Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

data ke so ta saka ranar auranta. Babu abinda babu a ciki hatta da undies Abbah ya siya mata na fitar biki tamkar yadda yayiwa Zahra lokacin auranta se dai nata har sunfi na zahra saboda zamani ga kuma qarin budi daya samu. " Komai yayi Abbah Allah ya saka da alkahiri Allah kuma ya qara budi" ta fada kanta a qasa. Nasiha ya shiga yi mata cikin nutsuwa irin tasa, Prof Ammani mutum ne me matukar nutsuwa da sanyin hali. Ko kadan bashi da Hayaniya hakan baya rasa nasaba da ilimin dayake dashi ta kowanne bangare. Hafizin alqur'ani ne kuma masanin littattafai da Hadisi sannan kuma riqaqqen dan boko. Har wurin 11 suna zaune a palour tana kallon wayarta na ta ringing an kira yafi sau 20 times amma taqi dagawa, sallama sukayiwa Abban kowa ya nufi makwancinsa.
Tanajin Zahra na mata magana akan ana kiranta a waya ta mata banza dan tasan Abdulmalik ne "wai bada ke nake bane tsabar rashin mutunchi a ringa kiranki ba zaki dauka ba". Seda ta buntsura baki sannan ta daga wayar tana qunquni "Babe ina kika shiga tun dazu ina ta kiranki" ya fada ba tare da ya damu da shariyar da ta masa ba. "Bana kusa da wayar ne" ta bashi amsa a tsaye.
"Ok I'm sorry ban kiraki tunda rana ba wallahi aiki ne yamin yawa kinga friday zan dauki hutu so i want to finish all my pending works"
"Oh Allah sarki" ta fada with i don't care attitude. Se yai shiru na dan wani lokaci aransa yana mamakin meya sameta haka, me yasa take magana kamar ba Hamdan daya sani ba? Daurewa kawai yayi yace mata "Naga kamar baki jin dadi ne ko dama na kirane na tambayeki an kawo kaya in akwai abinda be miki ba a ciki....." "No ba komai fa ni ban ma duba ba in dan wannan ne se da safe bacci nake ji" kit ta kashe wayar.
Sororo ya bi wayar hannunsa da kallo he can't believe it she just hang his call. Ahmad bestfriend dinsa daya gamajin duk abinda ya faru ya dafa kafadar sa tare da cewa "Chill Man is just pressure kasan mata da yawa in zasuyi aure suna shiga damuwa so se su ringa juye anger dinsu akan mijin da zasu aura so just be little patience in a week time zata zama taka" wannan ne ya sanyaya masa zuciya har ya shiga imaging irin abunda ze mata in sukayi aure.

**********************************
Yammata iya ganinka a compound kowacce ta isa a kalleta. Amarya Hamdah zaune a tsakiyar au Aysha sub tasata a gaba da tsokana wai dai karshen love story ya kuma Bae da Boo zasuyi aute. Babu wanda ta tankawa a cikinsu a zahiri kallon Dan dashe shen Zanen kunshi Baki da Ja da yar Sudan tayi mata take kallo amma a badini zuciyarta tayi nisa da Nigeria ma gaba daya. Yanda take kyalli da daukar ido dole Idan ka kalleta ka Kara abinka da mai kyau ga kuma ingan taccen gyaran Amarchi data samu Dan Anty Amna (kanwar Mumcy)har ma da Anty Zahra basu yi wasa ba sosai suka kara gyara Hamdan tasu. Hamidah ta tsallako mutanen dake zaune ta qara so gurinsu wayarta a hannunta
"Yah Hamdah for my whole life banta ba ganin couples dasuka dace da juna ba irinku wallahi kalli nan ki gani" screen din wayarta take nuna mata tana ci gaba da zuzuta irin kyan da Hamdah da Abdulmalik sukayi a pictures din. Karbar wayar Afeeya tayi tareda dropping pictures din a wayarta nan tashiga sharing ma friends dinsu dake wurin harma da wadanda basu zo ba within few minutes pictures suka shiga flying a social media kafin awa daya #*HAMMALIK* sun zama topic of discussion a ko ina. Haka aka ci gaba da guda nar da Hennah event din cikin kwanciyar hankali. Around 6pm Abdulmalik ya qarasa gidan da few of his friends, yayi kyau har ya gaji kana kallonsa ba se ance maka Ango bane bakinsa kaman ze tsage saboda Fara'a. Allah sarki bawan Allah jikinsa har rawa yake daya ganta dakyar Afeeya da Aysha suka fito da ita dan cewa tayi ita kanta ciwo yake bazata iya fita ba. "Look at My Wife Isn't she looking gorgeous" ya fada yana qare mata kallo.
"Ai dai Masha Allah kai dai ka haye saura mu amma nima ina ga fa banyi zuwan banza ba" Sagir daya daga cikin friends din Abdulmalik ya fada yana kallon Afeeya da tun fitowarsu ta dauke masa hankali. Haka sukayita wasa banda Amarya data ka bakinta ta gume tana kallonsu daddaya. "Babe menene" ya fada with so much concern. Kanta ta nuna masa, lokaci daya ya rikice ya shiga jera mata sannu yana fadin ko su tafi asibiti ne? Se kuma ya bata tausayi, tayarda Abdulmalik me sonta ne, insha Allahu zata taushi zuciyarta koda pretending ne ta ringayi in tana gabansa. Sallama suka mata yana qara jaddada mata akan tasha magani in kuma bata ji sauki ba zuwa anjima ta kirashi suje asibiti da haka sukayi sallama.

Tana yin sallar isha ta kwanta bawai dan tana jin bacci ba Aa sedan gujewa takurar mutane da suka cika musu gida da sunan bikinta. Tuni yan uwa na kusa da nesa suka gama hallara dan a gobe ne za'ayi kamu. Dangin Mumcy na Yola duk sunzo dukda bashi ne bikin ya da zatayi na farko ba amma sun mata kara kwarai dan Hamdah Favourite din kowa ce babu wanda zeso yayi missing auren yar gata.

*WAI INA INA LABARIN GURU*??????
Ku biyoni a next page its all about your favourite



















🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

*RUBUTACCIYAR QADDARAH*

🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

*By Maryamah* 💞💞
©2020

*PAGE* 1⃣2⃣
WACCEN RANAR.
Tun bayan daya sauke Hamdah ya bar kofar gidansu gudu yake shararawa kamar me barin duniyar. Tunda yake a duniya mace bata taba ci masa mutunci irin na yau ba, shi mace zata kalla tace waye ze aureshi? Shi zata cewa wai tana da wanda take so? Har ace yayi lalacewar da mace zata kalli idonsa tace bata sonsa? "Illar kula kananan yara kenan" zuciyarsa ta raya masa. Haka ne dan ya tabbatar inda tasan me takeyi bazata kasa gane matsayinsa a zuciyarta ba, ashe hasashen banza yai dayake tunanin gininsa ya isa yabe a cikin zuciyarta. Gefen titi ya faka motar ya kwanta a steery zuciyarsa kamar zata fashe zabar yanda take bugu, yanda yake sauke numfashi kamar wani wanda kunama ta harba ga zufa na keto masa dukda Ac dake busa cikin motar. "Yah Allah ka dubeni kar kasa na rasata, i have submitted all my love to her ita kadai ce hope dina". Hawayen da besan lokacin da suka fara zuba ba ya shiga sharewa yana neman wayarsa dan ya kira Fahad, shi ya bashi gurguwar shawara inda be nemi kusanci da ita ba da komai ya zo masa da sauki amma yanzu fa? Ta ya ma ze fara tunanin cireta a ransa?
" To tace bata sonka se yaya?" Zuciyarsa ta tambayeshi. Tabbas dole ya qyaleta ko da kuwa hakan zeyi ajalinsa tunda har ta budi baki tace bata sonsa. Yana can tunani har besan Fahad ya dauki wayar ba se da ya kashe yavkirashi ringing din ya farkar dashi."Where are you?" Ya tambayeshi a shake."Ina office meya faru" Fahad din ya tambayeshi yana mamakin me ya samu Abokin nasa dan daga jin muryarsa yasan babu lafiya.
"I'm sending you my location come meet me please" kit ya kashe wayar ya shiga WhatsApp ya tura masa da location din, kwanciya ya kumayi kawai ya rasa wanne tunani zeyi a ciki, me ya kamata yayi yanzu? Ya barta ne ko kuma ya ci gaba da pushing har seta amince dashi?. Besan tsahon mintinan daya dauka a wurin ba har Fahad ya zo. Window ya dan kwankwasa masa sannan ya cire lock din Fahad ya shiga motar. Kallon Abdul'ad yayi da idonsa suka kada sukayi Ja sosai da alama akwai babban abinda yake damunsa.
"Dr what's wrong ko baka da lafiya ne?.
Seda ya ja iska sannan cikin wata murya me nuna rauni yace " Fahad Hamdah ce, tace bata sona bazata aureni ba wai tana da wanda take so" ya qarasa maganar yana jin dacin kalaman a zuciyarsa, wani irin kishin ta yake ji ya tsani koma waye wannan daya rigashi shiga zuciyarta.

"Dr wasa takeyi" Fahad ya samu courage din fada bayan shirun daya yai. "Wasa Fahad, ni abokin wasan tane aka ce maka"
"Ba haka nake nufi ba may be tana so ne taga yanda zakayi reacting ne" se ya katse shi da cewa "Aa. Hamdah is very straight forward person, she talks everything straight from her heart. Kuma tun farko bata taba yimin karya ba dama ta gayamin tana da wanda take so, kai ka ce na gwada kuma yanzu gashi abinda nake gudu ya faru I'm heart broken".
Shiru Fahad yayi na dan wani lokaci, yasan duk yanda zeyi convincing dinsa a lokacin ba yarda zeyi ba dan haka yace masa " Believe me Dr tana sonka she just wants to play you around ne, amma kasan me zakayi yanzu" girgiza masa kai yayi alamar Aa yana jira yaji ya fada masa wata magana da bata gamsheshi ba ya naushe shi. Yasan halin abokinsa sarai, girma sukayi suka ga kansu tare baze iya cewa ga sanda suka fara Abota ba dan haka ya saita nutsuwarsa tsaf sannan yace "Give her some space. Kar ka qara kiranta mujira I'm very sure zata neme ka da kanta bet me".
Kallonsa yai na dan wani lokaci yana juya maganar a zuciyarsa. Ba laifi yayi Na'am da shawarar Fahad dan haka ya gyada masa kai Alamar ya yarda. Hakan ya bashi damar Ci gaba da bashi shawarwarin yanda ze shawo kanta, sun dade sosai sannan sukayi sallama kowa ya tafi gida.
A masallacin gidansu ya tsaya yayi sallar Magriba tare da Azkar dinsa sannan ya shiga gidan. Da sallama ya shiga palour wata Kyakykyawar Mace tana zaune cikin shiga me kyau ta amsa masa. Fara ce amma ba can ba tana da matsakaicin jiki haka tsahonta ba can doguwa bace. A kallo daya bazaka tantance shekarunta ba saboda hutu da ya taimaka wa jikinta wurin komawa kamar wata matashiya yar shekara 40. Kallonsa take tana murmushi har ya qarasa inda take ya zauna a qasa daidai kafarta " Ammi na sannu da gida"
"Yawwa Galadima ya aikin yau ka dade kai da kace min da wuri zaka dawo" ta fada tana shafa kansa. Kamar karamin yaro ya dora kansa akan cinyarta yana sauke ajiyar zuciya sannan yace "Ammi na dan biya wata unguwane sannan mun tsaya da Fahad a hanya".
" Ko dai gurin surukar tawa kaje ne" ta fada cikin sigar tsokana.
"Ammi can naje amma tace bata sona" Dariya tayi sannan tace "Haba dai anya akwai macen da zata ce bata son Galadima na santalelen saurayi son kowa kin wanda ya rasa kaidai kilan kayi mata wani abun ne take so ta hukunta ka, shiyasa na ganka duk wani iri kenan".
Muryar Kanwarsa Fadila ya jiyo tana cewa " Yaya wannan Farar budurwar taka dan Allah ka aureta wallahi Ammi baki ganta ba har na fara Imagining irin yaran da zasu haifa masu kama da Yaya Farare irinta". Kallonta kawai yayi tareda yin guntun murmushi sannan ya tashi ya nufi Dining dan yunwa yakeji.
Bin bayansa tayi tana cewa "Kaji Yaya ka aureta dan Allah yaushe ma zaka kaini mu gaisa da ita Allah ina sonta" "Fadila tace bata sona se ki bari idan na samo wata se na kaiki ku gaisa" ya fada yana zuba abincin dan a duniya baya wasa da cikinsa, kai ko bashi da lafiya seya ci abinci. Haka ta ringa masa surutu har ya gama cin abincin ya tashi Ammi na zaune a cikin palour tana musu dariya. Fadila ita ce Autarsu, duk cikin kannensa yana ji da ita sosai.
"Ammi ina su Khadija ne naji gidan shiru se wannan parrot din".
"Sun tafi gidan Amina na manta ban gaya maka ba jiya tayi barin yan biyu shine na turasu su taya ta zama tunda mijinta baya nan" Ammi ta bashi amsa. "Ayya Allah ya bata lafiya bari nayi wanka senaje na duba ta"
"Zan bika Yaya" Fadila ta fada kamar tana jira yace ze je gidan. "Kije ki shirya karki kuma batamin lokaci" ya fada yana fita daga palour zuwa part dinsa dan yin wanka. Har 11pm na daren ranar yana gidan Amina kanwarsa datake bi masa, Abdul'ahad mutum ne me matukar son yan uwansa. Yana matukar tausayinsu, Yayyensa biyu Saudah da suke kira da Hajia karama ita ce babbarsu, tayi aure tuntuni suna zaune a America da Yaranta hudu se me bi Mata Fatima ita ma tayi aure a Lagos tana da yara biyu da cikin na uku sannan shi se Amina me Da Daya se kuma twins dinsu Khadija da Hafsa sannan Auta Fadila. A zamansu ya duba wayarsa yafi sau dari duk a jiran tsammanin ganin text ko kira daga Hamdah amma babu ko daya a ciki har Amina ta lura dashi take tambayarsa ko lafiya dan dama tunda ya shiga tasan akwai wani abu dayake damunsa. Ba komi yace mata kawai yana duba lokaci akwai abinda zeyi dan haka yacewa Fadila ta tashi su tafi badan ta so ba ta bishi dan dai Ammi taja mata kunne akan karta kwana ne. A hanya duk irin surutun data ke masa be tanka mata ba har suka zo gida, a get ya tsaya ta sauka ya qara fita ita dai ta shiga tana mamakin me yake damunsa haka.

Cikin school ya tafi a daren dan akwai abubuwan dayake so ya dauka a office dinsa. Sanin ko karfe nawa ne akwai attendant a office din Registerer ya saka shi rubuta takarda yaje ya kaimusu sannan ya tafi gida lokacin har shabiyu ta gota. Ya riga yayi niyya baya jin akwai abinda ze dakatar dashi, a daren ya hada duk abinda yake da buqata, karfe shidda yaiwa Ammi da Fadila sallama ze tafi Abuja ze tsaya gurin Baba yai kwana daya sannan ya wuce Singapore akwai wani Team dayai joining zasuyi wani Research work akan Gene mutation in Snakes, A da ya jingine aikin amma yanzun shine right time daya kamata yayi, yana buqatar abinda ze dauke masa tunaninta daga ransa. Kwansa daya Abuja ya daga Kasar Singapore ya qudurcewa ransa yabar kowa da komai daya shafe ta, baya tunanin ze qara waiwayar Nigeria ma nan kusa.
Ba karamar wahala yasha ba kafin yai over coming tunaninta daga ransa dan abin kamar tishi harta kai idan yana aiki yana ganinta a ciki, duk macen daya gani kuwa sunanta Hamdah se dakyar abin ya fara rabuwa dashi ya ajiye batun aure ko soyayya a gefe, bayajin ze qara waiwayarsu nan kusa.
*****************
CIGABAN LABARI

Abdul-ahad zaune shida abokanansa Master, Aliyu se Mustapha. Abokanasa ne tun zamanin sa sukayi karatu tare a Cambridge, dukkansu mutanene masu hazaqa kamarsa shiyasa Abotar tasu tayi qarko yanzuma dukka tare suke research work din. Mustapha dake ta faman danne danne cikin waya ne yace "Nigeria is on fire wani yayi wuf da jewel yayiwa gayu game over" kallonsa sukayi gaba daya banda Guru da kwatakwata hankalinsa baya tare da hirar da sukeyu yarasa meke damunsa akwana biyunnan yana yawan tsintar kansa da faduwar gaba daya rasa dalilinta sannan ga tunanin HAMDAH AMMANU da ya addabeshi. Wani lokacin ya kanji kaman ya kirata amma seya kasa. Yana matuqar kewarta, sonta ya kasa barin zuciyarsa a kullum kamar qara masa akeyi.
"Kai gaskiya yarinyar nan ta qerun Guy dinnan yacu Maza dayawa wasa irin wannan zukekiyar yarinya haka" sambatun Mustafa ne yakatse shi bedai ce komai ba illah kallonsu daya keyi jin yanda suke zuzuta kyan yarinyar. Gaba daya suka hada kai suna kallon hoton se zuzutu sukeyi.
"Man Kalli ka gani mana I'm sure ko wannan Aljanar daya lashe maka zuciya bata kai wannan kyauba" Aliyu ya fada cikin sigar wasa. Murmushi yayi tareda karban wayar yana cewa "bana tunanin akwai wata mace dazata kai kyan HAMDAH a idona her beauty has no match to me...."maganar ce ta makale masa, Idan dai ba idanuwansa keyi masa gizo ba Tabbas HAMDAH ce wannan. Tayi kyau har ta gaji cikin wani hadadden Swiss lace black me adon flower red haskenta ya qara fitowa fuskar nan tasha light make up ze iya rantsewa be taba ganin tayi kyau irin wannan ba.

Wata irin juwa ce fara daukansa ga Amai na kokarin taso masa kafofin jikinsa babu wacce bata fitar da gumi, Scrolling din hotunan yaci gaba dayi aransa yana addu'a Allah yasa dai Kamace ko kuma mafarki yakeyi sedai addua'arsa bata karbu ba lokacin dayai tozali da bakin sako, katin gayyatar daurin Auran *Abdulmalik Kamalu Dala da Hamdah Ahmad Ammani* nan take yai zaman yan bori a qasa, baya neman sauran qarin bayani itace, itace za'a aura wa wani Babu ko tantama Hamdan sace.
"No it can't be possible" ya fada on top of his voice tareda cilli da wayar ta bugu da bango a take tayi kwatskwatsa, mikewa tsaye yayi jikinsa na rawa kamar mazari abin tausayi se kawai ya yanke jiki ya fadi a gurin.
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

*RUBUTACCIYAR QADDARAH*

🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

*By Maryamah* 💞💞
©2020

*PAGE* 1⃣3⃣

Gaba daya suka yi kansa a hankalinsu a tashe. Aliyu ne yai karfin halin kiran ambulance cikin lokaci kadan suka qara so aka dauke shi zuwa asibiti dan har lokacin he was still unconscious. Ko a asibitin tambayar junansu suke dalilin sumansa amma babu wanda keda amsar dan haka suka tsaya jiran likitan daya ke dubashi kilan shi yana da masaniya akan abinda ya sami Abokin nasu. Seda ya dauki awa daya sannan ya farka, kallonsu yake daddaya yana so ya tabbatar da abinda ya faru mafarki ne amma tambayar da suka fara jera masa yasa ya gane tabbas abinda ya gani gaskiya ne. "It happens in real" ya fada a ransa. Se ya shiga kokarin sauka daga gadon bayan ya fincike allurar karin ruwan da aka saka mas. Yana ganin jiri da komai haka ya nufi kofa yana dafa bango Duk kuwa da yanda suke masa magiyar akan ya tsaya jikinsa babu kwari tuni ya fice daga ward din gani in suka barshi ze iya zuwa ya illata kansa abanza yasa suka bi bayansa.
A motar Master suka koma apartment din nasa. Kayansa ya shiga hadawa a cikin qaramar jaka ba ji ba gani. Duk da tarin tambayoyin da suke yi masa be amsaba faman loda kayan da besan me zeyi dasu ba dan in aka zazzage kaf babu complete set dauka kawai yake suk wanda hannunsa ya taba har ya gama ya saka passport dinsa da duk waau muhimman abinda za'a nema a aljihu ya ja akwatinsa yai waje cikin wani matsanancin tashin hankali. Gani yakeyi taxi din daya hau bata sauri tamkar ya sauka ya taka da kafarsa haka yaringa ji. Ko a Airport din besan nawa ya bawa mutumin ba kaman zautacce haka yaringa tafiya duk da irin azabar dayakeji a jikinsa amma be tsaya ba yana tafe yana hada hanya kaman wani dan maye haka ya qarasa ciki sedai yayi rashin sa'a babu jirgin da ze tafi Nigeria a kwana biyu masu zuwa ma.
Zaman dirshan yayi a gurin kamar mace ya shiga hawaye, dabara ce ta fado masa ta yanemi jirgin wata qasar a Africa duk tsiya ko da kafa seya je Nigeria (lol) hakan kuwa akayi sedai yasha wahal kafin ya samu shima akwai transit biyu kafin su isa inda zasuje. Akace Dama dama haka ya zauna yana jiran lokacin tashin jirgin, gani yake agogo baya sauri awa biyu yau seta zamar masa tamkar kwana goma. Lokacin da aka fara announcing tashin jirgi kuwa Sujjada shukriya saboda tsabar murna, a yanzu yana da hope he is only some hours away from home.

*_HAMDAH AHMAD AMMANI_* Zaune gaban dressing mirrow. Kallon kanta takeyi tana karawa wai yau ita HAMDAH itace Amarya wai yau kamun bikinta za'ayi haka? daga yau ita ma zata shiga jerin matan aure? Dafata da Anty Zahra tayine yasata juyowa fuskarta dauke da qaramin murmushi da iya kacinsa lebe. Nasihar da Yah Abubakar yai mata jiya tayi matukat tasiri akanta. Bata san ya dawo gidan ba ya shiga dakinta ya tarar da ita tana sana'ar data zabarwa kanta yanzu kuka ta tasa pictute din Abdul'ahad a gaba. Cikin matukar tausayawa ya zauna a kusa da ita yareda janyota jikinsa ya shiga rarrashinta "Kiyi shiru ki gayamin me ke damunki" ya fada cikin kwantar da murya. Tana buqatar fitar da abinda ke zuciyarta kota ji sauki amma rashin wanda ze fahimceta yasa tazabi tayi shiru, tsaf ta zayyana masa komai data ke ji game da mutum biyu. Yah Abubakar ya sauke ajiyar zuciya sannan yace "tun farko kinyi wauta da kika amince da auren nan bayan zuciyarki ba a kansa take ba amma abin tambaya shi wancan din yana ina? Idan kika fasa wannan kina da tabbacin shi dagaske yake ze aureki? Yana ma ina a yanzu Hamdah kiyi tunani. Nasani ko ana tsakiyar taron daurin aurenki in har kika furtawa Abba baki son Auran nan se an fasa shi bazeyi miki dole ba amma ki tuna abinda ze faru, ki tuna irin mutanen daya gayyato, ki tuna kudaden daya kashw duk dan ya faranta miki Hamdah kinga gidanki kuwa? Kin san abinda Abba da Momy suka zuba miki kuwa. Na tabbatar sunyi ne dukka saboda kaunar da suke miki, yau ace wani suka dakko suka aura miki baki sanshi ba Hamdah ke me karba ce ki musu biyayya ko dan saboda fifitaki da sukayi a cikin mi 10 dasuka haifa.

Babu wanda be san banbancin da ke tsakanin ki da mu ba dan Allah karki karya musu zuciya, karki zubda musu a kima ta hanyar fasa auran nan. Ke kika kawo shi ke kika zabo shi babu wanda ya tayaki Hamdah karki sa ayi miki dariya ki rufawa kanki wannan asirin karki zubda mana da kimar gidan mu saboda son ranki. Kowanne bawa da yana *QADDARAR SA* take ba kowa ne yake samun abinda yake so a rayuwa ba, ki tuna wani baya haifar dan wani in da rabo ko kwana daya ne se kinje kinyi kin samo shi. Kiyi hakuri ki sawa zuciyarki kamar baki taba sanin wani Abdul'ahad ba a rayuwarki, ki Dauki wannan a matsayin *_RUBUTACCIYAR QADDARAH_* Cikin kundin rayuwarki idan a rabo a tsakaninku ubangijin daya hadaku ya kuma raba ku a sanda yaso shi ze kara hada ku, he will surely re-unite you again".
Tunda ya fara take kuka har ya gama, ta yarda da duk wata kalma daya fada ta kuma qudurce a zuciyarta zatayi hakuri. Abdulmalik ya isa masoyi yakuma cika dukka alkawarin daya daukar mata. Insha Allahhu zata goge guru da duk wani abu daya shafeshi a rayuwarta, she will live as if she never knows him, zata juyarda zuciyarta ga mijin da zata aura komai wahala kuwa insha Allahu baze taba samunta da wata gazawa ba.
*****************
Hawayen daya taru a idonta saka makon tunanin data tafi ne ya fara zuba akan kyakykyawar fuskarta, tissue paper Anty zahra tasa ta fara share mata tana cewa "yah haka kukan kuma na me nene kedai kin zama ruwa ruwa wallahi duk zaki bata kwalliyar bayab kinyi kyau sosai haba Hamdahn Abbah". Dole tayi murmushi tana qoqarin mikewa tace "Na gode Anty" hannunta ta kama suka fito daga dakin tana qara gyara mata zaman kayan jikinta.
Duk Wanda yake zaune a palour seda ya yaba yanmatan guda biyu kamanninsu daya in banda haske da Hamdan zata fi zahra kadan se kuma yar kiba da ita zahran ta fita dan ita ta haihu. Amarya Hamdah sanye take cikin hadadden Iro and Buba na asalin yarabawa

Please Login or Register in order to submit comment