Ashsha Ashsha Maryam menene haka kuma Dan Allah in baki rarrashi yarinyar nan ba kuma seki tayata kuyi tayi haka akeyi". Janyeta yayi daga jikin ta yashiga Dan bubbuga bayanta Kaman yana rarrashin jaririya har tayi shiru se ajiyar zuciya da take saukewa. "Yanzu kuma me ya kawoku da sassafiyar nan muma yanzu shirin zuwa gidan naku mukeyi" ya fada yana kallon saitin Abdulmalik daya kejin kamar ya nutse a cikin palour tsabar kunya alamar dashi yake. Seya duburburce ya shiga inda inda yama rasa ta Ina ze fara magana ganin yana neman bata masa lokaci ya sakashi cewa "Ok ya isa kasan halin mata akan zancen kishiya dole seka yi hakuri sannan komai ze daidaita tashi ka dauki Matar ka ku wuce Allah yayi muku albarka Allah kuma ya baka ikon yin adalci a tsakaninsu". Ai tuni ta daka tsallen albarka tace "wallahi ba inda zataje" ran Abbah ne ya baci ya daka mata tsawa "Are you that stupid Ina miki magana kina gayamin bazaki je ba ke kika haifi kanki ko mu muka haife ki?" Duk da wannan tsawar bata sa ta dena kukan se ma mikewa da tayi ta nufi dakin Mumcy da gudu tana fadin "Wallahi bazan bishiba yaje can ya auri wacce suke so ta haifar masu yayan". Tana jin yanda Farouk yake Bambami yana seya ballata Abban zatayiwa rashin kunya saboda ita bata da mutunchi ita dai ta qule a daki ta musu banza.

Hakuri Abbah ya shiga bawa Abdulmalik " Kayi hakuri kasan dan yau ne ka haifeshi baka haifi halinsa ba amma ina zuwa insha Allahu zata bika ku tafi yanzu ba se anjima b". Baze iya masa musu ba, wata irin kima da darajar tsohon ta qara ninkuwa a idonsa. Ya tabbatar da cewa shine mara gaskiya amma hakan besa sun goyi bayan yar su ba to shi kuwa in ya wulaqanta yarinyar nan yacewa Allah me? Se kawai ya mike ya kasa hada ido da ko daya daga cikin su yace "Aa Abba kabarta zuwa anjima insha Allah in ta huce sena dawo" yai azamar fita daga gidan dan shidai da kunya kuma ya zauna musu. Tunanin mafita yakeyi har ya qarasa gida ya tarar da Hajja ta tafi se wasu mata daya gani da sunan wai sun zo qarasa gyaran daki. Tijarar da shi kansa besan ya iya irinta ba ya zazzaga musu ya rantse in har ya fito ya tarar sa ko kurar motarsu a layin seya sa yan sanda sun kama su dan haka suka shafawa kansu ruwan sanyi suka tafi dan sun san tsaf ze aikata abinda ya fada. Seda ya bame qofofinsa dukka sannan ya fita yasan ko yaje office bashida nutsuwar aiwatar da komai dan haka ya juya kan motarsa ya tafi gidan Yusuf dan yasan yana gari.



🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

*RUBUTACCIYAR QADDARAH*

🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

*By Maryamah* πŸ’žπŸ’ž
Β©2020

*PAGE* 2⃣3⃣

Cikin Hikima Mumcy ta ringa fahimtar da ita rayuwa da abinda yake cikinta. "Ki gaya min gaskiya kina son mijinki ko Aa" mumcy ta tambayeta. "Ina sonsa Amma....." Seta yi saurin katseta "Babu maganar Amma dama abinda nake so naji kenan har yanzu kina sonsa dan haka tashi kije ki bawa Abban ku hakuri kizo kinji Hamdahna". Jiki a sanyaye ta shiga bedroom din Abban yana zaune idonsa da farin glass yana duba littafin Sahih Muslim. Gefe ta samu ta zauna kanta a qasa murya na rawa alamar son fashewa da kuka tace " Abba kayi hakuri dan Allah". Seda ya cire glass din idonsa ya kalleta fuskarsa dauke da murmushi yai mata alamar data zo, seta fada jikinsa lokaci daya ta sake fashewa da kuka. Be hana ta ba seda tayi me isarta ta gode Allah sannan ya fara mata Magana. "Mamana bansan lokacin da kika baci da taurin kai ba duk ina tarin hakurin nan da kike dashi? Kin manta hakuri da rashinsa banbancin dan taqi karamine. Duk inda akaje aka dawo in kikayi hakurinnan zaku zama daya kinji wuyarta daya yayi auran". " Abba niba auransa ne ya dameni ba meya sa ze boyemin tun farko be gayamin ba ai bazan hanashi ba amma Abba baka ga irin wulaqancin da yan gidan sukeyi min ba Abba cewa suke fa wai ni Juya ce bana haihuwa kuma wai ma Ni Mayya ce na lashe masa kurwa".

"Inji waye tace miki Mayya" ya tambayeta. "Hajja ce harda ma kannensa su Zainab da Khausar". Se yai murmushi irin nasu na manya sannan yace " Ina raye bazan taba bari ki wulaqanta ba kuma duk wadda ta qara hadaki da maita sena dauki mummunan mataki akanta mark my words, yanzu kiyi hakuri ki duba irin kaunar daya ke miki ki koma kinji mu kuma insha Allah zamu tsaya matuka ganin baki wulaqanta ba bi jahi rasulillah kema zaki haihu, se kin haifi dan da Duniya dukka zatayi alfahari dashi bama iya mu kadai ba". Da haka yai tai mata Nasiha har zuciyarta tai sanyi, zuwan Zahra da Hamida da yanzu take ABU zaria ya sa ta koma Dakin Mumcy suka hadu suka ci gaba da kwantar mata da Hankali. Kalamansu sun kashe mata jiki tareda raunatar mata da zuciya. "Waini in banda sakarcin irin nata ma tayaya zaki bari makiyanki su ci galaba akanki har ma suga gazawarki? Yanzu da kike ikirarin barin gidan wa kika yiwa kanki fa kin rasa miji me sonki tsakani da Allah su kuma burinsu ya cika. Dan Allah ki nutsu ki koma cikin hankalinki kidubi irin halin da kika saka kanki da mijinki a ciki kiyi hakuri ki fawwalawa Allah komai duk abunda ba'a ginashi a tafarki gaskiyaba ba inda zeje Insha Allahu bazaki tabe ba". Haka suka ci gaba dayi mata nasihohi tareda shawarwari, Anty Zahra ce ta kirashi akan ya barta tadan kwana biyu a gida ko zata qara nutsuwa sukuma sukayi amfani da wannan damar gurin yi mata duk wasu shirye shirye daya kamata. A kullum tunanin ta be wuce yadda zata iya Raba Abdulmalik da wata mace ba, ita bata san ya zatayiba ranar tanaga hadiyar zuciya kawai zatayi da dai ta jure ganin Abdul tare da wata a matsayin matarsa amma tayi matuqar dauriya wurin nuna komai ya wuce kodan ta kwantarwa da Yan uwanta Hankali.

Kwananta uku a gidan ta koma, yayi matuqar mamakin ganinta da chanzawar ta lokaci daya. Sosai ya ke godewa Allah da samun surukai masu karamci da sanin ya kamata. Sababbin furnitures yan ubansu Yaya Abubakar, Yaya Baffa da Yah Farouk suka mata gado uku kowanne daki da set din Kujeru Biyu Royal da Leather. Haka kayan kitchen dinta ko cokali Mumcy batabar mata tsohoba seda a ka canza harda Kitchen cabinet din kuwa sega gida ya qara fitowa ras jerenta har yafi na Amarya yar Governor kyau da suke ganin sun qure mata qarshen gata. Duk wannan budurin ita ko a jikinta dan ba wai sun birgeta ba ne ta dai sakawa ranta bazata qara shiga sabgarsa a gidan ba.

A bangaren su Hajia Hauwa kuwa Hankalinsu ya kwanta Da jin bata gidan azatonsu aikinsu ne yaci nan fa suka daura sabuwar damarar janyo hankalin Abdul din ya koma kan Haula gaba daya dan tuni sun gama da bangaren Hajja kamar Tv da remote haka suke sarrafata. Sun samu kanta ba kadan ba kamar Bawa da Ubangidansa haka take musu biyayya. Uwar gida Hamdah kuwa Shawarwari da nasihu daga yan uwa da abokan arziki tareda Addu'a data yawaita su suka taimaka wa zuciyarta wurin samun nutsuwa, ta mika lamarinta ga Allah tayar da wannan din ma wata *KADDARAH* ce *RUBUTACCIYA* cikin kundin rayuwarta zata kuma rungumeta hannu bibbiyu, a kullum rokonta be wuce Allah daya bata ikon cinye wannan Jarrabawa ya dora mata.
Lamarin Abdulmalik kuwa yanzu se addu'a dan itace ma me tausarshi akan abun. Ya zama kamar wani zautacce, ya rantse ya kuma rantsewa akan bazeyi wannan aure ba ita kuma Hajja ta gindaya tata rantsuwar akan in be auri Haula ba to sedai ta tsine masa yabi duniyar kowa ya huta. Tun abun nawa Alhaji dadi har ya koma bashi tsoro, duk yanda ze bi yasa ta hakura takafe dan har Yayyenya ya je Har Maidugurin da yake ganin sun isa da ita amma ta shafewa idonta toka tace a rabu da ita ai Dan tane bana wani ba. To se muce Allah ya daidaita wannan al'amari haka.
Some weeks later.

Tsaye take cikin kitchen hannunta na hagu rike da ludayi tana juya miyar da ke soyuwa a kan Gas inda dayan hannun daman ke rike da waya magana takeyi cikin nishadin da ta dade rabonta da irinsa. "Kai leefa baza dai ka chanza hali Ba wai ma gaba dayanka nawa kake ne na rantse wannan matar seta goyamu ta zagaye Kano kaf bata gaji ba ta fada tana shekewa da dariya in ta tuna da pictur daya turo mata na wata gandamemiyar mata wai a matsayin budurwarsa. Sun dauki lokaci sosai suna magana da kanin nata kafin sukayi sallama.Tsaf ta gyara duk inda ta bata sannan ta kara goge kan dining din, har zata wuce ta hango farin katon envelop din da Ahmad ya kawo dazu da safe ya ajiye kan centre table seta dawo da baya ta dauka. Katinan daurin aurene masu kyau an rubuta _ABDULMALIK AND HAULAT_ akai ga ranar Daurin aurenan wannan Asabar din me zuwa. Tabe bakinta tayi sannan ta ajiye Dan ita yanzu shirgin daya kwaso suma ba kallonshi takeyiba sedai ko me ta tuna oho ta dawo da sauri, zazzage katinan tayi ta ware wadanda take da tabbacin na Amaryar ne dan kalar su daban tashiga kitchen dasu, ta kofar bata ta fita bayan ta yayyafa musu kalanzir yanda zasu fi ci dakyau sannan ta qyaata musu ashana take suka kama da wuta bata bar gurinba seda ta tabbatar sun cinye tsaf sannan ta kwararawa tokar ruwa karma a samu koda irin barbadinsu tayi gaba abinta.

Sai bayan magriba suka shigo gidan shida Amininsa Ahmad, daurewa kawai yake wani irin azabar ciwo kansa yakeyi Kaman ze rabe gida biyu. Yanzun ma daga gurin Hajja yake duk akan dai maganar auran acan ya tarar da wannan gantalalliyar tsabar rashin kamun kai wai tazo gurinsa karbar invitation cards. Ahmad ne yace masa ya bugo su tunda safe ya kawo su gidan bayan ya dibi wadanda ze rabawa abokansu, badan yana tsoron bakin Hajja ba da ya gaya mata abinda zesa kota titin unguwar bazata qara sha'awar biyo wa ba. Haka suka bincike katinan tsaf amma babu alamar na Amarya se tulin na daurin aure kawai aka bari. Mamaki ne ya kama Ahamd da hannunsa ya ajiye katinnan fa ba wani ya aiko ba "Wallahi tare na karbo su gaba daya anan kagani na ajiye su dukka tare harda ma Gate pass na dinner data cemin a bugo". Be ko tankashiba ya nemi guri ya zauna yana jin yadda yake dada jaddada masa akan shifa ya kawo.
Takun takalmin uwar gida ne ya maida Hankalinsu gareta Tayi kyau Harta gaji cikin Maroon din atamfar data saka tun kafin ta karaso kamshinta yai musu sallama. Cike da kissa ta qarasa jikinsa ta rungumeshi tana masa sannu dazuwa se ya saki baki dan rabonda tayi masa hakan tun suna zaman dadi. Harar Ahmad daya dauke kansa gefe tayi a ranta tace " Munafuki dukda hadin bakinka ai". Se seda ya Dan janyeta sannan yace "Babe kinga wasu cards a nan kuwa?" Wata hararar ta kuma ballawa Ahmad sannan tace "To Jaan ni ka bani ajiya ne ko da aka kawo ni aka bawa". shidai Ahmad Murmushi kawai yayi dan yanzu tsoron lamarinta sukeyi tunda tayi musu bore se kawai yace "Kaga Abdul bari naje kawai na bada a buga wasu tunkan Hajja ta kara hura mana wata wutar" yai waje abinsa.
Abinci ta takura masa yaci Dan har ga Allah yanzu tana dan jin tausayinsa kadan gaba daya ya lalace ya fita hayyacinsa, gurin mayarda plates yaci karo da tokar cards din acikin sink murmushi yayi dan ko kadan abin be bata masa raiba saima dariya da salon kishin nata ya bashi.
*********************************

A kwance suke sedai ba bacci suke ba kowanne da kalar tunanin da yakeyi a zuciyarsa kara. Juyi tayi ta qara shigewa jikinsa tana qara matseshi ajikinta ta rasa dalilin dayasa akwanakin nan take tsintar kanta cikin faduwar gaba sosai musamman yau daya rage yan awanni yazama nasu su biyu, zuciyarta takan raya mata kamar zata rasa shi, gani take kamar Haula zata kwace mata Abdul dinta gaba daya. Tayi nisa acikin tunaninta ya kira sunanta cikin wata irin murya
"*AISHA*...." ya kira sunanta, Se ta dago da sauri ta kalleshi. Tunda take dashi be taba kiranta da Aisha ba wanda shine Ainihin sunanta da Dangin Maman Abba ne kawai suke kiranta dashi saboda sunan Kakarsu ne ta bangaren uba se wasu yan tsirarun mutane kamar Dr Guru sunan ya fado mata a zuciya, setayi surin kauda tunaninsa ta koma kan kiran da Abdul yai mata dab ita tsakani da Allah har mantawa take da sunanta kenan tunda ko a makaranta badashi take amfabi ba. Bugun zuciyarsa ne ya karu ga wani zafi da takeyi masa ya rasa abinda yasaka ya tsani wannan kallababben auran kwata kwata abin be kwanta masa a rai ba dai dai da minti daya Amma gashi Hajja taqi gane hakan, Karmar zata tsine masa yazamar mata jiki ayanzu.
"Please Aisha karki gujeni komai wahala kinji koda kuwa ina cikin halin hauka ne nasan ke kadai zaki iya zama dani" se ya fashe da kuka. Tsoro ma ya bata ita dan haka kawai ta saka masa kukan suka shigayi tare babu me rarrashin wani har seda bacci ya daukesu sannan sukayi shiru.

Shagalin biki ya kama gadan gadan tun daga ranar litinin har zuwa yau Alhamis ana kudi yaga tasku. Tun da suka fara wunin gidan ya gagareta saboda ba kaken maganganun da ake yaba mata har cikin dakinta suke biyota Mama Shuwa kadai ke kokarin kwantar mata da Hankali dan ma a wannan karon tadan samu goyon bayan Megidan dan dakansa ya shiga yake ce mata tayi hakuri. Shikansa uban gayyar yanzu seta wuni bata sakashi a idonta ba ita dai ta wa kanta alkawari bazata kara tayarwa da kowa hankali ba tasani hakuri baya taba faduwa banza Dan haka tacigaba da kaiwa Allah kukanta a koda yaushe. Ranar Juma'a sukayi wunin gidan Ango anan cikin gidanta, dafarko taso ta qi yarda amma Mumcy ta gargadeta akan tayi shiru anayi ne dan a tsokaneta ta tura musu aniyarasu ta barsu kawai, bangaren nata cike yake da faccalolin ta dakuma kannen Abdul din dasuke shiri haka yan uwanta da kawayenta da abokan aiki sun mata kara kwarai duk sunzo tayata wunin. Ba karamin kokari tayi ba gurin danne duk wani kishi da bacin ranta ta kure kwalliya cikin lace dan ubansu fuskar nan tasha make up tayi kyau qwarai dama me kyan ce abinda ya kara bakantawa yan korar Hajja su Kausar kenan Dan duk abinda akeyi anyine Dan a bata mata kuma gashi bata nuna hakan ba ko a kafarta ba.

Suna zaune a Babban falon ana ta hira wasu na tsokanarta akan ta basu sirrin wannan jarumtar datayi sedai tayi yake kawai tace "Ku bari se layi yazo kanku tukunnan se in gaya muku". "Aa ba Amin ba kibar shi kawai" suka hada baki gurin fada. Zainab ce da Kausar se Anty Khadija babbar yar Hajja suka fado dakin Kaman an harbo su
"Ke annamimiya mumafuka dangin mayu to wallahi tun wuri ki sakar mana kurwar dan uwa wato mun kwatoshi dakyar muna neman rabashi da wahala anje an qara yo binne binne ana neman kara mayar da shi ruwa ko to baki isaba ki tashi duk ma inda kika boyeshi ya fito Dan yau ba fashi se yaje dinner". Gaba daya matan dake dakin suka bisu da kallo batareda sun tanka suba. Khausar da ke tashen fitsara ta karasa kan Hamdah tareda ture mata dan kwalin daya kafu akan ta tace "Wato ga yan iska muna miki magana kin mana banza ko......" ai bata ida karasawa ba saboda marin data dauketa dashi, bata bari sun dawo daga mamaki ta shiga nunasu tareda yi masu kallon tsana tace "Tun daga kanki Khadija har zuwa ke karamar mara kunya (tana nufin khausar) ba wacce zan sake ragawa daidai nake da kowaccenku yar iska Dan shiru shiru ba wai tsoro bane Abdul kuma se kuje ku nemeshi Dan in naso hanashi auren nan da baku zo nan kuna babatun banza ba Dan haka kar wadda takuma gigin tako kafarta zuwa dakina in dai ba akhairi ya kawo ta ba in kuma ba haka ba wallahi sena aikata mata abinda batayi tsammaniba ko wace ce ita kuwa". Ai ba girma ba arziki suka bar gurin suna kumfar bakin bazasu yarda ba. Aysha ce matar Abubakar ta raka su da tsaki sannan tace "karyar banza daku tsaya mana in ba tsoroba wallahi kin birgeni da kinsan zaki iya hakan kika barsu suna taka ki son ransu".
Ko da suka fadawa Hajja surutan banzan ta tayi ta gama sedai batayi gigin zuwa ba Dan yanzu itama ta fara shakkar surukar tata abu daya dai wannan aure ba fashi dukda ita kanta halin da Dan nata yake ciki yana damunta Amma ji takeyi Kaman zata mutu idan baayi wannan aure ba.



🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

*RUBUTACCIYAR QADDARAH*

🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

*By Maryamah* πŸ’žπŸ’ž
Β©2020

*PAGE* 2⃣4⃣

Safiyar Asabar.
Tunda garin Allah ya waye take fama dashi akan ya tashi ya shirya saboda zuwa daurin aure, tanayin hakan ne kawai saboda cika umarnin Abbah daya kirata jiya da daddare yake ya ba mata akan qoqarin da tayi akayi yinin bikin lafiya ba tareda wani rikici ba. Sannan ya qara da cewa tayi qoqari ta sakashi yaje gurin daurin auran in ba dan haka ba taso ta nunawa su Hajja iyakarsu, zata qunshe shi a daki su zauna ko iya wannan ta baqantawa Amarya rai ace ko daurin aure ango be halarta ba. Ko jiya da daddare seda Hajja ta shiga tayi mata cin mutunci hade da zagi na tsamar nama akan rashin halartar ko daya daga cikin shagulgulan bikin da akayi musamman dinner da suka gabatar jiya da daddare wadda ita duk abinda akai ma batasan inda Abdulmalik din ya tafi ba dan ya mata sallama wai ya tafi dinner dama dai daga yana yin shigarsa beyi kama da me zuwa wani abu me muhimmanci ba har ta zauna tana risgar kukan kishi yana can tare da wata ashe shi bawan Allah hidimarsa kawai ya tafi bata ma san sanda ya dawo ba tana bacci se da Asuba ta farka ta ganshi manne a jikinta. Hawayen tausayinsa ne suka shiga sauko mata ganin yanda duk ya fita hayyacinsa sam bazakace Malik bane ne tashen gayu, kyau da Aji.

Bayan sun idar da sallah suna zaune zugum, gajiya da zaman shirun tayi seta mike ta shiga wanka dan tasan babu wani aiki da zatayi a lokacin. Tun daran jiya bayan taro ya watse Yan uwa da abokan arziqin da suka zo mata suka gyara mata ko ina tsaf kamar ba'ayi komai a gidanba sannan ga Hamidah kanwarta da Amal, Shukra da Ni'imatullah yaran Munubiya data bari su kwana su tayata aiki da safe. Harta fito daga wankan yana zaune inda ta barshi kamar gunki, kallo daya tai masa gabanta yai wani mummunan faduwa ba shiri ta furta "innalillahi wa inna ilaihi raji'un" da karfi da har saida ya juya a hanzarce ya kalleta "Babe

Please Login or Register in order to submit comment