Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da duniya lafiya kuwa" ya fada a saitin kunnenta.
Seta dago a fusace cikin tsiwa tace "cikin mu a samu wanda baya so ya gama da duniyar lafiya duk tsiya ni banje ina taba mazan mutane dole ba kuma wallahi zunibi a kanka tunda Allah yaga zuciyata bada son raina bane qarfina akafi". Ko a kwalar rigarsa kalamanta basu bata masa rai ba, seya shiga tuqinsa hankali kwance yana cewa
"Malam tambayarki nayi ina zaki ba cewa nayi kimin fitsara" baki ta tunzuro kaman zata tsireshi ya kuwa saka farcensa ya mintsineta a lips. Seta saka kuka dan taji zafi sosai
"Allah ya sakamin mugu kawai" ta fada in between tears, seya saki steering gaba daya ya janyota yana cewa "bari kiga qarshen mugunta yarinya ni kike wa Allah ya isa ko". Ihu ta ke iya qarfinta ganin suna yawi akan titi Allah ma yaso su kadai ne babu kowa saboda dare ya farayi dan har sha biyu ta gota.

"Mara kunyar qarya ashe kina tsoron mutuwa nazata kin qagu ae kibi tsohon mijinki tunda gashi kinje can kin kasa zama ko tunaninsa kike" ya fada yana matsa cikinta da dan qarfi.
"Wash Allah na" ta fada saboda azaba dan gurin aikinta ya matsa, dukda baya mata ciwo kwata kwata bata san wace irin ooeration bane wata hudu amma kamar ba'ayi shi ba dama ba dinki bane ko fatar gurin ka kalla layine guda daya inda aka yanka amma yanzun daya danna taji zafi kam. Seyai saurin kunna fitilar motar yana kokarin daga rigar dan shaf ya manta da aiki a jikinta. Wani irin yar yaji tundaga kansa har kafarsa lokacin dayai arba da farar fatar jikinta da yake a shafe kaika rantse bata cin abinci ma bare aje batun yaya biyu sun zauna aciki. Saurin sakin rigar yayi at the same time ya dagata cak ya maida ita sit dinta. Tafiya suka cigaba babu me cewa wani qala har suka qaraso gida, seda yai parking motar sannan ya bude ya fita, kofa ya bude mata itama ta fito tana cika tana batsewa kamar zata fashe shidai se munafukin murmushi yake binta dashi. Ransa fes ko haka aka tsaya ubangiji ya wanke masa damuwarsa.

"Hajia kinmanta jakarki" ya fada ganin tayi gaba ba tareda ta dauka ba. Badan keys dinta na ciki ba da bar masa zatayi , se taja ta tsaya ta zumbura baki, girgiza kansa yayi irin zanyi maganinki kafin ya dauki jakar ya biyo bayanta tana tsaye har ya wuceta. Seda ya bude mata kofar da kansa kafin yace
" Oya shiga Good night" ya janyota jijinsa tareda sakar mata light kiss a goshinta da kan lips dinta.
"Ji mana" ya fada harta turo kofar dan gani take in taci gaba da tsayawa to kuwa bazasu kwashe kalau ba ai ita ba yar tsanar roba bace da ze ringa daquma yanda yaga dama.

"Next time in zaki fita kiringa shiga ta mutunchi please kar na qara ganinki da wannan rakani gantalin" ya fada yana juyawa abinsa, seta tsaya kamar wadda aka kafe. Inba rainin hankali ba ita ze kalla yace wai ta ringa shiga ta mutunchi look at who is talking about decency. Tsaki taja tayi shigewarta cikin gidan ranta a matuqar bace ga Ice cream din da bata shaba ga bata mata lokacin da yayi haka ta kwana tana qunquni.

Knocking din da ake yi ne ya tada ita da Asuba, idonta cike da bacci ta sakko daga kan gadon tana mamakin waye wannan haka kuma seta kejin kaman kofar Bedroom din ake bugawa kodai bacci ne. Rigar jikinta me santsi ce da bata kai mata ko guiwa ba haka ta sake dogon gashinta daya ke har tsakiyar bayanta. Dan mayafin data gani ta dora akan nata dukda be rufe komai ba ta bude kofar Bedroom din ta fito.

Seta tsaya turus tana qara ware idanuwanta ta tabbatar daidai take gani ko kuwa dai magagin bacci take, Guru ne zaune akan couch ya harde qafa daya kan daya yana juya wayarsa idonsa fes akan kofar se tayi saurin komawa da baya saboda yanayin kayan jikinta. Tafi minti biyar a tsaye cikin dakin ta ma rasa me zatayi, abun ya kai mata har wuya wannan wane irin iskanci ne da rainin hankali waima ta ina ya samu hanyar shigo mata gida?
Kamshin turarensa da kuma takun sahun takalman dataji suka tabbatar mata ya shigo dakin, seta daure fuskarta ta mau ta juyo tana kallonsa

"Wannan wane irin is..... "

"Ya isa malama ni ba surutu ya kawoni ba ki wuce ki samamin abinda zanci yanzu ina da meeting karfe 8am".
Saboda tsabar mamaki seta nemi guri kawai ta zauna tana binsa da kallo, ta ma rasa abinda zata ce masa. Dakyar ta samu courage din cewa

"Zaman dadiro mukeyi ko yaya"
"A'uzu billahi" ya fada tareda saurin kallonta dan da hankalinsa yana kan wayarsa. Seyaci gaba da cewa

"Karki qara dangantani da wannan baqar kalmar ko nayi miki kama da dan iska ne?"
Seda ta watsa masa wani kallon banza sannan tace
"Meye marabarka da shi? Taba jikin matar da bataka ba ko kuma shiga gidan mace ba tare da izini ba ai kafi qarfin a kiraka da Dan iska ma sedai kwart....." Bata samu damar qarasa ba saboda cafkar da yayiwa bakinta. Cikin tsantsar muguntar da take nuna fushi yake kissing dinta tsabar Azaba seta saka kuka dukda baya fita saboda bakinta da yake a rufe.

Seda ya tabbatar da ta horu sannan ya saketa yana maida numfashi yace "Gobe ma ki qara jifana da wannan kalmar na rantse da Allah sena nuna miki qarshen Kwartanci ki kuma tashi kiyi abinda nace in ba haka ba kinsan in fada sena cika" yai ficewarsa daga dakin.

Kuka ta shigayi wiwi, wannan wane irin wulaqancine? Zawarci hauka ko kuwa saboda ta baro qasarta zuwa wata duniya shine ze biyota ya tozartata? Meyasa be taba mata hakan ba lokacin da suke a Nigeria se yanzu da ya ganta ita kadai inda bata da me kareta. Bata san lokacin data kwashe tana kukan ba saboda baqin ciki ta kasa denawa. Kamshinsa data qara jiyowa kusa da ita shiya sanar mata da dawowarsa, bata dago ba haka bata dena kukan ba yana tsaye yana kallonta hannayensa zube cikin aljihunsa, kasa jure kukan yayi a hankali ya qarasa inda take ya dagota gaba daya zuwa jikinsa ya mata kyakykyawan masauki a cikin broad chest dinsa.

Luf ta kwanta lokaci daya tana shaqar daddan turarensa dake kwantar mata da hankali. Bata san meya sa take samun nutsuwa a jikinsa ba kwatankwacin lokacin da take tare da Abdulmalik dinta kuma abun ya zarta nada. Lokacin baya a duk lokacin daya hada ta da jikinsa tana so amma tanajin tsoron kasantuwar haramacin haka amma ta rasa a wannan haduwar meyasa batajin haka, da so samune su dawwama a haka kar ta taba rabuwa da jikinsa. Seta fara qoqarin janyewa tunawa da haramcin abun da kuma sabon rainin hankalinsa gareta.

"Ka sakeni malam" ta fada a tsiwace tana janye jikinta, seya rufe mata baki da hannusa sannan ya dago fuskarta da daya hannun bayan ya saketa yana kallon idanunta zuwa qaramin bakinta da take budewa da niyyar sake masa wata masifar, he just can't resist her lips, seda yai brushing lips dinsa akan nata cike da mugunta ya cijeta kadan akan lips sannan yace
"Karki qara furta cewa na sake ki baby girl" seya jata kaman yarinya dukda yanda take turjewa amma seda ya danganata da kitchen. Gefe ya tsaya yana cewa
"10 mins ki samanin abinda zanci Malama I'm running out of time" ya shiga danna wayar daya zamar masa dabi'a. Kayan jikinta take kallo tana so taje ta dauko koda Hijab ne ta saka dan Jarabar tasa kuma ta zarce hankali gara ta dafa koya barta ta huta amma ya kasa ya tsare hanyar, ganin da tayi hankalinsa baya kanta yasa ta shiga aikin a ranta ko ta zageshi yafi cikin kwando harta tafasa masa ruwan Tea da toast bread ta dungurar masa da plate din a gabansa fuuu ta wuce.

Da murmushi ya rakata kafin ya kalli abincin, mug din ya daga ya fara kurban tea din a hankali wani irin dadi da gardi ya masa kamar be taba shan Tea a rayuwarsa ba lokaci daya ya bude ciki ya kwankwade. Beci bread din ba saboda he isn't fan of bread at all se ya juya kaman ze koma dakin kome ya tuna kuma se kawai ya fita.
A daidai kofarta suka ci karo da Zulaiha da take qoqarin shiga. Kallon mamaki ta ringa binsa dashi a ranta tace "ikon Allah Mr Abdul'ahad a apartment din Miss Hamdah so surprise" ita dai suka gaisa ya matsa mata ta shiga tana cigaba da juya abin a ranta.

Kuka kashirban ta tarar da Hamdah tanayi kai kace Mumcy ce ta mutu ko wani tana ganin Zulaihan ta qara volume shikenan abinda take gudu ya afku wane kallo mutane zasu fara mata dan ta tabbatar Zulaiha ta ganshi dan da fitarsa da shigowarta bekai minti daya ba.
Seta shiga kallonta kaman me son gano wani abu tattare da Hamdah. Shidai taganshi well dressed da alama ma office ze tafi kuma dai babu alamaun a gidan ya kwana ita kuma gata da kayan bacci tana kuka, se kuma wata zuciyar tace mata "they are all from Nigeria probably he is her relative, dukka su biyu babu me yawan magana bare su nuna haka" wannan tunanin yasa ta zauna a kusa da ita. Haquri ta shiga bata Allah sarki se kukan da take yi ma ya kore zargin komai daga zuciyarta haka tayita fama har Hamdah tayi shiru sannan ta shiga tayo wanka suka fita saboda dama wani guri suke son zuwa da sassafen.

Allah ya taimaketa tun daga wannan ranar bata qara kodajin horn din motarsa a gidan ba. Batasan inda ya tafi ba koma ina ne shi ya sani ita dama ya tafi kenan kaman yanda dama aka ce baya wuce sati daya sati biyu in kuma ya tafi se an ganshi. Ranar wata Monday kusan two weeks da tafiyar Guru da wuri ta shiga school kuma ko motarsa bata gani a parking lot dinba. Wuraren karfe biyu ta shiga cafeteria dan taci abinci bata samu ta karya a gida ba sannan tunda ta shiga makarantar take busy. Nurain wani course mate dinta, dan Nigeria ne shima dan asalin Kebbi State. Tun ranar daya fara ganinta a Airport yake bibiyarta har ya zama na ashe ma ajinsu daya. Yarone qarami dan befi da shekara daya da dan wani abu ya girme mata ba amma ya nace tunda ya ganta wai shi sonta yakeyi duk kuwa data gaya masa itafa ba budurwa bace amma yace yaji ya gani a cikin school kamar Jela kullum haka yake binta yauma haka tana shiga Cafeteria ta hangoshi da wani Austin da Juliet suma abokanan karatunsu ne suna cin abinci. Table din da suke ta qara suka gaisa kafin ta koma separate table tayi order abinda zataci tana ta baza hanci jin kaman kamshin turaren 'MR PROBLEM' take ji. Waiter na qoqarin ajiye mata abincin Nureen ya karba yayi settling bill din sannan ya ajiye ya shiga nade hannun riga acewarsa wai a baki ma zeyi feeding nata saboda yasan ta gaji sosai.

_ABDUL'AHAD_
Tunda ta shiga gurin hankalinsa yake kanta har zuwa lokacin da ta zauna. Magana sukeyi da wani farin tsohon bature amma ya karkata hankalinsa gaba daya zuwa kanta yana watching duk wani motsinta har zuwa sanda yaga wani Yaro me kama da yan Daudu acewarsa ze bata abinci abaki se ya mike a matuqar fusace in seconds ya isa wurin daidai lokacin Nurain ya kai mata spoon baki lokaci daya ya hambarar da abincin ya zube cokalin ya fadi can gefe dan.
Bakinta daya hada ya buge tsabar masifa ta dafe tana kallon yanda ya cakumi wuyan rigar Nurain din tareda falla masa mari ai ba shiri ta riqeshi ganin yanda jikinsa yake wani rawa kamar wanda ake kadawa gangi.

"Sakeni sena koya masa hankali gobe ma idan akace yaje ya bawa matar mutane abinci seya qara" ya fada a fusace yana tunkude hannunta daga jijinsa. Seta saka kuka ganin yanda yake faman naushin Nurain shi kuma ya tsaya kaman dolo har ya fasa masa hanci ga mutane har sun fara taruwa wasu ma daga waje suke shigowa kar abasu labari dakyar mutanen da suka sanshi suka janyeshi ya kuwa finciketa kamar leda suka fice daga gurin bayan da ya gama bawa securities din da sukazo statement cewa matarsa Nurain din ya kula har yana qoqarin taba mata jiki (kuji sharri). Yanda yake fizgarta da kuma takalmin kafarta yasa ta kasa saurin ma se kawai ya sunkuceta kamar wata jaririya har suka qarasa inda motarsa take, ita kam zuwa yanzu abin ya dena bata mamaki sema tsoro dan haka taja bakinta ta dinke har ya sauketa a cikin motar ya shiga ya kunna saboda programed ce se kawai ya fice ya barta a ciki bayan ya kunna mata Ac yasa lock ta waje yai tafiyarsa. Seda ta shefe awa uku cif a motar ba Azahar ba la'asar sannan ya dawo fuskar nan dinke tsaf kai ka rantse be taba dariya ba.

Kallonta yayi with a serious face yace
"Bayan shigar banza wato harda Yan iska kike kulawa ko?" Yanda yayi maganar ya bata tsoro amma bata ga dalilin da zesa ya ringa juyata kamar wata abin ikonsa ba seta dake taqi koda kallon inda yake.

"Ba dake nake magana ba kikamin banza" ya fada on top of his voice da har seda ta tsorta, fuskarsa data canza kala tsabar bala'i ta kalla tana rarraba ido to ita me zata ce masa wai, Eh ko Aa. Bata qarasa tunanin ba ya fizgo hannunta harseda yayi qara tsabar azaba bata san sanda ta saki kuka ba. Sosai ya matse hannun yana kallon yanda hawaye yake zuba a fuskarta kaman an bude famfo sema ya dauke kansa yana kallon wnai guri daban. Seda ya tabbatar dan kansa ta ladabdu sannan ya sake ta ya kunna motar dukda ko kashi goma na cikin bacin ransa be goge ba. Tsabar rainin wato tana zaune wani dan isaka wai ze bata abinci a baki.
Kallonta yayi ganin yanda take kuka sosai tana murza hannun, se kuma yadan ji tausayinta ganin yanda gurin yayi ja sosai kamar wadda ta qone da alama jini har ya kwanta a gurin a ransa yace "matsalar farar fata kenan" seya kamo hannun tayi saurin zabura a zatonta qara matsewa zeyi
"Dan girman Allah kayi haquri ni wallahi bani nace ya......" Se yayi saurin katseta ta hanyar ce mata Shiiiiii yana gangara motar zuwa gefen titi. Parking yayi kafin ya danna wani abu a jikin kotar se gaba daya Gear da hand brake din kuka shige wani guri wurin ya mata plate yanda ma wani ze iya zama batare da ya takura ba. Qara danna wani buttun din yayi kujerun biyu na gaba suka hade ya zamana suna kusa sosai shida ita seya kama hannun nata a hankali kaman me taba jariri ya janye hannun Silky Abayar jikinta idonsa akan smooth yellowish skin dinta da yake kyalli tsabar gyara.

Yanda take kallonsa tana jira taga me zeyi shima haka yake kallonta, a hankali kaman me tunanin wani abu yakai warm lips dinta kan skin din hannunta ya dan goga kadan ba shiri ta dauke nufashin jin wasu electric shocks na bin kowacce jijiyarta suna daurewa. Kallon fuskarta yayi yaga ta lumshe idonta se kawai ya bude bakinsa a hankali ya shiga tsosar gurin yana dan hura mata a hankali.
Sanyi da dumin harshensa da suke sauka akan hannunta a lokaci daya suka hadu suka caza mata kwakwalwa. Seta qara damqe idonta dan ita kadai tasan ya takeji har cikin kwakwalwar kanta. Seda yayi me isarsa sannan ya saketa idonta a rufe har lokacin ta kwanatar da kanta a jikin kujera tana sauke numfashi da ajiyar zuciya a lokaci daya, wayarsa ya dauko yayi mata hotuna guda biyu a jerw kafin ya tada motar ya fizgeta a tsiyace ya hau titi abinda ya dawo da ita hayyacinta babu shiri kenan ta ware ido tana kallonsa tana kallon titin.

"Anya bashida aljanu" ta raya a zuciyarta. Ya hade fuskar nan tsaf kamar yana tsaye gaban dalibansa a BUK. Baza ka taba cewa wannan mutumin ne na yanzu daya gama kaita wata duniya ba ya gudo ya barota acan se kawai ta saka kuka tsabar ta ma rasa me zatayi a lokacin.




🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

*RUBUTACCIYAR QADDARAH*

🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

*By Maryamah* 💞💞
©2020

*PAGE* 4⃣0⃣


Burki ya taka a tsakiyar titi Allah ya taimakesu babu kowa a bayansu ya kalleta da idanunsa da suka sauya kala lokaci daya tsabar masifa.
"Billah in baki rufe min baki ba sena baki mamaki yanzu a nan gurin se kin gayamin me na miki da zaki tasani a gaba ki ringamin kuka ko kuwa sabida na miki fada akan Dan isakan saurayin ki ke ko kunya bakiji ba yaron da kin kusa haifarsa kike bata lokaci dashi to idan ma haka kike so ki bari ba anan ba se kinje inda baki da kowa sekiyi duk irin abinda kika ga dama but not here". Seta dakatar da kukan tana kallonsa, wai Dan iska to shi kuma dan guguwa ko me?
Rasa me zata ce tayi sekawai ta kauda kanta tana kallon window daidai lokacin daya taka motar suka ci gaba da tafiya tace
"Idan shi dan iska ne me bawa mata abinci a baki me shigar musu gida ba izini kuma har ya ringa taba jikinsu ya sunasa". Seya juyo sosai yana kallonta, lallai ma yarinyar nan shi take gayawa magana haka wato tana nufin shine dan iskan kenan? Wani shu'umin murmushi da shi kadai yasan ma'anar abinsa yayi ya maida kai yana ci gaba da tuqi, har sukaje gidan ba wanda ya sake magana ko parking din kirki bata bari yayi ba ta fice daga motar tana sakin sabon kuka na tsantsar takaici.

Bata koyi minti uku da shiga ba aka fara Knocking, a tunaninta shine dan haka a masifance ta isa kofar niyyarta yau seta zageshi tas qila ya fita sabgarta sedai tana budewa taci karo da Yassar da Anty Islaha a kofar gidan. Seta qirqiri fara'ar dole ta dorawa fuskarta ta shiga yi mata sannu da zuwa tarefa bata hanya ta wuce. Seda ta kawo mata ruwa da dan abin tabawa dangin snacks da bata rabo dasu sannan ta zauna suka gaisa sosai tana tambayar Yassar ya akai beje school ba yace bashida lafiya ne, sannu ta masa da fatan Allah ya kawo sauki.

Wata leda datana gani ta san kota mece ce Anty Islaha ta miqa mata tana cewa
"Nasa Mumy ta miki bayani a waya amma dai tace na qara ja miki kunne in kuma bazaki amfani dasu ba ni ki bani tun yanzu na baki kudin". Seta turo baki kadan tana duba content din cikin ledar, goran Zuma ne guda uku se wasu gari a robobi suma uku, Gumba da dai sauran tarkace se wani turaren wuta dan kadan a yar leda da wata yar mitsitsiyar kwalba da ita ma take zaton turarene. Hamdala tayi dan dukkayan da zata iya ci ne a ciki masu Zaqi seta maida ledar gefe tana cewa
"Ae Mumcy ta iya barnar kudi inda a wannan fannin ne in ba haka ba nida ba aure ba bakuma shirin aure ba kawai a hadani da wasu tarkace in ta dirka" ita dai Islaha banda dariya ciki ciki ba abinda takeyi a ranta tace "yarinya zaki gane baki da wayo". Sun dan jima suna hira daga qarshe tace in ta samu lokaci tazo gidan ta tana son ganinta. Se bayan Magrib sannan ta tafi suka barta ita kadai. Sedata gama shirin bacci tsaf sannan ta dakko wayarta dake cikin jaka tuntuni. Message tagani gani akai,
"Cook dinner for me i will be late". Seta saki baki aranta tace ikon Allah dan ko bata san number ba tasan ba kowa bane se Gwani na gwanaye GURU. Quilt dinta taja tareda gyara kwanciya sosai sema ta kashe wayar tana cewa
"Ubana Ahmad Ammani seka tsireni tunda ban dafa ba" tayi tsaki tare da rufe idanunta.

Cikin bacci tajita tana yawo a sama, tunda ita dai tasan bata da fukafuki se ta qara maida idonta ruf a zatonta mafarki take sedai tafiyar dataji anayi da ita ne yasa ta dan bude idonta kadan dan ta tabbatar gaske ne ko mafarkin ai setayi saurin ware idanunta sosai lokaci daya ta dire daga Hannunsa tana rarraba ido kaman wadda taga Aljani. Tama rasa abinyi, ihu zatayi kome anya kuwa Abdul'ahad ne kodai wani Aljanin ne yake zuwar mata da suffarsa? Waima ta ina yake shigowa anya kuwa? Tunaninta ne ya tsaya lokacin daya nufo inda take fuskar nan a hade dukda babu haske sosai a dakin
"Wato ke ba'a gaya miki sau daya ko I'm very sure kinga text dina tsabar raini ne yasa bakiyi ba" ya fada dai dai lokacin daya qarasa kusa da ita ya dago fuskarta da hannunsa yana haskata da flash din wayarsa. Bata tanka ba sema qoqarin kauda kanta data shigayi saboda wani kuka data ji yana neman taso mata.

Wannan wane irin bala'ne haka yake bibiyarta mutum ya ringa keta mata mutunchi yana shigo mata duk sanda yaga dama a duk lokacin daya so koma wacce irin shiga ce a jikinta. Seta saki kukan data kasa riqewa daidai lokacin daya jata zuwa cikin jijinsa, kuka take yi sosai me nuna zallar takaici da baqin ciki. Be hanata ba sema matsawa baya da yayi yana kallon yanda ta durqushe tana ci gaba da kukan kamar ranta ze fita, se kuma tausayinta ya kamashi, ya sakata kuka da yawa Infact tunda suka fara haduwa take kuka amma ai ita dince ta fiya raguwar zuciya shi kuma yana son mace jaruma.

A hankali ya qarasa ya dagota tareda hadeta da jikinsa yana bubbuga bayanta a hankali
"Saboda nace kimin girki shine abin kuka, to shikenan barshi na kwana da yunwa kinga kafin dare se na mutu kawai tunda ni bani da kowa mata ta bata nan bare ta kula dani gashi kuma Amaryata ba abinda ta iya se kuka"
Seta dago kanta da sauri ta kalleshi, shima ita yake kallo a qoqarin son goge maganar daya riga yayi seya miqe da ita a jikinsa ya shiga bedroom din, har kan gado ya ajiyeya yaja mata duvet tareda kashe mata bed side lamp din yai pecking nata a goshi da lips ya juya ya fita. Seta gagara baccin kwata kwata, wai Amaryarsa taji yace fa to kodai ya fara shaye shaye kuma? Haka ta ringa juyi tana tunani har bata san da bacci ya dauketa ba. Inda ta godewa Allah washe gari tana zuwa makaranta aka raba musu wani mini project kuma ba'a cikin London zasuyi ba. Wani qauye zasuje can kuma kwana goma zasuyi qarin jin dadinta group dinsu daya da Umm Ashrab. A hanya suna komawa gida suna tsara yanda tafiyar tasu zata kasance, suna tsaye kofar Apartment dinta suna magana ya shigo tayi masa kallo daya ta dauke kanta lokacin da suke gaisawa da Umm Asrab. Shima ita yake kallo ransa na quna, wato shigar daya hanata ita tayi ta saka riga da skirt na wani baqin leshi yamata kyau kamar Aljana ga daurin datayi ana hango gashinta haka bayanta duka a bude saboda mayafin ba wani na kirki bane. Tsaki yayi ya wuce su ya shige gidansa bam ya buga kofar kamar meyi da wani seta tabe baki yayinda Umm Ashrab ta kalli kofar ta kalleta

"Anty Hamdah anya kuwa" ta fada in between dariya dan ta dade tana spying akan Hamdah da Abdul'ahad din tun farkon dawowarsa ta lura da irin mu'amalarsu. Har Zulaiha tayiwa magana da farko taji tsoron kar yaudararta yakeyi amma se Zulaiha ta nuna mata bata zaton Hamdah da wannan halin kuma shima Mr Abdul'ahad beyi kama da mutumin banza ba kilan dai akwai wani boyayyen al'amari a tsakaninsu su zuba musu ido kawai zasu gane koma menene. Murmushi ita ma tayi batareda tace mata komai ba daga nan sukayi sallama ta shiga gida.

Sanda ya shigar mata kamar wani me gida ya shiga gidansa babu ko sallama se daddaga kai yakeyi, lokacin ta fito da kayayyakin da zata tafi dasu ta ajiye akan Couch tana amsa wata waya. Kallo daya ta

Please Login or Register in order to submit comment