Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya nunawa Isah zallar bacin ransa, se kawai ya kama kansa ya fita yin abinda yace dukda dolensa yayi delaying process din, ko sun tafi wahalar banza zasu sha baya tunanin zata qara 48hrs a duniya saboda zuciyarya ta fashe wannan ciwon ne ya farkar da ita a gigice dazu. Shi kam akan lamarinta ya qara jaddada qudira ta ubangiji be taba ganin wanda akayiwa dashen zuciya dayai tsahon rayuwa haka kamarta ba. Haka ya shiga tattara duk wasu abu dayasan zasu buqata yana jiran kota kwana.

Wani bacci ne ya kwashe shi ba tare da ya sani ba. Bacci ne dake cakude da wasu irin mafarkai marasa kyau sam, cikin haka yaji ana kiran sunansa da farko ya dauka duk cikin baccin ne seda yaji kiran kusada kunnensa sannan ya bude idonsa babu shiri. Rana ta fito dal da yake da tabbacin safiya tayi tuni, beyi sallah ba, agogo ya kalla bakwai harda minti hudu se ya maida kallonsa gadon da Ni'ima ke kwance wanda daga nan yaji ana kiransa.

"Yaya Abdul mutuwa zanyi" abinda ta iya fizgowa dakyar kenan ta gaya masa. Se ya shiga goge idonsa dakyau dan tabbatar da matar da ta kwashe tsahon wata biyu a sume ce ta ke magana. Tsabar murna besan sanda ya rungumeta ba yana kissing goshinta Ba tareda Hamdala tabar bakinsa ba.
"I knew it zaki tashi Ni'ima I Know u are strong u will live for me and my baby". Wani murmushi tayi dayafi kuka ciwo ganin yana qoqarin fita kiransu Ammi ta daga hannunta dakyar ta dora akan nasa

"Yah Abdul karka kira Umma, she won't bear to see me dying kawai kace ta yafemin kaji mutuwa zanyi" se ya koma jikinsa har rawa yake ya dago kanta ya zauna sannan ya mayar da kanta kan cinyarsa yana shafa kanta da gashin ya karkade shi se yanzu ma ya lura.

"Shiii zaki fara surutun ki ko kiyi shiru bari na kira Dr ina ke miki ciwo yanzu"

"Yah Abdul komai ciwo yakemin from head to toe, Yah Abdul ina little" se yaji nauyin yace mata tana gidan su Hamdah dan haka ya kama hannunta a hankali cikin nasa yayi shiru kawai. Ci gaba tayi da magana tana cewa

"Yah Abdul i have no regrets nasan ka samu farincikin ka ko bayan raina bazakayi kukan rashi na ba, nasan zata kula dakai. I wish mun qara haduwa ko sau daya ne na gode mata da kulawan data baka Yah Abdul kaga yanda kayi kyau kuwa" seta danyi shiru, Allah kadai yasan me take ji a lokacin sannan taci gaba

"Yah Abdul ga Amanar Little nan ka kula min da ita dan Allah" seya dora hannunsa akan lips dinta yace "karki kuma, Little yata ce baki da buqatar gayamin na kula da ita but still zanyi, zan kula da ita iyakan iyawata shikenan" kai ta gyada masa tana murmushi, se ya kwanatar da ita ya miqe yana cewa "bari nayi sallah time yana tafiya".

Zuciyarsa qal ya tada sallar bayan yayo alwala. Ya dade yana godewa Allah cikin sujjadarsa daya tashi kafadun Ni'ima, tana kwance tana binsa da kallo duk motsinsa. Tana son Abdul'ahad kamar ranta ita ma batasan sanda ta fara sonsa ba. Bayan ya idar da sallar ya bude qaramin qur'anin dake ajiye a kan drawer gefen gadon ya dawo inda take ya zauna tareda sake dora kanta a cinyarsa ya fara karantawa tunda ta hanashi kiran kowa ta e ya bari sedai kawai suga ta taka qafarta. Cikin nutsuwa yake karatun tana sauraronshi a hankali kuma se ta fara bi in ya karanta seta maimaita abinda ya qara sa shi farin ciki kenan, sunyi nisa a karatun yaji tayi shiru, ga kanta daya qara nauyi a jikinsa seya dan leqa fuskarta. Murmushi ya saki tareda gyara mata kwanciya sosai a fili yace

"Sleeping beauty, dukka mata na masu kyau ne musamman in suna bacci" daidai lokacin da Dr Isah abokin fadansa ya shigo yai masa kallo daya ya dauke kai tareda hade rai, shi kam da murmushinsa ya qarasa yana masa sannu da tambayar ya me jiki, seyai saurin dakatawa yana qara kallon computer dake gefen gadon, cikin taraddadin meze faru ya kalleshi kafin yace

"Abdul'ahad kai ka kashe computer nan?" Se ya kalleshi sheqeqe, wannan yama raina masa hankali amma beyi magana ba sema miqewa da yayi dan yana so yaje yayi wanka kuma tunda tayi bacci yai ficewarsa. A kofa yatarar da Ammi da Umma se Umar da alama zuwansa kenan. Gungun likitocin da suka nufo dakin ya matsawa suka shiga kaman an korosu yana qara hade rai

"Nifa Ammi zan chanza mata asibiti ne, ji yanda suke tara mutane suta jagwalgwala matan mutane".

"Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un Dr Isah wannan ai ta dade da rasuwa" kalma mafi muni kenan daya jiyo daga bakin daya daga cikin likitocin da suka shiga dakin ai besan sanda ya bangaje Umar dake kokarin shiga ba shima jin furucin likitan yayi nasarar wurgar da Dr Gadanya gefe dayake cire alluran dake jikin Ni'ima. Se ya tsaya amma ya kasa taba ta. "Innalillahi wa'inna ilahi raji'un, Allahumma ajirni fi musi bati wa'aklifni khairan minha" sukadai ya iya furtawa hannunsa har rawa yake ya shafa fuskar Ni'iman, seya waiwaya kamar me koyon magana yace

"Ammi Ni'ima Babu, Ni'ima ta tafi"

"Lokaci yayi ubangiji yasa karshen wahalarki kenan Ni'ima Allah ya gafarta miki" abinda Ammi ta iya fada kenan tana qoqarin danne hawayen dake shirin zubo mata.

"Kar kuyi mata kuka dan Allah, Allahn daya karbeta yafi mu sonta ci gaba da mata addu'a kamar yanda kuka fara insha Allah mutuwar hutu ce a gareta" Umman Ni'ima tayi maganar, ya tabbatar Umma karfin hali kawai take to shi a wa da baze haqura ba. Cikin mintina kalilan mutuwar Ni'ima Mustafa ta karade birnin kano da kewaye, Yar gidan Senator Mustafa Isma'il matar Dr Abdul'ahad Abdullahi Galadima. Shi da Umar ne a cikin Ambulance din da aka sako gawarta straight gidansu aka tafi da ita kamar yanda Yarima Abdullahi Wato Baban Abdul'ahad ya bada Umarni. A dakinta akayi mata wanka tareda sutura kaman yanda addinin musulunchi ya tanadar.

Ta samu rakiyar mutane da dama wanda har mamaki yayi saboda yanda sakon mutuwar ya fita cikin qurarren lokaci amma duk da haka tayi Jama'a na ban mamaki. Seda aka sakata a rami ya dibi kasa ya zuba masa sannan hawaye suka balle masa, shikenan ya rasa matarsa uwar yarsa, mace me sonsa da tausayinsa me tsananin yi masa biyayya.

"Allah ya jiqanki ya gafarta miki Ni'ima, in dai nine muqullin aljannarki na baki a hannunki ki bude ki shiga ubangiji ya sadaki da sunanki a cikin kabarinki Allah ya raya abinda kika bari" se ya kasa danne kukan dole ya fita daga makabartar ya samu guri shi kadai ya ringa gunshekar kuka dukda bame sauti bane. Be taba zaton yan son Ni'ima ba seyau da tayi masa nisa na har abada. Har aka gama komai mutane suka watse yana zaune a gurin seda Alhaji Mustafa da kansa ya daga shi suka tafi gida tukunna.

Daidai wannan lokacin Hamdah Ammani tana zaune gaban Dr zahra tana jiran sakamakon gwajin da aka mata. Tun sassafe ta tafi asibiti dan tace bata yarda da wancan strip dinba dan haka tazo aka dauki jininta da fitsari, "As expected Mrs Hamdah kinada ciki har tsahon wata uku" Dr zahra dake duba farar takardar ta dago tana mata bayani.

"Dr ban yarda ba inaga kuma dai kun samu matsalan na'ura ne ko?" Tayi maganar cikin zallar kidima. Wata uku, ciki har na wata uku nan da six months kenan zata haihu takaiwa Abbah Doctoring Degree biyu kenan,
"So in kinaso ki tabbatar muje na miki scanning ki gani da idonki" cewar Dr Zahra a ranta tana mamakin wauta irin ta Hamdah. To aiko makaho ya shafata yasan me ciki ce. Bata musa ba ta kwanat akan gadon da ta nuna mata nan ta shiga mata scanning din.

Allah buwayi, sega da ko yar Abdul'ahad Galadima kwance a cikin Hamdah, kuka wiwi take yi dukda yanda taso ta danne shi ita ya zatayi??
"Ki zubar kawai" wata zuciyar ta raya mata. Ashe bata da bambanci da Abdurrahman kenan inda zata samu ciki ta zubar data sani ta zauna da auransa kawai da batayi cikin shege ba. Ledar magungunan da aka bata ta dauka tana tafe tana kuka duk inda ta wuce se abita da kallo zaton wasu ko mutuwa aka mata har suna mata Allah ya jikan rai. Tunani take yanda zatayi reaching Abdul'ahad da ko number sa bata da ita, dakyar ta iya kai kanta gida ta zube a palour tana ci gaba da kuka. envelope din daya bata ranar da ze tafi ce ta fado mata arai, tana cikin bedside drawer dinta dan tana dawowa ta saka ta a ciki seta miqe har tana faduwa tsabar sauri ta zarota ta zazzage tulin kudaden ciki Allah ya taimaketa sega complementary card dinsa ya fado. Hannunta na rawa ta shiga rubuta number shi ta Nigeria dake rubuce akai tana addu'ar Allah yasa ta shiga bugu daya kuwa ta fara ringing daya, biyu aka daga

Cikin muryar tashin hankali ta shiga magana "Abdul'ahad ko ina kake ka dawo munshiga uku mun lalace........."






🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

*RUBUTACCIYAR QADDARAH*

🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

*By Maryamah* 💞💞
©2020

*PAGE* 4⃣6⃣


Hannaye biyu yasa ya dafe kansa kafin ya miqe duk da jirin dake neman kadashi. Yana jin yanda take rusa kuka a wayar tana maimaita ta shiga uku ta lalace, seya kalli Fahad dake tambayarsa ina zashi ya masa alamar yana zuwa. Can gefe in da babu kowa nesa da yan karbar gaisuwar ya samu ya zauna kansa yana sara masa ba kadan ba. Idanunsa da suka masa nauyi a lumshe yana jinta har lokacin bata bar kukan ba. Gajiya yayi kuma bata da alamun yin shiru yasa ya bude baki yace

"Naji amma ke kadai kika shiga ukun yanzu dai meya faru keda baki da aikinyi se tayarwa da mutane hankali" yayi maganar a nutse cikin kwantaccen sauti, seta dakata da kukan kamar anyi ruwa an dauke. Lallai ma wannan yaci uwar rainin wayo wato ita kadai ta shiga uku? Ai kuwa ya tabowa kansa ya hadu da kwalba uwar sharri, seta sa hannunta ta goge hawayen da suke zubo mata tace

"Ni na shiga uku ni kadai ko, ok nayarda amma ka sani taka na zuwa ranar dana haife Dan shegenka na kawo shi gidan ku inda ake maka kallon mutumin kirki gurin matar taka daka tafi gurinta ka barni, ranar ni da kai se muga wanda ya shiga uku, koda yake tsaya bazan yi haka ba, kenan ma na qulla alaqa dakai tunda mun hada iri, bari kawai zan zubar dashi se nazo na musu bayanin irin zaman da mukayi nidakai a London, mtsw kashe wayar tare dayin jifa da ita a bango ta kuwa tarwatse nan take. Safa da marwa ta shigayi cikin dakin, ko kadan ita bata jiyo rauni da kuma damuwar da take a cikin muryarsa ba sema Izza da taqama kawai zuciyarta ta kitsa mata. Wato ya shanye mangwaro ya yada kwallonsa ko? Ya gudu ya barta to wallahi yayi kadan. Bazata daukarwa kanta zunubi biyu ba gana Zina gana kisan kai kuma Bazata fuskanci wannan abin kunyar ita kadai ba, zata raini cikin nan kawai ta haifeshi duk duniyar da yake seta iske shi ta kai masa daga nan ta yanke duk wata alaqa dake tsakaninta dashi. Ta yanda baze sameta ba bare ma ya liqa mata dan. Seta sake fashewa da wani kukan, ta yaya zata raini ciki har wata tara ta haife ba tare da wani ya sani ba? Kodai gurin zama zata canza ita yanzu tacewa su Zulaiha me? Anya bazata bar London ba ta koma wata qasar ta yanke communication da kowa har se randa ta haihu?

'Idan kika gujewa mutane ubangijinki kuma dayake kallonki a ko ina ya zakiyi dashi, zaki iya boye laifinki a idon mutane amma a gurin Allah fa?? Kenan ma kin zabi jin kunyar lahira akan ta duniya kenan?" Zuciyarta ce ta lissafo mata wadannan tunannen, seta durqushe a gurin tareda sakin sabon kuka me cike da dana sani da Nadamar da bata da amfani a cewarta. Shedan ya rudeta takai kanta ta baro. Dama wannan itace illar zaman mace ita kadai da mutane da yawa suka kasa fuskanta, iyaye suke daukar yayansu mata ko maza su kaisu wata uwa duniya su samar musu da duk wani jin dadi da sunan karatu basu san me hakan ze iya janyowa ba. Bazata ce duka ba amma ita kanta yanzu misali ce, nata iyayen sun yarda da ita a matsayinta na bazawara sun turata har London karatu ta zauna ita daya ba qarqashin kowa ba yanzu ga sakamakon data yo musu, ta biyewa so ta cuci kanta dan ba iyayenta ta cuta ba.

"Allah sarki Abbah, Mumy ku yafemin I failed you, i break ur trust i know you won't be able to forgive me for this" kalaman Abba na nasiha da yake mata kullum akan kamun kai ta tuna. Maganar sa kenan ta tsare mutuncinta kar taganta inda bata da kowa ta canza daga Hamdar sa zuwa wata daban gashi yanzu ta masa babban tukuici da cikin shege, Aman daya taso mata ne ya tsaida tunanin da kukan, nan ta shiga sheqashi babu ji babu gani. Ta jigata kwarai jikinta yayi laushi seta kwanata a gurin kawai tana maida numfashi tareda kiran sunan Allah tasan shi kadai ze kawo mata dauki a wannan lokacin, inama ta mutu kawai ta huta da wanna abin kunyar...

Nigeria

Wayar ya cire daga kunnensa ya kalla nan ya tabbatar da tayi hanging. "Idan na haife maka dan SHEGE na kawowa matar taka da ka tafi gurinta ka barni ranar se muga wane ya shiga uku tsakanina dakai" kalaman suke masa yawo akai, "SHEGE" ya qara maimaita kalmar, could it be ciki ne da ita?? Seya miqe kamar wanda aka ma allura ya shiga neman number ta, idan har da gaske ne dole ya taka mata burki, tsaf yasan Hamdah tana iya masa ganganci da ciki dole ya nutsar da ita ta koma taitayinta. Tsabar yanda ya rude bema gane wayar a kashe take a keta gaya masa ba seda ya kira kusan sau goma sannan ya gane. Jifa yai da wayar daidai lokacin da Fahad ya qaraso yai nasarar cafketa dan tun dazu yake lura da yanda yake ta zarya shi kadai.

Dafashi yayi ganin yanda yake huci yace "Abdul'ahad meya faru" seya fizge daga riqon da Fahad ya masa ya nufi gate yana cewa "I need to go back to London today or tomorrow" seya bishi da sauri cike da mamakin meke damunsa, mutumin dake cikin jimamin mutuwar matar sa jiya jiya me ya taso masa daya fi wannan muhimmanci a London din "Hamdah's issue" zuciyarsa ta raya masa seya qara sauri ya cimmasa lokacin har ya tsayar da Keke Napep ya shiga abinda be taba gani da Abdul'ahad ba tunda yake, se shima kawai ya fada suka fara tafiya.

"Fahad could you imagine she called my son or daughter SHEGE, wai zata zubar min da cikina saboda bata da hankali". Fahad yasan za'a runa, se ya cewa me Napep din ya dan tsaya zasuyi magana ya gangara titi yayi parking tareda fita ya basu guri, kwantar da murya yayi yana dan murmushi yace
"Imagine naje California aiki shekarata daya acan banzo gida ba, se kawai yanzu dana dawo Kano sena tarar da Ummi (yana nufin matarsa) da ciki wata tara tsahon shekara guda bama tare meye ze zo zuciyata"?? Kallon Abdul'ahad yake yana jiran amsar shi, kaman me koyon magana yace

"Ba cikin ka bane zaka tambayi a ina ta samo shi"
"Very good, same applied to your case, a sanin Hamdah bata da aure, ko batayi tarayya da Namiji ba kawai ta farka daga bacci taganta da ciki tasan bata aure ta same shi ba kuma duk wanda ya ganta da cikin same tunanin dazeyi kenan dan haka be soft with her, abunda nata qoqarin nuna maka kenan akan rashin amfanin boye mata auran ku amma kaqi, in duniya zata taru yanzu kallon mayaudari take maka ka cuceta ka dirka mata ciki kuma ka gudu ka barta dan haka karma kaga laifinta ka nemi hanyar da zaka wanke kanka kawai and Don't even think of involving any body kai ka kwaba abinka kai zaka gyara, ka kirata ka lallabata akan ta bari kazo se kusan abinyi kafinnan an gama zaman makoki kana iya tafiya ko ina amma yanzu bakayiwa Ni'ima adalci ba idan har ka tsallake ka tafi, ka nuna mata halin ko in kula tana raye yanzu ta tafin ma bata tsira ba".

Gaba daya se kalaman Fahad suka sanyaya masa jiki, tabbas yayi kuskure inda tun farko an gaya mata kaman yadda Abbanta yace da ba'azo nan ba, beyi magana ba har Fahad ya bawa me Napep din umarnin ya maidasu in da ya dakko su haka ya sauka ya shiga gidan jikinsa duk a sanyaye. Duk wanda ya kalleshi se ya zata mutuwar ce ke dukansa har yanzu amma shi abun biyu ne, yasan Ni'ima ta tafi har abada addu'a kawai ze bita da ita amma wannan fitinanniyar daya baro A London ita tafi daga masa hankali, ya rasa ya zeyi gashi baya samun wayarta, Master da ze iya turawa ya duba masa ita dan shi kadai ya yarda yaganta akaf abokansa na London kuma ya taho Nigeria tun ranar kwana uku shima da wasu daga friends dinsa sun zo masa gaisuwa, ya yanke shawarar kawai yabi ta Fahad din idan komai ya lafa ya je suyi duk wacce zasuyi amma ita zata jirashi har tsahon wata daya ba tareda ta aiwatar da abinda ta fada ba??

Kaf yan gidansu Hamdah da duk wanda ya shafeta yazo masa gaisuwa har lokacin little tana gidan sedai kullum suzo da Mumcy su wuni su koma da daddare da alama bata masan wainar da ake toyawa ba, data tambayeshi ina Mummy kasa bata amsa yayi se Ammi ce tace mata ta koma China tunda ita ta zama yar Nigeria yarinyar bata wani damu ba kuwa tace zata bi Dady in ze tafi lokacin Aunt Berbie tazo se su tafi tare. Haka aka share zaman makokin Ni'ima kamar yanda addini ya tanadar ranar kwana goma da rasuwarta wanda kuma ranat duk wasu belongings nata dake gidansa na China suka iso da yake yasa an tattaro masa komai, suka hada da na Nigeria akayi rabon gado kaman yanda addini ya tsara. Duk kadarorin Ni'ima kyaututtukane wanda Babanta ya mata dashi kansa Abdul'ahad din se kuma kayayyakin ta na sakawa da jeweries se motar hawanta guda daya da kudi a account. Da nasa dana little shi aka bawa, ranar yayi kukan da be zaci ze yi wa mutuwar wata mace ba. Haka aka watse Ni'ima ta zama tarihi.

One month later

Yana tsaye cikin dakinsu ada shida Ni'ima daya zama nashi shi kadai yanzu. Tun bayan rasuwarta be qara zama a dakin ba seyau da yake so ya dauki wasu ta kaddu a cikin. Airpod maqale a kunnensa yana duba I watch, tun dazu yake kiran number amma bata shiga. Takaddun ya dauka da passport dinsa har lokacin be gaji da kiran ta ba. Wata daya kenan tun bayan rasuwar Ni'ima, bata qara kiransa ba tun waccen ranar haka shima. Ya dai saka mata matakan tsaro yana sane da duk shige da ficenta. Duk wani asibiti dayasan tana zuwa seda ya kira ya kuma buga musu warning da babbar murya na su shirya shiga kotu duk ranar da wani abu ya samu cikin jikin Matarsa dan he believes bata da kai wannan zuciyar tata tana iya kaita ta cire masa ciki tunda ta fada. Tsaki yayi daidai sanda ya zauna akan couch a palour Ammi,

"Babana lafiya kai dawa kake tsaki?" Ammi ta tambayeshi. Seda ya shafa kansa kafin yace

"Ammi Hamdah ce, ta kashe wayarta for almost a month bana samunta".
Seda tayi yar dariya sannan tace "Amarya bata laifi ai kilan dai sarautar ce ta motsa ko, ni wai se yaushe zaka kawo mana yarinyar nan ne dai tunda ta Allah ta kasance akan Ni'ima ya kamata kuma ita wannan ka dawo da ita ai hada su ne baka so to Allah ya raba maka da kanshi" miqewa yayi ya fara tafiya yana cewa

"Ammi gobe nake so na koma daman, batasan da auran mu ba haryanzu bazan dakkota tazo tayi ta wa mutane shirme ba and kafin na tafi inaso a dakko little daga can gidan a kaiwa Umma ita, nasan kawai ci tayi amma zata so ta karbeta a madadin Ni'ima" se Ammi ta saki baki tana kallonsa.

"Wato Babana gobe zaka koma London badan na maka maganar ba sedai na nemeka na rasa ko kuma se zaka tafi sannan zakamin sallama" tayi maganar cikin sigar tuhuma.

"Ammi da Baba zamu tafi a Private Jet dinsa i thought ma ya gaya miki" seta masa daquwa "ungo nan Ja'iri shi Baban dan aiken kane ko yaya har ina murna ka chanza hali ashe abu gaba yayi ai wallai Aishan ma ita ce daidai dakai (da yake Aysha take kiran Hamdah sunanta na gaskiya) mutum se shegen miskilanci uwarsa ma se ya mata"

"To dama a gurin wa ya gado in ba fulani ba" Baba da shigowarsa kenan ya tarar tana cashewa dan lelen nasa ya katseta, seta juya tana hararar sa da wasa tace "Dama Baba ai kai ka daure masa qafafu yakewa mutane iya shege, in ba haka ba ya aje mata sama da wata shida bata san da auransa akanta ba....."

"To ya gaya miki uzurinsa yace matarnan kunnen qashi ne da ita irin nasa se ya tabbatar ya mata ciki sannan ze bari tasan da auran in ba haka ba bore zata masa a karo na uku" Baba yayi maganar yana yar dariya da tuna wani lokaci. Kunya kamar Abdul'ahad ya nutse a gurin ita kanta Ammi seda ta dauke kai tana dan murmushi tuna baya. Katobarar da aikata a baya a lokacin daya tasa Baba a gaba sukaje neman Auran Hamdah yace masa wai Prof Ammani ya bawa wani auran Hamdah a karo na uku bashi ba, a lokacin rudu da tashin hankalin da yake ciki suka rufe masa ido ya manta dawa yake magana. Ga Baba, ga Prof Ammin da qannen babansa da nata da Baffa da Abubakar duk a zaune ya miqe tsaye yace "Wallahi sena aureta kuma inna dauketa bazaku sake ganinmu ba sena tabbata na mata ciki yanda babu wanda ya isa ya qara rabamu" yai ficewarsa, shidai yasan washe gari dama ta kama friday kawai Fahad ya kawo masa sabuwar Shadda fara qal yace ya saka, ana sakkowa masallaci aka daura auransa da Hamdah, auran daya kafa tarihi har yau yana mamakin a yaushe aka gayyato jama'ar da suka halarci wannan daurin auran da ba'a taba makamanci sa a Kaf Kano ba. Abinda be sani ba tun ranar da Abbah ya karbi takardar sakin Hamdah Yarima Abdullahi yakai sadakin auran dansa Abdul'ahad saboda babu iddar Abdurrahman akanta.
Da yardarsa ta tafi London karatu duk cikin plan ne da shi Yarima Abdullahi da Prof Ammani suka shirya.

Shafa kansa ya shigayi ya fara tafiya dan barin palour Baba ya qara tsareshi, "ranka ya dade ina fatan ka cika rantsuwarka ko dan nidai tuni na fara lissafi nasa an fara kiwata ragunan suna ma guda hudu na siya dan nasan kilan yan hudu ka dasa ko" ai da gudu kamar yaro ya fice yana dariya. Ammi ta kalli Baba da shima dariyar yake tace
"Baba kamaida Galadima kamar abokin wasanka dai" seda ya zauna a kusa da ita sannan yace "fulani to so kike na barshi damuwa ta masa illah, ki godewa Allah danki jarumi ne, baki san meyake undergoing ba ganinsa kawai kikeyi"

"Yanzu goben zaku tafi kenan" ta chanza akalar maganar

"InshaAllahu, kina da saqo ne ko zaki bimu" seta girgiza kai Alamar Aa sannan tace " Yace a dakko Aisha qarama akaiwa Habiba ni kuma nasan wannan yar ba yarda zatayi ba, gara ya barta kawai a hannun Maryam din tunda su suka dauketa dakansu kar suga kaman an nuna banbanci ko har zuwa sanda dayar maman tata zata dawo nasan ko minti bazata yarda ta qara a wani guri

Please Login or Register in order to submit comment